← Book details Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 87

Sashe 73

Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kitchen din kasa, ba bata lokaci ta ciro belt din jikin injin nika ta dawo falon, da zabgegen belt din. har lokacin hajiya rafi ah na rike da wuyan nabeelah ta baya, naeema ta miko mata belt din injin ta amsa, ganin tana shirin zubawa nabeelah uban belt din yasa hajiya naja atu saurin tasowa ta iso ta rike bulalar kowa ya kasa dktar da hajiya rafi ah, se kallo kawai sukeyi se yanzu suka fahimci meke faruwa wato cikin shege yarinyar tayi? Dukkaninsu azabtar da yan aikinsu sukeyi dan haka se cewa sukeyi Gaskiya hajiya Karki sassauta mata dan kutmar ubanta, shaggu masu aiki yan iska mayun mata, duk fatsikaine sune muggan kalaman daketa fitowa daga bakunan mutanen. Karki daketa da wannan bulalar pls hajiya, kodan Albarkacin cikin jikinta koda na shegen ne ki kyaleta pls, Karki kashe ta in kika kasheta Allah vaze barki ba, iya wuya karka dau hakkin wani kwarai tsakaninka da ubangiji inyaga dama ze iya yafe maka Cewar hajiya naja atu data rike bulalar belt din hannun hajiya rafi ah. Fisge bulalar hajiya rafiah tayi tana fadin wani albarkaci Cikin shege ke garesa? Dan kutmar ubanta yau ita da cikin shegen duk nice ajalinsu, ko Alhaji sunusi inya shigo falonnnan be isa ya hanani na kashe yarinyar nan ba, tin fa Tana karama take gidannan, so kk ta Batawa gidan mijina suna? Tayi kadan dan bura ubanta,,, hajiya mommy ta karasheta tana sakin nabeelah daga rikon datayi mata, ta turesa kasan tile din falon ta hankadata seda ta mirgina ta buge kanta da kujera, Sam nabeelah taki yadda cikinta ya bugu hkn ne yasa ta bugu a kai, nan take se goshinta ya kumbura sbda ta bugu sosai abinka da farar fata batasan whla. Hajiya rafiah ta daga bulalar ta fara shimfidama nabeelah a jikinta da karfi, zafin bulalar ya shiga nabeelah ya ratsata tako ina ta fasa ihu cikin fitar hayyaci tana me basu hakuri. Amma ina ai kmr Tana zuga ta, naeema ta jawo wayar wuta, tashiga zubawa nabeelah, yazamana su biyu ke bugunta da naeema da hajiya mommy,. Hajiya naja atu de taga abu yafi karfinta taja gefee, tana tausaya wa nabeelah, yan falon de se zugawa sukeyi. Ita kam nabeelah dukta rikice se basu hakuri takeyi dukta rikice Gashi ta kasa motsawa ta gudu dagan inda take, se ihu takeyi kawai Tana kakkare cikinta, nan naeema tafi bugu, ita kam hajiya mommy tako ina kawai Kai mata dukan takeyi da karfinta tana dukanta tana Haki sbda da karfi take bugunta. In har bazaki gaya mana wani shege ya miki cikin shege ba, sena zama ajalinki wannan cikin sede ki haifo shegen cikin naki a kabari.., Cewar hajiya mommy. Yan falon se kara se zugawa yakeyi cikin sigar gulma, hajiya naja atu ita kadai ce keta aikin bada hakuri taki daddara, ita de gaskiya da sauran imani jikinta. Nan da nan falon ya rikice da hayaniya tako ina. Hajiya naeema da hajiya mommy se aikin dukan nabeelah sukeyi wadda keta ihu har yanzu, tini jikinta ya rufe da azabar zafi sbda sun faffasa mata jiki tako ina, har fuskarta ta fashe se jini kawai ke fita a fuskarta da wasu sassa a jikinta , rigar jikinta me Haske ce, dukta baci da jini,farar fatar nan tata tayi red sosai ba karamin duka suke mata ba, a zuciyar nabeelah ta kudirta ko kasheta zasuyi bazata gaya musu waye uban cikin ba, sbda ta tabbar in sukaji, tabbas wuta kawai zasu hada su sata ciki. Hayaniya Alhaji sunusi yaji wanda shigowarsa gidan kenan, ya fito daga mota yaji hayaniya tayi yawa, cikin hanzari ya nufo part din hajiya rafi ah sbda ya fahimci hayaniyar bata lafiya bace, yana shigowa falon yaga abinda ke faruwa, kokarin dakatar da hajiya rafiah yayi amma taki dakatawa tayi ma kmr bata San ya shigo falon ba, shi Sam bema kula dawa ake dukanba balle ya kula da cikin jikinta. Kawai de yaji hajiya nata fadin Sekin gayamin ubanwa ya miki cikin nan na jikinki? Sune kalaman dake fitowa daga bakin hajiyar, nabeelah kam tin Tana ihu ana ji har muryarta ta disashe yazamana tana ihun amma bame ji. daman kwance take kasan tiles din se kara rirrike cikin jikinta takeyi, har yanzu duk azabar da takeji ta kasa sakin cikin jikinta. Duk yadda Alhaji sunusi yaso Ya dakatar dasu abu yaci tura , yayi-yayi ma ta tsaya ta masa bayani amma ina, seda kyar naeema ta tsaya ta masa bayani se yanzu ne ya kallah yaga ashe nabeelah ce ga uban cikin yayi Totso a jikinta, naeema na gama masa bayani suka ci gaba da bugunta kmr wadda tayi musu wani mummunar kisan kai, Kai kace Ubangijine ya aikosu su daketa. Alhaji sunusi ya zubawa nabeelah ido cikin mamaki, shide dan bayadda zeyi ne amma a ransa yaji bayason dukan da Ake mata, dukda lefin datayi babba ne amma shi a ransa beji ya tsaneta ba,. Duk yadda yaso ya dakatar dasu abu yaci tura, yan falon de se kallonsa sukeyi daman duk sun San shi Mijin tace ne Sam basuyi mamakin danya Hana matarsa taki hanuwa ba a bainannassi. Hajiya rafiah bata taba bawa Alhaji sunusi rai ba kmr yau ganin yadda yayi-yayi ya hanata abinda takeyi ta masa bansa a karshe ma sede ta daka masa tsawa tace Ba ruwanka kaji kou!! In bazaka iya gani ba ka fita! Yaji zafin yadda ta masa hakan a gaban kawayenta, inda sabo yaci acee ya Saba Tasha masa hakan yafi a kirga a cikin mutane, ba kmr ma kawayenta, amma na yau ya masa zafi sosai. Paid book ne 1k 08101626484 NAMIJIN ZUMA 48... Har zasu nufa babban private hospital din aeezaad yace su nufa asibitin da nabeelah ke Awo , Sbda yanaso a duba masa babynsa sosai Da uwar babyn, Kuma ya yadda da Aikin doctor maryam. ba nisa da inda suke da asibitin,ba bata lokaci suka isa asibitin,. Doctor maryam ce ta dubata da ace aeezad ba security bane, da Sam bazata dubata ba ganin uban tabon bulalar dake jikinta, a fari doctor tambayar Aeezad tayi tace ''Hatsari kukayi ne?'' aeezad yace "aah doctor shaidar bulala ce..."doctor ta Kuma duba nabeelah da kyau taga bulalarce da gaske, har kwallah seda doctor tayi, doctor Maryam nada imani, Sam imaninta be fita ba akasin wasu doctor's da babu d'igon imani a zuciyarsu. Ba bata lokaci Doctor Maryam ta bawa nabeelah DUk Wani taimako da take bukata, ta duba babyn dake cikinta Nan take aka mata scanning, a nan taga akwai problem tabbas da ace cikin ya Kai 9months da yau yau za a mata CS a ciresa,. Doctors ta kira Aeezad office bayan an bawa nabeelah daki an mata komi da komi ansa mata drip Sbda galabaitar da tayi, sannan tayi 3days ba abincin kirki a cikinta. doctor tana Kiran aeezad jiki na rawa ya iso office dinta big hajiya ta biyosa, a baya, Zaks baya Nan ya tafi gida ya dawo ynzu, wata nurse aka bari a dakin domin kula da nabeelah. a zahiri da bad'ini kaunar da big Hajiya take ma Cikin jikin nabeelah bana wasa bane,. Doctor ta fara bayani Cikin nutsuwa idonta na kan Aeezad "A gaskiya nabeelah Ahamad, ta wahala sosai, sanadiyar Hakan yasa cikinta ke Cikin tsananin galabaita...." Kafin Doctor ta karasa big hajiyar dake tsaye ko zama batai ba ta amshe da "na shiga uku ni y'asu! Wallahi in aka kashe Cikin jikin yarinyar nan, dukse naci kaciyar bura uban rafi'ah da yarta,shaggu Yayan mage, yan babbar bura bura, matsiyata,'' Doctor maryam ta tsurawa big hajiya Ido, tace "Wasu be suka mata wannan dukan mama? Ni ai nasha barayi ne suka shigo muku sukayi wannan aika-Aikan...." Aeezad de ya dafe goshi ubangiji ne kawai Yasan irin bakin Cikin da yake ciki da Kuma tsanar hajiya mommy da na'eema dake kara ratsashi, ji yake a bakar zuciya irin tasa yana iya kashesu in har ya hadu dasu Yana kan dokin zuciya. Big hajiya ta amshe doctor Maryam dacewa "wad'annan sunfi barayi likita, kasurguman shaggu ne yayan tsiya jima'in rana tsaka, haihuwar tsakiyar kasuwa..." Doctor ta girgiza Kai Cikin tausayawa tace "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' Aeezad yace "Doctor amma ita ba Wani Abu Daya tabu a jikinta kou? Ta fannin lafiyarta?" Doctor tace "Aah Alhamdulillahi de za ace karka damu, Amma ai galabaitar da tayi ne ya shafi babyn, kasan me juna biyu ko zazzabi tayi se babyn cikinta yayi zazzabi, insha Allahu Amma ba Wani abu, sede shadin bulalarce dake jikinta, shima likitan fata zataxo gobe zata bata cream din daza a dinga shafa mata bulalar bazatai tabo ba ko kadan inta warke..." Aeezad ya sauke ajiyar zuciya a ransa shi ko a yaya mommy take Yana santa, shi daxa a bar masa ita a haka ma zeci gaba da santa har gabanin abadan, ya kara santa ma kan San da yake mata, shifa koda turata akeyi a baro Yana santa haka, ba abinda zesa santa a ransa yayi rauni, ajiyar zuciya ya sauke kana yace . "Yanzu yaza ayi da Cikin jikinta doctor? ki temakamin pls a kulamin da Cikin jikinta, Dan girman Allah kar a bari Wani Abu ya samarmin babyna dake cikinta pls,da itama Dan Allah ki temakrni doctor.... in abun bazeyu ba a gayamin in fita da ita waje pls inasan matata da babyna na cikinta banaso na rasa kowa Dan Allah....." Aeezad ya fadi Kmr ze kuka. Cikin muryar kwantar da hankali Doctors tace "Karka damu ranka ya dade, insha Allahu ba abinda ze gagara, da ace de cikin nata karami ne da dole ya zube, insha Allah Wannan ya riga ya girma ba abinda ze sameta, NASA mata drip da Allurorin ze taimaka mata sosai insha Allah, ,sede zaku zauna a asibitinnan har Nan da 2weeks kawai se a mata CS zuwa lokacin cikinta yashiga month dinsa na haihuwa insha Allahu, Amma sede za a dinga bata kulawa sosai,Muma zamu bata insha Allahu sir se kun dauki babynku cikin koshin lafiya..." Aeezad ya amshe da "Allah amin ...." A zuciyarsa yasan ranar daya dauki gudan jininsa Kuma nabeelah ce ta haifa masa ba karamin farin cikin zeyi ba, sannan shida kansa besan Wani irin SO zeyima babyn daya fito daga Cikin wadda yafi so ba a
Chapter 73 · 0% Book details