Sashe 36
Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dinga yiba dazu, kmr wanda zeyi hauka tuburan, Ina kula dake da abinda kk masa, koda baki sanshi be kamata ki dinga wulakantasa ba, ko ya-ya ne masoyi yafi makiyi, kuma bashi yasawa kansa ba, wlhi wanda yace yana sanka koda a fatar baki ne ya gama maka komi duniya da lahira, Balle shi wannan dayake kmr zararre, ki duba lamarin nan dannAllah saurarenta kawai nabeelah keyi amma babu kalmar datai tasiri a ranta, tama hauwa u uzuri sbda batasan mezeje ya dawo bane ita, ita kuma nabeelah tasani. Kawata koda ace bani na raini Aeezad ba ai kinsan ni ba sa arh soyayya dashi bace Balle Aure, ya fini gata, yafi kaf dangina kudi, yafi kowa nawa mukami, ga ilmi Kinganshi me ilmi ne ni kuma bani dashi, ban taba zuwa makarantar boko ba, kece kika koyamin saving suna da iya karantun hausa da rubutawa,,, ki gayamin ta yadda za ayi ace anyi kwad on tuwo da Toka? Ai kinga hkn bame yuwwa bane, sannan koda ban girmesa ba jama ah zasu zageni ace dan kudi zan Auresa a misali kenan ke kika damu da wad annan, shi SO ina ruwansa da Kudi ko nasana ko ilmi, So ba ruwansa da wannan, Kinga SO ba ruwansa da kunyar duniyar, meyin SO idanuwansa kullewa sukeyi, baya bukatar a kara masa zafi biyu, ga Zafin SO ga wani zafi can da ban,,,, Cewar hauwa U gabaki daya tinda taga yadda Aeezad keyi na yau kawai data gani tausansa ya cika mata zuwa. Kauda Kai kawai nabeelah tayi danta kula hauwa u bazata fahimci me take nufi ba. A bar mgnr kawai kawata bazaki gane ba . Na hadu da wani tin a kano Sadi, ya kwantamin a rai dukda ba wani fara sanshi nayi ba, amma kawai ya burgeni ne ya hada abinda nakeso a jikin d ana miji, inaga time yayi da zanyi Aure, naji a raina zan iya Aure ynzu a kan wannan bawan Allahn nabeelah ta kare da bawa hauwa u labarin haduwarsu da Alhaji Sadi da yadda akayi suka hadu, ta bata labarin komi bata boye mata ba. Jinjina zancen hauwa u tashiga yi a ranta,. Allah ya zaba abinda yafi Alkhairi shine kawai abinda hauwa u ta fadi yayinda a ranta tunannika tashigayi. Aunty nabeelah ta amshe da Amin amma a ranta tasan Alhaji Sadi nema Alkhairi gareta. Har waje fa zaki rakani napep zan hau zuwa gidan Aunty nafisa, kinsan da dreva ya ajiyeni kawai wucewarsa yayi gurin gyara, motar daman da kyar ta karaso Damu garinnan nabeelah tace Subhanallahi,,, Danma Allah ya rufa asiri duk kin bar yaran gida hauwa u tace . Eh wallahi, inda Allah ya temakeni kenan, da Bansanma yazanyi ba, Kinsan har mutuwa tadinga mana a daji motar nan Kai karfen nasara ba tabbatas gaskiya Allah ya kara tsarewa Cewar nabeelah . Hauwa u ta amshe da Amin yayinda sunaci gaba da tafiya zuwa bakin get. Suna tafe sunaci gaba da hirarrakinsu. nabeelah nata kara bawa hauwa u labarin Alhaji sadi, nan hauwa u ta kara tabbatar da tabbas Alhaji Sadi ya samu matsunni a zuciyar kawarta, domin tinda nabeelah take bata taba bawa hauwa u labari ba a kan wani saurayi. Daga haka suka iso bakin ti-ti, nabeelah na shirin tarewa hauwa u me napep, wata dankareriyar mota tayi packing daf dasu, motar bakace kirin , kirar Mercedes new model ta shekarar, dagani ko ba a gaya maka ba, Zakasan mamallakin motar ba karamin mutum bane , tako ina motar ta tara kyau se wal-wal takeyi Sam karamin me kudi be isa ya hau irin wannan motar ba. Ba bata lokaci ya bude motar ya ziraro kafafuwansa na zallar yan hutu wadanda launin kalar fatarsu daban take data kowa sbda Hutu. tin kafin ya karasa fitowa kamshin danyar shaddar gezner dake jikinsa ta doki kaf hancinayensu. Ya fito sanye da shadda launin C-green se walkiya shaddar keyi kmr bayan maciji, ya kafa hular sakar hannu ta kasar waje, hannunsa sanye da danyen diamond, se murmushi yake sakarwa nabeelah yayinda nabeelah tuni ta ganesa Alhaji sadi ne, tabbas ya kara shiga ransa, dukda bashi da kyau amma komi nasa ya mata. Ina wuni ranki ya dade ya gaishe da nabeelah cikin ladabin da SO kesaka ka koyeshi dole komin girmanka, ko ince komin mukami da isarka, Inkaga mutum na rawar Kai ka kyalesa kawai be afka so bane, SO ne kadai ya isa ya koyar da mutum ladabi da biyayya. Kafin nabeelah tayi magama hauwa u ta amshe da . Bawan Allah lafiya zaka tare mutane a ti-ti bamu sanka ba baka sanmu ba Alhaji Sadi ya kara fadada murmushinsa yace Allah sarki yar uwa kece baki sanni ba ita ta sanni kou? Nabeelah ta daga Kai hadi da Tabawa hauwa u hannu kasa kasa tace Shine wanda nake baki labari okay..yi hkri dan Allah nasha bata sanka bane Ina wuni hauwa u ta karashe da gaidasa cikin girmamawa sbda ko a ido tasan ba sa anta bane. Alhaji sadi daketa washe baki kmr yaga lafiyayyen gindi a bude yace Aaahh bakomai yayarmu ya amsa gaisuwar hauwa u danshi a zatonsa ko itace yayar nabeelah sbda ya ganta wata shirgigiya da ita tanada kyau sosai, amma jikinta da Fuskarta sun nuna masa alamar ta girmi nabeelah nesa ba kusa ba, a zahiri kuwa nabeelah ce ta girmi hauwa u,. Ba yayata bace kawata ce Cewar nabeelah. Alhaji Sadi dake tsaye yace. Af yi hkri kawarmu, kice itace a high table a dinner party dinmu wani murmushi ya subucewa nabeelah, bata taba tsayawa da namiji ba a lokaci kankani ta sakar masa wannan murmushin me tsada ba se yau,. Aiko nan take murmushin yayi tasiri a zuciyar Alhaji Sadi ya kuma narke wa a soyayyarta, nan suka shiga sakarwa juna murmushin Soyayya, ganin sun tafi a juna yasa aunty hauwa u matsawa gefe ta zubo musu idanuwa kawai. Kusan kullum senazo amma sojojin dake bakin get basa barina shiga , na rasa ya zanyi da sanki a raina, wlhi Ina sanki, so nakeyi se kun bar asibitinnan se inje gidanku na turo maganata na, a wacce anguwa kike a katsinar? Cewar Alhaji Sadi. Nabeelah da kanta ke kasa sbda kunyar da take dashi in Tana gaban namiji Sam bata kallansa, musammanma Alhaji Sadi Tana jin kunyarsa sosai, a kunyace tace ni ba yar katsina bace Alhaji Sadi seda ya lumshe ido sbda dadin muryarta daya ratsa shi. Kaji mace, ynzu zanyi Auren macee me aji wadda ko magana tayi se naji gabana ya tashi, ba mace me muryar maza ba Alhaji Sadi ya fadi a ransa, domin shi mutum ne me lafiya, yana bukatar mace, bashi da ciwo ko daya a jikinsa balle yasa al aurarsa rauni, mabukaci neshi sosai. Okay a wani gari kke? Niko yakai nan da birnin sin zanje garin masoyi ai baya nisa Alhaji Sadi ya iya kalamai Kai kace matashi ne dan shekara ashirin da biyar, dan haka nan da nan ya kuma narka zuciyatar nabeelah ya kara burgeta sbda tanaso ta Auri namiji d an soyayya sannan me jaraba, sbda itama tasan jarababbiya ce ta karshe tana tsaka da bukatuwa da d ana miji, kawai kawaici ne da juriya datake dashi, amma dataci ta koshi abu na biyu da take bukata d ana miji, tanada cikakkiyar lafiya itama datakeda tabbacin iya mata se ainifin jarababben namiji. A Niger nake cikin garin agadex cikin mamaki Alhaji Sadi yace haba ni ai nasan da mamaki wannan halittar ace a nigeria kike, ni ai nasha ko balarabiya ce ke ma iyayenki suka kawoki nigeria, ashe buzuwa ce, na kara sanki sosai, wani mataki kk a karatu? Nabeelah da kanta ke kasa tayi shiru bata basa amsarsa ba amma a fuskarta Alhaji Sadi ya fahimci amsarta. Karki damu ina sanki a haka, in mukayi Aure se muje Kasashen dasuka fimu ci gaba kiyi karatu a can, nide Ina sanki so me tsanani, dafatan kema haka ? Rufe fuska nabeelah tayi cikin kunya Alhaji Sadi ya bude baki zeci gaba da magana hauwa u dake gefe ta gaji da tsayuwa tace kawata inaga napep dinnan zan tara, sena dawo zuwa goben kawai naga yammaci na karayi har biyar na neman wucewa Alhaji Sadi ya amshe da Ina zakije? Hauwa u tace nan gidan yayata zanje dake nan hayin d an mani Alhaji sadi yace Toh nagane d an mani, inba damuwa ki shiga se in kaiki kawai hauwa u tace Aah ka barshi kawai zan hau abun hawa kar in katse muku zancenku nabeelah ta amshe da kawai ki hau a kaiki hauwa u inde ba damuwa hauwa u tace ba damuwa wallahi Alhaji Sadi yace To shikenan bari in kaikin,, minti biyu mu karasa mgnr mu hauwa u tace bakomai Ta d an kara matsawa daga inda suke. Alhaji Sadi ya koma Cikin motar ya dakko wata yar leda me azabar kyau pink, ya bude ledar kwalin waya ne a ciki , ya fito da kwalin wayar ya bude, nan iPhone 12prp ta bayyana, ya mikowa nabeelah wayar hadi dacewa Ga wayar danase miki tin rannan bansamu an barni na shiga ba aka cemin sir Ahamad ne ya hana a bar kowa zuwa inda yake nasa miki sim a ciki , kiyi using kafin ki koma gida seki cire sim dinki na dayar wayarki kisa a ciki, in kika shiga ciki seki fara da bude ICloud dinki first kafin ki fara dauko Apps nabeelah ta dago ta kalli wayar dayake miko mata, nan take ta girgiza Kai Alamar meyasa? Ki temakeni ki amsa, sbda innazo se in dinga kiranki ko fitowa ne se kiyi muyi zancenmu in koma base na shiga ba, inaga ma nan da 4days zan koma daman sbda ke nake zaune a garin nan.. nabeelah ta kara cewa Aah ya barshi ita tanada waya. Nan Alhaji Sadi yashiga rokonta Allah Annabi ta Amsa, da kyar ta amsa Sam badan taso ba, ta amsa tashiga jero masa godiya hadi da sakawa dukiya albarka, Alhaji Sadi ya kureta da ido yaji dadin adduarhta garesa, aduniya ba a taba masa adduah data dinga masa ba, ko matarsa da yake aure duk abinda ze bata bata taba masa irin wannan godiya da Adduarh ba, nan take Alhaji sadi ya tabbatar