← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 49 OF 66

Chapter 102

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 41 min read

After some few a hours…
Ahankali ta soma bude idanunta da suka mata nauyi sosai,lumshe su tayi ta sake budewa tana bin ko’ina da kallo, take komai ya dawo mata yanda ta shugo dakin and how she end up on his bed, cikin hanzari ta fara kokarin miqewa zaune tana janye duvet din, wani irin dumm kanta yayi mata dayasa tayi saurin dafe kan nata tana waiwaye ko zata ganshi a dakin idanunta kuwa ya sauka kan bedside alarm watch din dake gefen gadon nashi taga karfe 4 harda yan mintina, take gabanta ya fadi ta wani zaro idanu sosai ta fara innalillahi aranta, “me ya mata dayasa ta passing out for so many hours, idan zata iya tunawa ta shugo bedroom din dinan wajen karfe sha daya da hamsin da wani abu.
Hankali a tashe ta tashi tsaye a furgice, ta shafa kanta taji babu mayafinta wannan yasa tabi gadon da kallo tana kokarin locating inda yake, tana ganinshi kuwa cikin sauri ta janyo mayafin zata juya kenan ya futo daga bathroom da towel a waist dinshi.
Furgita tayi ganinshi tsaye unexpectedly wanda yasa ta furta “wayyo allah na”
Saurin kauda idanunta tayi ta hade rai sosai ta tunkari hanyar futa daga bedroom din.
Ko taku biyu batayi ba ya wulla hand towel din da yake tsane kanshi dashi ya kamo hannunta tare da janyota zuwa jikinshi da karfi.

Hankali a tashe ta zaro ido tana kallonshi, mamaki take sosai yanda akayi ya sauya don harta bar saudiyya zata rantse this is not the taj data bari, yanada ego sosai don alokacin daya samu sauqin nan wani gani gani yake mata musamman dayaji ita maid dinshi ce kuma khaal ya aura mashi ita, ko kadan bayasan kusanci da ita danma dai babu yanda ya iya ne saboda yana tunanin akwai cikinshi a jikinta, she can recall how yanda dakyar ma yake iya amsa maganarta idan tayi mashi, completely ya chanza mata from didin data sani her best friend to someone cold and very harsh.
Bai bata damar magana ba shima kamar ana ingizashi ya ja hannunta har zuwa bathroom, tirjewa ta somayi tana kokarin kwace hannayenta amma ta kasa .
“Dan allah ka kyale ni,what are you trying to do? Please leave me alone”
Bai kulata ba har saida suka shiga bathroom din, bai tsaya ko’ina da ita ba sai gaban pressure shower din bathroom din, tana facing dinshi, batayi auni ba kawai taji saukar ruwa mai dumi akanta ta kowanne angle, ta kanta, ta gefenta na hannun hagu da dama da pressure sosai wanda ya sa ta razana sosai ta kidime batama san sanda ta kamo arms dinshi ba ta rike gam.
Smirking yayi ganin yanda ta tsorata sosai gashi magana takeson yi ta kasa saboda yanda ruwan ke sauka a jikinta, matsowa yayi sosai don tsazarar dake tsakaninsu ba mai tsayi bace ruwan shima ya soma sauka a jikinshi kamar ba yanxu yayi wanka ba.
A furgice ta juya mashi baya tana kokarin lokacin inda faucet din shower din yake don ta kashe, yana lura da abunda take sonyi yayi hanzari hade bayanshi da nata zuwa bangon bathroom din, hannu biyu ta aza saman bangon tanajin bare skin dinshi a jikinta, ga hannayenshi daya dagasu ya sata a tsakiyan su.
Barr barr barr haka jikin ta ya soma rawa ga tsoro ga saukan ruwa ga kusancin dake tsakaninsu, rage pressure din ruwan yayi ya soma sauka kadan kadan wanda yasa nunfashinta ya dan daidaita,so take ta juyo amma tana tsoron yanda abun zata kasance don rigar jikinta bata kirki bace gashi bata saka bra ba wannan abun kunya, she can feel how her nipplea became so hard!!!! Lokaci guda tunda ruwan nan ya sauka a jikinta ga kuma cikakken namiji a gabanta, gashi bathroom din is so steamy saboda turirin ruwan dake sauka.
Take kafafunta suka soma rawa suna neman saki zata sulale ya zare hannayenshi biyu daya dafe bamgo dashi ya kamo waist line dinta, tana jin hannunshi tayi saurin runtse idanunta tana jin wani baqon yanayi yana neman riskarta.
Kamar kai rada haka ya sake matsowa dab da ita jikinshi na hade da nata ya soma magana na.
“Trying to escape from me hmm?”
Wani irin yamm taji a jikinta tsikar jikinta ta tashi sai faman wulla idanu take, tanason magana amma kamar ya dinke bakin nata so take kawai tayi tsuntsuwa tabar toilet din.
“Why didn’t you tell me that youre sick huh??im sorry for pressuring you okay?”
Sai a sannan ta samu damar yin magana ita kasa kasa kamar munafuka.
“Please let me go,”
Kamar ana fuzgarshi ya sake manne jikinshi da nata tanajin yanda kirjinsa ke bugawa sosai kamar ana buga ganga yace “i will never let go of you, not now not ever”
Dauke hannayenshi yayi daga waist dinta ya maidashi kafadunta ya fara kokarin juyo da ita, duk tirjewarta kasawa tayi yayi nasarar juyo da ita hannayenta na kan kirjinta ta tamkesu tam tare da kulle idanunta ko kallonshi bata son yi a wannan yanayin.
Kallon fuskanta ya somayi daga kan gashinta dake kwance kan fuskanta zuwa ga idanunta da lashe din sukayi wet zuwaga dan bakinta da ruwa yasa suka zama moist har wani jaja sukayi saboda cijesu data dunga yi ba tare da tasan tanayi ba.
Tun dazu yake hana kanshi daga kallon kirjinta da tunaninsu ke yawo throu his mind, batun yanxu ba tun a saudi, tun kafin ya koreta ma.
He doesn’t want to loose him self at the same time kuma ya kasa controlling kanshi.
Bitting lower lips dinshi yayi which makes him looks more hot and sexy yana hana kanshi wuce gona da iri, don ayanxu hes trying to win her first befor anything else.
“Please sir, this is not right, this is considered a biggest sin, please im begging you…”
Yatsanshi ya sanya kan lips dinta tayi saurin bude idanunta ya sauka kan huge kirjinshi ko ina is tame a murde.
“Fatima…i will never do anything that will hurt trust me,”
“Then let me go please” ta fada ahankali
“Let me check your temperature first..” yana fadin haka ya dan rankwafo, tana ganin fuskanshi dab da tata tasan kokarin kissing dinta yake wannan yasa tayi saurin kauda fuskanta gefe.
Ya bi fuskan nata da kallo for some seconds kafin ya danyi baya ya kashe shower din.

Inda towels ke jere ya janyo guda biyu ya kiqa mata daya ba tare sa ya sake kallonta ba yace “cover up”
Karba tayi da hanzari ta lullubama kanta, tana dagowa taga ya bude kofa alamun tazo ta wuce, kamar jira take kuwa ta futo shika ya futo, tana kokarin fucewa a haka ya dakatar da ita, baisan wazataci karo dashi a wannan yanayin ba amma bayajin zai barta ta futa haka.
“Wait a minute please, let me get you something else, don’t step out like this” yana fadin haka ya wuce closet, tana fakr idanunshi kuwa ta dauke mayafinta daya fadi kasa lokacin daya ja hannunta suka shiga bathroom, ko second daya batayi ba ta arce.
Yana futowa da jallabiya yaga wayam babu ita ba labarinta, kofar bedroom din ya bude daga saman stairs yana hango kasa daidai lokacin ta bude kofa harta fuce ta karo, bitting lower lips dinshi yayi babu yanda ya iya da ita ya kyaleta don bazai iya binta ba don shima daga shi sai towel kawai.
A gurguje ta dunga tafiya tana harde kafafunta kamar ga tsoro ga fargaba, tashin hankali yanxu me zata cema anty rabi? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.
Bude kofar kitchen tayi allah yaso babu kowa wannan yasa ta nufi hanyar dakinsu da gaggawa tana shiga nanma fatan allah yasa basira barci take tayi, aiko tana shiga ta ganta a jeme sai jero masori takeyi kamar yaqi, ajiyar zuciya ta sauqe a gurguje ta wuce bathroom ta tube kayan jikinta da suka jiqe, gaba daya ta manta tana period allah yaso bata rushing sosai amma yanda ta jike dunnan zata iya bata jikinta.
Kimtsa kanta tayi ta sake wanka kafin ta tsaya jikin mirror din bandakin tana duban kirjinta, gaba daya yanda sukayi roundy shape dinnan haka sukayi jaa sosai musamman wajen nipple dinta daya dan kumburo, har tsoron tabawa takeyi don this is the second time ta gansu sunyi mata haka.
Tana futowa daga bathroom rabi ta shugo da sallama, amsata sabeeha tayi tana kokarin hada ido da ita don ji take kamar ta ganota.

“Wannan shemanmiyar badai barci takeba har yanxu? Koda yake nima barci nayi ban dade da tashi ba ya jikin naki?”
Sauke ajiyar zuciya sabeeha tayi jin haka tace “da sauqi”
“Kin samu kinyi aikin?”
“Eh tun daxu nayi na gama” ta bata amsa.
“Toh amma ya fita kuwa? Ko yana nan? Don kinga bamuyi abuncin rana ba tunda naga basa wuni a gidan?”
Cikin sauri sabeeha tace “ya futa tun kafin na gama ma”
“Toh shiknan ma Bari mu fara shirin dinner, tashi wannan jemammiyar ku futo”
Da toh sabeeha ta bata amsa ta futa zuwa kitchen, tana futa sabeeha ta tada basira ita kuma ta shiga saka kaya.
Gaba daya ji tayi kamar batayi zazzabi ba kwata kwata hatta ciwon kafa da take yawan yi musamma first day of her monthly pp yau babu, ko me ya mata allah kadai ya sani, magana take da zuciyarta tana duban hannunta inda ya mata allura wajen har ya danyi jaa kadan.
Haka suka futo suka shiga kitchen don shirrin kammala dinner da wanda za a kai asibiti.

Hadiza kuwa bata dawo ba sai wajen karfe biyar da rabi, tana shigewa daki kuwa ta kwanta barci don a gajiya ta dawo ga wadda jamilu ya tara mata allah ya wadai.
Wajen karfe biyar da rabi ya futo cikin shirinsa fess fess, yau ya fara saka bespoke dinkunan da anne tasa aka mashi masu kyau, wani sky blue yadi, kayan sun mashi kyau sosai ba kadan ba don sun dan kamashi, ya dora da black givench slippers masu kyan gaske.
Kanshi wai kyalli yakeyi saboda gyara shi dayayi ga wani kamshi mai shegen dadi da yakeyi.
Futowa yayi yana duban agogon hannunshi, daidai compoud din gidan ya dakata yana duban main house, yanajin kamar ya shiga ya ganta.
Haka nan ya hakura ya nufi wajen motarshi ya shiga yayi reversing motar ya futa.

Bai tsaya ko’ina ba sai asibiti, yana parking ya futo daga cikin motar, as always koda yaushe idan har da mutane a asibitin nan daya gifta haka za a bishi da kallo kamar sabon gani, harya saba, mutane ba a iya ganin abu mai kyau ba wasu kallon ma kamar zasu fadi, gashi yaqi jinin irin wannan abun musamman ga mata, its a turn off for him.
Securities din dake wajen har sun saba dashi yana zuwa haka zasu mimmike suna sara mashi, kai tsaye ya nufi cikin asibitin inda aka kwantar da anne.
Da sallama ya bude kofar gaba daya duk suka juyo, duk suna zazzaune, anty fadila, nanna, anty mubina, maya, laila da hamad sai anne dake zaune tana kallonsu gaba daya taba murmushi, a saman kanta ko wani abun karafuna ne da aka saka mata.
Kamshinsa ne ya masu sallama mai dadin gaske, anne tayi murmushi tun safe yau batajishi ba gaba daya, haka ta dunga bidarshi nanna tace mata zaizo.
“Welcome tajudeen” anne tayi magana tana miqa hannunta daya tana fara a.
Murmusawa yayi ya karaso har inda take hamad ya miqe ya bashi seat din don ya zauna.
Hannunta data miqa mashi ya kama ya rike tare da kissing din hannun nata yana farin cikin progress din datake samu.
“How are you feeling anne?do you need anything?”
“Alhamdulillah deen, yau ban jikaba gaba daya”
“Im so sorry i wasn’t feeling well earlier so I decided to take a little rest”
“Masha allah that goods how are you feeling?”
“Alhamdulillah” ya amsata a natse, ahankali suke magana don su nanna basa jinsu sai murmushi kawai datakeyi ganin yanda dan nata keda kusanci sosai da yayarta, yanda suke shida anne da yanda ya damu da ita abun yana burgeta bama ita kadai ba harda fadila, kusan ma itace zata fadi yanda ya damu da anne, hidimar da yake da ita ko su yayanta basayi,saida ya tabbatar ta samu extra extra extra care din da basuyi tsammani ba, consultant dinnan daya kawo specifically saboda ita kawai ya kawo kuma har yanxu yana nan don yace sai sun tabbatar shes heal complete kafin ya koma kasar daya futo.
“Jeka gaisa da oummi ka saika dawo mugi hira”
Murmushi ya mata sannan ya tashi ya nufi inda suke zaune, tashi laila da maya sukayi suka bashi waje ya zauna kusa da nanna kamar dai yanda ya saba ya kama hannunta itama ya sumbaceta.
Suna gama gaisawa anty mubina da fadila suka gaishesa, don yanxu fadila wani girmansa take gani sosai dukda ta girmesa nesa ba kusa ba.
Mubin dake wasa a hannun laila ya tashi daga jikinta ya taho wajenshi da sauri, aiko ya daukeshi ya dora kan cinyanshi laila tace “good evening uncle taj”
Dan murmushi ya mata ba tare daya amsata ba, ta zubguri maya data kafeshi da idanu, tund aya shigo ta kasa dauke idanunta, at that point tagama macewa akanshi gaba daya ya rabbi.. ya mugun haduwa ba kadan ba, ya futa daban haka zalilka komai nashi ma, yau daya saka kaftan dinnan sai ruwan hausa fulani daya dauko daga nanna ya bayyana a jikinshi,typical classy husband material kawai.
Maido da dubanshi yayi ga mayar coincidentally ta wani kashe ido tace “hello uncle taj”
Ba tare da ya sauya yanayinshi ba ya daga mata kai kawai.
Dukda ba wani response look din kirki ya bata da za ayi bragging samun kanta tayi da shiga shauqi, shiko yau gaba daya wani irin dadi da kwanciyar hankali ya tsinci kanshi a ciki, definitely badan kowa ba saidan fatima.
Sake dagowa maya tayi suka sake hada idanu, saitaga kamar murmushi yake mata a nata illusion din, gaba daya ta rigada ta ya mace mata.
Laila ko na kallon ikon allah babu abunda take sai murmusawa, nanna ma tayi noticing irin kallon da mayar ke mashi amma bata kawo komai ba.
Hirarsu suka cigaba dashi sosai har akayi magrib, mazan suka fita, hamad dashi su kuma matan sukayi sallah anan dakin.
Suna dawowa hanad ya dubi su laila yace “ku tashi ku tafi, zanje na dawo da dinner”
“Hamadu bari mu tafi gaba daya kawai” nanna tayi magana.
Anty fadila tace “maman mubin, zaki bisune? Ko zaki jira daddy”
Cikin kunya anty mubina tace
“Ah ah zan bisu dai gwara na koma nabar su inti a gida da nanny ga dare yayi”

“Gaskia dai don dawowar daddy ba yanxu ba qila sai yakai har wajen 9, nanna zaki bisu ne ko tare da uncle taj din nasu zaku tafi?”
“Hanyarshi daban tawa daban daman bashi ya kawoni ba”
Shafa kanshi ya danyi kamar ya yaji mai tace, ya danyi smirking, well ya dan fara picking words dai kadan kadan na kalmomin hausa kodan saboda sabeeha yakeson ya koya sosai.

Maya da karfin hali ta dubi nanna tace “toh nanna zamu iya bin uncle taj? Munason mu dan kara zama”
“Ku zauna mana saiya taho daku”
Wani irin dadi maya taji aranta sosai laila ko tayi gumm batace kala ba.
Sallama nanna tayi dasu harma da anne sannan suka fita tare da hamad da anty mubina da mubin.
Suna fita dakin ya zama awkward gaba daya sukayi shuru, gashi shi bai iya wani jan conversation ba, anne kuwa daman bai dade da shugowa ba tayi barci saboda allurar da akayi mata duk bayan awa biyu.
Fadila na gyara mata duvet din da aka lullabata dashi sannan ta duba drip din da aka saka mata ganin ya kusa karewa yasa ta futa.
Tana futa laila ta dan sake ta dubi taj tace “uncle taj you look amazing in kaftan masha allah”
Da mamaki taji ya amsa ta “thanks”
Maya najin haka ta dago ta kalleshi tace “uncle taj how old are you?”
Wani irin kallo ya mata, ba tun yanxu ba yake ganin yarinyar kanta na rawa sosai, kuma daga gani zatayi raini da tsiwa shi kuma abunda yaqi jini kenan, bayason raini kwata kwata ko babba bai yarda ya raina shi ba balle yaro.
Ganin haka yasa jikinta ya mutu tace “I’m sorry if thats intrusive”
Bata gama karasawa ba taji yace “make a guess”
Gaba dayansu murmushi sukayi harma da laila ganin yau yana kulasu, laila tace “38? 39?”
Maya ta kalleta tace “dallah yiwa mutane shuru,” ta karashe tana hararata kafin ta kama habarta tace “let me guess uhmmm 35?”
Relaxing bayanshi yayi surutanshi harya fara damunshi, laila tayi saurin cewa “uncle taj who guess right?”
Bude idanunshi yayi ba tare da ya dago ba yayi pointing inda maya ke zaune.
Excitedly ta kyalkyale da dariya tace “uhm that my speciallity lol, na iya guessing”
“Uncle taj did you have a girlfri….” Laila ta jefo mashi tanbayar tun kafin takai aya shugowar fadila yasa ta guntse maganar tata, ya miqe yana duban agogon hannunshi wajen 8:30 kallon shi fadila tayi tace “zaka tafi ne?”
“Yes mami” dan murmusawa anty fadila tayi jin yanda ya kira ta “toh shikenan, ku tashi ku kuma, saida safe idan ta tashi zan fada mata ka wuce”
Girgiza kai kawai yayi ya fuce su maya da kaudi aka wani jaa mayafi akan kafada, laila ma ta dora nata aka sabida abaya tasa.
Kallonsu fadila tayi tace “ku kama kanku bana son shirita”
Sallama suka mata suka fita.
Yana kunna motar suka karaso, maya tayi saurin bude gidan gaba ta zauna laila kuma ta zauna baya.
Ko dubansu baiba yayi reversing motar suka fita daga asibitin.
Tafiya sukayi mai dan tsayi kadan, maya nason yin magana amma ganin yanda yanayinshi ya sauya gaba daya yasa taji tana shakkarsa.
Karahe dai dataga wannan is an opportunity for her wannan Yasa tace “uncle taj..can you please buy us some bobble tea and jelato?”
Bai kalli inda take ba kuka bai bata amsa ba saida ya wani jaa aji harta fidda rai kafin yace “set the map to the location” ya mata nuni ga screen din motar shi.
Maya fa duk a tunaninta yanda yake kulatan nan ya kamu ne a ganinta, wannan yasa taketa faman zaqewa, danna screen din tayi ta saka map sannan suka wuce wajen ice cream din, in less than 5 minutes suka karaso don babu nisa, wani capitative waje ne ta kawosu na masu kudi don motocin dake wajen saina yayan wane da wane,yana parking suka fiffito hardashi.
Yayi gaba suna biye dashi a baya, dadin wayewa kenan, zaka rantse ba yau ya fara zuwa wajenba, tafiya yake majestically kamar basarake.
Ciki suka shiga mutane na zaune samari da yan matansu anata shanawa, abun burgewa, suna shugowa kuwa kallo ya dawo garesu, ko ince gareshi,hadaddun matan nan haka suka dunga binshi da mayun idanunshi niko na taya sabeeha da lahaula tuff tuff karsu ci ye mata shi lol😹directly wajen order suka nufa ya dubesu yace “take what ever you like”
Maya tace “wow kasan zuciyanta,“
Haka suka fara order daman suka gasu yayan madara yayan class saida suka gama maya tace “what will you like to have uncle taj?? Would you like me to order for you? I promise you will love it”
Shuru yana kallon menu din, kamar mai tuna wani abu ya dago ya kalli wanda ke karban order din yace mashi “bubble gum and strawberry,”
“Toppings sir?” Mutumin ya tambayeshi.
“Just berrys”
“Okay sir your balance is 78,900”
Hannunshi ya sanya cikin aljihun rugarsa ya zaro wata hadadduyar lether wallet ya bude sannan ya fiddo da black card dinshi ya miqama mutumin, su laila basu lura ba saida mutumin yace “sir i’m sorry but this card …..”
Cikin husky voice dinshi ya dakatar da mutumin yace “that unlimited world wide currency black card”
Shidai mutumin nan bai taba ganin irin katin ba haka nan ya tura cikin pos dinsu,aiko yana sawa kawai yaga ya tambayi currency’, cikin sauri ya miqa mashi ya saka sannan ya danna pin kudinsu ya fita.
Maya ta saki baki beneath her breath tace “wow…this is luxury” aranta ko babu abunda take ayyana sai ay gata ta zama matarshi, zata fantama, ya da taga dama, the life she has been dreaming for, ada tana ganin babu mai kudin dazaiyi satisfying dinta yanxu ko ta gani.
Suna tsaye suna jiran a gama packaging order su kamar da wasa sukaji sallama, kwata kwata hankalinshi na kan wayanshi baima san anayi ba, maya da laila suka juyo din ganin waye.
Wata kyakyawa ce ajin farko don agaskia ba yarinya bace don zatayi 26 haka, looking peng gata fara sol kuma cikin shigar kirki take bata banza ba don atamfa ne a jikinta hannunta rike da LV baka tasha hand chains masu kyau.
Fuskanta babu kwalliya amma tana da kyan fuska.
“Hey!!”
Maya ta hade tai sai laila ce tace “hello!!” Suka wani kareshi don ya juya masu baya.
“Excuse me i will love to have a conversation with your brother”
Dariya maya ta danyi ta kalleta sama da kasa sanin bayaji hausa yasa tace “har kin isa kizo gabana sannan kice na matsa maki zakiyi magana da mijina? Kina hauka ne?”
Da mamaki budurwar ke kallo su don ta dauka kannensa ne.
“Well ku biyu na gani ko akwai sauran biyun ne a gida?” Maya taji wani maqoqon abu a maqogoronta zatayi magana don harta harzuka bataqi taci uwarta a wajenba dukda kamar ta girmeta laila tace “rabu da ita dan Allah,“
Tsaki budurwar tayi don tanada girman kai sosai gashi taji she felt embarrassing don akwai idanun mutane wannan yasa ta bar wajen nasu.
Karban order yayi ya juya sukabi bayanshi maya na gaba laila na baya har zuwa mota.
Basu suka iso gida ba sai wajen karfe tara, suna isowa yayi parking suka jarba ledansu sukayi mashi godiya, maya sai yima laila take signal tayi gaba itako ta kasa kwashewa, baibi ta kansu ba yana kashe motar ya dauka ledan icecream dinshi ya wucesu.
Maya ta dubi laila tace “ke wallahi kinada matsala, kinata maki signal ki tafi kin wani tsaya”
Tsaki laila tayi tace “au ni nasan me kike nufi naga kina tura baki sainayi tuannin ko duk cikin salon luring dinshi ne” tana fadin haka tayi gaba abunta, daurama kai wahala, kiri kiri kinsan yafi karfinki amma ki dage akanshi, sai yanxu ma ta kara tabbatar da maya fa tayi gaba sai a hankali kuma.
Part dinshi ya shiga yana bude kofar kamshin abunci ya mashi sallama, daman da yar yunwarsa don tun coffee dayasha bayajin yasha wani abu, aje ledan ice cream din yayi ya nufi wajen abunci, ganin yanda suke a jera kuka yana budewa yaga turiir ya gane bata dade da kawowa ba.
Wannan yasa ya juyo zuwa parlor ya dauka ledan ice cream din ya futa daga part din.
Main part ya shiga a natse, kamar dai koda yaushe babu kowa a kasan ba tare da wani tunani ba kawai ya nufi kitchenyana fatan ya ganta anan.
Anatse yake tafiya harya karyo coner wajen kitchen din yana dago da fuskanshi kuwa daga nesa ya hangita tsaye, wani irin sanyi yaji ya suake ajiyar zuciya anatse, abunci takeci a natse akan island ta dora hannunta daya ta dafe wajen ta juyama kofar baya.
Takowa ya somayi ahankali ya shugo kitchen din, bai yarda yayi making any sound ba dazaisa ta gane don kitchen dinma dai yana da girma sosai ba kadan ba, yana shugowa ya dubi left and right ya hango switch din dake gefe, hannunshi yasa a wajen ya kashe ligjt din take wajen ya koma duhu dumm, cikin furgici ta juyo ga wajen kofar ayko take taga mutun tsaye don ga shadow dinshi a wajen saboda hasken dake haskowa, bata gama processing ko waye ba ya rufe kofar ragiwar hasken dake dan futowa ya dauke, ya soma takowa ahankali, kokarin gudu take zuwa ga kofar backyard yayi saurin cin mata kamar yana iya gani da wannan duhun, “hey!!! Its me.. “
tana jin muryarshi amaimakon ta natsu saita kara burkice “innalillahi wa inna ilaihi rajiun na shiga uku wanna.,Wani irin abu ne har nan zai buyoni,idan aka shugo fa aka ganmu”
Kamar yasan zatayi magana da hausa yayi setting wayarshi zuwa ga translator tana magana kuwa wayar tayi translating yaji kuma ya maida wayar aljihunshi.
Zata iya cewa bata taba jin ya murmusa ba kaf zamanta dashi bayan ya samu lafiya sai yau, lokacin da bashida lafiya babu wanda ya kaishi fara’a.
“Prevention is better than cure,how are you today..prin..cess”
Cikin sauri ta dago kamar tana kallonshi, da mamaki sosai akan fuskanta don yana ganin fusknta saboda hasken wayanshi daya aje gefen island.
Tanason yin magana amma ta kasa sabod akaryayi translating, amma shes in so much shick, tanajin anya taj din data baro ne a saudi kuwa why the sudden change? Kai abun ya bata mamaki, shine kuwa? Why is he soft towards her? Was he not that cold? Was he not that harsh taj daya tsani ganinta ma ? Yake jin haushi auren su? Amatsayinta na yar aikinsa?.
Tana cikin tunani kawai taji lebenshi a kumatunta yayi pecking dinta “i missed you alot”
Wani shock din ta sake shiga ta kasa daina kallonsa, “are you surprised?” Girgiza mashi kai tayi kamar wawuya yace “hmm looks like were are on the same page right? Bibi..”
Tana jin haka tayi baya hartana bigewa da island tace “wash..”
Cikin sauri yace “sorry sorry…”
Yana fadin haka ya sanya hannunshi ga kugunta ya dagata chak ya azata ga island din ya zamana tsayinsu yazo daidai ya jawo ledar icecream daya shugo dashi ya bude ya zaro jelato din ya miqa mata, kauda idanunta tayi ya sake kaiwa wajen fuskanta ta kauda idanunta ganin haka yasashi ya soma sha, juyowa tayi ta kalleshi da mamaki, ta rasa meysa yake mata wannan abun, yanxu tama rasa yanda zata fara yi mashi, duk karyata kanta da takeyi yi yakeyi kamar bai san tanayi ba, ya kafe itama ta kafe,
Turashi ta somayi tana kokarin sauka ya matso tsakankaninta ya rike hannunta daya yace “shiiii, sit still before i do something else” tanajin haka ta kama kanta don da karfi yake magana kowa ma yaji kenan ko a jikinshi, ji tayi kamar tayi kuka ta rasa me zatayi, tsoron magana take kar ajiyo su don anty rabi zata iya shugiwa anytime.
“Sir please this is not right,”
Wani irin wahallaen kallo ya mata mai kashe zuciya da shanyayyun idanunsa baice komai ba ta sake cewa “this is haram islamically,you are not my muharram, touching my body or my hand is a grave sin, you have no right to do that just because i am your maid, this ia disgusting, allah said who so ever did that will be punish drastically, do i look like someone that givee her body to anyone? Do i look lust to you? Why are you doing this to me” ta wani fashe da kuka, baiyi wata wata ba icecream din dayake bakinshi ya hade da nata bakin ya tura mata, yanda ya hada da halshen ta dole ta shanye lokaci guda daga nan kuwa yabita da wani zazzafan kiss.
Hankali a tashe ta soma tureshi kamar zasuyi dambe, gaba daya ya tafi yaui nisa bayajin kira, garin buge bugenta taba kokarin dambe dashi haka ta ture plate din da takecin avunci daci, ta fara kokarin cike bakinta don hanashi access shiko ya kamo hannunta gamm sosai ice cream din ya soma diga a hannunta don narkewa yakeyi, ganin suna neman rasa nunfashinsu yasa ya cire bakinsa daga nata, adaidai lokacin nan hannunta taso dagawa saidai yajishi akan fuskanshi donta harzuka sosai kawai sukaji takun tafiya, hankali tashe ta soma girgiza kanta sai hawaye, ta fara innaliliahi wa inna ilaihi rajiu, ganin hankalinta ya tashi sosai ya sashi miqa mata ice cream din hannunshi yace “shii…hold on to this “ karba tayi da hanzari ya sungumeta da hannu daya ya dauka wayanshi ba tare da yabi takan abubuwan da suka watsar ba ta kofar backyard daya gani ya bude ya fuce.

Suna ficewa hadiza ta bude kofar, tana budewa taga duhu, tsaki tayi tashinta kenan daga barci yunwa ta ciyota, hasken ta kunna kafin ta dubu kitchen din, ganin tsakiyar kitchen din a watse ta doka tsaki ta wuce wajen diban abuncin su a kuka tana ganin kadan yayi saura ta doka ashariya, “yan bura uba marasa mutunci, ci kamar jakai maimakon su ragemi da dan saura shine suka barni da ragowar tukunya mteww”
Tana fadin haka ta dauka cooler din ta futa dashi, tare da banko kofar.
Tana tafiya sabeeha ta sauke ajiyar zuciya, suna jingine da bangon backyard din ya kareta, zaka rantse babu kowa agabanshi don ya rufeta ruff gaba daya, dauke idanunshi yayi daga kofar ya maida ga sabeehar ganin yanda kirjinta ke sama da kasa jikinta na rawa sosai gashi har zuwa lokacin hawaye take “shes gone” ya furta hakan yasa ta saki hannunta ta fashe da kuka tana dukan kirjinsa har ranta.
“Why are you doing this to me why? Why?? What it amma saw us? What kind of impression are you going to leave me with, how can i expalin to her, i am begging you, please and please leave me alone, i don’t know who you are who what i ever did to you to deserve this”
“That’s your mom???” Ya furta ahankali da mamaki sai kuma ganin yanda ta rikice kawai saboda taganta.
Tsaida hawayen nata tayi ta dubeshi tace “wallahi daga gobe bazaka kara ganina ba a gidan nan ba balle ka cigaba da min wannan Iskancin, gwara ma naje mama tamin auren kawai na huta da wannan bala’in”

Tana rufe baki kawai translator dinna ta mashi translating, daman automatically takeyi yanda yayi setting dinshi up, aiko yana jin abunda ta gama fada take yanayinshi ya sauya gaba daya, ya dubeta da kyau saida gabanta ya fadi ganin gaba daya ya sauya kamar bashi ba, har wani jajaja yakeyi jijiyoyin kanshi suka futo rudu rudu ya wani runtse idanu ya bude yana kokari danne anger dinshi, idanfa yayi fushi shi kanshi yasan baya iya controlling kanshi kwata kwata.

“Don’t you ever ever think of getting married to anyone ever again in your life,“

Yanda ya nuna bacin rai haka ta nuna nata rai a bace tace “why???? You have no right or say on my life, cause you’re no one to me,”
Ayfa wannan magana datayi ba karamin kunnashi tayi ba, anger level dinshi yakai wajen 90,
“I do have a right on you, and i have the right that no one in this entire world can intervene when it comes to you!!!!! Cause you’re mine! Fatima..you are mine!!!”
Wata iriyar bazawarar dariya tayi tana kallonshi, tana hango wani abu waishi kishi da boyayyan abu a tattare dashi wanda zata iya fasaarashi da so, amma kuma bata jin wannan zai taba kasance gaskia, taj bazai taba sonta ba evwn in her wildest dreams, that’s impossible yafi karfinta nesa ba kusa ba.
Zadai ta iya yarda da kishi shima dai bataga dalilin da zaisa yayi kishinta ba yanxu don babu wata alaqa a tare dasu, aure ne kuma yanxu babu shi don ya tsinkeshi tun kafin ya koreta ma.
“How did I become yours? How????? Toh bari kaji, wallahi wallahi babu abunda zai hanani yin aure, da in zauna ina ganinka gwara naje chan na auri koma waye…”
Jikinsa ne ya mutu ganin da gaske take, idan aka zafi da zafi suka hadu babu abunda zai haifar sai matsala gwara shi ya sauko kawai gashi bayason ya fada mata aurenshi na kanta har zuwa yanxu saidai yanda yaga reaction dinta ayanxu da yanda ta kafeta yasashi ya tsorata, ga wani irin kishi dake turnikeshi jin kawai tana maganar zata auri wani bayan kuma akwai auransa akanta kaii ina bazai yuwu ba.
Murmushi yayi wanda yasa ta shiga rudu, yanxu ta ganshi cikin bacin rai musmaman maganar datayi mashi lokaci guda kuma ya sauya kamar bashi ba? Anya lafiyarsa kalau kuwa ta tambayi kanta ya maidata kamar wata wawiya.
Hannunta daya bata icecream ta rike kafin ya sungumota ya kalla ganin icecrem din yana dripping,hannnun ya jawo daidai bakinsa kawai ya soma lasar yatsunta kamar lolipop, take ta nemi natsuwarta ta rasata gaba daya, kafafu suka fara rawa, saida ya lashe tass kafin ya karbi ragowar dake cone din yasa abakin shi, ya shanye tass,kallonshi take kamar wata wawiya, wallahi saida ta bashi dariya daga reaction dinta ya guntse dariya ta hanyar smiling kawai, how can someone not fall for his innocent face? Ya Allah.
Dab da ita ya matso ya sakala kanshi tsakanin wuyanta ya aje habarshi a wajen yana sauke mata nunfashi mai zafi yace “Da aurena akanki zaki je ki auri? Dama anayin aure kan aure ne ban sani ba?”
Ay tuni ta nemi shauqin da jikinta ya fara ta rasa, the got the shocking of her life at the moment.
Yana gama fadin haka yayi kissing gefen wuyanta, tayi saurin runtse idanunta sanyin lebbanshi har jijiyoyinta tajisu.
Matsawa yayi daga jikinta kafin ya hade rai soaai kamar bai taba dariya ba yace “the your little game ends here? If you insist on being stubborn you will leave me with no other option but to tell mama about us”
Yana fadin haka ya juya zai bar wajen hankali a tashe tasha gabanshi.
“What are you talking about? Taj”
Kai yanda ta fadi sunan sa har ranshi, saiyaji dama da didi ta kirashi dashi yafi son jin sunan a bakinta.
“Yea you heard me right…you are my wife and I’m your husband according to the sunnah”
“No karyane wallahi, karyane” ta fashe da kuka sosai.
Murmushi yayi ya kama kumatunta, shi abun dadi yake mashi wallahi, he find yanda take tsorata dashi attractive, abun dadi yake mashi sosai.
“Wow…seem like the fatima that i know is back already huh?? Kin bani wahala, why where you stubborn? Gashi baki iya karya ba”
Ay saita sake fashewa da kuka sosai, kamar ta dora hannu a kasa ta kwala ihu sosai haka takeji.
“Sabeehaaa…sabeehaa” basira ta kwalo mata kira
Cikin gaggawa ta juya harda leke ta taba ta bayanshi gabanta na faduwa ta nufi kofar, basira ta kalleta ganinta a furgice tace “yayadai? Kukan me kikeyi?”
“Abu ne ya fada cikin idanu na”
Yanda ta fada tana karkarwa kana ganinta kaga mara gaskia
Tureta basira tayi ta leka backyard din ganin babu kowa yasa tace “nanna tana kiranki”
Tana fadin haka ta wuce abunta sabeeha ta duba taga ya tafi gabanta baibar faduwa ba ta wuce cikin gida , wanke fuskanta ta fara yi kafin ta wuce sama wajen nanna.
Da sallama ta shugo part din wajen karfe homa ta girfta sosai.
Nanna na ganinta tace “shugo mata yarinyar kirki”
Sunkuyar da kanta tayi kasa ta kasa kallon cikin idanun nanna ba kamr da ba har wata kunya kunya taji tazo mata.
Har kasa ta duqa nesa da uga tace “nanna ina wuni ya mai jiki? Allah yasa kaffara ne”
“Jiki da sauqi bakuzo dubiya ba anne nata tambayarki”
Da mamaki sabeeha ta dagi tace “allah sarki, inaso naje wallahi toh anty rabi batace zamuje bane shi yasa”
“Karki damu gobe da safe saimuje tare, kafar tawa ce ta dan motsa shine nasa a kiraki kidanmin yar tausar nan muyi hira kafin karfe sha daya”
Dariya sabeeha tayi harta dan sake tace “toh nanna”
Matsowa tayi ta farama nanna tausa suna hira nanna ta tambayi meya samu idanunta tace abune ya shiga idanunshi shiyasa.
Sun wuce wajen 11:30 suna hira har taj ya kira sukayi sallama sabewha najin yanda yake tambayarta ko akwai abunda ke damunta tace mashi ah ah, da alamu dai ya samu cikin farin cikin datake mashi fata, uwar daya rasa a baya allah yayi yanada rabon samunta ayanxu.
Ganin dare yayi soaai yasa nanna tace mata taje ta kwanta da safe ta shirya zasuje asibiti tare cikin murna sukayi sallama.
Tana futa kasa ta sauko, damuwarta data mance ta dawo mata, haka ta koma daki ta tadda basira ta kwanta abunta, kwana tayi dai a zaune saboda maganganun da sukayi da taj, a karshe dai taqi yarda da abunda ya fada dukda deep down tasan it can be possible aurensu na nan tunda bai furta ya saketa ba kuma bata gani ba a rubuce kuma sakin na hannunsa idan baiyiba that means babu sakin kenan, innalillahi wa inan ilaihi rajiun, idan ya tabbata da auransa akanta ya zatayi? Me zata fadama mama? Me mutanen gidan zasu dauketa dashi kenan? Don tasan dai babu wanda zai amsheta hatta nanna datafi kowa kusanci da ita.

Bangaren taj ko sumul yayi barcinsa cikin kwanciyar hankali, har wani irin nauyi nauyi yaji kamar ya sauke akanshi, wani irin dadi yakeji, he never knew shawo kanta will be this easy.

Washe gari da safe tun bayan asuba suka tashi suka fara gyrae gyare koda wasa batabyarda ta tafi dakinsa ba, allah yaso breakfast ma anan sama yayi, wajen rabi taji wai a sama yayi wajen nanna.
Suna gama girki rabi tace mata “kike kiyi wanka nanna tace zakuje asibiti yanxu ko?”
“Eh” sabeeha ta bata amsa.
Fita tayi ta wuce dakinsu tayi wanka ta saka atamfa pink dake bata da babban mayafi wannan yasa tadora open abaya akai sannan ta yafa mayafin abayar ta fesa dan turarenta ta futo.
Dan normal takalminta tasaka mai kyan gaske ta futo kitchen, rabi tace “yarinya badai kyau ba, wallahi zamuyi kudi idan kika samu muji, kefa kalar masu kudi ce”
Dan murmusawa sabeeha tayi itafa yanxu maganar aure ma ba kaunar ji take ba kwata kwata wallahi.
“Dauki warmers din basira ta biyoki da sauran nasan yanxu hajiya zata sauko.
Dauka tayi ta futa ta gaban gida a tunaninta zataga driver a compund ko hamad taga babu kowa, tun futowarta ya hangota don futowarshi kenan shima, ya kafeta da ido, batasa anything special ba amma fa tayi kyau naturally, takowa yayi har taakiyar compound din suka hada idanu shida ita, ta dauke nata ta wnai juya mashi baya sai kawai yayi murmushi kadan shi kanshi yasan cikin kwanakin nan yana murmushi sosai abunda bai cika yi ba, tana tsaye basira ta futo itama da warmer, tana ganinta tsaye tace “ya kika tsaya”
Dagowa basira tayi bata gana mata magana ba ta hangoshi, tuni cikinta ya kada ta waniyi saurin aje warmers din a gaban sabeeha tace “allah ya bada sa’a saikun dawo”
“Ina zaki basira” sabeeha tayi magana kamar zatayi kuka”
Juyowa yayi bayan ya bude booth ya soma takowa inda takeyi ta soma yin baya hankali a tashe yana isowa ya wani hade rai kamar bai taba dariya ba ya karbi warmers din hannunta “pick up the remaining ones” yana fadin haka bai sake kallonta ba ya wuce, yabda yayi maganar babu wasa wannan yasa ta duka ta dauki wanda basira ta aje sannan ta tunkari motar.
Tana karsowa ya karbi na hannunta ya saka a booth din such a gentle man, yana rufe booth din yayi juyawarahi zuwaga wajen driver seat, yana shiga daidai nan nanna ta futo, matar nan badai kyau ba, ta hadu ta gaji da haduwa ba kadan ba.
Tana karasowa ta dubi sabeeha tace “kunata jirana ko yarinyar kirki”
Futowa yayi don ya hango nanna daga nesa ya tsaya jikin motar, sabeeha ta duka har kasa tace “ina kwana nanna”
“Lafiya lau tashi mana fatima nace ki daina duqamin kinji ko”
Sunkuyar dakai tayi nanna ta dubi kayan jikinta duk sun dan kode wallahi sai taji babu dadi kwata kwata kuma yau dai insha allah zasu biya ta saya mata sabbin kaya musamman abaysa don sunayi mata kyau sosai tunda utama fara ce sosai kamar halfcast.
“Sabahal khai oummi”
“Sabahal noor son, how was your night?”
“Hamdullah ya bata amsa kafin ya bude mata kofar gaba, tana shuga ya rufe ya dubi sabeeha, wani irin kallo ya mata mai wuyar fasaara dayasa ta wuce gaba ta bude kofar ta shiga ta zauna.
Tana zama ya dubeta yace “fasten your seat belts”
Duk a kidime take wannan yasa ta fara jan belt din ta cije, yana kallon yanda take struggling ba atre da wnai tunani ba kawai ya matsa kusa da ita don tana iya juyo nunfashinsa da azababban kamshin ya jawo belt din ya saka mata daidai nan nanna ta dago sai kuma ta sauke idanunta ta dan murmusa
Kallon mirror yayi ganin hankalin nanna na wayanta yasa ya kamo hannun sabeehar, cikin hanzari ta dubeshi, duk yabda taso ta kwace hannunta kasawa tayi ya kashe mata idanu daya dukda yanayin fuskansa na nan yanda ta taddashi dazu babu wasa.
Gabanta na faduwa haka yayi reverse ya futa daga gidan, saida yaga nanna na neman dagowa tukunna ya saki hannunta ya maidashi ga titi.
Karatun kurani ya saka masu sunaji cikin natsuwa ba hayaniya har suka iso asibitin.
Yana parking ya futo ya budema nanna ta futo sabeeha ma ta futo.
Cikin securities din wajen yasa suka zo suka kwashi warmers din sannan suka bisu har cikin asibitin.
Suna shiga direct bangaren anne suka nufa da sallama, aiko tana zaune tanabata dade da tashi ba, ba karamin dadin ganin su taji ba, sabeeha sai faman susunne kai take kamar munafuka.
Kunya duk tabi ta lulubeta haka kawai, da anty fadila zata wanke kwanukan jiya haka ta karba ta shiga kitchen ta wanke don ko wanne daki akwai toilet akwai kitchen da fridge harda faucet na wanke wanke, da closet duk akwai.
Fadila ba tun yanxu take yabin halin yarinyar ba don tanada natsuwa sosai ga kamun kai sosai, gaba daya opposite din uwarta ce, koda suna waya da bahijja haka take fada mata, gaba daya yarinyar kamar ba jinin hadiza ba.


Yaufa maya tun safe ta farka tana allah allah taji ance uncle taj zaije asibiti tayi siezing wannan opportunity din ta bishi, jiyafa ko barcin kirki batayi ba kwata kwata.

Misalin wajen karfe sha biyu ko saigasu maya da laila sunzo wannan karan da anty laila akazo,tanata mita jiya daddy ya kawo abty mubina itama yau wai saiya kawota shi kuma aikin office ya mashi yawa, daman itadai badai kishi ba dukda itace babba.
Maya nayin arba da sabeeha taji wani irin maqoqon bakin ciki aranta, gaba daya taji murnarta ta koma ciki, farin cikin datazo dashi ma na zuwan mummynta da dadynta da zasuyi basu fadama kowa ba sai ita ya kau.
Ta tsani sabeeha wuth so much passion ba kadan ba ji take kamar ta chaka mata wuka ta huta, ko ta kau da ita kawai, wannan kiyayya dai ba a cewa komai.
Bata gama tsanar sabeeha ba saida ta lura da duk dagowar da zatayi saitaga uncle taj na kallon kitchen kuma tasan sabeehar na kitchen din.
Fargabarta daya bai wuce allah yasa wannan almurar yarinyar batayi captivating dinshi ba, son wallahi zata iyayin komai akanshi koda kuwa kisa ne hmm.

Anty fadila ce tayi breaking silence din kowa tace “bahijja da majeed fa suna hanya,”
“Hanya kuma?” Nanna tayi magana,
“Eh wallahi nanna 4days ago mukayi magana
tace min tafiyar kamar bazai yuwu ba don bata samu leave ba sai shekaran jiyan da daddare ta samu shine sukayi booking flight jiya daddare suka taso, allah yaso ma akwai flight din england to nigeria, ay inaga in the next hour zasuzo”
“Masha allahu…allah ya akwosu lafiya”
“Ke maya bakuyi waya da mummynki ba?”
Fadila tayi magana, gaba daya hankalinta yayi nisa taj kawao take kallo kuma kowa ya kura da hakan, shes so lost in her thoughts, allah kadai yasan meke running a mind dinta, shi kuma wani waje daban yake kallo shima kuma, adaidai lokacin sabeeha ta fito duk sai kowa ya i inda yake kallo da kallo, sabeeha na ganin idanu akanta gaba daya ta rikice, nanna tace “zoki zauna ki huta fatima tunda mukazo kike aiki”
Samun wajen tayi ta zauna, anty laila ta mata wani irin disgusted kallo ganin ta zaune kujera inda kowa ke zaune, bata kaunar aiki matar itama irin matan nan ne masu cewa kowa ya tsaya a matsayar shi, itamafa ba yar masu kudi bace ba amma akwai fadin rai.
Shiyasa aduk family din kowa yafi ganin kirkin anty mubina babu ruwanta ita kowa nata ne.
Hamad ne ya sake shugowa da mamaki ya hango sabeeha, itama ta kalleshi suka hada idanu, smiling ya mata itama ta mashi akan idanun taj, take ranshi ya baci soaai ay baisan yanada kishi irin balayayyen kishi ba sai yanxu, kamar ana boiling dinshi haka yakeji.
Karasowa hamad yayi gefen da sabeeha take ya kaleta yace “how are you fatima!”
“Im fine ya hamad how are you too?”
“Alhamdulillah”
Kasa kasa suke magana don ba a jinsu amma taj kamar a kunnenshi don ya basu attention sosai, baisan cewa she will be this childish ba sai yanxu wato duk abunda ya fada mata ko a jikinta kenan? Batama yarda ba kenan? Aiko zai nuna mata a zahiri bawai a baki ba.
“Hamad zoka tafi airport ko? Karsu iso suyita jiranka”
“Okay mami” ya fada tare da wucewa
“Maya bazaki bisa ba?”
Kai tsaye tace “kaina na ciwo”
Nanna tayi shuru bata sake cewa komai ba,anty laila ta kalleta ganin yanda ta sauya lokaci guda, ta gana karantar maya gaba daya so tasan yanayin datake ciki, kuma daman ta fada mata tana son taj, saidai batasan meya kawo bacin rabta ba, kodan bai kulata ba data gaishesa da sukazo.
Futa hamad yayi bai tsaya ko’na ba sai airport yana isowa cikin minti talatin sai gasu sun fito, gwanin ban sha’awa daddyn maya yayi wani irin kyau yayi kiba daman gashi fari tass, ya tara saje baki wulul sai dan farin gashi daya soma futo mashi na manyanta dukda ba wani girma yayi ba sosai.
Bahija ma baku ganta ba dagwas dagwas, tayi kyau sosai tayi kiba, kana ganinsu kaga healthy couple. Cikin fara a hamad ya karaso ya miqa ma dady hannu, sai faman susune kai yake yace “welcome back daddy, anty ya hanya”
“Hamadudu, hanya alhamdulillah, kanata jiranmu ko?” Dady ya fada
Anty bahijja tace “wurin daddy zaka fara zuwa kabar uwarka anan ko?”
“Sorry mummy na ya hanya”
Dariya tayi tace “alhamdulillah hamadudu ya jikin anne? Ina baby?”
“Alhamdulillah da sauqi, tana aisibitin”
“Maysa batazo ba?”
Dadyy ne ya dubeta ya mata wani irin kallo dayasa tayi shuru kawai, daga isowansu ta fara.

Mota suka shiga hamad yasa kayansu a booth sai asibiti.
Cikin minti talatin suka iso asibiti, hamad na parking suka fito gaba daya ya jagorancesu ciki.
Shi ne ya bude kofar ya shiga fadila tayi saurin miqewa taba gyara hijab dinta nanna ta fara murmushi “lale lale marabaaa tafiya babu sanarwa”
Rungume bahijja fadila tayi cikin fara a tace “sannunku da suwa sannunku”
Maya na ganin mummy ta tashi a guje ta tafi ta rungumeta “mummyyyyyy naaaaa”
“Oh my baby” haka suka fara runguke rungume dady na daga tsaye yana kallon ikon allah, yasan sunyi kewar juna amma ya kamata ace bahijja ta aje wannan soyayyar datake mata ta fara duba mara lafiya,.
Murmushi nanna. Tayi tana kallonsu gwanin shaawa tace “shugo my inlaw bismillah sun tsaye rungume rungume an barka tsaye”
Cikin girmamawa ya karaso ciki aka bashi waje ya duka har kasa ya gaishe da nanna ya mata ya mai jiki.
Sai a lokacin bahijaa itama ta duka ta gaisheta maya na maqale da ita suka tambayi ya mai jiki nanna tace “yanxu nan ta fara barci kuwa dake ana mata allura duk bayan 2 hours”
Gabanta suka karasa dady ya mata adduar kaffara da samun lafiya.
Bahijja suka gaisa da anty laila daketa faman yake, ba tun yanxu take shawar tafiya kasar waje ba tayi mitar harta gaji, ita so take ya sameer ya barta achan kawai ta zauna saiya karata da amaryarsa anan da danginsa tunda sunfi santa.
Kwata kwata basu lura da sabeeha ba data rakube gefe saida aka gama gaishe gaishe ta dan duka tace “ina wuni hajiya ya hanya”
Juyowa sukayi daga dady har bahijja suka kalleta, bahijja tace “lafiya lau, wacece?”
Shuru kowa yayi anty fadila ce kawai tace
tace “yar hadiza ce”
Sai a lokacin bahijja ta ganeta wallahi garta manta da mai kama da ita gaba daya, yarinyar datayi mata satar bangle din da daddy ya saya mata, above all yar hadiza hmm.
Tunda ta dago daddy ya kalleta ya sake kallonta, ya kasa dauke idanunahi a kanta sai yaga tana mashi kama da kakarsa ta farko wadda tafi kamanni da babansa sosai, kuma kamar bawai haka kawai ba irin azababbiyar kama sosai, kuma shima yana kama da baban nashi saidai kawai banbancin launi dayake dashi.
Kallon dadyn maya tayi tare da matsawa kusa dashi ta rungumeshi tace “dady naa… i missed you so much dady”
Rungumeta yayi kawai saboda idanun jama’a badan komai ba khma he cant lie he missed her alot shekara uku ba wasa ba.
“How are you my princess”
“Lafiya lau daddy kayi missing dina?”
“Yes of course princess”
Ya fada tana riko hannunsa tsabar murna, gata dai ana gani ansan yar gata ce wajen iyayenta, don soyayyar maya ba karama bace a wajensu, shes like a treasure shiyasa so din ya rufewa mahaifiyarta idanu.
Sabeeha tund ata masu kallo daya ta sauke idanunta ganin yanda maya ke jefo mata harara,hawaye takeson yi amma ta hana kanta, bata taba ganin soyayyar uba da ya ba sai yau, saitaji babu wanda ya kaita maraici saboda bata taba experiencing haka ba ko sau daya.
Saitaji inama itace Maya ga uwa ga uba, bayan wannan uwa uba ga dangi a zagaye da ita.
Tashi tayi salaf salaf ta wuce ta gabansu dady ya bita da kallo, yanda take tafiya ma kamar na NANA (kakarshi kenan)

Tana futowa ta zauna anan reception hanad daya lura da ita yabiyo sahunta ya zauna dan nesa da ita ya fara janta da hira..

Yana cikin motarshi ya amsa call din salim, inda ya shaida mashi sunan asibiti da yake don yazo, yana isowa kuwa sunkai wajen awa guda a cikin motarshi suna magana yana nanata abunda salim ke fada mashi, yanajin kamar abun ba gaskia ba.
Da farko dai salim ya shaida mashi yanda sukayi da jamilu.
Daman ya shaida mashi cewa wanda fa mamanta ke son aura mata dan balaja’i ne, a iya binciken dayayi akanshi.
Wato jamilu kwaro ne, wayar jamila ya dauka ya dauki number dahiru sannan ya kirashi yana dagawa ko bayanin koshi waye baiyi ba yace mashi ya tura account dinshi, dahiru ya dauka irin scam dinnan ne aiko yace bari ya gwada sa a don tun safe gari yakesha yau kasuwa bataci ba aiko jamilu ya tura mashi zunzurutun dubu hamsin, jiki na rawa dahiru ya kira back, jamilu na dagawa dagiru yace “waye kai bawan allah? Haka kawai ka turan dubu hamsin karkace in maidota don wallahi ta shugo kenan ko kai dan mafiya ne saidai ka shanyen jini”
Dariya jamilu yayi yace “zaka samu abunda yafi haka kai daga kan nera dubu dati har zuwa dubu dari uku zan baka abunda yafi haka ma kawai so nake ka fada min abunda nakeso na sani”
Dahiru najin haka yace fadi koma menene ni dahiru akan kudi babu abunda bazan iyaba.
Take ya jefo mashi tambayar yanda akayi ya san hadiza da jamila, daghiru fa shika shege ne haka kawai bazai saki baki ba wannan yasa yace meysa kakeso ka sani.
Jamilu daya lura dahiru dan tasha ne tuni ya mashi barazana, “ka fada min tun muna ta arziki nima wannan ce hanyar samun arziki na inna samu mu raba don zai uya kiwa wajen miliyan ma yasin”
Dahiru najin haka yace chap bude kunenka.
Nan ya soma mashi bayani, “kai wallahi munyi zaman anguwa daya dasu ne kawai munsan juna don harka ce ta bariki, shine hadiza zata aurar da yar data tsinto zan taimaka mata”

“Tsintota kuma?? Ba cahnzota tayi ba? Dahiru najin haka yasan koma waye wannan yana gab da rafko sirrin su yayi saurin cewa “kai inji wa tsuntarta tayi, ba yarta bace, a titi ta tsinceta nake fada maka”
“Amma tasan iyayenta?”
“Ah ah wallahi neman kudi fa take da yarinyar naji ance kwanaki ta turata aikatau kamar ma yawo iskanci yarinyar ta dungayi a chan kasar waje” jamilu ya kama haba,“kai baka ganin akwai wata kiyayya taakaninsu?”
“Kai kuwa ya za ayi taso yar da ba tata ba? Ay bazai yuwu ba, babu uwar da zata bawa dan balaja’u riqaqqen dan iska kamar ni, harfa cutar aids ce dani”

Jamilu najin haka yace toh hikenan nagode yana kashe wayar ya bawa mai computer na anguwarsu yace ka fitar min da record din dan allah ka turawa wani na rubuta gidan kudi, aiko take ya turama salim dayayi ma saving da gidan kudi.
Yana turama salim shine ya kirashi ya shaida mashi harda number dahirun ma ya tura mashi yace in bai yarda ba su tuntubesa amma gaskiar magana shine rayuwar yarinyar nan na cikin hadari sosai, tunda salim ya fara fasaara mashi maganganun hankalinsa ya tashi soaai babu abunda yake fada aranshi sai “who are you exactly fatima? Who are your parents? Why would they abandon such an innocent girl, mey tayi masu da har zasu yardata a tsinceta gashi ta fada hannun azzalumai? Why why?? She didntt deserve koma suwaye iyayenta, saiyaji ya ta kara zama daran dam aranshi, dukda yaji cewa she can be yar zina amma ko soau daya baiji yanda yakeji game da uta ya ragu ba, hankalinsa duk ya tashi gaba daya.
“Do you think we can trust those peaple? We have to do some research on this”
Salim yayi magana taj yace “yea definately, i have to protect, i have to stand by her, i will find her real parent no matter what”
Shuru salim yayi yana son tambayarshi wacece ita a gareshi amma ya kasa.
Ganin yanda salim ke kallonshi bai tambayeshi ba amma yasa abunda ke ranshi wannan yasa shi cewa “she’s my wife!!!!”….
Toh Allah ya kaimu gobe🥺


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵 🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 49 · 0% Book details