Sashe 16
Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jikin wata diya mace ba. Lallausar hannunsa yakai ya dauki bolt din dake kan trea din wanda ke rufe da murfi fari irin wanda ake hango abinda ke ciki ya ajiye murfin a gefen trea din, nan da Nan kamshin fruits din ya kara bugun hancinsa ashe da ba kamshi yakeji ba, yaji madara sosai ko a ido kasan dole ma yayi dadih, Allah Allah yadingayi ya dauko spoon ya fara diba ya kai bakinsa, sbda dadih seda ya lumshe Ido, Duk duniya ba wanda ya iya hada fruits din dayakeso kamar ita ko Wani ya hada masa baya masa dadih kmr yadda in ita ta hada masa. A cikin lokaci kankani yagama shanye fruits din tass be bar komi a cikin bolt dinba daman ya mance when wani abu yashiga cikinsa tinda yadawo garin katsinar se tea kawai yakesha Daya gaji dashan tea din yadena Sha ma gabaki daya, tin jiya Wani Abu be shiga cikinsa ba se yanzu. Daukar trea din yayi ya nufa kitching din, byn yagama,, tana tsaye tana Karasa hada abincin dare, ya danno Kai, tanajin shigowarsa tayi kmr bata jiba, ya tsaya ya kureta da ido, in Yana kallonta Wani irin shaukin soyayyar uwa ke kwasarsa a kanta. Juyowa tayi taga Yana kallonta ta dauke idanuwanta a kansa Hadi daci gaba da zuba farar shinkafa A warmer. Ya ajiye trea din a gun wanke wanke, Yana cewa. "Mommy wai yanzu kin dawo Nan kenan bazaki koma gidan hajiya mommy ba, tin haihuwar nasmah dakikazo baki koma ba kusan 2yrs kenan fa..." Tanajinsa tayi masa banza, ta kula kawai so yakeyi ta masa mgna shiyasa yakawo wannan tsohon zancan. Jin bata bashi amsa ba yabawa kansa amsa da kansa. "Ni kwarama karki koma gidan mommy nafisanki a wannan gidan Nafijin dadih..." Duk tana jinsa ta masa banza, ya karaso yana kokarin rungumeta ta baya, ta matsa dasauri hadi dacewa. "kanaso ranka ya baci kou?" Cikin fushi tayi mgnr. Murmushi Aeezad yayi daman kawai So yakeyi Tayi masa magana kuma tayi, shifa ko fushi takeyi kyau take masa kuma dadih yakeji. "Aah banaso raina ya baci ba..."cikin kwaikwayon maganarta yayi mgnr. Dariya taso subuce mata Amma ta dake tace "bade kace Kai baka da kunya ba, duk abinda banso shi kakeyi kou toh muzuba Mugani..." Ta karashe dajan kwafa taci gaba da aikin gabanta,. Kama kunne Aeezad yayi yace "Kiyi hakuri bazan karaba mommy,,,tinda ba halin in fadi inaso inci gindi kawai banso inci gindi nadena Allah baki hakuri,..." "Fita kabar kichin dinnan!" Ta fadi Hadi da juyowa, ya kalli fuskarta yaga ta hadeta gam, Dan haka yace ''toh bari in fita se injiraki a falo in kikazo ma karasa mgna a kan yaza ayi insamu gindin dazan dinga ci..." Yana gama fadar hakan ya fice a guje daga kitching din,girgiza kai kawai nabeelah tayi. "Allah shirya..." Tafadi hadi daci gaba da Aikin gabanta tana me kallon time. Yana fitowa falon yaci karo da Aunty hafsat, sanye da rigar abaya doguwa ce ita tanada kyau sosai, kallo daya namata naga kamanninta sak da Aeezad sedeshi yafita kyau nesa ba kusa ba. "Ahhh lallai yau uban babane a gidan nawa, ..." Aunty hafsa tafadi tana washe baki, tana karasowa cikin falon tazauna me aikinta na bayanta yayinda take rike da Asmah Noor kuma ta kama masa hannu, yarsn kyawawa ne sosai , kmrsu daya da mahaifiyarsa kmr a sace, sanye suke da uniform. Karowa Aeezad yayi yazauna shima yana murmushi idansa nakan yaran, a guje Noor yakaraso yarungumesa yana fading "uncul uncul .." Aeezad ya rungum yaron cikin jin dadih idonsa nakan Asmah wadda ta zamo daga jikin Salma me Aiki ta rugo aguje ta fado jikin Aeezad ya hadasu da Noor ya rungumesu kwarai a kirjinsa se dariya yakeyi kamar Wani Wawa, a rayuwarsa yana matsifar azabar San yara, lokuta da dama har mafarki yakeyi ya haifa yara masu yawa kamar 30 haka sunzo sun zagayesa, duk ranar dayayi mafarkinnan seyayi sadaka, a kullum se yayi adduarh Allah yabasa yara masu yawa shifa ko guda hamsin ze haifa yanaso, su biyu ne a gurin mahaifinsa, dagashi se yayarshi Aeezad, shi yanada. Shaawar tara zuri'ah sosai. "Ina sanku yarana..." Yafadi Yana me kissing kan kowannensu, zuciyarsa fall da zallar san yaran a ransa se Adduarh yakeyi shima Allah yanuna masa randa zega gudan jininsa ya rungumesu a jikinsa. "Ina wuni uncul ..." Cewar salmah me Aiki data tsugunna har kasa ta gaidasa amsawa yayi fuska sake. Salmah ta fice a falon hannunta rike da lunch boxes din yaran Ta nufa kitching. "Nide bama atani..." Cewar Aunty hafsat datake kallon Aeezad da yaran sunata masa gwaranci kwarama Noor shi mgnrsa tarr, asmah Kam bata iya mgna sosai ba kuma tafi Noor surutu. "Ba haka bane Aunty .." cewar Aeezad Daya dago yana me kallon hafsa,murmushi Aunty hafsat tayi tace "bawani kaga yaranka ka manta da gudan jininka, ur one and only blood sister..." Aeezad na dariya yace " na kula kishi kikeyi.." hafsa ta daga masa Kai alamar ehh tana kallon yaran sunyi d'aro d'aro a kan cinyarsa. Dariya Aeezad yayi cikin nishadi yace ''Aunty hafsa inason yarannan..." "Kaima ka kusa ganin naka Ai insha Allahu..." Cewar Aunty hafsat. Nan da Nan face din Aeezad ta chanza sbda mgnr Aunty hafsa ta tunasar dashi na'eema,kokarin danne damuwarsa yayi saboda bayason aunty hafsa ta fahimci yana cikin damuwa. Aiko tini hafsat ta gano Aeezad nacikin damuwa, tin shogowarta kallo daya ta masa ta fahimta, Amma tasan dnwarsa bata wuce na'eema ko hajiya mommy, sune problems din family dinsu, gashi kiri-kiri sunaji suna gani hajiya mommy ta rabasu da ubansu se abinda tace daddy keyi, danma Allah yasa hafsat ta dace miji me kaunarta da tattalinta da batasan yazatayi da rayuwarta ba, mijinta daya ne tamkar da dubunnai, yafi dubu a cikin tarkace. "barkanku da dawowa ..." Cewar nabeelah data iso falon idonta na kan su Asmah da Noor tana kaunar yaran, Aiko sunajin muryarta suka gudo daga gurin Aeezad cikin murna suka fada jikinta suna fadin. "Aunty Aunty Aunty..." nabeelah ta tsugunna ta dauki Asmah ta mannawa Noor kiss a Kumatu. "Yawwanmu mommyn Aeezad..." Cewar Aunty hafsat cike da kulawa da girmamamawa ta amsa, daman haka suke cewar nabeelah Mommyn Aeezad, hatta Alhaji sunusi ma haka yake kiranta, har hajiya Mommy ma. Aeezad daketa kallon yaran da Aunty nabeelah, yadawo da dubansa ga Aunty hafsa yace ''Kinga abinda yarannan sukamin ko suna ganin mommyna sukayi kmr basu taba ganina ba..." hafsat ta kwashr da dariya tace "Kaga tin yanzu sun watsa maka kasa a ido, bade ka yadani ba ka daukesu ai shikenan na barka dasu...." Dariya kawai Aeezad yayi, idanuwansa na kan nabeelah, ko kallansa batai ba ita, ya bata mata rai sosai, murmushi Aeezad yayi yayinda yake kallonta ko kyaftawa bayayi tana kokarin cirewa yaran uniform din jikinsu, bakaramin so yaran ke mata ba, in har zasu ganta Sam basa damuwa da mahaifiyarsu. Aunty hafsat tabi Aeezad da ido se kallon Aunty nabeelah yakeyi bako kyaftawa, wasu lokutan kallon da Aeezad kema Aunty nabeelah yana bawa hafsat tsoro tana Yawan tsintar kanta a faduwar gaba, jikinta da zuciyarta nabata abubuwa da dama, amma takan kauda hakan dawuri tasan sharrin zuciya ne kawai. Nufar dakin yaran Aunty nabeelah tayi da Asmah a hannunta Noor na biye da ita. Duk Aeezad na kallonta harta bar falon ya sauke Ajiyar zuciya shi kadai yasan me yakeji a zuciyarsa Yana kaunar mommynsa Ainun yanada tabbacin ko mahaifiyarsa iya san daze mata kenan. mikewa yayi Yana mejin kiran Sallah. ''bari inje inyi sallah inaga daga can zan wuce gida ma kawai ina bukatar hutu..." Yayi mgnr da hafsat data zubo masa Ido. "Kaci abinci ne?" Daga mata kai kawai yayi alamar ehh, dukda ba hkn bane, besan mgna kuma yagaji da surutu, miskiline shi na karshe A gun kowa Amma banda gun nabeelah ita kadai yakema magana sosai. Ganin yadda ya amsa mata ta fahimci besan aja mgna tasan halin Dan uwanta da miskilanci,sannan ta kula kmr fada sukayi da mutuniyarsa, sede fadan ba a shiga dan inka shiga kai zakaji kunya. "Shikenan ,,,yaushe zaka koma bakin Aiki ?" A takaic yace "maybe gobe..." Aunty hafsa tace "To ka kula da kanka da Imaninka da Addininka dukda nasan daman Kai me Addini ne, nasan mommynka na maka fada sosai ni nawa kari ne .. Dan Allah Aeezad meyasa bakasan yawo da matakan tsaro ne bayan kasan bazaka rasa magautaba..." Cikin kosawa Aeezad yace "Kawai ni banason duk inda nabi Ayita bina zuuu kmr Wani wa-wa, ina garina ma baza a barni na hutaba, a Nan ne kawai ban bari securities suyita bina Aunty ..." "Ina tsoro, ni nafiso inganka da matakan tsaro Dan Allah Aeezad, kasan Kai waye a Nigeria be kamata kadinga yawo haka nan kara zube ba, yakamata ko ba yawa kadinga yawo da masu tsaronka,.." hafsat ta fadi cikin marairaita. "karki damu Aunty ubangiji na tare dani shine babban me tsaro kuma me tsarewa..." Cewar Aeezad, Shi Sam bayason wasu masu tsaro, haka mommynsa ma tadinga fama a kan yadena yawo haka shikadai yaki denawa yanzu harta gajima tadena masa mgna, kawai Adduarh takebinsa dashi ba dare ba rana, a kanshi da mahaifiyarta ne kullum take tsayuwar dare. Numfasawa hafsa tayi kana tace "To shikenan Allah ya tsare gaba da bayanka saboda Annabi SAW..." "SAW Amin ya Rabbih..." Ya amsa Yana kallon hadadden watch din hannunsa. Sallahma ya mata Hadi da lalubar Aljihunsa ya Ciro kudi kimanin 100k ya bata yace tabawa Aunty nabeelah 50k, 50k kuma akai yara gun shan ice cream. "Baka gajiya da wahala, to Allah yayi albarka ya tsare gabanka da bayanka yajikan mahaifiyanmu, Allah ya kara hada kanmu ya kauda shedann..." Aunty hafsat tadinga masa godiya da Addu'ur'i ya amsa da Amin kana ya nufa bakin kofar ficewa a falon harya murd'a handle din falon se ya juyo yace "A gayawa mommyna natafi tamin Adduarh . ..." Aunty hafsat ta amsa da toh. Ya fice a ransa yanaso ya kara ganinta sede yasan koyaje bazatabi ta kansa ba gani zatai kmr batsar zesake mata. Masallacin kofar gidan ya nufa yayi sallar azabar, kana yadawo cikin gidan yayiwa ma'aikatan gidan Alkhairi sunata godiya daman sunsan inde yazo gidan baya barinsu hakanan seyayi musu ihsani, shi