← Book details Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 87

Sashe 86

Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

uku ni rafiah yau kadarina ya karye! Yau asirina ya karye, yanzu yazanyi ina bokana! Ina bokayena! Nashiga uku! Ta fasa ihu zata cacimo Alhaji sunusi Aeezad ya fado falon tini ta dakata, ganin uban sojoji sun cika falon. daman kafin ya karaso ya kirawo motocin sojoji sunfi motocin daza a tsaya kirgawa,, suka shigo gidan, kusan sojoji hamsin suka shigo falon, guda Dari biyu suka zagaye gidan, Dari biyu kuma a wajen gidan. Aeezad ya musu izini su kama hajiya mommy da Naeema, Alhaji sunusi ya sakar dashi yace A barsu base an musu komi ba duniya ma ta ishesu Aeezad yaji haushi yaso ya kamasu dase sun karasa rayuwarsu a kurkuku. Alhaji sunusi kuka kawai yakeyi yayi nadamar Auren hajiya mommy a lokavin da babu Amfani, daman yaga komi daya kuma Tana kullawa A CCTV camera din dake gidan be taba gani ba se jiya, aiko bacci sede barawo yaga tashin hnkli daman kiris yake jira kawai ya saketa. Aeezad ya cacimo naeema ya fara bugu yana nishi yana fadin Kisan Kai! Mu zaku kashe! Yau nine ajalinku! ya hadasu da hajiya rafiah ya Kama bugu kmr ransa ze fita sbda tashin hankali. Alhaji sunusi yayi yayi ya dakatar dashi amma ya kasa, seda ya musu lilis, kana da kyar sojojin duka dagasa daga kansu, seda kaf ya canza musu kamanni, hakoran robar dake bakin hajiya kaf ya zubar mata dasu, kwance kawai ya barsu. Yace ya saki naeema saki uku. Ze kara ci gaba da dukansu Alhaji sunusi yasa sojoji suka rikesa suka kaisa gidansa. Kwashe su hajiya rafiah da naeema akayi kmr kayan wanki aka zuba a mota da kyar, alhaji sunusi tabi motar a baya har gidansu hajiya rafiah aka kaisu, aka zubesu a kn tantagaryar sumintin dake dakinsu,. Alhaji sunusi ya shaida musu komi daya faru. Nan mahaifiyar rafiah tasaka kuka, mahaifinta ma yasaka kuka sam basuka Laifin abinda akama rafiah ba, sema godiya sukama Alhaji sunusi, suka dinga basa hakuri. Alhaji sunusi ya basu dubu Dari yace a kaisu asibiti ya bar gidan a mota ma kuka ya dingayi. Direct ya nufa gidansu Aeezad a gidan ya tadda Aeezad se huci yakeyi a falo yana kwallah, kowa ma kwallah yakeyi sbda da ynzu suna lahira . A ranar aka sallami lantana A Aiki aka bata kudi kimanin 1M aka kaita har kauyensu, sam nabeelsh bataso haka ba, taso zama da lantana Alhaji sunusi da Aeezad suka ki. Ranar de haka kowa ya kwana basuci komi ba se Alhini akeyi a gidan sunata godewa Allah, washe gari aka tara maaikatan gidan aka musu natsiha, kan su rike amana, su maida gidan tamkar nasu karsu yadda subar wani abu ya cuci duk halittar dake gidan, wad danda ba a yadda dasu ba tini aka koresu aka kawo wasu daga company ba locals ba. After 1week komi ya fara natsawa Alhaji sunusi ya samu big hajiya da labarin yanasan ya Auri ummih, inta amince, in itama Ummihn ta amince. Farin cikin da big hajiya ta shiga baze misaltuba ta rangada kuda, aka shaidawa Kowa ma gidan nabeelah taji ddh sosai, ba kmr Aeezad yafi kowa Jin dadih. Aka nemi yardar ummih tayi shiru kunya ta rufeta, amma fuskarta ta bayyana amincewarta. Kowa yayi farin ciki a satin akaje Nemo aurenta A Niger , dayake anji kudi tini kowa na danginta suka bayyana , aka daura Aure ba bata lokaci Alhaji sunusi, after 2days bayan sun dawo Nigeria Alhaji sunusi ya fara ciko Cikon yima ummih passport , domin su bar kasar zuwa India a duba lafiyarta sosai daga can su wuce honeymoon. Ummih ta rokesa ya bari se bayan anyi bikin Zaks da Dr salmah se su tafi. Domin ynzu haka bikin befi saura 2weeks ba. Hajiya rafiah da yarta kam tini aka kaisu asibitin gwamnati tin randa Alhaji sunusi ya kawo su, aka samu suka farfado amma sede duk sunada kayaya a jiki, kwara na naeema a hannu ne, na hajiya mommy a kafafuwa ne Gashi ba hakori a baki, Gashi ba isashen kudin daze isa a dubasu sosai ga can gidanma ba abinci. Naeema tayi nadama, nadama mara amfani tayi kuka iya kuka. Tace da uwarta Duk ke kk cuceni mommy, kika hanani na haihu a gidan Aeezad, kika hanani karatu me zurfi, kika hanani zaman Aurena, kika koyamin bin bokaye,,, wlhi nayi nadamar da kikazo a uwata ta fashe da kuka wanda takesa ran harta mutu kukan zatayi tayi. Hajiya mommy kam sede ta rufeta da zagi da tsinuwa, brain dinta ya tabu, likitoci sun tabbatar data samu tabun hankali kadan a cikin kwakwalwarta, wuni take ta kwana Tana zancen Alhaji sunusi. Naeema tayi kuka, kukan mara amfani. Ana haka Suka samu labarin Auren Alhaji sunusi da mahaifiyar nabeelah, Nan take hajiya mommy ta Kuma hauka tuburan ta fita aguje ta hau titi mota ta bigeta, Nan take ta rasa kaf kafafuwanta gashi me motan Daya bigeta ya gudu, seda akasa taimakon masallaci aka samu aka biya kudin aiki aka yankewa hajiya mommy kaf kafafuwanta. Khady tazo ta dubasa a tsaitsaye ta basu dubu hamsin. hajiya naja'atu taxo gaidasu a asibitin sbda ta samu Labarin komi ta Basu kudi dubu Dari biyu, ta tausaya ainun. Hajiya naja'atu tabar asibitin tana Alhinin rayuwa, wato de duk me aikata Alkhairi baya lasting dole akwai ranar kin dillanci ynzu tin a duniya suke ganin ishara, base an mutu ba tin a duniya Ake hisabi, Su Fir'Auna ma tin a duniya ubangiji ya nuna musu ishara, komi zakayi ka aikata Alkhairi karka sake ka zalinci Wani, ubangiji baya zalinci tabbas kuma baya barin me zalinci. Hajiya mommy bata warke ba aka sallamesu saboda Basu da kudi, haka suka dawo gidan nanma abincin daza suci ya same musu matsifa, kawai sede suka koma bara kasuwanni kasuwanni, hajiya mommy na kan kujerar kuragu na'eema ke turata suna bara, sede yanzu ba Uhm ba Em bata magana bakinta ko motsi beyi haukar nata yazo mata da rashin magana, Amma tuburan take, gashi bata iya cin komi se Tea takesha kadan, duk sun chnza kamanni se uban kasusuwa a jikinsu, Wanda yasansuma inya gansu baya ganesu, sunsha haduwa da Aeezad inyaxo wucewa ya Basu sadaka sede Sam baya ganesu Amma su suna ganesa, duk sadda na'eema ta gansa se tayi kuka ta ciza yatsa, haushin uwarta seya rufeta, duk ita taja mata , yanzu de basu ga tsuntsu basu ga tarko! Maza nata fitowa zasu auri naeema dasun samu labari su sesu gudu, yanzu ko kuda bayasan tabata, uwar kibarnan dukta zazzage ga wani mugun duhu tayi, nonuwanta sun kuma ragargajewa, abinde ba dadinji ba dadin gani. Zaks kam sede yaji komi daga baya, yayi Alhinin Shima sosai , Kaf family ma sunyi Alhini har zuwa musu Allah kyauta akeyi, har ynzu sun kasa mance abinda ya faru, a kullum se big hajiya tayima hajiya mommy da na'eema Allah ya isa. Anyi bikin Dr salmah da Zaks , ta tare a sabon gidanta dake cikin garin kano akasha amarci ta kara kame Zaks sosai da kayan gyaran datasha, ynzu Kam yadena Neman matan. Baban Noor ma ubangiji ya shiryesa, saboda yaga ishara ga wani abokinsa mayen mata garin ciye ciye Gindi yaje ya ciyo gindin me HIV da ciwon hanta, at the ending sede mutuwa yayi bayan yasha jinya. , Amma sede ya kara Aure ya Samo wata bazawara ya Aura, Aunty hafsat ta damu a fari Amma seta daure, ta zage gun gyaran jiki, seya zamana ma hankalin mijin nata yafi karkata gareta ynzu tana gyara sosai bata wasa, kuka tana masa style's iri iri a sex akasin ada dase yadda ya juyata, bazawarar daya Auro daman bata haihuwa dan haka suka hada Kai suka rungume su Noor da Nasmah. Komi na ummih ya kammala suka shirya tsaf zasu bar kasar Kaf dangi aka hadu aka rakosu Airport a hanya suka hadu da na'eema da hajiya mommy se sukaji tausayi suka tsaya basu sadaka badan sun gane suba, seda suka gama Basu sadakar zasu juya Zuwa motocinsu se na'eema ta kalli Aeezad tace "Aeezad nice na'eema baka ganeni ba..." Seda kowa ya juyo aka zubo musu Ido se ynzu kowa ya ganesu. Duk seda suka tausaya musu suka kara Basu sadaka suka shiga mota sukayi wucewarsu kowa zuciyarsa ba ddh ganin isharar data saukarma Hajiya mommy da Na'eema. Big Hajiya kanta ta tausaya. naeema ta fashe da kuka, hajiya mommy ma ta fashe da kuka, a wannan karan har ita hajiya mommy tayi nadamar a zuciyarta dukda tana cikin hauka,. Karshen su hajiya mommy da na'eema a yawon bara suka kare, in suka fito tin safe se dare suke komawa gida, mu guji aikata sharri wlhi shi d'an aike ne. Alhaji rabi u da tawagarsa ma a kurkuku suka kare, ga aiki ke tsanani. Ba a sharri aga Alkhairi ai komi kayi shi ze dawo gareka haka tsarin yake ga ubangijin da baya bacci, in ana zalintarka kayi hkri wlhi da sannu ubangiji ze maka sakayya, kaide karka cuci kowa. Ummih da Alhaji Sunusi de tini suka isa india aka duba lafiyarta already Daman ta kusa warkewa, abinka da kudi Nan aka daurata a kn magani ta warke a cikin 1month ya zamana Se abinda baza a rasa ba,. Suka bar kasar suka shiga zagayen kasashe suna barje amarcinsu, already de Alhaji Sunusi yasan ummih bazata haihu ba, zuciyarsa da hankalina na kan jokokinsa, duk abinda ya gani na yara seya siya musu kullum cikin video call suke dasu,. A lokaci kankani ummih ta murje tasamu Hutu da lafiyayyiyar bura, Maniyyi kawai ke ratsata Tako ina, ta kuma kyau daka ganta Hutu kawai zaka gani a jikinta. A bangaren Aeezad Kam liyafa taci gaba, ya tattara iyalensa suka dawo garin Kano, ba jimawa ya samu Karin girma a Aikinsa, Tako Ina Arziki keta tinkarosu, nabeelah nata daurasa a hanya Yana taimako sosai. Itama nabeelah Arziki yaci uban nada, business dinta ya bunkasa sosai ta fara da hannun dama. A gaskiya ba abinda Aeezad zece da ubangiji se godiya, daze bawa mazan duniya shawara dayace su dinga Auran wad'anda suka girmesu a shegaru sunfi dadih Kuma sunfi iya tarairaya namiji. After 3yrs farin ciki ya kuma yalwata ga iyalan Tako Ina, Dr salmah ta haifa namiji a haihuwar farko shekarun yaran
Chapter 86 · 0% Book details