Sashe 37
Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nabeelah tasamu karatun addini me zurfi. Nine da godiya fatanade Allah ya nunamin ranar Aurenmu nabeelah tayi murmushi kawai, daman tini alhaji sadi ya fahimci yarinyar nada kunya me tsanani. Shikenan se munyi waya bari inje in kai kawarmu, zuwa anjima zan kiraki Cewar Alhaji sadi. Nabeelah tace Toh hadi da kara masa godiya har seda yace ta isa hakanan godiyar, kana nabeelah tayi shiru, ta Kira hauwa u dake kallon komi dasukeyi jinsu ne kawai batayi, ta nuna mata wayar da Alhaji yase mata nan hauwa u ta masa godiya itama, Alhaji yace bakomai. Hauwa u tashiga motar Alhaji Sadi gidan gaba, sadin yashiga dreva side, ya sauke glashinsa ya kure nabeelah da ido se murmushin SO da kauna yake sakar mata ki kula da kanki,,,, nabeelah ta daga masa Kai alamar toh, kana Alhaji ya juya motar yabar gurin idansa na kanta har seda ya kule ya dena ganinta kana ya rufe glass dinsa, nan ya farawa hauwa hirar irin San da yakewa nabeelah hauwa u najinsa ne kawai, amma a ranta tasan San da Alhajin sadi kema nabeelah ba komai bane ,akan San da Alhaji Aeezad ke mata a duniyar nan hauwa u ta tabbatar nabeelah bazata taba samun me mata San hauka kmr yadda Aeezad ke mata. Seda nabeelah tadena hango motar Alhaji sadi kana ta koma cikin asibitin wayarta rike da ledar dake dauke da kwalin wayar. A harabar asibitin packing space nabeelah taga motar Zaks, tin tsayuwarta ba jimawa taga motar zaks din tashigo asibitin amma bata lura da motar ta Zaks bace se yanzu dataga lambar motar domin kusan lamba daya suke using , lambobin mota daya suke using Aeezad da Zaks. ba tare da nabeelah tayi wani tunani ba, ta nufa ciki. Tana sako Kai ta gansa tsaye a falo, yayinda zaks ke tsaye kusa dashi yanata basa hkrin da nabeelah batasan ko hakurin meye ba, batasan tin shigowar Zaks daya ganta tsaye da Alhaji Sadi, yazo cikin raha ya sanar da Aeezad naga mamanka me kayan Alayu tsaye jikin wata mota tana zance da wani Alhaji me tumbin kudi Ai nan Aeezad yaji kamar an tsikaresa ya tashi a gigice, daman yaga ta juma sosai, big hajiya dake kusa bataji me Zaks ya sanar da Aeezad ba, kawai sede taga ya mike tsaye a gigice. Meya faru me suna me daraja? Big hajiya ta tambayi Aeezad wanda keta huci. Bakomai big hajiya.,. Kawai shine abinda Aeezad ya fadi besanma ya fadi ba sbda baya hayyacinsa ya fice a dakin gabaki daya kishi ya rufe masa ido da kyar yake tafiya, tinda ya fara ciwo be taka kafarsa ba se yau, ko ranar dasukaxo asibitin har kofar dakinsa mota ta kawosa ya fita taku kadan ya isa cikin dakinsa dake kasa downstairs. Hajiya se tambayarsa takeyi ina zeje amma Sam bejita ba ko ganin hnya beyi sosai ya kosa yaje wajen ya tabbatar da Abinda Zaks ya gaya masa. Hajiya zamuje ne ya d an zagaya Cewar Zaks. Big hajiya tace Toh ze iya tafiyar kou? Kode inzo in rikesa ne? Naga har yanzu nabeelah bata dawo daga rakiyar hauwa u ba balle ta rakasa ita ,,, Zaks yace Karki damu big hajiya ni bari in bishi, Big hajiya tace To d annan ka kulamin da jikana kagade hannun nasa ba wani warkewa yayi ba ni bari in shiga wanka Zaks yace To hajiya kana ya fice a dakin ya biyo Aeezad, nan bakin get ya gansa ya zubowa nabeelah da Alhaji Sadi dasuke tsaye ido , zuciyarsa ta cunkushe kmr zata tarwatse idanuwan nasa sukayi red, da badan nabeelah da Alhaji Sadi sun afka a kogin soyayya ba Tabbas dase sun hango Aeezad sbda basu da wata tazara sosai. Kaga renin hankali kou ? Ashe tad i zatazo yi, ta tsaya da wani shege se murmushi take masa, bari in karasa in kasheshi kowa ya huta Aeezad ya fadi a zafafe sbda bacin rai da kyar muryarsa ke fita. Zaks ne ya rikosa da kyar yashiga basa hkri, Ada yaso ya isa inda suke, Zaks yayi nadamar fada masa da yayi, tini Zaks ya fahimci Aeezad nasan nabeelah amma daya tambayesa yace masa kawai San uwa yake mata last zuwansa sukayi wannan maganar. Aiko zaks yaga hauka da kyar yasamu ya jawo aeezad zuwa cikin falon dakinsa, yashiga dannar masa zuciya yadda ya rikice wa Zaks din ba karamin tsoro ya Bashi ba, Tabbas Zaks ya kuma tabbatarwa da bakaramin SO Aeezad kema nabeelah ba, San da duk wanda ya rabasu dole se ubangiji ya kamasa. Nan ya kara rikicewa Zaks da kyar Zaks ya dinga basa hkri har yasamu ya tsaya a falon amma da dakinsa ze nufa ya dakko bindiga yaje ya kashe Alhaji sadi, ran maza ya baci nan take allurar sojojinsa ta motsa ya gigice ya zama kmr bashi ba, a haka nabeelah tashigo tasamesa tsaye ya zubo mata red eyes dinsa jikinsa se rawa yakeyi bata taba ganinsa a yanayin data gansa yanzu ba, dan haka nan take ta tsorata. Daga gun dan gidan uban wa kike? Aeezad ya tambayeta cikin kunar zuciya muryarsa ta kuma disashewa sbda zallar bakin ciki da azababben kishinta da yakeyi. Yadda yayi mgnr yasa jikin nabeelah rawa, nan take taji wani irin tsoronsa ya rufeta ledar dake hannunta ta fadi, itama ta gigice sbda bata taba ganinsa a yanayin da yake ba yanzu, yadda ya mata tambayar ya tabbatar mata da kila yaganta ne da sadin, sbda ta kula da kishin dake kwance Cikin fuskarsa. Ni zakiwa iskanci da wulakanci da cin mutumci, Ina tambayaki kinyi shiru munafuka!. nace daga gidan uban wa kke? Ya kara tambayarta Cikin tsawa Tabbas da muryarsa na fita dole se big hajiya dake ciki taji. Zaks dake tsaye yace pls sir ka sassauta dan Allah shi kansa Zaks din hankalinsa a tashe yake. Nabeelah kam Tana tsaye jiki se rawa yakeyi. Bazan sassauta ba Aeezad ya fadi cikin matsifa yana kallon Zaks, Zaks be kuma mgna ba ganin bala i na neman dawowa kansa. Ke bada ke nake ba? Aeezad ya fadi yayin da yake nufo kan nabeelah gadan gadan tsoro ya kara kamata ganin yana tinkarora, tayi hanzarin cewa murya na rawa daga daga .daga, .rakiyar,,,,hauwa,,,,u Hauwa un ubanwa? Ni zakima karya? Kina wasa dani kou? Ni zakima karya dan wulakancin banza da hofi zaks kaji me take cemin kou? Kaji Tana min renin hankali bayan na ganta tsaye da Tsinanen nan tanata masa murmushi kmr kanin ubanta, ashe ke mayyar maza ce bansa ba, ni zaki mayar dan iska, toh yau zan tabbatar miki ni waye a duniyar nan yana mgnr ne bayan ya karaso daf da ita duk yabi ya rud e ya rikice hankalin nabeelah kam in yafi dubu seda ya tashi . Easy mana pls sir,,, kayi hkri Cewar Zaks daya fadi a tsorace dan shima tsoronsa yakeji sbda kar yadawo Kansa dan yanzu in ya rufe nabeelah da duka shi ba iya kwantaeta zeyi ba dukda hannunsa daya ne me lafiya. Durun uwar hakuri zanyi,,, ni wannan yarinyar zata renawa hankali wlhi bazan hakura ba! Aeeezad ya fadi yana kallon Zaks, nabeelah jiki se rawa yakeyi yayinda kalmar daya fadi ta yarinya ta tsaya mata a rai a zuciyarta tace Lallai raininsa ya shahara wai yau itace Aeezad kecewa yarinya a zahiri de babu bakin mgna sbda tsoro. dukawa Aeezad yayi ya dauki ledar da nabeelah tashigo da ita ta wurgar a kasa, ya fito da waya da makudan kudi rafa daya na dollars , Sam nabeelah batasanma Alhaji Sadi yasa mata kudi a ciki ba Tasha waya ce kawai a ciki. Ni zakima karya? Kince daga gun hauwa u kk? Waya baki wannan wayar da kudinnan? Nabeelah tayi shiru yayinda kmr muryarsa zata fasa mata dodon kunne sbda daf take dashi. Bada ke nake mgna ba ni zakiwa wulakanci,, wlhi wlhi senayi maganinki, wani dan Tsinanniyar ne ya kawo miki wayarnan da kudinnan!? Ya karashe hadi da buga wayar da kasa cikin zafin zuciyar dashi kansa besan yanadashi ba se yau, nan wayar ta tarwatse a kasan tiles ta fashe ta gaba ta baya, ya wurgar da ledar kudin dake hannunsa ya dago hannunsa me lafiya, ya watsawa nabeelah wani irin mari me tsananin zafi ji kake tasssssssssss! Wani irin zafi ya ratsa fuskar nabeelah zuwa kaf jikinta nan take ta farajin kukan tsintsaye na mata shawagi a cikin brain dinta sbda azabar zafin dataji na marin, nan take ta dafe kuncinta wasu zafafan hawaye suka wanke mata kunci, ga zafin Marin daya mata ga zafin wai yau itace karamin yaron data raina ya mareta, a haihuwar kaji tini zata haifesa . Zaks dake gefe yaji tamkar a fuskarsa Aeezad yayi marin. dan Allah kayi hkri mana Zaks ya fadi hadi da karasowa inda Aeezad da nabeelah ke tsaye. Sam ma Aeezad bejisa ba. Aikin banza aikin hofi,,,ni zakima haka, ni zaki ma wannan iskancin kinje gun namiji kina min karya saboda reni,,,wannan yarinyar har ta isa ta renani wlhi baki isa ba kedin banza da hofi, Wulakancinki na banza, wlhi baki isa ba, yau zan maganinki, yau zaki gane waye ni , gabaki daya karyar iskanci kkyi Aeezad ya fadi a zafafe yayin dayakeji Sam be huce ba dukda Marin daya mata,. A matukar wani zafin Aeezad ya fito hannunta da hannunsa me lafiya ya fisgota suka fice a falon zuwa farfajiyar Asibitin Zaks ya biyosu yana tambayar Ina zakaje da ita? Ina Sam Aeezad bebi ta kan zaks ba, nabeelah ta kasa katafus se janta yakeyi kikiki kmr tsohuwar mota, yayinda har yanzu hannunta ke dafe da kuncinta. Tinda Aeezad yajata basu tsaya ako ina ba se a bakin motar zaks, tinda zaks yaga ya tinkari motarsa tini ya bude motar kafin ya kara sa, Aeezad ya bude gidan baya ya wurga nabeelah ciki, ya bude gidan gaba fannin me zaman banza ya shiga ya kulle motar da karfi Kai kace motar ce ta masa lefin. Ba tare da zaks yajira Karin bayani ba domin shima a tsorace yake da Aeezad duk ya chanza kamanni, cikin hanzari kawai Zaks yashiga dreva side yayi reverse ya fice da motar a asibitin ya jefata titin yamma, ba tare dayasan ina zasuje ba , kuma yana tsoron tambaya,