← Book details Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 87

Sashe 41

Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ayi a kashemu nida ita I don t care, zuciyata ita kawai takeso a kaf fad in duniyarnan Zaks ya sauke Ajiyar zuciya yayinda idanuwansa suka kasa sauka a kan Aeezad , Fuskarsa da idanuwansa tini suke gaskata duk abinda ya fito daga bakinsa,. Yaushe ka fara mata wannan SAN? Zaks ya tambayesa shifa har yanzu abun mamaki yake basa hadi da daurin kai. Muje ciki Aeezad ya fadi ba tare daya bawa Zaks amsar tambayarsa ba, suka fara takawo zuwa cikin, tako ina haskene a asibitin Kai kace safiya ce. Baka amsamin tambayata ba pls Aboki Cewar zaks. Aeezad yayi murmushi yau de murmushi yaki gushewa a kan fuskarsa mutumin dase yayi 3month beyi murmushi ba kullum fuska a gimtse . Tinda uwata ta haifoni duniya aka mika mata ni ta raineni na fara santa .ban San santa nakeyi ba se kwanaki, kawai ni naji I can t live without her ita kadai ce ke chanzamin mood inna ganta, komi nawa kawai itace a zuciyata wlhi duk duniya ba wanda ya taba soyayyar da nakewa Aunty nabeelah, in ban ganta ba kmr zan hauka, in tana gabana se in mance da komi na rayuwar duniya, banganin kowa se ita zaks daya saki baki lamarin ya fara bashi tsoro abu kmr aikin sihiri, kai ko sihirine tabbas samun wanda ze irinsa da wuya. Ka dakko dala da gwauron dutse Cewar Zaks dake hango matsifun dake gaba. Babban dutsen America na dauka na tarihi kuma ko nauyinsa banji, nauyin santa dake raina ya wuce nauyin a dauramin kaf nigeria a kaina .wallahi da ace san aunty nabeelah zahiri ne kowa na gani da kogin maliya za acemin a fagen santa base ka fadi ba ni shaidane, idanuwanka da kaf gabobinka sun gaza juriya a kan boye santa Cewar Zaks. Aeezad ya amshe da Tabdijan! Karamin so ake boyewa nata yafi gaban a boye, inna boye ai sede a Wayi gari aga gawata Zaks ya amshe da I see, abinda kakeyi a aikace ya wuce kalaman da kake fadi,, ka zama kmr ba kaine commander of army ba, kawai ga kanan ne Alhajin Allah me ciki bakwai Zaks ya karashe hadi da kwashewa da dariya Aeezad ma dariyar yayi yace dabadan kawaici dakai zuciya nesa ba da tini na mata ciki hansin! zaks ya kara kwashewa da dariya hadi dacewa zaka aikata din hakan, inde a kan mommy ne dai-dai suka iso Cikin falon suka samu big hajiya da nabeelah zaune kasa big hajiya na zaune kan kujera. Tana ganinsu ta zubu musu idanuwanta masu cike da tashin hankali. Wai Ina kukaje min ne da jikanane, na fita na dubaku tako ina ban ganku ba, likitoci sunzo yafi a kirga , gabaki daya kun dagamin hankali har waje na fita nemanku, naga banganku ba ki nabeelah ma bangani ba,,,,se yanzu ita nabeelah ta dawo duba kuga idanuwanta duk sun kumbura sunyi luhu-luhu, inagama kuka tayi, inata tambayarta meya faru tace bakomai, tacemin kuna waje gakunan shigowa, Zaks da Aeezad suka kalli juna , karasowa Zaks yayi ya zauna kasan carpet , Aeezad ya zauna kan kujera Zaks ya zubowa big hajiya idanuwa hadi da jinjina Kai yace Bari, bari, bari, wayyohhh! Hmmmm kede big hajiya, wani luntsumemen hatsarine ya afku a nan gaba damu kadan, jirgi da mota katafila suka so su hade,, shine mukayi sauri muka isa muka hana faduwar hakan, amma fa dukda haka, mutane dari uku da saba in da digo tara da mita uku ne suka jiggata . Shiyasa kikaga mommynmu nata kuka, duk Imani ne ya ratsata ganin irin mummunan hatsarin daya wakana Zaks ya shimfido mata karya, abinda da tsufa nan take ta amince ta dauki sallallami da salatittika ta karanta fatiha yafi sau ashirin kana ta fara kwallah Tana fadin Wayyo , Allah ya jikansu C Allah ya bawa iyalensu hakuri, Allahu Akbar da anyi mutuwa dana tuna da mijina Na Allah, Allah yajikanka na Allah seta kara fashewa da kuka. Aeezad kam wata iriyar dariya ya kwashe da ita kasa kasa, nabeelah kam se binsu takeyi da ido ita abinda yake damunta yafi gaban tayi dariya, duk tabi ta rakube, Aeezad se kallonta yake yana karkashe mata ido daya kmr tsohon karuwan namiji, ita kam dasun had a ido seta balla masa harara. Kiyi hkri hajiya, dukkaninmu lokaci muke jira Cewar zaks. A fusace big hajiya ta dago kai hadi dacewa Kuke de jira, shege ja irin yaro, sede ku mutu ku duka ku barni Zaks da Aeezad suka kwashe da wata iriyar dariya data kasa boyuwa daman big hajiya bata kaunar mutuwa. Nan ta hadesu ta fara sirfafo musu zagi, seda ta musu San ranta kana ta mike zata nufa daki se taci karo da waya da kudin da Aeezad ya watsar nan kasan. Sam Dazu big hajiya bata Gansu ba sbda tashin hankalin bataga jikanta ba. Ta tsugunna ta dauka kudin da wayar ta juyo ta nunawa musu Tana fadin kunga wasu makud an kudi, da wayar salula irin wadda saifu jikana na gurin wannan d an ke rikewa ko ku kuka yar? Zaks ya amshe da Aah inaga ganima ce ta isoki har gida, daga sama ta fad o inaga na wad anda ke cikin jirginnan ne dasukayi hatsari suka mace big hajiya ta amshe da kwarai kuwa, Allah ya bani Arziki har gida, kaga irin wannan wayar ta yaran zamani ce, , ga kudi masu yawa dalar Amurka ce wannan na ganeta,,kaga dabadan wannan d an ba ai tini na bude shagon ice a GRA kusa da gidan shi wannan d an, inada kudi dayawa nayi-nayi wannan d an ya hana in bude shagon saida icce,,,,, icce kuma big hajiya Cewar Zaks Aeezad kam se dariya kawai yakeyi. Big hajiya ta zaburowa zaks Eh iccen mana dan kutmar ubanka, ai sana a tace tin Na Allah mijina nada rai, nidashi ai sana ar muce saida icce a daji muke yowa Zaks da Aeezad suka kara kwashewa da dariya big hajiya ta nade ledar kudinnan bayan ta jefa wayar ciki ta saka a cikin lalitarta dake cikin zani ta mayar ta kulle se murna takeyi , domin hajiya akwai San abun duniya , ita har yanzu kudi basu zama bakinta ba. Uwarku da ubanku kukewa dariya, shegun yara masu Kama da yara maza a zamanin fir auna,! Muna godiya hajjaju, ai girmanki ne kiyi komi ba komi Cewar Zaks daketa dariya har lokacin. Hajjaju ta miko masa dakuwa hadi dacewa Kaci uwarka da ubanka kaida godiyar, shege da idanuwanka irin na tsinannun zamanin farko, da Kai kmr na bazawarin karuwa Zaks ya kuma kwashewa da dariya hadi da dunkule hannu ya kara Rissinawa yace Ina kara godiya hajjaju ikon Allah big hajiya batabi ta kansa dan ganin yana neman haukatata, daman tasan halinsa shakiyyin yaro ne na bugawa a jarida. Ta maida dubanta kan nabeelah tace Taso muje ciki diyyata, kiyi hkri kinji, kai wannan diyya da imani kike har yanzu jimami kikeyi kenan Zaks ya amshe da Eh kede bari big hajiya ai mommy Zuciyar fal take da imani hadi da madarar rauni big hajiya ta amshe da Tabbas, duba kaga yadda farar fuskarta tayi ja-jawur kai kace a fuskarta hatsarin ya faru big hajiya ta fadi Tana tsurawa nabeelah ido wadda ta tashi tsaye, se Mika takeyi Aeezad kam idanuwansa na kan monuwanta, dataketa bankarosu tsigar jikinsa se tashi takeyi, ji yakeyi kmr yaje ya duddumbesu. Zaks ya amshe da Ai mommy nada fadin zuciya me cike da imani Cewar zaks daya fadi yana jinjina Kai. Big hajiya ta amshe da wayyo nabeelah ta kalli zaks ta gallara masa harara harshi haushinsa taji tanaji. da girman kujerarki gimbiya me mulkar farar zuciya Zaks yayi mgnr da Aunty nabeelah, bayan ya kula da aiken hararar da nabeelah ta masa, nabeelah da Aeezad ne kawai suka fahimci me zaks ke nufi amma big hajiya bata fahimci komi ba, a zatonta shakiyyancine kawai irin na zaks, suka shige cikin dakin big hajiya da nabeelah. Aeezad ya kalli Zaks yace Kai zanci kutmar ubanka fa in kana hadawa da iyalina a iskancinka Zaks yayi dariya yace da girman kujerarka dawisu me mulkin mallaka,,,sannu Mijin mommy kuma mahaifin mommy kuma mahaifiyar mommy, sannu waliyyin mommy shugaban yan iskan duniya, me ciki bakwai Aeezad ya kwashe da dariya hadi da watsoma zaks wani gangariyar ashariya, Zaks ya kwashe da dariya. Aeezad ya mike yana dariya ya kalli Zaks yace Dan iska, kaje ka Kira doctor yazo yasamin drip Dina na yau na farajin hannun namin zafi yanzu Zaks ya mike hadi dacewa okay yana fadin hkn ya fice , Aeezad ya nufa cikin dakin. Ranar gabaki daya nabeelah batayi bacci ba, Zaks nan ya kwana a falo, ita kam ko rintsi batai ba, kafin Safiya tayi ta kara fice wa a hayyacinta har Rama tayi, ita banzan jikine da ita, tashin hankalin awa biyu ka seya ramar da ita, ba wani jikine da ita ba kayane na Alatu kawai gareta tako ina , irin kayan da dole in namiji ya ganta hankalinsa ya tashi, ko mace ta kalleta seta tabbatar nabeelah macece ta bugawa a jarida macece wadda ta Riga ta Kama kasa tanada komi da namiji ke bukata a jikin mace. Washe gari da safe Zaks ya bar asibitin zuwa karfe sha biyu hauwa u tazo, da manyan baskets masu dauke da manyan warmers , abinci ta kawo musu kusan kala biyar da farfesu nau i daban-daban kala uku, sannan da drink kala uku shima. Dole nabeelah tayi feeding Aeezad badan tanaso ba, hauwa u na ankare da nabeelah tin zuwanta ta fuskanci tanada damuwa ba haka ta barta ba jiya Gashi bataga alamar wayar da Alhaji sadin ya bata ba, daman hauwa u tasan za a rina hakan. Bayan nabeelah ta gama bawa Aeezad abincin hauwa u tayi dabara taja nabeelah waje,. Kawata Meya Faru daga jiya zuwa yau kinyi fige-fige hauwa u ta tambayi nabeelah bayan sun fito wajen sun kefe gun wata bishiya. Nabeelah tace bakomai.. hauwa u ta tsareta da tambaya, badan nabeelah taso ba se dan bata da yadda zatayi yasa ta kwashe komi ta sanar da Hauwa un, bata boye mata komi ba. Tabdijan!! Hauwa u ta fadi tana me jinjina lamarin ita kanta jinta take kmr a
Chapter 41 · 0% Book details