Sashe 79
Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bacci ya dauketa. Se shabiyu hajiya Maryam suka bar gidan,big hajiya ta nuf dakin da Aeezad da nabeelah suke da babys a hannunta, tana fadin Dani suke zancen. Itama Nan daKin ta kwanta tsakiyar Aeezad da nabeelah, danma gadon uban fadi be dashi se mutun biyar su kwanta basu matsu ba,babys Kuma Daman an riga an shirya musu gadonsu Nan ta kwantar dasu, Aeezad Yana farkawa yaga big Hajiya a tsakiyarsu, Allah yaso be Kai mata raruma a nono ba, girgiza Kai kawai yayi a zuciyarsa yace "Nida matata..." Kawai ya tashi ya bar dakin ya koma dakinsa, big hajiya ta masa kora da hali Wanda yafi kora da sanda, ya saba kwana yana tattaba nono yanzu Kuma se a hnkli besan yaze kasance ba. ummih Daman an bata dakinta can ta kwana, Daman ita ba Wani bacci take ba, ibada take tayi tanawa yarta da jikokinta Addu'ah,toh ynzu ta Kuma kara zage dantsi gun musu Adduah,. Washe gari tin da duku-duku Hajiya mommy da na'eema suka bar gidan ko asibitin Basu fara Zuwa ba, suka nufa gurin boka can cikin daura. Bokan na ganinsu ya kyalkyake da dariya irin ta wad'anda aka Cirewa Imani gabaki daya yace "wato magana ta fito Kenan...tinda na ganki da yarki asiri ya bayyana,,,,hahahahahaaaaaaa.." se yanzu naeema ta Kuma tunawa da abinda bokan yace Ashe tin lokacin ma da auren Aeezad da nabeelah, da ynzu Wani labaarin akeyi ba wannan ba Amma tunaninsu ya bace, in Abu ze faru de baka da tsumi baka da dabara. Hajiya mommy ta bude baki zatayi mgna bokan ya dakatar da ita dacewa "Aita haifa wannan Cikin yau ma yaran kwanakinsu tara....hahahaha duk Ina biye da taurarinku, a taurarinki nake ganin meke faruwa, Aiki aka mata aka cire mata yara Yan Uku!!!'' ya kwashe da dariya dajin ya amsa. Dukkaninsu hantar cikinsu ta kad'a suka kalli juna, Hajiya mommy seda ta tsugunna sbda tashin hankalin tace "Yanzu shikenan inya mutu komi na yaran ne Kou boka mu Kuma se abinda Muka gani?" Bokan yayi dariya yace "Da wuya ma kugani .." a wannan karan itama na'eema seda ta tsugunna, dukda ita bayan kudin da takeso tanasan mijinta ma, . Hajiya mommy ta daura hannu a ka tace " Nashiga uku ni rafi'atu! Wace iriyar matsifa ce ta tinkaroni nida diyyata ...ynzu yaza ayi boka? ka temakeni boka ka kashemin yaran first ita uwar a haukatata, irin haukan dazata dinga yawo tsirara, sannan asa mata warin tamkar warin sabon ZAWOOO, inda hali ma asa mata Fiye da haka... A fara Dasu Daga baya Ayi ta uban gayyar... " Bokan ya kyalkyale da dariya yace an gama. Se yayi Shiru na wasu dakiku, kana ya kuma fashewa da dariya yace "Zeyi wahala wannan aikin domin kullum Cikin Azkar suke da yaran, dadin dad'awa dukkaninsu suna wanka da Wani magani Wanda bamu Isa muje kusa dasu ba,, sede ku bari in an samu damarsu a aiwatar da wannan aikin...." Na'eema ta fashe da kuka kawai, tana rokon boka ya temaka mata, ko kashe nabeelah ne yayi ita da yaran. Hajiya rafi'ah itama ji take uwa ta fashe da kukan Amma ta dake tasan aikin babba ne tinda har boka yace aikin ze wahala. "ka temakamin boka, bani dame temakona sekai boka, ka dubeni boka, ka rufamin asiri boka, karka bari suka karshena, banasan wannan yaran da uwarsu duka, gabaki daya komi nawa na neman kalacewa..." (hajiya rafi'ah ta mance da duk duniya bame taimakonmu se Allah) Boka ya kyalkyale da dariya yace "duk karki damu hajiya, ke zakiga bayansu, kin taba ganin nasa Abu a gaba banyi galaba ba? Zanta bibiyarsu harse nayi galaba a kanku ki kwantar da hankalinki....kuje gida kuyi bacci kawai..harshi uban gayyar bazan barsa ba, sena dawo dashi ga yarki tamkar yaro mara wayau... ." Ya Karashe Yana kwashewa da dariya. Nande hajiya da na'eema suka dinga magiya boka yace karsu damu, suka ajiye masa uban kudi suka koma gida na'eema ke driving motar, Amma hankalinta tashi yake, dukkaninsu bame mgna kowacce tashin hankali ya shafe tunaninta. Ranar ko asibitin Basu jeba, dukkaninsu ji suke damn mutuwa sukayi da wannan Labarin. Ranar haka suka wuni jugum jugum kamar an Aiko musu da sakon Mutuwarsu yanzu-yanzu. Alhaji Sunusi ya kula da yadda suke kmr marasa lafiya ko abinci basuci ba. Ya tambayi Hajiya mommy lafiya de ko tace masa lafiya Lau kawai Amma inside Abu na nukurkusarta, ta kula alwalar safe na Neman kaita la'asar, ta raina d'an hakki gashi ya shiga idonta ya addabeta da yawo Tako Ina. Ta tambayi Alhaji Sunusi nabeelah ta haihu Ashe? Nan Alhaji yayi mamakin yadda akayi taji Amma seya Waske yace shi be sani ba, ya nuna mata ma besan mgnr gudun kada Allura ta tono garma. Ranar de bacci gagarar Idanuwan Hajiya mommy da na'eema yayi, Abun har ya fara basu tsoro da mamaki, wai me Aiki tazo har gida ta Aure ma yarta miji, tsohuwar mace, kuma ya juyawa yarta baya ita da take sabon jini ya komawa tsohuwar mace. wannan abun a duba ne, ko yanzu nabeelah ta gushe tasama na'eema da Hajiya mommy bakin Cikin da baze gushe ba har abadan, Kai Wani abun fa dole sede insun kwanta Dama, basuga abinda zasuyima nabeelah ba su samu sassauci.. Karku manta Muna saida kayan gyaran Aure akwai pridal package manyan mata Kuma ba a barku a baya ba kuzo ku gyara jikinku a sabanta jiki. 08101626484 This book is 1k 08101626484 NAMIJIN ZUMA 51.... Bayan dawowarsu Asibitin da kwana hudu aka fara shirye-shiryen suna, Anata shirye-shirye domin so akeyi Ayi bikin suna irin wanda ba a taba irinsa ba a kaf duniya.anata tsare-tsare da Aunty hafsat, tini har an kama kaf hall din dake cikin garin katsina, tin ana saura 3days sunan Yan ukun, w'anda Aunty hafsat ta musu Lakani da Manaal itace me sunan Mahaifiyar Nabeelah, Mushfiqa itace me sunan Big hajiya, Mahnoor itace me sunan mahaifiyar AEEEZAD,. Alhaji Sunusi ya kuma wa yaran akwatunan fitar suna kowacce dozing-dozing, kana yayima nabeelah akwati biyar cike da kayayyakin alfarma. Aeezad Kam kayan fitar suna akwatunan dozing biyu yayima nabeelah, yaransa Kuma ya musu dozing biyu-biyu DUk daya seda aka mata akwati dozing biyu na zallar kaya na Alfarma kawai. Yawancin kayan da Aeezad yayima nabeelah a fitar sunan kusan Shima yayi irinsa. ana saura 2days sunan tafiya ta kamasa zuwa Kano haka dole bdan taso ba, ya bar yaransa da nabeelah da santa ya kuma ninkin ma ninkin a zuciyarsa. Seda ya Isa garin kanon yaga Ashe kiran a kan Alhaji rabi'u ne da tawagarsu, Wanda aka kamasu a gurin Wani boka matsafi, sun kashe wani sun kai masa zeyi tsafi a kan a raba Aeezad da duniya, shine akaje kama bokan saboda n kama wata mata asibiti taje satan jarirai, dataji duka shine tace bokan ne ke sata Wannan sana'ah tsawon shekaru ashirin tana masa Wannan Aiki na satar jarirai a asibitoci. Da akaje kama bokan shine akaga su Alhaji rabi'u sun kawo gawar mutum namiji d an shekara Ashirin da uku. Daman sojojine sukaje kamo bokan. Da aka kawosu office sukaji duka shine suka fallasa komi har barin dasuka kaiwa Aeezad, komi akayi recording aka bawa Aeezad yana isowa garin kanon yaji, yayi mamakin meyasa suke binsa da bita da kulle bayanshi besanma da zamansu a duniya ba, tare suke aiki amma su Sam besan da zamansu ba, su kawai burinsu su kashesa Alhaji rabi u ya maye gurbin kujerar Aeezad. Nande aka tura Alhaji rabi u da tawagarsa kotu, duk yadda sukaso su kubuta beyu ba, nande aka yanke musu hukuncin daurin rai-rai a gidan yari,. Allah yasa mufi karfin zukatanmu. Kwanan Aeezad daya a kanon ya dawo garin katsina, aka cigaba da shirye shiryen suna daza ayi gobe insha Allahu,. Zuwa ynzu hajiya mommy da naeema suna samun labarin komi ta hanyar wata kawar naeema sumayya wadda take kawar hawwa u ce aminiyar Nabeelah da ita ake komi, ita kuma da sumayya take zuwa komi ta haka Hajiya mommy ke samun labarin komi. Ranar suna Ansha shagali Amarya da Angon Karni se shiga sukeyi ta alfarma, jarirai ma se shiryasu akeyi, daga safe zuwa rana sun chanza kaya yafi kaloli talatin, sutura kawai ta alfarma suke sawa,. Ummih ma Alhaji sunusi ya mata kayan fitar suna akwati biyar, yayima big hajiya ma akwati biyar, yayima aunty hafsat ma Akwatuna biyar. Kowa se shiga yake ta Alfarma, . Tako ina mutane ne makil a gidan wasu ma ba asan daga ina suke ba. Nabeelah Tasha makeup, daga shahararriyar ne makeup dinnan Hajiya Yasira (Gayu). Ga kunshi tasha ns design , tako ina walkiya takeyi Gashinan na kanta yasha gyara ta kashe dauri, duk inda tabi camera kawai ke daukarta photo , ita da mijinta da Yaranta da duk abokan Arziki, big hajiya kam ta Kama yara ta rike gam. Zaks ma ba a barsa a baya ba, abu nasu maganin a kwabesu, shima Gashi ga Dr Salmah, da family dinsa,. Hajiya maryam kam da zuriarta a gidan suka kwana Dazu aketa hidindumu, Alhaji sunusi ma se yabar gidan ya dawo yanata kallon jikokinsa, dasuka fito sharr sukayi kyau. Besan kyaun ummih ya shahara ba se yau datasha simple makeup ita yace ta zubo masa abincin gidan sunan shida abokansa dasuka kebe a wani babban falon, ta kawo musu abinci iri iri da drinks. Alhaji sunusi se binta yake da kallo Tasha doguwar riga wadda ta bayyana dirinta, a dire take sosai komi ya fita zarr shaawah, Alhaji sunusi yaji kmr ta zauna karta fita a dakin. Babban Amininsa Alhaji adamu ya fahimci irin kallon da Yaga yanama Ummih, se Adduah yake a ransa Allah yasa abinda yagani da idonsa ya bayyana a zahiri, duk cikinsu kowanne ya dace macen Arziki amma Banda Alhaji sunusi kuma duk yafisu nagarta da kudade, Gashi mutum na gari Sam bashi da nakaso. Da daddare akasha dinner wanda ya tara manyan mutane, Kama daga kan maza zuwa mata, duk wasu abokan Arziki sun hallara, manyan yan jaridu sunzo se dauka sukeyi akayi hira da Aeezad a ranar ne ya bayyanawa duniya nabeelah matarsa ce domin mutane da dama basu sani ba, aiko a Daren akasa duk wata dauka da akayi A manyan Gidajen talabijin da Manyan Accounts din TikToks. Manyan