Chapter 70
Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 14 min read
Bayan wasu yan kwanaki…
Abubuwa da dama sun sauya,musamma tsakaninta dashi, ya dan fara sakin jikin shi da ita, ba dan komai yayi hakan ba sai dan cikinshi dake jikinta, saidai har yanxu idan ya tuna ta yanda aka samu cikin ranshi na baci sosai, dan dole yake danne abunda ke ranshi don idan yace baya son cikin yayi karya, bayan wannan ma ya maida hankalinshi wajen karantarta sosai, don sanin kudirinta da abunda ke ranta, abu daya daya lura da ita shine shes so soft and calm, dukda wani dogon magana baya shiga tsakaninsu haka baisa ya lura da yanda take da respect ba wannan yasa yake dan jinta aranshi.
Monday morning Fit gym…
5pm
Gudu yake sosai kan treadmill, yana sanye da riga da gajeran wando wanda suka amshesa sosai,ya dade sosai a tsaye kunneshi a toshe da pods, saida ya dauka wajen minti talatin yana abu daya kafin ya kashe ya danyi relaxing tare da panting kadan kadan ga zufa na sauka akan fuskanshi,juyowan da zaiyi ya sauko daga treadmill din yayi daidai da isowar mutallib wajen fuskanshi wasai, taj ma na ganinshi ya dan murmusa abunda bai saba yima mutane ba kwata kwata, hannu mutallib ya miqa mashi sukayi musaba, “gym buddy finally na ganka yau,kullum idan nazo da safe bana ganinka”
Kai tsaye ya amsashi, “na chanza schedule ne”
Yana fadin haka suka nufi wajen karafunan wajen,taj na gaba shima mutabblb na biye dashi, weight bench taj ya hau ya kwanta yayin da mutabblib din ya zagayo ta wajen fuskanshi dago mashi weight ya soma dagawa,yana dagawa mutabblib na taimaka mashi, saida yayi press wajen sau biyar kafin ya dan dakata mutallib ya taimaka mashi.
“This is the perfect time, shiyasa na sauya, wajen nan ya fara zama so croudy”
Da mamaki mutabblb ke kallonshi don baiyi tsammanin zai kulashi ba bayan maganar daya mashi da farko,ba karamin dadi yake ji ba ganin kusanci na shiga tsakanin su ahankali ahankali.
“Thats true, yafi dadi ay idan babu hayaniya, mutun saiya samu sakewa sosai, dukda na lura saboda kai wajen ke cika yanxu” mutabblib ya karashe yana kashe mashi idanu daya harda yar dariyarshi.
“Saboda ni kuma?” Taj ya jefo mashi tambaya.
“Yea sir, saboda kai, bakaga mata sunfi yawa ba, compare to lokacin daka fara zuwa”
Tabe baki taj yayi kafin ya miqe daga wajen, “zaka wuce ne yanxu?”
Uhm.. ya fada yana girgza mashi kai, “kaifa?”
Taj ya jefo mashi tambaya? “Eh”
Kusan a tare suka fito da kayayyakin gym a jikinsu, mutallib nason tambayarshi abu saidai ya rasa ta inda zai soma da kyar dai ya dake yace “why don’t we grab something light..akwai wani mini halal bar anan kasa”
Shuru taj din yayi kamar bazai yarda ba chan kuma ya amsa da “okay”
Murmusawa mutabblib yayi kafin
Kowa ya shige motarshi, suka fuce daga wajen, duban mirror taj ya soma yi yana mamakin rashin ganin motar dake yawan bibiyarshi yau kusan sati kenan kenan.
Gaban wani mini bar mutabnlib yayi parking daman taj din na biye dashi shima ya cinno bakar lambor dinshi yayi parking kafin ya kwashe wayoyinshi ya fito.
Kusan a tare suka shiga cikin bar din suka samu waje suka zauna.
Mutallbi ne ya masu ordern beverages, tunda ya soma latsa wayarshi bai dago ba, ban taba zama irin haka ma da mutumin daya hadu cikin abunda bai wuce wata biyu ba,kwata kwata bashi opennesss shiyasa yake komai shi kadai but this time around yanajin sakewa around wannan guy din, wannan yasa ya dan sake ko zai samu avubuwan dake ranshi su fitar mashi.
Yanxu focus dinshi gaba daya akan yarinyar nan ne, hankalinshi gaba daya ya koma gareta, a zahiri kamar ba hakan take ba saidai a chan cikin zuciyarshi baya sakkani bata fadi mashi arai ba musamma yanxu da cikinshi ke jikinta,kauda ido kawai yake amma deep down yana tsananin kaunar abunda ke jikinta, cikin lokaci qanqani abun ya shigeshi ba tare da ya sani ba, tun bayan rashin lfiyan nan datayi har yayi tunanin ko cikin ne ya zube ya taorata sosai wannan yasa yake dan sassauta mata sosai, kuma ya kudirci kula da abunda ya shafi cikin jikin nata harma da lafiyarta, ko barci yake haka zai farka ya duba ta, don ya tabbatar tana lafiya kafin ya koma.
Kwata kwata baisan a wani mizani zai sakata ba, ma’ana yanda yakeji game da ita.
Gyaran murya mutallib yayi yana mai fuskantar taj din daya maida hankalinshi ga wayar dake hannunshi “bismillah!”
Ajiye wayar taj yayi ya dauka moctail din yakai bakinshin kafin ya ajiye.
Hira sukayi sosai, tun taj din na baya baya dashi harya sake sosai suka dunga hira kamar abokanan da suka san juna shekara da shekaru da yake mutabblib din is very easy going person saiya zamana ya shiga ranshi sosai,har sukayi planning fita tare don ya nuna mashi gari sosai.
Wajen karfe tara ya shigo gidan, tun daga bakin kofa ya soma jin hayaniyar mutanen gidan, su afiya ne zaune a kujerun sitting room sai wasu kawayenta su wajen uku harda sonata anata hira, tun yamma suke abu daya babu wadda tayi tunanin tashi tayi sallah, sai hira, duk sunci hadaddun abayas kana ganinsu kasan suma yayan masu shi ne.
Duk basu lura da shugowarshi ba don hankalinsu naga sonata data miqe ta nufi bakin stairs daidai nan sabeeha ta fito daga bangaren ammu ta nufi wajen stairs din, kodata hango sonata saida gabanta ya dan fadi don tunda ta sauko suke binta sa kallo gaba dayansu.
Tundaga bakin kofar ya hangosu,both sonata da sabeehar, sabeeha na sanye da doguwar riga blue sai mayafin rigar data rufe kanta dashi,kallo daya ya masu ya kasa dauke idanunshi akansu.
Chan bangarensu sabeeha kota kanta batabi ba batama tsaya sauraron maganganun datake jifanta dashi ba don kallon mahaukaciya take mata yanxu ta nufi sama harta daga kafarta daya zata hau saman batasan me ya faru ba sai kawai jinta tayi, tayi baya suuu kamar wandda aka turo baya, harta runtse idanunta jiran faduwa kawai take a kasa taji akasin haka, shi kanshi baisan lokacin daya zo wajen ba don gaba daya hankalinshi lokaci guda ya tashi tunda ya hangosu daga nesa kuka ya tabbatar da abunda idanunshi suka hango masa, ranshi ba karamin baci yayi ba, take idanunshi yayi jaa sosai tsabar bacin rai, sabeeha data luntsuma jikinshi kasa tashi tayi ta qanqameshi saboda ta tsorata and ko ba a fada mata ba tasan kamshinsa ne wannan.
Sonata na ganinshi jiki ya soma tsuma, ba karamin mamakin ganinsa tayi ba a daidai wannan lokacin,fatanta daya allah yasa yanxu ya shugo kuma baiga abunda ya faru ba, abunda bata sani ba kuwa shine sarai yaga komai.
Bakinta na kyarma ta washe hakoranta ta soma magana “babe ka dawo”
Jajayen idanunshi da sukayi jaaa sosai kamar an zuba garwashi ya zuba mata, babu abunda ke kwance a fuskanshi sai tsantsar bacin rai, ganin yanayinshi haka yasa gabanta yayi mugun faduwa.
Ahankali ya zarota daga jikinshi, ya kama damtsen hannunta ya mata nuni da sama,mutanen dake zaune a parlor babu abunda suke sai kura masu idanu kamar sunga tv, kowa da abunsa yake ayyanawa aranshi, waenda basu taba ganin shi ba kuwa baki bude tsavar zalama.
Sadaf sadaf sabeeha ta wuce sama ba tare da ta sake kallon inda sonata ke tsaye ba ta wuce sama abunta, shiko tana wucewa bai sake kallon inda sonata ke tsaye ba ya mara mata baya shima.
Cije yatsa sonata tayi don ba haka taso outcome dinba, taso sabeehar ta fadi a kasa ko cikin ya bare kowa ya huta, sai kuma aka samu akasin haka, yanda taga bacin rai kwance a fuskanshi ya tabbatar mata akwai matsala.
Muryar kawayen afiya ne ya dawo da ita daga tunanin data fada, “babe waye wannan sharp guy din? Woww.. kai amma ya hadu waiii”
Banza afiya tayi dasu don ranta ba karamin baci yake ba da zarar an fara maganarshi, ko idan akayi noticing dinshi, ita bataga abun tada jijiyoyin wuya ba akan wannan guy din ba.
“Thats my fiancee” sonata ta katse su, dake kawayen afiyar suma yan ayi ne sai suka fashe da dariya, suka juya harshe.
Achan saman kuwa yana hawa saman ya tadda dakin fess fess yanda yake, saidai bai ganta a ciki ba wannan yasa ya soma rage kayan jikinshi, bathroom ya shige dirwct ya watso ruwa mai dumi sosai a jikinshi kafin ya fito daure da towel, samun kanshi yayi da zama bakin gado bai dade da zama ba sai gata ta shugo dakin.
Hannunta rike da tray ta hado mashi coffe da fruit data yanka mashi daman tun dazu take jira ya dawo, data gaji da zaman shine ta sauko kasa wajen ammu suka gaisa.
Dunta da hangoshi daga bakin kofa ta sauke idanunta, he’s barely half naked dagashi sai towel a kugunshi yana latsa waya.
Sallamarta ya amsa ciki ciki harta karaso bakin gadon ta ajiye a gefen bedside.
Tana kokarin barin wajen ya miqar da kafarshi don tabbatarda nazarin dayayi dazu, yanda take tafiya kamar bata kallon gabanta wannan yasa tayi tipping hartayi gaba ta daidai tasuwarta.
“Are you blind? Bakida ido ne?”
Yanda yayi maganar ya tabbatar mata cikin bacin rai yayi wanann yasa ta suake muryarta kasa tace “i’m sorry ban lura bane”
“Let me warn you, daga yanxu duk inda zakije watch your steps, kina tafiya kamar wadda bata ganin gabanta, what if kin fadi? What if wani abu ya faru dazu? Kinsan risk din faduwa with pregnancy? Are you blind ne?”
Haka ya soma jero mata tambayoyin, tama kasa gane inda ya dosa, sai kawai tayi shuru tana sauraronshi, chan bangarenshi saida ya saka kafarshi ya tabbatar da faduwar data kusa yi tadiyeta sonata tayi, yanxu badan yayi hanzari ba da tuni shikenan wani mumunnar abu ya faru itama da fault dinta, yanda take tafiya da wasu abubuwan cikin sanyi abun yana bata mashi rai, yar tsuqa yayi yabar wajen ya bufi closet, jiki a mace sabeeha ta zauna bakin gadon tayi shuru, koba a fada mata ta hango tsantsar fargaba akan fuskarshi lokacin daya tallabeta data kusa faduwa a kasan, ko ba a fada mata ba tasan saboda cikin ne.
Ta dade zaune harya fito lokacin wajen karfe goma daidai ya nufi chan gefen gado inda yake kwanciya ya zauna kafin ya soma latsa wayarshi.
Sun dade a haka tana tunanin magnagnunshi harta fuskanshi inda ya dosa da dalilin bacin ranshi, kafin ta yanke shwarar bashi hakuri.
Yan yatsun hannunta ta soma jujuyawa cikin sanyi ta soma magana “.. kayi hkuri, insha Allah zan kiyaye”
Tunda ta soma magana ya dakata da abunda yakeyi yana sauraron calm voice dinta, dake dare ne dakin yayi shuru, sai ya zama sautin nunfashin su ne kawai ke sauka kawai.
Daman tasan bazai amsa ta ba kuma ta tabbatar ya jita wannan yasa ta miqe ta wuce bathroom din ita tayi anka sannan ta sauya kaya zuwa marasa nauyi sosai kafij ta nado kanta ta shugo bedroom din.
Adaidai lokacin ya rage haske dakin ya zama dim dim babu haske sosai, saina bedside, kallonshi tayi ganin zaune yanda ta barshi dazu saidai wannan karan ya danyi relaxing bayanshi a bakin gadon ya lumshe idanunshi,kauda idanunta tayi daga kanshi ta maida ga tray din data kawo mashi fruit dazu da coffee ganin bai taba ba yasa taji babu dadi aranta,daukan tray din tayi ta juya ta nufi kitchen dashi, fitilin parlor ta dan rage kafin ta shiga kitchen din ta kunna lights din kitchen din.
Kallon tray din tayi babu abunda ya taba har coffee dinma yayi sanyi, bowl din fruit din ta dauka zata saka a fridge daidai nan wutan gidan gaba daya yayi fluctuating, take gabanta ya bada wani irin damm don ko ina ya bade yayi duhu dumm ko yatsun hannunta bata hangowa.
“Innalillahi wa inna ialaihi rajiun” ta furta ahankali, da zarar taga duhu gabanta ke faduwa sosai musamman irin wannan unexpectedly, tunawa da yanda taj ke tsoron duhu yasa gabanta faduwa,gaba daya tama manta yanxu fa ba taj din data sani a baya bane,
Cikin gaggawa ta juyo ko rufe fridge dinma bata ba ta fara dube dube cikin duhu, “didi didi..” ta soma furtawa ahankali, hartana bugewa da kitchen island, ba karamin bugu tayi ba amma kwata kwata bataji zafin ba ta cigaba da lalube, karaf taji an kamota, cikin furgici ta tashin hankali ta soma furta innalillahi a fili, allahumma ajirni fee museebati… bai bari ta karasa ba ya toshe mata bakinta da palm dinshi, dukda ciki. Duhu suke sosai hakan baisa yaga fararan kwayar idanunta ba, da suke sheki cikin duhu,ganin tana neman daburcewa don a tunanin ta ko aljani ne wannan yasa ya dan duqa daidai saitin kunnenta ya soma magana ahankali, “hey!! Hey!! Its me…”
Kasa yarda da barazanar muryarshi da kunennta ke mata tayi saika ta sake burkicewa jin muryar mutun..”innalillihi wayyo didi..didi…”, haka ta soma kiran sunanshi, duk a tunaninta har cikin zuciyarta aljani ne donta tsorata sosai, bata kawo shine ba don a sitting room table barshi kwance don tama dauka barci ya daukesa.
“ke…ki natsu, its me,…”
Ya daka mata tsawa wanda hakan yasa wata natsuwa tazo mata, “why are you so careless?ina zakije cikin duhun nan?meysa bazaki tsaya wutan ya dawo ba?”
Ya jefo mata tambaya wannan karan muryarshi ta dan sassauto,
Sai a lokacin ta samu damar bashi amsa,”
“daman…wajenka zanje saboda naga kana tsoron duhu..”
Jimm yayi yana nazarin dalilin daukewar wutar dakin, at the same time yana tunanin maganarta, “wayace maki ina tsoron dubu?”
Yanda yayi magana tana jin saukar nunfashinsa akan fuskarta wannan ya tabbatar mata da kusanci daya shiga tsakaninsu a daidai lokacin don bata ankara ba sai yanxu, gashi ya kama kafadunta gaba daya ya rike gam tana facing dinshi.
Faduwar glass bowl din data fara kokarin sakawa a fridge kuma bata rufe fridge dinba ta juya yasa ta furgita batama san lokacin data damko kugunshi ba, dake ya fita tsayi sosai wannan yasa ta tsaya daidai kirjinshi, fuskanta na kan kirjinshi nashi tana shakar kamshin sa.
Take yanayin bugun kirjinta ya sauya,kamshinsu ya hade lokaci guda, har nashi yaso rinjayar nata, hannunta kuwa data damke kugunshi dashi har zufa yake.
Sun dade sosai a haka baice bata qala
Ba haka zalika itama batace mashi komai ba har suka dauki wajen 15mins a haka kafin wutar gidan ta dawo gaba daya.
Tunda wutan ya dawo ya bude idanunshi yana kallon gashinta dake kwance an mata kitso guda hudu ta daureshi daga baya tayi kamar dough, mayafin data daure kan dashi ma ya zame,har zuwa kafadarta.
Bangaren sabeeha batama san an kawo wutar ba saboda idanunta data rintse gam goshin har zuwa lokacin yana kan kafarshi, hannunta na kugunshi ta kankame shi, tana ji ya sauke hannunshi daga kan kafadarta, “zaki kwana ne a haka?” Take tambayar nan tashi ta shiga kwakwalwarta, tayi saurin bude idanunta, take taga hasken ya bade kitchen din, cikin hanzari ta zame hannunta daga kugunshi tayi ba, yanda take tafiyar nan ganin tana kokarin zuwa wajen glass din bowl din daya tarwatse a kasa yasa shi saurin takowa, taku daya ya damko hannunta ya janyota gaba ta fado jikinshi, hazel idanunta ta zaro tana mai kallon cikin idanunshi, wani irin yanayi mara misaltuwa ta tainci kanta a wannan lokacin, shika kallon cikin idanun nata yakeyi ya kasa daukewa, fuskan nan nashi tana nan yanda take, “kinada taurin kai ko? Didn’t i warn you earlier?“
Bata gane me yake nufi ba saida ya sake magana, “don’t make me repeat my self again, the next time na sake maki magana…..”
Ya tabe baki tare da jefanta wani irin kallo mai wuyar fassara kafin yace “watch your steps”
Yana fadin haka ya juya har zai bar kitcehn din ya dakata, “bring me coffee”
Yana fadin haka ya fuce daga dakin yana tuna maganarta, daman tun futowarta daga bathroom harta dauki tray din ta futa dashi yana ankare da ita, bayan futar tata kuwa ana dauke wutan nan kawai yaji wani abu zqi iya faruwa fa ita wannan yasa ya futo cikin duhun nan har zuwa kirchen din, lafiyarta matters to him yanxu sosai.
Ta dade sosai a tsaye tana calculating maganganunshi kafin ta daidaita natsuwarta ta dauka standing broom ta tattare kwalbar sannan ta sake reboiling coffee din ta zuba a wani mug din kafin ta futo.
Saida ta daga kafarta ta soma jin zafi sosai saboda buguwar datayi haka dai ta daure ta shigo dakin bakinta dauke da sallama.
Tunda ta shigo ya mata kallo daya kafin ya duake idanunshi harta karaso inda yake, taqi yarda su hada idanu saboda wata iriyar kunya dataji ta lulubeta lokaci guda.
“Bismillah” ta furat ahankali,karba yayi kafin yace “thanks” chan kasan maqoshi.
Tana bashi ta zagaya gefen gadonta zauna kamar me neman gafara, harya gama shan coffee din ya miqe zai futa dashi ta dakatar dashi, “kawo nakai kitchen din”
Bai tanka ta ba fuce daga dakin, yana futa ta shingida jiki a mace ta kwanta abunta.
Harya shugo dakin ya zagayo tana jinshi saidai bata yarda ta bude idanunta ba, shima yayi kwanciyarshi, itadai cikin mintuna qalilan barci ya kwasheta shiko ya dade kafin barcin ya fuzgeshi..
Abuja nigeria….
Abubuwa da dama sun sauya cikin ahalin gidan Anne, masu dadi da marasa dadi, rayuwar maya ta sauya gaba daya sai ya zamana kamar yanxu ne ta bude sabon babin rayuwarta yanda taga dama babu idanun daddy akanta, har zuwa yanxu suna zuwa makaranta ita da laila saidai ko’ba a fada ba da an gansu za a gane banbancin halayyansu,musamman wajen maida hankalin wajen karatun,ayanxu suna matakin 300 level.
Duk abubuwan da maya keyi babu wanda ya sani sai laila dake tare da ita koda yaushe, bata maida hankali wajen karatun kwata kwata, itace bin yayan manya, da yake makarantar ta yayan wane da wane ne kowa yana ji da kanshi, a hakan ma taso a ce a hostel take don ta fantama yanda take so saidai hakan bai yuwu ba, yanxu idanunta ya gama budewa saima tafi jin dadin rayuwa anan fiye da lokacin da take acahn california.
Kullum zasuyi waya da mummynta da daddy, ada idan sukayi waya babu abunda take yawan tambaya sai lokacin da zasu dawo naija suma, yanxu tama daina complaining dawowar tasu saboda hakan yama fi mata dadi saboda tasan halin dadin nata.
Bata da matsalar komai daidai daga kan kudin kashewa, daddy na tura mata haka zalika anan gida ma anne tana basu allowance.
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID