← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 47 OF 66

Chapter 100

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 40 min read

Saida yakai ta karshen bangon kamar zai hade jikinshi da nata ya kureta da idanunsa da sukayi jaa sosai hannayensa kuwa har zuwa lokacin da jikinsa bari suke kamar mazari, tsoro gaba daya ya dirar mata amma ta danne sosai taki yarda su hada ido don gani take kamar zai gano ta.

Bakinta na rawa tace “you’re hurting me” ta fada ahankali idanunta na kawo kwalla, allah allah kawai take ta kubce masa.
Word by word yake kallon bakinta yanda take magana, yabi fuskarta da kallo tundaga kan idanunta zuwa hancinta da dan bakinta dake motsawa, ya shagala sosai wajen kallonta kuma bai saki hannun nata ba rabi ko na daga tsaye gaba daya mamaki ya gama cikata.

Wayarsa da karar ta katse moment dinne yasa shi dawowa hayyacinsa, yayi saurin sakin hannunta dayayi jaa tsabar kamawa da yayi, yana sakinta kuwa tayi hanzarin rabawa gefe wajenda rabi ke tsaye, gaba daya a furgice take ita kanta.
Runtse idanunshi yayi bai sake kallon inda take ba ya futa daga kitchen din.

Kallonta rabi tayi tace “akwai wani abu ne tsakaninku?”
Dam gaban sabeeha ya bada ta fara wulla idanu kamar munafuka, “ni ban taba ganinshi bama sai yau,ko magana bata taba shiga tsaknaina dashi ba anty rabi”
Shuru rabi tayi don tunaninta gaba daya bai tsaya ko’ina ba sai kodan maya tace sabeeha ce tare da anne lokacin data fadi, amma da sabeehar ta mata bayani saita fuskanci komai, don tana barin wajen anne ta wuce dakinsu sabeehar ta shiada mata anne na nemanta ita kuma sabeehar ta hau sama.
Gaba daya jikinta mazari yakeyi har ta futa daga kitchen din bata waiwayi rabi ba, gabanta wani irin mumunan faduwa yakeyi ta wuce daki, tana shiga ta tadda basira kwance kan gado, toilet kawai ta shige idanunuta na cicikowa da hawaye ta shiga ta rufe kofar tare da tsayuwa jikin kofar, kukan da take boyewa tun dazu ta fashe dashi sosai, gaba dayan taa koma wata jajawur abunka da farar fata, fuskanta ya kankance sosai batama san ta zube a kasa wajen kofar ba, hade jikinta tayi bakin kofar tare da chusa kanta tsakanin kafanta tana hawaye kasa kasa “ya zanyi? Innalillahi wa inna ilaihi rajiu’n yanxu idan ya ganoni ya zanyi? Noo..i will never let that happen,“ tana fadin haka ta sake fashewa da kuka, daga nan ta fara sakawa da wararwe da zuciyarta, “kodai nace wa mama ta maidani lafiya?” Tunawa da karatunta yasa taji wannan ba option bane, harga allah tana son karatunta sosai, akullum in taji hadiza na cewa zata maidata wajen dangin ubanta saitaji gaba daya hankalinta ya tashi sosai, tsagaitawa tayi da kukan da bazai amfanera ba ta tambayi kanta? Ya zanyi na kubce masa?” Tasan cewa tunda har ya ganta bazata iya masa wasa da hankali ba ta hanyar karyar cewa ba ita bace ba, kuma ta dauki kudirin duk yanda za ayi saitayi denying dinshi, bazata taba bari ya gano ita ce ba.
Maganganu ta soma ji daga cikin daki wanda yasa ta wanke fuskarta gaba daya ta budo kofar tare da futowa,“ yauwa babarku ta shigo yanxu tana kiranki” basira tayi magana tare da juyawa tana latsa yar nokia ta.
Gyaran dankwalin dake kanta tayi tare da fucewa daga dakin ta nufin dakinsu bakinta dauke da sallama.
Hadiza dake zaune bakin gado wayar dake makale a kunenta tayi saurin ajewa tana kallon sabeehar daga sama har zuwa kasa, “zauna mana kin tsaya min a ka” hadiza tayi magana babu wasa.
Zama sabeehar tayi gefe yanda hadizar na fuskantar kafin hadizar tace “daxu da kikaje bangaren hajiya kafin ta fadi kunyi wata magana ne?”
“Ah ah, ina shiga na tadda ta yanke jiki ta fadi”
Shuru hadiza tayi tana wani nazari kafin tace “zamuyi wata magana, yanxu, bawai ina neman yardarki bane ko amincewarki, umarni ne zan baki, kuma daga dangin ubanki”
Tunda hadiza ta soma magana gabanta ke faduwa sosai ba kadan ba.
“Kanin ubanki ya kawo mijin aure kuma na amince don harna bada ke, saboda haka inason ko hajiya ta tambayeki amincewarki kice kin amince kina jina ko”
Ta karashe kamar da fada fada, wani irin gumi ne ya karyowa sabeeha kamar ta watsa mata garwashi a jiki, “zaki iya tafiya”
Tunda ta miqe ko gabanta bata gani kwata kwata, don wani irin duhu duhu take gani, haka ta lallaba ta wuce daki allah yaso basira bata ciki ta zauna gefen gado tare da dafe kanta dake mata azababben ciwo sosai, abubuwan sun mata yawa ta rasa wanne zata dauka.


Ban garen taj bayan futarshi daga main house bai tsaya ko’ina ba sai part dinshi, har zuwa lokacin jikinsa bai dawo daidai ba, kanshi yayi rudu rudu jiniyoyin duk sun tashi, ya karade ya koma jaa sosai.
He’s so confused at the moment ya rasa wani tunanin zai fara.
Yana shigowa bedroom ya wuce sama direct tare da zama gefen gadon ya dafe kanshi moment din dazu na zuwan mashi, ko a mafarki bazaiga fatima ya kasa shaida ta ba balle a zahiri,gaba daya daga jikin shi har zuwa zuciyarsa sunsan da presence dinta a kowane lokaci, tunani da yake yawo akanshi bai wuce “to kodai he’s mistaken ne? Koba fatimarshi bace? Amma zuciyarsa ta rigada ta amince da itace, fatima ce duk denying din da takeyi, amma meysa ta nuna kamar bata sanshi ba? Why? Why?” Shine tambayoyin daya kasa bama kanshi amsa, sai amsa guda, daya bama kanshi, “kodai saboda abunda ya mata a baya? Ko saboda korar wulaqanci daya mata? Infact ay a wajenta babu komai a tsakaninsu, tunda ya yanke duk wata alaqa a tare dasu lokacin daya mata korar wulaqanci, saidai kuma ta bangarenshi daya san cewa matarshi ce har a zuwa yanxu, don bai saketa ba, dukda a lokacin daya gano cewa babu cikinshi a jikinta har ya janyo ya koreta daga gidan har hidaya ta kawo mashi takardar divorce baiyi gangancin rabuwa da ita ba, zuciyarsa bata taba yarda da yin haka ba, kuma bata amince da yin haka ba, don tun a alokacin ya san cewa bazai taba iya rabuwa da fatima ba, ya kasa rabuwa da ita, yakai wajen awa guda bai motsa ba yana wani dogon tunani, kanshi wani irin ciwo yake masa tsabar confusion din da yake ciki.

Acahn asibiti kuwa nanna ce kawai ta lura da baya wajen, sunkai wajen 3hrs lokacin ana gab da magrib har zuwa lokacin anne bata farka ba, nanna tasa hamad ya maido dasu maya da laila, ya rage daga anty fadila sai nanna da ya sameer, matanshi da sukazo suma nanna tasa ya maidasu gida saiya zamana daga nanna sai anty fadila ne kawai yanxu a Asibitin.
Anty fadila ta kira anty bahijja ta shiada mata, yanda hankalin kowa ya tashi itama haka nata ya tashi sosai ba kadan ba.
Misalin karfe takwas sai gashi ya dawo asibitin, cikin dakin ya shiga ya tadda anty fadila gefen gadon inda anne ke kwance ita kuma nanna na kan sallaya bata dade da idar da sallah ba.
Sallamarsa tasa suka juyo gaba daya bayan sun amsa
Nanna tace “ ka dawo?”
“Eh” ya amsata kasa kasa tare da tambayar ya mai jiki sannan ya gaisheda antyy fadila dake zaune.
Wajen da take zaune ta tashi ta bashi waje ya zauna yana kallon anne dake sanye da kayaj asibiti, an daura mata oxsygen a hancinta don ya taimaka wajen regulating nunfashinta, lokaci guda gaba daya ta rame sosai, wani irin tausayinta yakeji don allah kadai yasan irin abunda takeji, cuta ba mutuwa ba Allah ya tashi kafadunta Ameen.
Gaba dayansu kowa tsoron rasata yakeyi, don itace jigon su gaba daya.
Tashi yayi ya koma gefen nannan don tana kusa da 3 leather seater anan ta shimfida abun sallah, kafin kasa kasa ya soma magana da ita “oummi, ina ganin maizai hana a futar da anne kasar waje? I believe sai tafi samun kulawa ta musamman achan tunda akwai kwarrun neurologist around the world”
Shuru nanna tayi tana nazarin maganganunsa kafin tace, “ina ganin mu fara gwada na nan din tunda doctor barau yace she’s under treatment idan abun bai yuwu ba sai a fitar da ita”
Suna cikin magana dr ya sake shugowa da kanshi, aka cire drip din da aka saka mata tare da daura wani sabo, sannan yayi mata yan gwaje gwaje kafin ya futa.
Futarshi babu jimawa uncle sameer ya dawo, yana shugowa nanna tace “harka dawo babban yaya?”
“Eh ya mai jiki?” Ya tambayeta
“Da sauqi”
“Allah ya tashi kafadunta”
Gaba daya suka amsa da Ameen.
Sun jima sosai a asibitin har wajen karfe goma, dinner da aka kawo daga restaurant din asibitin babu wanda ya taba bawai don wani abu ba saidai gaba daya kowa yayi loosing appetite gaba daya.
Taj dai tunda ya zauna kan kujerar nan babu abun da yake sai tunani, he looks so lost and disturbed, ba tun yanxu nanna ta lura da haka ba tunda ya shugo taga hakan a fuskanshi, abunda da farin mutun.
Ahankali nanna ta dafashi ganin yayi nisa cikin tunanin da yake kamar baya jinta gaba daya, tunani take mai zai sashi fadawa dogon nazari haka ta har zata kirashi wajen sau uku amma bai jiba.
“You look disturbed, are you okay?”
Hannunshi ya aza ga fuskanshi ya shafo lallausan gashinsa tare da sauke ajiyar zuciya yace “yes I’m fine”
Shuru nanna tayi kafin tace “ ku koma gida zan zauna da yaya,kai sameer ka maida fadila ta dan huta gashi tabar iyali a gida”
Cikin hanzari tace “ah ah nanna, zan kwana anan kece ya kamata ki tafi saboda yanayinki kema”
Jin fadila tayi magana yasa sameer cewa “gaskia hakan ya kamata, tunda ga yanayinki kema nanna”
“Nidai da kun barni na zauna da yar uwata nayi jinyanta” ta sake magana tana dafe kirjinta dake mata dan ciwo ciwo tun daxu amma ta daure, yawan stress ke jawo mata hawan jini sosai.
Da larabci ya soma magana yana kallon nanna, “please oummi, anne would not be happy idan kema kika kasance a kwance anan, you don’t look alright as well kuma kinsan abunda doctor yace you shouldn’t be stress out okay?”
Badan taso ba tayi shuru kawai batace komai ba.
Dagowa yayi ya kalli anty fadila da sameer kafin ya suake ajiyar zuciya yace “uhm..ina ganin kuje kawai gaba daya zan zauna anan, kamar yanda nanna tace, yayi nuni da anty fadila “she also have a family waiting for her, kuje kawai zan zauna da ita duk wani abu daya taso i will inform you immediately”
Jinjina kawai sameer yayi sukayima taj sallama harda anty fadila wadda itama bataso tafiyan ba suka fita.

Actually he needed alone time specifically a wannan lokacin da kuma situation din da yake ciki, he needs to sit and think critically about everything.
Tun bayan futarsu sau biyu doctor barau ya sake shugowa don duba yanayin anne, ya kara ma taj bayanin situation din nata yanda zai gamsu don harga allah shi yana recommening a futar da ita sainyanxu ya gane a wannan yanayin futar da ita can risk her life dama dai ba a fara treatment bane to da sauqi.
Yana daga zaune by the 3 seater dogayen kafafunshi na kasa while jikinshi gaba daya yayi relaxing a jikin kujerar, babu abunda yake sai tunanin fatima,wani irin fargaba yake jin datake sashi shiga yanayi.

Washe gari da sassafe anty fadila da sameer suka iso asibitin tare da hamad, nanna na gida saboda jininta daya dan hau, bayan sun gaggaisa suka tambayeshi ya jikin anne ya masu bayani kafin sameer yace “ya kamata kaje ka huta, we will handle”
Jinjina kai kawai taj yayi, kana ganinshi kasan baiyi barci ba kwata kwata daren jiya don daga yanayinshi ma zaka gane.
Sallama ya masu ya futa daga asibitin ya shiga motanshi.
Yana kunnata yayi reverse bai tsaya ko’ina ba sai gida lokacin wuraren karfe takwas da rabi ta dan gifta.
Yana isowa yayi packing tare da kashe motar ya futo, ya nufi hanyar part dinshi, bai kaiga karasawa ba ya dan dakata ya dubi main house, a dai dai wajen da idanunshi ya sauka kan inda ta tsaya iiya lokacin daya fara ganinta a gidan, saurin kaud akanshi yayi ya wuce part dinshi direct.
Wanka yayi ko cire towel din jinkinshi baiyi ba ya hau kan gado ya kwanta ko minti goma baiyi ba barci ya kwasheshi.
Barci ne yakeyi bawai don dadi ba saidan jikinsa na buqatar hakan don kwana yayi yana tunani aranshi.

Ta bangaren sabeeha ma hakan ta kasance don bata samu tayi barci ba, kwana tayi tana rokon allah ya shiga lumuranta, maganar auren nan da mama ta bujiro mata ba karamin girgiza ta yayi ba idan zata so kanta harga allah babu maganar auren a burikanta na yanxu, karatu takeso tayi ta inganta rayuwarta, wannan karatun yasa ta taji tana da hope a rayuwa.
Bayan wannan tunanin yanda zasu dunga haduwa da taj take, ta yaya zatayi avoiding haduwa dashi?ya rigada ya ganta, gashi ta kasance itace yanxu mai gyaran part dinshi, tunawa da wannan kadai yanasata shiga tashin hankali.
Gaba daya duk tayi sanyi haka ta futo suka shiga kitchen da su rabi.
Tana tsaye kan counter tana fere dankali gaba daya kowannensu yayi jugum jugum, tun jiya gidan bai dawo daidai ba saboda abunda ya faru da anne.
Cikin abunda hai wuce 2hours ba suka kammala komai kafin a fara jerawa dining, suna gama komai ta koma daki ta zauna tare da tagumi.

Tsoron futa take gaba daya gudun karta hadu da kowa, tunawa da maganganun rabi datayi dazu na cewa duk sun tafi asibiti yan matan ne kawai a gidan da nanna yasa tayi tunanin allah yasa harda shi.

Batasan da shugowar basira ba sai ganinta datayi tsaye a gabanta “bazaki tafi kiyi aikinki ba yau kika zauna?”
Dagowa tayi da rinannaun idanunta ta kalli basira tace “dan allah zaki iya taimaka min yau? Cikina ciwo yake sosai”
“Gaskia bazan iya ba wallahi, ayyuka sunmin yawa lokacin da nake son yi ba a bani ba sai yanxu, bayan wannan ma daman saboda naga balaraben nan ne tunda baya gidan babu amfani”
Sabeeha najin haka hankalin ta ya kwanta sosai.

Yau Kwanan anne biyu asibiti, alhamdulillah ta farfado kuma shes under treatment, gaba daya yan gida duk safiyar allah suke tafiya asibiti, daga ranar da taj ya kwana anty fadila tayi insist kan cewa itace zata dunga kwana da anne, shi namiji ne ba kowanne irin hidima da ita zai iya ba musamman yanxu data farfado dukda akwai nurses specifically da suke kula da ita sosai.

Cikin kwana biyu nan kiri kiri sabeeha taki yarda taje tayi gyaran part din shi gudun haduwa dashi, su rabi ma duk sun ziyarci asibiti amma banda ita, harda hadiza ma.
Bangaren shi kuwa saiya shugo main part sau nawa da zarar ya dawo daga asibitin hoping ko zai sake ganinta amma abun ya ci tura, kamar babu existence dinta a gidan.

Don ya kara tabbatar da ita dince wannan yasa salim ya kira jamilu, suka sake zuwa har estate din jamilu ya shaida masu anan suke ita da babarta,kuma ya kara tabbatar masu da itace dai yarinyar da suke nema.


Saturday morning..
Bayan sun gama breakfast an jera wanda za a kai asibiti sai kuma na yan gida wanda zasuci, suna gamawa ta wuce daki direct ta zauna tana tunanin yanda zatayi, tunda rabi ta lura kwana biyu batayi gyaran part din chan ba yasa tace mata taje ta gyara.
Daman karyar ciwon ciki takeyi, kar abun yayi yawa yasa ta danne zuciyarta kawai ta miqe tare da gyara hijab din data saka ta futo.
wannan boye boyen da datakeyi ne zaisa shi ganewa itace, and bataga dalilin da zaisa ta dunga boye masa ba, koda ya gano itace batada wani alaka dashi he’s a completely stranger to her kuma she will stand by it.

Gaba daya tayi wani fayau har yar rama saida tayi saboda tunani ya mata yawa,Sauri take kamar zata harde kafafunta ta nufi part din nashi, ahankali ta bude kofar tare da sanyo kafafunta a ciki, duk fitilun part din a kashe suke alamun babu kowa a ciki wannan yasa aggaguce ta wuce kitchen ta dauko vacuum da mops ta futo dasu ta fara gyaran part, da kasa ta fara kuma babu wani dattin kirki wannan yasa ta gama cikin sauri.
Tana gamawa tayi yan goge goge, bayan ta gama ta dauka vacuum din ta wuce sama, tunda ta fara hawa stairs dun ta rasa dalilin dayasa gabanta ke faduwa kamar ana lugude, duk a tsorace take gaba daya.
Ahankali ta sanya hannu ta bude kofar bedroom ba tare da tunanin yana ciki ko baya ciki, tadai san adaidai irin wannan lokacin idan tazo gyara mostly baya dakin.
daga waje baka hango komai saboda dakin gaba daya duhu ya lulubeshi, sanin inda switch din fitilun suke yasa ta saki kofar ta rufe ta nufi wajen switch din, tana kaiwa wajen ta sanya hannunta a wajen taji kamar hannun mutun a wajen, take gabanta ya wani irin fadi, zata kwala ihu yayi saurin kunna hasken, gaba daya hasken ya bade ko’ina, gabanta ya wani irin bada damm ganinshi a tsaye a gabanta,taga taga tayi zata fadi don yana kunna hasken idanunshi ya shiga nata, yana tsaye dagashi sai towel kamarma futowanshi kenan daga wanka don ga leman ruwa na sauka a huge kirjinsa, jikinsa sai glowing and tempting yake, wallahi jintayi kamar tayi futsari abun yazo mata ba zata, fuskanshi ko babu wasa ya dubeta da kyau sai wani kakkauda ido take kamar munafuka.
Zuciyarsa kamar zata fito tsabar bugawa da takeyi, daya sake arba da ita a karo na biyu, babu abunda zuciyarsa keyi sai tsalle, kallonta yakeyi sosai tunda ga sama har kasa, abun yana mashi kamar a mafarki, hannunshi na jikin switch din ya kasa cirewa,tana sanye da bakin hijab fuskanta ta dan rame, kyawunta ko yana nan babu abunda ya sauya, bayajin akwai wadda yakejin komai nata na burgeshi kamar na sabeeha kodan ta kasance wani bangare na rayuwarshi, yanaji kamar ya kamata ya rungumeta a jikinshi kozai daina jin tiririn dake tsatso masa, kokari yake sosai wajen dannewa.
Zama yayi tare da yin dogon tunani da nazarin dalilinta na nuna kamar bata sanshi ba, yanda ta dunga avoiding dinshi da yanda take shugowa dakin da hijabi ta rufe fuskanta tana avoiding haduwa dashi, Hakan ya kara tabbatar mashi da komai,kwata kwata tunda take zuwa gyaran part din bata yarda su hada idanu ko magana batayi saboda karya ganota shiyasa ma yayi tunanin kodai she’s mute don bai taba ganin fuskar yarinyar dake zuwa gyaran part din ba, yadai san house maid ce kuma bawai yana basu attention bane, lokacin daya fara jin murayanta kuwa a part din nanna saida yaji wannan spark,kuma ba tun yanxu ba yakeji tana kusa dashi jikinsa na bashi hakan amma bai lura da hakan ba.


Bayan wannan maganar da jamilu yayi na cewa ita da mahaifiyarta aiki suke a gidan yasa shi kara tabbatar da ita ce, wannan kakkaucewar da takeyi saboda karya ganta ne donta ganshi shi, baisan dalilinta ba amma zai bita a haka har saita fallasa kanta.
Yanda ta nuna batasan koshi waye ba zai bita a haka amma zaisata da kanta ta tona kanta.

Tundaga ranar daya ganta ta nuna bata sanshi ba kuma bata taba ganinshi ba bai sake ganin ta ba sai yanxu, boyewa ma takeyi karya ganta and for sure yanxu haka batayi expecting ganinshi ba.

Cikin gaggawa ta soma daidaita natsuwarta, ta fuske tare da hade rai sosai tana kauda kanta gefe tace “I’m sorry sir, bansan akwai mutun ba a cik…”
Da gatsali tayi maganar kuma abun ba karamin mamaki ya bashi ba, don zai iya rantse wa this is not the calm and peaceful fatima daya sani, this is the other side of her da bai taba sani ba don at this point he can believe ba itace ba, amma he wants to take everything slowly, ya gama yarda da dalilinta na nuna kamar batasan dashi ba saboda abubuwan dayayi mata ne.

Dauke idanunshi yayi bai sake kallon inda take ba ya nufi wajen bedside ya dauka remote din ac ya kashe sannan ya aje tare da juyowa tana ganin haka ta nufi hanyar futa cikin hanzari harta sa hannunta jikin handle yayi saurin dakatar da ita “i mistake you for someone else…my apologies”

Chak ta tsaya tare da mamakin maganarsa sosai, bai gano ba? Ya yarda ba ita din bace? Wata ajiyar zuciya ta sauke jin maganar tasa and how cold he is compared to jiya daya ganta.
Har ta bude kofar muryarshi ta sake dakatar da ita this time around saida taji wani iri, “stop there waya baki iznin fita? Aren’t you here to do your job? Then do it properly”
Sakin kofar tayi ta dawo jiki a mace hannunta rike da vacuum din da abubuwan goge goge, har zuwa lokacin bata yarda ta dago ta kalleshi ba ta wani hade rai ko kallon fuskansa bata sonyi.
Yana ankare da yanayinta which make him wants to go easy on everything.

“Why are you here? Whats your job here ?” Ya tambayeta ba tare da ya kalleta ba

Kai tsaye tace “I’m assign to take care of this part,“
“Are you also assign to disrespect your masters?” Da sauri ta dago ta kalleshi ta rasa inda ya dosa gaba daya.
“No sir” ta bashi amsa a gadarance trying to show him apposite of fatiman daya sani.

Daga yanayin fuskanshi zaka gane babu wasa shima, indai har ya yarda ba itace sabeeha ba to dole zaiyi treating dinta as yar aiki,and she wouldn’t mind hakan indai har bazai gane itace ba, duk wani abu daya danganci tarihinta a saudi dashi ta bunne shi kuma bata fatan tonoshi, yama za ayi ta bari asan cewa ta kasance matarsa a baya lokacin da baya cikin hayyacinsa, inda ya taka ma bata isa ta taka ba no one will believe that gwara ma a tsaya a haka bata sanshi ba kwata kwata, tunda ma bata da wata alaqa dashi ayanxu, this is for the best.

“Okay.. i have my rules and you must abide, firstly zakiyi gyaran part dinnan sau uku a rana, and you must be on standby when ever i need a job to be done asap, secondly my breakfast lunch and dinner will be served here as early as possible, and you have to be clean as well i hate to be disgusted, thirdly don’t you dare step in here with the intention of disrespecting me” yana kaiwa nan ya dubeta don ganin yanayinta.
Kwata kwata yanayinta bai sauya ba, saima hade rai datayi sosai chan cikin zuciyarta kuwa mamaki ya gama cikata sosai.
Gyaran murya yayi dayasa ta dan dago ta kalleshi shima ya kalleta fuskanshi ba yabi ba fallasa, “okay sir” ta amsa
“What are you standing here for? Do your job”
Kofar ta bude ta futa tare da rufewa, tana futa ya runtse idanunshi ya budesu lokaci guda suka karade sukayi jaa sosai, kamar yau ya fara jin muryanta a kunneshi, yarinya ce dole ya bita a haka, bazai iya misalta irin shauqi da dadin da yakeji ba da zarar ya ganta.

Baiga laifinta ba idan ta nuna bata sanshi ba don harga allah bai mata adalci ba bai mata halarci ba kwata kwata.
Bai taba tunanin it will turnout like this ba kwata kwata its time for him yayi mata halarci ya biya alkhairin datayi masa.

Bangaren sabeeha ta rasa me zataji aranta zafi ko dadi? Tafi jin dadin haka don duk a tunanin ta ya yarda ba ita din bace, ta wani bangaren kuwa wani iri takeji ta rasa dalili.

Cikin gida ta koma ta shaidama rabi komai da abubuwan daya buqata, rabi tace “toh shiknn tunda daman gyaran part din na hannunki”
Tana son tambayar yaushe za akawo wadda zata karbi aikin part din don kwata kwata bata son shiga bangaren nasa, saitaga kamar hakan bai dace ba.
Wannan yasa ta har harda komai ta dauka tray din ta wuce part dinshi dasu.

Tana zuwa ta jera a dining, tana cikin yin hakan saigashi ya sauko kasan, kamshinsa ne ya bugi hancinta daya sa ta dago da sauri, yana daura agogon hannunshi, sanye yake da jallabiya fara tass, da bakin takalmi gashinsa ko sai walqi yakeyi sosai, yana kokarin juyowa inda take ta dauke idanunta.
Smirking yayi tare da tunkarar dining din ya ja kujera ya zauna,
Bata yarda ta kalleshi ba fuskanta babu walwala kwata kwata tace “what would you like to have sir?”
“serve me anything preferably to my taste”
Sanin abunda yafi so kafin yaci komai coffee ne yasa ta deba mashi a mug tasa sugar cube biyu kawai turawa gabanshi, aynxu hakan ma ta fallasa kanta ba tare da saninta ba.
Kallon mug din yayi bai dagoba yace
“I never mentioned having coffee first”
Tana kokarin bude warmers kwata kwata batasan doguwar magana ta shiga tsakaninsu allah allah kawai take ta fita daga part din batama san tace
“You prefer having it first before having meal”

“How did you know?” Ya jefo mata tambaya unexpectedly
Chak ta tsaya da abunda take gabanta ya wani mugun faduwa ta fara wulla idanuwa, batasan banbaramar dataso yi ba sai yanxu, “uhm????” Ya sake tambayarta yana relaxing bayanshi akan dining din tare da hade hanneyenshi kamar wanda ke questioning wanda ake tuhuma ya kureta da idanunshi.

This time around yanda yayi maganar clamly yayi, kuma tanajin yanda idanunsa ke yawo akanta.
“You ask for anything preferable to your taste, and I assumed you will prefer having coffee first”

Smirking ya sakeyi wanda ya karama fuskanshi kyau sosai bai sake cewa komai ba, he wanted the conversation to be long saidai bayason ya bata impression din cewa ya gano ta.
Baitaba tunanin yarinya ce ba shar sai yanxu, in badan yarinta ba how can she even think of tunanin bazai san itace ba.

Tana gama serving tabar wajen tare da hawa sama don tsaftace wajen.
Harta gama yana zaune dining ya kasa cin abunci coffee din kawai yasha, dake daga hannunta ya futo sai yaji ya fita daban, he missed yanda take kula dashi sosai acahn saudi, everything about her is just different.
Tashi yayi daga dining din ya dawo sitting room ya zauna.
Tana gamawa da saman ta sauko kasa ta tattara abubuwan dake dining din ganin ko abunci bai taba ba sai coffee din kawai dayasha ta fara tunanin ko bai iyacin abuncin nan din bane kauda tunanin kawia tayi ta kwashe komai ta nufi hanyar futa ba tare da takai idanunta ga sitting room ba inda yake zaune tana gab da futa Wayar shi tayi ringing yayi sauri dauka tare
dakaiwa kunnenshi “wa alaikum salam khaal”
Chak ta tsaya jin abunda ya fada yanxu, da larabci yayi magana kuma taji komai, cikin sauri ta juyo ta kalleshi, ya kauda idanunshi kamar bai ganta ba ya cigaba da wayanshi.
Juyawa tayi ta bude kofar ta futa tana contemplating abunda kunenta ya jiyo mata, tabbas taji yace khaal, saurin girgiza kanta tayi tana hana kanta tunanin komai, da wani khaal din yake waya? Khaal din daya mutu? Kai abundai yana neman hargitsa mata tunani.

***
Karar wayar dayayi yawa ne yasa jamilu miqewa ya zare charging wayar sunan daya ga anyi saving da dahiru ne yasa shi daukan wayar da mamaki.
Yana kaiwa kunnenshi dahiru ya soma magana “wai wannan wani irin wulaqanci ne jamila?ya kuke neman yimin yawo da hankali ne karku nemi ku raina min hankali, tun jiya nake kiranki bakya dauka, wallahi tallahi idan kuka nemi raina min hankali zan tona ta fashe da kowa na rantse da allah, tunda har na kwallafa rai akan yarinyar nan nima saina ci moriyarta, ki fadama uwarta, kunce min sati mai zuwa za a gama komai na gama shiri na inata kira kuma bkya dauka, ban manta yanda kika sauyo ta ba wallahi”
Kit wayar ta dauke, jamilu gaba daya bai gane inda zancen ya dosa ba amma jin muryar namiji yasa ya wuce daki a fusace.

“Jamila jamila.. ya budo labulen dakinsu hannunsa rike da wayar ta futowarta kenan daga bandaki daure da zani a kirjinta, ya dubeta yana mai mata nuni da wayar hannunsa “waye dahiru????”
Gabanta ne ya fadi ganin wayar tata a hannunshi gashi kuma yana tambayar waye dahiru, kame kame ta somayi kamar mara gaskia “waye dahiru jamila? Karuwancin naki kika koma ban sani ba? Wacha mu’amala ce tsakanin ki dashi?”
Saurin nutsar da kanta tayi tace “ah ah wallahi haba jamilu, ya zakayi irin wannan tunanin?”
“To meya hadaki da wani gardi? Eh???”
“Dan allah ka dan sarara kaji abunda zan fada maka,”
Wani irin ashariya ya qudundumo yace “ki fada min waye dahiru ya kiraki wajen sau biyar ina zaune a parlor, na daga naji yana kiranki da wani suna gatsai? Daman baki bar karuwancin naki ba dukda na rufa maki asiri na aureki?”
“Haba jamilu ya kake wannan maganar ne mara kan gado, ba kowa bane wanda zai auri yar hadiza ne fa,”
“Wanda zai auri yar hadiza? Toh uban meysa yake kiranki? Ke meya hadaki dashi?”
Shuru tayi ta rasa ansar da zata bashi, gaba daya kana ganinta kaga mara gaskia, “haba jamilu, yanxu baka yarda dani ba?”
“Chap ana taba yarda da karuwa ne? Tsohuwar bugaggaiya ma ta bugun karshe? Ke har kin manta yanda na tsamoki ne na rufa maki asiri”
“Kai jamilu kar fa tasan kar, muka dai rufawa juna asiri, kaima fa nasan irin rayiwar da kakeyi, yaya nawa kayi wa cikin shege? A anguwar nan amma nasan yanda nayi na rufa maka asiri mukaje aka zubar da cikin ba tare da kasani bama, yauwa ehe,”
Tsit yayi bakinsa ya mutu murus, ya wullo mata wayarta,
“Tun tuni bata aurar da ita ba sai yanxu? Inace neman kudi take da yarinyar? Har tanada kudin aurar da ita?” Ya jefo mata tambaya
“Eh, dan uwansu ne auran gida zatayi mata, toh ay gwara da aurar da ita ma huta da nemanta da akeyi, karma ta jawo mana masifa”

Shuru dahiru yayi kafin ya zauna kusa da ita yace “jamila nasan hadiza kawarki ce tunda tare da ganku, ni kuwa wannan yar tata anya ta hanyar sunna aka sameta kuwa ko shegiya ce don kwata kwata ban taba ganin wani daga dangin ubanta yazo ba tun tasowarta kodai itama a gantalin ta samo ta?“
“da ubanta mana,meysa zakayi tunanin haihuwar titi ce?”
“Hmm..toh ay naga yanda ita kanta uwar keyi da yarinyar ay abun tambaya ne, ba tun yanxu ake gulmar nan ba a anguwar nan, yanda take bobboyeta kamar batasan duniya tasan da ita kodai satota tayi?”
Shuru jamila tayi tama kasa shafa vaseline din da take, shiko jamilu kallonta yakeyi sosai ba tun yanxu yasan akwai wata kullaliya da suke boyewa ba ita da hadiza game da yarinyar nan yanxu daya daga wayar dahiru yaji maganganun da yake don duk a tunaninshi da jamila yake wayar baisan cewa jamilu ne ya duaka wayar ba yasashi dasa ayar tambaya.

Jamila na futa daga dakin tayi hanzarin kira dahiru, yana daga zaune ya gama fentin dakin da zaisa amarya dakanshi ma yayi, abun duniya ya mashi yawa kwana biyu kenan yana kiran jamila bata dauka, gashi ya kwallafa rai kamar tsohon maye, baiga yarinyar ba dake tangararren dan iska ne ji yake kamar ta gama hada komai zaisha romo kawai, tauntsu daga sama gasasshe.
Kaf kauyen nan kowa yasan dahiru nada cutar zamani wato HIV wannan yasa babu iyayen da suka amince da aurar da yarsu ga shi saboda karya sa mata cutar shiyasa baiyi aure ba, ta yanda aka gano kuwa shine yaran daya dunga bi yana nemansu yana shafa masu cutar.
Yan iskan da yake nema ma sun daina bashi gudun karya shafa masu wannan yasa abun ya mashi yawa, gashi jararrabe dukda ya jeme gaba daya.
Yana ganin kiran kuwa ya miqe tsaye yana kama ta tsula “jamila jamila!!!”
“Dalla malam dakata, kai wani irin dan buhun uba ne, meysa zaka dunga kirana haka eh? Kashe min aure kake son yi?”
“Jamila wallahi kuna wasa da qanin shaidan, na rantse da allah idan kuka sauya magana zan nuna maki ni tijararre wallahi”
“Me zaka iyayi? Babu abunda zaka iya wallahi,”
Cije lebe yayi don tabbas bashida abunda zia iyayi tunda baisan asalin iyayen yarinyar ba balle yaje ya tona asirin nasu dole ya bisu da lallaba ya gano.
“Toh yanxu ya ake ciki ne? Na fada maki ina cikin matsi in kunsan zaku jaa da nisa ay da saiki fada min na daina durawa cikin maganin karfi”
“Bana son maganar lalaci, ka saurareni, in bazaka iya dakatawa zuwa dan wani lokaci ba..”
“Kamar yaushe kenan? Eh?” Ya jefo mata tare
“Kaidai ba tace ta baka ita ba? Ay magana ya kare kawai, kawai dai da zarar anyi abunnan ka tabbatar ka rike yarinyar nan duk abunda kaga dama kayi da ita, karka bata mana shiri”
“Tuni zan dirma mata ciki tana haifewa na kara mata wani, mu kare rayuwar mu a kauye ina cin abata hahahah” ya lashe baki
“Kai takaddarin dan iska ne dahiru, “tare muka fara ay wai jamila su waye iyayen yarinyar nan? Da alamu dai kun iya boye sirrin nan shekara da shekaru haka”
“Babu ruwanka da tambayar su waye iyayenta, kaidai kawai tunda an baka ita ay shikenan saikaje chan ka karata”
“Toh toh shikenan, dan allah ki dunga ansa wayata dan insan matsayar mu,”

Tana kashe wayar ta ajeta gefe tare da miqew wajen sip ta fiddo da kaya.
Jamilu dake rabe jikin kofar dakin bai futa ba kaf conversation dinsu yaji daga farko har karshe, kanshi gaba daya ya gama qullewa.

After 1 week…
Bayan sati daya..
Cikin sati gudan nan abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa harda progress din samun lafiyar anne, ana bata treatment sosai, har hiring wani special consultant sameer yayi daga india wanda barau yayi recommending yazo har abuja akayi accommodating dinshi.
Alhamdulillah tana tashi tana zama kuma tana magana sosai, inka ganta bazakace tana da brain turmor ba, kuma treatment din ya karbi jikinta don abun mamaki healing take sosai.
Anty bahijja kullum saita kira a waya ta duba yanayin anne.
Anty fadila ce har yanxu ke jinyanta, nanna ma anan take wuni saidai kuma da daddare ta koma.
Shima taj koda yaushe yana asibitin, yawanci ma dai gaba daya yan gidan kusan kullum sai sunzo.
Anty madina matar uncle dameer ita anan take wuni kullum ba kamar dayar uwar gidan ba da kullum take zuwa ba da zarar tazo ma bata kaiwa hour daya take tafiyar ta.
Cikin kwanakin maya ta koma bangaren anty laila, akuyar daure an samu sake, fantamawa take son ranta, sannan ta futa duk sanda taga dama ta dawo duk sanda taga dama, rayuwarta dai babu abunda Ya sauya saima gaba daya ke yi.
Maganar taj ko har yanxu tana nan, ada ta dauka crushing take akanshi data gane cewa akwai aure tsakaninsu wannan yasa ta kudirci duk yanda za ayi saita mallakeshu, dok harta fara fadama mummy ita tanasonshi, bahijja dataji wannan abu ba karamin dadi taji ba don daman suna maganar aurar da ita kawai ita da majeed, tunda taji an anne tayi maganar an ganta a hotel hankalinta ya kasa kwanciya, mai zaikai budurwa kamar maya hotel?batadai fatan abunda take tunani shine amma gaskiar anne ce maya nada rawar kai, and she wants what is best for her.
Yau saura sati biyu su koma school, laila da maya nata shirye shiryen komawa, sun fita sunyi shopping tare,driver yakaisu.
Tunda anty fadila ta koma jinyar anne a asibiti laila ta dan samu sakewa, saidai idanun hamad baisa ta wuce iyaka ba balle ma ita tafi maya hankali sosai ba kadan ba kawai dai rayuwar yan mata ayanxu basa rabo da hira samari.

Bangaren sabeeha ta dan sake sosai, babu abunda ke kaita dakin taj sai gyara,, safe da yamma, sannan haka zata kai abuncin sa safe rana dare, duk yanda zatayi saida tasan yanda tayi tana avoiding hada hanya dashi.

ada idan tana gyaran dakin ko’ina yana kasancewa neat amma yanxu zatazo taga ko’ina a hargitse kamar yanayin hakan intentionally.

Yau daga asibiti ya wuce inda suke haduwa da salim inda yazo tare da jamilu da tunda suka bashi zunzurutun kudi miliyan guda, da zarar sun kirashi yake zuwa jiki na bari, ya samu hanyar tatsar kudi a wajensu.

Kuma yana fatan abunda zai fada masu saiza su bashi wani kudin, tunaninshi har zuwa yanxu dalilin da yasa suke neman yarinyar badan komai bane saidan wannan balaraben ne ke sonta ya biyota har nan kasar,yarinya da shegen wayo tayi aure sannan tasa farin balarbe ya biyota,ko shi kanshi yasha saka rai akanta amma gudun tijarat jamila yasa bai kai hari ba.
Yarinya ce daka dora idanu akanta zakaji ka mace, tun kafin ta wanku tun tana cikin kazantar talauci balle yanxu kuma data sauya gaba dayanta in banda yanxu daya ga hotonta da suka nuna mashi zai rantse ba yar hadiza bace ta wahalr duniya ta kodar da ita.

Kafin ya soma masu bayani jamilu ya dubi salim yace “yallabai dan allah inada tambaya? Kafin na fada maku komai Dan allah mene alaqarku da yarinyar nan idan kuka fadamin zan fada maku komai game da ita, duk wani abu dana sani game da ita da rayuwar datayi ma gaba daya”

Kallon taj salim yayi ya fada mashi abunda jamilu ya fada, taj yayi shuru baisan ya fadi komai a wannan lokacin wannan yasashi yima salim magana da turanci, “I don’t need his service anymore,“
“But sir let’s listen to what he’s about to say”
Yana fadin haka ya dubi jamilu yace “tunda har muka iya baka kudin mu kuma har zuwa yanxu babu abund aya faru da ita harma dakai kasan cewa bazamu cutar da ita ba,”
“Toh amma meysa kukeson sanin komai game da yarinyar nan? Yarinyar da ake tunanin a titi aka haifeta”
“Me kake nufi da hakan?”
Shuru jamilu yayi jin basu fara maganar kudi ba tukunna kafin ya ce wani abu salim daya gane yayi saurin cewa “wannan karan anyi doubling kudin malam jamilu”
Jamilu najin haka ya bude baki yace “toh bismillahi, nidai bansan dalilin dayasa kuke bibiyar rayiwar yarinyar nan ba amma agaskiyar magana nidai na auri kawar babarta shekaru sha wani abu da suka wuce, ba a gabana akayi haihuwarta ba don zuwa sukayi anguwar mu nan dutsen habuja, tanada shekara goma sha wani abun, kuma bamu taba ganin ubanta ba andai ce ya mutu wai, daga ita sai kakarta da dan uwan babar tata suke zaune anan dutsen habuja, kafin kakarta ta mutu, talakawane yanda kuka gani tunda kunga gidan da suka tashi kuma ba a taba ganin kowa daga dangin ubanta ba yazo inma akwai ni zan fara gani tunda sunfi kusa damu nida matata, wannan yasa ake cewa ko a titi uwar ta haifota,“
Shuru salim yayi yana sauraronsa saida ya gama kafin ya dubi taj ya masa bayanin abunda ya fada.
Shuru taj yayi jamilu na bayani salim na fassara mashi da turanci.
“Meysa mahaifiyarta ta turata aikatau? Wata kasar daban maysa ba a barta tayi karatu ba?”
“Ita datake talla ina maganar karatu? Ko futowa uwar bata barinta tayi daga gidan shiyasa ma ake tunanin shegiyasa ce, kai daga yanda alakarta take da uwarta zaka gane ba haihuwar so bace don ba a boye dan sunna saidai shege”
Sakin baki salim yayi da jin wannan batun, jamilu ko yana sane da irin maganganun da yake dagowa ba komai zai fada masu a yanxu ba sai ya tabbatar da komai don ahankali ahankali yakeson yana yagar nashi kason.
“Yauwa kace meysa aka turata aikatau ko? Shekaru biyu da suka wuce kafin ta tafi kakar tana da ciwon zuciya tana gab da mutuwa babu kudin aiki da za ayi mata wannan yasa babarta tasa na nemi inda ake kai yara aikatau ko na shekara nawa ne taje tayi don ta samo musu kudi”
Daga impression din salim taj ya gane cewa maganganun da sukeyi ba masu dadin ji bane, haka nan ya juyo ya mashi bayanin komai, gaba daya tunda ya kureshi da ido ya kasa dauke wa,babu abunda yake sai kallon bakin salim din, wato wannan ne dalilin dayasa aka turota aikatau?Bai tana tunanin talauci da ake fama dashi a rayuwar wasu yakai har haka ba.
Abunda yafi tsaya mashi shine maganar da salim yayi na cewa wai ana cewa kamar bata da uba,baice komai ba dai yana sauraron su

Jamilu yace “yauwa namaji matata tace uwar aurar da ita zatayi”
“Aurar da ita?ba aikatau kace sukeyi ba?”
“Eh wai wani dan uwansu za a aura mata”

Kallon taj salim ya sakeyi ya fada mashi abunda jamilu ya fada, tunda salim ya soma magana ya karade ya wani sauya yanayinshi gaba daya.
Tundaga nan maganar tasu ta tsaya don gaba daya yanayin taj dun ya sauya yasa salim ya sallami jamilu kawai suka raba hanya gaba dayansu.
Tunda ya shiga motarshi babu abunda yake sai saka da warwara, kwata kwtaa batasan cewa auransu na nan ba don shi bai saketa ba, wannan shirmamman wasan nata dole ya tsaya a yau.
Shi kanshi gaba daya baisan cewa hankalin ya tashi ba da jin maganar,
Gudu yake sosai a motar kamar zai tashi sama, cikin abunda bai wuce minti ashirin ba ya iso gidan.
Bude motar tashi yayi lokacin ana kiran sallar magrib, alwala ya farayi ya shiga masallaci yayi sallah kafin ya futo ya wuce main house.
Yana shiga kamar kullum babu kowa a kasan sai wajen dining dayakejin kamar ana shirya dinner.
Ba tare da wani dogon tunani ba ya tunkari wajen, yana isowa ya tadda laila a tsaye tana kokarin diban abunci.
Cikin sauri ta aje plate din fuskanta dauke da murmushi tace “good evening uncle taj”
Bai tsaya sauraran gaisuwar ta yace
“Go in there and call fatima”
Da mamaki ta tsaya don bata gane wa yake nufi ba, wace fatimar uncle taj zaice a kira masa.
“You mean the house help? Sabeeha?”
Wani irin kallo ya mata baice komai ba wanda yasa ta gane ita yake nufi.
“Inform her to come along with dinner”
Bayason creating wani suspicion wannan yasa ya fadi haka sannan ya juya yabar laila tsaye galala, tasan sabeeha ke kula da bangarensa wannan yasa bata kawo wani tunanin aranta ba amma ganin yanayin sa yasa ta dan dakata.

Kitchen ta shiga inda sabeehar ke tsaye tana harhada nashi dinner din tace “sabeeha!”
Juyowa sabeeha tayi ta kalleta tace “naam”
Kureta da idanu laila tayi kafin kuma ta kauda tunanin dake ranta tace “uncle taj ne yace akai mashi dinner yanxu”
Saida gaban sabeeha ya dan buga don bai taba aikawa a kira ba tace “tohm nama gama shiryawa yanxu zan kai”
Murmushi laila tayi mata sannan ta futa ta dauka plate dinta ta wuce sama.
Maya na zaune tana kallon call din salim taqi dagawa tunda ta gane sunsan juna da uncle taj ta daina daga wayarshi, batasan duk wani alakarta ta waje a sani a cikin gida.
Wato tasan cewa abunda takeyi zai iya affecting rayuwarta nan gaba.
Kalon wayar laila tayi tace “ke ko ki daga wayarshi mana why are you ignoring him? Na tunda yanda yake maki wulaqanci kina shanyewa yanxu is pay back time kenan”
Ko kulata batayi ba ta cigaba da kallon da takeyi a laptop dinta, laila ta gyara zama tace “yanxu uncle taj ya shigo” tuni ta aje laptop din ta kalli laila tace “maysa baki fada min na sauko ba?”
“Ta yaya zan fada maki? Daga shugowarshi ya nemi a kira mashi sabeeha”
Zaro idanu maya tayi take ta wani irin sauya gaba daya, “meysa yake neman ta”
“Dinner zata kai mashi but..something seems off about this duo, manta da maganar yar aiki ce yarinyar nan nada kyau fa sosai kuma babu namijin da zai ganta bazata shiga ranshi ba qila shiyasa ma ya hamad ke yawan kallonta shika, hmm nasha kamashi wallahi yana kallonta ta gefen idanu”
Wani irin boiling jinin maya ya soma yi, jikinta ya soma tsuma an kunnota, bata kaunar ayi maganar sabeeha kwata kwata ko kadan balle kuma a dangantata da taj shiyasa bata kaunar taga sabeehar ta shiga part din nashi, tunawa da wannan useless uwar tata yasa tayi saurin sauka daga kan gado daga ita sai wata singlet da tight damamme sosai gata dai ba shape mai jyau ba amma dai iyayi da gayu.
“Ina zakije kuma?” Laila ta tambayeta tayi banza da ita ta futa.

Bangaren sabeeha tana shugowa sitting room din bakinta dauke da sallama ta ganshi zaune kan sitting room, sallamar datayi ma ko amsawa baiyi ba yana latsa wayar hannunshi, ganin haka yasa ta wuce har zuwa inda yake kanta a kasa ta wani hade rai tace “good day sir”
Nanma baice mata kala ba ta nufi wajen dining ta aje abuncin ta jera su sannan ta fidda dinner set kafin tabar wajen.
Tana dawowa sitting room ta taddashi yanda ta shigo a zaune, “dinner is ready sir”
Tana fadin haka ta nufi wajen kofa muryarshi tasa ya dakata,
“When Are you going to stop this pretending game?” Chak ta tsaya ta kasa karasawa bakin kofar, “fatima!!!!l” ya kirata a kausashe, gabanta ya sake faduwa tayi hanzarin tunkarar kofar kamar batasan da ita yake ba tasa hannunta kan handle din kofar tajita a rufe, murdawa ta sakeyi da mamaki taji kofar a rufe take hankalinta ya dan tashi ta bude smart lock din kofar taga an saka locked.
Gaba daya rasa yanda zatayi tayi batama san ya miqe tsaye ba ya zuba hannayenshi cikin aljihun jallabiyar dake jikinshi, sannan ya zuba mata jajyen idanunshi.
Cikin sauri ta juyo tana kallonshi tana kokarin cire duk wani tsoro da fargaba dataji ya durar mata.
“Just because you denied who you and pretend as if baki taba ganina ba doesn’t mean i will believe you are other wise”
“Sir please i dont know what you are talking about, i dont know who you are referring me with but nidai bansanka ba, ive never seen you in my entire life”
Smirking yayi kafin ya soma takowa inda takeyi gashi takai bangon kofar, batasan cewa tsoron da take ba ya gama bayyana akan fusknta, ya ranshi sosai kamar bashiba shima.
Saida yazo dab da ita sosai don tana jin kusancin su sosai ba kadan ba nunfashi na neman yi gogayya da juna ga kamshinsa daya kara burkitata ga inuwarsa a gabanta dayasa ta kara tsorata sosai.
Hannayenta biyu tasa tare da dafe kofar kamar zata tura jikinta cikin kofar,
“Look into my eyes say what you just said now”
Ya fada yana kafeta da idanu sosai, kirjinta dake cikin hijab babu abunda yake sai sama da kasa tsabar gaba daya tana neman rikicewa.
Hannunshi daya ya zaro daga aljihunsa tare da sanyashi wajen jaw line dinta ya dago da fuskanta ya matso da tashi dab da tata trying to lock both eyes dinsu.
“Look into my eyes and denied who you are”
Kin yarda tayi ta hada idanu dashi saima runtsesu datayi sosai.
Bakinta yabi da kallo da suke motsawa ahankali ahankali, “why are you doing this? “
Ta fada muryanta na breaking sai hawaye daya sauka kan fuskanta, sake matsowa yayi sosai don kiris ya rage kirjinshi da nata basu hadu ba ya sake matso da fuskanshi daidai nata fuskan don sai da rankwafo yace “you will sleep here idan har baki aje wannan pretending din da kike ba,”
Cikin saurin ta bude idanunta jin nunfashinsa akan fuskanta tace “please sir this is not right”
“What stops it from being right?we normally sleep together remember”
Saurin runtse idanunta tayi ta budesu tare da kauda fuskanta don kusancin yayi yawa sosai ba kadan ba,
“I never knew you’re this stubborn bibi…”
Yaja kalmar ta karshe kamar wanda ake fusga sosai.
Bayason ya fada mata har yanxu da aurenshi akanta don ba lallai ta yarda ba but thats the fact.
“Looks like one knows the life you live with me, you really want to keep it to your self right?”
A zafafe ta dago rai a bace ko girman jikinsa bata gani ba yanda ya wani zagayeta gaba daya tace “I dont know what you’re talking about, let me go please”
“Idanunshi kamar hawaye zasu fito tsabar yanda ya kafeta dasu “still being stubborn right, you’re making things very hard for both of us, inma mantawa kikayi let me remind you,” yana fadin haka ya sa hannunshi daya ya zagaye kugunta dashi ya zageyeshi gaba daya to the other edge ya wani matso da ita tabar jikin kofar har suna bugun kirjin junansu ya wani irin lumshe idanunshi da sukayi jaa sosai dayan hannunshi dake yawo ya sanya shi jikin kofar ya dafe kofar dashi having control of her all bayi wata wata ba yanda ta dago fuskantan nan in so much shock ya rankwafo tare locking lip dinshi da nata a gaggauce kamar wani mayen zaki, gwalo idanu tayi sosai tashin hankalin da ba a sa mashi rana, abun yazo mata a bazata ya kama bakinta sosai ya shiga kissing dinta deeply, gaba daya furgicin da take boyewa ne ya bayyana a fuskanta har ma da jikinta, take jikinta ya soma bari, taj ko tunda yasa bakinsa cikin nata yaji gaba daya kamar ana kwance notikan kanshi daya bayan daya, yanajin yanda kirjinta ke sama da kasa suna gogan faffadan kirjinshi, tuni ya sake deeping suck din da yake mata, giving her the perfect kiss of her life, ko ince life threatening kiss don neman shidewa ta soma yi, he takes control of her body gaba daya da yanda ya kama kugunta ya danqe sannan ya dafe kofar giving in all his strength.
Wani irin futsari futsarin fargaba ta soma ji hankali a tashe ta daga hannayeta tana bugun kirjinshi gashi ya banqarota sosai babu damar turashi.
Me zatayi banda hawaye, tanajin yanda yake shiga ko’wanne lungu da sako na hole din lips dinta, lips dinshi na saman nata ya kama na kasan ya kama na sama, harshenta ko yasha juyi sosai ba kdan, saliva dinsu kam ya gama zama taste daya.
Yifa yakeyi babu ji babu gani kwata kwata baijin turashi da take dadi ma shi abun ke mashi, da ya samu chance din gasping breath dinshi ba tare da ya cire bakinsu ba sai yayi wani irin intimate moaning gently alamun abun na mashi dadi sosai, shi kanshi yasan there’s a beast within him daya sashi kasa sakinta, so yake dole da kanta tayi acknowledging presence dinshi, he has had enough of this little drama, he was giving her chance saboda guilt din abunda ya mata idan ta zabi ta nuna kamar bata sanshi ba bazaiyi forcing dinta ba, amma bazai yarda su zama strangers ba, ya gama amincewa da he’s also here for her as her husband.
Musamman yanxu dayaji maganar mamanta zata aurar da ita what if he loose her for good?, bayan yasan shi mijinta ne har yanxu kuma aure kan aure haramun ne.

Murda kofar maya tayi hankali a tashe, ta wuce 20mins a sitting room din main house tana jiran sabeeha babu ita ba labarin ta take hankalinta ya tashi ta fara sake sake aranta, tana isowa part din kuwa ta murda kofar tajita rife, ay batasan sanda ta soma bugun kofar ba kamar yaqi.
Sama sama ya fara dawowa hayyacinshi, saboda kncking din, ya zare bakinshi da gaba daya danyi jaa sannan ya bude idanunshi da sukayi jaa sosai suma ya dan saketa kadan bai matsa daga jikinta ba ya duvbeta ganin yanda idanunta yayi gaja gaja da hawaye, lebenta garya dan kumburo kamar wadda akayima lip filler.
Smirking yayi kafin ya dan rankawafa daidai kunenta yakai bakinsa yace “أفتقدك كثيرا لها”. I’m sorry, I missed you bibi…”
Yana karashewa ya saketa tare da danna pins din kofar, maya tayi hanzari budewa gabanta na faduwa, abunda batayi expecting ba kuwa ta idanunta ya gane mata,zuciyanta na gudu sosai kamar ana tsere, kallo daya ya mata ya juya ya wuce ciki, maya ta dubi sabeeha dake kokarin daidaita natsuwarta tuni ta goge hawaynta da gaggawa tunda ya soma danna pin din kofar zai bude.


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵 🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 47 · 0% Book details