Sashe 83
Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nemesa. Aeezad de ya bita da ido yaga se wannan abubuwa takeyi abinda bata saba masa ba, seyayi tunanin ko ta fara zama karuwa karuwane, bazeyi mamaki ba sbda yawan duniya ba inda bataje ba, ba fitar kasashen waje, shi baya zargin na'eema da zina sbda a farko Daya Aureta shiya fara kusantarta. Bazan iya zamaba gaskiya,,,bansan kamshin dake part dinnan ki biyoni part dina, inasan mgna dake... yana fadar hakan ya juya ya bar falon ya fice, direct part dinsa ya nufa, haka kawai ya tsinci kansa da nadamar ma dabeje part din ba, sbda kamshin part din nata ciwon Kai yaso yasa masa. Yana zama a falonsa ya lalubi wayarsa ya kira lambar nabeelah Tana kwance kan gadonta, tinda ta shiga dakin ta kwantar da manaal ta kwanta ta rasa abinda ke mata dadih, ji takeyi daman bata gidan yau naeema ta dawo gidan, kmr zatayi kuka haka takejin zuciyarta gabaki daya zuciyarta bata mata dadih. Wayarta dake kan gadon tayi ringing tin kafin ta dauka ta gane Aeezad ne sbda ringin tone dinsa ma daban yake ita tasa da kanta,. Tanaji ya mata kira uku bata daga ba kuma batajinma zata daga ko kira Dari ze mata, kawai ma se tasa wayar silent sbda kar karar wayar ya tasar mata da yarinya. Duk kiran da yake mata yasan tana gani amma taki dauka, se yaji hankalinsa ya tashi. Ya mike ze bar falon naeema tashigo ya bita da ido, da kayan daya sameta falonta dasu tazo ba ruwanta da kunyar ma aikata. Ke haka kika keta masu aiki tsirara! Ya fadi cikin tsawa. Naeema tayi kasa da kanta kawai ba tare datace komi ba. Kwafa yaja yace look tin wuri ki gyara, Bazan dauki halinnan ba abinda kkmn a farko ynzu bazan dauka ba, sbda bake ke Aurena ba nike Aurenki ynzu baku isa ku juyani ba keda uwarki, jiya ba yau bane,,, yana gama fadar hakan ya fice a falon naeema ta isa kujerar 3ctr ta zauna a zuciyarta tanaji zata jure komi daze mata tasan kafin ya shigo hannu ne daya shigo shikenan, amma fa tasan zatasha whla, dukya chanza mata ba kmr Ada ba, kalamansa na ynzu ma sun bata haushi da mamaki, batasan duk abinda zasuyi yadinga Sako uwarta ciki. Yana shiga falon gidan yaga Aunty hafsat tazo da yaranta , zuwan Aunty hafsat dinne yasa nabeelah fitowa falo, Tana ganin yashigo ta mike ta bar falon ta koma bedroom , Aunty hafsat da ummih sun kula da saboda zuwan Aeezad ne yasa ta koma daki, shima kansa gogan ya kula da hakan. Gaisawa sukayi da Aunty hafsat, ta masa Allah yasa Alkhairi sbda big hajiya ta shaida mata naeema tadawo gidan. Ba tare daya amsa ba ya nufa dakin Aunty nabeelah gabaki daya hankalinsa ya tashi Dazu ma yasan sbda shi ta tashi a falo ynzu ma haka, wato batasan ganinsa toh meya mata be sani ba?. Hankalinsa yafi na barawon asubah tashi, duk yabi ya rikice a lokaci kankani, da kyar yake hadiyar Yawun bakinsa. ya turo kofar dakin yashigo zaune ya sameta gefen gado, kallo daya ya mata yashiga hankalinsa sbda ta hade rai ba Alamar wasa, Sam be saba ganinta hk ba, Nan hnklinsa ya kuma tashi. Hankalinsa in yafi dubu seda ya kuma tashi ya karaso ya zauna kasan kafafuwanta, shi tsoronta ma yakeji, yau kawai duk yabi ya shiga taitayinsa. Ina wuni mommy ya gaidata cikin rudewa, ya rasa ma yazeyi. Ko uffan batace masa ba se tayi ma kmr batasan da halittarsa ba. Yayi kasa da kansa ya kasa ma kallanta sbda fuskarta tsoro take basa. Ci gaba yayi da magana a daburce lokaci kankani yazama kmr bashi ba, tsoronta ma yakeji Wallahi. mommy naga kmr kina fushi ne Dani? Koda kikaga ni ina fushi wallahi na hakura ma yanzu kawai mu koma normal in saboda ni ina fushi kika dau fushi toh kiyi hkri pls ni na hakura, rayuwata zata shiga garari in kina fushi Dani mommy, ki rufamin Asiri Kadan ka gani ta fadi a ranta a fili batace uffan ba. Harya gama sambatunsa ya mike tsaye ya kalleta yace Ko zaki samu zuwa part Dina, inaso ne in muku natsiha keda naeema, sannan a fidda kwanakin dazan dingayi a gun kowacce bazanje ba, kaje na bar mata Kai duka, kwananka a gurina bana bukata, wlhi na bar mata kai ka dawwama a gunta, tinda kaje ka dawo da ita danta baka gindi aise kaje kayita ci wlhi nide jikina yazama haramiyyarka, kaje gunta, ko Ka kwana guna ba abinda zakamin, banaso tayi magana kishi fal muryarta da fuskarta. Idanuwa yafita dashi bata taba masa mgna da muryar data masa yau ba, nan da nan ya fahimci Azababben kishi ne ke damunta. bazan yarda ni ki barwa Wata niba... duk duniya ba macen dazata iya Dani mommy seke bazan iya rayuwa ba tare dake ba wallahi mommy, dan Allah ki rufamin asiri Karki dagamin hankali,,,in wani abun ma miki ki gayamin dan Allah wlhi zan tsugunna in baki hakuri kuma bazan kara ba insha Allahu, bacin ranki bazarana ce ga rayuwata ya karashe kmr ze fashe da kuka, ji yayi duniya ma bata masa dadih saboda baya dadih da ita, yanzu yanzu duk ta chanza masa yau kawai amma ji yake kmr sunyi shekara a haka, dukya rikice. Komawa tayi ta kwanta yaga Alamar bata niyyar tashi, ya dinga bata hakuri amma Sam taki bi ta kansa dole ya fice a dakin bayan ya jima sosai. Ko sallahma bema kowa ba ya fice a falon, Fuskar nan tasa shima ba Annuri, ya nufa part dinsa. Har ynzu naeema na nan, taji haushin jimawar da yayi be dawo ba, kuma tasan part din nabeelah yaje. Jeki part dinki, Wani time nayi mgnr ya fadi fuska ba Annuri ta bude baki zatayi mgna ya daka mata tsawa Ki tafi part dinki nace!! Dole naeema ta fice a part din amma ba haka taso ba, wato dai yau ba nasara. Haka ta koma part dinta zuciya fal bakin ciki. Zirya Aeezad yashigayi a falonsa yana tunanin shi toh meya ma nabeelah haka ta dauki wannan zafin dashi? Shi se yanzu ma yake nadamar fushin daya mata, seda ya jima a tsaye yana nazari kana ya fara tunanin kode kishi ne ke damunta? Dantaga naeema ta dawo Gidan, kila tanasha koshi yaje ya dawo da ita, amma kuma ai yayi ma big hajiya bayani ai kuma tana falon. Ya fahimci wannan ne matsalar sbda a kalamanta ma ya fahimci hakan. Komawa part din yayi kmr wanda aka mintsila, ko sallahma beyi ba ya shigo sede big hajiya da ummih da Aunty hafsat da bata tafi ba har yanzu, suka gansa tsundum a falon. Dakin nata ya nufa, ya taddata kwance idanuwanta rufe Amma ba bacci takeyi ba Tana tunanin rainin hankalin da Aeezad ke mata ne kawai, tanajin shigowarsa kuma tasan shine ta hanyar kamshin turarensa, taki bude idonta. Yasan ba bacci takeyi ba ya tsugunna yace nasan ba bacci kkba mommy In dan dawowar naeema ne kk chanza wlhi bani nace ta dawo ba, dan Allah ki rufamin asiri gabaki daya duk kin dagamin hankali, ko miyau da kyar nake hadiyewa, ki temakeni yadda Allah ya temakeki mommy.. nabeelah ta tabe baki , batace masa komi ba, harya gama maganganunsa ya gaji ya tashi ya fita ya koma part dinsa, duk yabi ya fita hayyacinsa dayazo fita se binsa da ido kawai su Aunty hafsat da big hajiya da Ummih sukayi gabaki daya ya susuce. Haka de ya kwana yana shige da fice a part din ranar ummih ta fahimci ba lafiya ba. Big hajiya kam seda ta masa magana tace yadena musu shige da fice ya barsu suyi bacci, amma Sam beji ba, sede ya shigo yaga nabeelah da yaransa ya fice. Da Asubahi yana idar da Sallah daga masallaci nan yayo kmr mahaukaci ya tadda nabeelah da big hajiya suna lazimi suma jam i sukabi da masallaci ynzu suka idar da sallah. Ko kallansa nabeelah batayi ba, Balle taji tausansa, bazama taji tausansa ba, jiya ko bacci batayi ba sbda Azabar kishin dake cinta, tasan dakin naeema ya kwana, dukda Rabin darensa a nan part din yayi amma tasan komawarsa ai dole zasuyi wani abu da naeema yadda yake a hannun nan, zuciyarta ta bata tabbacin ai dole ma zeyi wani abu da naeema tinda daman dan yayi wani abun da ita ya dawo da ita, amma shine yazo yake mata kalaman yaudara in banda beda kunya shi har yanada bakin gaya mata wani abu. Bayan sun gama lazimin ta gaida big hajiya, idan big hajiyar yasa ta gaidasa ya amsa Cikin hanzari kmr yana jira ya gaida big hajiya ta amsa Tana tsuresa da ido se Kallan nabeelah yakeyi, ita kanta big hajiya ta fahimci ba kalau yake ba gaskiya. Nabeelah ta koma ta kwanta big hajiya ma ta kwanta suka barsa zaune ya duba yaransa da basu tashi ba, ya dawo ya zauna har karfe bakwai tayi kmr me nazari se kuma ya tashi ya fice ya koma part dinsa ko bacci be ba se zirya yake a falo, ya rasa yazeyi, babbar matsifarsa ga nin yadda bata sakar masa fuska ko kadan gani yake kmr ma ta tsanesa. Tin daga ranar gabaki daya ta kuma rikice masa, daka gansa zaka fahimci baya cikin kwanciyar hankali, data gansa ko tana zaune falo seta tashi, ynzu shiga daki ma takeyi ta rufe knta dole hknan yake hakura, basu big hajiya ba da ummih, har aunty hafsat ta fahimci akwai matsala, Amma batace komi ba tsakanin mata da miji se Allah. gabaki daya ta rikita Aeezad har wata rama yayi ta tashin hankali. Ummih ta samu nabeelah ta kebance da ita ta tambayeta meke faruwa tsakaninta da Aeezad nabeelah tace bakomai. Ummih tayi tayi amma nabeelah tace ba komi dole ta kyaleta ta mata natsiha kawai. Big hajiya kam ta fahimta amma batace komi ba ita a zatonta ko duk a kan a bashi gindi yake wannan gigitar. Gashi kullum cikin daukar wanka take na riguna matsasu inya ganta kullum hankalinsa kuma tashi yakeyi Gashi bashi da damar daze taba ko hannunta, a kullum kara bashi tsoro takeyi ba fuskar da ko kallanta ze fiye