Chapter 80
Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 23 min read
Tunda aka shigar da ita motar babu abunda take sai hawaye, duk yanda taso ta hana kanta kasawa tayi, zuciyanta ya karaya sosai, at least she was expecting him to listen to her, amma ya rufe ido, ya fada mata to her face bayason ganinta ya tsaneta, and yana mai baqin cikin ranar data shugo rayuwarshi.
Bangaren taj yana nan tsaye kamar statue ya kasa motsawa, afiya da hidaya ko kwafa sukayi suka koma bangarensu ya rage dagashi sai fadwa, gaba daya wani irin dadi takeji aranta ba kadan ba.
Yana cikin yanayin nan ta kamo hannunshi tana mai sauke murya kasa kasa, “don’t upset yourself cause of useless people who fooled you, they have bad intentions against you, i know you’re hurt baby brother just know that i will always be here for you”
Kallon daya mata saida gabanta ya fadi, ya maida dubanshi ga hannunshi data kama ta rike.
“I don’t fucking need you or whoever, and don’t you ever put your filthy hands on me”
Yana kaiwa nan ya juya afusace ya wuce sama kamar zai tashi sama.
Yana shiga dakin ya banko kofar ya wuce closet, ashe kiran da aka mata ninke kayanshi take don gasu harta ninke akan table island din dake closet din harda nata a gefe.
Saurin dafe kanshi yayi ya runtse ido ya wani irin naushin iska, “noooooo whyy!!! Why!!! Whyyyyyy”
Ya fada cikin ihu yana dafe table din, accessories dinshi dake wajen ya watsar gana daya a kasa ya dafe table din.
Yakai wajen minti goma a haka kafin ya wuce bathroom ya sakarma kanshi ruwan sanyi ko kayan jikinshi bai cire ba.
A taqaice dai isolating kanshi yayi, tun bayan da ya sakarma kanshi ruwan sanyi zazzabi mai zafi ya soma lullubeshi, gashi tun breakfast baisa komai cikin shi ba sai kwanciya da yayi.
Fadwa na waya afiya ta shugo tayi saurin katse wayar, suna kallon juna suka kyalkyace da dariya afiya tace, “lets have a dinner date, bills on me”
“Sure!!..will spoil you with some goodies as well to celebrate our victory”
Haka suka dunga murnar korar sabeeha da sukayi, tafiyar da ammu tayi ma ba wani damunsu yayi ba kwata kwata.
Afiya na fita fadwa ta kwanta kan gado tana sauke wani irin nunfashi imagining gata ga taj yana tasha jikinta making love to her, gaba daya illusion din abun yasa ta mance a wani yanayi take, sai taba jikinta tace tana moaning auzubillahi, ta rigada tayi nisa bata jin kira kwata kwata.
Wajen karfe goma ya bude idanunshi, tun wajen karfe hudu dayayi sallah ya koma barci ko zaina jin zafin da yakeji aranshi, aiko barcin wahala ya kwashesa bai tashi ba sai yanxu, gaba daya he feels weak, tired and lost, komai haushi yake bashi,haushin kanshi ma yakeji sosai ba kadan ba.
Dakyar ya lallaba ya miqe zaune yana dafe da kanshi kawai ya soma jin echo din muryar sabeeha a kunnenshi, cikin hanzari ya dago saiko ya ganta gabanshi tana mashi murmushi, “didi ka tashi? Ga coffee na kawo maka”
Harya miqa hannu kawai ya kifta ido yaga babu ita a wajen, saurin girgiza kanshi yayi ya sake bude idanunshi yayi tsuka kadan sannan ya miqe ya wuce bathroom yayi wanka da ruwan zafi sosai sannan ya dauro alwala dukda yanajin jiri jiri sosai.
Yana futowa daga bathroom ya saka jallabiya ya nufi wajen praying section chan ya sake hangita zaune tana jiran isowarshi suyi sallah, rai a bace ya soma magana da kanshi ya runtse idanunshi “stop it stop itttt”
Tun bayan ya idar da sallah ya zauna kan sallayan yana azkar, abunda cikinshi bai cika yi ba sai gashi yau ya fara, wato kukan yunwa, bai taba lura da bai damu da cikinshi ba sai yau, saboda sabeeha ta dauke mai komai, 3 square meal dinshi yarinyar nan ita ke handling, adaidai lokacin da bai buqata ba tasan zaiji yunwa zata kawo mashi,kallon bedside watch dinshi yayi wajen 11 saura kafin su kwanta by 10 haka take kawo mashi coffee da fruit.
Haushin kanshi yakeji gaba daya for depending on her unknownly.
Haka nan ya tashi ya zame jallabiyan shi ya rage dagashi sai irin dogon wandon nan, ya futa daga bedroom din, kallon sitting room dinau ya dungayi yana ganin kamar zai ganta a kwance kan couch, daya tuna karyar data mashi sai kuma ya fara jin haushin kanshi, wata yar tsuka yayi ya nifi kitchen nan ma dai yana kunna haske ya soma ganin kamar gata tsaye tana mashi murmushi, haushi da takaicin kanshi yasa ya futa daga kitchen din rai a bace, why would he be remembering her? Whys he like this? He hate being like this, and he çanta stop him self”
Wallahi oga a zaune ya kwana, tunda ya zauna kan couch din bedroom yayi relaxing bayanshi ya rufe ido babu abunda yake sai tunani, tunanin rayuwarshi ta baya har kawo iyanxu,he feels lonely, tunanin lokacin dayake shi kadai a uk ne ya dawo mashi da zaman da yayi a gidan nan kafin ya tafi, same exact feeling yakeji.
Washe gari tun wajen karfe shida ya fuce daga gidan dukda yana jin zazzabi ya wuce gym wai ko dan zai samu sarari ya daina ganin yarinyar nan duk inda ya motsa, closet ne bathroom ne kai ko’ina ganinta yake, kamshinta yakeji, he’s feeling her presence ako’ina and he hates it so so much.
Yana cikin workout kamar zai illata kanshi mutabbl yazo, yana kallonshi surprisingly, intentionally shi yazo wajen don yasa receptionist suna informing dinshi idan yazo.
“Hello buddy what a coincidence yaushe kazo nan,”
Shuru taj yayi bai bashi amsa ba yana abunda ke gabanshi, don ko magana baya son yi, anything da zai futo daga bakinshi yanxu bazaima mutun dadi ba.
“Is everything okay? You’re going too far taj karka illata kanka”
Wani irin kallo taj yayi mashi tare da aje thumbells din daya dauka mai weight sosai yabar mashi wajen ya koma kan threadmill yasa speed sosai yana gudu.
Mutallib na kallonshi yayi gudun yayi gudun har yana neman faduwa mutallib yayi saurin kashewa ya dafe hannunshi yana mai dubanshi with concern akan fuskanshi yace “please kayi hakuri, you’re hurting your self taj, what is the problem?”
Bugun mills din taj yayi rai a bace idanunshi sunyi jaa sosai ga gumi ya gama keto mashi yace “i fucking hate liars…betrayerssss”
Saida gaban mutabb ya fadi don ya dauka dashi yake wallahi, “i’m sorry taj…what ever happens it happens for a reason”
“No she has no reason..she has no right to lie to me, to fool me, to trick who d hell is she?”
Ajiyar zuciya mutabb ya sauke yana son mai son jin karin bayani yace “im sorry for meddling in your business but if you want to talk i’m here okay”
Zama sukayi taj yana ajiyar zuciya, yana mai duban mutbb yace “you what i hate the most in my life is karya..bana son karya bana son ayi fooling dina, but this..this girl…she lied to me, i was so invest in the pregnancy she claim is mine, i was so happy”
“You mean your wife?”
Da mamii taj ya duveshi ya akayi ya sani, “ sorry you mentioned her once ranar da muka fita tare kace min zaka tsaya mall ka saya chocolate for your wife”
“Don’t ever call her my wife, it’s done…i never want to see her face ever again”
Tunda ya soma magana hankali mutabb ya tashi, tabbas yasan fatima yake nufi, amma yanason yaji karashen zancen.
“Toh yanxu ya zakayi da ita?”
“Na koreta, i dont need people like her around me”
Shuru mutabble yayi yama rasa tunanin da zaiyi.
“I’m sorry amma ina ganin hakan da kayi baka kyauta ba, what if batada kowa what if batada wajen zuwa? Are you sure you made a right decision?”
Shuru taj yayi, kwata kwata baiyi nazarin ya akayi mutabble yasan bata da kowa ba kuma bata da inda zataje ba sai maganganun nashi da sukayi tasiri aranshi.
Sai wajen karfe sha daya suka bar wajen, suna rabuwa mutabble ya bazama neman fatima, mutanen daya sani na cikin gidan securities ya fara nema, adan zaman da yayi dasu he got close to one of them nan yake shiada mashi abunda ya faru a jiyan da yanda aka tafi da ita.
Mutallib yaji rashin dadi ba kadan ba, ayau da khaal na raye bazai bata bari a wulaqantata ba.
Around karfe sha biyu aka fiddata daga cell din, inda akayi transferring dinta zuwa domestic workers organization, mutallib ne yayi hanya akabi tanan aka karbeta, yayi hakan ne yana gudu kar a cutar da ita don yasan tunda ta fita daga gidan tasan sirrikansu bazasu taba barinta haka ba.
Cikin gaggawaa anan organisation din sukayi clearing dinta za a maidata kasar data futo washe gari.
Da yamma mutallib ya buqaci ganinta nan ya masu karyar ay yar uwarsa ce shima aiki yake a wani organization din daban, babu wani dogon bincike aka barshi ya ganta.
Lokacin data futo taga mutallib tayi mamaki sosai, ba karamin tausayinta yaji ba, amma ganin ta da yayi cikin koshin lpy yaji dadi sosai.
“Fatima kiyi hakuri…kinyi ma khaal halacci, ina fatan bazaki sake shiga irin wannan rayuwar da kika shiga ba”
Hawayen dake neman fitowa daga idanunta ta hanasu saukowa ta girgiza mashi kai kawai,kora dai taj ya mata korar wulaqanci, leavung her miserably, koda yake daman rayuwarta gaba daya is miserable tun daga haihuwarta, uwarta ma tayi abandoning dinta balleshi? She has no reason to complain, ita dai haka tata kaddarar take kuma ta amsa hannu bibiyu.
Wata leda ya bata tare dayi mata fatan alkhairi bayan ya jaddada mata karta sake ace za a kaita wani waje, ko tafa alamun za a kaita wani waje ko she sense something suspicious ta kirashi a waya, nan ta shaida mashi babu waya hannunta.
Daya daga cikin wayoyinshi ya bata kafin ya mata sallama ya tafi.
Yana tafiya ta bude ledar, ga mamakinta taga kudi ne kuma da yawa, nannade ledar tayi ta koma ciki ta doka tagumi, yanxu gove goben nan zatabar kasar nan, kuma har abada bata fatan sake sanya kafafunta a kasar.
Shin ko me zataje ta tadda a gida? Koma dai an mance da rayuwarta gaba daya? Shekara kusan biyu kenan.
Haka ta kwana ido biyu, ta kasa runtsawa, tayi alkawari daga ranar data guta daga kasar nan bazata kara kawo tunaninshi aranta ba, zata goge gaba daya memories din zamanta dashi don babu wani amfani da zai mata.
Da daddare ganin baizo dinner ba yasa hidaya tazo har bedroom dinshi da divorce papers da papers din next guardian dinshi don har yanxu sabeeha na matsayin next kin dinshi, and she wants that authority back.
Koda ta aje mashi papers din kasa cewa komai yayi, i need this papers gobe.
Tana fadin haka ta fuce yabi bayanta da kallo.
Without seconds yayi signing paper din ya aje a gefe.
Washe gari ta kama monday, tun kafin ta wuce office ya sauko kasan ya bata papers din, tayi mamakin ganin ba duka ya bata ba saidai the most important one din daya bata shi tafi buqata so batace komai ba ta kara gaba.
Sabeeha baiwar Allah tun wajen karfe bakwai aka fitar dasu ashe ba ita kadai bace su kusan uku ne za a maida, sauran shekarun aikin su a kasar ya cikaza a maidasu, ba kamar nata case dinba da ta shiga record don da an kaika police station to ka shiga record.
Cikin wata bus aka zubasu sai airport, kowanne aka bashi passport dinshi, ma’aikacin organization din saida ya tabbatr sunyi boarding kar su gudu don wasu abunda suke kenan kafin ya kara gaba.
Flight din nasu sai wajen yamma zai tashi, cikin airport din akwai restaurants, Akwai boutique, duban kayan jikinta na tun shekaran jiya tayi, ko sauyawa batayi ba da tayi wanka shi take maidawa don bata da komai, haka ta futo daga gidannan.
Wannan yasa ta shiga boutique din da kudin da mutallib ya bata ta saya riguna guda biyu da pants sai sabon takalmi da yar bagpack dinnan ta yan makaranta mai kyau sannan ta shiga bathroom ta sauya kaya ta zuba sauran da wanda ta cire cikin jakar sannan ta fito.
Wajen yamma around 6 haka jirginsu ya daga sai NIGERIA………
Lokaci guda yaji gabanshi na wani irin bugawa fat fat fat ya rasa dalilin, lokaci guda ya rasa natsuwarshi, tunanin yarinyar nan ya addabeshi ya kasa ganema kanshi, duk motsin da zaiyi saiya tuna da ita a ko wanne lokaci, memories din dayayi loosing ko haka suka dunga mashi flashing, yanda take kula dashi, yanda koda yaushe take tare dashi in yana kuka tana kuka idan yana dariya tana dariya.
He’s loosing it gaba daya, ya rasa meke mashi dadi,ga maganganun da sukayi da tareeq ya tsaya mashi arai sosai, he’s hating this kind of feeling, she lie to him ta mashi karya amma meysa yakejin gaba daya kamar bashi ba, yanajin kamar part of him is gone, magnganun ammu ne suka soma mashi yawo akai, ya soma magana da kanshi.
“No no i will never regret my decision, she’s just my maid, what’s so special about her?”
Haka ya dunga reminding kanshi, wallahi daren ranar bai runtsa ba ya kasa gane meke damunshi, abunci ko banjin akwai abunda yasa ma cikin shi between jiya da yau, sai ruwa da yake yawan sha, bai ma bi takan cikin nashi ba kawata kwata cause yayi loosing appetite gaba daya.
closet ya shiga zai dauka laptop dinshi ko zai samu ayyukanshi su dauke mashi hankali, daga gefe ya hango kayanta a jere fess fess saurin kauda kanshi yayi don ko gani baya son yi, daga gefe kamar ance ya daga idanunshi yaga chocolates din daya suyo mata ta jera su cikin wani dan bowl.
Takowa yayi har zuwa wajen ya dauka daya ya fito daga closet din ya zauna bakin gado yana kallon ledar, chan kuma meya tuna kawai ya wulla chan gefe ya kunna laptop dinshi, zaman da yayi a dakin ji yayi kamar ana suffocating dinshi ya koma closet din sai yaji he feels some kind of ease daya dawo nan saboda kamshinta dayakeji, ko nashi bayaji sai nata amma ya kasa accepting saboda hakan ne.
Adaidai lokacin da ya rasa natsuwarshi haka ta kasance a wajenta don a daidai lokacin jirginsu ya daga, wani irin emotional moments ta shiga tana tuna yanda tazo garin da first encounter dinsu, sanda ta shiga daki ta ganshi zaune shi kafai lokacin da baya cikin hayyacinshi the first din dayyi mata shine murmushi dayayi melting zuciyarta, da farko tana ta tsoron haduwa dashi don ana cewa duk caregiver data tunkareshi aranar take barin gidan, gashi saita kasance itace caregiver ta farko daya fara amincewa da ita, ya kaidata bestfriend dinshi, ya bata damar kula dashi, ya zame mata wani sabon farin ciki a rayuwarta da bata taba samu ba, tayi kokarin hana kanta tunashi amma ta kasa, kamar ana ingiza zuciyarta, tayi rauni sosai.
5 daidia ya bude idanunshi a razane, wani irin mummunan mafarki yayi, ashe barci ne ya dan daukeshi na yan mintina kan resting chair din dake closet dinshi, don har wajen 4 idanunshi biyu, bazaice ga abunda ya tabaka ba.
Nnamdi ezikwe international airport abuja…
Misalin karfe takwas flight dinsu ya sauka saboda time difference dake tsakani, da clearance da komai da akayi masu saida ya dauka wajen awa biyu, tund ata sauka gabanta ke faduwa, sai yanxu takejin wani sabon tashi hankali, nan bathroom din airport ta shiga tayi alwala tayi sallah anan masallacin dake ciki kafin ta fito tana dube dube, abu na farko data farayi shine chanza kudin da mutallib ya bata, aiko wajen dubu dari kudin donma ta kakkashe wasu a boutique.
Tana karba ta saka su cikin bagpack dinta sannan ta nufi hanyar futa masu taxi suka tareta don jin inda zataje, ta rasa ma me zata ce masu, daga karshe kuma ta masu bayanin inda zasu kaita.
Tunda suka tunkari layin kayefi dake garin dutsen habuja gabanta yake faduwa, abubuwa da dama sun sauya anyi rusau, mutane dake saye da sayarwa bakibaki wajejen anguwan duk babu su anyi vacating wajen gaba daya, iya inda taxi din zai iya shiga ya tsaya sannan ta bashi kudinshi sannan ta gyara zaman jakarta ta nufi hanyar cikin anguwar, data gifta sai ayita kallonta, daman ba saninta akayi ba so babu wanda ya shaideta, tana isowa gaban gidan hayansu ko kirjinta ya cigaba da lugude, hannunta har karkarwa yake tsabar tsoro, dan dole ta danne abunda ke cinta ta shiga gidan tana yaye labulen kauren dake gidan.
Gidan na nan yanda yake a cike tam, ga uwar rana da ake kullawa data babaye tsakar gidan, ga wani irin doyi da warin kwata hade dana bandaki daya wani buso fuskarta, tayi saurin runtse idanunta ta bude.
Maman chidi mutuniyar inna wadda ita kadai suke mutunci a cikin gidan tana hangota tace “ahh batan hanya kikayi ne? Ko kinzo sayan zobo ne fine gurl?”
Sabeeha na ganinta ta gane ko wacece saidai ita bata ganeta ba kwata kwata, duban dakinsu sabeeha tayi tace “maman chidi ni…ce”
Tabe baki matar gwarin tayi don bata ganeta ba kuma tasan kaf zuri’arsu babu mai kyan yarinyar gata fara kuma yar hutu, kana ganinta babu wahala a jikinta.
“Kai me i no no you o, who are you looking for”
Nuni tayi mata da bangarensu na da tace “hadiza? Are you looking for hadiza?”
Girgiza mata kai sabeeha tayi daidai nan hadiza ta futo daga dakinsu tana kokarin rufe kofar dakinsu, tana sanye da atamfa da wani gyale daya dan kwana biyu, gaba daya ta fara fita hayyacinta saboda wahala.
Koda sabeeha ta hangota saida gabanta ya bada wani irin dammmmmm, tana juyowa suka hada ido da ita kuwa tayi saurin sauke nata, hadiza ko bata shede ta ba ta nufi hanyar futa don bataga ta zama ba, neman aiki take ido rufe duk wanda ta samu yinshi take donta rufama kanta asiri ga kawu na police station tana kiciniyar yanda zata yi ta fiddoshi.
“Hadizaaa this girl dey look for you”
Tsayawa hadiza tayi harta kusa wuce su ta dakata, kallon sabeeha tayi don har zuwa lokacin bata ganeta ba, “toh fa? Ni kuma?”
Sai a lokacin sabeeha ta dago sukayi ido hudu, take hadiza tayi baya har tana yarda yar purse dinta a kasa, hankali a tashe, fuskar da bazata taba mantawa ba a rayuwarta ce ta bayyana a gabanta, fuskar mahaifin sabeeha.
“Ma…ma..”
Sabeeha ta kira sunanta hawaye na sauka akan idanunta, saida sabeeha tayi magana ta gane itace, abun yazo mata kamar a mafarki kuma ba zata,babu abunda hadiza keyi sai innalillahi, “innalillahi wa inna ilaihi rajiun na shiga uku na lalace asirina zai tonu ni hadiza”
Batama san tana fada ba, don batayi tsammanin wannan sabeeha ce ba, ta sauya gaba daya,duk wata dauda wahala, yunwa da wannan gyatson nata duk babu su, gashi ta kara wani irin masifaffan kyau tayi qiba, gata nan dai budurwa cirr a gabanta.
Ay batasan san sanda ta fuce daga gidan ba ko waiwaye batayi ba sai gidan jamila direct, tun bayan tafiyar sabeeha da watannin data gano jamila da mijinta cutarta suke kusan duk kudin aikin data tura sabeeha rabi aljihun su yake tafiya sauran kuma saisu bata, data gano anyi bura’uba tanan sukayi baran baran ita da jamila, dake sunsan sirrikan juna wannan yasa basuyima kansu tone tone ba.
Jamila na gaban risho taga hadiza tsulum a gidan kamar mahaukaciya, “malama ya haka kamar an jefoki babu sallama”
“Jamila na shiga uku… ta dawo ta dawo”
“Wacece ta dawo?”
“Sabeeha..”
Zaro idanu jamila tayi taja hannun hadiza suka shiga uwar daka ta dubeta tace “toh data dawo se akayi yaya?”
“Jamila asirina zai tonu, yarinyar nan ta sauya gaba dayanta, kamanninta na asali sun fito, kinga ke kika bani shawarar mu turata chan toh yanxu gashi ta dawo ya zanyi da ita?”
“Mteww shine abun tashin hankali? Ke shine damuwarki? Toh seme inta dawo? Zaki bari a ganta ne? Yanda kika faro haka zaki karshe, na dauka kin daina zuwa gidana yanxu maiya kawoki? Neman mafita ko? Toh kije ki nemi mafitarki”
“Ay wallahi jamila baki isa ba, kinsan babu wajen wadda zanzo wajenta da maganar nan saike, ke kadaice kika san komai tunda ke kika sauya su”
“Na sauya su? Waye yace na sauya su? Ke badan amincin dake tsakanina dake ba ina ruwana a cikin lamarin nan, amintar dake taakanin mu ne yasa naji tausayinki nayi miki abunda kika buqata ehe”
“Yanxu dai mubar wannan fadan..ya za ayi kenan”
“Muje chan gidan naga abunda yasa kika Rikice haka, ko mutuwar inna bata sakaki burkicewa haka ba sai wannan karamar matsalar mteww”
Atare suka fito suka nufi gidan, tundaga nesa da jamila ta hangita bakin kofar dakin jamila ta kama haba, itama ta tsorata ba kafan ba wallahi kamannin sun baci da mahaifinta ba kadan ba.
“Ah ah sabeeha…kece haka, masha allahu..allah sarki ashe rai zai ga rai, yarinya kin girma”
Wani irin kallo hadiza tama jamila tayi shiru, kyauren dakin jamila ta bude suka shiga ciki sabeeha ta shigo itama a rakibe tana bin dakin da kallo, jakarta ta ajiye a kasa tana mai duban dakin kasa kasa.
“Zauna” hadiza ta bata umarni, babu wani fara a ko nuna farin cikin ganin ta dawo.
Zama sabeeha tayi a natse a kasa, suka suka zauna kan matattun kujerun dakin mai 2 seater guda daya duk suka zuba mata idanu hadiza tayi tsaki ta kauda kai.
“Meya dawo dake?”
Shine tambayr farko da hadiza ta jefo mata?
“Keko hadiza ya haka baki tambayarta ya hanya”
“Jamila kimin shuru saita fada min meya dawo da ita tukunna, yanda muke cikin wannan wahalar rayuwar kika dawo ki mani uban menene? Ko baqin cikin kudin da ake dan turowa na aikin kikeyi? Shiyasa yau wata biyar kenan aka dena turowa? Ki fadamin me kikayi? Sata? Ko kisa? Don wallahi bazaki jajibo min masifa ba”
Hawaye ne ya soma gangaro mata tayi saurin gogewa “bazakiyi magana ba nace?”
Sai a lokacin sabeeha ta dago ta kalleta tace “banyi sata ba, kawai sun maido no ne,”
“Karya kike, ki fada min gaskia nace”
“Wallahi mama banyi komai ba..kawai sun maido dani ne”
Koda gigin wasa sabeeha batayi gigin fada mata dalilin dawowarta ba, bazama ta iya ba don batasan yanda zata dauki abun ba.
“Ay shikenan, tunda kin dawo zaki cii da kanki kenan, don abunci sau uku ni kaina gagarata yake,”
Tabe baki kawai jamila tayi ta miqe tace “toh ni bari na wuce gida”
Ta fita hadiza ta bita da ido, kasa zama hadiza tayi ta tashi ta nadi mayafinta ta fuce itama.
Haka sabeeha ta tashi ta tsaftace dakin kamar ya kwana goma ba a gyara ba, tayi wanke wanke sai a sannan matar gwari ta gane ta da sauran matan gidan sunata mamakin yanda ga sauya, daman tun tafiyarta basu sake jin zancenta ba, a wajen matar gwari takejin inna ta dade da mutuwa, haka ta wuni tana hawaye, ashe inna ta rasu, tayi mata addua sannan ta zauna ta doka uban tagumi tana tunani reaction din mahaifiyarta.
Kaf gidan babu wani alamun abunci a cikin dakin, gashi ko karyawa batayi ba wajen karfe biyu dataga yunwar ta mata yawa haka ta fito ta saya abuncin sayarwa da matar gwari keyi ayko taqi karban kudinta shinkafa da wake da stew babu nama, haka ta zauna tana turawa gwanin ban tausayi.
Hadiza bata dqwo gidan ba sai wajen karfe bakwai saura, koda sabeeha tayi mata sannu da zuwa ko kallon inda take batayi balle ta tambayi shin taci abunci ko kuwa.
Sabeeha ko batayi gigin zuwa inda take ba, anan kan 2 seater din ta kwanta ga uban sauro.
Bnagren taj gaba daya shi kanshi ya kasa gana kanshi kamar wanda akayi ma baki, ya kasa sukuni gaba daya, tunaninta ya gama addabarshi, idan ya tuna da labarinta da yanda tazo garin nan sai yaji wani irin nauyi a zuciyarshi, he’s trying so hard to convince zuciyarshi da qinta amma ya kasa, duk abunda tayi mashi bai kai ace ya bari an tafi da ita ba he’s not that heartless, saboda ego wani shegen abu shike sashi jin ay she deserve koma menene yayi mata, zaman gidan kam ya gama isarshi, yanajin kamar anyi isolating dinshi and he needs air, he needs to clear his mind dole ya koma uk.
Da ace ma yanayin wani abu nan kasar ne da da sauki.
Saidai kuma baisan yanda zai tunkari hidaya ba, bai taba tsallake maganarta ba, tunda tace ya dawo dole ya dawo ya hkura da komai nashi, baisan yanda zata karba al’amarin ba yanxu.
Yau suit baqi da inner white ya saka yayi kyau sosai kamar bashi ba, ya saka tie da wrist watch daya shiga da kayan sannan ya zari wayarshi da keys dinshi ya futa daga dakin, koda ya sauko kasa babu kowa wannan yasa ya fuce gaba daya ya shiga motarshi ya futa daga gidan.
Direct taheel company ya nufa straight, koda ya shugo direct wajen parking din visitors ya nufa, yana parking ya futo, yayi motar key hannunshi daya rike da wayoyinshi ya tunkari cikin reception, wallahi tunda ya fito ake binshi da kallo, mutane da dama basu sanshi ba waenda suka sanshi kuwa sunyi masifar mamakin ganinsa, kuma basuma tabbatar ko shi din bane ko bashi bane don ance ya samu tabin hankali amma gashi nan garau lafiya lau.
Anan reception ya karasa wajen rwceptionst suka gaishesa tare da tambayar wa yake son gani kuma idan yana da appointment
“Nan ya shaida masu sunanshi sannan ya buqaci ganin hidaya”
“Ceo is not on ground now..but do you have an appointment with her?”
Nan ya shaida masu bashida shi, saidai ya dan dakacesu a kira office dinta tukunna, ana kira kuwa aka shaida masu ay tana meeting haka nan ya samu waje ya zauna a reception din, after like 30 mins haka ya miqe don harya hkura harya juya kawai yaga an taho inda yake cikin sauri kuma irin manya manyan mutanen nan ne, futowansu kenan daga budget meeting wannan babban shareholder din ya hangoshi, “sir tajudeen taheel, oh my god, who kept you waiting here, bakusan koshi waye bane ba? This is the only heir of this company”
Aiko nan take kow yasha jinin jikinshi receptionish dinnan mai zasuyi banda bowing suna bata hkuri “we are very sorry sirr”
Da mamaki sosai taj ke kallonsu, don baiyi tunanin har an sanshi ba, “this way please sir”
Mutumin ya mashi nuni, gana daya shareholders suka bi bayanshi suka shiga lift.
“Were very happy to see you sir,daman we need a helping her, ay basusan ka samu lafiya ba”
Girgiza masu kai kawai yayi basuka bashi damar fada masu wajen hidaya kawai yazo ba, haka suka dunga janshi gar factory house inda mutanen dake aiki a wajen ke shirin yin yaji aiki saboda hidaya taqi kara masu albashi gashi ta kara masu aiki, ana ganinshi kuwa suka fara sauke kai aba gaishe nan babban shareholder din ya soma mashi bayani, ga abunda ke ciki ga matsalolin da suke ciki, abun yazo mashi a bazata kuma gaskia ba wannan ya kawo ba amma dake shi professional business tycoon ne tuni ya gano inda matsalr tasu take, yasa aka bashi plan book din su yayi en gyare gyare sannan ya fidda bugdet din mutanen yanda bazai shiga cikin expenses ba, kai wallahi he impressed mutane da dama don yayi abunda duk zaman hidaya akan kujerar bata iya yin shi ba, tuni ya saye zuciyar mutane, ayko wannan mutumin yana ganin anyi solving wannan matsala sai ya sake fado mashi matsalolin da suke ciki da risk din hakan don hidaya bata dauki matsalolin a bakin komai ba, kuma ko’ba dade koba jima wannan sabon partnership din datayi zai iya ruguza kamfanin gaba daya, don ta karba maqudan kudi daga partners din asunan zasu juya a cikin riba saisu fidda ma partners din.
At the end ya shaida masa kamfanin da take partning dasu wato kamfanin abdulbasit wanda kowa yasan competitor ne na taheel company.
Hidaya dake zaune a office dinta secretary dinta ya shugo ya shaida mata abund ake faruwa, unexpectedly abun yazo mata a bazata, mey zai kawoshi? Meysa zaizo? Why at this moment?
Nan ta bada umarnin abarshi yazo, ya shugo office din, mikewa tayi hankali a tashe rai a bace tace “meya kawo ka? Mene zaisa ka biyo ni har nan bazaka iya jirana chan din ba saika biyoni nan? Menene kudirinka na yin haka? Whats your intention? To show your self? Or to show the world that yourw back to normal”
Yayi mamaki sosai jin maganganun da take,”im talking to you”
Ta daka tsawa don ranta ya baci.
Zama yayi akan kujera dake facing nata ya daura kafa daya kan daya kamar wani boss, wallahi ganinshi haka datayi gabanta saida ya fadi, kafin ya soma magana “I’m sorry first love for coming un announced, i wanted to talk to you in personal and check how the business is going..”
“Check what? Suddenly youre having interest on the family business? “
Saurin katseta yayi abunda bai taba yi ba “there’s nothing wrong with that first love isn’t it? “
Kai saida gabanta fa ya fadi,ta samu waje ta zauna trying to calm her self down.
Sai yaji wani irin rashin dadi don bata taba magana ya maida maga kai tsaye ba saboda yanda yake ganin girmanta da darajarta
“I’m sorry first love, i just came here to inform you inason na koma uk but idan har baki
Amince ba babu matsala i will…”
“Yaushe zaka koma din?” Ta amsa shi kai tsaye
“Anytime..from now”
“No problem idan chan yafi maka nan babu matsala” wani irin dadi yaji aranshi ya tashi yayi pecking kumatunta ya mata sallama.
Tunda ya futa ta kama haban tana wani iri. Nazari, zuwa kawai yayi office dayayi yasa ta shuga tashin hankali inaga ance ya karba kamfanin? No impossible bazata taba barin haka ta kasance ba dole ta nisantashi da nan gaba daya har abada….
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID