← Book details Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 87

Sashe 70

Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fahimtar kalamanta yace bangane ba? Kmrya? Dauke idanuwa tayi a kansa tace kamar yadda kaji, gaskiya bazan iya yawo ? Da abun kunya ba, bansan da wani ido zan kalli mahaifiyata ba, uwa uba matarka da hajiya mommy, sbda komin daren dadewa nasan se sunji komi , gaskiya Bazan iya ba, kawai zubda cikinnan zanyi wlhi idanuwa ya zaro cikin mamakin kalamanta nan da nan annurin fuskarsa ya gushe rannan yayi bakikirin. Cikin shege ne a jikinki da kk wannan mgnr banzar? Naga ai cikinnan cikinane ni nayishi kona shege ne inasan abuna, balle na sunnah,,,daman shiyasa tinda akace kinada Cikin kika shiga bakin ciki kiketa hade rai? To wallahi wallahi ki kiyayeni, inna karajin kalmar zaki zubarmin da ciki wlhi se raina da naki ya baci ya fadi cikin fushi. Tashi zaune nabeelah tayi tana kallansa tace cikin matsifa harga Allah batasan cikinnan . Wallahi sena zubar da cikinnan ko ka yadda ko karka yadda ya kalli kwayoyin idanuwanta, nan ya tabbatar da tabbas da gaske take dan ada ya fara tunanin wasa takeyi. Murya babu alamar wasa yace Wallahi Billahillazi na Miki rantsuwar d an musulmai, In kika zubarmin da ciki wlhi wlhi nabeelah kinji na kuma rantsuwa, wlhi sena daureki, kaf danginku ma sena musu daurin rai da rai, ummih ce kawai zata tsira sbda ina ganin darajarta, amma wlhi wlhi dake, da wanda tasa hannu , da wadda ta zubar min da cikina, da asibiti da aka zubar min da cikina, da makarantar da wadda ta zubar min da cikina tayi dukse na hadsu dake duka na muku daurin rai da rai har mutuwarku, bade Tonon asiri kike gudu ba zan tona miki , in kika zubarmin da cikine zakiga jahilci, wlhi se duk duniya tasan komi , kin ganni nan mahaukaci ne tuburan in haukar kikeyi ni na fiki hauka nabeelah, ki zubarmin da ciki kigani, wlhi sena miki abinda harki komawa ubangiji bakiyi tsammani ba yana gama mgnrsa cikin matsifada gargadi, a yadsa yake mgnr shima dole zaka fahimci tabbas ze aikata duk abinda yace ze mata a kan ciki. Wallahi sena zubar sede kayi abinda kace zakayi tayi karfin halin fadar hakan Tana kuka wannan karan, ita wlhi harga Allah batasan wannan cikin , da tasanma tana dashi da tin kafin wani yasani zata zubar dashi, suna abu a boye Gashi ynzu asiri ya tono, tunaninta ma mgna ta Kai kunnen hajiya mommy ko naeema uwar kishi, ga mahaifiyarta kuma. Ki zubar ki gani, wlhi ke karamar yar iska ce, nine babban ya fadi cikin fitar hayyaci duk yabi ya rikide ya shiga wani Hali, Jin tace zata zubar masa da ciki, kuma yasan zata aikata. Ya fice a dakin cikin fushi da matsifa, ya tadda big hajiya da hafsat a falo, nan ya shaida musu komi da nabeelah tace, kuma yace su zama shaida ko a mistake cikinsa ya zube wlhi seya daureta da kaf danginsu, yayi rantsuwa ya kuma rantsewa. Aunty hafsat ta fara bashi hkri, Ina bebi ta knta ba ya fice a gidan zuciya a dagule yaja motarsa zuwa gidansa, yama mance yaushe rabonsa da gidan nasa. Yana fita aunty hafsat da big hajiya suka taso suka nufo dakin nabeelah zaune suka sameta tsakiyar gado tana kuka. Big hajiya ta rufeta da fada kan karta sake ta zubar mata da jininta, ta inda big hajiya ke shiga bata nan take fita ba. Aunty hafsat de se rarrashinta takeyi Tana mata natsiha hadi da nusar da ita zunubin dake cikin zubda ciki, aunty hafsat ta fahimci me nabeelah ke tsoro, sosai tadinga mata natsiha, har tayi shiru amma fa bata jiba. Ba jimawa bacci ya kwasheta abinka dame ciki suka fice a dakin sunata jinjina rashin hankali irin na Aunty nabeelah. Tinda Aeezad yabar gidan be dawo ba sbda ta bata masa rai sosai, shi a ganinsa inde batasan cikinsa, duk San da yake mata ze iya mata abinda batayi tsammaniba, besanma Mommy bata sanshi ba seda cikinnan ya bayyana. Ya fahimci bata kaunarsa bata kaunar me kaunarsa, wai harshi take gayawa zata zubar masa da ciki, yayi bakin cikin wannan kalmar, besan me yayima mommy ta tsanesa haka ba,shi kuma Gashi Allah ya jarabcesa da santa, amma shi kiyayyarsa takeyi , Gashi har gudan jininsa ma ta tsana. A ranar farko taji wani kala data kwana ba tare dashi ba sede tadinga juyo kawai har tayi bacci. A bangaren goganma da kyar yasamu yayi bacci a Daren ranar ya saba da ganinta, ko beci ba inya ganta sanyi yakeji, balle ko beci ba yasha Nono koya taba nonuwa. Washe gari da sassafe aunty hafsat tazo ta dubata sosai, ta bata abinda takeso kana ya fice zuwa aiki, big hajiya taci gaba da dubata. Nabeelah ta Kira kawata hawwa u kan yaza ayi tasamu wanda ze zubar mata da cikinnan.. hawwa u tace What ? Zubar da ciki kuma shi Aeezad din yace ki zubar ne ko meya faru zaki zubar da ciki? Kai nasanma Aeezad bazece ki zubar da ciki ba gaskiya kawata aunty nabeelah tace Ni nakeso na zubar, wlhi bazan iya renon cikinnan ba har in haifesa, Kinsan akwai kalubale a gabana gaskiya bazan iya ba hawwa u tace Ki fawwalawa Allah komi kawata, Karki zubar da cikinnan, bakisan meke zaki haifaba, dan Allah Karki kashe rai kawata hawwa u tadinga nata natseeha, nabeelah tayi kmr taji amma Sam batajiba, itafa tinda Aeezad yace ta aubar tagani, shikenan tajima tanaso ta zubar da cikin sbda taga abinda da ze mata , wai har ita yake cewa ze daure kaf danginsu, sbda raini danyaga su talakawa ne, nan ta kara daura damarar seta zubda cikin, taga mezeyi. Ta kira doctor salmah ta tambayeta meye mgnin zubda ciki? Doctor salmah tace ita bata zubar da ciki, sbda Tana tsoron kashe rai. Duk wata hanya da nabeelah zatabi ta zubda cikin tabi amma ba mafita, Gashi na halin ta fita, dana ace zata fita ne se taje ko pharmacy ne t NAMIJIN ZUMA 46.... kafin a kira Assalatu Hajiya mommy ta nufo dakin domin ta tashi nabeelah Sbda ta daura girki da wuri, jiya mutane nata santin abincinta, Sam ma sauran abincin ba a Wani cicciba anficin Wanda nabeelah ta dafa. Ta kira sunanta, bayan ta shigo dakin ta tsaya a kanta,kwance nabeelah take tana kallon Saman dakin ita kadaice kwanciyar datake iyayi, bata ita wata kwanciya bayan wannan. Idanuwa Hajiya mommy ta tsure cikinta nabeelah dashi wanda ya bayyana, Amma se Hajiya mommy Tasha ko idonta ne, dukda taji Wani mummunar faduwar gaba, ta lumshe idanuwanta ta kara budewa a kan cikin nabeelah,. "toko tumbine?" Hajiya mommy ta tambayi kanta da kanta, haka kawai ta tsinci knta da fadawa duniyar tunanin da bata San kona menene ba. Tafi karfin 5mnt tsaye kan nabeelah wadda keta sheka bacci batasanma hajiya mommy ta shigo ba, kaf maaikatan dakin bacci sukeyi kusab su hudu kowacce da d'an gadanta me daukar kafita waya sha biyu, dakunan masu Aiki a gidan tafi daki ashirin Kuma ko wanne da masu Aiki a ciki kusan mutum hudu, shida na Maza shida na mata. Hannu takai ta daki nabeelah a kafada, da karfi, a firgice nabeelah ta tashi zaune idanuwanta suka sauka a kan hajiya mommy, cikin hanzari nabeelah ta kalli cikinta a ranta tayi Addu'ah Allah yasa de hajiya mommy bata gani ba...'' "tashi kije Ki daura girki,,," nabeelah tace Toh ta diro daga kan gadon tana kallon Agogon dakin taga karfe uku ne da Rabi na dare, ko hudu batayi ba, Sam baccin be isheta ba, ji tayi kmr Yanzu ta kwanta aka tasheta, Wani irin azababben ciwo taji kanta nayi, ga azabar ciwon ciki da taji Yana taso mata, ji take kmr ta koma ta kwanta, Amma dole ta lumshe idanuwanta ta bude, ta karfafa jikinta ta fice a dakin hajiya mommy nata binta da kallo haka kawai taji a ranta bata yadda da nabeelah ba, yayinda kiyayyarta ta yawaita a zuciyarta, a sukwane hajiya mommy ta biyota kiching din, se kawai nabeelah ta ganta kwatsam seda gabanta ya fadi, yaga de se binta take da kallo tako ina, zuciyar nabeelah na bugu zuciyar hajiya mommy na bugu, dukkaninsu ba a natse suke ba ba kmr ma nabeelah ita tasan dalilin rashin nutsuwarta ita Kuma hajiya mommy bata sani ba, itade kawai taji ta kasa nutsuwa. "Ai nagaya Miki abubuwan daza kiyi tin Jira kin fahimtar kou? Akwai komi a kitchen din kasa dazaki bukata,..'' cewar hajiya mommy aunty Nabeelah tayi hanzarin amsawa da "toh...na fahimta..." Hajiya mommy ta shiga kare mata kallo, jikin Nabeelah ya fara Neman bari, kanta na kasa a ranta se Adduah takeyi zuciyarta nata fatt fatt fatt. Hajiya mommy ta juya xata fice a kitchen din se Kuma ta juyo ta sake kallon Nabeelah se kawai ta juya ta karasa ficewa a kitchen din haka kawai ta tsinci zuciyarta da saka da warwarar da batasan Kona meye ba a ranta de se tunani takeyi Kmr ciki tagani jikin nabeelah Kuma kamar tumbi,hakade Hajiya mommy tadinga saka da warwara. A ketchin din Nabeelah jiki ya mutu Se Kara adduah takeyi ta fara aikin tanayi tana layi kmr Yar maye, gashi ko Ina a jikinta azababben ciwo kawai yakeyi. Haka tadinga Ayyukan da kyar tanajin mararta kmr zata bude, inda ace da hali ma kwanciya zatayi , ji take kmr ta saka ihu, har akayi asubahi ta tsaya tayi sallar asubah, haka ta wuni tsaye yauma gashi cikinta ba komi se ruwa data sha, Aiko tanashan ruwan taji cikinta ya fara motsi, ada hatta tsorata, Dan haka ta dauki ayaba taci sosai Sbda tsoro takeji kar cikin ya dena motsi, a asibiti in taje awo doctor Maryam nace mata in ciki yadena motsi hanzari akeyi Azo asibiti wato da matsala, harga Allah batasan Wani Abu ya sameta koya samu d'an cikinta. Tukunya shida ta daura a wuta, tana Aikin ne da kyar, innah sadiya tazo ta tayata a tsorace take tayata gudun kar Hajiya mommy tazo ta ganu, sauran maaikatan nso su tayata Amma Suna tsoro. Haka suka gama aikin cikin temakon ubangiji, mutanen suka yawaita a gidan, hajiya mommy se shiga Ake ta alfarma ana fitowa it's a dole matar Alhajin Allah. Nabeelah da wasu Wanda aka dakko Dan serving
Chapter 70 · 0% Book details