Sashe 25
Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
adamu a kafa Nan ya fadi kasa Yana ihu Yana fadin "ka gudu kawai sir..." Aeezad ya tsaya ze dauko Adamu, Nan suka samu nasarar Harbin Aeezad din, seda suka sakar mata bullet kusan goma yana kaucewa dayar ce ta samesa Nan ya zube kasa warwas,idanuwansa suka kulle ruf bakinsa da kalmar shahada. Jin jiniyar motar Yan sanda ga jirgin daya fara zagaye ta samansu, ai tini Bashiri barayin sukayi saurin guduwa , cikin farin ciki sbda sun tabbar sun samu nasarar kashe Aeezad. Ayi hkri da rashin editing tsoffin fans Dina sun San baba editing book. Wannan littafin na kudi ne 08101626484. NAMIJIN ZUMA PAID PAGE12 *Wannan littafin na kudine 1k only 08101626484* A bangaren nabeelah tana shiga cikin gidan a daddafe ta zube kasan tiles din falon kawai ta fashe da Wani irin kuka, abinda yasa kenan take ja baya da AEEEZAD sbda batasan mgnr Nan ta rashin kunya ta shiga tsakaninta dashi, ji takeyi tamkar yayi zunubi ne a gareta me girma. "ta yaya d'a zece yanason uwarsa kuma Yana sha'awarta!..." Nabeelah ta fadi a zahiri tana meci gaba da kuka tamkar ranta ze fice daga jikinta."wannan raini ne me tsanani!'' nabeelah ta fadi a zahiri tamkar zararriya, gani takeyi Tamkar ma Aeezad ya gama rainata ne tass, kuma karya yakeyi ba aurenta zeyi ba, kawai danyaga tana kasansu ne shiyasa ya bijiro mata da hakan saboda ya lalata mata tarbiya, sanin kanta ne tasan Aeezad mazinaci ne, to tabbas shima zinar yakeso yajata da aikatawa, ta tabbatar Sha'awarta yakeji so yakeyi ya lalata mata tarbiyarta, tin tini Ashe kallon da yake mata kenan nasan yayi Zina da ita, tabbas duk wanda ze iya fadin gatsal Yana sha'awarka a gaban mutane tabbas ze iya aikata komi gashi ko ya aikata Zina da ita bata da yadda zatayi dashi cewa za ayima ta masa sharri sbda shi d'an gata ne ita Kuma bata da gata sena ubangiji. Koda ace ma aurenta zeyi ita Sam bazata iya aurensa ba koda ace za a kasheta, Aurensa tamkar zata Kai kanta ne ga wahala inma yanaso kenan, domin a duniyar Nan nabeelah na azabar tsoron Hajiya rafi'ah tazauna dasu bataji dadin ba Sam, balle ace wai ita zata zauna kishi da na'eema ai ta tabbatar sena lahira yafita jin dadih duniya, har kwarama ta mutu da hakan ya faru, bama wannan ba tabbas ko ta rasa mesonta a duniya bazata iya auren Aeezad ba, koda za a kasheta sede a kasheta. "Har abadan!'' ta fadi tana meci gaba da kukanta,ta dago hannayenta data dinga marinsa dasu ta kallah, Wani irin tiriri zuciyarta ta dauka me azabar zafin Daya haifarwa da jikinta ketowar zufa, haka kawai taji bata kyautaba saboda marirrikan data masa, Nan take fuskarsa ta fado mata idanuwa a yayin data masa kallon karshe kafin ta shigo cikin gidan, duk hannayenta sun kwanta a kn fuskarsa , gashi ta fasa masa baki da marirrikan data dinga masa, kukan da yakeyi kmr ze haukace ya kara fadowa tunaninta, taga tamkar yana gabanta ne, ji takeyi kmr ynzu abubuwan ke faruwa, Nan take ta kara zama kmr mahaukaciya tace "meyasa na masa wadannan marirrikan? Kawai danyace Yana sona Yana shaawahta!!" Ta kara fashewa da kuka Hadi da kwanciya a kasan tiles din falon, "Dan Allah kayi hakuri Dan gatan Nabeelah...dan Allah ka yafemin ,kwata-kwata baka chanchanci abinda na maka ba, kawai dankace kana sona? Shine na maka wadannan marirrikan .... Kwata-kwata baka can-can-ci abinda na maka ba Jarumina! Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!! Ya Rabbih!'' ta shiga sambatu cikin gigitar fitar hayyaci, se yanzu take nadamar marirrikan data dinga masa,,, a matukar zabure ta dafe kuncinta yayinda takejin tamkar zafin marirrikan data dinga masa ne takeji a kan tata fuskar. "Ka yafemin....bazan Kara marinka ba, nayi nadamar marinka Dan Allah kazo ka rama...ka rama please!'' ta fadi a rude kaf bata cikin hayyacinta, ta mike a zabure ta fito kofar harabar gidan takai dubanta inda ya tsugunna yanata kuka, daman tasan tini sun bar gidan sbda taji ficewarsu a gidan. Nan kasan datake tsaye ta zube kan guiwowinta tana kuka me tsuma zuciya yayinda kaf siffarta seda ta chanza sbda kukan datasha, Kanta ko hula babu tini hular kanta ta fadi a falon, uwar sumar nn kanta ta barbaje tsakiyar bayanta. "Ka dawo Dan Allah,! Aeezad kadawo Dan Allah, Dan girman Allah kadawo ka rama marirrikan danai maka Dan Allah!!!'' ta fadi tamkar zatayi hauka,takai hannayenta kan fuskarta tashiga Marin kanta da karfi,,dakanta taji zafin marin datakema kanta ina magashi, Nan ta kara fashewa da kuka tana Marin kanta tana fadin. "na tabbatar zafin da Aeezad yaji yafi zafin da nakeji ynzu haka A Marin da nakewa kaina...wlhi Bazan yafewa hannayena ba dasuka mararmin kyakyawar fuskar Aeezad dina ba....'' ta fadi se sambatu takeyi kaf ta zare, ma'aikatan gidan suka taru suna kallonta su a zatonsu ko iska ne suka tashin mata,. mata kuwa ma'aikatan suka shiga kokarin riketa a mata rukiya, kusan su goma nabeelah ta zubar dasu ta nufa cikin gidan a guje tashige dakinta suka biyota tasawa dakin key, suka dinga mata Addu'ur'i Hadi da kiran sunanta zuwa can har suka gaji suka watse. ita kadai tasan meke damunta, kwara ace aljanun ne da ita suka tashi, da tashin hankalin datake cikin,Nan kasan tiles din dakin ta zube Hadi daci gaba da kukanta tanata bubbuga hannayenta a kasan tiles din dakin, tamkar zata zare , yayinda zuwa yanzu takejin zuciyarta kamar zata buga sbda azabar bugun datake mata. "Wani Abu ya samu Aeezad!!'' ta fadi a matukar kidime,tabbas in tanajin wannan bugun zuciyar to Wani Abu ze ze samesa, a yau bugun zuciyar datakeji baze misaltuba bata tabajin irinsa ba, ko ciwo zeyi setaji a Jikinta kuma makusancin bugun zuciyarnan takeyi in Wani Abu Ze samesa, Amma ta yau ta shahara domin har jikinta rawa kawai yakeyi kmr zararriya, ta haukace yau tuburan, tako ina zafi takeji a jikinta, hatta jinin jikinta ya dauki zafi se azabar zufa kawai takeyi, . Kmr an tsunguleta ta tashi ta nufa bedside tanata tangal tangal jiri na neman dibarta, Wayarta ta dauko wadda ke ajiye a bedside kirar Samsung ce wayar, tin kafin ta bude wayar taga sunansa dauke da messages a kan wayar, jikinta nata kakkarwa tashiga kokarin bude wayar, Nan wayar ta fadi kasa sbda jikinta daketa kakkarwa, wayar ta bugu da kasan tiles, jiki na rawa tabi wayar ta dauka, abinka da Samsung ashe faduwar da wayar tayi taci screen, farr-farr wayar tayi, tayi wasu layi layi, kuka nabeelah ta kara fashewa dashi yayin data zube Nan kasa ta ajiye wayar a kan cinyoyinta tana fadin "meyasa zakici min haka, banga messagee dinsa dayaminba, inaso in kirasa inji ina yake inaso in gansa! Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Ya Rabbih ka rabani da mummunar kaddara..." Nabeelah ta karashe tana kukan dayafi kaf kukan datayi a fari, jikinta se kakkarwwa yakeyi, ta kara dago wayar, taga ta Dan rage layi-layinn datayi, jiki na rawa ta karkata wayar gefe, tashiga kokarin cire wayar a lock daman Sunansa ne security din wayarta AEEEZAD! da kyar tasamu wayar ta fita daga lock Sam bata gani SOSAI seda kyar wayar nayi tana far-far, a haka tashiga taga messages din da kyar ta iya karantawa. Tana GAMA karanta sakon ta kife taci gaba da kuka yayindatake Nemo lambarsa tayi dealing taji a kashe, ta kira kusan sau talatin Amma a kashe wayar take, (tinda ya wurgar da wayar kasan motar ta mutu) nabeelah ta kara fashewa da Wani irin kuka tana fadin "Wayyo Allah na! Wayyoh Allah na! Wayyoh Allah na! !! Wayyo rayuwata!'' sune kalaman daketa fitowa daga bakinta yayin datake kuka kmr zatayi hauka, bugun zuciyarta na kara kidima jikinta, se buga kanta takeyi a kasan tiles din dakin Sam ko zafin hakan bataji, abinda takeji a zuciyarta ya wuce tunanin duk Wani me tunani, se dealing number dinsa takeyi Kamar hauka Nan take tayi masa kira yafi kira dari biyar Amma duk a kashe. A bangaren Aeezad. tini jirgin Yan sanda dana sojoji sukama dajin saukar angulu, tako ina ma'aikata suka cika dajin tini Yan ta addan sun tsere. Bashir ne yasamu damar Kiran Wani abokin Aikinsu ya sanar dashi halin da suke fiki, kasancewar Aeezad ba karamin mutum bane a Nigeria, tini aka sanar da shuwagabannin sama, shine aka shiryo wadannan tawagar jirage guda biyu, motocin Yan sanda da sojoji Kam sunfi motoci hamsin. Nan wasu suka fada dajin domin dubo Yan ta addan Amma ina ai babu su babu dalilinsu. Yayinda tini aka dauki aeezad dake kwance kmr matacce aka sashi a cikin jirgi kana aka dauki Adamu na aka sashi a jirgin, a cikin jirgin harda chief of army, ba karamin kaunar Aeezad yakeyi ba sbda kokarinsa a hukumar sojojin, ganinsa kwance kmr ba Rai seda yayi kwallah,. "Jarumin maza.. Namijin fama..." Chief of army ya fadi Yana me kallon Aeezad a kwance tamkar matacce,kowa jikinsa ya sare gani sukeyi da wuya Aeezad ya rayu,dukda basu sanma a ina aka harbesa ba, kawai de jini se kwarara yakeyi a hannunsa jinin me dumbin yawa ya zuba daga jikinsa,hkn ne yasa suke tunanin da wuya Aeezad ya rayu sbda jinin daya zubar yayi yawa., har kwara Adamu ma yana iya rayuwa sede kafarsa da wuya ta moru. Cikin hanzari jirgin ya tashi sama aka nufa cikin garin Kano dashi domin Nan yafi musu saukin zuwa, direct babban asibiti aka nufa dashi, tini Yan jarida sun fara watsa labaran hakan a gidajen Redio da gidajen TV, domin tini Suma sun hallara dajin tin kafin a dauke Aeezad da adamu suka samu nasu rahotannin,, Nan da Nan Nigeria ta kideme da zallar tashin hankali, iyalansa dasukeda tabbacin a cikin sojojin dasuka rasa ransu akwai nasu suka hau koke koke. ** ** ** Dai-dai Alhaji sunusi dake zaune falonsa Yana kallon news wannan Labarin ya fado masa, aka nuna konewar motar sojojin sannan aka saka picture din Aeezad Dana adamu, cikin tashin hankali daddy ya tashi tsaye, sbda tini ya gane dansa ne tilo dayafi kauna a fadin duniyar Nan, ko daga bacci ya tashi ze gane d'ansa koda a cikin dubu dubu ne. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' alhaji sunusi ya dauki salallami kusan sau uku a jere cikin ihu tamkar ze fasa falon nasa, ya jawo wayarsa