← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 14 OF 66

Chapter 68

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 31 min read

Tunda ya shigo bedroom din ya zauna babu abund ayake sai nazarin abunsa kunnuwanshi suka jiyo mashi, yana nan zaune ta shigo bedroom din, tunda ya dago yake kallonta ya kasa dauke idanunshi, yaqi yarda da abunda zuciyarshi ke raya mashi, “she just saved me”
Abundaa keta faman yawo a zuciyarshi kenan, take memory din lokacin dayaci peanut a dining ya fado mashi,abun kamar an bude mashi faifai lokacin haka yake gani, fuskarta na mashi flashing lokacin da take kuka, he was struggling sosai nunfashinsa na fira kyar, abunda yafi daure mashi kai kuwa yanda yafa kusan kowa na zaune a dining din lokacin da abun ya faru, kuma sabeehar ce da kanta ta saka mashi peanut din, lokaci guda ya shiga confusion again, maganganun da akayi a lokacin duk sun dishashe mashi, dukda yaga itace ta shafa peanut din a cikin bread din da yaci hakan baisa zuciyarshi ta aminta da cikin rashin sani tayi hakan ba, don he can clearly see yanda take faman kuka, sautin kukan ta alokacin yana echoeing akanshi, yayi zurfi sosai cikin tunanin nashi baima ji maganar data fara yi mashi ba saida ta sake cewa, “didi!!!!”
Yaune second time dayaji ta kirashi da wannan sunan tun bayan a asibiti, saurin rintse idanunshi yayi ya budesu ahankali ya maida dubanshi gareta yace “what are you exactly?, why re you confusing me?”
Calmly yayi maganar kamar bashi bane ya gama daga mata murya dazu, saurin dagowa tayi ta kalleshi cikin idanunshi da sukayi jaa, jijiyoyin kanshi zun fito rudu rudu,kwata kwata babu walwala a tattare dashi,koba a fada mashi ba tasan akwai abunda ke damunshi kuma its eating him up,
Miqewa yayi tsaye ya wuce bathroom kawai, tana ganin haka ta wuce ta dauka hijab dinta sannan ta fuce daga dakin ta sauka kasa wajen ammu.
Atare suka futo ita da ammu zuwa compound din gidan, daya daga cikin motocin gidan ammu ta dauka suka fuce daga gidan sabeeha na daga zaune a gaba.
Hira suka dunga yi sosai ita da ammu, yawanci ammu ce ma ke janta da magana, saidai ta amsa ta da uhm ko uh uh, tunanin takeyi tunda suka fito har suka isa insa zasuje.
Gaban drgon mall suka tsaya, ammu na parking suka fito atare, yau ce rana ta farko data futo ita kadai ba tare dashi ba yawanci duk fitar da zasuyi itada taj dinne sai jamid, tunda suka fito take bin wajen da kallo,wajen ya burgeta sosai daga waje ma kenan ba a shiga daga ciki ba.
“Muje ko fatima”
Girgiza mata kai sabeeha tayi sannan suka shige daga ciki, sayyayya sosai ammu tayi mata kamar babu gobe, itadai sabeeha binta kawai take da idanu don batasan ita akema sayyayar ba, wato ammu ma wata rich anty ce, tana da nata kudin sosai, ga inheritance din mijinta data samu donma ba a gama settle kudadenshu ba don shima attajirine haka ta dawo saudi ana kan wannan gabar bayan rasuwarshi.
Daga kan mayukan zamani na jiki zuwa ga na gyaran kai da personal hygiene babu wanda bata saya mata ba, harda wasu arnayen nighties masu shegen daukar hankali da kyau ta kwaso mata, da turarruka masu kamshi sosai, sun dade sosai a wajen kafin su fito su shiga shagunan da ake saida sutura masu kyan gaske na larabawa, yawanci dogayen riguna ne haka ta sayo mata masu kyau, don ta lura kamar bata da wani kayan arziki sosai, sun dade sosai a wajen sabeeha na biye da ita kamar akala,batayi yunkurin daukar komai ba haka zalika ammu batayi forcing dinta ba don ta lura sabeehar akwai kawaici, kuma tana jin nauyinta wannan yasa ta yanke zatayi mata komai kawai dan dole ta cire kunyar da tsoron da sabeeha ke mashi, ita yanxu burinta bai wuce cikin ya tabbata da gaske ba, ta yanda zasu kamashi da kyau, shiyasa takeson su kasance tare.
Daga nan suka wuce spa akayi masu pedicure da manicure sannan aka gyara ma sabeehar gashi, ammu tayi mamaki ganin irin yawan gashin yarinyar sosai, badan tasan yar africa bace zata rantse iyayen ruwa biyu ne, ko ta hada jini da larabawa, sai a lokacin ne ma take ganin yanayin halittar yarinyar, kamar halfcast take, kuma tana da haske sosai wanda baiji mai me tsada ba da zai fidda kyauwun shi,batama san lokacin data furta “masha allah ba” tana kallon yanda ake warware gashin sabeehar data nannadeshi kamar ta nade kaya, wani irin dauri ta mashi sosai saboda karya kwance, masu gyaran na kwance gashi take ya sauko gaba dayanshi har bayanta masha Allah, silky and oily, shima sai baiji gyara bane a haka.

Ammu na daga zaune aka gyarata tsaf, sabeeha sai kallon ikon allah kawai takeyi, yauce rana ta farko data taba samu wannan special gurly treatment din, ba a taba mata irin wannan gatan ba, bata taba benefiting irin wannan jin dadi ba, she feels so soecial ayanxu taci albarkacin wasu, ada saidai taga anayima wasu bata taba tunanin itama za a mata ba saboda talaucin da suka taso cikinshi, bayan wannan ma ta isa ta samu irin wannan gatan? Take tunanin mahaifiyarta ya fado mata da irin rayiwar da sukayi a baya.

Tunda ta doka tagumi take tunani batamasan an gama mata ba saida ta dago ta kalli fuskarta daketa sheqi anyi mata kitso weaving guda hudu saboda santsin gashinta yasa akayi hudun sannan aka nade jelar aka kitse yanda bazai dameta ba, ana hango yellowish fatar kanta data haska baqin gashin bata sosai, ada tana ganin gashi yana wani brown brown yanxu da aka gyara saita ganshi baki siddin, ko wadda ta gyara mata saida ta kalleta ta sake kallonta, muryar ammu sa sukaji ne yasa ta dago ta kalleta “masha allah abnati”
Murmushi sabeeha tayi mata, ita kanta ba karamin dadi taji ba ganin ta sauya gaba daya kamar ba itace ba.
Sallamarsu ammu tayi suka fito zuwa mota suka zauna, suna zama sabeeha ta dago ta kalli ammu tace “jazakallahu khair ammu, nagode..”
Saurin tarar nunfashinta ammu tayi tace “karki godemin kinji, ina fata da rokon zakiyi amfani da wannan damar da kika samu yanda ya kamata fatima,”
Girgiza mata kai sabeeha tayi kafin subar wajen, wani wajen suka kara nufa lokacin har dare ya somayi don garin ya soma yin duhu, tunda ta juya wajen window babu abunda take sai appreciating view din garin, Allah mai yanda yaso, ya kaika inda allah bai taba kaika ba, bata taba tunanin kaddararta zato zo wata kasar ba daban, kasa mai tsarki kamar wannan, kuma yanxu da auren wani akanta.
“Yayi kyau ko?”
Ammu ta katse mata tunaninta, “eh akwai kyau sosai ammu”
“Danma bakiga makka ba, you’ll love it more there, chan yafi nan jedda kyau”
Cikin hanzari sabeeha ta dago ta kalleta tace,”makka makka dai?”
“Eh,insha Allah wata rana zamuje muyi umra idan komai ya lafa…. insha Allah”
Cikin jin dadi sabeeha ta girgiza mata kai, take taji wata ni’ima ta saukar mata, wayaganta yau a makka, allahu akbar.

Tunda ammu tayi parking ta futa ta barta cikin motar bata bar yin murmushi ba, haka kawai taji zuciyarta tayi mata sakayau.
Cikin swiss arabia ammu ta shiga cikin yan mintuna kafin ta futo, tana futowa ta shiga motar ta ajiye jakar data futo da ita a baya sannan ta kunna motar sukabar wajen.
Hanayr gida suka nufa, cikin mintuna qalilan suka iso, ammu na yin parking ta dubi sabeehar tace “idan ya tambayeki ina kikaje kice mashi munje asibiti, nasan da wuya ma ya tambaya”

“Tohm ammu”
“Wannan sayyyar duk takice fatima, duk abunda muka sayo na ki tabbatar kinyi amfani dasu kinji,…karki gode min, kiyi abunda kawai ya dace okay?”
Sauke kai sabeeha tayi muryarta chan kasa tace “insha aallah ammu”
Wannan jakar ammu ta dauko wadda ta shigo da ita daga swiss arabia, ta miqa mata, “tauraruka ne masu kyau, ki dunga amfani dasu idan zaki kwanta”
Girgiza mata kai tayi suka fito daga cikin motar inda ammu ta taimaka mata da wasu few kayayyakin suka shiga cikin gidan daidai nan motar hidaya Ta kunno kai, tundaga bakin gate ta hangosu har suka shige cikin gidan.
Tana parking ta janyo wayarta takai kunenta, ana daga wayar ta soma magana,ta dade sosai tana wayar kafin ta ajiye wayar.

Har sama ammu ta rakata suka ajiye kayan a sitting room kafin ta mata sallama ta sauka kasa, ita kuma ta shige daga ciki.
Sallama tayi ta shugo, idanunta ya sauka akanshi, yana zaune ya saka wani fari glass akan idanunshi ga hasken system din dake gabanshu gabanshi yayi relaxing bayanshi yana sanye da fararen kaya.
Chan kasa kasa ya amsa sallamar tata yanda ba lallai taji ba.
Sadaf safaf ta wuce wajen closet don ajiye jakukunnan da ammu ta bata, wajen kayanta ta nufa ta ajiye kayan data saya mata a ciki, sai a lokacin ta lura da kayan barci data kwaso mata da inner wears masu kyan gaske da daukar hankali, bata bubude su ba saboda a gajiye take don haka ta ajiye jakkunan kawai a wajen da kayanta suke sannan ta ajiye turarukan data bata,
futowa ta sakeyi zuwa sitting room ta kwaso sauran sannan ta dawo dakin, duk wannan shige da fucen da takeyi zaka rantse bai sanma anyi ruwanta a wajen ba nan kuwa yana kallonta ta w idanu,inda taje ba damuwarsa bane don haka ya kauda kanshi ma kawai.
Sabulan da ammu ta saya mata ta kai bathroom wajen inda nashi suke ta ajiye a gefen, sauran abubun personal hygiene dinta kuma ta ajiyesu cikin cupboard din mirorr dake bathroom din suma ta jerasu kafin ta fito, tunawa da sallolin dabata samu tayi ba yasa tayi wanka gaba daya ta dauro alwala ta futo.
Misalin wajen karfe goma ya kashe laptop din dake gabanshi ya ajiye gefe sannan ya tashi ya wuce bathroom, tundaga array row din dake connecting tsakanin bathroom da closet ya soma jin wani irin kamshi mai dadin gaske wadda yayi capturing sensing dinshi lokaci guda, kallon closet room din yayi yasan tana ciki don tunda ta shiga wajen bata futo ba, kauda kanshi yayi ya nufi bathroom din. Sabeeh dake dakin kaya tana jin karar kofa ta tabbatar ya shiga bathroom wannan ya bata damar saurin ajiye turarukan da ammu ta bata ta fito da kayan barcinta ta shimfida su sannan tayi kwanciyarta ta jawo hijab dinta.
Fitowarshi kenan saga bathroom ya nufi cikin daki, daga nesa ya hango ta kwance a kasa,shuru ya danyi yana wasu nazari, ya zaiyi ya hanata kwanciyar kasa? Which ya gani is not good for a pregnant woman saboda sanyi zai iya shigarta, ya dade sosai yana wannan nazari baima san ya shagala da yi ba, sai daga baya kawai yayi kwafa ya nufi kan gadonsa ta chan daya sakon yayi kwanciyarsa bayaj ya kashe lights din dakin gaba daya ya rage na bedside kawai, tunda ya kwanta yakejin wannan kamshin na mashi ziyara daga inda yake kwance wanda ya fara damunshi sosai.
Haka ya dunga juyi kan gado barcin ma gaba daya ya kaurace mashi, sabeeha tunda ya futo taji motsinshi tayi saurin rufe idanunta,tasan ba magana zai mata ba.
Zumbur ta miqe zaune ta fara gulping saboda aman dataji yana taso mata sanadiyar kamshin turaren daya shigeta itama sosai, dazu kafin tasha maganin nan ba karamin dadi yayi mata ba harta goga duka jikinta yanxu kuma sai takeji ya hau kanta sosai.
Take ta fara neman kwaranyo amai har sautin na fita sosai daga dakin, cikin hanzari ta miqe take, taj dake kwance yanajin yanda ta fara gulping dinnan yayi saurin bude idanunshi,
Tundaga bathroom din yakejin saukar aman da takeyi, ta dade tanayi sosai,

miqewa yayi zaune ganin abun yaqi ci yaqi cinyewa, chan kuka yaji shuru ta daina kakarin, karar faduwar dayaji ya biyo baya ne yasa yayi, ya maida dubanshi ga kofar kamar wani mai yin nazari chan kuma yayi saurin saukowa daga gadon cikin azama ya nufi hanyar bathroom din hankali a tashe,cikin saurin ya bude bathroom din chan ya hangota zaune kasan tiles ta jigata sosai, ga kafarta data malqwaye gefe da alamu ta miqe ne ta fadi, ganinta zaune yasa ya sauke ahiyar zuciya ya tunkari inda take hannunshi na cikin aljihun wandosa yaba fuskantarta ya soma magana kamar wanda aka saka dole, “are you okay?”
Ahankali ta dago da fuskarta ta dubeshi da shanyayyun idanunta da yayi jaa sosai,ganin shi dinne ba kunenta ke mata gizo ba yasa tayi saurin gyara zamanta “eh” tana fadin haka ta fara kokarin miqewa, kafarta tasha jini tana zugi wannan yasa ta koma tana mai kama yar karamar farar kafarta da babu gashi ko kadan tace “washh!!!”
Yana ganin haka ya gane yanayin da take ciki, ba zato ba tsammani ta ganshi a gabanta a tsaye dagowar da tayi yayi daidai da miqo mata hannunshi da yayi, bin huge hannun nashi tayi da kallo, tana kallon yanda fatar tafin hannun tayi jajaja, kwata kwata bata gane helping hand yake bata ba saita zama so confuse,ganin kamar bata gane me yake nufi ba yasashi cewa “hold up and get up”
Tana jin haka tayi saurin kallon hannun nashi, ta kasa motsawa tsabar mamaki, dakyar ta iya daga hannunta daketa faman zufa ta dora akan nashi, ya kama dan karamin hannun nata ya riqe yana mai jin dumin hannunta ya taimaka mata ta miqe tsaye,tana miqewa zugin ya kara jaa wanda ya sata neman dukawa yayi saurin tallabo arms dinta muryarshi chan kasa kasa kamar mai rowar magana baimasan lokacin dayace “sorry ba”
Ita ko kunnenta kasa gasgata abunda taji takeyi, abun mamaki yake bata sosai, meysa hes being nice to her yanxu kuma?bayan magnganun daya fada mata da safe?.
Da taimakonsa suka dawo bedroom din a lokacin kafarta ta rage zugin don haka tayi saurin zame hannunta dake cikin nashi don tunda ya rike mata hannun takejin wani irin “thank you im okay now”
Taba fadin haka tayi kwanciyarta, taja hijab dinta ta rufe jikinta.
Yana kallo tayi barcinta, yanda take wannan aman ya kara convincing dinshi tabbas da cikin shi a jikinta, daman yau gaba daya wuni yayi yana researching akan pregnancy, babu abunda bai dubo ba, kuma alamun sa daya gabi a tattare da ita ya tabbatar mashi da sickness din daya gani a research din da yayi, yanxu dolenshi yayi supporting dinta in some ways, da kyar yakejin zai iya kauda grudges din da yake dashi akan ta yayi focusing akan abunda ke cikinta which happens to his mold of blood, har yanxu baibar jin tsanar abunda tayi mashi ba for taking advantage of him, amma yanxu dole ya kauda wannan kodan abunda ke tattare da ita.

Dakyar ya samu bar ci ya dauke shi da wannan tunanjn aranshi.
*****
Misalin wajen karfe biyu tareeq ya bude idanunshi, hannunshi ya sanya wajen da take kwanciya a gefe yaji wayam, miqewa yayi zaune ya kunna bedside lamb gake haske ya bade ko’ina, kallon gefwn gadon yayi ya tabbatar bata nan, miqewa yayi ya nufi bathroom ya danyi knocking ko zaiji motsinta, nanma yaji shuru, tunawa da mood din datake cikin kwanakin nan yasa yayi tunani ko lafiya, bai kawo komai a ranshi ba don haka ya shiga bathroom cikin yan mintina kasan ya fito, yana futowa ya fuce daga bedroom dinsu ya nufi nata, yana karasowa daidai bakin kofar harya saka hannu zai bude kofar ya jiyota daga cikin dakin, “don’t fucking tell me to calm down, how can i calm down?”
Dake wayar a speaker ne ya bashi damar jin wanda take wayar dashi kuma namiji ne dukda bayaji sosai yanda ya kamata, “baby you need to be calming, karkiyi messing up what we have worked for over the years”
“No…i want her out, zan iya yin komai, i can’t afford to see anyone around him”
Sai kawai ta fashe da kuka, take wanda ke cikin wayar ya soma lallabata, “ki daina kukan shikenan we’ill come up with a plan, we have to be very careful saboda we are at the edge of ending this game,don’t do anything stupid da zaisa ya gano komai, tunda yasan ke kika fada mashi maganar accident din, you need to be meticulous”
Ita ba wannan take son ji ba don haka tayi saurin kashe wayar ma gaba daya ta jefata gefwn gado take ta tarwatse gaba daya, wani irin huci takeyi mai zafi sosai rai a bace, ta furta “khaal!!!! Khaal!!”
Wanna ce kalma ta karshe data furta daya ji kafin yayi saurin barin wajen ya koma bedroom dinsu, kanshi gaba daya ya kulle da wannan almari, “da wa take waya? Koma wanene it has to be someone close to her, kuma daga yanayin yanda mutumin ke mata magana ya tabbatar mashi da saurayinta ne, she’s with someone kenan? Sannan wata fadama maganar accident? Wani accident din?taj!!!! Abunda yazo ranshi kenan, idan har kanshi yayi wrapoing din komai yanda yayi hasashe tasan da plan din accident din da taj yayi kenan? Tunawa da wannan recording din dayayi na maganar accident din da mutabblib yayi da sabeeha yayi, kamar wani karamin mahaukaci haka ya dunga saka yana warwarewa dan dole yakeso ya gano komai saidai ba duka tambayoyinsa ya samu amsarsu ba, karar koda dayaji yasashi saurin kwanciya ya rufo kofa, itace ta shugo dakin, ko kallon inda tareeq din yake batayi ba ta kwanta cikin bacin rai.

Asuba nayi sabeeha ta farka da matsanancin ciwon mara, cikin hanzari ta miqe ta shige bathroom allah yaso bai farka ba, a gaggauce tayi wanka ta gyara jikinta sannan tayi brush ta fito ta wuce closet ta sauya kaya marasa nauyi sannan ta maida hijab dinta ta dawo dakin, kayan barcinta ta tattara ta ninkeau har zuwa lokacin barcinsa yake hankali kwance barcinma yayi nisa sosai saboda bai samu ya tufe idanunshi ba saboda tunanin daya kwashe rabin daren yana yi.
Tundata fito take kallon fuskanshi, yana facing celying ya jango duvet ya rike, saita shagala da kallonsa, ganin lokacin sallah na neman kurewa yasa ta soma tashinsa ahankali, “didi didi”
Muryarta ya soma ji ahanakli kafin kamshin nan na jiya ya soma shiga hancinsa, Ahankali ya soma bude idanunshi harya sauke akanta, cikin sauri tayi baya “lokacin sallah yayi”
Tana fadin haka ta juya ta fuce daga bedroom din ya rakata da idanu, yana mai tuna yanda take tashinsa lokacin da baya cikin hayyacinsa, miqewa yayi ya shiga bathroom din ya dauro alwala sannan ya futo ya tada kabbarar sallah, ya dade sosai yana azkar a zaune.
Chan parlor sabeeha gyara ta tsiri yi da safiyar allahn nan, daman alreday ta saba da wannan lokacin datake aiki a gidan, tun 5 suke tashi a gidan so wannan ba abune mai wuya a wajenta ba, saida ta gama gyaran ta fara kokarin dafa mashi coffee latte, da taimakon youtube da ammu tace ta duba ta samu tayi, tana gamawa ta wuto dakin lokacin wajen 6:50am ta gifta ana neman 7:00am, lokacin data shugo yana cikin bathroom yana wanka wannan ya bata damar shiga closet room ta bude wajen inda yake ajiye kayayyakin daya ke yawan fita dasu cikin kwanakin ta kwaso mashi su sannan ta futo daga dakin ta ajiye mashi kan gadon yanda dai take mashi idan zai shirya, tana gamawa ta futo zuwa kitchen ta sake reboiling coffee din kafin ta zubo mashi cikin mug ta daura shi kan saucer ta fito, fatanta allah yasa yasha.
Lokacin data shugo yayi daidai da fitowarshi daga closet cikin shiri, shi baima san ta ajiye mashi kaya kan gado ba don haka ya nufi closet ya dauka kayanshi ya saka, saida ya karaso tsakiyan dakin yaga kayan, saikuma gata a tsaye tana kallon na jikinshi, taji wani iri a ranta amma haka ta kauda komai ta karaso inda yake, daman yace mata karta sake taba komai daya danganceshi so idan bai saka ba batada right din jin haushinsa.
Har fargaba tunkarar shi takeji da zarar taga fuskanshi, da hes lively yanxu kuwa kwaa kwata fuskar na nan yanda take kamar bai taba fara’a ba.
“Sabahal khair didi…”
Daga bayanshi ya jiyo muryarta, kokarin zipping jakarshi yake amma ya dakata, ya dauka wajen minti biyu a tsaye bai motsa ba saida ta sake cewa “bismillah ga coffee”
Juyowa yayi ya kalleta kafin ya kalli coffee din hannnuna nata, yama rasa me zaice mata, duk maganar da zai fito daga bakinsa
Bamai dadi bace ba saboda duk waennan abubuwan da takeyi haushi suke bashi musamman idan ya tuna da wasu abubuwan, bai ce mata tak ba ya dauki jakarsa ya fuce saga dakin.
Saurin runtse idanu tayi jiki a mace ta futo daga dakin zuwa kitchen…
Da yamma ammu tazo nan ta shaida nata period dinta yazo, nan ammu ta bata yan dabaru da zatayi yanda bazai gane komai ba,sannan ta dakatar da ita da shan wannan maganin.

Yau kwana biyar kenan, babu abunda ya sauya tsakaninta dashi, zai tashi kota gaishesa baya amsa ta kwatakwata, magana ma bata shiga tsakaninsu, inama taga fuskar, hakan baisa ta fasa kyautata mashi ba, yanxu har abunci ma takeyi ta ajiye kuma yana gani amma bai taba koda kallon abunci ba kuma ya lura da batada hayaniya sosai, duk wulaqancin da yake mata bata nuna tayi fushi ko tashi haushi ko sau daya, yanxu har dare yana kaiwa bai dawo gida ba kuma da zarar ya dawo zai taddata zaune kamar wadda ke jiran dawowarshi.

Yaune rana ta karshe da period dinta zai dauke, daman dayazo karashe take yawan ciwon baya da kafa, gaba daya kafarta ta sage mata, tama kasa tashi, tun bayan aikin safe datayi ta dawo parlor ta zauna ta doka uban tagumi tana dan matsa kafar.
Tundaya futo daga wanka ya shirya yake kallon kofa, harya saba kullum zata shugo da coffee a hannunta yau da baiga shugowarta ba sai yaji kamar ya damu dukda yaki yarda da damuwar yayi, he’s enjoying yanda yake treating dinga bata nuna gajiyawarta da kosawarta, rai a bace ya miqe ya fuce daga dakin ya nufi sitting room nan ya taddata zaune a kasa ta tankwashe kafafu tana matsawa da alamu abun na damunta sosai, harya kauda idanu ya tunkari hanyar fucewa ya dan dakata yana mai fusantarta, yama rasa me zaice mata, baisan lokacin da bakinsa ya furta “where’s the coffee?”
Da mamaki sabeeha ta dago take kallonsa, tayi mamakin jin furucinsa kamar a mafarko, tama manta da ciwon da kafarta keyi tsabar murna tayi saurin miqewa tace “yana kitchen bari na kawo”
Ta shige kitchen din tayi reboiling,tana murmushi, saitaji wani irin dadi aranta daya tambaya, ashe yana sane da ita, yana gama reboiling ta futo fuskanta harta sauya annuri ya bayyana akanta tace “bismillah” kallon don hannunta yayi kafin ya amshi coffee din, yakai bakinsa yadansha kadan ya tabe baki ya miqa mata,”disgusting” yana fadin haka ya miqe ya fuce daga parlorn, amaimakon taji haushi sai kawai murmushi ya kubce nata, ita wannan achievement ne a wajenta, yau da kanshi ya buqacu avu daga hannunta ba karamin dadi takeji ba, shi bangarensa tunda ya fuce ya fara wasi wasi da tuhumar kansa na tambayrta coffee din da yayi yanxu saitayi tunanin wani abun, tsaki kawai yayi yana mai jin haushin kansa for doing that.
Borin kunya😂

Yana isowa gym ya nufi wardrop ya ajiye jakarshi daidai nan mutalib ya shugo wajen,suna hada idanu ya suakeka taj din murmushi kafin ya miqa mashi hannu, kallonsa taj yayi irin who are you dinnan, ganin haka yasa mutabblb cewa “salam alaikum”
Yana jin sallamar musulunci da yayi mashi yasa ya miqa mashi hannu suka gaisa, suna gama gaisawa yabar wajen zuwa wajen gym, mutabbli ya biishi da kallo.
Tunda ya fara workout mutane ke kallonshi, matan dake wajen ko kasa duake idanunsu sukayi akanshi, hes so charming and charismatic, macen data sameshi wannan ta gama samun komai a wajen namiji, kyau, aji, uwa uba kana ganinshi kasan kudi ya zauna, tsakanin lokacin daya dawo ahyyacinshi zuwa yanxu ya sauya sosai, physically ma, ya maida jikinshi na da yanda yake a baya, kamarma yana neman yafi da din, hes so cute and handsome at the same time…
Cikin mutanen dake observing dinshi garda mutabblib daya karba membership din wajen saboda ya samu kusanci dashi, yau kwanansa biyar kenan da zuwa wajen, duk yanda yazo ya samu kusanci dashi avun ya gagara saboda he’s not opeb kwata kwata,bai karaya ba don haka ya cigaba da approaching dinshi.
Takowa yayi inda taj yake zaune yana warming thighs dinshi, yanxu haka ma sallama ya sake mashi, dakyar taj din ya iya amsa mashi don shi bai fiye son mutane suna shiga harkarshi ba, bashida sakewa kwata kwata, shake din da mutabblib ke miqa mashi ya duba kafin ya maida dubanshi ga mutalib din daya soma cewa “bismillah!!!”
Kai tsaye ya amsa shi da “no thanks”
Yana kaiwa nan ya miqe daman ya gama yabar wajen.
Yana futowa ya shige bathroom yayi wanka ya shirya kafin ya futo da jakarshi, ya fuce daga wajen.
Harya shiga motarshi yayi reverse ya soma jin horn daga bayan motarshi, da farko ya dauka bashi akema ba sai daga baya ya lura da motarshi akema horn, daidai nan mutallib ya karaso da tashi motar ya zuge glass yana mai fuskantar taj din ya miqa mashi airpod dinshi daya mata a cikin gym din, “sir ka manta da wannan, I believe naka ne”
Kallon airpod din taj yayi sai a lokacin ya tabbatar nashi ne don haka yayi saurin miqa hannu ya karba tare da cewa “thanks”
Yana fadin haka mutalib ya sara mashi ya figi motarshi yabar wajen, shuru taj yayi yana wani nazari, yanajin kamar ya taba ganin fuskarsa saidai ya rasa a ina ya taba gani.
Ahankali yaja motar yabar wajen shima, yaron black dake binshi kuwa yana biye dashi a baya, ya lura da motar dake bin nashi ba tun yanxu ba, shi abunma yanxu ya maidashi wani joke, for almost over 2months kenan ana bin nashi, kwata kwata baya jin wani darr ko tsoro kwata kwata.
Bangaren sabeeha tun bayan ya futa take fama da wani irin matsanancin ciwon ciki, gashi yau ya kamata period dinta ya tsaya balle ace shine, kaffaunta duk sun sage sosai, ta dauka ciwon normal ciwo ne kuma zai daina saitaga akasin haka, don kamarma gaba gaba yake mata sosai, tun bayan data futo daga wanka ta kasa koda saka kaya ne, batama san lokacin data hau kan gadonshi ba ta kwanta tsabar azaba.

Karfe sha biyu ya shigo gidan, tunda ya shugo part dinsu ya soma jin kuka qasa qasa, bai kawo itace ba saima mamakin daga ina kukan ke fitowa daya dunga yi, cikin bedroom ya nufa nanfa yaji sunan ya tsananta cikin hanzari ya bude kofar ya shige daga ciki nan ya ganta zaune a kasa ta tabkwaro kafafunta daketa faman karkarwa saboda zugin da suke mata, take hankali ya tashi amma ya danne ya karaso inda take muryarshi a kaushashe ya soma magana “ke!!! Ke!!”
Sama sama ta soma jin muryarshi wannan yasa tayi saurin dagowa tana kallon shine tayi saurin miqew tsaye take kafarta ta amsa wand ahakan yasa ta sake zubewa a kasan,jini ya soma sauka daga kasanta kuma tana jin yanda yake zuba dukda ta saka pad a jikinta, jikinta gar tsuma yake, fatanta daya allah ya jefo mata ammu don batasan irin karyar da zatayi mashi ba idan yaga jini gashi ta kasa tabuka komai saboda azabar da take ji, kamar da wasa kuwa ya fara hango jini wajen kafafunta bai tabbatar da hakan ba saida ta sake wata yar kara ta zakusa gefe saboda murda nata da cikin yayi take yaga jini kwance akan hijab dinta harya bata hijan din nata sosai, take ya zaro idanu tunawa da research din da yayi inda akace idan har jini ya ballema mai ciki to zubew zaiyi, take hankalinshi ya tashi sosai, ya tsugunna gabanta hama rasa me zaice mata, “hey!!! Hey!! Whats wrong with you?meke damunki?”
Ay gaba daya batama san me yake cewa ba tsabar azabar da takeji sosai,lokaci guda ta furgice ta sake fashewa da wani kukan baima san lokacin daya sanya hannunshi ba ya dago da fuskarta ganin yansa take kuka shabe shabe he can see yanda takejin wahala inda baima san daga ina bane ba, tsoronshi daya karya zama cikin ne, gashi ta kasa fada mashi abund akw damunta,
Dagoda idanunshi da zaiyi ya sake ganin jini na saukowa a kafarta take hankalinshi ya tashi sosai babu abunda yake sai innalillahi a zuciyarshi yaka rasa mai zaiyi mata, daidai nan aka budo kofar, hankali a tashe ammu ta shigo dakin ta tunkari sabeehar, taja karasowa itama taga jinin, take hankalinta ya tashi sosai, saboda daga ganin wannan jini ansan bana lafiya bane, gashi taj na tsaye a wajen balle ta tambayeta ko dama haka take idan tana period, tama rasa me zatayi saida ya dago ya kalli ammu din yace “whats wrong with her? Whys she bleeding like that? Pregnancy dinne?”
Tambayoyin daya jero ma ammu kenan, ganin itama ta rude yasa ya kinkimi sabeehar gaba daya hankali a tashe yace “muje asibiti”
Hankali a tashe ammu ta zaro idanu tana kallonshi harya nufi hanayr futa da sabeehar a hannunshi, dan dole ammu tabi bayanshi cikin hanzari suka sauko kasa daidai nan su afiya suka fito ita da sonata, ganinshi da sabeeha a hannu yasa kowa ya visu da kallo cikin mamaki, har sonata zatabi bayansu afiya ta dakatar da ita,
“Saboda me zaki hanani binsu”
“Kina tunanin idan kika bishi zai saurareki ne? Bakiga yanayin da take ciki ba,”
Da mamaki sonata ke kallonta fuskanta da alamun tanbaya tace “ban gane ba”
“Looks like kamar cikin ya zube bakiga yanda suka fito ba ga kuma jini a jikinta”
Sonata najin haka ta waro idanu take wani irin dadi ya ziyarceta mata misali, batama san lokacin sata rungume afiya ba, su sunma qayyade cikin ne ya zube, take afiya ta doka fadwa da hidaya kira a waya.

Acahn asibiti kuwa suna isowa aka wuce da sabeeha emergency room, taj dai ya kasa natsuwa kwata kwata, ni kaina na rasa gane yanayin da yake ciki, deep down fargaba ce kunshe a cikin zuciyarshi, sai a yanxu yasan jini ba abun wasa bane, take ya soma jin haushin kansa, idan wani abu ya samu wannan cikin he will be devastated, ya kasa natsuwa kwata kwata, ammu na ganin yanda ya zama restless lokaci guda, take taji wani irin rashin dadi a zuciyarta ko ba a fada mata ba kuka d ayanda yake kauda kai hakan baisa ta ta hango yanda lokaci guda ba ya sauya gaba daya, ayau rana ta farko ta hango tsantsar furgici a cikin idanunshi tarw da fargaba, “those that mean ya damu da cikin kenan?”
Tambayar da ammu ta tunda ga ma kanta kenan, so its true dayace he will responsible for it kenan.
Shuru ammu tayi taba nazari, yanda sukayi nisan nan batajin its time to give up, ayanxu ma da basu samu damar fayyace mashi komai ba kenan, dole she has to rwmove all of teh emotions dake zuwan mata.
Wannan yasa ta fuce daga wajen, takai wajen 30mins kafin ta dawo cikin asibitin, tana dawowa ta tsaya daidai nan likita ta futo ta buqaci ganinsu.
Taj din na daga gaba suka shiga office din doctor suka zauna, suna zama doctor ta dubi ammu ta miqa mata hannu, karbar hannunta ammu tayi kafin doctor din tace “congratulations ma’am, you dont have to worry, the baby is perfectly healthy”
Wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke yana jin kalaman doctor din na karshe, har zaida ammu ta jiyo sautin, murmushin yaqe ammu tama doctor din kafin tace “thank you doc”
Miqewa taj din yayi baima tsaya ba ya fuce daga office din.
Yana futa doctor ta dubi ammu tace “hauwa..gaskia this is risky, meysa zakiyi wannan karyar, yanxu badan ina duty ba ya zakiyi kenan?kinsan dai this ai illegal ba”
“Im sorry doctor farhana, bazaki gane dalilin dayasa na tsaya akan wannan maganar ba, wannan yarin da kike gani maraya ne, dana ne, wannan ne kadai gatan da zan mashi wanda nake fatan yayi nsanadiyar kubutar dashi daga ukubar da yake ciki”
Jinjina kai kawai farhana tayi kafin tace “shikenan hauwa i trust you, maganar yarinyar wannan maganin dana baki data sha dinnan shine ya jawo mata over glow during period dinta, ya kanata ta dauna sha haka karya mata illa”
“Ay ta gama sha ma”
“Zataji sauki, na bata injections dazai dakatar da flow din zaku iya tafiya ma yanxu, akwai pain relievers dana mata allurarsu zaisata barci sannan zai haifar mata da kasala”
Mikewa ammu tayi itama doc farhana ta miqe auka rungume juna ammu tayi mata godiya sosai kafin su fuce zuwa dakin sabeehar, suna fitowa suka hango taj din yanata faman waya, hidaya ce daman ta kirashi, ammu na karasowa inda yake tace “bari na fito da ita mu tafi, doctor tace zata iya tafiya”
Jinjina kai kawia yayi ya maida hankalinshi ga wayar da yakeyi, “zamu dawo yanxu” yana fadin haka baima saurari amsarta ba ya kashe wayar, da mamaki hidaya ke kallon wayar daya katse mata ko sauraronta bai gama yi ba, lamarinshi gaba yakeyi sosai.

Chan asibiti kuwa ammu tabfito tare da sabeeha suka nufi motarshi lokacin yana daga zaune a gaba, kayan jikinta an saya mata su zuwa wasu sabbi anan asibitin, dake farhana tasan ammu sosai wannan yasa akayima sabeehar arrangement.

Tunda ta shiga motar tare da ammu a baya babu abunda take sai layi, gaba daya she’s weak saboda allurar da akayi mata, babu ahunda ammu ke mata sai sannu, shiko sau daya ya dago ya kalleta ta mirror kafin ya dauke idanunshi har suka karaso, suna fitowa daga cikin motar ammu ta shigewarta cikin gidan ta barshi da sabeehar, tana sane daman tayi hakan, ya dade sosai a zaune yana kallonta ta jikin mirror yana tuna irin fargabar daya shiga dazu, zai iya kiran abun da fargabar rasa something new thats part of him, sai kawia ya fara imaging da ace cikin ya zube fa ya zaiyi? Baya ma fatan tuna wannan don haka ya futo daga motar ya nufi baya inda take zaune ya bude kofar ya zubama fuskarta idanu sosai, kanta ne ya nemi langwabewa yayi saurin tallabota da hannunshi daya take fuskanta yayi lapping akan palm dinshi, she looks so innocent, take kawai yaji tausayinta ya darsu a zuciyarshi, he has a very soft side daya kasa sanin yana dashi sai akanta,ya dade yana kallonta babu ko kiftawa kafin ya sanya hannunshi duka biyu ya dagota nan take tayi yuuu ta fado jikinshi ya dauketa da hannu daya ya rufo kofar motar kafin ya shige daga ciki.
Yana shiga ya tadda sonata a taaye tana tsumayen ganinshi, itafa gaba daya murna takeyi dontama ji a jikinta cikin ne ya zube, hangoshi da take yana rike da sabeeha a hannunshi ba karamin takaici taji ya tsaya mata arai ba, for now bama wannan ba tukunnan, so take ta tabbatar babu cikin ko akwai don hka ta tunkareshi, “hey! Babe”
Ko kallon inda take baiyi ba saima jin kalmar ta karshe da yayi data sanya shi wullo mata wani mugun kallo
“Oh noo!! I’m so sorry babe cikin ne ya zube ko?”
Daga yanayin yanda ya kalleta ta tabbatar da akasin haka, take jikinta ya soma kyarma kamar mazari, bai sake kallon inda take ba ya nufi sama da sabeeha a hannunshi, fadwa data futo daga dakinta tana hangoshi da sabeeha a hannunshi take komai ya dauke mata.

Da kafarshi ya budw kofar dakin ya shiga daga ciki, dakin yayi wani dimn kadan babu yalwar haske sosai, ga kamshi mai dadi dake tashi kadan kadan, an gyara dakin fess fess wanda ammu ce tasa ayi kafin su iso,
Gado ya nufa da ita a hannunshi, yana kokarin kwantar da ita ya sauke idnaunshi akan fuskarta, ta nanikeshi gaba daya kamar wadda za a kwace shi daga jikinta, batasan ma tanayi ba saboda effect din allurar da akayi mata, dakkyar ya samu ya kwantar da ita ya gyara mata kwanciya, yana kokarin mikewa ta kamo gaban rigarshi wanda hakan yasa yayi mata runfa gaba dayashi, fuskanshi na gab da tata har goshinsa na bugun nata, kallon fuskarta ya soma yi daga kan hular asibiti da aka saka mata wadda ta dan zamo gashin kanta ya bayyana kadan zuwa ga gashin baby hair dinta dake kwance a goshinta ga girarta da idanunta dake rufe kawo wajen bakinda dake bude kadan ga pink braces dinta ya fito, kusancin dake tsakaninsu yayi yawa sosai don nunafshinsu har gogayya yake da juna,gashi sai sake matso dashi takeyi zuwaga jikinta kamarma sanyi takeji ko zazzabi ne ke neman rufeta, sun dade a haka kafin yayi saurin zame hannunta ya mike tsaye ya wuce bathroom yayi wanka.
Ya dade sosai a bathroom kafin ya fito ya sauya kaya zuwa marasa nauyi sannan ya wmfuce zuwa kitchen,yana karasowa ya tadda casserole akan tray da alamu abunci ne a ciki, harya dauka chocolate zai futa yadan dakata, ya nufi wajen da casserole din suke ya bude, pasta ne tayi a ciki dayji kayan lambu veggies da chicken breast,aamun kanshi yayi da daukan fork din dake wajen ya dan diba yakai bakinshi, tun bayan dayayi loma daya baisan lokacin dayakai ta biyar ba kafin ya ajiye fork din ya zari ruwa a futo daga kitcehn din.
Dakin ya nufa nan ya hangota kwace tanata faman kakkame jikinta da alamu sanyi takeji wannan yasa ya janyo mata duvet dinshi ya rufe mata gaba daya jikinta ya rage sai fuskanta kawai,ya dade tsaye a gabanta yana kallonta kafin ya miqe ya zari laptop dinshi ya wuce zuwa sitting room ya kuna laptop din ya fara aiki, ya dade sosai yana video call da managers dinshi suna bashi update kan ayyukan dake chan.

Wasa wasa saida yakai har wajen karfe tara anan sitting room din, salla ne kawai ke kaishi daki, wannan ke bashi damar dubata, yana idarwa zai dawo,baiyi mamakin ganin irin barcin da taketayi ba saboda doctor tayi bayanin an bata pain killer wanda zai sanata zama drousy.

Shugwoa dakin yayi da laptop a hannunshi, idanunshi bai sauka ko ina ba sai kanta, bathroom ya wuce ya sake sabon wanka ya suaya zuwa kayan barci, yana gama shiryawa ya nufi dakin yana nazarin yanda zai kwnata, karshe dai ya yanke komawa sitting room kawai, harya nufi kofar ya dakata jin yanda take fidda aautin nunfashi da sauri sauri,takowa ya somayi ahankali ya nufi inda take ya tsaya akanta, fuskanta ya kura ma idanu ganin hawaye na saukowa akan fuskarta kamar wadda ke mafarki ga bakinta na motsawa ahankali sai kuma dan karkarwa datayi, dan duko da kanshi yayi daidai bakinta don jin abunsa take fada, “didi…didi..bazasu yi maka komai ba..i will always protect you..din allah karka tafi ka barni didi..”
Dukda a rarrabe take fada hakan baisa ya hade maganganun nata ba, yana mamakin mafarkin me takeyi, jin sunan dayaga tana kiranshi dashi yasa ya gane mafarkin hardashi takeyi kenan, amma meysa take kuka tambayar daya dunga na kanshi kenan, why would she cry out while calling his name, “didi….” Abunda ya sake ji kenan saidai baiji karahen zancen ba, hannunshi daya ya daga ya dorashi kan fuskarta, yanajin temperature dinta yayi saurin daga hannun nashi ya miqe ya shige bathroom, kafin ya gitk da bowl a hannunhsi da handtowel ya zauna gefen gadon, ya rasa dalilin dayasa yakejin zafin da takeji, kamar an dauka ciwonta an saka mashi haka yake ji,ya rasa meysa yake jin haka game da ita, itace mace ta farko daya taba yima haka, and yana tunanin saboda cikin shi dake jikinta ne,saurin kauda komai yayi daga tanshi ya saka towel din a cikin bowl din yana matsewa ya dagoshi zai saka akan fuskarta memory din lokacin da bashida lafiya ta zauja tare dashi yazo mashi, gaba daya kamar an tunkudo memoriws din haka suka zo mashi batch by batch, take ya fuskanshi dalilin dayasa yakejin abunda yakeji game da ita, which he can define it as utmost respect he has for her, aduk lokacin da zai tsinci kanshi cikin kunci zai ganshi da ita suna hawaye,she has become part of him acahn baya, ya samu soyayyar da kulawar kusanci da bai taba samu ba a wajen kowa, zai iya fasaara hakan da soyayyar da uwa kema danta uncontrollably fond, tund aya saka towel din akan fuskanta yake kallonta sosai, zuciyarshi ta gaka aminta da ita, koda kuwa yayi denying to yayi ma kanshi karya.
Ya dade a gefenta har saida zazzabin ya sauka sauka daga jjikinta wajen karfe daya kafin ya koma gefen gadon ta dayan barin ya zauna, anan zaune barcin ya tafi dashi….


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 14 · 0% Book details