← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 42 OF 66

Chapter 96

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 26 min read

Suna zazzaune a kan dining anty bahijja, maya, anne sai hamad da shugowanshi kenan,suna karin kumallo cikin kwanciyar hankali, tunda suka zauna bahijja ta lura da yanayin maya daya sauya gaba daya, hankali kamar baya jikinta ta tafi wani tunanin daban, kallonta bahijja tayi tace “baby eat mana..ko bai maki ba? You want something else?”
Daga hamad har anne babu wanda ya dago ya kallesu, sai wani lallabata take kamar wata karamar yarinya, hamad ya miqe ganin time dinsu na neman kurewa.
“Go and call fatima time yana kurewa” ya fada yana kallon maya, “bazanie ba yau”
“Are you not prepping for exams?Ba test zaku fara ba next week?”
“Mummy please i want to be with you the whole day”
Murmushi bahijja tayi ta dubi hamad tace “ku tafi kawai hamad”
Anne da bata tanka su ba tun daxu ta dago ta kalli mayar tace “tashi ku tafi”
Kwalla ce ta soma zuboma maya, harga allah yau batayi niyar zuwa school dinan ba kwata kwata, ganin tana son yin hawaye yasa bahijja cewa “anne a barta monday zaita je tunda yau friday and its a short day”
“Bakiji me hamad yace bane?“
Ganin yanayin anne ya sauya yasa bahijja yin shuru dole maya ta miqe ta wuce sama don shiryawa harda hawayenta.
Har bahijja ta miqe anne ta dakatar da ita, “binta zakiyi? Saboda me?”
Komawa bahijja tayi ta zauna hamad kuma ya fita.
Yana fita ya sameer ya shugo main house din don gaisheda anne, duk safiya yake zuwa gaisheta kafin ya tafi office.
Hamad na karasowa wajen moto ya tadda sabeeha tsaye, sai laila ya bude masu kofa suka shiga kafin maya ta futo daga baya rai a bace.

Ya sameer na zuwa yaga yanayin anne ya gane cewa ranta a bace yake, bahijja ko taqi yarda ta hada ido da ita don anne nada zafi sosai.
Yana gama gaisawa dasu ya fita anne ta wuce sama bayan ta buqaci bahijjar tabiyo bayanta.
Suna hawa saman anne ta hau kanta da fada sosai, “wannan wani irin shashanci ne bahijja? Daman ku kuka lalata yarinyar nan? Zatayi abunda taga dama bazaku mata fada? Zaman kasar waje hauka ne eh?”
Shuru bahijja tayi ta kasa cewa komai jiki a mace sai bata hkuri kawai tayi ganin yanda ranta ya baci.
Koda tabar part din anne ta nufi inda ta sauka anan saman wayarta kawai ta zaro ta soma dilaing number majeed.

Bangaren taj bayan yabar wajen nanna part dinshi ya koma abal yazo suka dunga hira sosai yana nuna mashi abubuwan daya danganci kamfanin sa a laptop, lokacin lunch nayi kuwa anne tasa rabi ta aika akai mashi part dinshi.
Anty fadila ma ta aiko masa da tuwo da miyan egusi mai dadin gaske.

After 2 dayss
Cikin kwana biyun nan taj ya sake sosai da mutanen gida, abal is one if his favorite don suna tare dashi, a cikin kwana biyu anne tasa ya sameer ya kaishi kamfaninsu ya gani, haka ya zaga dashi ko’ina yaga yanda suke tafiyar da kasuwancinsu.
Tsakanin shida mahaifiyarshi kuwa sai godiyar Allah, minti kadan zata kira taji ya yake me yake, haka zalika shima zaije wajenta sau nawa, haka take janshi sosai a jiki don sanin komai game dashi.
Kwata kwata batayi kokarin tambayarshi rayuwar da yayi a saudi ba bayan tafiyarta, da abunda ya shafi mahaifinsa harma da yan uwansa, she’s trying so had ta mance da komai.

Maya ko tana tare da mummy ta kullum, qin yarda ma tayi ta koma bedroom dinta, inda mummynta ta sauka nan ta dawo for the mean time.
Sabeeha tun ranar da suka hadu da rabi a sama ta shaida mata ta daina kwana wajen nanna din tunda ta smau sauqi wannan yasa shugowarta main house da part din nanna ya ragu ba kamar da ba.
Kullum tana bangarensu, babu abund ake fiddata sai aikin da zatayi na gida, data zauna a daki ko karatu takeyi na shirin test da zasu fara, gaba daya ta maida hankalinta wajen karatun yanda ya kamata.
Duk sanda ta shugo kitchen ko sai taji yan matan gidan nan na maganar baqon daya zo wanda suke alaqantashi da dan nanna da sukaji ana fada da yanda suke zuzuta siffarshi kamar ba bahaushe ba, ba yawan shigowa cikin gida take ba, balle zagaye cikin sauran apartment din don bata da alaqa da wajen, aikinta na nan kirchen tana gamawa daki kawai take komawa, gashi ita ba ma’abociyar shishigi ba wannan yasa bata famu da sanin mutanen gidan ba banda ya hamad.

Yau ta kasance monday morning…
Tun wajen asuba data tashi bata koma ba take karatu, gudun kar mamanta ta tashi yasa ta wuce backyard ta zauna wajen kujerun dake wajen, dake ko’ina na gidan akwai haske kamar rana.
Bata tashi daga wajen ba har saida gari ya soma haske, ta koma daki ta aje littafanta lokacin yan aikin gidan kowa ya rigada ya futo duk sun fara aiki, kallon inda hadiza ke kwance tayi, mayafin da take lulluba dashi sabeeha ta jawo mata ta rufa mata ganin ya yaye kafin ta futa.
Daga shugowarta hadiza taji motsinta ta farka, tabi kofar data futa da ido, Sai a lokacin tayi ta tashi tayi sallah.

Sabeeha na shugowa kitcwhn ta gaisheda rabi da sauran waenda ta tadda a wajen sannan ta basu helping hand.
Ana gama breakfast suka soma fifitowa da avubuwan karin kumallo.
Su bilki na gaba da warmers while sabeeha na biye da suka aje kafin su juya don sake kwaso sauran warmers din.
Adaidai lokacin nanna ta sauko kasan cikin shiri, bahijja ma ta sauko kasan, suka nufi dining.
Bilki dake kokarin komawa kitchen ce tace “sabeeha dan allah jera plates din bari na dauko flask”
Da toh kawai ta amsa ta tana kokarin jera plates din su nanna suka karaso.
Tana ganin isowarsu tayi saurin rissinawa tace “ina kwana nanna”
Murmushi nanna tayi tana mai dubanta tace “lafiya kalau fatima, daga tayani kwana kika gudu kuma,”
Dan dagowa sabeeha tayi tana dan murmusa tace “anty rabi ce tace na dawo kasa”
“Toh ay shiknan, kwana biyu da ba’ayi min tausa ba sai naji kafar na min zugi kuwa”
Sunkuyar dakai saveeha tayi tace “in muka dawo daga school zanzo nayi maki”
“Toh allah ya kaimu, allah ya bada sa’a”
Nanna na rufe baki bahijja data zuba ma sabeeha ido ta kasa daukewa tace
“Ina muka samu yarinya haka”
Dan kallonta sabeeha tayi kafin tayi saurin rissinawa har kasa cikin ladabi tace “ina kwana hajiya”
“Lpy kalau”
“Yar hadiza ce ay,fatima sunanta” nanna ta bata amsa.
“Wata hadiza kenan nanna?”
Sabeeha najin sun fara magana bayan sun nufu mazauni tayi saurin juyawa ta wuce kitchen.
“Hadizar dai wadda kuka taso tare tar wajen inna mai aiki”
Zaro ido bahijja tayi da mamaki tace “hadiza dai?”
“Itafa rayuwa dai sai godiyar allah, innar ma ta rasu, ashe anan bayan gari suke zauna cikin ikon allah kawai sukazo bikin sufyan,“
Girgiza kai tayi da mamaki bayan ta gama sauraron.
Sallamar taj tasa suka juyo gaba dayansu, nanna ta sauke murmushin su na manya, anty bahijja tace “oh rabona dakai tun ranar birthday nanna,” da turanci tayi magana wannan yasa ya danyi murmushi har hakoransa na futowa yace “good morning a natse, “morning how are you”
“Hamdullah!!” Ya bata amsa tare da karasawa wajen nannna suka gaisa ta tambayeshi how was his night.
Yauma nanna ce tayi serving dinshi bahijja na kallon abun gwanin ban sha’awa, sai suka burgeta sosai.

Saukowa ta soma yi daga bene hannunta rike da wayanta sai jakarta, gaba daya hankalinta na kan waya wannan yasa bata lura da waenda ke dining ba.
“Baby kin sauko” bahijja tayi magana.
“Yes mummy, good morning!!”
“Morning dear,”
Dagowa tayi karaf idanunta ya sauka kanshi, yana gefen nanna, yauma yana sanye da jallabiya, gashin kanta ya kwanta lub kamar na jariri, ta kasa dauke idanunta.
“Maya..come have a sit”
Nanna tayi magana, tayi firgigi ta kalleta “good morning nanna”
“Morning” ta amsa ta
Jan kujera tayi daidai da inda yake, tunda ta jaraso bai dagoba balle tasa ran ya kalleta, yanada wani irin kwarjini, haka nan tana ganinshi komai ke kulle mata.
“Baki gaida uncle taj ba” bahijja tayi magana tana kallonta ganin irin kallon da take mashi.
Muryanta ba karyewa tace “good morning uncle taj”
Kallo daya ya mata ya kauda idanunshi tare da dauka glass of orange juice dake gabanshi kamar baison magana yace “morning..” kai tsaye.
Wallagi jintayi kamar an tsundumata a aljanna, muryanshi akwai dadin gaske.

Yauma dai ba wani cin kirki tayi ba don gaba daya hankalinta ta tattara zuwa gareshi kamar mayya, shiko baima san da ruwanta ba a wajen kamar she doesn’t exist gaba daya.
Wayanshi daketa faman vibration a gefen table daya aje ne ya kalla ganin sunan dake kiransa, tunda yaga kiran merk babu qaqqautawa yasan akwai matsala wannan yasa yayi excusing kanshi ya miqe nanna ta bishi da kallo, yana tashi ko minti biyu batayi ba itama ta miqe, “mummy byee”
Ta futa, “allah ya tsare ta amsa ta.
Gaba daya daga main sitting room ya futa zuwaga harabar wajen shugowa cikin gidan don a tsayen nan yana hango motocin gidan dake surrounding din wajen shugowa, da alamu ma fita za ayi da motar.
Wayar ya daga tare da kaiwa kunnenshi, maya dake sauri sauri ta karaso inda yake tanajin yanda yake zuba turanci tabi bayanshi da kallo, hes so huge, kai yana burgeta, wani irin kamshi yake mai dadi gaske, ya wani irin saka hannunshi daya cikin aljihun jallabiyan, daya kuma ya kai wajen kunneshi, ga slippers din kafafunshi sun karbeshi sosai saboda hasken fatarsa.
Kai dole ma tasan yanda zqtayi ta zama so close to uncle taj, he doesn’t seem friendly amma duk yanda zatayi saitasan yanda tayi ta zama close to him.
Ta gefenshi ta raba kamar zata wuce saita juyo fuskanta dauke da murmushi tace “bye uncle”
Shi bai kalleta ba shi bai amsa wayar da ake mashi ba saima kurama waje daya idanu dayayi.
Daga chan nesa kuwa sabeeha data biyo ta bayan backyard, direct ta wuce wajen mota, ta bama inda yake tsaye da maya baya, a daidai lokacin data juya allah ya bashi ikon kallon direction din wajen saidai kuma side viewdinta kawai ya gani kafin ta juya baya tana sanye da abaya baqa tayi rolling kanta da mayafin.

Gaba daya tunda ya zuba ma wajen idanu ya kasa daukewa kamar wani wanda ke nazari yana calculating abu, height dunta exactly irin na sabeeha harda jikin ma.

Maya na ganin inda yake kallo kamarma baisan tana magana ba taji wani irin maqoqon abu a zuciyar ta.
“Are there? Hello sir” maganar da akayi daga wayar ne yasashi maida hankali a wayar yace “yes yes go ahead”
Jiki a mace maya ta wuce wajen motar, daidai nan hamad ya karaso tare laila, sabeeha dake tsaye jikin motar wajen budewar baya tana jiran isowar su batayi auni ba kawai taji an wani tureta gefe an bude motar, har littafanta na watsewa a kasa.
“Excuse me!!!” Maya tayi magana tare da banko kofar, hamad bai lura dasu ba don sauri yakeyi don ya samu ya saukesu.

Tunda ya aje wayar da yayi da merk ya koma ciki nanna tace ya je ya shirya zasu fita tare da ita.
It was a pleasant day for him, nanna tayi driving motar suka wuce har office dinta, inda take gudanar da business dinta, tanada cute iffice da facilities sosai daman tana harkar interior,kuma da manyan companies take dealing idan an bata kwangila irinsu nnpc da hotels.
Sun dade sosai kafin yamma su dawo.

4 nayi hamad yazo daukansu tare da abal daya damu saiya biyosa.
Laila ce ta fara fitowa tana hango abal a tsaye bakin mota tace “ya hamad da wannan futsararran kukazo?”
“Ke ban girmeki ba kike cemin futsararre?”
“Waka girma din? Age dinmu daya”
“Kamata yayi ki dunga gaisheni kina kirana da yaya tunda na fuki da 5months”
“Wallahi karya ne mami tace shekarunmu daya ao don’t feel like your head is big”
Daidai nan maya ta karaso, abal ya kalleta kafin yace “hey!!! Ashe kin dawo nigeria da zama? Lol how do you cope?”
Wani irin kallo ta mashi kafin tace “what sort of a question is that? Do i look depressed to you?”
Abal najin haka yasan daman mai hali ay baya chanza halinsa, tun tuni daman yar masufa ce tun suna yara, shiyasa baya ma shiga har karta.
“Nawa for you…” ta fada yana galla mata harara.

Tsaki tayi ta bude kofar baya ta shiga, sabeeha daketa faman sauri sauri har tana haki ta iso itama, “salam! Ina wuni ya hamad”
Ganin yanda take panting yasa hamad cewa “wa alaiki salam, why are you panting”
“Inata sauri ne karna bata maka lokaci” ta bashi amsa a natse babu hayaniya, abal ya zuba mata idanu sosai yace “ya hamad who’s that?”
Ko kallonshi baiba yace “get in”
Bude gaba abal yayi wannan yasa sabeeha tsayawa sarere ta rasa ya zatayi, saida taji horning yasa ta saurin bude baya batama san maya ce a ta wajen ba tana bude wa ta bita da wani makirin kallo kamar a kusa take da ita tace “are you mad??? Badai tunanin zama tare damu kike ba?”
“Fatima get inn!!!” Hamad ya bata umarnin haka
“Ya hamad wallahi wannan qazamiyar yar aikin bazata zauna kusa dani ba saidai ta nemi abun hawa”
“Saidai ke ki sauka ki nemi abun hawan, don’t waste my time”
“Wallahi bazata zauna a bayan nan ba, munafuka kawai kina wani sunne kai kamar wata ta Allah”
A fusace ya juyo kamar zai maketa yace “don’t you ever insult her again, in kika sake sai ranki yayi mugun baci”
Dake bata da kunya kuma ba sanin darajar babba take ba wannan yasa ta cewa “wallahil azeem bazqta zauja a baya ba,who is she not be insulted? Ba yar aikin bace? Yar wanke wanke”
Ay baisan sanda ya futo ba rau a bace ya bude seat din baya da take zaune yace “get outttttt, fita min a mota”
Jikin maya har tsuma yake tsabar masifa, ya dizgata gaban yar aiki, “bazan futa ba, wallahil azeem bazan futa ba akan wannan abar zaka sani na sauka a mota? Motar ta ubanta ce?“
Hannu ya daga zai kwasheta da mari laila tayi aaurin interfeing tace “yaya dan allah kayi hakuri, hannunshi gar karkarwa yake tsabar bacin rai,
“Ay wallahi idan ka mareni saina rama” kiri kiri fa take magana a gabanshi kamar wani sa’anta kai yarinyar nan batada kunya sam sam, very disrespectful,
“Yaya bari na futo na zauna a bayan tare dasu”
“No karka sake ka futo,” hakad ya fada yana kallonshi, kafin ya maida dubanshi ga maya yace “ke motan na ubanki ne?”
“Ni ka zaga saboda wannan?”
“In ya making zafi zaki iya futa, find your way home”
Ay ko yana rufe baki ta bude kkfar ta futo rai a bace ya kalli sabeeha babu wasa yace “shiga”
Jiki na bari ta shiga fa zauna inda maya ta tashi, suka wuce, akan idanun maya ta shiga motar ta zauna a seat dinta.
Suna barin wajen maya ta zaro wayarta tayi dialing number mummynta.
Bahijja dake tare da fadila suna hira tana ganin call din mayar ta dauka taka dauka ko sun dawo ne bata ganta ba,“ yes babu…”
“Mummy……..”
Miqewa bahijja tayi tana sauraron wayar nata tace “calm down ki fada min menene kukan me kikeyi?”
“Mummy na fada maki basa sona, kowa baya sona ni bansan mey nayi masu ba, ya hamad,sun tafi sun barni anan saboda yar aikin nan, har marina saida yayi, wai na fita a mota na nemi mai kawoni”
“Shi hamad dinne ya mareki?”
“Eh, sun barni a school babu kowa, mummy tsun tsaneni kowa na gidan nan, marina yayi wai na fita a mota tund aba motar ubana bane”
ta karashe tana fashe wa da kuka ta katse wayar.
Kiran duniya bahijja tayi mata wayar a kashe tuni hankalinta ya tashi.
Fadila data lura tace menene “wai hamad ne ya barta a schoo ita dayal”
“ hamad din?”
Ay bata tsaya saurarobta ba ta miqe tace “bari naje school din”

Futowa tayi tasa cikin drivers ya dauketa suka wuce school dinsu gaba daya hankalinta a tashe.
After few minutes da futarta saiga su hamad sun dawo, gaba daya daga laila har sabeeha da abal jikinsu duk yayi la’asar gaba dayansu.
Hanad ko hes fed up with her drama da rainin ta wannan yasa yayi maganinta, gaba daya futoqa sukayi ya rage hamad dinne kawai sai sabeeha data kasa tafiya ta tsaya ya futo.
“Ya hamad dan allah kayi hkuri mu koma a daukota”
Yanda take magana jikinta na bari yasashi gane cewa a tsorace take
“Go inside i will get her back”
Wani irin ajiyar zuciya ta sauke badon san rabta ba ta shiga ciki.

Wayarshi dake ringing ya dauka ganin sunan mamin shi, yana dagawa ta sima fada “kai kana ina? Me kayi ma maya? Meysa ka barta a school eh?
Haka fadila ta soma balbaleshi da fada sosai batama tsaya sauraronsa ba, karshe ma dayaqi kulata kashe wayar tayi.
Kalamanta na karshe yasashi shiga motar ya futa daga gidan, wallahi badan mami ba bazai dauko ba yau dinnan saidai tasan yanda zatayi.

Bahijja na zuwa school ta samu mayar zaune a gefen school entrance kai kace wata abar tausayi ce, tayi jabe jabe da hawaye.
Jikin bahijja har rawa yake, tana kaunar yarta kamar me shiyasa ko kukanta batason jin ko kadan ita kadaice allah ya basu, kaunar da take mata babu measures.
Tsakanin da uwa sai Allah, harga allah bahijja taji zafin abunda hamad yayi na barin mayar, saita fara tunanin toh kodai bason zaman mayar ake a gidan ba, tun ba yanxu ba tasan anne bason mahaifin mayar take ba, har lokacin tana tsoron kar avun ya shafi yar tata, sai yanxu take ganin abun kamar haka ne, ba sau daya ba ba sau biyu ba maya ke kira ta tana complain ba a sonta a gidan an takura mata.

Koda suka shugo gida gaba daya kowa na zazzaune a sitting room, fadilana gefe babu abunda take sai harara hamad din don anne tasashi ya dawo gida tunda bayijja ta tafi daukota, kuma kiri kiri anne ta hana fadial ta mashi fada har suka iso.
Maya na ganin kowa a zazzaune harda anne take tasha jinin jikinta.
Da ta wani maqale bahijja gwanin ban tausayi kai kace yankata akayi aka watsar.
Zama sukayi anne ta dubi hamad tace “babana meysa ka barta a school?, nasan haka kawai bazaka barta ba tunda kaina bama jagorancin kula dasu da harkar makarantarsu.”
Sunkuyar da kanshi yayi ya kasa dagowa yana jin kunyar anty bahijja sosai, sai yaji dama bai barta ba wallahi.
“I’m sorry raina ne ya baci hakan bazata sake faruwa ba”
Anne tace “tayi maka rashin kunya ne?”
Bai bada amsa ba yayi shuru kawai anne ta kalli mayar babu wasa tace “kinyi mashi rashin kunya ne?”
Kukan munafurci ta fara “ni ban mashi rashin kunya ba, kawai sabd nace fatima bazata zauna inda nake zaune ba shine yace na sauka tunda ba moton ubana bane” ta karashe harda share kwalla.

Laila datayi tsuru anne ta kalla tace “ke me tayi mashi?”
Yanda anne ke tambayr me maya ta mashi ba tare da sauraron abubuwan da ya fada ma mayan ba yasa bahijja jin babu dadi.
“Mun shiga mota ne sai yaya yace fatima ta koma baya saboda abal na zaune a gaba shine maya tace bazata zauna damu ba,”
Dan dakatawa tayi ganin irin kallon da maya ke mata kafin ta cigaba, “maya was insulting towards sabeeha tace wai ita dake yar aiki bazata zauna damu ba tunda ba ubanta ya saya motan ba, shine yaya yace karta sake zaginta..shine shine…”
Ta kasa karasawa anne ta sauke ajiyar zuciya tace “a gidan nan ba’a goranta ma na kasa damu, bama wulaqanta wanda ke hidima damu, idan yar wanke wanke ce itama iyaye ne suka haifeta,ni nasan haka kawai hamad bazaice ta sauka motar nan ba, ga abunda tayi nan,ninasa yarinyar nan tana binku makaranta don itama yace kamar kowa anan, don bata da gata bashine ya baki liberty din yi mata gori ba, karna sake jin haka, karna sake.. this should be the last time da zan sake jin haka”
Maya ta fashe ta kuka sosai ta shiga jikin mamanta bahijja ta rukota zuciyanta na mata daci, judgement din bai mata dadi ba ganin yanda mayar ke kuka.
“Amma anne ba laifi bane dan tace bazata zauna da yarinyar ba, tunda su yan gi…”
Wani irin kallo anne ta mata dayasa ta rufe bakinta kawai, anne ta miqe rai a bace ta wuce sama.
Fadial ta kalli hamad tace “kai kuma wani iri babba ne? Are not supposed to protect them? Ka bani kunya”
Tana cikin yi mashi fada bahijja ta miqe da maya suka wuce sama, fadila saitaji babu dadi kwata kwata, bahijja akwai son yaya kamar me, bataga laifinta ba tunda maya kawai allah ya basu.
Suna hawa sama bahijja ta danna ma majid waya, ta insa take hawa ba tanan take sauka ba, daman tund amayar ta dawo shi take blaming don shine ya turo ta don yayi punishing dinta.
Tun daga ranar maya ta kullaci sabeeha sosai aranta tsanarta ta tsananta sosai ba kadan ba.

Bayan kwana biyu.
Yau yayi daidai da saura kwana biyu komawan bahijja saboda hutun data dauka daman just is just a week ne, babu abunda take sai tunanin komawa da maya kawai chan don hankalinta yafi kwanciya saidai batasan ta inda zata bulla anne ba.

Hadiza na zaune a daki, yau kusan kwana nawa rabonta da futowa duk a sunan wai batada lafiya, wanda ba hakan bane futowa ne kawai batason yi don karsu hadu da bahijja.

Tana zaune misalin wajen karfe biyar daidai maya ta kira ta a waya, kamar kullum jiki na bari ta dauka, tana dagawa takai kunne, “meysa baki zo kin gyara min part dina ba yau kusan kwana nawa”
Da tsawa tayi maganar wanda hakan yasa hadiza saurin miqewa zaune tace “yi hkuri hajiya ta takaina, banajin dadi ne kwana biyu shiyasa amma bari nazo”
“Ah ah ki zauna ki tura yarki tajw ta gyara kin part din sannan kisa ta kwaso kayana dake part din mummy a wankesu”
“Toh yanxu ma kuwa yi hkuri kinji”
Kit ta kashe wayar, sabeeha na shugowa da plate din abunci hadiza tace “aje ki wuce sama ki gyara part din maya sannan kije bangaren ….”
Shuru tayi tama rasa me zata ce tace “ki tambayi rabi ta nuna maki bangaren mamanta ki kwaso kayan wanki kizo ki wanke su yanxu yanxun nan”
Aje abuncin data debo tayi a kasa, jiki a mace yau ko lunch batayi ba sbd haya batazo ba daman ita ke saya masu, gashi ta kwaso gajiya sosai.
Saman ta wuce allah yaso daidai lokacin dayar kai aikinsu dake gyaran sama ta futo nan ta tambayeta ta nuna mata.
Kamar yanda hadiza tace tayi hakan tayi ta gyara ko’ina kafin ta futo ta shiga na mummyn maya ta kwaso kayan laudry din sannan ta futo ta sauka kasa ta fara wanki.
Saida ta wanke tas gaba daya har ana kiran sallah kafin ta samu tayi sallah taci abunci ta fito backyard da littafinta tana karatu.
Motar da suka fita ne da isa ta tsaya a harabar gidan maya ta futo da kayanne shopping da yawa da mummynta tayi mata, murna take soaai ka kadan ba,bahijja ko dadi takeji ganin yar tata na cikin farin ciki.
Shugowa sukayi daga ciki babu kowa a kasan bahijja ta dubeta tace “ jeki sama bari na leka part din mami ko”
“Okay” maya ta bata amsa, saman ta wuce ita kuma ta futa.
Bata dade ba ta sauko kasan tana dube dube kafin ta wuce hanyar kitcwhn har zuwa bangaren su sabeeha,koda ta shugo cikin dakin babu kowa wannan yasa taji wani sanyi aranta.

Tana gab da futa daga dakin hadiza ta fito daga toilet.
“Subhanallahi nema kike baki ganni ba ko? Kinga wanka na shiga ne, ay da baki wahalar da kanki kin zo ba!!!”
Yaqi mayar tayi ta kalleta tace “inason fresh pineapple juice yanxu”
“Toh bari nazo nayo maki, shikenan ko akwai wani abun?”
“Ah ah babu shikenan” tana fadin haka ta futa da sauri.
Tana futa ta sauke ajiyar zuciya tare da smirking allah kadai yasan abunda ke ranta.

The next day!!!!
Tun daga ranar da abunnan ya faru sabeeha ke dari dari da al’amarin maya, wallahi badan dole ba bata son ma zama inuwa daya da mayar.
Bangaren taj ko yanxu babu abunda ke addabarsa kamar tunanin sabeeha, daga yaci ya koshi ya kwanta shikenan sai tunaninta saima tunanin ya zamana kamar yafi na da, yanajinta kamar tana kusa dashi jikinsa na bashi hakan.

Gashi ya kasa kiran khaal ya tambayeta akanta, inama zai iya, gaba daya neman ta ya rasa ta ina zai fara.
Wata dabara ce tazo mashi, mutun daya yazo ranshi wato salim, ya buqaci ya nemo mashi agencies din dake nan abuja dake kai domestic workers kasashen wajen, koda ya sashi nema mashi bai tsaya wani bata lokaci ba ya nemo masa few daga cikin waenda ya buncika.
Har gida salim yazo suka fita tare, daga ranar ya fara stepping forward wajen neman sabeeha, har zuwa lokacin kuwa hes guilty if abubuwan dayayi mata.


Anty bahijja nata faman shirye shiryen komawa gobe, duk yanda taso tafiya da maya kasawa tayi saboda karatunta da kuma fadan da sukayi da majeed dayace bai amince ta dawo da ita ba, kuma idan tayi haka batayi kara ba sam sam anne bazata ji dadi ba.
Dole ta hkura ganin kamar mayan ma bata nuna tanason binta ba don tasan washe gari zata tafi, dubaga yanda take ta son komawa chan abaya.

Shugowa maya tayi da wayanta a hannu ganin mummynta na shirya kaya yasa ta marairaice “mummy please karki tafi,ki bari bayi hutu aaimu tafi tare”
“Baby i can’t, inada aiki sosai i cant abandon mu duties kinji”
Shuru maya tayi batace komai ba har bahijja ta gama prepping kayan nata ta bude handbag dinta don kwaso jewlries dinta tasa a box dinsu.
Da mamaki take zazzage jakar surprisingly ganin bataga bangle din da dadyn maya ya saya mata ba,bangle din na diamond ne yawanci yana hannunta koda yaushe bata cika cireshi ba.
“Mummy are you looking for something”
“Yea baby bangle din dake hnnuna koda yaushe i cant find it”
“Wannan diamond bangle din? Diamond Bulgari?”
“Yes…bade saceshi akayi ba?” Maya tayi magana tana tayara duba kayan.
“I kept it here jiya kafin mu fita shopping”
“Hold on..jiya nasa yarinyar nan ta dauka min kayana anan badai ita ta dauka ba?”
“Wa kenan? Who would do such a thing a thing”
“Hmm daman ta taba sata a school wallahi mummy, definitely itace”
“Wacece ita din?”
“Wanna yar aikin mana fatima, ai wallahi saita futo dashi.
A fusace maya ta sauko kasa jiki na bari bahijja tabi bayanta tana kwalla mata kira.
Bata tsaya ko’ina ba sai bangaren su hadiza tana zuwa ta banka kofa kamar zata balla,
“Wallahil azeem saikin fito da diamond din da kika dauka barauniya”
Hadiza dataga shugowa tana tsaka da figar kaza tana ganinta ta miqe,”meya faru karamar hajiya?”
Sabeeha na daga zaune tana kokarin yin shimfidar kwanciya.
“Dallah yi mana shuru, idan ta sato ke zata kawoma ay wallahi bata isa ta dauka abun mummy na ba karyanku keda ita”
Ta soma buncike dakin nasu tana watso da kayansu, daidai nan bahijja ta karaso dakin tana maya, tana kicibus da hadiza ta tsaya, hadiza tayi saurin sakin kazar dake hannunta, bahijja ta hade rai sosai ba kadan ba kamar bata taba dariya ba.
“Mummy i told you…gashi nan gashi nan..”
Ta fada tana fidda bangle din, “a cikin nan na ganshi mummy”
Hadiza da abun kunya ya mata yawa bataso bahijja ta tsince ta a wannan yanayin ba na qasqanci.
“Daman na fada maki mummy yarinyar nan barauniya ce itace ta dauka ta kawoma mamanta, because she is jealous of me, tana jin haushi allah bai basu daukaka ba”
The fact that bangle din daga majeed ne kuma abune datake treasuring sosai yasa ran bahijja baci ta kalli sabeeha tace “ya akayi wannan yazo nan dakin?”
Jikin sabeeha ya soma tsuma tsoro ya bayyana a fuskarta abunka da someone that is innocent.
Hadiza ta cin mutun ya mata yawa ta rasa ina zata saka kanta ta dubi sabeeha tama kasa ce mata komai saida maya tace ,
“Mummy why would you ask, jiya nace taje ta kwashi laudry na a wanke propably ta haka ta samu damar dauka”

Sai a lokacin hadiza ta fuskanshi abunda ke faruwa ta dubi sabeeha “dan abu kaza kazan ki ya akayi abunnan yazo dakin nan eh????, banace karki sake ki jawo min abun magana ba”
Sabeeha data fara hawaye ta kalli maman nata tace “na rantse da allah mummy ban dauka komai ba, ban dauka ba”
Rufeta da duka hadiza ta soma yi kamar zata illata, “yau saikin fada min yanda akayi kika dauko wannan abu”
“Kibar dukanta” bahijja tayi magana tace “ay ba lallai laifinta bane qila tarbiyar da kika mata kenan”
Kai wannan abu yayi ma hadiza zafi sosai ba kadan ba, “maya lets go”
Suka fita gaba dayansu,hadiza ta dubi sabeeha tace “na rantse da allah gobe goben nan zan maidaki lafiya babu makawa, shegiyar yarinya haihuwar ki bata amfane ni da komai ba, fita ki bani wajee”
Ta daka mata tsawa tana fita ta soma kiran jamila a waya tana dauka kamar tayi hauka ta soma magana “jamilaaa…”

Sabeeha na fita daga dakin tayi kicibus da maya data dawo, kallonta tayi sai kawai ta soma dariya wani irin dadin takeji sosai,
“Ay wallahi bakiga komai ba, ni nan sainayi sanadiyar barinki gidan nan, this is just the beginning”
“Meysa kika tsane ni me nayi maki?”
“Ke har kin isa na baki dalili?”
Murmushi sabeeha tayi tace “takamarki bata wuce saboda kunada arziki ba, amma inaso ki sani baki fini da komai ba, kina ganina a wulaqance ko? Toh babu wulaqattace sai wanda Baisan darajar dan adam ba,”
Mari maya taso yi mata ta kama hannun nata gamm tana kallon cikin idanunta babu tsoro tace “kinyi kadan ki taba wannan fuskar, mahaukaci mara tunani”
“Ubanki ne mahaukacin, auu sorry qila ma
Bakida uba”
Ji kake tassssss sabeeha ta dauketa da mari, har sharin hannayenta na futowa akan fuskar maya.

Saida maya ta daidaici isowr mutun kawai tayi baya ta fadi kasa, da gudu yar aikin dake labe ta wuce don kiran maman maya.
Suna isowa maya data kama wuyanta tana kakakin amai sabeeha na tsaye na kallonta tana kallon makirci iya makirci.
Bahijja na ganin maya a kasa hankali tashe ta tunkareta “baby menene? Menene?”
“Mummy shake min wuya tayi wai saita kasheni saboda na tona mata asiri”
Bahijja batayi wata wata ba ta dubi sabeeha ta kwasheta da mari tass tass, wajen sau uku, idanunta sunyi jaa sosai sabeeha tayi baya zata fadi
“How dare you lay your hands on her eh???? Ina uwar taki hadizaa hadizaa”
Rabi dataji hayaniyar tayi yawa sosai ga abunda ke shirin faruwa tsoro yasa ta wuce sama don shaidama anne abund ake faruwa.
“Ay daman nasan zuwanki bazai taba zama alkhairi ba, a da chan baya ma bai zama alkahir ba balle yanxu?”
Maganganu fa sosai bahijja keyi tsabar bacin rai, masu aikin gidan kowa yabfito, hadiza kamar ruwa ya cita.
Bahijja nada ahkuri sosai ba kadan ba amma idan aka tabota babu sauqi tanada zafi sosai, musamma akan maya da abund aya shafi maya.
Wayanta dake hannunta ne ya soma ringing ta kaasa dauka saida rabi ta karaso tana bata hkuri ta miqa mata wayanta tace “ hajiya na magana”
Ko kallonta bahijja batayi ba taja maya suka wuce sama.
Suna zuwa ta tabbatar mayar is not hurt kafin ta wuce wajen anne.
Tana zuwa batama bari anne ta tambayeta meya faru ba ta soma magana “ anne wani ganganci ne yasa kikabar hadiza zuwa agidan nan a karo na biyu? Bayan kinsan abubuwan datayi min a baya? Bama ni kadai ba wani abu hadiza batayi ba? Amma a karshe taci amarnarmu,? Wajen zama da aka basu bai isa ba abu har yakaiga sata yanxu yarta na kishi da maya? Har tana ikirarin zata kasheta? Toh wallahi saidai subar gidan nan kona dauki maya mu koma”
Saida anne ta barta ta gama babatunta tass har tana cewa “ ba tun yanxu ba na lura ba indai akan abunda ya shafi maya ne akwai banbanci akan komai ma, at this young age har tasna an takurata an tsaneta, dukdan saboda tana ganin banbanci, kuma badan komai saidan ubanta bare ne a cikinmu, zan dauki yata mu koma kawai bazan iya barin ta ba”
Ran anne ya baci sosai ta dakatar da ita “lallai bahijja kin bani mamaki, ashe kece kikayi contributing wajen lalacewar yarki, kikace an tsaneta? An takurata? Duk abund aya shfeta akwai banbanci saboda ubanta ko toh bari kiji, banbancin daga tarbiyyar da kuka mata ne,baku mata tarbiyya mai kyau ba sam sam batasan darajar dan adam ba dana gaba da ita, a kananun shekarunta hartasan taje hotel? Duk cikin zuri a ta wake zuwa hotel da wani eh???? Sau biyu ana kawomin wannan korafin, what did you do as a parent about her upbringing eh?
You failed bahijja as a mother you failed saboda son yarki ya rufe maki ido, abun ai ba hauka bane, maya is going no where, idan har nina haifeki baki isa ki tafi da ita ba anan zata zauna,”
Idanun anne yayi jaa sosai tsabar bacin rai, bahijja ko jikinta lokaci guda yayi la’asar da jin batun anne babu abunda take sai innalillahi, maya a hotel? …


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵 🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 42 · 0% Book details