← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 40 OF 66

Chapter 94

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 18 min read

Cigaban labari….

Da sallama rabi mai aiki ta shiga part din anne don amsa kiran datayi mata, tana shiga ta duka cikin ladabi tace “hajiya gani”
“Yauwa rabi cikin yanmatan nan ki dauka mai hankali daya ki tura part din nanna ta dunga kwana achan saboda a samu mai duba yanayin ta”
“Toh Hajiya,“
Tana fadin haka ta futa zuwa kasa, da sabeeha taci karo a kitchen tana wanke wanke tana ganin rabi tayi saurin juyowa ta kalleta, tunda aka dawo da nanna takeson a basu damar zuwa suyi mata sannu.
“Anty rabi ya jikin nanna? Dan allah zan iya zuwa na dubata?
Kallonta rabi tayi ganin yanda ta damu yasa ta saurin cewa “eh zaki iya, hajiya ma tace a samu mutun daya dazai yi hidima da ita a sama kafin ta samu sauki sosai,“
“Anty rabi zan iya kula da itan?”
Sabeeha ta fada kamar mai jin tsoro, kallonta hadiza tayi, daman babu wanda yazo ranta koda akce a samu mutun daya cikin yan matan masu aikin gidan.

“Eh, kije ki dauka hijabinki saboda sallah don achan zaki kwana”
“toh” sabeeha ta fada tare da wucewa dakinsu, hijab dinta kawai ta dauka da wayarta ta futo, rabi tayi gaba sabeeha ta bita a baya har zuwa part din nanna.
Suna shiga part din rabi tayi mata nuni da dakin dake gefen corridor wajen sitting room, irin dan karamin extra rooms ne haka, “ga daki nan saiki kwana achan, idan ta buqaci wani abun saikiyi hanzarin yi kinji ko, idan har da wata matsala kuma kiyi gaggawar saukowa ki fada min”
“Toh anty rabi”
Rabi na fita ta nufi hanyar bedroom, daidai wajen kofar tayi knocking a hankali, sake knocking tayi kafin daga ciki aka bata izinin shugowa.
Ahankali sabeeha ta bude kofar tare da yin sallama, ido hudu sukayi da nanna dake zaune gefen gado hannunta na kan bedside drawer tana kokarin aje hotunan data fidda.
Takowa sabeeha tayi cikin natsuwa har taakiyar dakin sannan ta duqa har kasa tace “barka da dare nanna ya jiki? Allah yasa kaffara ne”
Cikin muryanta dake nuna alamun tayi kuka don harta dashe sosai tace “Jiki da sauqi alhamdulillah fatima, ya makaranta?”
“Dagowa sabeeha tayi sai a lokacin taga idanunta, da tanada hurumin tambaya data tambayi meya sameta, don duk ta rame lokaci guda ga damuwa kwance akan fuskanta,“Alhamdulillah, akwai abunda kike buqata? Ko abunci? Idan akwai ki fada sainaje ayo maki yanxu”
“Ah ah babu abunda nake buqata fatima, nagode”
“Daman hajiya ce tace nazo na zauna anan ko zaki buqaci wani abun, anty rabi ta nunamin dakin dake parlor tace na kwanta anan”

“Yau na samu yar tayin kwana kenan?”
Murmushi sabeeha tayi tace “eh”
“Toh a kawo min hot coffee”
Cikin sauri sabeeha ta miqe ta sauka kasa cikin qanqanin lokaci ta dawo saman da coffee har zata fita nanna tace tayi zamanta a bedroom din.
Aiko ta zauna jwfi jefi take tambayr ko nanna na buqatar wani abu.

Zuwan sabeeha ba karamin dauke mata damuwa yayi ba, sabehar na tare da ita har wajen karfe goman dare tana mata tausa suna dan hira jefi jefi, around 11 tasata taje ta kwanta abunta kawai.

Hadiza ko data dawo daga hidimar maya batama tambayi ina sabeehar ba saida rabi ta fada mata cewa ta turata sama don kula da nanna.

Washe gari da safe saida ta gama hidima da nanna kafin ta tafi school.


Saudi pre trial detention center…..

Budo kofar cell din wata balarabiya dake sanye da kayan security tayi tana duban waenda ke zaune cikin dakin kafin tace.
“Inmate 235 You have a visitor”
Shuru babu response wannan yasa ta buga kofar cell din da karfi kamar zata balla karfen wajen da wani stick dake hannunta mai kauri sosai “call on inmate 235”
Dagowa hidaya tayi ta kalleta sannan ta miqe tabi bayanta, saida ta futo haske sosai na bita da kallo dakyau,tana sanya da kayan inmate riga da wando sai hijab da kowacce inmate take nadashi a kanta.
Gaba dayan wajen mata ne babu namiji ko daya don mata ke operating wajen.
Gaba daya tayi wani sanyi kamar ba hidaya ba, tunda suka kawota wajen bata samu kanta daidaiba, har zuwa lokacin shock din sirrin magaifiyarta bai barta ba gashi taqi bada hadin kai ayi trial din allegations din da ake mata, ko questining dinta da aka soma yi qin bada amsa tayi ta koma kamar wata kurma wannan yasa aka turota pre trial detention center kafin shi wanda akayi kidnapping din ya samu lafiya sannan har zuwa lokacin evidences ake gathering, wani abun mamaki ko lawyer daya babu wanda ya dauka case dinta the whole hodaya, hatta personal lawyers dinta wanda ta aminta dasu sosai babu wanda ya karba case dinta balle akaiga su tsaya matq.
Satinta biyu kenan a detention center she couldn’t bring her self together, gaba daya bata cikin hayyacinta,abubuwan da ke waje kuwa batasan meke faruwa ba.’
Abun ne har zuwa lokacin tana jinshi ne kamar a mafarki.
Tun kafin ta karaso wajen da visitor ke zama ta kura mata idanu tun daga nesa, fadwa dake zaune tana sanye cikin kaya na alfarma saidai fuskarta babu kwalliya babu komai tayi wani kalar abun tausayi tana ganin isowar hidayar tayi saurin miqewa da hanzari ta karaso inda take zaune ta rungumeta “ukty…”
Tunda fadwa ta rungumeta wani irin zafin ya soma rufeta kamar an watsa mata garwashi, saitaji gaba daya kamar an fiddota daga kogin data fada.
Sakinta fadwa tayi tana mai dubanta harda kukan munafurci “I’m sorry ukty…i’m sorry ukty, bansan ya zanyi da rayuwata ba, kamfaninmu ya lalace ukty..duk lawyers din dana nema maki sunqi karbar case din, all our supporters turns out to be our betrayals”
Tana gama fadin haka ta jaa kujerar dake facing ta hidayar ta zauna, tashin farko gaba daya hidayar ta sauya, ta kasa daina kallon fadwar da itama ta kura mata idanu.
Sai kawai hidaya ta fashe da dariya, dariya sosai take kamar zautacciya tana kallon fadwar,wannan dariyar datayi ya tabbatarma da fadwa da abunda tazo dubawa
Dakatawa hidaya tayi jin fadwar itama tana kyakyacewa da dariya sosai harma tafi da hidayar ta soma share hawayen dake kan fuskarta tace
“Oufff i just wasted my precious tears, kindawo hayyacin ki kenan”
Zuba mata idanu sosai hidaya tayi ba kadan ba tana kallonta.
“Hidaya….hidaya the almighty and powerful hidaya, yau kece a kaskantaccen waje kamar haka bazanyi mamaki ba idan har akace kin zauce don wannan kadai zaisa ki zauce”
Nunfasawa fadwa tayi tare da dora kafarta daya kan daya tana fuskantar hidayar, “at last kin gano gaskiyar komai kenan? It was a splendid game tho, you played and i take the lead”
Kallon cikin idanunta hidaya keyi idanunta yayi jaa sosai, babu abund ake yawo a kwakwalwarta sai tunanin wato this is the taste of betrayal?cin amana
Kallon agogon dake hannunta tayi na gold kafin ta maida dubanta ga hidayar ta bude jakarta ta zaro wasu takar du, tana gama fiddasu.
“By now nasan kinsan how we end up here, sign it,” ta fada tana mata nuni da papers, ko kallon takardun hidaya batayi ba ko ba a fada mata ba tasan na menene, idanunta sun gama budewa gaba daya, nannade hannayenta tayi a kirjinta ta koma asalin hidayar ta, ganin haka yasa fadwa hade rai, wato dukda ta rasa komai yanxu and shes behind bars saita nuna isarta.
“Fadwa fadwa fadwa abdul-basit!!!!, asalin sunanki kenan ko? Wannan wasan nina shiryashi kuma na jagoranceshi, kuma na barki ne kawai kin samu shiga ciki, ke ba komai bace a tafin hannun hidaya, basai na fada maki ko wacece hidaya ba, ke ba komai bace youre just a pest roaming around hidaya, kina tunanin saboda ina nan i will loose everything ko? Nop ki jira kankanin lokacin da zanyi facing dinki, keda wulaqantaccen ubanki ba komai bane a gaban hidayaaaaa!!”
Tana fadin haka ta buga table din dake gabansu, daga ganin fuskar fadwa zaka gane irin bacin ran dake fuskarta da fargaba,karfin halin hidaya na bata mamaki, ita zata fadi ko wacecec hidaya ciki da bai.
Hidaya na ganin yanayinta ta kamo Hannunta tana kallon cikin idanunta.
“Kinason na baki kamfani?ke a
Matsayin wa? As far as im concerned ke ba jinin taheel bace, you’re just a bastard haifaffiyar asara, lets say na baki taheels what do you think the world will see you as idan suka gano kedin ba yar…”
Hannun fadwa har karkarwa yake gaba daya ta koma jajawur kamar zata furzar da hayaki daga nunfashinta tsabar bacin rai, har yanxu hidaya is above her, har yanxu dukda yanxu tana jail, she’sss above her, and she sworn saita hau ta taka hidaya, a take ba ta chanza plans dinta ada tana kokarin sassauta mata amma yanxu wannan plan din ya kau,she will give her the worst.

Daman tasan za ayi haka wannan yasa tazo da shirinta tsaf, hotunan dake cikin jakarta ta zari ta aje gaban hidayar, cikin saurin hidaya ta kwashi hotunan tana kallonsu, barad ne a school dinsu fadwar ta dauka hoto tare dashi ta rungumeshi yana kuka da alamu ya samu labarin mahaifiyar tashi.
Dagowa hidaya tayi jikinta har rawa yake ta dubi fadwar, wato threatening tning dinta take da danta.
Matsowa daidai fuskar hidaya fadwa tayi yanda daga ita sai ita ne zasuji maganganun da suke saboda akwai cameras a wajen.

“Tunda har na iya kashe MIJINA(tareeq), saboda sirri na,na Kashe TAJUDEEN da taimakon ki a karo na biyu, sannan na shafe babin khaal this is just a piece of cake, I’m capable of doing anything anything don na samu abunda nakeso, zan iya kawar dake nayi wiping tarihin hidaya gaba daya…”

Duk yanda taso taoro ya bayyana akan fuskar hidaya qin bayyanashi tayi, saidai ga mamaki nan karara akan fuskarta data boye tsoronta dashi, Tana nufi zata iya kawar da barad kenan?

saurin daga hannu hidaya tayi zata kwasa mata mari fadwar tayi saurin rike hannunta tana zaro ido kamar yanayinta idan kaganta aka bata wuqa zata iya dabama mutun ba tare da second daya ba.
Duk wata uwa danta ne weakness dinta, zata iya komai akan danta koda kuwa bada ragowar nunfashinta ne.
Fadwa na tsaye hidayar taja papers din tayi signing gaba dayansu, gaba daya komai ya tashi daga hannunta ya komawa fadwa, komai fa duk wani abu datayi inherinting.
Tana gamawa fadwa ta kwashi tanardun ta dubi wajen securities din dake wajen ta daga ma wadda ta shugo da hidaya wajen hannu sannan ta juya ko second daya bata sake ba.
Tana gab da futa hidaya dake zaune tace “wallahil azeem idan kika sanya hannunki akan dana saina zama ajalinki”
Juyowa fadwa tayi ta mata kallo daya sannan tayi fucewarta a fusace.

Tunda ta shiga motarta take wani irin mahaukacin driving kamar zata tashi sama harta iso guest house din mahaifinta.
Tana bude kofar shugowa tayi karo da secretary din abdul basit, dagowa fadwa tayi kamar mahaukaciya ta kwasheta da mari both kuncin ta, ta shaqo wuyanta kamar zata kasheta, abdul basit dake zaune sitting room din yana kallon komai kuma baiyi yunqurin hanata ba, ga wadda ta shaqe kamar zata mutu, bai hanata venting anger dinta ba ya qaleta yana kallonta wama zai iya hanata koshi mahaifin nata bai isa ba, saida secretary dinnan ta daina nunfashi ta saketa.
Tana sakinta tabi ta kanta ta wuce cikin sitting room din ta watsa jakarta a wajen ta kama kanta tana ihu.
Hannu basit ya dagama black da personal asistant dinsa suka wuce wajen secretary din suka kwasheta suka fita ya rage daga shi sai ita.
Miqewa yayi ya kamo hannun fadwar ya rungumeta yana tapping bayanta “should i end her for you?just say a word”
Fitowa tayi daga jikinsa tana kallonsa idanunta kamar gauta tace “not yet, i want her to be miserable, so nake naga tsoro akan fuskarta, so nake na aje mata babban tabo a zuciyarta for messing with me”
“Well you can if you want to, ba kince danta ne weakness dinta ba? Give her that pain she deserves.”
Murmushi fadwa tayi tana kallon baban nata ta rungumeshi sosai tace “okay!!!!”

Hidaya na komawa cell babu abunda take sai hawaye, nidai zan iya cewa ban taba ganin hidaya ta taba yin hawaye ba sai yanxu, babu wanda ya fado mata arai sai jamid.
Wazai duba mata barad? Ya zatayi da danta?Dole tasan yanda zatayi ta kubutar da danta daga sharrinsu.

Haka nan ta kwana a zaune ko rintsawa batayi ba, maganganun da fadwa tayi mata na yawo akanta, wayo tayi underestimating dinta sosai ba kadan ba, ta kashe mijinta? Daman itace behind bacewar taj? Sannan itace ta kashe khaal?.

Zaman nan datayi ko motsawa batayi ba,abunci ko da aka kawo mata ko kallonshi batayi ba har safiya.
Wani inmate call dinne ya kara zuwan mata cewa tayi visitor, koda ta buqaci sanin wanda yazo din akace mata family member ne taqi futowa.
Da daddare kuwa da securities sukazo round checks aka tadda ta sume, dole akayi shifting dinta to clinic aka bata taimakon gaggawa.
Batama san ta sume ba sai the next very day ta samu farfadowa tana farkawa idanunta ya sauka kan doctor din dake dubata, ruwan da aka saka mata aka cire tana kokarin miqewa zaune ta kasa saboda cuffs din da aka saka mata.
Discharging dinta akayi security suka rakata zuwa dakinta, tana shiga wani visiting call din yazo mata.
Duk a tunanin ta fadwar ce ta sake dawowa don bata kawo ko afiya ce ko wani family member ba daban.
Security suka rakota har wajen visiting area kafin su barta a tsaye dago da kanshi yayi ya sauke akanta, saurin yin baya hidaya tayi wuth so much shock, karara akan fuskarta, hannunta ta sanya kan fuskarta ta mutsuka idanunta don tabbatar da jamid ne a gabanta, mikewa yayi tsaye ya tunkari inda take tabi kafafunshi da kallo har zuwa hannyanshi daya sanya ya kamo nata ya zaunar da ita sannan ya dawo wajen zamanshi ya zauna.
Saurin kauda shock din dake fuskanta tayi ta kauda idanunta irin kamar batayi mamakin ganinsa ba.
“You must have work hard on your self, Yaushe ka samu lafiya?”
Girgiza kai yayi, this is hidaya, bazata taba chanzawa ba.
“You must be happy to see how i end up here,…mind you i still don’t regret my actions, i still stand on my grounds duk abunda nayi a baya”

“Nasani, babu wanda zai fadi ko wacece hidaya saini, amma inaso ki sani duk abun dayake faruwa dake yanxu baikai kwatankwacin pains din da kika saka yaron nan a ciki ba, and alhakin sa ke binki, baku hakura ba saida kukaci galaba akanshi, ay bakiga komai ba ma tukunna you contributed in destroying alot of peoples life, dukdan saboda power, saboda arzikin da zamu mutu mu barshi, saboda hatred, kin mance kema uwace, kin haifa kema, idan naki ne yayi experiencing abunda kikayi ma yaronnan…”
Ya dan dakata jin wani irin daci a zuciyarsa kafin ya cigaba, “yanxu ina arzikin?ina power din?

Idanunta ne yayi jaa sosai, tsakanin kwanakin datayi a wajennan yasata reflecting abubuwa da dama, musamman da fadwa tayi threatening dinta akan danta, bata taba regretting abubuwan datayi ma taj ba sai yanxu, ta dandani zafin cin amana musamman ga wanda ka yarda dashi.
Shida ta nemi wulaqantawa, shida ta nemi salwantawa rayuwa ta rabashi da kowa hatta mahaifiyarsa ta karfi da yaji ta maishesa kamar wani dan kwikwiyon da take juyawa san ranta, kuma ya yarda da ita sosai, ya bata matsayinda ko mahaifiyarsa bai bama in return tayi betraying trust da yardar daya bata da girman daya, infact bata taba considering dinshi matsayin dan uwanta ba ko sau daya, dukdan saboda mahaifinsu ya auri mahaifiyarsa.

Wani abu ne ya soma sauko mata a fuska kamar hawaye, she couldn’t believe hawayen takeyi, wannan hawayen nata ya bama jamid answers din da yake nema, ko zata kwana tana denying batayi nadamar abubuwan datayi a baya ba yasan yanxu tayi.
Saurin gogewa tayi ta dubeshi, “are you done?” Tana fadin haka ta miqe tsaye zata bar wajen yayi saurin dakatar da ita.
“You’re a victim as well, Its not too late to repent, its not too late to make things right,”
Dan dakatawa tayi kafin ta juyo, ta kalleshi, “khaal yana raye! Bai mutu ba?”
“Bai mutu ba? Yana raye?”
“Kwarai da gaske,” ya bata amsa
“He was never dead to begin with,”
“Wa kenan????” Hidaya ta tambayeshi kamar bata sani ba
“yar uwarki fadwa, !!!”ya bata amsa kai tsaye,
“I was one of her victims, itace sanadiyar paralyze dana samu, tana amfani dake ta hanyar cinmma burinta da boye duk wani sirrikanta.
Shuru hidaya tayi tana wani nazari, mamaki ya gama cikata sosai.
Kamar an tsunguleta ta dago ta kalli jamid tace
“Barad…!!! He’s in danger,ka daukeshi ka boyeshi,”
“Barad??” Ya kalleta ganin yanda gaba daya ta nemi rikicewa.
“Me zai samu barad?”
Dubansa tayi dakyau hannunta gar karkarwa yake, “fadwa ba kanwata bace, fadwa yar abdul basit ce”
Confusely yake kallonta, “ni take hari,kuma zata iya yin komai don ganin ban bayyana wannan sirrin nata ba, you need to take barad, ka boyeshi, karta cutarmin da daa”
Gaba daya jamid ya shiga confusion, yanxu wannan ne babban sirrin nata daman?….


Nigeria….
Karfe 5 daidai suka dawo gida, as always duk sun fita itace last, tana fitowa ta rufe motar saida ta jira hamad ya kashe motar ya fito kafin ya zagayo ya tadda ta tsaye, laptop din dake hannunshi ya miqa mata.
“Kiyi presentation din dashi”
Da mamaki take kallonshi don kwata kwata batayi maganar presentation dinba ya akayi ya san zata buqaci laptop?
Ganin ta tsaya yasashi “ko na aje abuna?”
Cikin hanzari ta karba murmushi ya kubce mata tayi saurin sunkuyar da kanta tace “thank you ya hamad”
“You’re welcome muje ciki”
A tare suka shiga main house ya bude kofa ta shiga kafin ta shiga, saida tazo wucewa part dinsu ta sake juyowa ta dubeshi bakinta ta dan motsa ahankali tace “thank you” sautin muryanta bai futo ba amma yanda ya kura mata ido ya gane abunda ta fada, tana fadin haka ta wuce ya bita da kallo, ya sauke wani murmushi ahankali, he just loves to seeing her smiling.
Saida yaga ta shiga ya juya ya futa daga main house din.

Da sallama ta shiga dakinsu, hadiza na zaune tana ninke bras da panties din maya datasa sabeehar ta wanke da asuba.
“Ina wuni mama”
A daqile hadiza tace “lafiya” kafin ta miqe da kayan datake ninkewa ta futa.
Sabeeha ta bita da kallo tana tunani wani abu ranta.
A gurguje tayi wanka tasa doguwra rigar da aka bata cikin kayan laila kafin ta fito zuwa kitcwhn, tana shugowa rabi dake tsaye a kitchen din tace “har kun dawo?”
“Eh anty rabi yanxu muka shugo”
“ga abuncin ki nan,”
“Tohm akwai aikin da za ayi?
“Ah ah jeki huta abunki kawai”
Murmushi sabeeha tayi tace “toh”
Daukan abuncin tayi ta fita rabi ta bita da kallo, haka kawai take tausayin yarinyar, babu ruwanta ga respect

Da sallama anne ta shigo bangaren nanna dake zaune da laptop kan cinyarta, zakayi tunanin aiki takeyi saidai gaba daya natsuwarta bata wajen kwata kwata.
Sallamar da nanna tayi ne yasa ta dawo hayyacinta bayan ta amsa.
Zama anne tayi suka gaisa anne ta mata ya jiki, “badai aiki kike ba hajara keda akace ki huta”
“ alhamdulillah naji sauki ay anne”
“Inason zamuyi magana” anne ta fada tana kallonta.
Nanna tasan maganar dazatayi mata wanda a yanxu dai bashi takeson ji ba kwata kwata, amma haka nan ta daure tace “ toh yaya allah yasa lafiya”
“Tajudeen zai dawo nan gida da zama, zamanshi a hotel bai daceba, ina amfanin zaman hotel ga gida na bari ne daman ki samu sauqi tukunna”
Take nanna ta hade rai kamar bata taba dariya ba tace “zaman me zaizo yayi anan? Bazai zauna anan ba, idan ya gama abunda ya kawoshi ya koma chan inda ya fito”
“Hajara kinsan me kike fada kuwa? Na kasa gane maki? Wannan wani irin kafiya ne? Danki ne fa? Shekara nawa kina mararin ganin danki?”
“Yaya, banida da, na dade da ajiye zama uwa a gareshi, tunda har banida mahummaci a rayuwarsa”
“Ya isaa!! Ya isa haka nan, saurareni da kyau hajara,karki sake ganin laifin danki na qin waiwayarki dayayi,kin tafi kin barshi yana da kananu shekaru ba tare da tunani wani hali zai shiga ba dukdan saboda laifin ubansa, mey laifinsa? Ya za’ayu bazaiyi tunanin kinyi abandoning dinshi ba? shin kinsan irin rayiwar da yayi achan? Kinsan ya childhood dinshi ta kasance achan? Wannan abun da kikeyi ba komai bane face huce takaicin tsohon tabon dake dan qare aranki ya hanaki moving on shekaru wajen nawa ya hanaki yin aure, tun wuri ki dawo hayyacinki ki rungumi danki karki tafka babban kuskuren da zakiyi dana’sani,”
Kuka sosai nanna keyi anne na mata fada yau ko tausayinta bataji ba don furucinta ya bata mata rai.
Ganin yanda take kuka sosai yasa anne kama hannayenta ta rukosu tace “haba hajara kamar bakida tawakkali? Mene laifin yaron nan? Eh??ki godewa allah daya sa zaku sake ganin juna kuma wannan dama ce allah ya baki na zama uwa a karo na biyu, duk wani abu daya faru dama chan haka allah ya kaddara saiya faru bamu isa mu chanza shi ba”
Kallon ta anne tayi tare da bata qwarun gwiwa, “danki na buqatarki hajara,ki zame mashi uwarda ya rasa tun yana shekara bakwai, ki bar komai ya wuce, ko zamo mai karbar kaddara duk yanda tazo maki, ki mance da baya kamar ba ayi ba”
Runtse ido nanna tayi kafin ta bude idanunta ta dafe kanta anne na ganin haka ta fara kallon gefen gadon ko zata ga maganinta idanunta ya sauka kan bedside drawer dake bude, taci karo da hotunan taj din, yana baby da lokacin daya fara tafiya, har zuwa lokacin daya girma ya zama saurayi.
Murmushi kawai anne tayi ta balla mata magungunan tace “dadai aje wannan kafiyar kikayi kikaja danki daya fi maki, don wallahi idan har kikayi watsi da wannan damar taki ya koma zuciyarki ce zata buga, wllah ya sawaqa”
Tana fadin haka ta fita.
Gaba daya nanna ji tayi jikinta yayi sanyi sosai, dukfa wannan abun da take a baki ne, tunda ya rike hannunta ranar yana kuka a gabanta gaba daya ta sare, ta fara blaming kanta for komai, what kind if a mother zata tafi tabar danta ba tare da tayi wani difon tunani ba tunawa da wannan kadai da abunda mahaifinsa ya mata kesata karaya.

Anne na fita daga part dunta ta wuce nata ta soma dialing number taj, cikin ikon allah kuwa ya dauka cikin gaggawa, kwananshi biyu kwance yana zazzabi saida salim ya kawo mashi doctor ya dan samu sauqi.
Ko jiya da sukayi waya da anne kasa fada mata yayi abunda ke damunshi.
Yana dagawa suka gaisa ta soma magana kamar haka.
“Inason gobe ka dawo gida, ina dana ina zaman hotel, come back home kaji ko”
Shuru yyi gabanshi na faduwa sosai, “oummi??”
“Karka damu tajudeen, tana nan tana jiranka tajudeen, allah yayi maka albarka yasa muga aurenka da yayanka tajudeen, ni zan aurar dakai ma” ta fada tana murmusawa, maganar aure datayi saida gabanshi ya fadi.
Amma ta wani bangaren ba karamin dadin kalamanta yaji ba datayi na kan cewa oummi na jiranshi, ahankali ya furta “Alhamdulillah, take yaji duk wata ragowar rashin lafiyarshi ta kau gaba daya, saidai kuma gabanshi ba karamin bugawa yakeba sosai at the same time kuma lokaci guda sabeeha tazo ranshi.


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 40 · 0% Book details