← Book details Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 87

Sashe 20

Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

kawarta asiya itama bazawara ce. ita tabasu shawarar su Kai photos dinsu gidan me dalilin aure shine suka Kai, cikin sa'ah rafi'ah tasamu mijin Aure wato Alhaji sunusi. Dukda Alhaji sunusi yaga talakawa ne su rafi'ah na gidi, Sam be damu ba a tunaninsa ze samu kwanciyar hankali da ita. Aiko sati daya da Auren sunusi da rafi'ah komi na rayuwar Alhaji ya chanza, rafi'ah ta kwaso Rabin danginta takawosu gidan daman tin randa aka kawota a matsayin Amarya taxo da yarta Na'eema wadda bata da kunya ko kadan idanta tsakiyar Kai, bata bin maza ammafa sam bata da tarbiya. Tin Alhaji sunusi na magana a kan wasu abubuwan da rafi'ah keyi marasa kyau har yazo yadena mgnr ma baki Daya, rafi'ah ta shanyeshi tass be iya komi,gashi bata kaunar yaransa, sbda ta kula yana san yaransa. Aeezad ne kawai ya zame mata kadangaran bakin tulu. Tinda zuwan na'eema ta kyallara Ido a kan Aeezad tace ta kamu da Azababbiyar soyayyarsa, tin baya kulata harya dawo ya fara kulata,shima ya kamu da Azababbiyar kaunarta, zuwa lokacin tini yazama soja shida Zaks sede shi Aeezad ya fito da babban mukami yafi Zaks, Asalin sunan Zaks (zakariyya),. Tin lokacin Aeezad na tare da Esther, da akasa ranar bikinsu da na'eema ne Aunty nabeelah ta matsa dole Aeezad ya rabu da Esther , itama se lokacin tasan suna tare da Esther din, Tasha fama sosai kafin Aeezad ya rabu da Esther. Esther yar asalin osun state ce, tanada tsananin kyaun fuska Amma sede a jiki bata da shape, Aiki ne ya kai Aeezad can osun din suka hadu da Esther iyayenta nada kudi Allah ne kawai ya jarabceta da soyayyar Aeezad har tabiyosa garin Kano suka dinga sha'anin rayuwarsu kusan 1yr suna tare, Aeezad ne ya fara bare Esther a cikin leda. Yanajin dadinta Sbda nabeelah kawai ya rabu Da Esther ta koma gidansu bayan sunyi kaca-kaca, a zuciyarta har yanzu bata bar sanshi ba, kawai ja da baya tayi tasan dole akwai ranar daze nemeta ko ita ta nemeshi. Zuwa lokacin tini Hafsat yayar Aeezad ta gama karatunta na low ta hadu da Wani babban Dan kasuwa sukayi aure daman ta kosa ta rabu da gidan ubanta sbda ba dadih kwata-kwata Tin zuwan hajiya rafi'ah ta rikita gida, ta raba Sunusi da uwarsa ko gidanta baya zuwa, ta rabashi da Dan uwansa Daya tilo Alhaji Abubakar Wanda keda iyalansa yaransa hudu biyu mata biyu maza,, Sam Alhaji Abubakar be rabu da Dan uwansa ba duk yadda Rafi'ah taso su rabu abun beyu ba, time to time Yana zuwa da iyalansa gidan su gaisa ya tafi dasu, Sam baya damuwa da Amsar karnukan da hajiya rafi'ah ke musu, ita Sam bata kaunar taga kowa ya rabi gidan inba ita da danginta ba, kaf Yan uwanta Da kawayenta sun maida gidan Alhaji sunusi kamar gidan ubansu, hatta wanda yayi sanadin aurenta da sunusi wato alhaji hamza seda rafi'ah ta rabasu da sunusi . A haka Aeezad ya Auri na'eema Daren farko kawai yasamu ya kusanci na'eema 2tyms,daga lokacin be kuma samun abinda yakeso ba kullum na'eema na gidan hajiya mommy, hajiya mommy kuma liyafa taci gaba tini ta bude manya manyan kantuna wanda akeji dasu a garin katsina, ta shiga tura na'eema kasashe saro kaya domin ita hajiya rafi'ah bazeyu taje ba sbda ba boko, na'eema ce tayi karatu Sosai daman kuma kasuwanci ta karanta, itace a kan komi na kasuwancin hajiya rafi'ah ita bata San komi ba, ba Arabi ba boko, a haka itama na'eema take gina nata kasuwancin. Auren Na'eema da aeezad Ba abinda yasawa Aeezad se dumbin bakin ciki, ada bashi da wata damuwa seda ya Auri na'eema yashiga tashin hankali mara misaltuwa, nabeelah ce kawai ke bashi hakuri a kan na'eema wallahi da tuni ya saketa, nabeelah tace wlhi inya saketa bashi bata, shine fa Aeezad ya shiga taitayinsa kawai yaci gaba da hkrin zama da Na'eema Amma fa Yana cikin bakin ciki, tin Yana 20yrs yayi Aure Amma Auren mara amfani, gashi ba halin yayi mgna se kallo kawai. Hajiya rafi'ah kuwa duk yadda ta kaiga San ta haihu da Alhaji sunusi, Allah beyi ba, ko bari bata taba samu dashi ba,tabi bokayen harta gaji. A bangaren Hafsat ta haifi yaron farko yaci sunan Alhaji sunusi ake kiransa da Noor, hajiya bilkisu tazo ta zauna da ita hartai arba'in, haihuwar ta biyu ce datayi tace a kawo mata Aunty nabeelah sbda hajiya bilkisu takuma tsufa sosai. tinda nabeelah tadawo gidan bata koma ba, daman tagaji da zaman gidan hajiya rafi'ah, sbda kiyayyar da rafi'ah ke nuna mata ya shahara, ita ke kaf girkin gidan, sam bata kaunar taga nabeelah ta zauna,ta tsaneta tsana me tsanani,haka itama na'eema ta tsani nabeelah sosai, har marinta ta tabayi Aeezad ya rama mata, Aiko ranar ansha fada a gidan , rafi'ah tace dole se Nabeelah ta bar gidan Aeezad yace baze yuba,, da kyar akayi settling problem din. Nabeelah batayi karatun boko ba Amma tayi na islamiyya har ta sauke alqur'ani a gidan, Amma batasan komi ba a kan karatun boko ba sede ta iya hausa kadan-kadan, tana saving number sosai Nabeelah takeson karatun boko tin tana karama Amma Allah be rubuta zatayiba. Sun taba zuwa da Aeezad kasarsu sau biyu ya rakata yaga mahaifiyarta wadda a ynzu tana iya komi da knta sede kullum cikin shan magani take, Aeezad ya yaba da dattako irin na mahaifiyar Nabeelah, Nan ya nemi madaidaicin gida yase mata a birnin niger ya zuba mata kayan Alatu, Ya Kaita unrah da hajji,. murna gun nabeelah baze misaltuba, sosai kima da darajar Aeezad ta karu a kwayoyin idanuwanta, saboda darajar mahaifiyarta da Aeezad ke gani yasa nabeelah Kara kaunar Aeezad tasawa ranta itama insha Allahu wata rana seta biyasa da ALKHHAIRINSA gareta, sede tasan har abadan ba wannan ranar saboda bata da abinda zata biya Aeezad dashi a rayuwarta. Sosai Nabeelah kejin dadin zamanta a gidan Hafsat, a fari de tasamu cikass ta yadda mijin hafsa ya fara nunawa nabeelah so na aure, taki yarda da hakan, shi kuma mijin hafsa ya kamu da soyayyarta,yadawo yace ko bazata Auresa ba ta bashi kanta domin ya riga ya kwad'aitu da surar jikinta, a Nan nabeelah tashiga tashin hankali, daman tin zuwanta gidan ta fahimci Baban Noor din nada neman mata, lokuta da dama in hafsa ta tafi Aiki har mace yake kawowa gidan su gama abinda zasuyi su tafi, Sam nabeelah bata sanar da Hafsa ba, kuma tayi alqawarin bazata sanar da ita ba har abadan, shima kuma baban Noor din ya kula nabeelah nada sirri shiyasa har yake wannan iskanci, a karshe yadawo kanta wai ze aureta yaga babu nasara yadawo yana nemanta da iskanci, Aiko nabeelah tace wlhi in be rabu da ita ba zata sanar da matarsa komi, Sam baban Noor ko a jikinsa domin yasan da wuya kota gayawa matarsa ta yarda, sbda ya gama mata komi, be raketa da komi ba,shi mutum ne me rike gida sosai ko cokali hafsa bata taba siya ba a gidan shike komi, aiki datakeyi raayinta ne, Amma duk month seya mata salary ita da yaranta, akwaisa da kokari, Amma sede yanada azabar neman mata,har yanzu kuma matarsa bata Saniba, domin yana bata so da kauna be taba chanza mata a fuska ba daze nuna yana neman matan waje ba. kalubalen Aure nada yawa, babu macen dake samun a dakin aurenta dole seta samu nakaso a wasu abubuwan sede Adduarh kawai yanayin mazan yanzu marasa control se hkri. Da Adduarh nabeelah tasamu ta kaucewa kaidin baban noor, amma fa har yanzu da kwad'ayinta a ransa,ita kuma nabeelah wannan shine kalubalenta nazaman gidan Hafsat gashi intace zata tafi hafsat zata dasa question mark a kan nabeelah, Dan haka dole ta jure daman ita damo ce sarkin hakuri, ba kasafai ka fiye gano damuwar taba, tanada dauriya da juriya. Gameson littafin namijin zuma da Namijin duniya ze biya 1500 a wannan account din 0542703718 Saadatu Abdullahi gT bank cantact 08101626484.
Chapter 20 · 0% Book details