← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 17 OF 66

Chapter 71

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 22 min read

Washe gari da safe tun wajen karfe biyar ya farka kmar kullum juyowan da zaiyi ya ganta gaba daya ta gangaro inda yake kwance ta hade jikinta waje guda don yana hango yar fuskarta sleeping peacefully hankalinta kwance, ya dauka wajen minti biyu yana kallonta, memories dinsu shida ita na flashing a fuskanshi,lashes dinta dake kwance yabi da kallo har zuwa dogon hancinta dake miqe,she looks so young and innocent, saurin kauda idanunshi yayi akanta ya tashi zaune kafin ya ambaci sunan allah ya sauko daga gadon yana miqa ahankali.
Bathrroom ya wuce ya dauro alwala kafin ya fito ya sauya zuwa jallabiya fara qal sannan ya dawo dakin wajen inda yake sallah.

Bude kofar dayayi yayi daidai da farkawarta, saida ya tasa kabbarar sallah kafin ta miqe itama, tana taku daya taji kafarta ta rike kyamm… sai a lokacin ta tuna da bugewar datayi jiya da daddare, “washh” ta furta ahanklai saboda wani irin radadi dataji saboda kafar tayi tsami, tunawa da warning din daya shumfida mata jiya yasa ta daure ta wuce bathroom cikin natsuwa ta dauro alwala tana jan kafar, sannan ta wuce wajen closet ta dauko hijab dinta ta saka kafij ta fito daga dakin, daga nesa ta hango yana sujjada a natse.
Nufar wajen da yake tayi daga gefenshi wajen carpet din itama ta tsaye daga bayanshi kadan har tana jin kamshin turaren dake jikinsa,sai ha zamana kamar tare zasuyi sallahr don tana daga gefenshi gwanin sha ‘awa,
Raka’atainul fajir ta fara tana idarwa ta ganshi tsaye,harya tada kabbarar sallar subh, a gaggauce tabi bayanshi ya jasu sallah.
Tunda suka idar da sallah ya ankare da ita saidai ya nuna kamarma baisan tana wajen ba, ya dade sosai yana addua’oin mafi yawa cikinsu shine na neman tsari, wasu adduao da yake ma kwata kwata bata iyasu ba sai a bakinsa ta taba ji, kuma tayi mamaki sosai yanda yake da addini, da farko data zo gidan lokacin da bashi lafiya batayi tsammanin yanada ilimi ba.
Shafawa yayi itama ta shafa, daman tasan miqewa zaiyi wannan ya bata damar cewa “sabahal khair didi”
Shuru ya danyi na yan saqanni bai tashi ba haka zalika baice mata uppan ba saima jingina da yayi da bango, kamar bazai ce komai ba chan kuma ya amsa ta a natse “sabahal noor”

Yana fadin haka kowannen su yayi shuru, daman batayi expecting jin komai daga gareshi ba don haka tayi shuru abunta kuma batayi kokarin tashi ba, “akwai abunda kike buqata?Akwai abunda ke damunki? Do you need anything?”
A jere ya jefo mata tambayoyin kamar wani lawyer,in so much concern for her.
Saurin sauke kanta tayi qasa sai taji wani irin farin ciki ya lulubeta,yanda yake mata magana gaba daya ya sauya daga yanda yake a baya, wani sa’in har mamakin abun take, yanxu maturedly yake komai.
“Alhamdulillah bana buqatar komai, and babu abunda ke damuna”
Ta amsa shi a tsanake, tunda ta fara magana ya juyo yana kallonta, zai iya rantsewa baima san sanda ya juyo ba,akwai wani abu da muryarta dake tasiri a cikin zuciyarshi,baisan yanda zai fassara abunba kwata kwata.
Jin shuru yasa ta dawo karaf idanunta ya sarke da nashi kamar anyi magneting dinsu waje guda, sun dade a haka harta soma jin idanunshi sun mata nauyi sosai wannan yasa tayi hanzari kauda nata.
Tana son tambayarshi abu amma saitaji kamar an kulle mata bakin nata, dakyar ta iya bude bakinta tace “a kawo maka coffee?”
Tana fadin haka ya kauda idanunshi daga nata sannan ya miqe tsaye ya wuce closet ya cire jallabiyan ya rage dagashi sai mini short dinshi, har zai futo haka ya tuna bashi kadai ke zaune a dakin ba, baya son matsi kwata kwata shiyasa bayason kowa ya shigo dakinshi, idan yana daki zamanshi yake confortably babu takura babu matsi.
Cikin set of bathrobe dinshi ya jawo daya fara khaal ya saka akan short din kafin ya fito ya nufi gado ya kwanta, sabod ayanxu ya daina futa da safe daman futar bata wuce zuwa gym yanxu kuma ya sauya timing din zuwanshi zuwa evening.
Akan idanunta ya futo yayi kwanciyarshi, tayi mamaki sosai don tasan a wannan lokacin wanka yakeyi sannan ya fara shiri.
Mikewa tayi ta zare hijab din jikinta, shaf tama manta babu mayafi akanta haka ta nade mayafin ta ajiye sannan ta shiga bathroom ta soma wanke.
Wani irin barci ne mai dadi ya fuzgesa, baima san lokacin da barcin ya kwashesa ba.
Ta dade a bathroom kafin don harda feww kayayyayakinsa dake cikin laudry ta wanke kafin ta fito, wace walk in ta gyara kayanta tsaf, tana gamawa ta futo, tundaga chan nesa ta hangoshi ya kwanta yayi irin rub da ciki dinnan, kaffaunshi na hanging a bakin gado, kallo daya ta mashi ta gane he’s fast a sleep wannan ya bata damar takowa bakin gadon wajen inda yake ta tsugunna a kasa wajen gefenshi tana mai kallon kyakyawar fuskarshi da gashi ya zagayeta, ga sumar kanshi a kwance tasha gyara kamar gashin jariri, samun kanta tayi da murmusawa kallonshi kawai da takeyi, hannunta ta daga kamar mai jin tsoro ta fara tattare gashi daya dan zubo mashi akan fuskanshi, wannan ya bata damar ganinshi da kyau.
“Masha Allah” vakinta ya furta…tana fadin haka ta sauke murmushi, shuru tayi tana tuna rayuwarsu a baya da yanda yasha wahala wajen yan uwansa, saitaji wani irin aranta take emotions da wasu feelings ya darsu a zuciyarta, she really want to protect him, bata son ya cutu ko wani abu ya cutar dashi ko kadan, itace zata bada labari irin wahalar rayuwa daya hannun makusantansa dayake masu kallan ahalinshi.
“Allah ga wannan bawa naka, karka bari yasha wahalar dayasha achan baya lokacin da baya cikin tunaninshi, ya allah ka tsareshi daga duk wani sharri, allah kaine sheda, kuma kaine ka jarabceshi da wannan, allah ka fayyace mashi gaskiyar lamarin rayuwar dayake ciki da wanda yayi a baya, ya allah karka barshi yasha wahalr dayasha a baya, ya all..” sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya a hankali, saurin toshe bakinta tayi gudun karya farka, saida tayi mai isarta kafin ta bude idanunta a hankali, ta saukesu akanshi sai hannunta mai dumi dake kan fuskar shi.
Gabanta ne ya bada dam ganin idanunshi da sukayi jaa a bude, lumshesu yayi ya sake budewa a hankali kamar wani maiyin maye haka yake kallonta, dumin hannunta datake caressing fuskanshi ne ya farkar dashi daga barci sai dan sheshekar kukanta daya soma ji kadan kadan, tunda ta fara maganganunnan yake sauraronta tundaga farko har karshe, a daidai lokacin itakuma ya rufe idanunta bata ma ya farka ba, dukda ya farka da matsanancin ciwon kai wannan bai hanashi jin duk abubuwan data fada ba.
Gaba daya ta gama confusing dinshi da kalamnta,tunda ya kafa mata idanu ya kasa daukewa harta bude idanunta, hannunta dake kan fuskanshi kuwa allah kadai yasan yanda yakejinsu akan fuskarshi, she was caresing him with so much affection, ya rasa ta yanda zaiyi describing abun.
Saurin dauke hannunta tayi daga fuskarshi jikinta na tsuma sosai kamar mazari, duk saita tsorata lokaci guda, tunda ta dauke hannunta yake binta da da ido, cikin hanzari tayi baya tare da saurin miqe jikinta na rawa a daidai lokacin idanunshi ya sauka kan boucing boobs dinta da bai taba yi masu kyakyawan kallo ba sai yau, dukda cikin kaya take abun saiya zo mashi a bazata lokaci guda yayi noticing gashi jikinta na rawa.
“Daman…daman zan tambayeka ne ko zaka sha coffee”
Tana fadin haka tayi saurin juya mashi baya,jin shuru babu response yasa ta dan juyo kadan da mamakinta taga ya koma barcinsa hankali kwance.
Take taji wani irin sanyi a ranta, cikin sauri tabar dakin ma gaba daya.
Tana futa ya bude idanunshi, daman yayi hakan ne don kartayi tunanin koya ji duk abunda ta fada wannan yasa yayi pretending ya koma barci.

Maganganunta ne suka fara mashi yawo a kwakwalwar shi, daga yanda take magana he can see and feel how sincere she is, saita barshi da zulunmi daw rudani a cikin zuciyarshi ya gama na’am da ita don yanajin akwai wani abu a ciki Maganganunta, shi karan kanshi ne yaqi yarda da ita completely.
Ya dade sosai a kwance yana dogon nazari abund ayafi tsaya mashi arai shine “what is she talking about? Meysa take neman mashi tsari daga wajen allah? Wake kokarin cutar dashi? Meya faru dashi a lokacin da baya cikin hayyacinsa?wacce irin wahala yasha datake rokon allah karya bari yasha wahalar yanxu? Wace gaskiyar lamari take rokon allah ya fayyace mashi?”
Hes so curious about everything, ada yabar komai kawai tunda first love tace yabar komai daya wuce a baya, dukda hea so eager yo know everything amma yanxu baya jin zai iya hakura, wannan maganganun nata is like a call up for him, he wants to know everything, amma where wilm he start from? What if wani plot ne yarinyar nan keyi? What if??” Shuru yayi duk yanda yaso yayi doubting ko ya karyarta magnganun yarinyar nan ko masu wata fassara daban ya kasa zuciyarshi ta gama aminta da maganganunta kamar an dasa su a wajen sai ayanxu yakeji there has to be something saboda bai taba jin irin haka ga kowa ba sai ita, hidaya kawai yakema irin wannan yardar datayi magana shikenan zuciyarhsi ta aminta da ita completly.


Istanbul…
Bude mata kofa tayi ta sanyo kafarta ahankali, hidaya ce sanye da classy doguwar riga ta alfarma, daga kan daham dake jikinta kadai is speaking luxury, tafiyar sassafiya tayi yau dinnan zuwa istanbul saboda wani muhimmin meeting da zatayi da sabbin investors din data samu, dakyar ta samu sukayi scheduling meeting dinnan inda suka buqaci ita da kanta tazo da proposal din abunda kamfaninsu ke buqata.
Gefenta secretary dinta ne yana biye da ita da takardu da laptop dinta,
ta kwama wani irin tsadaddan shade a fuskarta sai handbag data rike a hannunta mai tsadan gaske.
Kallon tafkeken hotel din da suka tsaya a wajen tayi kafin ta maida dubanta ga secretary dinta daya zagayo inda take, “are you sure nan sukayi scheduling meeting din”
“Yes ma’am”
“Wannan wani irin organization ne dasu? This is so unprofessional”
Shidai sacretary shuru yayi yana hiye da ita tana gaba, ciki suka shiga har wajen conference address din da aka basu suna zuwa daidai wajen daya daga cikin receptionist din ya jagorance su zuwa conference meeting lounge din.
Suna zuwa wajen ya dan dakatar da ita sannan ya danna wani button kafin kofar ta bude, babban lounge ne kamar hall yasha haduwar tables da kujeru hadaddu masu shegen kyau sosai.
Ahankali ta soma takowa babu abunda ke tashi sai saurin takalminta kwas kwasa harta karaso ciki, tana shugowa ta fuskanci inda taga mutun zaune sai wani a tsaye a gefen mutumin shi,

A hankali na zaune ya soma juyo da kujerarsa harya juyo inda take fuskantar kujerar,cikin hanzari ta sauke shade din dake gabanta don tabbatar da wanda ke gaban nata, “wait what the heck is going on here?”
Ta furta ahankali tana mai abdul basit, owner of BB companies, kuma baban family enemie dinsu kuka competitor din taheel company.. rai a bace take kallon secretary dinshi don tabbatar da yasan da wannan banzan hadin dayayi? Saurin girgiza mata kai yayi don shima duk ya rude, kwafa tayi ta maida dubanta ga abdul basit dake kallonta yana murmusawa sosai, “welcome to my empire mrs hidaya”
“Whats the meaning of this?”
“It is what is it my dear…please have a seat, wanna. Meeting din zai amfanemu gaba dayanmu.”
Badan taso ba taja kujera ta zauna, tana zama yaronahi ya zagayo inda take ya ajiye mata proposal paper dinsu, kafin ya koma wajen oganshi, yana komawa abdul basit ya bashi damar futa, yana gab da futa ya kallo nata secretary din, wannan yasa ya buqaci ta bashi damar futa shima, batace komai ba ta girgiza mashi kai ya bi bayan dayan suka fuce suka barsu su biyu a zaune.
Tunda ta zauna yake kallon fuskarta yana murmushi, wani irin dadi yake ji sosai ganinta da yayi kawai, saita tuno mashi da fuskar da bazai taba manta da ita ba kaf duniya, fsukar datayi sanadiyar arzikinsa, mace mai babban matsayi a zuciyarshi.

Tunda ta zauna akan kujera take bin proposal din dake gabanta da kallo,
“Zan baki power, zan baki duk Abunda kikeso, kudi..arziki..power..”
“Hahahaha.. ta kece da dariya vatama san lokacin da dariyar ta kubce mata ba..” what a joke?”

“You have all the time for your self, everything is clear and simply, I’m giving you power, ki zauna kiyi tunani akai, i have no bad intentions on this, i want you to join hand with us, zakiyi duk abunda kikeso da kamfanin,this is only chance for you to save your company...bayan wata biyar zaki iya tarminating proposal din”
“Why are you doing this? Why does it have to be from you? Kana tunanin zan taba yarda dakai? You our biggest competitor, duk wani trick and snitchy dirty works din da kakeyi don gannin kamfanina ya lalace na sani, now this? You want me to believe this? Why? Give me a reason to believe this”
Mikewa yayi taaye fuskanshi dauke da murmushi, gadararta da rashin taoronta yana burgeshi kuma shike tuna mashi da mahaifiyarta, “do you really need a reason?”
“Yes”
Wata iriyar dariya yayi kafin ya sake kallonta cikin ido yace “saboda dalilin dayasa kikeson kamfanin ya zamo naki ke kadai…. I dont have to go into details, inason kije kiyi tunani akai…kamar yanda nace its a win win for you only.. babu abunda zanyi gaining a cikin wannan, after 5months zaki iya tarminating proposal dinnan.. “ yana kaiwa nan ya tunkari hanyar futa daga wajen ta dakatar dashi..
“Meysa zakayi hakan? Saboda me?”
Dariya kawai yayi yana mai sake juyowa ya kalleta sai kawai ya girgiza kai ya fuce.
Tund aya fuce daga wajen ya barta cikin zulumi da tunani, ta kasa wrapping kanta gaba daya tama rasa irin tunanin da zatayi, har secrwtary dinta yaso, saida ya kira sunanta tunkunna ta dawo daga dogon nazarin da ta fada kafin ta fuce daga wajen, “ma’am… sunyi mana reserving 5star hotel dinnan”
Shuru tayi tana sauraron shi gaba daya kanta ya gama kullewa da kyar ta samu secrwtary din ya karba masu keys ya rakata har zuwa dakinta sannan ya mata sallama.
Tunda ta shugo dakin take tunani, gaban tafkekn windown dakin ta nufa tana kallon wajen compund din hotel din.
“saboda dalilin dayasa kikeson kamfanin ya zamo naki ke kadai….”
Wannan kalma tashi ta tsaya mata arai, gashi tana cikin tight position, dole ta nemi supproting hand, she really needs that power, ko duniya zata hadu bataji zata taba yarda da enemy dinta, wannan yasa ta yanke shawarar playing along, idanma playing dinta suke son yi, bayan wannan ma hes the perfect supporting hand din da take buqata, she need that power, dukda its a dangerous move shes ready to go for it.
Haka ta kwana da nazari, ta kulla chan ta kwance chan hartayi concluding amincewa da support din abdulbasit, don ta haka ne kawai zata iya samun power da zata iya yin duk abunda takeso, kuma wannan zai bata damar kawar da matsalar ta cikin sauqi, idan ta samu abund atake so zatayi tarminating proposal din nasu.
Washe gari da sassafiya ta buqaci secretary dinta ya kira secretary din basit ya shaida mashi tanason meeting da oganshi, hakan kuwa akayi by 10 am daidai basit ya iso hotel din, daman hotel din nashi ne.
Zama sukayi kamar jiya yana fuskantarta tana fuskantarshi.
“Ive agreep on this amma inada sharadi daya”
Girgiza mata kai yayi yana sauraronta..”zanyi tarminating din propsosal dinnan aduk lokacin danaso?”
“Considered that done, and what next?” Ya jefo mata tambaya.
“Bana ajiye debt akaina, i want to know me kake buqata daga wajenmu? Shares ne? Or what?”

Wata iriyar dariya ya kece da ita kafin ya kalleta yace “lets do this…inason 5 percent of your achievements”
“5..??” Ta nanata a ranta, kai this is unbelievable, ta kasa amincewa definately akwai abund ayake hari kod ayake a shirye take itama
“Okay..” tana fadin haka ta moqe tsaye tana kallon wani irin kallon da yake mata data kasa fassarawa ko wane iri ne, mikewa shima yayi yana mai takowa inda take yana kallon hannunta, saurin rintse idanunshi yayi abubuwa da dama na yawo aranshi kafin ya daga nashi ya saka cikin nata sukayi shaking “its a deal” ya furta
“Deal”
“Duk sauran abubuwan da zaki buqata you can send it to my personal email, just say a word duk abunda kike buqata considered it done”

Saurin zame hannunta tayi daga cikin nashi cause she feels do unconfrotable da wannan tsohon, sa’an ubanta.
Yau utace ta fara fita ya bita da kallo fuskarshi wasai.
Tana futa sakatarenta ya tako inda take fsukanshi wasai ya bata good news din kudin da suka buqata da kamfanin basit suka turo, har an cigaba da production dinta daya tsaya…
“Inason mu wuce dubai, kayi booking flight yau”
Ta umarci sakatarenta..
“Yes ma’am”

Taheel residence….
11am…
Tunda ta futa daga dakin taki shugowa, achan taci abuncinta ta koshi ta zauna a parlor ta doka uban tagumi.

Tun bayan futarta awa kusan biyu yayi a zaune ya kasa tashi, ya saka ya kulla ya rasa ma inda zai tsaya da nazarin da yakeyi, da kyar ya tashi zaune ya jawo wayanshi ind ayaci karo da mesaage din hidaya inda take shaida mashi tayi tafiya, abunda bata taba yi ba kenan.
Miqewa yayi tsaye ya wuce bathroom ya watso ruwa mai zafi sosai, ya dade a bathroom din kamar mace ya goge chan ya wanke chan kafij ya futo da wani dan towel a kugunshi, yayi mamakin ganin babu towels din dayake jere, saidaga baya ya lura ashe zubasu tayi cikin automatic washing machine ya wankesu, wand aya rage ne kawai ya dauro a kugunsa ya futo.

A natse ya futo ya shige closet room hannunshi na rike da gaban towel din sabod akarya fadi, gaba daya wani irin tiririn kamshin lavender seruo jung shower gel yake, jikinshi gaba daya ya murde, so huge and attractive, kallon gashinsa ya somayi a jikin mirror inda ya dunga baya dashi, ya dade a gaban dresser yana feshe feshensa kafin ya fara kokarin fidda kayan da zai sa.

Daga chan sitting room kuwa ta gama gajiya da zaman, wannan yasata miqe ta shugo dakin, koda wasa batayi gigin kallon gadon ba kuma koda ta shugo ahankali ta budo kofar don duk a tunaninta barcin yakeyi don saboda dakij is still dim babu hasken kirki kuma bata son tashinsa , direct wajen closet ta nufa don daukan hijab dinta harzata shiga ta dan dakata meta tuna allah kadai ya sani sai iuyawa tayi ta nufi bathroom a natse.
Bata wani dade sosai ba tayi wankanta sharp sharp ta maida under skirt dinnan a jikinta tana kokari daukan doguwar rigar barcin data cire kawai taji sound din vibration vooo vooo lokaci guda ta dan tsorata, ta rasa a ina take jin wannan karar dan matsowa tayi gaban wajen wash hand basin don daga nan ne tafi jin sautin sosai, dukawa tayi har kasan wajen tasa kanta ko zataga abund ake vibrating din tana tura hannu chan ciki kuwa hannunta ya tabo wani abu, jawo abun tayi nan take taga wani dan jan box ne yanata blinking jan haske, still tana jin vibration din wannan yasa ta tabbatar ba abun bane don haka ta sake tura hannunta ta dayan sakon tana turawa kuwa ta jawo wayar,tana ganin wayar ta tabbatar tashi, jujuya wayar tayi kafin tace “me ya kawo wayarshi nan?” tana fadin haka ta fara kokarin miqewa, gaba daya ta manta da irin zaman datayi gashi jiya ta dan bige kafarta a kitchen.

Wata uwar kara data kwallah tundaga closet ya jiyo ta dake closet din yana opposite da bathroom wannan yasa yajita sosai, cikin hanzari ya ajiye abunda yakeyi, ya zaka shorts dinshi kenan yana kokarin saka dogon wando yaji karar tata,yana futowa daga clost din yaji muryarta a bathroom
“wayyo allah kafa na”
Yanajin haka ya tabbatar daga bathroom ne baiyi wata wata ba kawai ya bude kofar ya shugo hankali a tashe, a zaune ya taddata wajen basin din ta kama kafarta data dan kumbura lokaci guda saboda bugun wajen data sakeyi, cikin saurin ya tunkari inda take ya duqa gabanta ganinta zaune tana rike da kafarta.
“Whats wrong? Meya faru? Menene? Eh? Whats woorng”
A furgice ta dago ganinshi datayi ba zato ba tsammani cikin bathroom din, harda yar kwallarya a ido kuwa, saboda taji zafi sosai,
“Menene? Meya sameki? Kin bige ne? Cikin ki? What wrong with yiu?
Ya sake jero maga tambayoyi,yanda yake magana da yanda ya nuna tsataan damuwa da rudani lokaci guda yasa ta fara kokarin daidaita natsuwarta saima boye kafar data farayi don bataso ya gani, shiko binta ya dunga yi da ido yanason yasan meke make mata ciwo, kota bige ne inda bai kamata ba.
“Bakida baki ne? Speak up”
Ya daka mata tsawa tabara furgicin daya shiga,ganin haka cikin ya tsure saibinshi kawai take da kallo yanda ya duka a gabanta babu komi jikinshi sai wani matsoyaci. Short gashi dai gaba daya a haka a gabanta sai taji gabanta na faduwa don bata taba ganin babba haka ba, idanunta ne ya sauka kan cinyoyinshi donta sauke kanta kasa taki yarda su hada ido, saurin rintse idanunta tayi saboda inda idanunta ya kaita, kirjinta kuwa kamar ana lugude tsabar bugu saboda kallo daya datayi ma gabanshi cikin wannan dan mini short din.
Shima dai kallon nata ya dungayi don yaga abunda ya sameta harta kwala ihu haka, tundaga kan gashinta datayi wetting wajen wanka zuwa kafadunta da fatar kenan luwai luwai kamar ta sabon jariri har wani jaja takeyi, shes just glowy naturally,har zuwa dan under skirt din dake jikinta data jawoshi kirjinta baima rufe kirjin ba sboda ga cleavages dinta nan yana gani rudu rudu sun fito in a circular motion, yana hango tudun boobiessz dinta, zuwa ga kafarta data kama da hannu daya kamar mai kokarin boye abu,
Kurama kafar tata idanu yayi ganin hannunta na karkarwa a wajen, baima san lokacin daya sanya huge hannunshi ya janyo kafarta guda daya ma, kafar saita zama yar kucila a hannunshi, saurin runtse idanunta tayi jin hannunshi kan fatarta, kurama kafar idnau yayi sosai haryayi identifining wajen da yayi jaa sosai kuka ya kumbura, dayan hannunshi ya dago ya shafa wajen a hankali, batasan lokacin datayi wani irin gasping breath ba nunfashinta ya nemi sarqewa, dan danna wajen yayi ta sake kwalla wata karar tare da kama damtsen hannunshi, “way…yo didi akwai zafiii shiiiii akwai zafiii sosai”
Bai saurareta ba ya sake danna wajen don ya tabbatar iya nan ne ke mata zafin ko tayi buguwar qashi ne a wajen
“Wayyo ka barii akwai zafi sosaiii washhhh, didi stop it…” tana fadin haka tayi saurin dauke kafarta, yana ganin haka ya hade rai sosai tamau ya soma magana cikin izza da fada fada “how did you get that? Bakyaji ko?…didn’t i war..”
Bata bari ya karaeh ba ta katse shi, cikin shagwaba batama san tanayi ba harda turo baki “dan allah karkayi fushi.. nasan zakace kayi warning dina banji ba, ni wallahi.. bansan zan buge ba a duhun”
Tundata soma magana ya kasa cire idanunshi akanta, she looks so cute kamar wata yar karamar yarinya, wallahi kallon barad yake mata gaba dayanta,
“Didi…” saida ta kira sunanshi ya dawo hayyacinshi, “karkayi fushi dan allah,wallahi na ji warning dinka kuma I’m being careful, yanxu ma naji vibration ne shine na duka zan dauko abunda ke karar shine na buge”
Ta karashe tana nuna mashi wayar da dan black box dinnan data zaro dake blinking wuta.
Kallon abun ya dungayi da wayar..karba yayi daga hannunta yana jujyawa, “meya kawo waya bathroom dinshi?” Sannan if hes not mistaken wannan abun dake blinking looks like a spy recorder,
“Ina kikaga wannan din”
Nuni ta mashi da karkashin basin din “anan ne”
Tana fadin haka ta kauda idanunta daga kanshi ta fara kamarin rufe jikinta ta hanyar nado hannayenta a kirjinta, gaba daya tama manta yanayin data ciki dazu sai yanxu ta lura.
“Get up” tana jin haka gabanta ya bada dam, ya za ayi yace mata ta miqe a haka,
Wani irin kallo ya mata irin are you deaf…gaba daya taka rasa ya zata mashi me zata ce mashi, gaskia tana kunyar jikinta sosai ko bugin hauka ke famunta bazata miqe a haka ba.
Wata dabara ce tazo mata “washh akwai zafi bazan iya tashi yanxu ba,”
Yana jin haka ya danyi jim, a tunanin ta dauka ya barta ne ya fucewarshi ga mamakinta saitaga akasin haka
Wayar ya ajiye tare da wannan black box din a gefen basin din sannan ya miqa mata hannunshi trying to help her out, “innalillahi!!! Waishi bazai gane bane” ta fada aranta, tana mai turo bakinta kamar zatayi kuka, yanda kasan zata yi kuka, tama rasa me zatayi, ganin tana neman bata mashi lokaci ya dan duqa tare da kamo hannunta daya, cikin hanzari ta dago tana kallon cikin idanunshi, da taimakon hannunshi ta miqe tsaye tsulum,saijinta tayi kamar ya dagata gaba dayanta ta tsaya akan kafafunta, yanada wani irin karfi sosai.
Tunda ta mike take sunne kai tana kare kare, duk ya lura da hakan amma ya nuna kamar baiga komai ba, miqewar datayi dinnan ya bashi damar ganin abubuwa da dama amma ya basarwa, ganin ta mike kawai ta fara kokarin danne zafin da takeji ta fara takawa, ay bata gama takun bama ta dakata savoda zafib dataji, yana ganin haka kawai ya sungumeta gama dayanta kamar ya dauki yar tsana,
Innalillahi yanda kasan ya ta nitse haka taji, kunya babu irin wanda bata lulubeta ba, shiko ko a jikinshi haka ya fiddota daga bathroom din har daki ya ajiyeta akan gado.
Yana ajiyeta ya wuce closet room wajen inda yaga kayanta suke, baima tsaya wani dube dube ba ya jawo wata riga, har zai rufe closet din ya dakata inda idanunshi ya sauka kan inners dinta a jere wanda ammu ta sayo mata masu kyau, yar tsuka yayi ya jawo bra da pant ya futo daga closet din, inda ya barta nan ya taddata, ajiye mata su yayi a gefe kafin yace “dress up” yana fadin haka ya koma bathroom din ya dauko wayar nan da wannan box din sannan ya wuce closet ya cigaba da shiryawa.

Tunda ya ajiye mata kayan take kallon rigar, idanda ya warware rigar zaiga yanayin yanda take rigar, rigar shan iska ce amma fa wata arniyar riga ce, irin ta aza room dinnan, mai shegen kyau, daga gaban rigar anyi tattara shapes din hallitar mace idan ta saka zai fito.
Da zama haka gwara ta saka, haka ta fara kiciniyar saka bra ta zura pants din sannan ta saka rigar, allah yaso akwai mayafinta daya cire jiya da daddare tana barci akan gado wannan yasa daukeshi ta yafa ya dan rufa mata kirjinta daya fito sosai daman gashi allah ya bata kamar zaifi karfinta ma.

Saida ya dauka wajen 30mins kafin ya fito, yana fitowa ko kallon inda take baiyi ba ya fuce daga dakin ya wuce kitchen yana wani observation, chan naga ya tunkari wajen sakon kitchen cabinet ya zura hannunshi kafin ya fiddo da hannunshi daga wajen, irin wannan black box dinne data bashi daxu ya gani a wajen, juya abun ya dunga yi da mamaki yana kallon black box din, ta yanda yasan da wannan anan kitchen djn kuwa shine ranar daya shugo dinnan da duhu ya hanngo abu na blinking,take instint dinshi ya bashi yazo kitchen din ya sake dubawa ko same abu ne ya gani, yana zuwa kuma yanxu ya tabbatar.
Gaba daya ya rasa tunanin da zaiyi ma, me ya kawo spy recorders a cikin part dinshi? This is suspicious.

Dakin ya koma indaya taddata yanda yabarta,wayoyinshi ya zara da keys din motarshi kafin ya fuce daga dakin batare da yace mata tak ba
Yana fita ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya tana jin wani iri aranta duk a tunaninta ko yayi fushi ne.




✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 17 · 0% Book details