Chapter 99/100
Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 42 min read
Cikin sauri ta fuce daga wajen ko ganin gabanta batayi kirjinta na bugawa tayi saurin saka hannunta dake rawa akan kirjin nata, ji take kamar zuciyarta zata fado, marin fuskanta ko tayi yayi wajen sau biyu ko zata tashi daga mafarkin da take tunanin shi takeyi.
Samun waje tayi a backyard din ta zauna yar a kasa, hawayen dake sauka kan fuskanta ko batama san tanayinsu ba.
“Tajudeen ta gani yanxun nan? A cikin gidan nan ? Kuka shine dan nanna?”
All this while tana tare dashi cikin gidan nan batasan shine ba?duk zamanta a saudi bata taba sanin cewa mahaifiyarsa yar nigeria bace, tadai tuna lolacin da ammu ke bata labarin yanda yazo gidan, an rabashi da mahaifiyarsa tun yana kankani, shiyasa ya taso bashida mahaifiya a tare dashi sai hidaya daya yarda da ita sosai.
Harta fara jin emotional feelings na ganinsa datayi, tunawa da abubuwan da suka faru achan saudiyya yasa lokaci guda ta daqo sense dinta.
Take duk abun da ya faru ya soma dawowa akanta, rayuwar da sukayi shida ita achan da abubuwan da suka faru tsakaninsu da yanda tabar gidan, duk Kokarin datayi na ganin ta danne zafi da dacin abun kasa wa tayi kawai ta fashe da kuka, harga Allah ta cireshi daga rayuwarta ta, kuma bata fatan ta sake hada hanya dashi har abada, ta binne rayuwar datayi a saudi gaba daya kuma bata fatan wata rana ta tono shi, amma yanxu da suke inuwa daya ta ina zata fara?? Kai wannnan wace iriyar kaddarar rayuwa ce? Rayuwarta juyawa kawai takeyi yanda bata so kuma bata tsammani, ba haka takeso ba.
Ta dade zaune bata ma san da mutun a gabanta ba saida taga inuwarshi a gabanta yasa tayi saurin yin baya gabanta na faduwa.
Handkerchief din dake hannunshi mai kamshin gaske ya miqa mata yana kallin cikin idanunta, yanayin yanda wajen keda haske kamar hasken rana saboda wutar lantarki yasa ta gane yanad ne a gabanta,
“Please wipe your tears”
Samun kanta tayi da sauke kanta kasa ta kasa karban hanky din sai jinshi tayi kan fuskanta kamar ana sharewa, da sauri ta dago fuskanta ta kalleshi “meysa kike kuka fatima? Meke damunki?”
Kasa magana tayi saboda yanda takeji aranta kamar tayi pouring out komai ko zataji sauqi.
“Fatima!!!” Ya sake kiran sunanta a natse, “meysa kike kuka?An maki wani abu ne? Bakida lafiya ne?”
Girgiza kanta ta soma yi ahankali taqi yarda su hada ido dashi.
Shuru shima yayi gaba daya yayi sanyi sosai ganinta tana hawaye haka.
“Ko baki fada min fatima i see loneliness in you, i see pain in your eyes, please share your pains and burdens with me, I’m willing to listen to you”
Sama sama ta soma sauke ajiyar zuciya, hawayen fuskanta kuwa sunqi tsayawa tana sauraronsa, “dan allah ki fada min damuwarki, bana son ganinki cikin damuna kinji..”
Nanma shuru tayi ta kasa cewa komai tana kokarin daidata kanta.
“Fatima i…i…”
Saurin karban hanky din hannunsa dake dab da fuskarta tayi ta share hawayen dake fuskan nata idanunta har sunyi jaa sosai kafin ta miqe tsaye shima ya miqe yana kallonta.
Murmushi ta kakalo da kyar tace “ya hamad babu abunda ke damuna kaina ke ciwo ne shiyasa”
“Baki iya karya ba,”
Surprisingly ta kalleshi ya kureta da ido tayi saurin dauke nata tace “ba karya nake ba ya hamad”
Dan murmushin da bai shirya yi ba yayi yace “shikenan, but please inason ki sani, im here for you okay? Idan abu na damunki don’t hesitate to tell me”
“Meysa ya hamad? Niba kowa bace a wajenka, ni yar aiki ce kawai, babu dalilin da zaisa ka damu dani”
“Waya fadi maki haka? I care for you, i can see alot thru you, don’t keep it to your self okay?”
Yaqe kawai tayi tace “nagode ya hamad” tana fadin haka tabar wajen da sauri.
Maganr haya ce ta fadi mata akanshi, haya keeps telling her that yanasonta ita kuwa bata fatan karama ka ta wani bala’i,she wants to stay on her limit don yafi karfintaa and she has had enough.
Wanke wanken da bata karasa ba kenan ta wuce dakin rabi, ta roketa ko zata iya kwana dakinsu basira tunda bilki ta tafi kuma akwai extra gado tace mata eh.
Koda ta fada ma hadiza bata wani damu ba tace mata taje.
Aiko kwana tayi kan sallaya tana kai kukanta ga Allah, akan ya nema mata mafuta.
Jamila na komawa gida dahiru yayita faman kiranta, karshe ma dai kashe wayar tayi ta aje.
Washe gari, tun wajen karfe shida da rabi duk suka fito domin daura sanwar breakfast, gaba daya kana ganinta zakace bata da lafiya she looks so pale and sick, rabi ta tambayeta meke damunta tace ciwon kaine kawai.
Haka suka gama komai rabi tace suje su jera komai kan dining, tsoro da fargaba ne ya durar mata, yanxu the least abunda zata bari ya faru shine yasan tana nan, wanda bazata taba barin haka ta kasance ba, gashi batada dalilin da zatace bazata kai ba.
Wata dabara ce tazo mata ta kunce dan kwalin dake kanta dake yanada girma sosai wannan yasa ta yafashi suka soma futarda warmers din, woof datakai zata dawo, lokacin har sun fara saukowa, dake yau weekends kowa na gida.
Laila da maya ne suka fara saukowa kasan don a dakin maya laila ta kwana jiya, hayaniyarsu ce kawai ke tashi, shugowarshi ce tasa sukayi tsit gaba dayansu, maya da kaudi tace “good morning uncle taj”
Laila ta gaishesa ya amsa su a taqaice kafin ya wuce sama, sabeeha dake labe wajen shugiwa dining din tana jin muryarshi ta dakata gabanta na faduwa, saida taji laila na cewa “da alamu dai yau nanna a sama zatayi breakfast”
Daga mata gira daya maya tayi kafin tace “gashi nan ya wuce sama, anya maya zaki iya…?”
Hade rai maya tayi sosai tace “kisa ido mana kigani idan ban sa hankalinshi ya dawo gareni ba”
Dakatawa tayi da maganar tare da yima sabeeha wani mugun kallo, laila ko tsoron yima sabeeha magana take kar mayan taji haushi.
Abunda ta kawo ta aje zata juya maya tace “kinga zobenki kuwa? Naji dazu kina nema, kinsan gidan ne yanxu a cike yake da masu hannun bera”
Bude baki laila tayi da mamaki jin karyar da maya ta zugo dukdan ta kunsa ma sabeeha itako tayi wucewarta ko takanta batabi ba.
Dawowa kitchen rabi tayi tana kallon su suna wanke abubuwan da aka gana amfani dashi, yau gaba daya qnai zazzabi zazzabi takeji sosai wannan yasa ta barsu da sauran gyaran.
“Sabeeha..dan allah ga warmers din bangaren nanna nan kije kikai sama, ta buqaci yin break a sama yau”
Dam gaban sabeeha ya vada, tabbas dazu taji muryanshi kuma taji sanda laila ke cewa da alamu a sama zaiyi breakfast, yanxu ya zatayi kenan? What if ya ganta kai bazata bat hakan ta kasance ba.
“Anty rabi bari na karasa wanke wanken basira takai saman”
“Ah ah ke zaki kai, ita ta cigaba da aikin”
Basira kamar ta hadiye zuciya dan bakin ciki, ta wullo ma rabi wata iriyar harara kamar idanunta zasu futo.
Hankali a tashe sabeeha tace “toh”
Rabi na komawa daki gabanta ya tsananta, ya zatayi yanxu?.
Juyawa tayi ta koma daki ta dauko hijab dinta ta futo ta dauka tray din ta nufi hanyar futa, har zuwa lokacin gabanta faduwa yake, su maya na breakfast basuma lura da wucewarta ba kwata kwata.
Haka ta bi stairs dinnan kamar karta kai karshe tsabar fargaba ta nufi part din nanna.
Kafun ta shiga tayi saurin jawo bakin hijab din nata wajen bakinta ya zamana iyakacin idnaunta kawai ake gani ta gyara tsayuwarta kafin tayi knocking.
“Yes come in”
Akayi maganada daga ciki,runtse idanunta tayi ta bude kofar tare da sallama ciki ciki,
yana zaune kan kujera idanunshi na kan wayanshi kamar yana karanta abu, kwata kwata bai dago ba, itako tana arba dashi taji kamar tray din zai kubce mata, ya sauya gaba daya kamar bashi ba, tana hango kwanciyar hankali a tattare dashi gashi ya wani irin kara kyau sosai, kamar ba taj ba wallahi.
Ajiyar zuciya ta suke abubuwa da dama na yawo akanta ta nufi dining ta aje ta soma jera komai.
Gaba daya attention dinsa baya ga wanda ya shugo, yana replying messages din dake wayarsa, harta gama jerawa ta juya zata futa daidai nan nanna ta futo.
“Har an kawo breakfast din” nanna tayi magana don batasan wacce daga cikin yaran ta kawo ba.
Gyaran muryanta tayi kamar wadda ke mura yanda baza a ganeta ba tace “ eh ina kwana nanna”
“Ah ah yarinyar kirki yau kece kika kawo min breakfast din,”
“Eh,”
“Toh sannu”
“Ya Naji muryarki haka, ko mura kikeyi?”
Kamar mai tsoron magana dukdan karya gane tace “eh”
“Toh kunsha magani kuwa ko a kaiki asibiti?”
“Eh nasha” ta fada muryanta na breaking ganin ya dago ya mata kallo daya tayi saurin sauke kanta kasa ta kawar dashi gefe.
“Toh allah ya sawaqa”
Ko ameen din bata iya fada ba ta juya kafarta na harde ta futa daga part din.
Kallonshi tayi ganin ya yi saurin aje wayar tunda ta futo, ba tun yanxu ba tayi sensing kamar akwai abunda ke disturbing dinshi kuma bata takura don ya fada mata ba amma tanason sanin koma menene.
“Ga breakfast ko? An kawo”
“Okay oummi”
Suka zauna suka fara cin abunci bayan nanna tayi serving dunshi, janshi take yi sama sama da hira musamman hiran business haka.
Suna gana karyawa zai wuce nanna ta dakatar dashi.
“Zauna tajudeen”
Ya zauna sitting room itama ta zauna tana fuskantarshi.
Shuru ne ya biyo baya kafin ta tattara courage dinta tace “ina kawunka? Banji kana maganarshi ba?”
Khaal take nufi kenan, shuru yayi yama rasa me zaice mata, bayason tasan komai ayanxu tukunna sai yayi resolving komai.
“Yana nan lpy,”
“Are you sure babu abunda ke faruwa tajudeen? Is there something that i need to know? Meysa kazo nigeria”
“Saboda ke oummi”
“Nasani amma…”
“Oummi please…zan fada maki komai amma ba yanxu ba,”
Sauke ajiyar zuciya tayi ganin haka yasa tace “toh shikenan, inason ka hadani dashi, its been ages rabona dashi”
“Insha Allah” ya amsa ta kafin ya mata sallama.
Bayan fitar sabeeha cikin gaggawa ta wuce part din shi wai don tayi using wannan opportunity din tayi gyaran part din kafin ya dawo.
Allah yaso babu wani datti a part din da zaisa ta wani dade, gyaran gado ne kawai da wankin bathroom sai kuma vacuuming da zatayi.
Da dakin ta fara cikin gaggawa ta wanke toilet din kamar tayi tsuntsuwa ta gama haka takeji tana gamawa ta futo zuwa sitting room, goge gogen ko’ina ta fara ta saka humidifier saannan ta kunna ac parlor din, tana tsaka da kashe electric vacuum din taji karar kofa, ta zaro ido waje, abunka da batada wani yawa tayi saurin juya baya ta duqa a gaban vacuum cleaner din kamar zata dauka abu.
Shidai yaga mutun a tsugunne ga karar vacuum cleaner sai yayi tunanin ko wadda ke zuwa gyaran part din ne.
Bai bama wadda ke wajen attention ba don bashi time din wannan ya tunkari stairs tanajin tafiyarshi har zai hau sama ya dakata, tare da juyowa yace “are you done???”
Tasna da ita yake and bata son raising anything da zaiyi suspecting itace ko ya gane ita ce wannan yasa tayi saurin girgiza kai.
Shi ganin abun yayi ma kamar rainin wayo sai yayi tunanin ko kurma ce, ya wani juya bai sake kalon inda take ba ya wuce sama.
Cikin sauri ta dafe kirjinta tare da janye hijab din data rufe kusan duka fuskanta dashi saboda nunfashinta dataji yana neman dauke.
Ay ko second daya bata sakeyi ba ta arce hartana tuntube.
Yana gama abunda yake ya futa daga gidan shima.
Yauma neman jamilu suka koma yi, gidan ma a rufe yau suka taddashi an saka kwado.
Sabeeha ko tana komawa daki ta samu waje ta zauna ta doka uban tagumi.
“Anya bazata hakura da karatun nan ba? Saitaji dama maman nata ta maida lafiyan kawai,“
…
Misalin wajen karfe hudu na yamma jamila ta dawo, mai shagon saka chargy dake gefen gidan na ganinta ya shiada mata motar datazo jiya sun sake dawowa.
Tana shiga cikin gida ta kira hadiza, ta dunga Zazzaga masifa itafa wallahi idan aka kama jamilu bazata yarda ba gwara hadiza tasan yanda zatayi tun wuri, hadiza ta shiada mata wallahi babu irin tsoratar da sabeehar da batayi ba akan ta fada mata ko wani abun tayi aka korota ta shaida mata ita wallahi aiki kawai taje tayi suka gaji suka sallameta, jamila tace ay wallahi duk wadda kikaga an sallamota haka toh duk yanda akayi wani abu tayi.
“Amma jamila in wani abu tayi suke nemanta mutanen nan ba hukuma zasu saka a ciki ba?,kuma kince masu kudi ne”
“Eh kuma haka ne fa, ke harda wani balarabe fa toh kodai….kodai santa yake ne ya biyota har Nigeria?? Dan jamilu yace daga agencies suke wai, kuma wallahi wanda ke nemanta shi balaraben ne kuma dan sauudiyya”
Shuru hadiza tayi tana nazari tace, “kuma kince masu kudi ne?”
“Eh mana jiya kinga jibegegiyar motar da sukazo da ita”
“Ina zuwa jamila”
Kit ta kashe wayar ta futo zuwa kitchen bataga sabeehan ba ta zagaya backyard saiko ta ganta tan shanyan kaya.
“Ke zonan”
Aje bokitin sabeeha tayi tabi bayanta suka shiga daki hadiza ta dubeta tace “akwai wani wanda yace yana sanki ne achan saudiyyar kafin ki dawo?”
Cikin sauri sabeeha ta dago gabanta na faduwa, “ah ah” ta amsa ta a natse,
“Dan uwarki me zaisa wasu suzo nemanki anguwarmu? Eh??“
Sauke kanta kasa tayi tana nazari, badai taj ke nemanta ba? Ina babu abunda zai shashi nemanta.
“Ba magana nake maki ba kike sassauke kai kamar munafuka? Babu yanda za ayi wani balarabe yazo yana nemanki indai bakiyi wani abun ba, karuwanci kikayi achan??”
Cikin jin zafin maganr maman nata ta dago ta kalleta “wallahi mama ban taba yin abunda allah ya haramta ba ni bansan su waye ba”
“Na rantse da allah kika jawo min bala’i ina tsaka da jin dadin rayiwata tun ban tsufa ba allah ya daukemin talauci a wannan shekrar wallahi wallahi sai kin gwanmaci bin ubanki lahira,”
Tana gama fadin haka ta korata, sabeeha ta fita jiki a mace.
Yanxu idan mamanta ta gano cewa tayi aure a saudiyya fa? Idan ta gano abubuwan data boye mata ya zatayi? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, take gabanta ya soma faduwa tunawa da maganganun da mamanta tayi, ko ba a fada mata ba tasan taj ke nemanta, amma meysa zai nemeta? Batada wani alaqa dashi kuma, alqarsu ya gama yanketa tun kafin ta Sanyo kafarta a kasarnan ya mata kora ta wulaqanci duk halarci datayi masa.
Tana fita hadiza ta kira jamila, tana dagawa tace “jamila munafukar yarinyar nan taki fada min komai wallahi, …”
“Haba hadiza yarinyar nan tafi karfunki ne? Eyy?”
“Bari nasan dabarar da zanyi, baki cemin komai ba gameda shi wanchan”
“Shege yanata faman kirana jiya naqi dagawa dana gaji blocking din shege nayi”
“Amma bkya tunani zai iya jawo mana matsala jamila? Kinga yanxu…”
“Kinga dan allah kibar maganar wannan dan wiwi din, babu abunda zai iya, kuma ay baisan cewa…”
“Jamilaaa jamilaaa….” Jamilu daya bankadi dakin ya soma kiranta.
Saurin kashe wayar tayi tana kallonshi gaba daya sai warin rana yake tsabar an bugu.
“Da wa kike waya?”
“Hadiza ce”
“Mutanen nan bin yan unguwa suke suna bincike akaina, wallahi zan fada masu gaskiar al’amari ni banida wani hadi da ita”
“Haba mai gida, so kake ka tona mana asiri, ka manta kudaden da muka karba? Da albashinta da muka dunga karban kusan rabin kason kudin?”
“Toh hadizar fa? Kin fada mata me tace?”
“Ka zauna mana” ta fada tana kallonshi yanda yaketa faman gumi.
“Me gida banajin mutanen nan wani abu tayi masu suke neman, ni nafi zargin ko daya daga cikinsu ne tayi aiki a gidansu yake sonta shine ya biyota”
Dam gaban jamilu ya bada, idan bai manta ba da kanshi ya bada aurenta ba tare da tunani ko na sakan daya ba, kuma jamila bata sani ba kwata kwata, maquden kudade aka basu shida ogan agencies dinsu kuma suka raba a tare.
Toh kodai dalilin dayasa ake namanta kenan, bazia manta irin maqudan kudaden da suka raba ba shida oga har fili saida ya saya a duten habuja duk jamila bata saji ba badan kudin sun kare da wuri bama ta hanyar chacha da yakeyi ay da har aure zai karo.
Sai kawai jamila taga yana murmushi a ranshi yace “harka ta samu kenan”
“Yanxu dai kinsan inda hadizar take ko?”
“Eh har gidan naje wallahi”
“Toh ay shikenan” ya fada tare da wucewa daki, ko minti biyu baiba ya kwado mata kira aranta tace jarababbe.
Tunda ya dawo gida bai sake futa ba sai wajen karfe biyar, yana futa sabeeha ta lallaba ta wuce part din nashi, tayi abunda zata ta fuce.
Yana cikin workout cikin gym din daya fara zuwa wasu yammata sukazo inda yake tare da mashi sallama.
Irin classy abuja babes dinnan ne da sukagaji duniya sosai dan kowacce da yan kudadenta a jiki, ansha bbl duwawu tuku tuku kana gani kasan na natural bane ga attchment da sukaji akansu da suka daurama dankwali.
Sallamr da sukayi ne yasa ya aje abunda yake ya dago shi kwata kwata baima san dashi suke ba harya miqe zia bar wajen daya daga cikin babe din wadda tayi dayar kyau tace “hey!!!, can i have a minute with you”
Fuskanshi babu yabo ba fallasa ya tsaya ya kalleta daga yanda take magana ya gane irin matan nan ne da suke flirting da mutane.
“If you don’t mind can i have your digit?handsome?”
Smirking yayi kai tsaye yace “taken, excuse me please”
Yana fadin haka yabarau tsaye a wajen suka bishi da kallo, “teets daman na fada maki ba duka fararen nan ne masu son mata ba”
“Karya ne wallahi babu namijin da zai ganni baiji wnai abu ba”
“Okay then keep trying your luck”
“Kiji wai he’s taken?, ay wallahi ko mata goma ne akanshi teets saita sameshi,”
“Shegiyar gari” suka fashe da dariya harda tafawa.
Yana futowa daga wajen salim ya kirashi, ya shaida mashi yanda sukayi da agent din agency dinnan wanda ya basu information din jamilu.
Yana aje wayar ya sauke ajiyar zuciya beneth his breath yace “where are you? FATIMA…..?”
…
“Mama..ana kiranki a waya” dan jamila ya kawo mata, kallon wayar tayi ganin yaron ya dauka kamar ta kwada mashi mari tace “tafi dan ubanka bana hanaku daukan min waya ba”
Futa yaron yayi jamila ta kai wayar kunenta, dahiru yayi dariya yace “jamila kenan, tun jiya inata kira bakya dauka”
“Kai dahiru nifa matar aurece, kiran da kakemin bai dace ba karka sake kirana dan Allah”
“Ay baki isaba wallahi jamila, dole na kira ki dauka”
“Inkai ubana ne saika snai na dauka,kai wallahi jamilar daka sani a sa ba itace yanxu ba wallahi”
“Toh toh madallah, nace ba? Yar kawarki harta girma ashe? Ina nufin yarinyar da..”
“Dahiru…..!”
Ta kira sunanshi da karfi, “jamila kenan, kina tunanin zaku rufen baki ne? Kina tunanin na manta ne? Shekaru ashirin da doriya da suka wuce keda kawarki..”
“dakata haka ya isa, ay ban manta ba, bari zan kiraka anjima mijina ya dawo” ta kashe wayar kit…
Jamila fa har zufa take sosai, ada tayi tunanin ta raina mashi hankali ashe yasan me yake, ya zatayi da wannan shegen?”
Kiran hadiza tayi a waya “hadiza akwai matsala…”
After 2 days…
Kwanan rabi biyu tana zazzabi, ayyukan daya shafi gyaran sama sabeeha ce keyi, ita ke dafa abunci da ake yima anne da nanna na karin lafiya.
Tundaga ranar ta kara tabbatar da yarinyar nada kazar kazar, sannan tana da amana, don sau wajen biyu anne na aje kudi intentionally ko zata dauka amma ko mataar dashi ba a yi kwata kwata, gashu duk sanda zata gaishe da babba saita duqa har kasa saboda respect.
Lokaci guda anne taji yarinyar ta shiga ranta, nanna ko daman babu wanda zai yabi sabeeha kamarta.
Tana gama ayyukanta zata wuce dakinta ta zauna, kwata kwata bata yarda ta hada hanya da yan gidan, allah ya taimaketa ma suna hutun makaranta.
Bangaren taj ko duk sanda zataje saita ambula hijabi ta rufe fuskarta kwata kwata bata yarda ta bari ya ganta ba, kuma allah ya taimaketa duk zuwan da take dakinsa tana gyara basa taba haduwa.
Akwai ranar da suka kusa yin clashing shida ita, ta futo daga part din anty fadila datasa azo a dauki lunch dinshi rabi tace taje ta karbo saboda su laila basa nan sun fita.
Haka ta zumbula hijab taje ta karbo abunci sannan ta dawo, tana gab da bude kofar part din aka budo daga ciki, cikin sauri ta matsa tare da kauda fuskanta, kallo daya mata ya kauda kai ya wuce abunshi, ta sauke ajiyar zuciya tashiga ta aje sannan ta futo.
Kwata kwata bai taba kai attention dinshi gareta ba. Toh ta ina ma zai fara tunanin itace?
Cikin kwanakin nan taj yaje agency dinan yafi a kirga, da salim ya lura kamar raina masu hankali sukeyi suna karbar kudi dayaji haushi kawai yace ma taj babu kamshin gaskia atattare da mutanen, taj believed so aswell wannan yasa salim yayi threatening dinsu indai basu kawo jamilu ba zasu saka hukuma a lamarin, don gaba daya basu da gaskia.
Abokin jamilu kuwa dayaji yayi saurin kiransa ta sabon layin daya chanza ya shaida masa komai, jamilu fa ido ya raina fata, idan aka gano komai zai iya shiga matsala, gwara tun kan akaiga hukuma ya fada masu gaskiar shi bashida alaqa da yarinyar kuma ya kaisu inda take kar ace za a kamashi.
Waehe gari da safe da kanshi ya tafi agency, oga ya nemi salim a waya don ya bada katin sa, ya shiada mashi jamilu yazo, salim ya kira taj ya shaida mashi threat din da suka masu yayi aiki don jamilun ya bayyana kanshi, ko abunci kasa tsayawa taj yayi yaci ya futa.
Harya gane wajen don da kanshi yakai kanshi suka hade da salim.
Suna shiga jamilu yayi kuri kamar munafuki a zaune.
Oga ya kallesu yace “dan allah kuyi hakuri, kar kusa hukuma a ciki gashi nan wannan ne jamilu”
Salim ya dubi taj yace “this is jamilu,“
“Oga dan allah kuyi hkauri, dan darajar allah karku kamani”
Salim ya kalleshi yace “babu abunda zamu maka, tambaya daya biyu zamu maka”
“Kasan wannan yarinyar??”
Kallon hoton jamilu yayi yayi kamar bai ganeta ba
“Tayi wani laifin ne? Sata tayi ne? Kamata zakuyi?”
“Ah ah babu abunda tayi ka kwantar da hankalinka babu abunda zamu mata”
“Toh a gaskiya nidai ba marikinta bane,anguwwar mu daya nida mahaifiyarta wadda ta kasance kawar matata, toh shine daman ta nemi alfarmar a nema mata aikatau, saboda yarinyar bata da uba shine na rubuta nine marikinta”
Salim ne ya dubi taj ya mashi fassarar komai taj ya mashi magana da turanci shi ba wannan dogon bayanin yakeso ba, he wants to know inda take.
“Yanxu tana ina ita da mahaifiyar tata?”
“Sunbar anguwarmu kuma wallahi babu wanda yasan inda take”
“Ba kace mahaifiyarta kawar matarka bace”
“Eh…ay muma bamusan inda suka tafi ba”
Salim na fassara mashi ya runtse idanunshi kafin ya bude jijiyoyin kanshi na firfitowa he’s so fed up, he wants to find her, he wants to see her.
Shifa salim kwata kwata irin mutanen nan ba abun yarda bane, basa gane kowanne yare saida kudi, Ganin haka yasa salim cewa, “daga kan dubu dari biyar zuwa miliyan daya idan har kayi mana kokarin nemanta a duk inda take zamu baka abunda yafi haka ma”
Jamilu najin zunzurutun kudi haka ya bude idanu, kunenshi har motsi suke, salim na ganin haka yasan cewa duk munafukai ne.
“Toh zanyi kokari.. zan tuntubi matata, tunda tasan babarta sosai”
Murmuahi salim yayi ya fada ma taj komai, ogan agencies din yace “toh oga gashi mun kawoshi…za a bamu namu kason ko?”
Aje masu few notes sukayi sukabar wajen bayan sun bama jamilu card dinsu.
Jamilu bai taba sanin sanadiyar yarinyar nan zaiyi arziki ba auren da bai kara ba yanxu da kudaden nan zai kara saboda haka dole ya nemo masu yarinyar nan.
Washe gari yasa jamila a gaba, tun daren jiya yake mata sababi akan saita kaishi har inda hadiza take, tayi tayi ya fada mata dalili yaqi, karshe dai ya fada mata mutanen nan sunce zasu kawo hukuma idan har bai nemo masu inda yarinyar nan take ba.
Jamila najin hukuma hankalinta ya tashi, jamilu yace indai bata kaishi inda hadiza take ba saidai aurensu ya kare a anan dole ta shirya suka tafi ya hanata kiran hadiza duk asunan wai kartaji abunda ke faruwa ta dauki yarta ta gudu.
Motar haya suka hau shida ita har maitama, suna isowa estate din jamila tace “bazasu barmu mu shiga ba sai an kira daga ciki”
“Yanxu anan take? Hadizar da yar tata?”
“Eh”
“Toh me takeyi anan? Nadaisan duk danginsu babu masu arziki”
“Aikatau mana, aiki takeyi anan din”
“Toh shikenan muntafi kawai”
The next day..
Gaba daya ayau bai samu sun hadu da salim ba saboda asibiti daya kai anne treatment din da ake mata.
Basu dawo gida ba sai wajen yamma, har zuwa yanxu babu wanda yayi suspecting rashin lafiyar anne dagashi sai ita.
Kai tsaye ya wuce part dinshi ya dan kimtsa kafin ya futo ya wuce main house.
Yana shugowa ya wuce sama direct bangaren oummi, bakinsa dauke da sallama ya bude kofar sitting room, kamshin turaren wuta nee mai dadi ya mashi sallama,da yasashi sauke ajiyar zuciya,knocking din kofar dakin nanna yayi daga ciki ta bada izinin shugowa, kafin ya bude kofar, sabeeha dake tattara lunch din da nanna tasa azo a dauke tana jin sallamarshi gabanta ya wani fadi, allah yaso ta saka hijab dinnan saidai bata rufe fuskarta dashi ba, aiko wuff tayi saurin janyo shi wajen bakinta.
“Har kun dawo?” Nanna ta tambayeshi tana dubansa fuskanta dauke da murmushi, shima maida mata yayi da murmushin kafin ya amsa ta “eh”
“Hmm wannan futa da kukeyi daga kai sai anne cikin sirri ina fatan babu abunda kuke boye mana”
Ganin irin kallon da take mashi bayan tayi tambayar ne yasashi kauda kanshi, don bayason su hada ido don bayajin zai iya mata karya.
“Laaa oumi, babu komai, munje factory ne kawai”
“Toh ay shikenan in tayi tsami maji,kayi luunche?”
Girgiza mata kai yayi yana jujuya wayan dake hannunshi, yanda ta mashi tambayar nan yasan cewa ta gane suna boye wani abu shida anne.
“Fatima zuba mashi kafin a futa da sauran abuncin”
Tunda ya shugo baima lura da mutun a wajenba amma dayaji anne tace fatima sai kawai yaji yanason kai hankalishi zuwa ga wajen.
Sunne kanta tayi kasa sosai yanda baza a hango fuskanta ba kwata kwata, gashi ta duqa tana arranging plates da warmers din kan tray zata futa dashi, shiko ya dage ya bita da ido sosai at the same time gabanshi na faduwa ya rasa dalili.
Kallonshi nanna tayi ganin yana kallon inda sabeeha ke tsugunne, ga sabeehar itama bata dagoba kamar wadda ke tsoron za a kamata da wani abun”
“Fatima??…”
“Na’am” sabeeha ta amsa ta, ciki ciki “jeki kawai,”
Naam dinnan datace ne ya kara sashi kallon inda take don ya dauke idanunshi akanta,kamar wani mai nazari haka
Sabeeha ko nanna na ce mata ta tafi tayi saurin miqewa ta futa.
“Bari na zuba maka da kaina” nanna tayi magana don ganin yanda ya kalli sabeehar ya tabe baki kamar wanda ke kyan kyami yasa nanna tunanin ko ba kowa yakeson ya sa mashi abunci ba, itama don taga fatiman nada tsafta ne sosai yasa tace ta saka mashi, amma ganin irin kallon daya mata yasa tace fatiman kawai ta tafi.
Kallon dayama sabeeha ya gane itace take zuwa part dinshi tana gyarawa, shi gaba daya ya dauka she’s mute ashe tana magana, amma ko sau daya bata taba gaishesa ba kuma duk ma’aikatan gidan idan suka ganshi kamar su tsugunna mashi,
Sabeeha na fita daga dakin ta sauka kasa, itafa wannan abu ya fara damunta, kullum tsoro da fargabar haduwa dashi take, shiyasa take kokarin ganin ta raba hanyar dazai sadata dashi gaba daya, Har Allah allah take su koma school.
Zaune take bakin gado ta dora kafa daya kan daya tana sanye da irin camisole dinnan dake kama jiki sosai, hadiza na daga zaune bakin gado sai faman yaqe take yi.
“Hajiya karama dan Allah kiyi hkuri….”
Wani irin disgusting kallo maya ta mata tare da cewa “hkurin me kike bani?”
“Wai naga kwana biyu idan nazo gyara sai rabi tace kince karna sake zuwa bangarenki sainayi tunanin ko dan saboda abunda Fatima tayi ne”
“Meysa zan yarda dake? Yarki barauniya”
Murmushi hadiza tayi tace “laifin yata saiya shafeni?”
“Na tsaneku wallahi, dake da yarki, ko ganinku bana sonyi”
“Bakya son zamanta ne a gidan nan?”
Kai tsaye tace
“Eh..”
“Toh saina maida ta inda muka futo indai zamanta anan yana damunki”
Kallon mamaki maya kema hadiza, “akan farin cikinki ay zan iya komai kuma zan iya sadaukar da komai”
“Harda yarki?”
“Eyy wallahibki yarda dani,”
“Kina tunanin zan yarda dake ne?” Maya ta jefo mata tambaya, “hajiya karama kenan, nasan fa ba yarinyar nan ce ta dauki abunku ba ranar da kika shugo dakinmu aranar kika aje abunnan kuma na ganki da idona amma ban fadawa kowa ba saboda banason a bata maki ranki, yanxu zaki iya yarda da maganata”
From the shock on her face zaka gane cewa mamaki ne karara akan fuskanta, kallon hadiza kawai take abubuwa na circulating aranta.
Sai kawai maya tayi murmushi don babu abunda yazo ranta sai tunanin duk yanda akayi sabeeha yar kishiyar hadiza ce, uwarda ta haifeta dai bazatayi wannan abun ba amma ita meya dameta da wannan, she just wants to see the girl miserable don kawai akwai something off datake ji about yarinyar, wanda ke sata feeling anxious and scared kuma ta rasa dalili.
Chan bangaren jamila, dahiru fa baibar kiranta ba kuma taqi dagawa saida taga ya mata wani dogon text yasa tayi saurin kiranshi, yana dagawa tace “dahiru me kakeso?Ehh”
“Jamilaa..jamilaaaa ki daina qin daga wayata, wallahi kinsani babu kai, karkiga wai girma yazo wallahi cikakken dan tasha nake”
“Toh me kake so? Ehh?”
“Kuna tunanin zaku yagi arziki ku barni ko? Toh wallahi baku isa ba,”
“Me kake nufi kenan?”
Dariya ya kyakyace dashi yace, “naji ance yarmu ta girma, madallah ashe dai da rayowar imani aranku keda kawar taki,“
“Me kake so dahiru, ka daina kirana tun kafin jamilu ya gane”
“Toh toh..saurareni, tunda kunci moriya nima sai a barni nasha romo ko?”
“Me kenan?”
“Kinga shekara nawa kenan tunda kika gujeni banyi aure ba, kuma da kumari na wallahi, man power nake sha duk sati kuma abar tawa kullum bata kwanciya, shine nakeso ku bani yar tamu ko? Asirin namu yafi rufuwa dakyau ko ya kikace”
“Wai kana nufi hadiza ta baka yarta??”
“Ah ah ke kuwa yarta kuma? Kodai yar da kuka chanzo”
Dammm gaban jamila ya bada, wallahi karamin hauka ne dahiru bai sata ba, tashin hankali da ba a sa mashi rana.
“Kinga saimu rufawa juna asiri ko?” Ya karashe yana kyakyacewa da dariya.
Saurin danne abunda ke ranta tayi tunawa da babu abunda zai iyayi,“idan muka qi fa? Me ka isa kayi? Meka sani dahiru? Bakasan komai ba, barazanarka ta banza ce wallahi dahiru,mteww dan wahala”
Tana fadin haka ta kashe wayar, ta soma kiran hadiza, hadiza na dauka ta labarta mata komai wayar da sukayi da dahiru, hadiza tayi shiru tana wani nazari.
“Dake shi tsinannne wai tunanin yayi min barazana zaiyi, bayan babu abunda zai iya, kowa idan talauci ya gama bugunshi sai kuma hauka, kinyi shiru bakice komi ba?”
“Jamila…anya wannan ba shawara ce mai kyau ba eh? Zamanta anan yana kawo min matsala, na kasa jan yata a jiki, kuma farin cikinta shine damuwa ta ayanxu,”
“Yanxu me kika yanke kenan”
Dariya hadiza tayi tace “dahirun ne daman daidai da ita, ay namayi kokari rikon danayi mata shekara nawa?ki kirashi ki shaida mashi na bashi ita wallahi, zansan yanda zanyi da hajiya”
“Kice kawai dangin ubanta ne sukace lokaci yayi kuma an mata miji, ina wannan matsolon kanin dalha, ki bashi yan chanji kawai ki rufe bakin sa”
“Hakan ma za ayi, kinga kuma kwa huta da masu nemanta, inama zan bari tayi associating da masu kudi, kamar yanda kikace ne kila wani ya ganta yakeso shine yake bibiyarta ay bazan taba bari a sauya mata rayuwarta ba wallahi,ina ribar tawa kenan?”
“Oh hadiza kishiyarki ta shiga uku…”
“Ay kishiya daya gareni a duniya, ba a taba abunda hadiza ta kwallafa rai akai a zauna lafiya, wallahi zan iyayin komai jamilaa…”
“Haba waa dama chan kinyi sanyi ne hadiza yanxu nasan asalin hadiza ke magana, kinfi shaidan” suka kyakyace da dariya….
….
The next day..
Yau ta kasance Saturday’, da sassafe ya futa gym don ya saba da hakan yana dawowa gida lokacin wajen karfe tara saura, wayarshi ya dauka ya soma kiran salim, yana dagawa ya tambayeshi any update akan jamilu, ya shaida mahsi gar zuwa yanxu bai nemesa ba, taj yace anya kuwa ba guduwa yayi ba? Salim ya shaida mashi ay irin waennan mutanen idan har sukaji maganar kudi babu abunda baza su iyayi ba, haka nan sukayi sallama gaba daya ya kasa samun natsuwa, a matse yake da yasan inda take, shin ko tana cikin koshin lafiya? Wace rayuwa take yanxu? Tunawa da sanda ta bashi labarin ita marainiyace yayi, da kuka abubuwan datayi mashi, He wants to pay back for everything taht she did for him, she stood by him alokacin dayafi kowa buqata, ta kula dashi dukda tasan rayuwarta na cikin hadari.
Ta wani bangare na zuciyarsa kuwa begenta yake, kuma mararinta ganin ta yake,ta rigada ta kamashi sosai withouthis acknowledge,bai gama sanin cewa tabbas ta zama wani bangare na rayuwarsa ba saida ya koreta da kanshi, yanajin kamar he’s incomplete without her.
Sauke ajiyar zuciya yayi yana akan kujeran sitting room din, ya dan rufe idanunshi kamar maijin barci.
Kafin ya futa ya shiada ma nanna zai futa bazai samu yin breakfast ba, so kafin ta futa wani meeting za zatayi da wasu client dinta tasa rabi akai mashi breakfast.
Rabi ko babu wanda zata sa yakai breakfast din banda sabeeha tund aitake kula da bangaren nasa.
“Suna zqune a daki ita da basira, tana bude handout din da aka rarraba masu a school rabi ta shugo da sallama.
“Fatima zo kije kikai breakfast chan bangaren da kike aiki”
Tund ataji ance tazo takai tasan cewa yana nan, duk taoron da takeji haka ta danneshi ta tashi ta ambula hijabi wata davara ce tazo mata daman akwai wata doguwar riga da aka taba bata tanada kayafi baqi, daukan mayafin tayi ta fuce daga dakin,
Nufar part din tayi daidai nan maya data hangota ta balcony din hutawa na sama da aka kawatashi da greenish grass carpet ta sauko, waya takeyi fa da wani friend dinta amma tayi saurin katse wayar ta sauko kasan,
wajen bakin kofar ta tsaya ta nada mayafin a fuskanta tayi kamar niqab dashi kafin ta bude kofar tare da sallama.
Kafin maya ta iso harta shiga ciki,
Sabeeha na shiga ta hangoshi a zaune sitting room din tayi saurin sauke kanta kasa bata yarda ta sake kallon inda yake ba ta tunkari wajen dining ta ajiya abuncin.
Tana ajewa ta ko jerawa batayi ba juyo zata bar parlorn maya ta shigo cikin part din kamar an wullo ta.
Kallo daya tayi ma sabeeha dukda tana cikin nikab ta kalleshi yana daga zaune kawai wani irin kishinsa ya turnike ta.
Da sallamarta da motsin shugowarta duk akan
Kunenshi, saidai hankalinshi baya kanta kwata kwata, yadai san mutun ya shugo part din kuma ya gane koma waye, yarinyar dayyi tunanin shes mute, ashe she is not, the girl dayaji nanna ta kirata da fatima, wani rainin hankali ko sau dari zata wuce ta gabanshi bazata taba bude baki ba tayi magana, very disrespectful, bawai yana bama starngers attention ba ko ya damu kawai dai rainin hankalin yarinyar nan ne ya tsaya mashi arai baima san sanda yasa abun aranshi ba kodan yaji ranar an kirata da fatima ne? Kuma ta tuna mashi da mai sunan.
“Ubanwa yace ki shugo da kazamin jikinki nan bangaren?”
Sabeeha banza tayi da ita don bata da lokacin wannan allah allah kawai take ta futa, A daidai lokacin ya bude idanunshi.
“Fatima…!” Ya kira sunanta anatse
Itako hawan ruwa ne batayi ba, ta tsaya chak kana ganinta kaga mara gaskia gaba dayanta,
“Fix the meal?” Ya fada yana miqewa tsaye bai kalli inda suke ba ko ya basu attention, maya tayi saurin cewa
“Good morning uncle, can i do that instead?”
“Let her do her job” ya bata amsa yana wucewa sama, hes so cold towards maya ko me yasa? Ita kanta she keeps wondering haka, amma yanxu kuwa daya kira sabeeha da sunanta sannan a gabanta yace sabeeha ce zata zuba mashi abunci ay kawai sai maya taji kamar an taru an watsa mata garwa.
Idanunta sunyi jaa sosai ta dubi sabeeha cikin idanunta sabeeha ko ta kalli cikin idanunta tana hango tsoro da fargaba ko ba a fada mata ba tana ganin yanayin maya tasan cewa she’s jealous, ana wata ga wata.
A fusace ta futa daga part din kamar zata tashi sama.
Sabeeha tayi kwafa tace “matsalarki ke daya mtew”Tana gama abunda take ta futa.
Jamila ta kira dahiru ta shaida mashi yanda sukayi da hadiza, kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha,harda godiyar munafurci, aranshi ko tunanin da yake da abunda yake kullawa shi kadai yasani, jamila ta gama raina mashi hankali batasan cewa ya fita tashanci ba.
Hadizq ko ta nemi kanin dalha tsohon mijinta rabonda ta nemesu tun bayan mutuwar dalha da sukazo daukan sabeeha tace basu isaba ba suka barta da yarta, ta shaida mashi komai da hukuncin data yanke, bashida jaa akai kuma bazaiqi shiga lamarin ba don yar dan uwansa ne wannan yasa yace toh shiknan.
Dahiru yayi yayi yazo ya ga sabeehar jamila tace bai isa ba, kawai dai ya jinkirta za a nemeshi, da yan kudadensa a jiki ya soma shirye shirye.
Washe gari da safe hadiza ta shiada ma rabi tanason ta samu hajiya anne, akwai maganar data taso tanaso ta fada mata, rabi ta mata iso wajen anne tajw don ta shaida mata, tana zuwa ta soma mata bayanin kanin mahaifin sabeeha ne yace ya mata miji, kuma lokaci yayi daya kamata ayi mata aure.
Anne najin wannan magana ta nunfasa, ta tambayi hadiza ita ta amince ne da batun nasu tace mata eh ta amince.
Na farko dai anne tayi mamakin yarjewar hadiza don kowacce uwa zata so taga yayan ta sun samu ilimi wanda zai taimakesu koda bayan sunyi aure, daga yanda ta amince lokaci gida anne tayi sensing kamar hadiza bata damu da karatun yar tata ba.
Gashi yarinya mai hazaqa da basira, kuma ga dukkan alamunda yanda hamad ke fada mata yarinyar nada interest akan karatu kuma tanada kwakwalwa don duk tafi su laila nesa ba kusa ba dukda ita ce tazo a bayansu.
Tambayarta anne tayi ko yarinyar ta amince, hadiza tace ay bata fada mata ba.
“Toh ay kamata yaui ki tambayeta, we’re on the 20th century hadiza an daina auren dole a wannan zamani in khma karatu take sonyi fa?”
Anne ta tanbayeta hadiza tayi shuru, “ni zan tambayi yari yar dakaina naji idan karatu takeso saidai ki basu hakuri, hadiza dai kasa cewa qala tayi daga decision din anne, yanda kasan an rufe mata baki ruf kodan tana shakkar anne ne ko kuma don tana mata kwatjini ne allahu a a lam, ita da yarta amma tana jin kamar an fita iko akanta.
•••
Tunda Salim ya kirashi ya shaida mashi cewa jamilu ya kirasa ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya aje duk wani abunda yake ya futa, yana isowa inda zasu hadu da salim ya tadda har ya dauko jamilu, zuciyanshi wani irin harbawa yake kawai so yake ya ganta.
Taj na karasowa ko tsaywa gaisawa ma baiyi ba ya dubi salim yace “has he found anything?”
‘Murmushi salim yayi yace “yes sir, he will be taking us where she is”
Wata nauyayyiyar ajiyar zuciya mai dauke da relief ya sauke ya dubi salim yace “what are we waiting for????”
“Sir calm down, he wanted to be paid before…”
“Ka tura mashi 2m” zato ido salim yayi, ya kara jaddada mahimmacin wannan yarinyar a wajen wannan balaraben mai danyen kudi.
“Okay sir”
Jamilu dai kallonsu kawai yake kan babu arabi babu boko, salim yace “idan ka kaimu har inda take yace a baka miliyan daya”
Jamilu ya wage baki yace “yanxu kuwa”
Suka shiga mota a tare sai maitamaaa…..💃🏻
“Innalillahi wa inna ialaihi rajiun” sabeeha ta furta tare da saurin rarrafawa wajen da anne ta yanke jiki ta fadi, kanta ya bugu da gefen center table “hajiyaa…hajiya….” Sabeeha tayi magana tare da dago kan anne da jini ya soma malala, hannunta na karkarwa ta kidime ganin jinin duk yabi hannunta, gashi anne bata nunfashi kwata kwata, cikin abunda baifi sakam biyu ba sabeeha na daga zaune bayan rabi tace hajiya na kiranta ta hau saman rabi kuma bata dade da sauka ba kafin anne ta futo ta zauna, tana futowa ta gyara zamanta zata bude baki kenan ta gaishe da anne kawai annen ta yanke jiki ta fadi, a guje sabeeha ta futo daga bangaren anne, jikinta na tsuma sosai ga jini nan a hannunta ta tunkari stair “anty rabii…anty rabii….”
Ta soma kiran rabi, a daidai nan maya ta futo daga bedrrom dinta kunnenta maqale da apple headset tana jin kida, ganin yanda sabeehar ta futo a rikice ga jini a hannunta yasa ta cire abun kunenta.
Daga nan sama tana jiyo muryar sabeeha dake cracking tana kuka “ku taimaka… hajiya ta fadi..ta fadi…”
Maya najin haka ta shiga part din anne da sabeehar ta futo, ta ganta kwance ga jini na bin fuskanta, ay batasan sanda ta kwala kara ba jikinta na bari, daidai nan rabi da sabeehar suka hau sama sabeeha kamar za a zare mata rai hadiza ma ta hauro saman.
Hannu aka rabi ta dauka ta taho a guje kamar zatayi supa ta tsugunna gaban anne ta tallabo kanta “innalillahi wa inna ialaihi rajiun hajiya??? Hajiyaa?????meya sameki hajiya? Na shiga uku ni rabi,basira yi gudu kije bangaren hajiya fadila ki kira ta, ko hamad ki sauri”
Maya dake cikin shock din ganin anne ta kalli sabeeha dake ta faman yin kuka.
Wayar dake rabi dake jikinta tayi saurin lalubowa ta kira nanna, wajen sau biyu tana kira ba a dauka ba ta soma kiran ya sameer, shika bai dauka ba, gaba daya kowa sai kuka, musamman sabeeha harma da rabin, hadiza ko gizau, maya kam ta tsaya tana kallon sabeeha allah kadai yasan me take kissawa.
Basira na zuwa ta shaidawa anti fadila ta fito da gagagwa ko mayafi bata saka ba, hamad da laila basa gidan ta tura su zumunci gidan uncle dinsu kanin mahaifinsu.
Fadila na haurowa saman jiki na bari ta taho da gudu wajen anne, “innalillahi wa inna ialaihi rajiun, meya faru??? Meya sameta???” Fadila ta fada ta karfi cikin tsoro da fargaba da tashin hankali, ga anne dai a kwance bata motsi bata nunfashi.
“Na shiga uku ni fadila…”ta tallabo kan anne ta dora kan cinyanta jini duk ya bata mata hannu utama, ay jini. Data gani ne yafi kidima ta.
Sabeeha dake tsaye tana hawaye Batayi auni ba kawai taji maya ta turata jikin bango idanunta yayi jaa sosai ta fara wani kukan munafurci, “me kikayi???? Me kikayii ma anne?????? Kece kika futo daga dakin, ga hannunki nan duk jini what have you done???”
Hadiza na ganin maya na kukan munafurci itama ta fara, “na shiga uku ni hadiza”
Kota kansu anty fadila batabi ba bataji bata gani tsabar tashin hankali ta kalli rabi tana hawaye tace, “taimaka min rabi”
Suka cicibeta harda hadiza, suka sauko kasa da ita, gaba daya.
Sabeeha nata kuka baiwar allah kamar ranta zai futa abun tausayi.
Wayar rabi na hannun basira nanna ta kira back, daukan wayar basira tayi, “hajiya..hajiya babba ta fadi, bata nunfashi”
“Rabi me kike cewa? Meya faru? Ki nutsu kimin bayani”
“Hajiya bamusan meya faru ba, mun shigo mun tafdata cikin jini, babu kowa a gidan”
Gaban nanna ya fadi take taji hawan jininta ya motsa, “innalilillahi wa inna ilaihi rajiun, sameer baya nan, tajudeen fa? Ku kaita asibiti ku kira ambulance”
“Hajiya duk basan nan?Amma ga anty fadila nan”
“
Kit nanna ta kashe wayar ta soma dialing number taj.
Su taj ko suna shawo corner layin estate din ya kasa cewa komai tsabar shock, baidai ce komai ba jamilu nata jawabin hanya, daidai lokacin nanna ta kira wayar, ya dauka.
“Tajudeen…kana ina? Anne ta fadi, sunce bata nunfashi, innalillahi wa inna ialaihi rajiun, karna rasa yar uwata”
Tana magana tana kuka sosai ba kadan ba, ai yafi kowa faduwar gaba da jin wannan zance shida yasan condition dinta.
Tuni ya kashe wayar ya dubi salim yace “speed up please kayi dropping dina a gida lets do this some other time, its emergency please”
Da gudun gaske salim ya karama motar speed har gaban estate din, jamilu yace “kai yallabai ay nanne esitati din, anan suke wallahi ita da babarta ance aikatau sukeyi”
Gaba daya hankalin taj baya ga jikinshi, amma dukda haka yayi mamakin maganar jamilu, yama kasa cewa komai, wayar nanna ta sake shugowa ya dauka, “oummi ki kwnatar da hankalinki babu abunda zai sameta gani nan ina cikin estates,babu abunda zai sameta” yayi magana da larabci, jamilu dai sai rarraba ido yake, bai taba shugowa cikin gidaje haka hadaddu ba, gaban gaban mansion din satura’kis suka saukeshi suka juya, security suka bude ma taj kofa da gaggawa ganin yanayinsa.
Adaidai lokacin gaba daya suka futo hankali a tashe, yana hango anne a bayan fadila yayi gaggawar karasowa wajen jikinsa na bari yace “meya sameta? Meya faru da ita how and when did this happen? This can risk her life”
Fadila na kuka tace “bamu sani ba sunce faduwa tayi”
Maya data samu chance din magana ita bama ta tashin hankali da ake ciki take ba blaming game kawai take shirin yi,
“Wallahi itace, itace ta futo da jini a hannunta daga dakin part din anne”
.
Tayi nuni ga sabeeha yayi saurin maido da dubanshi ga sabeehaaaar…
Damm Gabansa ya fadi kamar zuciyansa zai fito yanda heart beat dinshi ke bugawa.
Baiwar allah Sabeeha sharf tama manta da wani batun yar buya da takeyi dashi, gaba daya a tsorace take,rabon da taga abun tashin hankali kamar wannan tun lokacin da take saudi.
Ahankali ya furta fatima….. gaba daya ya rikide ya sauya, abu biyu sun taron mashi, ga fargabar anne ga kuma fatima dayake ta nema a gabanshi.
After 3 hours..
Gaba daya daga kan sameer nanna taj da su hamad kowa gaba daya rankata kaf family din sun iso asibitin sun cika emergency ward, gaba dayansu, nanna nata addua charbi a hannunta fadila ko kuka take sosai laila tana tausasa ta, taj ko ya kasa tsayuwa shida yasan komai.
Futowar doctor barau yasa duk suka miqe nanna da idanunta suka kankance tayi saurin yin magana “doctor meke damunta? Meya sameta?is she okay?”
Shuru barau yayi yama rasa me zaice masu, ya dubi taj yace “i think its about time daya kamata su sani”
Nanna ta dubeshi tace “what are yiu talking about”
“Hajiya nada brain tumor”
“Whatttt!!!!!”
“Innalillahi wa inna ialaihi rajiun” kow aya fara yi
“Bataso a fadama kowa ba, taj was the only person that knew about this,kuma ta nemi alfarmar kar a fada ma kowa kar hankalinku yabtashi”
“Doctor…tell me she will
Be fine?”
Nanna tayi magana, sameer yace “how bad is it?”
“Shes on her treatment, idan har jikinta bai karba treatment dinba dole saidai ayi mata surgery a cire, yanxu its just a minor attack ta samu for now, thankfully bai taba brain dinba completely don zan iya cewa yana saka mutun ya zama paralyze”
Gaba daya suake ajiyar zuciya sukayi, doctor yace an kaita recovery room for now sannan dole ta zauna asibiti saboda a dunga tracking improvement na treatment din har sai an gama.
Godiya suka mashi gaba daya suka dunguma recovery, basu samu damar shiga ba suka tsaya bakim kofa suna hangota an saka mata oxygen.
Taj na zaune nanna tazo ta dafa ganin duk ya shiga damuwa sosai ba kadan ba, dazu da suka shigo da ita an dauka an rasata gaba daya.
Dafashi tayi tace “Meysa baka fadamin ba? Meysa ka boyemin?”
“Im sorry oummi, i had to, she will
Be fine i promise insha allah, she’s a strong woman”
Murmuahi nanna ta mashi tace “muyi ta mata addua”
Tunda anne tayi regaining conscious tuannin sabeeha ya dawo mashi, he actually saw fatima? Daman jamilu yace estate dinne, those that mean daman tana gidan all this while bai sani ba? Amma how? Kwata kwata bai kawo utace yarinyar dake mashi aiki ba don yanxu ne yake ganiyar tunani.
Yama rasa wani karatu zuciyarshi ke rerawa, he’s so shocked and so amazed at the same time.
Karshe dai kasa hakura yayi da zaman asibitin ya lallaba ya futa.
Bolt ya kira yana isowa ya hau ya wuce gida bayan ya kira salim akan cewa ya kawo mashi motanshi gida.
Yana isowa har wani mazari mazari jikinsa keyi, yana son kara tabbatar da bibi ya gani a gidan nan, bibim shi.
Babu kowa a kasan ko’ina shuru, tunawa da abunda jamilu ya fada kafin su karaso estate din ya sashi nufar kitchen, d more yana tunkarar wajen the more gabanshi ke faduwa, ya karaso kitchen din tana daga tsaye ta juyawa kofar baya tana hawaye.
Tundaga sama har kasa yake binta da kallo, yana ganin abun kamar a mafarki.
“Fatimaa!!” Ya kura sunanta ahankali, yanajin wata iska na kada gaba daya duk wata kofar gashin jikinsa tsikar jikinsa na tashi sosai.
Itako dataji muryansa ta wani zaro ido, gabanta na faduwa sosai taqi yarda ta juyo.
“Bibi… is that you?” Yayi magana da larabci, nanma taqi juyowa tana kokarin hadiye hawayen datake ji.
Ganin taqi juyowa yasashi tahowa kitchwn din gadan gadan ya sanya murdadden hannunshi ya kamo dan hannunta ya juyo da ita tana facing dinshi, heartbeat dinshi ya sauya yana arba da ita ga closure.
Cikin hanzari ta kai idanunta dake azabtar dashi ta watsa mashi su, gaba daya ta daukw wata rahama dake kan fuskarta kamar ba sabeeha ba.
Yakai wajen minti biyu yana kallonta ya kasa cewa komai itama ta kasa cewa komai.
Ya futzar da wata iska sai jikinsa na karkarwa ya wani irin rungumota gaba dayanta zuwa jikinshi ya mata rumfa hannayenshi biyu ya zagayeshi ga waist dinta ya kankameta soaai kamar za a rabashi da ita, tana jiyo yanda zuciyarsa ke bugawa sosai jikinsa na karkarwa ya wani lumshe idanu trying to procesa moment din, its life and direct bibinshi ce wannan, wadda yake tsumayin ganinta dare da safewya wadda kewanta yake mashi illa, wadda ta kasance weakness pount dinshi baima sani ba.
Kuka takesonyi don taj taj kam ya zame mata wata kaddara datake hunting dinta,.
Azafafe ta wani irin tureshi daga jikinta saboda yayi lakwas he’s weak gaba daya, ya nemi sake maidata jikinshi rai a bace cikin harshen hausa tace “malam menene haka??? Wannan wani irin iskanci ne haka?ya zaka zo ka rungumeni? Ance maka ni yar iska ce?”
Tafa san baya jin hausa amma da dage, shiko mamaki bai barshi ba yana kallonta kamar ba didinshi ba.
“Bibi” ya kira sunanta yana kokarin sake kamo
Hannunta tayi baya tace “don’t you dare touch me,”
Jikinta na karkarwa tace “do i even know you? You have the audacity to touch me? Just because we are maids doesn’t give you people the right”
Tana fadin haka ta juya a zafafe zata futa ta barshi tsaye da mamaki fall cike ranshi…..bata ganeshi bane? Kodai he’s mistaken? Kai ina babu yanda za ace kamanni take da fatima, daga muryanta zuwa height dinta kamanninta da komai uwa uba zuciyarshi bazata maahi karya ba fatima ce…then whys she acting kamar bata sanshi ba?
Ay ko taku biyar batayi ba zatabar kitchen din sake kamo hannunta ya jawota sosai jikinsa yana kokarin kallon cikin idanunta taqi yarda su hada idanun, ta fara kokarin kwace hannunta, shi kanshi hes confuse at the moment.
“Ka sakeni mana mene haka wai? Na shiga uku anty rabi, anty rabi”
Ta kwalo ma rabi kira, “fatima!!! Ya sake kiranta, tayi kamar batasan me yake cewa ba,
Rabi ta shugo kitchen din da sauri, “sabee…”
Saurin dakatar da ita sabeeha tayi saboda gudun karyaji sunan data kirata dashi, tunda ya ganta bata da option daya wuce ta nuna batasan shi ba batasan mai kama dashi ba.
“Anty rabi kinga ya wani riken hannu, ni bansan me nayi ba, na shiga uku” ta fada tana neman fara kuka.
Rabi babu english,😂ta rasa yanda zata tambayeshi me yakeso.
“Yallabai kayi hkuri dan Allah,” rabi tayi maganadon ta dauka ko maganganun da maya tayi daxu ne sukayi tasiri ganin yanda kowa hankalinshi ya tashi da aka fitar da anne.
Ay baima san tana yi ba kallon sabeeha kawai yake tana kokarin kwace hannunta kamar kurma.
“Ki fada mashi da turanci bakisan me ya faru ba dazun tunda shiga kika yi kika taddata ta yanke jiki ta fadi”
Sabeeha najin haka tayi saurin kallonshi tace
“Sir please leave me alone, I didn’t do anything, i just went into the room and saw anne,”
Tundata soma magana yake kallon labbanta yana karantar abunda take fada don gaba daya ta gama gaukata mashi kwakwalwa da confusion.
Waye baki rabi tayi ganin yanda yake matsowa dab da sabeehar gashi ya kankame hannunta har suka kaiga bango, jikin sabeeha na bari ta kasa kallon cikin idanunshi trying as much as possible karya gane itace,
“who are you???”…tambayar data futa a bakinsa kenan a zuciyarsa kuwa ga gama yarda da sabeeha ce wannan, amma yabrasa wani tunanin zaiyi.
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵 🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID