← Book details Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 87

Sashe 72

Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta fita daban wallahi) Na'eema ta fara fuskarta tasawar cikin nabeelah tin jiya ta fara fahimta Amma se tasha ko tumbine kmr yadda uwarta tayi tsamnanin hakan,. To yau da nabeelah na serving dinsu a breakfast seta kuma ganin de Abu kmr ciki, se kallon Nabeelah de takeyi wadda keta faman boye cikin jikinta, Amma Ina baze boyu ba saboda tsananin girnansa, duk wanda ya kalleta a natse dole ya fahimci akwai ciki jikinta. ita kanta hajiya mommy Sebin Nabeelah takeyi da idanuwa Kawai so takeyi ta gaskata zarginta, Amma de abu ne gashinan baro-baro.tinda naeema ta daura idanuwanta a kan Cikin jikin nabeelah taji hantar cikinta ta kad'a. bayan sun gama break, hajiya mommy ta nufa dakinta tana amsa waya, na'eema ta biyota dakin ta taddata zaune gefen gado tana wayar da bokanta a kan kasuwancinta sbda so takeyi ta kara bude Wani shagon,yanzu shagunanta sunfi biyar, na shida takeso ta bude. Naeema ta karaso bedside zata zauna uwar ta dakatar da ita da hannu sbda inta zauna mata a bedside tana iya lalata mata drower din side din, gashi gado na manyan kudade. na'eema ta fahimci me take nufi Dan haka ta zauna kasan carpet tana hade rai, ita ta rasa me uwarta ta maidata kawai Dan tayi kibarnan shikenan, ita Sam mafa bata ganin kibar tata, duk Wannan nonuwan nata Dake reto bata gani, nonuwa him bra sede tase ta manya-manyan mata irin manyan cups dinnan Kai kace katon kan mutum za asa, inta cire bra ta ajiye ko uwarta inta gani tsorata takeyi, itade tasan yarta nada nonuwa Amma ba kmr na yanzu ba da tayi year kibar ban. Allah-Allah na'eema tadingayi uwarta ta gama wayar ta shaida mata abinda tagani Amma Abu yakici yaki cinyewa,. Seda Ta jima tana wayar kana ta ajiye wayar, Kuma bata tsaya jiran cewar naeemar ba ta tashi ta nufa hanyar fita tana fadin "bari inje part din baban Aeezad..." Ta fice ba tare data tsaya jinn me na'eema zatace ba. Haka na'eema ta tashi ta fice a dakin, ta nufa part dinta da aka ware mata a gidan da tunani a ranta tayi wanka ta kwanta, kawai so takeyi ta tabbatar da dagaske cikine jikin nabeelah, domin itade idanuwanta ciki suka ganar mata. A bangaren nabeelah a tsorace take Sbda ta fahimci an fara Gane da ciki jikinta Aiko a tsorace take. Da yamma misalin karfe hudu da Rabi,falon Hajiya mommy cike yake taf da jamaah kaf kawayenta be yanzuma se na'eema, khady bata Nan tana gidanta tazo dazu da azahar zuwa karfe uku ta tafi. Nabeelah keta zirga zirga a Falon tana jide musu manyan tray cike da kayayyakin lambu na Motsa baki, wato kayan fruits nau'ila daban daban. Kusan seda ta kawo tray tara wannan ne na taran shine wanda ta ajiyesa a kan table din gaban Hajiya mommy wadda suke zaune gata ga Hajiya naja'atu, se na'eema hajiya mommy din akasa a tsakiya. Bayan nabeelah ta ajiye tray din a kan table din su hajiya mommy, tayi-tayi ta tashi Amma ta gaza tashi, saboda kafarta data makale , seda ta tsugunna sannan ta ajiye tray din, kafarta ta rike gam, tayi tayi ta tashi ta kasa. Hajiya mommy da na'eema da hajiya naja'atu suka zubo mata ido. "Lafiya kika zauna kinata kallonmu kmr kinsamu TV,,,," hajiya mommy ta fadi tana kallon Nabeelah a wulakance. Na'eema ma ta kureta da ido, the more tana kallanta se taji zuciyarta na azabar bugu. "Kafata ce ta rike..." Nabeelah ta fadi a tsorace, sbda yadda hajiya mommy ta mata mgnr, zabura tayi ta mike da duk karfinta da kyar tasamu ta tashi tana Nishi da haki, ji tayi kmr an rike mata kafar ta-ta cikin hanzarin ta bar Falon. Na'eema da hajiya mommy suka kalli juna Sbda cikin dasuka gani baro baro a jikin nabeelah. Hajiya naja'atu ma ta gani tin shekara jiya datazo tagani, Amma we tayi shiru a tunaninta sun sani, ynzu ma tanaso tace Wani Abu Amma tayi shiru. Na'eema ce tace "Mommy naga Wani abu...." Ta fadi yayinda zuciyarta ke bugu, kowa hankalinsa na can suna kallan TV Kuma suna hira Dana kusa dasu, Hajiya naja'atu Kam idanuwanta na kan TV. Hajiya mommy da itama zuciyarta ke mugun harbawa, ta kalli na'eema tanaso tayi Mgna Amma ta kasa magana. Sede ta tsinci bakinta dacewa "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" Itace kalmar dataketa maimaitawa , Apple ne a cikin bakinta Amma ta kasa hadiyewa sede ta fiddosa waje, ta ajiye a gefen tray din. Dai dai Nabeelah ta dawo falon da Wani tray din ta ajiyesa a dayan table din Wanda shi kadai ya rage ba'a ajiye tray din a Kai ba. Zuciyar Nabeelah se bugu takeyi, bugun da bata tabajin irinsa ba ta juya zata bar falon, cikin hanzari hajiya mommy ta mike ta kawo mata hijjabinta ta baya cikin zafin nama. nan ta dakatar da ita sbda shakurewar datayima wuyanta data RIKO mata hijjabi har kakarin amai tashiga yi, nan take hankalinta ya kara tashi bugun zuciyarta ya kara yawaita, seda d an cikinta yayi wata iriyar mummunar harbawa, ta cire hijjabin jikinta kawai sbda neman shidewa da takeyi ta zube kasan kafafuwanta cikin dimauta da tashin hankali mara misaltuwa, bata ma hayyacinta Sam sbda tashin hankali, takai hannu ta rufe cikin jikinta, shi kawai take ji. Nan idanuwan kowa na falon ya dawo kansu dan ganin meke faruwa. hajiya naja atu tayi hanzarin cewa hajiya meye haka zaki shakurewa mace meciki wuya? Kuma tsohon ciki bayan da kyar kake numfashi in kanada tsohon ciki , aise kisa numfashinta ya daukee Hajiya naja au batasan mugunta ita Sam. . Juyowa tayi ta kalli naeema wadda tini itama ta mike tsaye, a tare ita da naeema suka kalli hajiya naja atu suka hada baki gun cewa Ciki? Naeema seda ta dafe kirjinta sbda wani azababben bugu da yakeyi. Innalillahi wa inna ilaihirraju Itace kalmar da nabeelah ta fadi a zuciyarta, ubangiji ne kawai yasan a wani Hali take ciki so takeyi tayi kuka ko zata samu nutsuwa a zuciyarta amma ta kasa, yaude asirinta ya gama tonuwa, d an cikinta kuwa se azababben motsi yakeyi, motsin dabe taba irinsa ba se yau, in kasa ido har ta saman rigar jikinta zakaga harbawarsa, takai hannu ta RIKO kasan cikinta hadi da rintse ido, ta sadakar yau, daman jiya kwana tayi muggan mafarkai, ta RIKO cikin jikinta gam, a ranta Adduah takeyi Allah yasa kome ze faru ya tsaya a kanta kawai kar a taba mata ciki, yau ta tabbar har kasheta hajiya mommy na iyayi,. "Cikin shege! Haba biri yayi Kama da mutum, amma cikin shege a family din Alhaji Sunusi,, tabdijan! Hajiya mommy ya fadi afirgice, zuciyarta na tsananta bugu, ta rasa dalilin dayasa takejin tashin hankali a kan cikin jikin yarinyar. Sbda tashin hankali Nabeelah taji kmr zuciyarta ta fito fili, se azabar bugu takeyi, ta rasa Ina zatasa rayuwarta taji dadih, ji takeyi kamar zuciyarta zata buga, se Adduah takeyi, ta rasa ma Wacce Adduah zatayi sbda tashin hankali tayi kasa da kanta, danma ubangiji ya rufa mata asiri, ta basu baya . Hajiya rafiah ta karasa ta juyo ta da ita ta yadda zata fuskanceta sosai ta tabbatar tabbas ciki ne a jikin yarinyar.ta kurama cikin jikinta ido , idanuwan nabeelah na kasa, jikinta se kakkarwa yakeyi ta tallabo cikinta ta rike sosai kmr za a kwace mata shi, ita cikin kawai takeji batajin ta kanta, abinka da zuciyar uwa, cikin se mugun harbawa yakeyi, hankalin nabeelah inyafi dubi seda ya tashi. A kallo uku hajiya mommy ta tabbatar da ciki ne a jikin nabeelah kuma tsoho, ta tabbatar kuma hafsat nada masaniya a kan cikin, koma menene da bakinta zata fadi sbda ba karamar azaba zata mata ba yau. Naeema ta matso daf da nabeelah nan ta kara ganin cikin baro-baro, ta kuma dafe kirji, tashin hankalin data Shiga baze misaltuba, ta kumajn tsanar nabeelah sosai, haka itama hajiya mommy nan take ta kumajin tsanar nabeelah sosai. Kowa de ya zubo ido amma Sam basu fahimci meke faruwa ba. A gidan uban wa kika samo ciki? A gidan wa kika samo cikin shege? Yau se kinci uwarki da uban ubanki, yau sekin gayamin cikin waye wannan jikinki? Inmates hafsat ce ke Miki kawalanci yau duk senaji komi Hajiya mommy ta fadi cikin tsawa da karad i. Jikin nabeelah ya kuma daukar rawa, ta kumayin kasa da kanta, hajiya mommy ta kuma tambayarta cikin tsawa Cikin waye ga jikinki? Nabeelah ta kasa mgna se azabar bugu da kirjinta keyi ta lumshe idanuwanta gam gam. bake ake tambaya ba dan ubanki! Ni daman na tsaneka wlhi, ne kaunarki ma bansansa,,, yau sekin gaya mana wani dan iskan ne ya miki ciki? Zakiyi magana kose jikinki ya gaya miki naeema ta fadi jikinta na tsuma, ji takeyi kmr tayi ball da ita da cikin jikinta, inda Hali ma Tana iya zama ajalin cikin jikinta, kawai taji ta tsani cikin sosai. Nabeelah tayi shiru ta kasa cewa komi kawai se kukan zuci takeyi,jikinta se kara rawa yakeyi.. hajiya rafi ah a hasale tace Dan ubanki uban wa ya miki ciki? Shegiya karuwar banza, daga yau zamanki ya kare a nan gidannan, zakiyi magana ko baza kiyi mgna ba yar iska ta kama ciken shege ta rike, dan kutmar ubanki ki gayamin uban wa ya miki cikinnan na jikinki? Nabeelah ta girgiza Kai ta kasa mgna kawai se yanzu taji kwallah masu zafi sun wanke mata fuska,. Hajiya rafi ah ta dagota da hannu daya ta wanketa da uban marirrika guda hudu, a Dukkanin kuncinanta biyu. Zafin Marin ya shigeta amma ta kara RIKO cikinta sosai ta fashe da wani irin kuka mara hawaye na zallar tashin hankali, se ihun haka kawai takeyi. Uban wa ya miki ciki? Hajiya mommy ta kuma tambayarta, still tana rike da bayan wuyanta ta riketa gam ta bayan wuyanta. Bazaki gaya mana uban wa ya miki ciki ba? Cewar naeema hajiya rafi ah ta Ansha da jeki ciromin wayar injin wallahi yau nice ajalinki da cikin jikinki, Nima ai ba kaunarki nake ba, dan kutmar ubanki yau zan kasheki na kashe banza na kashe hofi ba abinda aka isa Amin naeema ta nufa kitchen domin ta ciro bulalar jikin babban injin nika dake
Chapter 72 · 0% Book details