Sashe 81
Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kmr ranta ze fice daga jikinta. Bakin ciki ya cika zuciyar hajiya mommy ita kanta taga kamannin yaran da ubansu, ji yake kmr taga yaran gabanta ta musu kisan gillah. Nan de ta dinga rarrashin naeema kan gobe zasuje gun wani boka a illori dasunje dmwarsu ta gushi. Ranar nan falo suka kwana suna saka da warware duk cikinsu ba wanda ya rintsa, asubar fari suka bi private jet suka bar garin ko Alhaji sunusi bata sanarwa zatayi tafiya yau ba, tashin hankalin da take ciki ya isa, Sam batasha wankin hula ze kaita rana ba Gashi yana neman ya kaita dare. Suna isa illorin kawar hajiya mommy , Hajiya nanah ta rakata gun bokan, wani kasurgumin kafuri, matsafine sosai, shigarsu ta farko dakin bokan, suka fara cin karo da kwarangwal din mutum. Duk seda suka girgiza amma ina basu ji Imani a ransu ba. Haka suka tsugunna gaban bokan suka zayyana musu bukatunsu,. Boka yayi dariya yace Me kukeso a mata? Naeema tace So muke a haukatata, a nisantata da garin katsina hajiya mommy ta amshe da boka inda Halima a dauketa ta bar kasar duka a kaita can bangon duniya inda babu mutane, can a hadata da Aljanu su kasheta, kafin ta mutu ta whla, whla me tsanani, a hadata da muggan aljanu dazasu mata tsirara, tadinga yawo Tana yankar naman jikinta tanaci su kuma yaran a bokan ya katseta dacewa Su kuma yaran mu zamu dakkosu muzo muyi farfesunsu nida d an Autan Aljanu namatsito mu kasheshi tassss Bokan ya karashe yana kyalkyalewa da dariya. Wannan kalamai sunma hajiya mommy da naeema dadih duk seda suka murmusa hajiya mommy tace Indan wannan ne an bar maka Boka, mude burinmu bukatarmu ta biya boka yace tama biya Ai zaku Nemo gawar mace da namiji yammata birnewar yau wad anda basu taba sanin namiji ba, kuma yan shekara asirin da biyar-biyar hajiya mommy ta bude baki tace Wai bamusan ina zamu samu ba, ko ba haka ba hajiya nanah ni tsoron gawa ma gareni ta karashe Tana kallon hajiya nanah, wadda ta daga Kai ta kalli boka tace Gaskiya sede a aiki d an Autan aljanu shi ya samo mana, semu biyasa boka ya kyalkyale da dariya yace Angama zaku biya nera cikin charbi Dari hudu hajiya mommy da naeema suka kalli hajiya nanah cikin rashin fahimta suka hada baki gun cewa Bamu gane ba nawa yake nufi? Hajiya Nanah tace Million hudu yake nufi..kmr sunyi yawa kou? hajiya mommy tace Bakomai zan bada yanzu ni inde da biyan bukata ai shikenan ga 2M a bag dina zan baki cikon ki kawo masa ta bude bag dinta ta fiddo 2M rafar yan 1k. Sannan ta kalli boka tace Zuwa yaushe aikina zeci? Bokan ya kwashe da dariya irin ta marasa Imani yace Zuwa nan da jibi aikinku zeci farin ciki ya rufe su hajiya mommy, da murna suka bar gurin, kafin su bar garin hajiya mommy ta cire 2M ta bawa hajiya nanah ta kaima boka. Suka baro garin cikin farin ciki, har Allah Allah sukeyi suyi jibi tayi. Akayi kusan 3days amma sukaji shiru basuji mummunan labari ba, har Sumayya hajiya mommy tasa taje gidan amma sema ta bata good news akasin bad. A ranar suka koma bokan, bokan yace shi baze iya wannan mugun aikin ba, dayasanma haka yarinyar take shi dabe Amshi wannan Aikin ba.. Hankalinsu kaf ya tashi, duk kawai suka fashe da kuka, ga uwar asara sunyi Gashi ba biyan bukata. Nande suka kuma bazama gun wani bokan a chart nanma ba biyan bukata ha uban kudi suna Narkawa a inda bazasu fidda uwa ba balle riba. Duk inda de suka samu labarin boka se sunje, sune har Cameron har Indian amma abu yaci tura, saboda karfin Adduah da Azkar sun kasa samun galanba a kan nabeelah da Yaranta, shima gogan sun kasa samun galabarsa, kai bala i de goma da ashirin, Gashi Alhaji sunusi ma big hajiya se amso masa taimako takeyi Tana bashi yanasha, akasin ada dako ta amso masa baya sha, aiko ynzu sha yakeyi. Gabaki daya lamarin hajiya mommy na neman tabarbarewa na yarta de daman already yariga ya tabarbare, Gashi bata da wata kawa ta Arziki yanzu hajiya naja atu ce daman kwara-kwara a cikin kawayen nata toh yanzu har ita ta gujeta bata zuwa inda take kuma bata daukar wayarta, Gashi Alhaji sunusi yau yanata kata fad a kan ta cika yawo ayan kwanakinnan, abinda ya kuma daure mata Kai da ban tsoro kenan, wai yau har ita Alhaji sunusi kema fada harda shouting gaban yaranta, Lallai tashin hankalin dayaci uwar nada yana niyyar tinkarota. Aiko yau da sassafe ta aika naeema zuwa gidan Hajiya naja atu domin ta Kira mata ita sbda ita Alhaji yace wlhi inta kuma fita se ranta ya baci. Da kyar de hajiya naja au tabiyo naeema sukazo gidan hajiya mommy, ita abinda ya batawa hajiya naja atu rai yadda ta dinga bawa hajiya mommy hkri a gaban mutane dasuna dukan nabeelah amma sukayi burus, suka nuna mata ita ba komi bace a gaban mutane. seda naeema tadinga bata baki kana tashigo motar naeema suka iso gidan. Hajiya mommy na ganin aminiyarta ta fashe da kuka ta shaida mata kaf halin da take ciki. Hajiya naja atu ta girgiza dajin wannan labarin tin shigowarta ya firgita da ganin hajiya mommy dukta chanza kmr ba ita ba, tayi zuru-zuru dukta ramen tayi mugun duhu to ba kwanciyar hankalin daza ayi gyare-gyare da shafe-shafe. Hajiya naja atu taja dogon numfashi tace Ki kwantar da hankalinki hajiya mommy komi zeyi farko, Karki sake wannan ya baki tsoro, tin tini bamu tsorata ba se yanzu, Karki Damu ki kwantar da hankalinki hajjaju, yanzu de first a fara sanin yadda za ayi da naeema ta koma gidan mijinta sauran duk se aji dasu daga baya, Aimu bama karaya a nan de hajiya naja atu ta bada shawarar naeema ta koma gidan mijinta. Nan suka kissima yadda za ayi naeema ta koma gidan Aeezad. Ranar de har yammaci hajiya naja atu na gidan se after magrib ta bar gidan. A Daren ranar hajiya rafi ah, ta samu Alhaji sunusi a falonsa, ta masa mgnr komawar naeema gidan Aeezad. Nande ta kanainayesa da baki, hajiya mommy nada lafazi ko ba asiri zata shawo kan mijinta ta wani fannin, domin lafazi da iya magana, makirci babban quality ne ga diyya mace a gurin d ana miji, duk girman namiji kanar yaro yake a gaban mace in har macen tasan kanta. Nan taje Alhaji sunusi ya Kira Aeezad ya shaida masa ya shirya dawowar naeema gidansa zuwa gobe, kuma ya gyara mata wani part a sabon gidan nasa Aeezad zeyi mgna Alhaji sunusi ya katse wayar, sede yayi shiru yabi wayar da kallo, kwance yake a makemen bedroom dinsa dake part dinsa, yanzu ya koma part dinsa wancan part din ya barma nabeelah shi, har yanzu fushi yakeyi da ita ko magana be mata se in yaga idon mutane shine yake rangwanta mata ya dan dinga mata mgna amma yanayi yana basarwa, Sam nabeelah de takibi ta kansa, shine ma ya tattara ya koma part dinsa, yanzu be fiye zuwa ma inda take ba, se in yanaso yaga yaransa ne yake zuwa part din da take, su gaisa dasu ummih da big hajiya , yanzu part din cike yake da ma aikatan dake aikin gidan. Nabeelah taji saukin jikinta sosai Kai bakace ma ita akama CS ba, yau da kanta tashiga ta dafa abinci big hajiya ce ma ke hanata wani abun amma ai da tuni Tana aikace aikacenta. Washe gari, dasafe hajiya naja atu da kawayenta su takwas sukaxo gidan, Alhaji sunusi ya basu adress din gidan daman already aeezsd yasan da zuwansu, ya fito ya basu key din part din da barma naeema zata zauna suka bude sukaga akwai komi sabo dal ba a bukatar komi daman sunzo da masu aiki gida uku mata manya, suka tayasa aka gyara ko ina, aka jefa asiriin da aka amso hajiya mommy ta bawa hajiya rafiah tazo dashi gidan suka sassaka lungu da sakon part din naeema. Wuraren azahar suka bar gidan da la asar sukayo mota kusan motoci goma cike da kawayen hajiya naja atu wad anda ta gayyata, domin itade hajiya mommy ynzu ba wasu kawayen Arziki se tsiraru. Nabeelah da ummih da big hajiya dasuke zazzaune a falo , sede sukaji ana gud a, nabeelah taji gabanta ya yanke ya fadi seda tace Innalillahi wa inna ilaihirraju un, ta dafe kirji, yara ne a hannunta su duka ukun biyu sun mama Nono sunasha, amma ta manta dasu jikinta tashiga kokarin mikewa domin ta isa window taga su waye masu gud ar, saura kiris ta fadar da yaran duka uku dasuke kan cinyarta seda big hajiya ta daka mata tsawa kana tadawo hayyacinta,ta rike yaran da kyau. Big hajiya ta amshi yaran yana fada, Sam nabeelah batabi ta kan me big hajiya kecewa ba ta lega ta window dai-dai naeema ta fito daga cikin mota aka nufa part dinta da ita. Nan da Nabeelah Hankali ya tashi, wato yau matarsa ke tarewa amma Sam be sanar Dani ba, saboda Na hanasa jikina shine yaje ya Nemo wadda zata dinga basa tinda ni ina jego kou? Nabeelah ta fadi a ranta jiki a sanyaye tadawo falon ta zauna. Kinje kin gani hankalinki ya kwanta kou? Cewar big hajiya. Nabeelah tayi shiru batace komi ba ita kadai tasan me takeji a zuciyarta. Ummih ta kalleta ta fahimci chanzawar mood dinta. Su waye ke gud ane ko makwabta ne? Big hajiya ta tambayi nabeelah ita da sam batasha ma a gidan ake gudar ba. Nabeelah ta sauke Ajiyar zuciyata tace nan gidan ne, Naeema ce take tarewa big hajiya ta zaro ido tace tarewa kuma? Au yau take tarewa amma shine Baku gaya mana ba keda Mijin naki nabeelah da duk ta marairaicewa tace Ai Nima be gayamin ba wlhi,,,, big hajiya tace Au be gaya miki ba? Wani irin abune wannan shi kuwa yayi? Gaskiya be kyauta ba .Amma zezo ya sameni, zanci ubansa wlhi ynzu kuma ai dole mu dukufa da Adduah da Azkar wannan shaggu sun dawo gida Kai namiji munafukine! big hajiya ta Kama matsifa. Ummih tace Inaga de shima