Sashe 63
Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
drowers uku manya ya siyo Kuma duk an cikasu da kayayyakin daxe dauki maza da mata. da kyar nabeelah ta lallashesa sosai ta rakasa har bakin mota, yayinda securities sunfi mutum dari na tsaronsa sbda a mota ze tafi garin kanon sannan shida Zaks zasu tafi. Bayan ya shiga motar ya kamo hannunta , ta tsuresa da ido, idanuwansa fal kwallah yace "Mommy ki kulamin da babyna Dan Allah, sati Daya zanyi in dawo na Baki amanar babyna, daga can zanje American in karoma babyna kayayyaki dukda babyn nawa ta boye kanta taki bari aganta, Amma inasan ran insha Allahu mace zaki haifa mommy,,,," nabeelah tayi murmushi karfin hali gani takeyi kmr inya tafi bazasu sake haduwa ba. "Ka kyale babbynnan da kaya kayayyakin sunyi yawa, wasuma har abadan baza a sasu ba sbda sunyi yawa pls ka bar kudinka haka Nan ba abinda fa baka siya ba,,," Aeezad yayi murmushi yace "Bakomai ai inasan maman babyn ne, Shiyasa nake san babyn, ke bakisan wai zan iya bada komi nawa Dana mallaka ba a kanki mommy..." for the first time dataji tanaso ta furta masa kalmar soyayyar kmr daga sama tace "Wallahi Ina sanka!" Wani irin mummunan bugu zuciyarsa tayi, be taba tsammanin A rayuwarsa mommy zata fusta masa kalmar SO ba, wasu sassanyar hawayen farin ciki suka wanke ma Aeezad idanuwa ya kara damke hannunta cikin nasa yace "Mommy kina sona? Yau kece kike furtamin kalmar soyayya? Wow! Wlhi Ina sanki, Ina Kara sanki, Ina Miki Azababbiyar kaunar, ke rayuwata ce, wallahi da in rasaki kwara in rasa rayuwata, saboda Rashinki a cikin rayuwata Yana iya haifarmin da mutuwar azaba, har kwara inyi mutuwar farat Daya, Amma inna rasaki mommy mutuwa zanyi bayan nasha wahalar jinya,, Ina rokon Ubangiji a kullum innasa goshina a sujjada, Allah ya barni dake, Allah yasa mu mutu tare, sbda in kika mutu kika barni bazan jure rashinki ba mommy, Ina rokon Ubangiji ya karamin sanki, sbda sanki shine dadih me fidda sinadari a cikin rayuwata!I love you Naji dadih yau kin furtamin kalmar SO zanyi tafiya cikin farin ciku, Kiyi min adduah inyi juriya da hakurin rashinki a kusa dani, ina sanka ki kulamin da maniyyina daya zama gudan jini a mararki, I wish in iya Kai 1week dinma bandawo ba da wuya,, ko mu tafi tare? " Nabeelah tayi shiru yayinda kalamansa na soyayya suka ratsata, duk abinda ya fadi direct daga zuciyarsa yake fitowa. "Ki shigo mu tafi mommy, daga can semu wuce America a Miki CS acan,," ya fadi cikin magiya kawai beso ya tafi ya barta. Nabeelah ta girgiza Kai tace "aah, ni bazanje ba, Nafiso na haihu a Nigeria kusa da kasata,ba asan yadda hali zeyi ba..." Aeezad ya Ya kula tinda cikinnan nata yakai wannan watannin take a karaye, cikin karfafa guiwa yace "Zaki haihu lafiya insha Allahu mommy na, Ina gefenki, za ayi Miki CS insha Allahu zamu rayu tare sekin haifamin yara ashirin ..." Murmushi nabeelah tayi, da kyar tasamu ya saki hannunta, sukayi sallama da Zaks, suka fice a gidan se daga mata hannu yakeyi itama tana daga masa. Seda taga ficewarsu kana ta juya zata koma ciki, taga baban Noor ya fito daga part dinsa, kallo daya ya mata yayi hanzarin dauke idanuwansa a kanta shi tsoronta yakeji ynzu tin abunnan daya faru da abokinsa alhaji sadi, Daman Kuma ba karamin tsoron Aeezad baban Noor keyiba, basa shiri Sam da Aeezad, inya gansa sede shi baban Noor din ya gaidasa Amma Sam shi Aeezad baya gaidasa kawai jininsu be hadu ba, ya rasa dalili, ynzu Kam shida nabeelah se kallon nesa kallonma na tsoro, Yadda yake ganin Aeezad na gidan gun nabeelah kullum shike kara tsorata Baban Noor a kan Aeezad. Nabeelah ta gaidasa ya amsa , cikin hanzari ya wuce ya shiga motarsa ya fice a gidan, nabeelah ta shige ciki, zuciya fal kewar mijinta, Nan falo ya ta zauna gun big hajiya da Aunty hafsat kasancewar yau Sunday bata zuwa aiki, Nan suka wuni suna hira, se dare tashiga daki ta tadda miss call din Aeezad yafi miss call hamsin, daukar wayar tayi ta kirasa, bugu daya Aeezad ya daga,, "Ina kika ajiye wayar inata kiranki Wife?'' cewar Aeezad daga cikin wayar,. Nabeelah tace "Tana daki Wlhi Nima inataso in kiraka Muna falo ne munata hira dasu big hajiya,," AEEEZAD yace " Shine xaki bar mijinki cikin tashin hnkli inata kiranki, Baki kirani ba kinji Yana Isa kano? Toh na isa lafiya my wife and I miss you, ,," "am sorry pls..."cewar nabeelah "Ai bakya lefi ya abun dadihna?:'' nande suka shiga hirar soyayya. seda sukaci juna a waya kowa ya kawo, har karfe biyu na dare kana sukayi sallahma da juna, Aeezad so yayi su kwana suna waya. After 2days da tafiyar Aeezad kullum cikin waya suke. Yau karfe goma na safiya, nabeelah nakwance tana bacci, ta kashe wayarta danta samu tayi bacci yau, sabuwar shekara Ce yau new year 1january yau ba aiki. Kmr a mafarki nabeelah taji aunty hafsat na tabata, ta bude Idanuwan ta a kan aunty hafsat bakinta dauke da Addu'ah a kwanakinnani tana yawan muggan mafarkai.,kallo Daya nabeelah tayima aunty hafsat ta fahimci tashin hankali kwance kan fuskarta, tasan bata taba tashinta in tana bacci ba se yaj, hasalima ko TV ba a kunnawa asa volume in tana vacci. "Mommy tashi Maza ki dakko zumbulelen hijjabi kisaka hajiya mommy Ce tazo, wai kindena zuwa mata Aiki duk bayan weeks,se hauka takeyi tana shouting, kinsantade mahaukaciyar banza,ihunta ne ya tasheni a bacci, danma Allah ya temakeni bata San dakinki ba dasede ki ganta a knki, ubangiji ya rufa mana asiri dase taga komi..." aunty hafsat ta karashe maganarta tsoro na Kuma bayyana a kan fuskarta, jikinta har Neman fara rawa yakeyi gani takeyi kmr asiri ya gama tonuwa yau. yauce rana ta uku da hajiya mommy taxo gidanta, Daya a haihuwar noor, biyu a haihuwar Nasmah, se yau da maman Noor ke tunanin tsautsayine ya kawo hajiya mommy gidan. This book is 1k 08101626484. [18/07, 6:58 PM] +234 701 497 9567: NAMIJIN ZUMA Kowa ya ankare da yanayin da nabeelah tashiga amma babu wanda yabi ta kanta , sbda farin ciki, Aeezad yafi kowa farin ciki ji yakeyi kmr bashi ba, kmr a mafarki, ya kamo hannun doctor tace pls doctor are you serious nabeelah na, nada ciki? Doctor da fuskarta ke dauke da mamakin wai basu san da cikinba? Harshi me cikin, abun ya bata mamaki har tsawon 4month. Yeah sir cikine da matarka har tsawon wata hudu juyowa Aeezad yayi ya kalli nabeelah wadda bakin ciki ya turniketa kmr zata hadiye zuciya ta mutu sbda bakin ciki da kunya, ita Sam bata shirya amsar cikin d anda ta raina ba, kuma ma da wani ido zata kalli duniya? AlhamduLillah Aeezad ya fadi a bayyane, idanuwansa suka ciko da kwallar farin ciki mara misaltuwa, nan take ya zube yayi sujjadar godiya ga ubangiji , yana kuka yanama Ubangiji godiya daya bashi abinda ya jima yana nema., tako ina yasan Aurensa da mommy ya cika, daurin Auren da Akayi a babban masallacin sultan bello, inda Aeezad yace shine waliyyin amarya seda akazo daurin Auren Malam yace ai bazeyu wanda ze auri mace yazama waliyyintaba, a nan de babban malamin yazama shine waliyyin amarya a matsayinsa na babban me shari ah kuma babban malami a masallacin, Zaks shiya zama waliyyin ango, shi tamkar dan uwa na jini yake ga Aeezad. Bayan haka, kuma ya sanar da mahaifiyar nabeelah bayan tazo dubasa a asibiti dabeda lafiya, dayake ummih me fahimta ce kuma burinta nabeelah tayi aure, nan ta fahinta kuma ta amince, amma taace Dangin baban nabeelah sune damuwa zasu iya cewa basu amince ba Aeezad yasan su sbda ya taba zuwa gaidasu dayaje kasar shida mommy, dan haka ya bawa ummih kudade dayawa yace inta koma gida ta basu injisa duk sun sanshi sbda dayaje ya jikasu da kudi sosai, yanada alheri, shi a kn mommy ba abinda baze iya ba. Duk a boye sukayi hakan, kuma ya shaidawa ummih karta gayama nabeelah kuma karta nuna mata, ummih ta musu addu i sosai, dasa Albarka kuma ta barwa cikinta sbda batasan dalilinsa dayace karta nunawa nabeelah ba, ita a duniya sun gama mata komi shida mahaifinsa , ba abinda Aeezad Ze nema a gareta bata masa ba in har tanada iko da abun, kuma da abun kunya ai kwara irin wannan Auren dade a kawo mata abin kunya, kuma ta kula Aeezad nada rawar kai ze iya aikata komi, Gashi koda kashe nabeelah yayi basu isa su masa komi ba, saboda yanada kudi kuma yanada power ita a bangarsn ummih Aeezad ya gama mata komi sbda wannan tamkar rufa mata asiri yayi daya auri yarta. Da ummih zata tafi har lambar limamin daya daura musu auran ya bata kuma ya kirasa a gabanta ya tabbatar mata da tabbas shiya zama waliyyin nabeelah, kuma akwai shaidu dayawa. ummih taji dadih sosai,dana koma Niger ta sanar da yan uwan mahaifin nabeelah a fari sukace basu aminta ba, seda ta fada musu waye Mijin da kuma abun Arzikin daya basu kana suka amince da Auren suka sa albarka, daman Sam ba mutanen kirki bane su , basu taba taimaka mata dako Sisin kwabo ba bayan rasuwar Mijin nata, kuma suma tankar yan uwa suke a gareta, sbda Auren zumuncine tsakaninta da baban nabeelah. Shiyasa shifa Aeezad hankalinsa kwance a kn nabeelah babu wanda ya isa ya hanasa zaman Aure da nabeelah, yanzu de mahaifinsa ne matsala, shima kuma be maidasa matsala ba, sbda malamin babban me shariah ne, yasan daddy ma ba dmwa bane hajiya mommy da naeema suna babban case din dake gabansa. , big hajiya se washe wawulo takeyi tace Alhamdllh yafi sau ashirin, aunty hafsat kam baki har kunne, ita knta doctor da nurse din se murmushi sukeyi, suna Tayasu farin ciki, nabeelah kam ta hade rannan gam, se tunanin tunani takeyi, kan asirinta ya tonu a duniya, zuciyarta ta cunkushe Sam bata farin ciki ji takeyi daman cikin ya bare ynzu, babban tashin hankalinta yazata kalli mahaifiyarta da wannan abun? Uwa uba kuma Dangin mahaifanta da Alkhairi baya kawosu gidan. Se kallan big hajiya takeyi Tana kallon aunty hafsat su se murna sukeyi ba kmr ma