← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 20 OF 66

Chapter 74

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 13 min read

Har suka hau sama hannunshi na cikin nata, tana biye dashi a baya, wani irin dadin kasancewa a haka dashi take, batasan dalilinshi na yin haka ba amma abun ya mata dadi, she feel protected.
Suna shigowa dakin daidai tsakiyar dakin ya saki hannunta, ba tare da ya kalleta ba ya dan juya ya soma magana, “karki sake sauka a haka, put on your hijab next time”
Yana kaiwa nan ya nufi ciki, da idanu ta bishi da mamaki, chan kuma bata san lokacin da murmushi ya kubce mata ba, meysa yace karta sake fita haka? Is there something with her dressing, ba wannan bama, tunda ya nuna hakan yakeso dole ta amsa umarninsa.
Tana daga zaune ya futo sanye da kayan barci da laptop a hannunshi, ta gabanta ya gifta ya samu waje ya zauna bakin gado bayan ya cire bedroom slippers dinshi sannan ya daura kafarshi cikin duvet, tana ankare da duk abunda yake don ta kasa dauke idanunta akanshi.
“Yadai? Do you need anything?”
Yanda yayi maganar yasa ta danji kunyarshi, “di..di”
Ta kira sunanshi ahankali, dagowa yayi ya zuba mata wannan idanun nashi, take ta daburce tama rasa me zata ce mashi, “ka koshi?do you need anything? Ko a kawo coffee?”
“No thanks”
Yana fadin haka ya maida dubanshi ga aiyukan dake gabanshi.
Itakuma ta juya cikin dakin ta dauko kaya masu dan nauyi na barci sannan ta wuce bathroom ta sake wani wanka saboda period din datake, allah ya taimaketa ma bata ciwon mara saidai na jiki.
Saida ta tabbatar ta tsaftace jikinta tsaf ta yanda bazai ganeba sannan ta futo, tana tunanin yanda zata kasance da asuba, yanxu kusan a tare suke sallah shida ita, batason tuannin komai a wannnan lokacin don haka ta bari sai zuwa gobe idan allah ya kaimu.
Futowa tayi a natse ta tunkari gadon, tana zuwa daidai inda take kwanciya ta zauna, tana fuskantarshi, harda nade kafafu, puzzle box dinshi data futo dashi daga closet ta fiddo tana kokarin murza abun, kwata kwata bata iya ba amma haka ta dage tana juya abun,
Tunda ta zauna ya ankare ta, tun kafinma ta karaso idanunshi suka kai gareta ba tare da ta snai ba harta zauna ta fuskanceshi, ta dade tana murza abun nan shiko ayyukanshi kawai yake, bini bini yake kallonta ta gefen idanu,data gaji da abun saita ajiye kawai tana tabe baki.
“Wannan abun akwai wahala wallahi”
Banza yayi da ita baice tak ba, ganin haka ya sa ta dan matso kusa dashi sosai tare da dan lekowa wajen laptop din nashi don ganin abunda yakeyi, yanda ta rankwafo da kanta a gabanshi yasa baima ganin screen din, sai yabi kanta da kallo yana mamakin yanda baya iya dakatar da ita daga wani abubuwan, “laa wannan motar tayi kyau sosai, musamman for family trip haka ko idan mutun zai yi packing wannan dai tayi qanqanuwa saboda masu qiba, nidai banida wiba zan shige zurup”
Da hausa ta karashe maganar, Tana fadin haka tayi baya tare da kallonshi, yanda take kallonshi haka yake kallonta harma suka shagala, saida ya danyi gyaran murya kafin ya maida dubanshi ga design din da yakeyi, wata sport car yake designing latest ford gefenta kuma irin manyan motocin nan ne na suv.
Shuru yayi yana nazarin maganganunta, da yake professional business tycoon ne, he use every opportunity as a business idea wannan ya bashi damar adding more factors,
“Thanks for the idea”
Da mamaki take kallonshi, wace idea kuma? Ta tambayi kanta,
Tana son tambayarshi ko shine yayi designing din motar saidai kuma tana tsoro, don haka tayi baya ta gyara zamanta harda dan tagumi, tana kallonshi a fakaice, ta lura da an fara kallonshi yake ganewa, kuma tasan ba kallonta yayi ba wannan yasa take mamakin ta yanda yake sanij tana kallonshi.
Ya kai wajen an hour or two yana abu daya, saida ya gama kaf sannan ya turama manager dinshi kafin ya kashe laptop din.
Dagowan da zaiyi ya ganta tana barcinta hankali kwance ta jingine da bangon gado, tashi yayi ya maida laptop dinahi inda yake ajiyeta kafin ya dawo kan gadon, hannu ya daga har zai tasheta ya dakata, da taimakon hannayenshi ya gyara mata kwanciya ta.
Asuba ta gari…
Misalin wajen karfe biyu daidai ya farka sakamakon wani mumunan mafarki da yayi, koda ya farka wani irin turirin zafi yaki jikinshi nayi, yayi zuba jargab duk sanyin ac nan, cikin hanzari ya mike zaune yana ambaton allah, kafin ya kunna bedside lamp, yana kunnawa ya dubi ind atake kwance, kafin ya tashi ya wuce bathroom, bai wani dade ba ya fito.
Bakin gadon ya koma ya jawo wayanshi ya fara dube dube, ya shiga chan ya futa nan, maganganun mutabbalb dasu ya kwana, qila ma shiyasa yayi mafarki don ya saka maganar aranshi, ya dade sosai yana bin labaran internet, ganin abubuwan da yake gani yana mashi wasi wasi da tunani yasa ya ajiye wayar ya dafe kanshi dake mashi azababban ciwo, dan jingina yayi da bakin gado kafarshi daya na kasa dayar kuma na bakin gado ya lumshe idanunshi yana nazari.
Yanacikin wannan nazari yaji ta gangaro bangaren da yake kwance tana mai komarin cusa kanta gefenshi hartayi nasarar yin pillow da thigh dinshi, duk a tunanin pillow ne, baiyi kokarin hanata ba saima zuba mata idanu da yayi, yana kallon fuskarta, ya dade yana tunani kala kala aranshi kafin ya dafe kanshi dake mashi ciwo.
Da kyar barci ya fusgeshi wajen karfe uku da rabi.

Cikin ikon allah ta farka wajen karfe biyar dot, bude idanun ta da zatayi kawai ta ganta a gefenshi ya zagayo da hannayenshi wajen kafadunta,yayi facing sama both hannayenshi na opppsite sides, dayan ne ke wajen kafadunta, ita kuma ta zagayo da nata hannayen wajen kirjinshi, ba karamin faduwar gaba taji ba a wannan lokacin, da dabaru ta samu ta matsa daga jikinshi yanda bazai tashi ba, tana tashi tayi saurin wucewa bathroom ta duba jikinta, allah yaso batayi stain ba wannan yasa tayi azamar yin waka ta tsaftace bayin sannan ta futo ta suaya kaya ta zurma hijab sannan ta futo ta samu waje inda suke sallah ta zauna, fatanta allah yas akarya tashi yanxu.
Saigashi bai tashin ba kuwa sai wajen karfe shida ya bude idanunshi, kanshi yayi masifar yi mashi nauyi, da sunan allah ya tashi zaune sannan ya dubi ind atake kwance ganin bata nan yasa ya maida dubanshi ga wajen sallah, nan kuwa ya ganta kwace abunta.
Duban agogon wayarshi yayi ganin wajen shida yasa ya mike ya dauro alwala yayi sallah….

Yau kwana biyar chirr allah ya taimaketa ta gama cikin ikon allah, cikin kwana biyar dinnan abubuwan da dama sun sauya a gidan, yanxu gaba daya suke dinner amma fa ammu bata yarda wata maid tayi ba, tare sukeyi ita da sabeeha, don bata yarda kowa ba, kuma tasan gaba dayansu yanxu kowa harinshi don ya cutar da sabeeha ne, kuma hanya mafi sauqi wajen yin haka kuwa shine wajen cima, thats the simplest yet easiest way to end someone, wanda bata fatan haka.
Bangaren sonata duk yanda taso ta ida kudirinta abun yaci tura, gashi tana tsoron mu sosai ba kadan ba, fadwa ko tayi sanyi a zahiri, don har shiga wajen ammu takeyi, ammu dai kallonta kawai take amma bata yarda da dunkansu ba, jinin mahaifiyarsu ba abun yarda baneba kwata kwata.

Yau kwanan hidaya bakwai cir, anan chan anata faman neman hadaka partnership da manyan mutane, duk wani abu da take buqata abdul basit ya bata, da maqudan kudaden da take buqata da products din da take nema sannan yayi introducing dinta to manyan mutanen daya sani as business partner dinshi, harma da mutanen da suke illegal transportation, ita wannan hadaka is an eye opener for her, she make sure that shes into everything for power and fame, abunda takeso kenan, inda tasan haka ne da tun wuri ta hade bb companies da taheel wannan hadaka ba karamin dadi tayi mata ba.Wannan yasata dade bata dawo ba.
Yau ta kasance friday, duk kowa na gida babu wanda ya fita.
Barad ne ya shigo part din nasu, anan sitting room ya tadda sabeeha taba daga zaune, haka ya jata suka futa har zuwa garden daman ta dade bata futan ba.
Taj na daki kwata kwata baisan ta futa ba, babu abunda yake sai karance karance a laptop, mutabblib ya tura mashi information din komai gameda scandal din khaal, hatta gidan shi da goverment ta kwace har an saidashi, har information din purchaser din saida mutabblb ya tura mashi harma da information din iyala khaal, inda suke ayanxu duk saida mutabblib ya tura mashi, bincike ne kwakwara sannan daga gani akwai kulallaiya a ciki.
Akan idanun su afiya ta fita tare da barad, zuwa garden area, its been long rabonta da wajen, tana kallon barad yayi ta wasan shi itakuma ta samu waje ta zauna, a wajen kujerun dake wajen tana kallon ciyayin wajen koraye sharr kala daban daban, tunawa tayi da lokacin da suka hadu da mutabblib a wajen da bayanan daya bata, akullum tana tunawa dashi, idan ta tuan saidai tace ko shin yana ina? Allah kadai ne masaniya.
Tunawa tayi da lokacin da taj da barad ke yawan wasa a wajen, bata san lokacin da murmushi ya kubce mata ba.
Barad ne ya wullo ball din gefen inda take zaune, gaba daya hankalinta baya wajen har ball din ta wuce ta inda take ta koma dayan exetension din garden din wajen pool, bata ankareba saida yace “aunty the ball”
Sai a lokacin ta lura wannan yasa ta mike tsaye “sorry bari na dauko maka”
Tana kaiwa nan ta tunakri inda ball din take ta wajen sakon dayan extension din, tana duqawa ya kama hannunta, cikin hanzari tayi saurin miqewa tsaye tare da yin baya ganin tareeq, take gabanta ya bada wani irin dam…
Saurin fusge hannunta tayi ta hade rai tamau, shiko mai zaiyi banda washe baki, he wasn’t expecting her at all, dawowan kenan gidan baima kaiga karasawa ciki ba fadwa ta kira a waya kan cewa yazo garden ya sameta,bangaren fadwa kuwa tabbas taga futar sabeeha zuwa garden din, a daidai lokacin kuwa saiga tareeq ya dawo wannan ya bata damar aywatar da abunda takeso.
“Karka sake rike min hannu please this is not right”
Lashe kasan levenshi yayi kafin ya dubeta daga sama har kasa, fatarta tayi liwailuwai, gatadaj batada qiba da girman jiki saidai allah ya bata kyakyawan cikowar albarkatu.
Ball din da bata dauka ba kenan ta juya zata bar wajen ya sake kamo hannunta yayi baya da ita wannan yasa jikinta ya kusa bugewa da nashi, tayi saurin matsawa ta juyo tana mai fuaksntar, tanajin kamar ta watsa mashi mari, “wow…you look fresh…”
Wani irin matsiyacin kallo ta mashi kafin ta fara kokarin goga mashi magana, “karka sake kuskuren taba wannan katsamin hannun naka mai dauke da najasa a jikina, kaf rayuwata ban taba ganin kare ba irinka, koda yake bazanyi mamaki, tunda har ka iya kaci amanar matarka da qanwarta babu abunda bazakayi ba”

Muryar barad ne yasa tayi saurin barin wajen, ranta ba karamin baci yayi ba, shima kanshi tareeq din ya shaqa, idan ya fahimci abunda take fada tasan yayi mu’amala da afiya kenan, “shit”
Ya furta yana kai cije lebe, fadwa ko data samu abunda take nema tayi saurin komawa cikin gida tana mai kallon hotonsu data dauka, yanxu tanada evidence guda biyu kwarara, saidai idan ta nuna mashi tasan bazai yarda da ita ba dole ta biyo ta hanyar hidaya, hidaya ce kawai zata nuna mashi wannan ya yarda, shi kuma tareeq its high time ta kaudashi daga rayuwarta bashida wani amfani a yanxu.
Achan garden ko har zata juya tabar wajen tsabar takaici ta dan dakata ganin barad zaune,dago mata hannu yayi don ta karaso inda yake,takowa tayi gar inda yake ta zauna gefenshi ganin snack da juice a gabanshi, “yaushe aka kawo wannan?” Ta jefo mahsi tambaya, “ammu tasa maid ta kawo”
Tana jin haka ta dan murmusa, allah sarki ammu, daukan juice din yayi ya miqa mata ta amsa, saida ta dan jinkirta kafin ta fara kokarin kaiwa bakinta, bata ida kaiwa suka jiyo
Muryarshi kamar saukar aradu ya kwala mata kira saida ta girgiza, “FATIMA!!!!”
Chak ta dakata da shan juice din har yana neman barewa, jikinta har kyarma yake tayi saurin miqewa tsaye, takowa ya soma yi majestically harya karaso gabanta kafin ya amshe juice din dake hannunta ya jujyashi, tare dakaiwa wajen hancin sa.
,”uncle tajjj..you wnat to join us?dazu nazo wajenka anty sabeeha tace you’re busy”

Baima jin abunda barad din ke cewa, “waya kawo wannan?”
Ya tambayeshi yana mai mashi nuni da juice dun,shi kanshi yaron saida ya tsorata da yanayin uncle din nasa,
“Maid ta kawo, tace ammu tace a kawo mana nida aunty”
Ammu dake biye da taj din hankali a tashe ta karaso wajen, daman taj din na saukowa ita ya tadda a sitting room har tana tambayarshi ina fatima, nan ya shaida mata bata sama, shi yaka dauka wajen ammun tazo, ashe ba wajenta tazo ba, wannan yasa ya futo, haka kawai yaji ya kasa sukuni rashin ganinta da baiba, yana futowa ya hango tareeq daya futo daga garden din, harya wuceshi shibaima lura da taj din ba a tsaye, saboda tsabar bacin rai, harya kauda kai kawai yaji ya kasa sukuni ya nufi garden din yana zuwa daidai nan take tambayar barad waya kawo mashi juice haryake fada mata ay maid ce ta kawo tace ammu ta bayar a kawo masu.
Yanajin haka take gabanshi ya fadi, just a minute ago ya tabbatar ammu batasan ta sakko ba and now????…
Cikin ikon allah instint dinshi ya bashi this is not right wannan yasa ya dakatar da ita cikin gaggawa.
Maganar ammu ce ta dawo dasu,
“Au ashe kuna nan, har kunsa gabana ya fadi”
Rai a bace ya juyo ya kalli ammu, “ammu is this from you ke kika bawa maid ta kawo masu juice?”
Ya mata nuni da juice din, da mamaki take kallonshi, “ni kuma? Ba anan ka taddasu da shi ba? Maid kuma? Ay ni banma san sun sauko ba”
Confusedly sabeeha ke kallonshi da ammu din, take jikinta ya fara karkarwa idanunta ya fara kawo ruwa, ganin yanayinta yasa ammu saurin cewa, “meke faruwa ne? Fatima?”
“Nima ban sani ba ammu, nabar barad anan zanje na dauko ball dinshi daya wulla acahn shine..shine bayan na dawo yacemin wai kin aiko maid ta kawo mana juice da snack”

“Na shiga tara ni…banma san kuna nan ba? Wace maid dince? Meysa zatayi karya dani…”

Shuru taj yayi baya son yayi making din wannan into an issue don shima bai tabbatar da zargin da yake ba don haka ya kalli inda sabeehar ke tsaye tayi tsuru ya ja hannunta suka bar wajen, janta yake kamar wata yar baby har suna shigo cikin gidan, mutanen gidan daya sauko bai gansu a kasa ba sai gasu, kowannen su zaune ido wiki wiki kai kace gaba dayansu sunada gaska, nanko kowa da abunda ke ranshi na rashin alkahiri.
Bai sake hannunta ko ina ba sai dakinsu, yana sakin hannunta tayi saurin shafa wajen don haryayi jaa sosai taji ruko, shafa gashin fsukanshi yayi tare da runtse idanunshi kafin ya bude, take gabanta ya fadi don yanayin idanunshi ya sauya sosai, ba zato ba tsammani taji ya kama kafadunta yayi baya da ita har bakin bangon dakin ya kureta da idanunshi babu wasa ya soma magana a kakkaushe, “wa ya baki right din futa daga part din? How dare you step out of this house ba tare da sanina ba? Didnt i warn you not to even walkout without hijab?,”
Harga allah lokaci guda taga ya chanza mata, tama kasa gane inda ya dosa, why is he acting up like din, “are you deaf?” Ya sake daka mata tsawa,
Bakinta na rawa ta soma magana “nida barad ne kawai mukaje garden wallahi,”

“What where you doing there? Kinsan daga waye juice din yake da zaki sha? Are you going to act dump just to risk your life and my childs? Eh!!!”
Ya sake daka mata tsawa kamar yasan ana kokarin cutar da ita ko cutar da ita za ayi,
Kamar zatayi futsari a tsayen nan haka takeji, “dan allah kayi hakuri didi…I’m sorry bazan sake ba”
“Listen to me, daga yau karna sake ganinki waje, stay here, and dont you ever take anything from anyone, i repeat anyone..understood”
Yana fadin haka cikin hanzari ta girgiza mashi kai, “understood!!!”
“Yes..” ta amsashi,…

✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 20 · 0% Book details