← Book details Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 87

Sashe 64

Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

uban gayyar da tinda yayi sujjada be dago ba, seda yayi 10mnt yana kuka, kana ya dago , AlhamduLillah taki barin bakinsa, ya karaso ya rungume aunty nabeelah se faman godiya yake mata cikin sambatu, be taba farin ciki kamar wanda yake ciki ba a yau. Nan take yayima doctor kyautar kujerar hajji, itama nurse ya mata kyautar kujerar hajji,. Suka dinga godiya nurse harda kwallah sbda farin ciki, daki de ya rikice da farin ciki Aeezad se murna yakeyi aunty hafsat da big hajiya ma ba a barsu a baya ba, nabeelah kam bakin ciki suke kara mata in suna murnar nan ta kasa hada ido da kowaccensu sede tayita satar kallansu kmr barauniya. Har wuraren 2;pm kana doctor ta fice a dakin ita da nurse se murna sukeyi kafin doctor ta fita tace da Aeezad ya sameta a office zuwa gobe. Ranar de kwana akayi ana farin ciki da murna, har seda sukayi sallar asubahi kana suka kwanta, drip din daman ya kare tin asubahi aka cire mata, ta kwanta ita kan ta kasa bacci, se kallan cikinta takeyi, tana ayyano yadda za ayi ta rabu da wannan cikin kaddarar dan ita bazata iya da wannan abun kunyar ba. Tini aeezad ya Kira mahaifiyar nabeelah ya sanar da ita, tayi farin ciki sosai, duk nabeelah bata sani ba, daman shi yana boyewa ne sbda iya wuya kar nabeelah ta gudu ta barsa, yasan akwai matsalolin a gabansu yana tsoron in komi ya bayyana kar nabeelah ta koma Niger ta barsa, ynzu kuwa yasan bazata iya barin gidanba sbda tana tsoron inta je can mexatacema mahaifiyarta. After 2days , Aeezad na bawa nabeelah kulawa ta musammanma ji yake da ita tamkar kwai, ya rasa Ina zesata dan murna, aunty hafsat da big hajiya sun fahimci nabeelah bata murna da samuwar cikin shide gogan Sam be fahimta na farin ciki ya hanasa ya fahimta a ganinsu Aunty hafsat kenan , basusan yana ankare da komi ba. Kwanansu uku a asibitin aka sallamesu bayan doctor ta jaddada ma Aeezad banda sex ya barta harnan da 1month, sannan Banda aiki dayawa, banda Yawan tafiya me nisa, sannan adinga barinta tana samun bacci sosai, a takaicede an bata bed rest. Aeezad har rubutawa yayi sbda beso ya mance ko abu daya gudun kar cikinsa ya zube ji yakeyi daman ana daukar Cikin ya dauki abinsa ya rike kayansa,. Zaks ma tini yasani shima yayi farin ciki sosai, dashi aka dinga jinyar nabeelah a asibitin, , kafin Subar asibitin Aeezad yayi kyauta kudi yafi millions of naira. kyauta kawai yadingayi kmr besan zafin kudi ba. Har gida seda yasa aka sake ma maman nabeelah sabo a niger ya zuba mata kayan alatu, bayan sun isa gida yau kawai nabeelah taga mamanta ta kirata ta tambayeta ya jiki, nabeelah tace dasauki, daman tasan bata da lafiya tin randa aka kaita asibiti Aeezad ya sanar da ita aiko se Kira takeyi dasuna asibitin nabeelah ta kula mahaifiyarta na Cikin farin ciki amma batasan Kona meye ba. , nunawa kawaj Ummih keyi kmr batasan komi ba. Ummih tace tayima Aeezad godiya.. se a nan nabeelah kejin ya chanza musu gida har mota yasiya ma ummih da dreva, ta kallesa se kimtsa dakin yakeyi tinda suka dawo yake tsaye sbda beso tayi aiki duk abinda yasan zatayi seya yakeyi da knsa, ita kuma Tana zaune a gefen gado ynzu aunty hafsat da big hajiya suka fita a dakin. Godiya sosai nabeelah ta masa, kan abin Arzikin daya ma mahaifiyarta. Aeezad ya kalleta yayi murmushi yace Abin arziki ai yana jikinki mommy, fatanade ubangiji yasa ki haifamin yarona ko yarinyata lafiya, Allah ya miki albarka wlhi na kara sanki, ke sanadin Alkhairi ce a rayuwata ba tare da tace komi ba ta koma ta kwanta, ita duk haushin komi takeji, Gashi cikinnan tinda ya bayyana se amaye amaye, wai a haka ma dan an kakkara mata drip sosai, Gashi ba komi take iya ciba , abubuwan dake shiga cikinta Kala hudu ne,, daga tasha zuma se taci kilishi , se taci ayaba, se ruwan sanyi, ba abinda tafi bukata kmr ruwan sanyi tana kaunarsa, Gashi ance ta rage sha. Wata iriyar kulawa Aeezad ke bata ta musamman, kullum yana manne da ita, big hajiy da Aunty hafsat ma suna bata kulawa sosai ba kmr ka big hajiya , wuni takeyi Tana dafa mata abubuwan ciye ciye na gargajiya wasu taci wasu ta kasa ci, har kwarama dambu inta mata dambun masara tanaci sosai, tinda aunty hafsat ta mata bayanin Aurene tsakaninsu da Aeezad ba zina ba, tamata bayani sosai yadda zata gane, aiko nan ta kara San nabeelah da d an cikinta, itafa ko ada batasan nabeelsh yanzu Tana santa sbda Tana dauke da cikin jinintan, daman ba yawa ne dasu a family dinba, Gashi big hajiya naso taga jininta sunyi yawa sosai dan haka ita d a kona shege ne tana so inde daga jininta ya fito, ballema tanasan Aeezad sosai, nabeelah tazama yar gata a gidan, duk jarabar Aeezad ya kyaleta sbda tanada ciki, amma daurewa kawai yakeyi ta kula da hakan, inya ganta se yayita kallo, wanibin har yawu yake dalalarwa. Sau uku hawwa u na zuwa dubata tin zuwan farko ta fahimci ciki ne da nabeelah , Gashi aeezad yaki basu guri su zanta, se yau da nabeelsh ta masa dabara tace yaje ya Siyo mata gwaiba, shine ya fita ya basu guri su zanta da hawwa u. Yana fita nabeelah ta kalli hawwa u tace Wai cikine Dani na Aeezad? Da wani ido zan kalli duniya ni nabeelah! Nabeelah ta fadi kmr zata fashe da kuka, ta kuma kyau da fresh ga wata uwar kiba tanatayi ba lallai ka gane cikine jikinta ba sbda cikin yabi hips da nonuwa. Hawwa u da farin ciki a kan fuskarta tace Nafaga kayan arziki, wannan ciki ai d an gata ne, tako ina naga lelebki akeyi musammanma agun Miji tabe baki nabeelah tayi tace lelen me, bayan an cuceka kou.. fuska dauke da rashin fahimta hawwa u tace Kmr ya? kina mgna sekace cikin shege, pls kidena irin wannan abun gaskiya, wani na nema ke kina nuna kmr bakiso tin rannan na kula, se wani abubuwa kkeyi, keda ya kamata kiyima Allah godiya ga miji ya baki Danye sharaf, ga ciki ya baki cikin gaggawa nabeelah ta kuma hade rai sbda ta fahimci hawwa bata San me take ma tsoro ba. Da wani ido zan kalli ummih? Babban bala inma yazanyi dasu hajiya mommy da matarsa naeema wlhi ban shirya daukar bala innan yanzu ba.. hawwa tace Au baki shirya ba, amma shine kika dinga gwale gindi anaci? Kinga wlhi ki nutsu nabeelah , ki bar tunanin wadannan, domin ynzu rabo ya rantse ba abinda suka isa suyi, in rabo ya tsinke daraba bacewa takeyi, ki rungumi mijinki da cikinki kawai Aunty nabeelah, ba abinda su hajiya mommy suka isa su miki tinda basu hana faruwar wannan kaddarar ba aiko kinga ba yadda zasuyi dame zuwa nabeelah tayi shiru kawai badan taji abinda hawwa tace mata ba, duk natsihar daya mata a banza, har tabar gidan, washe gari ta tashi tanata fushi abu kadan seta hau Aeezad da matsifa Sam be damu ba sbda yaji ance wani lokacin masu ciki nada matsifa shiko dukansa zatayi bazece uffan ba, shide ta renar masa cikinsa shine dadinsa, kome zatayi ze dauka kuma ze jure. Se rigima take masa yau, tace mkrnta zataje yace baze yuba, yadinga lallamarta da kyar ta amince ta hakura. Yau kimanin 2weeks da dawowarsu asibitin Sam ya kasa gane kanta, se tayita fushi fushi Tana hade masa rai ko mgna bata masa se yayita mata mgna tayi masa banza, amma Sam beji ya gaji ba, sbda yasan duk halin daya shiga sbda shine. After isha i kwance take a kan bed, shi yana zaune kasan kafafuwanta se mammatsa mata kafafuwa yakeyi, sanyin AC kawai ke aiki da kamshin turarukan wuta a dakin, yanzu shike komi har wankin kayanta nasawa shike mata dukda akwai marching din wanki, da kuma me wanki, amma Sam baya bari su wanke shike wankewa ya gyara mata gashin kai, ya mata wanka har askin gashin gabanta seda ya mata jiya,ya aske mata gashin hammatarta duka, ba abinda be mata. Ta kallesa ta numfasa, se tsotsar wani d an karamin kilishi takeyi a bakinta, sbda in batasa wani abu a bakin nata ba se tayita zubda yawu. Ta kuma numfasawa idanuwanta na kansa ta hade rai tace Nifa gaskiya bazan iya rikon cikinnan ba har yakai 5month ko fin hakan,,,, Aeezad dake matsar mata kafa ya dakata ya dago ya zuba mata idanuwa cikin rashin fahimtar kalamanta yace bangane ba? Kmrya? Dauke idanuwa tayi a kansa tace kamar yadda kaji, gaskiya bazan iya yawo ? Da abun kunya ba, bansan da wani ido zan kalli mahaifiyata ba, uwa uba matarka da hajiya mommy, sbda komin daren dadewa nasan se sunji komi , gaskiya Bazan iya ba, kawai zubda cikinnan zanyi wlhi idanuwa ya zaro cikin mamakin kalamanta nan da nan annurin fuskarsa ya gushe rannan yayi bakikirin. Cikin shege ne a jikinki da kk wannan mgnr banzar? Naga ai cikinnan cikinane ni nayishi kona shege ne inasan abuna, balle na sunnah,,,daman shiyasa tinda akace kinada Cikin kika shiga bakin ciki kiketa hade rai? To wallahi wallahi ki kiyayeni, inna karajin kalmar zaki zubarmin da ciki wlhi se raina da naki ya baci ya fadi cikin fushi. Tashi zaune nabeelah tayi tana kallansa tace cikin matsifa harga Allah batasan cikinnan . Wallahi sena zubar da cikinnan ko ka yadda ko karka yadda ya kalli kwayoyin idanuwanta, nan ya tabbatar da tabbas da gaske take dan ada ya fara tunanin wasa takeyi. Murya babu alamar wasa yace Wallahi Billahillazi na Miki rantsuwar d an musulmai, In kika zubarmin da ciki wlhi wlhi nabeelah kinji na kuma rantsuwa, wlhi sena daureki, kaf danginku ma sena musu daurin rai da rai, ummih ce kawai zata tsira sbda ina ganin darajarta, amma wlhi wlhi dake, da wanda tasa hannu , da wadda ta zubar min da cikina, da asibiti da aka zubar min da cikina, da makarantar da wadda ta zubar min da cikina tayi dukse na hadsu dake duka na muku daurin rai da rai har
Chapter 64 · 0% Book details