← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 56 OF 66

Chapter 109

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 34 min read

Cigaban labari….
Deeda hospital abuja.
Ahankali ta soma bude idanunta da suka mata nauyi soaai harta sauke akan doctor dake kokarin dubata, “if you can hear me bling your eyes”
Doctor ya fada wanda hakan yasa ta kifta idanunta, sannan ya dubi hamad dake tsaye yace “shes stable now..shock ne ya sa ta shiga stage din semi coma,“
“Thank you doc”
Doctor na fita komai ya soma dawoqa maya, kamar sabon faife.
Tuni wani hawaye ya soma sauko mata mai dumi tayi kokarin miqewa zaune hamad ya fara kokarin dakatar dashi ta fara dube dube kamar mahaukaciya “mummy daddy ina mummy na da daddy”
Shuru hamad yayi yana kallonta cikin tausayi , “wheres mummy??????”
“Calm down, you’re not okay yet”
“Ka fadamin ina mummy na?? Daddy fa? Please mafarki nayi ko? Wani mummunan mafarki nayi ya hamad wai mummy da daddy ba parents dina bane, god forbid Wai parents din wannan yar iskan yarinyar yar mai aikin nan mteww, please ina mummy na?”
Tana fadin haka ta fara kokarin sauka kamar mahaukaci ya dakatar da ita ta hanyar kama hannunta, “ba mafarki bane maya…”
Take gabanta ya bada wabi daammmm, idanunta ya nemi kankancewa ta dubeshi tace “ina mummy????????”
“Calm down maya…”
“Don’t tell me to calm down ya hamad…why im i here kuma mummy bata tare dani?, da gaske ne kenan? Niba yar mummy bace,?? Ni yar mai aiki ce??? Wannan yarinyar itace yar su mummy ehhh??” Ta fashe da kuka sosai ta fara fusge fusge kamar mahaukaciya hamad na kokarin kamata tana tureshi ta cizge drip din hannunta ta futa a guje yabi bayanta.
Tabbas wannan ba mafarki bane, gaskia ne, tunda har za a iya kwantar da ita a asibiti bataga mummy a gefwnta ba bata ga daddy a gefenta ba.
Innalililkahi wa inna ialihi rajiun ta dora hannu a ka lokacin dataji wani irin jiri na dibanta yuu tayo baya hamad ya tarota ta zube a kasa, ta fashe da wani matsanancin kuka mai fitar rai, “na shiga uku…meke shirin faruwa da ni?“
“Maya…mayaaaa listen to me, dan allah ki natsu, ki natsu pls”
Tana shesheqa tace “dan allah ya hamad ka kaini wajen mummy, wallahi babu wanda ya isa ya rabani da ita ina rokonka da Allah”

Dakyar hamad ya lallabata suka koma ciki doctor ya hata magunguna sannan suka fito, suna fitowa ya bude mata seat din gaba ta shiga ta zauna, gaba daya saita zama kamar batada sauran kuzari, sai hawaye kawai takeyi kamar ranta zaj futa.
Suna isowa gida hamad ko gama parking baiba ta wuce part dinsu cikin gaggawa, tana shiga kai tsaye ta nufi part din mummy, tana shiga dakin ko sallama batayi ba ta hango bahijja zaune nanna a gefenta, a abunci a gefwnta amma ta kasa cin komai, yau kwana biyu kenan da tashin hankali daya faru a gidan, ta kasa tattara gaba daya natauwarta, an kara mata ruwa yafi guda shida, ta kasa ci ta kasa sha, ta kasa magana da kowa, sai kuka, nanna ce kawai ke forcing dinta tanashan koda dan tea ne, shima tanasha yake futowa, gaba daya lokaci guda ta fita hayyacinta ta rame sosai kamar ba bahijja ba, as expected blaming kanta take tare da tsanar kanta na abubuwan datayi ma diyarta ta asali a baya, tayi kukan tayi kukan harta godema allah, nanna saidai tazo tayi ta mata nasiha, tana nuna mata ba laifinta bane, saidai tace da wani ido zata kalli yarta? Da wace fuska zata kalli yarta ta asali? Dubaga duk abubuwan data mata, ta wulaqanta yarta, ta mata korar wulaqanci, saboda idanunta ya rufe akan yarda ba yarta ba, tabbas bata illatata amma ta illata alakarta da yarta ta asali, she can never forget wannan tabon da hadiza ta mata ta cuceta ta cuceta ta cuceta.
Tana cikin wannan tunanin tana hawaye saijin maya tayi a jikinta, “mummy…mummy kece mummy na ko? Karya suke ko? Nice yarki ta asali ko?”
Maya na magana amma bahijja ji take kamar ana watsa mata gauta a jikinta, tayi saurin rintse idanunta jininta na boiling, muryar maya takeji amma kamar maganar hadiza ce ke echoing a kunenta, yar hadiza ce data rike a matsayin nata, ta bata so da kauna ta fifitata da komai kuma sanadiyarta ta kusa illatata yarta ta asali, innalillahi wa inna ialaihi rajiun, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, abubuwa da dama na yawo a kwakwalarta, wanda bataji ya kamata maya ta bayyana a gabanta adaidai wannan lokacin dukda tana kaunar mayar har cikin zuciyarta, ayau sai taji ko ganinta bata kaunar yi, bata son ganinta kwata kwata, “mummy pls talk to me…mummy kimin magana” maya ta fada tana shesheka, nannan batasan sanda hawaye ya soma saukar mata ba, maya na jijiga bahijja tana rokonta amma ina, itama bahijjar hawaye take sosai, kamar wadda ake tunzirawa ta miqe da gaggawa ta janye hannun mayar daga jikinta idanunta yayi jaa sosai ta wuce bathroom maya tabita a guje ta kamo hannunta, bahijja ta fusge hannun ba tare da ta kalleta ba ta wuce bathroom nanna tayi saurin kiran maya “maya…kyaleta.. tana cikin wani yanayi yanxu, she needs time alone kinji”

Bahijja na shiga bathroom sai hawaye, tanajin maya na bugun kofar bathroom din tana ihu tana kuka,
Ko gajiya batayi don ta dade sosai, har saida ta jigata nannan ta kamata ta tashi tsaye suka fuce daga dakin zuwa bedroom din mayar, nanna ta sata tayi wanka dakyar sannan ta sauka kasa tasa basira ta kawo mata abunci taci.
Yau kwana biyu kenan, gidan gaba daya ya zama wani iri babu walwala babu farin ciki, tabbas hadiza ta masu abunda bazasu taba manta ba, cuta kam ta cucesi saidai kuka allah baya barci don shine majigon bayinsa, aun karbi kaddarar da allah ya kaddaro masu, ka bazasu taba maida hannun agogo baya ba, tunda ya rugada ya faru kuma haka allah ya kaddara kuma ya rubuta zai faru, farin cikinsu daya da allah ya kawo karashen komai ya bayyana masu yarsu bayan shekaru dai dai har shekara ashirin da doriya.
Emotions din da aka barsu dashi ne dai har yanxu yaki barin su, kowa yana cikin wannan hali na shiga shocked.

Nanna na barin bangaren bahijja ta wuce main house, ita kadaice ke kokarin ganin ta basu courage gaba dayansu, anne kam saida aka sake komawa asibiti da ita don jikinta sake rikicewa yayi amma ko kwana daya batayi ba tasa aka dawo da ita, nannan kuwa saida jininta ya dan hau.
Yallabai taj ko kullum yana zaryar part din nanna, saboda nannan da kanta ta kawo sabeeha da itama gaba daya har zuwa yanxu she’s down, itama kullum cikin kuka, kukanda ta rasa na menene, farin ciki ne ko akasin haka saidai tafi dangantashi da na farin ciki, ammafa tanajin zafin cutarta da hadiza tayi, ta cuceta ta cuceta ta saboda ita kadai tasan irin rayuwar datayi, ta rabata da asalin iyayenta, ashe tanada gata haka? Gatan da bata taba tsammanin tana dashi ba a duniya ko zata sameshi, ya allahu…
Ranar da majeed ya rungumeta da kwalla a idanunshi saida ta jita kamar yau aka kawota duniya, sai taji duniyarta ta sauya a daidai wannan lokacin, ta dunga ayyana aranta wannan mahaifinta ne? Mahaifinta na asali? Ashe tana da uba? Allahu akbar.
It was a heartbreaking moment, tana hawaye yana hawaye, ta sanya hannayenta ta goge mashi hawayen dake fuskanshi ta kasa cewa komai, haka zalika shima.
Bahijja ko kasa hada idanun tayi da sabeeha tun daga ranar, da wani idon zata kalli diyar tata? Duk tafi bawa kowa tausayi don babu wanda yasan yanayin da take ciki sai ita kadai.

Nanna na shugowa sitting room ta tadda taj zaune ya shiga tunani, gaba daya shima ya shiga wani yanayi, duk sbaoda sabeeha da tun ranar ya kasa ganin, duk yanda yaso ya ganta babu hanya, da zarar ya shugo part din nannan take guduwa bathroom bata yarda ma su hadu,
Har zuwa lokacin shima shock bai barshi ba, ta yanda fatima ta kasance jininshi ce? Yar uwarsa ce ta jini mafi kusa, ba tare da ya sani ba.
Yafi kowa murna da hakan, yafi kowa murna, ashe bunciken da yake didn’t go to waste, ashe iyayenta ba asali ba tare da ita, kuma bawai abandoning dinta sukayi ba, rabata akayi da asalin iyayenta saboda mugunta kawai da rashin imani, duk wanda yaji abunnan saiyaga kmar wasan kwaiwayo.


Yayi nisa sosai cikin tunanin da yake nanna ta dafashi sannan ya dawo cikin hayyacinsa, nanna ta zauna gefen sa tana dubansa,
Ya gaisheta a natse ta amsa sukayi shuru daga shi har ita kafin ya dubi anne yace “ya take?” Yana nufi bahijja kenan?
Sai ganin hawaye kawai yayi akan fuskar nannan tace “tausayi take bani tajudeen, daman saitafi kowa jin zafi, haka zalika diyar tata ma, tausayi suke bani gaba dayansu, she’s shattered, mutane babu allah a ransu, all this while she was raising maya unknowingly to her that her biological daughter was switched just because of hatred kuma she wasn’t treated properly, ta taso mara uba mara gata,kuma a wulaqance, ita datayi haka a tunaninta taci galaba akan ta batasan cewa kanta ta cuta ba,”

Ta danyi shuru na yan mintuna, kana ganinta kasan abun na mata zafi itama, ya dago yana son ya tambayi ya sabeehan take ita ma ya kasa, dakyar ya tattara courage din shi yace “how’s fatima? Is she okay”
“She will be fine Insha allah, bari na shiga na dubota” tana fadin haka ta wuce bedroom, tana shiga ta tadda sabeehar zaune ta hade jikinta waje guda, itama duk ta rame gaba daya kamar ba ita ba.
Nannan ta yi murmushi ganin ba kukan take ba ta karaso inda take a zaune a kasa ta kamo hannayenta ta maidota kan gado ta zauna nannan ma ta zauna tana kallonta tana murmushi.
“Allah ya maki albarka fatima, allah ya maki albarka fatima, allah yasan meya shirya shiyasa ya hadani dake batare da munsan juna ba, ina farin ciki da kika kasance yar bahijja kuma jininmu, bamusan irin rayuwar da kikayi ba a baya ba don ke kadai ce zaki fadi irin rayuwar da kikayi amma ina godiya ga allah dayayi mana protecting dinki, ya kuma kareki ya maido mana ke wajenmu, alhamdulillah alhamdulillah…duk muna kaunarki, muna sonki sosai, kuma kinada gata, kinji ko”
Sabeeha na hawayen farin ciki tace “nagode nanna… kukan da nakeyi kukan farin ciki ne, ban taba tsammanin inada gata haka ba, na kasa yarda da hakan, idan na tuna irin rayuwar danayi a baya..”
Sai kawai tayi breaking hawayen dake fuskanta, ya soma saukowa sosai, nanna ta rungume ta sosai tace
“Ki mance da komai kinji, karki saka komai aranki kinji ko? Duk abunda ya faru mukaddari ne daga allah dama chan allah ya rubuta hakan ne zata kasance bazamu san ke jininmu bace sai bayan wannnan shekarun masu tsayi,You have us all, kina cikin gata da soyayya, Ina fatan kuma zan ganki da mahaifiyarki..”
Saurin saukar dakai sabeeha tayi, jikinta yayi sanyi sosai wani sabon hawayen ya soma sauko mota.
Nanna ta lura da hakan tayi saurin jawota jikinta ta rungumeta, “tsakaninki da mahaufiyarki bahijja? Shin bakya farin ciki data kasance mahaifiyarki”
Nanna na gama magana kamar ta tsokalo mata wani abu kawai ta fashe da kuka, ta girgiza kanta, “meysa baza kije wajenta ba?”
“Bata sona!!!” Sabeeha ta fada kai tsaye.
“Karki taba tunanin haka, wallahi babu wanda yakaita sonki duk soyayyar da muke nuna maki, bansan meya shiga tsakaninki da ita ba da har yasa kikayi wannan tunanin amma inaso ki sani duk avubda ya faru cikin rashin sani ne,ki bude zuciyarki fatima, wannan dama ce allah ya bamu harda ke, ki dauki abun kamar an sake haifarki cikin wata ni’imatacciyar sabuwar duniya kinji ko?”

Magangnun nanna ba karamin dadi sukayi ma sabeeha ba kuma suka sake kwantar kata da hankali,

……..
After a week…
Cikin sati gudan nan abubuwa da dama sun faru ciki kuwa shine tabbatatuwar rayuwar sabeeha data chanza on a blink of an eye, tun bata amince da hakan ba tana ganin abun kamar wasa harta yarda, soyayya take samu da gata ta kowanne bangaren, har ta soma sakin jikinta baiwar Allah, ganin abun take kamar a mafarki tana jin kamar za a ta tashi, dukda ta san kowa a gidan tunda sun kusa shekara da zuwan su gidan ita da hadiza jinsu take kamar yau ta fara sanin su, mutanene masu daraja da son jininsu fadin irin farin cikin da take ciki bata lokaci ne, a da kullum cikin kwanakin saidai taita kuka tana tuna irin rayuwar datayi a baya, amma kasancewar nanna da anne da anty fadila a gefenta uwa uba kuma mahaifinta, wanda har zuwa lokacin ta kasa yarda da ita sabeeha wai tana da uba kuma tana da gata, soyayya suke nuna mata babu adadi, from left and right ta kowanne bangare, bangaren ya sameer ma da nashi iyalan suna farin ciki, musamman anty mubina, hamad ma ya samu damar yin magana da ita kuma yana mai farin cikin kasancewarta yar uwarsa ta jini, laila ko har zuwa lokacin ta kasa zuwa ta ga sabeehar saboda tunawa da irin abubuwan da suka mata ita da maya, yanxu ashe duk wannan lokutan maya ba asalin cousin dinsu bace yar matar da ta sauya masu cousin dinsu ce? Kai ba lailan kadai ba duk wanda ya tuna da wannan abun sai yaji gaba daya baya son ganin mayar.

Yan uwan majeed ko tattaki sukayi tun daga Lebanon suka zo, iyayensa daman sun rasu, sai sisters dinshi, yanda kowa ya shiga shock haka suma suka shiga saida suka zo sukaga sabeehar, it was an emotional moment for all of them abun dai ba a cewa komai.
Kamar dai yanda majeed yaji lokacin daya fara ganin sabeeha har yaga kamanninta da kakarsa haka suma yan uwansa suka dunga fada, ranar dai sabeeha taga soyayya, haka suka dunga rungumeta suna sumbatarta a kumatu yanda suke a aladarsu suna murna harda masu hawaye itama dai hawayen farin cikin take.

Fadila kam ko maganar mayar ma bata son yi, akwai ranar da laila ta shiga part dinsu mayar donta dubota saboda hamad yace ta dunga zuwa tana dubata, yanda taga mayar hankalinta ya tashi sosai har kwalla saida ta mata saboda tsakani da allah tana sonta har cikin zuciyarta kuma ta kasa yarda da ba cousin dinta bace ta asali, shes a replacement of sabeeha, bayan wannan yanda taga mayar ta koma ma saida ta tsorata, ranar sunsha kuka sosai maya na tambayarta shikenan yanxu ita ko kowan kowa bace kuma ba yar mummy da daddy bace yar mai aiki ce? Kuma yanxu shikenan tunda batada alaqa dasu za a koreta ko? Kuma duk sun daina sonta ko? Laila dai nata tausasata tana nuna mata cewa bazasu tsaneta ba tunda itama yarsu ce kuma ba laifinta bane, itama haifarta akayi, batada laifi,
A haka dai suka rabu ta fito daga wajenta,
Tana koma part dinsu ta fada ma mami (fadila) yanayin data tadda maya tana hawaye fadila ta daka mata tsawa sannan tace mata karta sake kawo mata maganar wata maya, gaba daya saitaji tsanar mayar daman tun farko tana doubting yarinyar kamar ba yar bahijja ba,ashe hunch dinta gaskia ne,

Bahijja ko har zuwa yanxu ta kasa tattara courage din fuskantar yarta ta asali wato sabeeha, a cewarta bata chanchanci kasancewa mahaifiya a gareta ba saboda irin abunda tayi mata a baya, ta nuna tsana a gareta.
Nanna da fadila kullum nusar da ita suke illar kauracema sabeehar na qin fuskantarta da takeyi, kuma blaming din kanta da take bazai amfaneta da kkmai ba, ta kama yarta, ta jata jiki, abunda ya faru ya rigada ya faru bazqsu iya sauyawa ba, kuma rubutattacen al’amari ne, cuta dai hadiza ta cutar dasu cuta mafi tsanani wanda allah kadai ne zai saka masu kuma zai sakama sabeeha.
Su hadiza ko kamar an shafe babin su, babu any track of them, dss ake magana fa😂tunda suka tattara su ko alamun motsinsu ko tarihin su ba a ji, ana chan ana shan azabar da sun gwammaci a kashesu ma, musamman hadiza da basa sassauta mata.
Jamilu kuwa kwana daya biyu uku da baiji motsin jamila ba, ya kira wayoyinsu da hadiza shuru haka kawai jikin shi ya bashi akwai matsala wannan yasa ya tattara yayansa ya sayar da gidan da suke ciki ya tasa su sai kauye.

Maya ko, bana jin zan iya fayyace maku a wani yanayi take ciki, ta shiga wata ukubar rayuwa, taga go no go, ta tabbatar da tabbas ita ba yar gidan bace, sabeehan dai datake wulaqantawa takema kallon wulakantacciyar itace asalin yar gidan, ita kuma yar mai aiki ce, yar mai aikinda bama ta da asali ko tayi tunanin tana da uba, bata iya cin komai, bata iya chan komai, har wata yar natsuwa ce tazo mata, wato wargi ma waje ya samu, ko shaye shayen ma batabi ta kanshi ba, don ba kwaya ba ko roci ce batajin zata iya magance mata matsalar dake kanta, she cant bring her self to believing that ita yar hadiza ce kai ta cuceta data kawota duniya kuma mummy da daddy ba iyayenta bane na asali, innalillahi wa inna ialaihi rajiun, cikin kwana biyu ta rame ta kanjame, tayi la’asar, kullum tana daki bata fitowa, ay bata gama yarda da gaskiayra dake gabanta ba saidata yi kwanakin nan bahijja bata shugo dakinta ba yanda ta saba, matarda bata iya barci bataji motsinta ba, shikenan tata ta kare, yanxu idan komai ya lafa tunda sun samu diyarsu korarta za ayi kenan? Kai tsanar datakema hadiza ko mutuwarta, tana jin inama za a tasheta ace mafarki take ko zataji sauqin abunda takeji.
Basira kullum saita kawo mata abunci, amma yanda ta kawoshi dakin nan haka zata daukeshi don bata tabawa, kuma duk maganar da zata mata bazatace uppan ba, kullum tana daki futila a kashe,tana kuka.
Nanna ce kawai ke yawan dubata, sai kuma hamad da daddy (daddyn sabeeha🥹 lol)dadyn nema yasa basira na kula da cinta bayan shiga dakin dayayi sau daya don ya dubata, yaga yanda ta koma, da ya tuna abunda hadiza ta masu na sauya yarta datayi da tasu saiyaji gaba daya zuciyarsa ta tsinke, he cant help it, yanajin zafin abun sosai saidai kuma ya kasa yaji tsanar maya saboda ya rike ta a matsayin yarsa kuma har zuwa lokacin yanajinta yarsa ce itama, kuma ba karamın tausayi take bashi ba don itama bata da laifi, laifin mahaifiyarta bazai shafeta ba.

Babban tashin hankalin da suka shiga a satin kuwa shine heart attack din da bahijja ta shiga, saboda damuwar data sama ranta, ranar gaba daya kowa ya shiga tashin hankali mara misaltuwa musamman majeed, da nanna da suka san abunda take ciki.
Saida likitoci wajen uku suka hadu akanta kafin a samu kanta da daidaituwar nunfashinta.
Idan ka ganta dole ta baka tausayi, lokacin da gaba daya ahalin sukaji cewa zuciyarta na cikin barazar bugawa sun shiga wani maquyacin hali.
Sabeeha ko tafi kowa shiga tashin hankali, duk kwanakin da suka dunga yi a asibitin tana gefen bahijja bata matsa ba, kuma basu hanata ba suka barta, anne cema tace su barta kusa da bahijjar saboda bahijjar tafi buqatarta a irin wannan lokacin.
Haka zata kwana tana salloli tana rokon ma mahaifiyarta lafiya, ko barcin kirki bata iya yi sosai, majeed ma yawanci a asibitin yake wuni, da daddare yake komawa gida.
Duk sanda yazo yaga sabeehar kusa da bahijjar tana rike da hannunta sai yaji wani irin dadi a cikin zuciyarsa farin ciki mara misaltuwa ya lulubesa.
Kwanansu wajen uku a asibiti kafin bahijja ta farfardo, ranar data farfado wajen karfe shida na safe tana bude idanunta taji hannunta cikin na mutun, kwata kwata batayi tsammanin sabeeha ce a gefenta ba don tana bude idanunta komai ya dawo mata, ta fara kokarin tashi zaune har zuwa lokacin hannunta na jikin na sabeeha da barawon barci ya dan tafi da ita tayi saurin farkawa.
Ashe tana kwance gefen ta ta dora kanta bisa gadon da bahijjar ke kwance, kafin barcin nan ya dauketa sallar asuba tayi ta dawo kusa da bahijjar ta zauna tana kuka tana kallon fuskarta, tana ayyana ma ranta cewa wannan mahaifiyarta ce ta asali kuma itace ta tsugunna ta haifeta, tana jin yanda she’s blessed, don ba tun yanxu ba takejin tana son bahijhar sosai musamman yanda taga tana son maya sosai, tasha rokon allah dama ace itama tana samun irin wannan so da gatan
Tana cikin wannan emotional state din barci ya fusgeta, sai yanxu data soma jin motsi ta farka.

Bahijja na tabbatar da sabeehar ce a gefenta kawai saita fashe da kuka, tana hawaye sosai gwanin ban tausayi dayasa sabeehar itama ta soma kukan har zuwa lokacin hannunta na cikin na bahijja idanunta yayi jaa sosai, samun kanta tayi da rungume bahijjar sosai kamar zata shige jikinta, hannunta na karkarwa, itama kanta bahijjar jikinta karkarwa yake ta kankame sabeehar sosai, suka rasa wa zai lallashi kowa.
Sun dade a cikin wannan yanayin basu san ma majeed ya shigo ba yana tsaye daga gefe tare da taj suna kallonsu.
Saida sukayi mai isarsu kafin bahijja ta iya bude bakinta ahankali dukda tana cikin wani yanayi na rashin kuzarin jiki tace “bansan da wani irin kalamai zan nemi yafiyarki ba, I’m sorry my daughter I’m sorry for all that you have gone through I’m sorry for not being by your side when you grow up, my heart felt so so heavy a duk lokacin dana tuna ko rikeki ban samu nayi ba bayan na haifeki, i just had a glimpse of you lokacin da aka ciroki daga jikina, when i was unconscious, i am so devastated for not recognizing you? How can i live with this kind of pain???? A tunanina inata rayuwar kwanciyar hankali kuma ban rasa komai ba, allah ya azurtani da komai ashe kina chan cikin wata rayuwar da bata kunshi komai ba sai kunci, hadiza ta cuce ni hadiza ta cuci, allah ne kawai zai min sakayya, ta cuceni….I’m very sorryyyyy my daughter.. ki yafeni, ki yafemin abunda na maki a baya, wace uwace zatayi ma diyarta abunda na maki…da wani ido zan kalleki, ki yafeni yata”
Ta karashe tana kuka mai karya zuciya, wallahi majeed dake tsaye saida kwalla ta zubo mashi, taj ko kasa tsayawa yayi ya futa daga dakin ya koma mota ya zauna.
Sabeeha na kuka harda majina tayi saurin tashi daga jikin bahijja ta tsugunna a gabanta kanta. Kasa tana hawaye ta soma magana “dan allah karki nemi yafiya a wajena, saukar hawayenki masifa ne a gareni, ni ce zan nemi yafi ya a wajenki…ma..ma!!!”
Wannan kalmar mama da sabeeha ta fada ba karamin shigar bahijja yayi ba, sai kawai taji wani sabon kuzari ya zo mata tama manta da canula dake hannunta ta sauko daga kan gadon ta tsugunna gaban sabeehar itama ta rungume sabeeha sosai, sai a lokacin majeed ya karaso cikin dakin yana murmushi bahijja na hangosa ta dago sabeeha ya hadesu gaba dayansu ya rungumesu, sai ya kasance sabeeha na tsakiyansu sun rungumeta, a daidai wannan lokacin me zatayi banda godiya ga Allah, wani irin ni’ima ce ta lullubeta taji ko allah ya dauki ranta yanxu to zata kasance wadda tafi kowa farin ciki a duniya, yau taji kuma tayi experiencing abunda ake kira soyayyar iyaye ga yayansu.
It was so genuine an emotional moment 🥺ya allah.
Gyaran muryar da akayi ne yasa suka daqo daidai, fadila ce ta shugo gefenta laila da hamad sunzo dubiyar bahijjar.
Fadila na dariya ta dubesu tace “what a happy family.. kodai mu koma ne mu barku ku cigaba da moment dinku”
Dariya duka sukayi gaba dayansu, kowa yana kallonsu, bakin sabeeha ya kasa rufuwa, data kalli bahijja saita kalli majeed.
Gaggaisawa sukayi gaba dayansu, aka sha hira bahijja tace itafa a sallameta su koma gida taji sauqi, fadila nata mata tsiya, hardasu cewa wai ay sabeeha tafi kama da dangin ubanta, saboda launin fatarta.
Laila ko tana samun dama ta kamo sabeeha ta rungumeta sannan tace “welcome to the family fatima, im so glad we’re cousins”
Murmushi sabeeha ta mata suka dan taba hira, hamad ma ya shiga cikinsu aka sha hira.
Bahijja dai yau tasan tayi breakfast na kirki rabonta da abunci tun ranar da taji cewa sabeeha yarta ce ta asali wadda hadiza ta mata replacing da diyarta wato maya…sai a yanxu ta tuna da maya.

Sallamar taj ce tasa duk suka maida hankalinsu zuwa ga kofar, yana shugowa idanunshi ya shiga cikin na sabeeha, samun kanta tayi itama da kallonshi.
“Ah ah ashe kana tafe kaima” fadila tayi magana,
Dan murmusawa yayi, majeed yace “ay tun dazu yazo, kusan ma a tare muka iso asibitin”
“Good morning..ya mai jiki” taj yayi magana
Bahijja ta amsa, fadila ma ta amsa, laila ta gaishesa haka zalika hamad, sabeeha ma ta dago ta mashi kallo daya tace “good morning..”
Jiki a mace ya amsa har yana tambayar how shes doing, ta amsa da shes fine..sannan ya samu waje ya zauna yana facing dinta, tana daga zaunen nan tana jin idanunshi akanta.
Bahijja ma ta kasa duake idanunta kan sabewhar, data kalleta saita yi murmushi, shea the happiest mother on earth, wani irin so take ma sabeeha mara misaltuwa, yanda takeji game da ita daban ne, she will do anything to protect her and love her unconditionally……

After a month!!!!
Alhamdulillah alhamudulillah…

Sallamar da akayi ne yasa ta juyo wa da sauri tare da aje duvet din dake hannunta, nima dana rako hamad da paper bags bansan sanda na sakesu ba tsabar mamakin dana shiga, shi kanshi kasa duake idanunshi yayi akanta, tayi wani azababban kyau, wato kwanciyar hankali ma wani abu ne mai mahimmaci ga rayuwar dan adam, wallahi in kunga sabeeha bazku taba cewa itace ba duk kyan datayi a saudi bai kai kyan datayi ba yanxu cikin wata guda, don wannan ya qunshi kwanciyar hankali, farin ciki da kuma natsuwa, ga uwa uba gata ta ko’ina, tayi bul bul abunta fuskanta sai annuri take, sutura ko yanxu saidai sabeeha ta bama sutura baya, mayukan da take amfani dasu so hmm ba a magana, dady ya saya mata dankareriyar wayar da ake yayi, fadila ko ranar daya ta kashe ta shiga shopping mall tayi mata sayyayyar budurwa, lokaci guda suka chanzata, bahijja ko cewa take arzikinta bashida amfani idan har sabeeha bata amfanu dashi ba, duk wani properties dinta ya koma karkashin sunan sabeeha.
Dakinta ko da aka ware mata abubuwan da aka saka mata a ciki ba a cewa komai, anan main house ma aka fidda mata part dinta don anne da nannan sunce wajensu zata zauna hakan fa baisa bahijja taqi organizing mata part dinta ba anan bangaren su kusa dana maya.
Dakin nan an zuba dukiya kamar me, ko quarter shi maya bata samu ba, duk gatan da sukayi ma maya bai kai ko 10% na wanda akema sabeeha ba don komai suna yinshi ne extra yanda bazatayi lacking komai ba a rayuwa, zasu maye mata gurbin abunda data rasa a baya.

Talking of maya, bayan dawowar bahijja daga asibiti aka zauna akayi magana, tsakanin majeed da bahijja dasu anne, manya dai kawai suka zauna sukayi magana akanta.
Da aka zauna maganar mayar fadila na maganar a nemi chan dangin maya na chan kauyensu a miqata wajensu,suma su san da zamanta tunda bata da uba kuma shegiyar uwar tata tana chan a kulle, sai kuma bahijja tace bazata taba yarda a rabata da mayar ba tunda itama yarta ce, koda kuwa bata haifeta ba koda kuwa sanadiyarta suka rasa yarsu suka reneta a matsayin tasu she’s still their child, kuma zasu riketa kamar tasu itama.
Fadila dai bataji dadin wannan zance ba don gudun abunda zaije ya biyo baya, jinin hadiza ce fa? Barinta cikinsu abu ne mafi hadari,kuma she expect duk abunda hadiza ta masu bazasu yarda su rike yarta ba a matsayin tasu.
Duk wani abu daya danganceta ma abun kyama ne kuma abun gudu ne, saidai kawai allah ya rufa asiri.
Amma kuma duba ga yanda mayar tayi sanyi, ta koma wata saliha saliha sai duk kowa ya soma jin tausayinta anne ma tace a bunne maganar kawai yanda take tunda babu wanda yasan da cewa ba yarsu bace in banda hadizar da mutanen gidan gaba daya, duniya bata san da zancen ba don haka ya tsaya a haka kawai saidai abun gudu shine idan har aka tashi aurar da mayar, idan anzo buncike.

Amma kuma duk wani abu da ake mata baza a fasa yinshi ba, kama daga kan karatunta, gatan da ake mata da komai babu abunda zai sauya, laifin uwarta bazai shafeta ba, sun rugada sun karbi kaddarar abunda ya faru, kuma babu wanda zai iya sauya komai tunda ya wuce.


Shugowar hamad da sallamarsa yasa ta juyo tana kallonsa, fuskanta dauke da murmuahi da kullum cikin yinshi take, tana sanye cikin wani dankararrwn lace, zata iya cewa wannan ce sutura mafi tsada data taba sanyawa a jikinta, tayi bulbul, yarinya cikin wata guda ta sauya gaba dayanta, tsabar kwanciyar hankali, da farin ciki da take ciki.
“Ya hamad!!!” Ta kira sunansa firgigi ya dawo hayyacinsa, ya sauke mata wani murmushi mai kyau.
“Ina kwana ya hamad?”
“Lafiya lau my beautiful cousin” baima san ya fada ba, ta sauke fuskanta tana blushing, wannan ne first time daya fadi hakan, shima baisan yayi subutar baki ba saida ya gama fada.
Paper bags din daya shugo dasu ya aje mata a gefe sannan yace “mami tace a kawo maki,”
Ahankali ta danyi blushing sannan tace “mami bata gajiya, ace mata na gode allah ya kara arziki mai albarka”
Ya amsa da ameen, “hmm kije mata godiyan da kanki, daman tace kwana biyu baki shigo ba kinyi breakfast??”
“Ah ah” ta amsa shi tana murmusawa
“Let me wait for you ki gama sai Muje muyi a kasa” ya fada kai tsaye, ta danyi shuru, sannan ta cigaba da gyaran gadon shi kuma ya zamu waje ya zauna kan wani dan pink couch da akeyi decorating dakin dashi, samanshi irin furr blankies ne a jiki, komai fess fess, ga dakin sai kamshin bakhoor yake.
Tana gamawa ta tattara paper bags din ta aje su closet sannan ta futo, ya miqe tsaye, hannunshi ya zuwa cikin aljihunsa ya zaro abu daga ciki sannan ya dubeta yace “can i see you palm”
Dan murmushi tayi surprisingly sannan ta bude mashi palm dinta ya sauke mata wata yar sarka mi kyan gaske jikin pendant din sarkar akwai letter F a jiki fatima kenan, sannan ga wani dan diamond stone pink a tsakiya.
Tana ganin sarkar ta bude baki zatayi magana yace “don’t thank me, its a gift from me”
Shuru ta danyi wani irin dadi na dabaibayeta, tun safe kowa ke gifting dinta da abubuwa ta rasa dalili, koda tajw gaida anne da safe haka ta bata wani zobe har tana bata tarihinshi, tun tana budurwa babanta ya saya mata shi, irin customize unique gemstone ne made of emerald and sapphire akayi zobe dashi, wane diamond wane gold, value dinshi ba karami bane don arziki ne mai zaman kanshi.
Daman bata samu wanda ya chancahnci yayi inheriting dinshi ba tun daga kan yayanta sai yanxu, zuciyarta ta aminta da babu wanda is more valuable da zaiyi inheriting sai sabeehar.

Haka nanna ma ta gwangwajeta da gifts da batama bude wasu ba, don basa gajiya da saya mata abubuwa, set of abayas ne, gadget ne, kai komai ma babu abunda ta nema ta rasa, wasu yan zobunan gold nanna ta saka mata a hannunta da kunenta, wai tana mace ya kamata ace tana gayu karta zauna hannunta babu zobe.
Oh wai hannun sabeeha ma kanshi dauke yake abubuwa masu daraja, haka yan chukwi chukwin hannayenta suka fito fess fess cikin zobunan.

Saukowa sukayi ita da hamad, tana gaba yana biye da ita a baya yana cracking jokes da ita, gaba daya ta gama sakewa da kowa, ta zama wata yar gayu sosai kamar ba ita ba.
Suna karasowa dining din idanunta ya suaka kan na taj, yayi kamar bai gansu ba, tunda suka kusa karasowa ya kafeta da idanu, haka kawai yaji he’s not confortable yanda ya ganta da hamad tunda ba muharraminta bane, kuma har zuwa lokacin akwai aurenshi akanta.
“Kin sauko yarinyar kirki” nannan tayi magana tana murmushi, dan murmusawa sabeeha tayi tace “eh nannan”
Kujera hanad yaja mata zata zauna kenan taj ya dago da idanunshi ya nata wani kallo daya dayasa cikinta rudawa, ta kasa fassara irin kallon gaba dayanshi, don gaba daya yanayinshi ya sauya tunda suka karaso.
Saurin kauda idanunta tayi tana hana kanta sake hada ido dashi, ta zauna a natse, daidai nan laila tayi sallama hannunta rike da warmers mai aikinsu na biye da ita.
“Good morning nanna..good morning uncle taj..”
“Good morning dear” nannan ta amsa ta taj ko ko dagowa baiba ya wani hade hannayenshi a kirjinshi, “mami tace a kawoma uncle taj da sabeeha breakfast”
“Ah lallai mami naji dasu fa, wannan exquisite breakfast haka” nanna tayi magana,
Kamshin turaren da sukaji yasa duk suka dago, anne ce ta karaso da yar sandar ta dake taimaka mata wajen takawa saboda kafa, doctor yace ta dunga yawan saukowa kasa karta lamunci zama a sama tana breakfast, wannan yasa yabxu take saukowa ayi da ita ba kamar da ba da rabi ke kai mata sama.
Rabi dake shige da fuce daa warmers da sabbin yan aiki da aka kawo su biyu tana karasowa ta fara kwasar gaisuwa sabeeha tayi saurin minkewa zata tayasu rabi tace “ah ah kiyi zamanki hajiya karama…”
“Anty rabi ki daina kirana da hajiya karamar nan ki kirani da sunana pls” ta fada adan shagwabe, duk sauta bawa kowa sha’awa so cute har wani lumshe ido take tana tabe baki, hamad ya kasa daina kallonta taj ko idanunshi na kan sa, anne ta murmusa tace “toh kin daiji ko rabi? Karki maida min jika tsohuwa, koda yake hajiya tace, ki jira taje ta sauke farali tukunna saiki kirata da hajiya da hujja”
Duk aka kyalkyale da dariya, rabi ta soma serving abunci cikin jin dadin yanda ake mata a gidan kamar ba yar aiki ba, kowa sonta yake sosai basa kyamatarta.
kai rabi tayi ma sabeeha murna sosai, tayi murna ba kadan ba, daman fa tun farko tana ganin yarinyar tasan jinin masu arziki ce, don akwaita da kyau.
Cikin natsuwa kowa keyin breKfast, babu abunda kake ji sai sautin faranti da chokula, suna gamawa rabi ta futo zasu kwashe sabeeha da laila suka tayasu, su anne kuma suka koma sitting room ita da da nanna da taj.
Laila da sabeeha na futowa suka nufi sitting room, suna karasowa sukaga babu kowa a kasan, daidai lokacin hamad yayi ma laila flashing a wayanta tana ganin call din ta dubi sabeeha sannan tace “muje garden”
Sabeeha dai binta kawai take suka futo tare, suna karyo corner wajen garden daga nesa kawai sabeeha taga an kawata wajen, suna shiga kuwa gaba daya yan kananun yaran gidan suka soma ihu harma da iyayen, “happy birthday!!!”
Wani irin shock sabeeha ta shiga ta bi kowa da kallo daya bayan daya, su anne na daga tsaye da nanna a gefenta ga bahijja da majeed suma a tsaye rike da flower bouquet ga hamad a gefensu da fadila, anty mubina ma da ya sameer na daga tsaye anty laila ce kawai bata wajen, su abla na rike da bubbles da ballons, taj kuma na daga tsaye shima daga chan gefe ya saka hannayenshi cikin aljihun sa, har zuwa lokacin yanayinsa bai dawo daidai ba.
Laila ce ta jawo hannunta zuwa gabansu ta tsaya tabi ko’ina da kallo yanda aka kawata wajen ga wani decor da akayi daga gefw an rubuta Happy 23rd birthday Fatima.
Tana kallonsu batasan sanda hawaye ya sauko mata ba, all this while bata san asalin date of birth dinta ba da cikakkun shekarunta don da an tambayeta saidai tace 20.
She can’t express yanda taji a daidai wannan lokacin saidai hawayen farin cikin kawai.
Bahijja ta tako inda take ta rungumeta sannan ta soma goge mata hawayen fuskanta kafin tace “yau kin cika shekara ashirin da uku a duniya, allah ya yi maki albarka ya kare daga duk wani sharri”
Tana gama fada ta gige hawayen datake kokarin boyewa, tunda sabeehar ta karaso wajen taji wani abu ya daketa, dakyar take dannewa kawai.
Bouquet din ta miqa sabeeha ta karba, “don’t cry okay??” Girgiza mata kai sabewha tayi alamun bazatayi ba, kafin ahankali tace “thank you Maamah na”
“Love you always and forever” bahijja ta fada tana pecking khmatunta,
Majeed ya karaso shima ya rungumeta sosai yana farin ciki yace “happy birthday my princess…”
“Thank you dada” sabeeha ta amsa tana murmushi, haka suka bita daya bayan daya suna rungumeta, she felt their unconditional love har cikin zuciyarta.
Bahijja ta fidda wata dankararriyar set din sarkar gold da tasha wani mahaukacin package, ta fiddota waje sannan ta saka mata a wuyanta, tana gama saka mata tace “toh muje muga gift din daddy ko”
Duk suka dunguma zuwa compound din gidan, suna fitowa maaikatan da sukayi delivering package din suka soma budewa, wani katon kwali ne mai girman gaske suka soma dagawa har sukayi nasarar cireshi gaba daya ballons masu shegen yawa suka zubo, take wata dankareriyar mota ta bayyana, fara tarr irin Porsche dinnan ta mata, shock din data shiga ita kanta ji take kamar ba a dubiyar take ba, daddy ya danqa mata keys din porshe din mai kyan gaske, “this is from daddy, but….saikin gama school zaki fara tuqawa okay???”
Bai gama magana ba sabeeha ta duqa har kasa ta rasa da wnai baki zata masu magana, she’s speechless,
“Oupps anne fa tace kujerar hajji na jiranki next year insha allah” fadila tayi magana tana murmushi, sabeeha najin tayi sujjada ta godema Allah tana kuka, jikinta da bakinta na rawa tace “bansan ta yanda zan gode maku ba, allah yasa da alkairi, ban taba tsammanin zan samu irin wannan gatan ba maamah, dada,.. im bery grateful allah ya saka maku da mafificin alkahiri yaza kufi haka ya daukka ku ya tsareku,” tana gama fada ta dubi ta dubi sauran dake tsaye sannan ta cigaba “anne..nanna…mami,(fadila) ya hamad dady abla (uncle sameer) anty mubina, cous (laila) sunan da take kiranta yanxu kenan, ya hamad..daidai wajen taj ta dan dakata tana kallonshi cikin ido sannan tace “uncle taj… i will like to thank each and every one.. bansan da me zan saka maku ba,“
Yanda take magana saida ta basu tausayi, magana take jikinta na rawa tsabar murna.

“Mami ku bari na daukemu pictures” laila tayi magana aka tsa tsaya ana picture, kowa har rushing suke wajen daukan picture din da ita, laila ta dubi ya hamad tace “ya hamad ka shiga a maku”
Dan matsawa yayi gefen sabeeha rike da bouquet aka dauke su a hoto, ganin sun danyi nesa da juna yasa laila cewa “ya hamad ka matsa sosai mana baiyi kyau ba ka tsaya kamar soja”

Tana fadin haka ta dan matsar dashi kusa da sabeehar sosai, anne da nanna suka murmusa, anty fadila ma murmushin tayi kawai.
Ana gamawa laila ta dubi taj dake tsaye ya hade rai shidai bazaka taba tantance yanayin da yake ciki ba koda yaushe mood dinshi daban ne.
“Uncle taj picturesss”
Kamar bazai motsa ba chan kuka kawai sai ya matso, shi baima tsaya ya bama laila damar cew baiyi kusa da sabeehar ba don baima bada wani gap ba jikinsu na gogan juna,
Laila ta soma daukan pictures din, kai wallahi ba karamin matching sukayi ba abunda, sai wanda ya hango hadewarsu.
Ba a gama daukan hoton ba sabeeha ta zaro idanu gabanta na faduwa jin hannunshi a ta wajen ass dinta, cikin sauri ta dubi su bahijja ganin hankalinsu baya garesu yana ga motar da dady ya saya mata suna dubawa ita kanta lailar bata lura ba don ta baya ya dora hannunshi a wajen, daya tashi ma palm dinshi biyar ya bude yayi ya dora a wajen kamar wanda zaiyi spanking ass dinta.
Juyowan datayi ta dubeshi in so much shock yasa shima ya kalleta fuskar nan babu annuri kwata kwata, jikinta ya soma rawa cikin sauri ta matsa daga kusa dashi kamshinsa ya biyota.
Gaba daya aka tattara aka koma cikin gida.
Maya dake labe wajen entrance din apartmanı dinsu duk abunda ya faru akan idanunta, tun bayan futar bahijja daga dakinta don tana tashi da safe bahijja ta shugo dakin ta don taji ya jikinta, don kwana tayi da ciwon kai, gaba daya ta daina sakewa sosai kullum tana daki, har abun ya soma damun bahijja,ta nuna mata ta cire komai aranta ta mance da komai amma taqi, tana shigowa dakin as usual yanda ta saba duk zagayowar shekara she will be the first da zatayi wishing mayar tare da mata adduar shekaru masu albarka don bazata taba mancewa da ranar haihuwarta ba musamman yanzu da komai ya sauya.
Haka ta shigo mata da gift sannan tayi wishing dinta, gidan yan boko kenan😂
Maya na kuka ta karba gift din tare da rungume mummyn, atleast yanxu ta kara tabbatar da suna sonta kuma yace a wajensu dukda basu suka haifeta ba.
Saidai kuma tunawa da wani abu yasa taji jikinta yayi sanyi sosai, idan yau birthday dinta to tabbas yau ne na sabeeha ma, kai wannan wace iriyar kaddara ce, ta rasa wanne yafi mata zafi aranta the fact that ita ce aka sauya da sabeeha kuma ta kasance itace yar mai aiki ko kuma sabeeha data kasance yar masu gida, duk ci cika bakin nan nata a banza, da wulaqancin data dunga yima sabeehar ta kirata da yar talakawa mara uba mara gata ashe itace da wannan matsayin ba sabeehar ba, idan ta tuna da wannan abu ji take kamar….
Kafin bahijja ta fita daga dakin ta shiada mata ta futo tayi breakfast tace mata kanta na ciwo, hakan yasa bahijja tace toh basira zata kawo mata, allah sarki duk yanda tayi haka bahijja ke binta dashi, babu abunda ta sauya game da kulawa da take mata, tana son maya hakika har cikin zuciyarta sosai ba kadan ba.
Tun bayan futar bahijja ta kasa natsuwa, wani abu na ce mata ta futa, haka kawai taji shes restless tayi gathering courage dinta ta futo, tana futowa bata kaiga shiga main house ba ta jiqo muryoyinsu daga compound tana karasawa taga surprise din da aka shiryama sabeeha, saida taji wani dumm akanta kamar zata fadi, ta kafesu da idanu batasan sanda hawaye ya soma sulalo mata ba ta koma part dinsu da gudu, a daidai lokacin su kuma suka fito daga garden, bata hakura ba ta sake lekowa nan ne kuma ta kara ganin abunda ya sake hargitsa mata lisaafi, ta kafe kaff ta kasa motsawa ta bisu da ido daidai lokacin da daddy ke presenting motar daya sayama sabeeha, daga nesa tana hango fuskar sabeeha ta kafeta da idanu, reaction dinta na sauyawa kamar ba ita ba, da kuka take amma tuni kukan ya kafe abubuwa na running a mind dinta, wani zunzurutun shaidani na tunzirata yana ayyana mata negative abubuwa a mind dinta, take taji tsanar da takema sabeeha a baya ma ay wasa ne, yanxu ne takejin tsanarta ninkin ba ninki, babban farin cikin ta a duniya yanxu shine taga sabeeha bata nunfashi a doron kasa.
A daidai lokacin ne kuma aka fara duakar hoto,gaba dayansu tana kallon yanda sukema sabeehar saitaji dukkansu ta tsanesu suma, sanda taga hannun taj a kan ass sin sabewha kuwa batasan santa ta dunkule hannunta ba zaro zaron farcenta ya soma ji mata ciwo don harta fara bula fatar tafin hannunta, ya soma fidda jini, idanunta yayi jaa sosai, ta soma magana ahankali.. “,sanadiyarki na rasa duk wani farin ciki na, kinyi nasarar kwacemin komai nawa, i wish you never exist, you can have it now while it last kafin na kwace duk wani abu da kika rabani dashi… nayi alkawari bazan barki ba koda kuwa zai zamo na kasheki ne da hannuna saina dandana maki pain din da kikayi sanadiyarsa a cikin rayuwata”
Tana kaiwa nan ta wuce part dinta sai kuka, kuka take wiwi wiwi saida tayi mai isarta kafin ta dakata tunawa da kuka yanxu ba nata bane, dole ta samu hanyar da zatayi ta mallki taj kota halin qaqa, yanxu trick din da takema mommy bazaiyi amfani ba don idan tayi a lokacin tana amatsayin yarta da duk abunda ta nema zata mata yanxu ko ba lallai ta yi mata abunda take so ba, kuma ta tabbata yanxu da suka san asalinta babu wanda zai sake maganar aurwn nasu musamman mummyn ma, balle kuma akaiga anne, da tun tuni daman bata amince ba balle kuma yanxu?, dole tayi fiding solution duk yanda za ayi ta mallaki taj kota halin qaqa ne, atleast tasan daga nan duk wani abu da zai biyo baya mai sauqi ne.


MATAR TAJ (destined with you)
   Written by 
          Queenmarh

Book2 
PAID
Chapter 56 · 0% Book details