← Book details Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 87

Sashe 75

Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

karka ce aah, sannan in aka ciremin babynka, se in baka yarka ko d'anka, kawai seka sawwakemin Aurennan naka dake kaina Dan Allah wlhi bazan iya ba,, wata rana se a dauki raina a kanka! Dan Allah Ka sawwakemin kawai, Ka maidani kasata na har abadan, bazan dawo kasarnan ba wlhi, zaman Aure mutum biyu Akeyinsa, nide bazan iya ba kayi hkri Dan Allah Ka sawwakemin kawai na huta da fargabar dake tunkaroni yanzu!...." Ta karashe cikin magiya da roko kawai so takeyi ta bude Ido ta ganta a dakin uwarta, Kuma taga babu auren Aeezad a kanta shine burinta. Tinda Taga irin dukan da Naeema da hajiya mommy suka mata ama basusan cewar cikin jikinta na Aeezad bane, Ina maga yanzu dasuka Sani tasan next time kawai kasheta zasuyi har lahira, so maganin Ayi kar a fara,dukda tasa sansa Amma ta shirya kawai kwara ta rabu da Aeeezad shine kwanciyar hankalinta. Ko kadan ba editing se hkri. This book is 1k 08101626484. NAMIJIN ZUMA 49... Wani irin kallo Aeezad ya mata, yaja dogon numfashi, yayi humming kana ya fara magana "Wani mahaukacin ne yace na fara sanki ne Dan in Dena mommy? Ko na Aureki Dan kice in sakeki, ni Kuma se in sakeki kou? Tinda gani sauna ko sakarai kou? Wallahi bazan sakeki ba, har abadn, Na fad'a Miki zan sake fada miki Wallahi ban fara sanki Dan in dena ba, in duk duniya zasu taru bazan sakekiba mommy, koda Baki bani gindi na hauba wlhi bazan rabu dake ba balle ma kin bani gindi na hau Naji dadih, bazan iya rayuwa in ba ke ba mommy kece Mahadin komi nawa na rayuwa, Dan Allah ki koyi juriya a kaina mommy, ni nariga nama kaina alkawari ba abinda ze rabani dake sede mutuwa mommy, Dan Allah kema kisa hakan a ranki, kada abinda su hajiya mommy suka Miki yasa ki bijiremin, in kika barni se in lalace, Dan Allah ki tausayamin Kodan darajar cikina dake jikinki Mommy...karki dagamin hankali pls.." ya karashe maganarsa Yana daura hannayensa kan cinyoyinta, Cikin magiya, Yana me kumajin haushi da tsanar hajiya mommy da na'eema shide Alhamdulillahi tinda ya saketa, Amma fa be fanshe haushinsu dake tattare Dashi ba, gashima suna Neman targad'a masa Aure. Nan de ya dinga lallabata, taki yadda, dole seda big hajiya, da Zaks suka Sako Baki aka tasata gaba da ban baki, da natsiha, kana ta hakura a zahiri, Amma a zuciyarta bawai ta hakura bane saboda bazata iya zama da Aeezad da na'eema ba ga Hajiya mommy a gefe, ai duk me hankali yasan zaman baze yuba. Haka de Aeezad ya dinga lallabarta Kmr kwai ba kulawa Yana bata ta musamman,. After 3days tini doctor din fata tazo ta duba nabeelah ta dubata Sosai abinka da kudi, tini ta bata Wani cream data dinga shafawa wannan shadin bulalar ya warke cikin hanzari ba tare da tabo ba. A kullum se Aeezad yaje inda aka ajiye masa hajiya mommy da na'eema da tawagarsu, kullum seya duka na'eema duka Sosai kmr de yadda ya mata a farko, a sume yake barinta, se inya dawo ya yayyafa mata ruwa ta farfado ya kuma jibgarta, Sam be kara dukan hajiya mommy ba, dukda ita ce tafi lefi a gurinsa, Kuma yafijin haushinta a kan na'eema, kawai yasan ma dukan da yake ma na'eema yafi mata zafi a kan ace ita ya daka,Aiko hakan ne, Hajiya mommy ji takeyi kamar zuciyarta zata fashe in Yana dukan na'eema. A kwana ukun shida Zaks suke zuwa inda suke, yau da kyar Zaks ya dinga lallabarsa, yasamu ya sakesu Amma ada yaso suyi 1week a kulle Yana azabtar dasu, direct ana sakinsu asibiti aka nufa da hajita mommy da na'eema ga uban sauraye duk sun cijesu a dakin, domin dakin yanada matsifaffun sauraye, ba karamar azaba suka shiga ba. Kawayen hajiya mommy Kam kowacce tayi gidanta, Wasu sanadiyyar mutuwar aurenta, Wasu Kuma dasuka samu suka Sha da Auren nasu, sukayi gum da bakunansu saboda in suka fallasa abinda ya faru mazajensu bazasu goyi bayansu ba, sbda sun kaisu kwano a wannan karan, koda asiri ai wata ran akwai gajiya, Amma fa dukkanimsu seda sukaje asibiti aka dubasu. Hajiya mommy ta Ari waya ta kira Alhaji sunusi ta gaya masa Suna asibiti, jiki na rawa Alhaji sunusi yaje asibitin da Hajiya rafi'ah take da naeema, wad'anda tini aka Basu gado, na'eema Kam sede emergency aka nufa da ita, Danma Asibitin na kudi ne sosai da Baza a amshesu ba, tako ina jikin naeem yayi kace-kace da bulala Kai kace sararta akayi. Hajiya rafi'ah tana ganin Alhaji sunusi yazo ta rufesa da fada da zagi kamar uwarsa, wai kanme ze bari Aeezad ya kwashesu ya rufesu gabansa, hakuri Alhaji ya dinga bata, hajiya rafi'ah bata sauraresaba takoma ta inda take shiga bata Nan take fita ba,,Alhaji sunusi hankalinsa ya tashi hakuri kawai yake bata,.ganin ya rikiceN yasa hajiya mommy Kuma fashewa da kuka ta zayyana masa karya da gaskiya kan abinda Aeezad ya mata ita da yarta da kawayenta, ta shaida masa har sakin na'eema da yayi, Nan hankalin Alhaji sunusi ya tashi, ya fice daga asibitin zuwa gidan Aeezad,. Yana shiga dai-dai Zaks na shirin fita daga gidan, sukayi kicibus da daddy. Dole Zaks ya dakata ya tsugunna ya gaidasa,. Sam Alhaji sunusi be amsa gaisuwar Zaks din ba, ya rufe Zaks da fada, mommy ta Kuma rikitasa, tana zuwa asibiti ta Ari waya ta kira malaminta ta shaida masa komi dake faruwa, Amma tace first a Kuma rikita mata Alhaji sunusi yanzu-yanzu, daga baya taji da Aeezad. "Wani irin hauka ne wannan ? Duk na kiraku ba wanda ya dauka, saboda rashin sanin darajata,da wulakanci," ya shiga matsifa inda yake shiga bata Nan yake fita ba, Kai dagani kasan baya hayyacinsa, zaks ya dinga basa hakuri kawai,. "Ina shi Aeezad din ?'' Alhaji sunusi ya tambaya cikin fad'a da matsifa, yaxo gidan yafi Sau ashirin a kwana hudun da Aeezad ya kulle masa mata, Amma baya ganinsa. Zaks yace "Baya Nan daddy, Yana asibiti tare da nabeelah bata da lafiya, tin randa ya dauketa daga gida asibiti aka nufa da ita saboda dukan da hajiya mommy da na'eema suka mata ma ya haifar da problem a cikin nata. " se Kuma Alhaji sunusi yayi sanyi, yayi Shiru yayi kasake, se yace "Da gaske ne Auren yarannan da yarinyar Nan? ka gayamin gaskiya Zakariyya?'' Nan Zaks ya kwashe Labarin komi ya gayawa Alhaji sunusi, nan take,. Alhaji sunusi yayi jim, yace "ai nasan limamin masallaci sultan bello, Abokina ne,,," Nan take ya dauki waya ya kirasa, ya tambayesa komi Hadi da masa kwatance Aeezad, ba bata lokaci malamin ya Gane, Nan ya shaida masa Ai shi ya daura masa Aure da wata yarinyar nabeelah, ya kama sunanta, Kuma shima ya fadi sunan Aeezad din na Ainifin, a Nan Alhaji sunusi ya tabbatar da maganar Aeezad gaskiya ce,.besan meyasa ba ya tsinci kansa Dama limamin masallacin godiya Kuma ya shaida masa Aeezad din ai d'ansa ne. Da nishadi Sukayi sallahma da limami, kana Alhaji sunusi yadawo da dubansa ga Aeezad yace "Ka kaini asibitin da Aeezad din yake..." Zaks yace toh,. Sam badan yaso ba sbda be sanar da Aeezad ba, gudu yake kar Wani Abu ya faru Aeezad yaji haushinsa. Dole badan yaso ba Alhaji sunusi ya shiga motarsae, yaja motar suka fice gidan zuwa asibitin. Zaks ya fara sako Kai dakin, yaga nabeelah kwance aeezad na gefenta, se aunty hafsat zaune kusa da big hajiya yanzu ma tazo asibitin ta rakube Aeezad yaki bata fuska, se yau tasamu direction din asibitin Zaks ne ya bata ta waya tazo, tini zaka ya shaida mata komi daya faru, tsoro ya hanata zuwa asibitin, se yau ta daure tazo, ta kawo musu abinci da kyar Aeezad ya bari nabeelah taci, shima danyaga ta nuna kwadayinta nasan taci abincin, taliya ce jelop aiko taci sosai , tinda ta fara laulayin cikinnan se yau abinci ya shiga cikinta, amma daga kilishi, se zuma, se ruwan sanyi take iya sha, se ayaba data koma cinta sosai yanzu. Da Aeezad yaga taci abincin yau yaji dadih sosai, se munna yakeyi, shine fa tad an fara sakarwa Aunty hafsat fuska, Nabeelah ta kula da hakan taso ta masa magana kan meya hadasa da yar uwarsa, ya shaida mata komi, ta fahimci wato a kanta ne, taso ta basa hakuri amma yaki yadda ya tsaya ma ta basa hakurin. Zaks na shigowa Alhaji sunusi ya sako Kai, duk kallo yadawo kan Alhaji sunusin. Ya karaso ya tsugunna ya gaida mahaifiyarsa big hajiya ta amsa fuska ba yabo ba fallasa. Aeezad ya tsugunna ya gaidasa, tinda ya gansa yaji gabansa ya yanke ya fadi, yasan da wuya in Alkhairi ne ya kawosa, kila ko yasamu labarin Azabar dayayima hajiya mommy ne, nabeelah da hafsat suka gaidasa ya amsa ba yabo ba fallasa. Aeezad dake tsugunne har yanzu gabansa yana shirin dagowa kawai yaji Alhaji sunusi ya daukesa da wani mahaukacin Mari. Aeezad ya dafe kuncinsa , seda nabeelah ta tashi zaune sbda Jin zafin Marin tayi har cikin ranta. cikin fada Alhaji sunusi ya fara magana Ashe baka da mutumci , ashe baka da kirki, ashe wulakantacce ne Kai, har zaka kullemin mata da yarta ka dinga bugunsu harka zazzage mata hakoran baki duka, dan ubanka in uwarka ce zaka iya mata haka? Bayan haka ka dawo ka saki naeema ba tare da kwakwaran dalili ba, maza ka maidata ko in tsine maka Albarka dan ubanka kaji na gaya mak kafin ya karasa shima hajiya Babba ta daura masa wani irin mari, seda tayi tsalle kana ta watsa masa marin saboda bata kaisa tsayi ba, Alhaji sunusi yanada Asali wato yanada tsayi. Idanuwa Alhaji sunusi yabi big hajiya dashi ya bude baki zeyi magana yace A kan matarka ka shimfida masa wannan marin? Kai dadih Aure kou, baka diba abinda ita tsinanniyar matar Taka tayi ba dan wulakanci da rashin sanin ciwon kai, kaide Allah wadaranka da Halinka, mace na haifawa kai, ai Gaka ga macen nan,,,, big hajiya ta fadi cikin fad a da takaicin dake tattare da ita shekara da shekaru. Hakuri kawai Alhaji sunusi ya shiga bata sbda mahaifiyya ce dole sede a lallabasu a rabu lafiya, abinka da uwa da d
Chapter 75 · 0% Book details