Sashe 30
Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abokinsa yake Amma ya kula ita hajiya rafi'ah Sam ba ciwon Aeezad bane a gabanta se wasu iskanci-iskanci takeyi. Doctor Nazir ya zubowa hajiya rafi'ah daketa faman hayyako masa kamar zata maresa gashi kowa ya gaza magana a kan abinda take masa ya kula tanada power sosai shi a zatonsa itace mahaifiyar Aeezad. "Bakar tukunya me fidda farin tuwo..." Dr Nazir ya fadi a zuciyarsa ya tsaya kawai kmr an dasashi Be tankawa hajiya rafi'ah ba. "Doctor ga Nabeelah Nan..." Hajiya bilki mahaifiyar Alhaji sunusi ta fadi Hadi da nunawa doctor inda nabeelah ke zaune ta sadda kanta kasa. Nan kallo yadawo kan nabeelah, hajiya rafi'ah taji kmr ta hadiye zuciya ta mutu ta juya ta gallarawa hajiya bilkisu harara dabadan idon mutane ba tabbas dase ta zagi hajiya bilkisu daman tasaba mata takakkiya ta mata zagin babbar bargo, ko ince suyiwa juna zagin babbar bango sbda itama hajiya bilkisu ba kanwar lasa bace cikakkiyar bakatsiniya ce bakatsin Kam kunya garesu bade kara ba, kowa yasan ba a nunawa bakatsine yatsa a maido da yatsa yadda yake. "Ki shigo sir Aeezad na nemanki please..." cewar doctor Nazir Daya zubowa nabeelah ido, wadda ta gaza motsi sbda tsoron abinda hajiya rafi'ah zata mata. "Tashi ki shiga, inga yar ubanda zata hanaki shiga kiga jigana,,,Dan bura ubar mace, inga wake ubanta ga garin katsina..." Cewar hajiya bilkisu data taso da kyar da sandarta a hannunta tashiga takowa zuwa inda nabeelah take a zafafe,, Nabeelah tamike cikin kwarin guiwa saboda maganar da hajiya bilkisu ta kuma Yi, Amma still a tsorace take sbda irin mugun kallon da hajiya rafi'ah da na'eema ke Aiko mata dashi. "bade ubana ba, sede uban wata wlhi, Dan ubana yafi karfinku..." Cewar hajiya rafi'ah datayi maganar cikin tsiwa se zaburowa hajiya bilki takeyi kamar sa'arta. "Ke karki sake ki zagarmin uwa wallahi yanzu zan nuna miki iyakarki..." Cewar Alhaji Abubakar dayayi mgnr a zafafe, duk abinda Rafi'ah keyi be taba magana ba se yau, ta kaishi kwano ne yanzunma sbda zagar masa uwa datake neman tayi a gabansa wlhi dabadan a asibiti suke ba da tini ya mareta. alhaji sunusi yana gani Amma ya gaza magana kamar ruwa yacishi, a zuciyarsa Yanajin tsananin zafin abinda takewa uwarsa a gabansa, Amma ya kasa tafuka komi. "Bismillah shege ka fasa Dan halak se yanka,,,,duk Dan shegiyar daya fasa nunamin iyakata ya raina uwar sa da ubansa..." Cewar hajiya rafi'ah datake mgnr cikin rashin tarbiya da tsananin tsiwa. Ran alhaji Abubakar ya kara baci Ainun Nan idanuwansa suka rufe dominshi a rayuwarsa bayaso ka taba masa uwarsa, yasan darajar uwarsa sosai bayason abinda ze taba masa martabar mahaifiyarsa. Zaburowa yayi ze karaso inda rafi'ah take,hajiya Maryam matarsa ta riko masa hannu sbda bataso a raba abun kunya a asibitin. hajiya bilkisu tayi hanzarin dakatar dashi dacewar. "kyaleta karka damu Kawai Alhaji, duk wanda ya raina iyayen wasu ai besan darajar nasa bane..." "ko kuma wasun ne basu San darajar nasu iyayen ba..." Cewar hajiya rafi'ah idanuwannan kyar na marasa tarbiya. "Pls ya isheki haka,,,wallahi ki iya bakinki,abinda kike fadi a kan hajiya babba yafa isheki fa, ke bakifi kowa rashin kunya ba, kawai Dan iyayenmu na kwab'a mana ne dako Tari baki isa Kiyi a Nan ba...kina Kara cewa Wani Abu a Nan wallahi zan bazar dake...." Cewar babban Dan Alhaji Abubakar Saifudden. Aiko Nan hajiya rafi'ah tayi mukus sbda tasan waye saif ya tafa kusan marinta dayaje gidansu ya zagi uwarsa wato hajiya maryam da kyar aka hanasa dukanta Amma da ya rufe gida ze mata dukan tsiya, saif irin Mutanennan ne Yan a mutu ko Ayi Rai gashi da bakar zuciya, again irinn Yan dabannan ne. Nan bakin hajiya rafi'ah ya mutu se harara taketa aika musu dashi na'eema ta bude baki zatawa Saif rashin kunya hajiya rafi'ah tayi hanzarin kwabarta ta hanyar bige mata hannu dole itama tayi shiru, se harare harare kawai suke bin kowa a gurin dashi. "Kar Wanda ya kara magana please sbda kar mu raba abun kunya Dan wasu sun saba rabawa ba yau farau ba .." cewar hajiya Maryam mahaifiyar Saif. Hajiya rafi'ah ta watso mata wani mugun kallo, Hadi da harara. Saif ya amsa da "Insha Allahu mommy....Aunty nabeelah wuce kiji Kiran da blood Aeezad Ke miki,.." saif ya karashe mgnrsa Yana kallon Aunty nabeelah dake tsaye knta kasa tana sauraren dibar albarkar da hajiya rafi'ah tayi a gurin.kmr tana jira saif yayi maganar ta nufa dakin kanta kasa, doctor nazir Kai kawai ya girgiza a zuciyarsa Yana me kyamar hajiya rafi'ah, ya marawa aunty nabeelah baya zuwa dakin da Aeezad ke kwance. hajiya rafi'ah taji kmr ta hadiye zuciya ta mutu saboda zallar bakin cikin shiga dakin da nabeelah tayi, Amma sede ta dauka a ranta tabbas anci bashi, ita Sam ba a mata abu aci lilis dole seta rama. na'eema ma taji kmr ta mutu Dan takaici tinda tazo bataga mijinta ba, Amma Yana farkawa wai ya tashi da sunan wata banza nanny mara lasisi, "Yar iska ballagaza..." Na'eema ta fadi a bayyane ta yadda mahaifiyarta dake kusa da ita ce kawai taji me tace, juyawa rafi'ah tayi ta kalli Yar tata Nan taga hawaye ya wanke mata kunci, bakin ciki ya kuma wanke zuciyar hajiya rafi'ah. "Kiyi shiru ki barni dasu kawai..." Cewar hajiya rafi'ah datayi mgnr hadi dajan hannun na'eema suka bar gurin zuwa Wani gurin a cikin asibitin, Alhaji sunusi yabi su da Ido kawai a zuciyarsa Ji yakeyi kamar ya rabu da rafi'ah ya huta Amma a zahiri baze iya hakan ba,Sam baze rayu in ba hajiya rafi'ah ba. Nabeelah nashiga dakin tayi tozali da gogan, kwance yayinda kwayoyin idanuwansa ke kallon kofar shigowa, idanuwansa nayin tozali da ita yaji tamkar an basa aljannarh duniya, ya sauke ajiyar zuciya, yayinda Wani irin murmushi ya subuce masa, kallo Daya ya mata ya fahimci tashin hnkli mara misaltuwa Hadi da rud'u a tattare da ita,duk tayi Wani kala kamar tayi ciwon shekaru, yasan duk sanadinsa tashiga wannan yanayin. Karasowa tayi inda yake kwance kan bed din marasa lafiya, idanuwanta kur a kansa, duk yabi ya rame marirrikan data masa suna Nan kwance radau a kan fuskarsa abinka da fuskar hutu, Wani irin tausansa ne ya cika mata zuciya Nan da Nan idanuwanta suka ciko da kwallah,. "Am still love you Mommy, ni ko zaki kasheni wlhi ina sanki!'' Aeezad ya fadi Yana mejin zuciyarsa na bugawa kamar zata fito masa fili yayin da santa ke kara ninkuwa a birnin zuciyarsa, wallahi shi kadai yasan me yakeji a zuciyarsa a kan nabeelah. Wadansu hawaye ne suka wanke masa fuska, yayin datake tsaye jigin gadon doctor nazir na bayansu, doctor nazir dayaji kalaman da Aeezad ke fad'awa nabeelah. kwallah suka ciko mata idanuwa itama Nan take suka zubo kuncinta duk dauriyarta Amma ta gaza daurewa. Ya Miko mata hannunsa wanda ke daure da drip yayin dayan hannunsa an cire masa harsashi sannan an masa dauri, domin harsashin ya taba masa k'ashi guiwar hannu kad'an. Haka kawai ta tsinci kanta da mika masa hannunta itama ta kama nasa hannun gam. Wani irin sanyin ni'ima me azabar mugun dadih ne ya ratsasu su duka Biyun, bakamar mashi Aeezad, ya kara Luntsuma a kaunarta.ya rike hannunta sosai cikin nasa Hadi da zubo mata Ido kwallah na zubo masa, yayin da itama tana kallonsa tana kwallarh, shaf sunma mance doctor Nazir na dakin, ganin haka yasa doctor saurin ficewa a dakin, ya kula sun shiga shauki. Hankalin nabeelah ya Dan natsa yayinda hannunta dake cikin nasa ya sama mata natsuwa me yalwa, irin nutsuwar da ruhinta ke bukata a halin yanzu. "Kuka kika dingayi saboda an harbeni ko?" Cewar Aeezad. Batare datayi aune ba ta tsinci kanta da daga masa Kai alamar Eh. Wani dadih ya ratsa Aeezad tabbas ko makiyinsa yasan yanasan aunty nabeelah. "Kin fara Sone Mommy pls?...zaki aureni Dan Allah? "Ya fadi kmr zautacce,. Lumshe Ido nabeelah tayi ta bude a kansa Sam batason mgnr SO da Aure tsakaninta da Aeezad. Kauda mgnr tayi dacewa "ya jikin naka jarumin nabeelah?" Aeezad ya amsa da "Dasauki Amma Dana ganki ne naji saukin, sanki ya kuma habbaka a birnin zuciyata, ke sinadari ce ga lafiyata! Inajin yawonki a jinin jikina..."ya fadi ba kunyar idanuwanta yakureta da Ido kmr bashi ke kwance a kan gadon asibiti ba, se kalamai yakeyi, zuciyarsa se azalzalarsa takeyi da Azabar santa. Dauke Kai nabeelah tayi ta maida dubanta gefen dakin Sam batason jin kalaman a bakinsa basa mata dadih se daci ma dasuke mata. "Ka yafemin pls?" Ta fadi ba tare data kalleshi ba, still hannunta na cikin nasa, se kara rike hannunta yake gam a cikin nasa, soft and soft sun hadu abun zar dadih. "Me kika min? "Dana mareka..." Ta fadi still bata kalleshi ba. Murmushi Aeezad yayi yayin dayakeji kamar ya jawota ta fado jikinsa yaji duminta yaji dadih, tafin hannunta laushinsa ya shahara ya tabbatar jikinta seyafi tafin hannunta soft. "Bakimin komi ba, Marin da kikamin dankin isa ne kikayiminshi yanzu in Wani ya isa ya mareni mana yagani,,ke isashshiya ce a fadar zuciyata ciki da wajenta,,kina mulki!,," juyowa nabeelah tayi ta kallesa Sam batasan ya iya wadannan kalamanba se yau, mamakinsa kara rufeta kawai yakeyi, duk yabi ya rikide mata ya chanza hali gabaki daya, rashin kunya zallarta kawai ke damunsa, dabadan Yana kwance gadon asibiti ba shi kansa yasan dabe isa ta tsaya Yana gaya mata wadannan kalamanba balle harda rike hannu. "Allah ya baka lafiya bari in koma waje kasamu ka samu ka huta.." Cewar nabeelah. "Aah karki fita ni ganinnki yafimin baccin daxanyi Dadih..."cewar Aeezad. "Meyasa ka chanza halinka , bazan iya zama ba in kana irin wadannan kalaman..." Nabeelah ta fadi Hadi da kwace hannunta daga cikin nasa. "Wani kalaman nayi kawai dannace ina sanki, nifa bacewa nayi inaso naciki ba, sanki nace inayi mommy, azabar sanki nakeyi JARUMA...." Wani irin kallo nabeelah ta Watson masa, wato shi bakinsa baze mutu ba koda yake kwance gadon asibitin se yayi batsa. "Kinga ciwonnan da yake hannuna...." Aeezad yayi mgnr Yana nuna mata hannunsa dake nade da bandeji an sagalesa sama. Nabeelah ta kallah, ta lumshe idanuwanta tin-tini tagani Amma taki kalla sosai sbda tsigar jikinta tashi takeyi, ji taji tamkar a jikinta ciwon hannun nasa yake. "Kingani kou?'' nabeelah ta