Chapter 90
Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 26 min read
Taheel residents…
Safa da Marwa take tsakanin dakin ta, gaba daya she’s restless, tunda tayi confirming taj ne ya fita a daren ranar da accident dinnan ya faru, wallahi fadin irin tashin hankalin data shiga vata lokaci ne, kuma very soon za a gano shine tunda anyi declaring dinshi missing.
Ta rasa me zataji aranta farin ciki ko bakin ciki, maganar batanshi ta girmama sosai, its been more than 7days, and idan an nemi mutun sama da kwanakin nan za a fara tunanin koya mutu, ko wani abu ya faru dashi.
A cikin kwanakin kamafinin sunyi asarar da ba a taba yi ba, waenda ke partnership da kamfanin duk sun ja baya gaba daya, before her eyes taheel is going down, shareholders nata faman saida shares dinsu, ga rumors din slush funds da akace akwai a kamfanin (irin secret kudaden da ake samu a business ta haramtacciyar hanya), da kuma allegations na forced labor da akema workers, wannnan rumors din sun zama manya threat ga ko wanne kamfani idan har an fara rade radin hakan, kuma tasan idan abun ya zurfafa za a binciki kamfanin.
Lokaci guda tasa a kira board meeting don solving wanna issue din, ana shugowa aka zazzauna nanma ba a tsira ba, hayaniya ta barke, ga sabon report daya shugo na kamfanin is going bankrupt saboda wannan product din data sama kudin kamfani sosai yaqi selling, anmayi banning production din don wajen production anyi using wasu cheap products, kuma anyi leaking information din wanna yasa aka dakatar dashi daga sales market.
Ga biggest partnership dinsu da TT investment ya tsaya gaba daya, hope din kamafanin daya ne a yanxu, shine partnership dinta Da BanB companies.
A gaggauce ta futa daga board meeting room din ta wuce office dunta daidai nan saiga secretary dinta ya shigo, biye dashi wasu mutanene sunkai su goma sha sanye da suit da.
Kallo secretary din nata tayi don sanin kosu waye kuma da dalilin barinsu su shigo, “mrs hidaya abdallah taheel, we have a warrant to take all the taheel company documents for business fraud investigation”
“Wait what…”
“Step aside madam”
Tana ji tana gani suka tattare duk wasu abubuwan kan desk dinta, laptop ne, transversal din data na kamfanin da komai, saida suka bincike komai na office din, daya daga cikin officers din ya bude drawer datake aje abubuwa masu mahimmanci a ciki, take gabanta ya fadi ta wani zaro ido, anan take aje da wayar taj da yayi accidents da ita for the past year, wani ikon allah kwanaki ta dauke wayar daga nan ta maidata gida cikin study room dinta.
Bayan officer din ya zaro avubuwan dake wajen ta wani sauke ajiyar zuciya.
Suka gama kwasar avunda zasu kwasa suka fita dashi sannan suka shiga sauran offices din building din suka kwashi duk wani important documents sannan suka fita.
Achan kasa reporters kamar jira suke suka zazage investigators din da tambayoyin.
“Shin Ya tabbata da allegations din da akema kamfani?”
“Munason musani ko rumors din da akeyi akan kamfanin ko gaskia ne? Shin kamfanin na cikin masu black funds?”
Haka suka dunga jeroma investigators dinnan tambayoyi babu wanda yake amsasu.
Har suka shiga motarsu suka bar wajen, suna barin wajen saiga human right activist suma sun shigo, saboda allegations din da akema kamfanin na forced labor.
Tana daga tsaye a jikin glass barrier window din office din tana hango duk abubuwan dake faruwa a kasa, dandazo mutane da yawa yan jarida ne, human right activist, ga workers.
Kicinaya ya haure, juyowa tayi ga tv daketa faman aiki, kowanne station babu abunda ake sai maganar taheel, idanunta yayi jaa sosai ta duaka remote din tv ta wullashi ga tv har saida ta fashe ratsa ratsa, sai faman juye juyen idanu take ta rasa me zatayi, jakarta da wayarta ta dauka ta futa daga office din secretary dinta na biye da ita a baya, ya jagorance ta ta gate din baya inda babu mutane, tana futowa bata tsira ba tana shiga mota haka kawai from no wherw aka wullo dutse kan glass din motarta ya fasa glass din, da gudu driver yabar wajen.
Tunda ta zauna anan baya babu abunda take sai nazari, tunanin yanda zatayi over coming wannan problem din, bata taba tunanin it has come to this point ba, babu wanda take blaming sai taj, tunda ya bayyana a idan duniya shikenan komai ya lalace, ta tsaneshi dukda baya doran kasa.
Jujuya kujerar da take zaune ta somayi, tana shan coffee tare da kallon tafkekwn tv dake jikin bangon office din.
Irin luxurious office ne na manya, dayasha abubuwan daukan ido masu kyau.
Budo kofar da akayi ne yasa ta dago tana mai kallon baban nata.
Takowa yayi secretary dinshi na biye dashi ya zauna akan kujerar baki, tare da aje papers din daya shugo dasu.
“Hello my little princess, yaushe kika shugo office?”
“Banida right din shugowa ne duk sanda naga dama papi?”
“No not at all princess”
Dauke idanunta tayi gareshi ta maida ga tv tana kallon drama da akayi a taheels company.
“I have a gift for you princess zo ki gani”
Tasowa tayi ta karaso inda yake ta zauna gefenshi ya wulla mata pappers din ta bude, tare da karantawa take wani murmushi ya bayyana akan fuskarta.
“Congratulations princess, you’re the highest shareholder of taheel company as promised”
Saurin rungumeshi tayi tana mai farin ciki sannan ta kalleshi tace “thanks for this papa, but this is not enough”
Yasan me take nufi wannan yasashi cewa, “be patient okay?, you’ll have that very soon”
Murmushi ta sakeyi tare da daura kafa daya kan daya tana taunar cingum.
Shugowar secretary dinshi yasaahi maida dubansa garesa, “sir you have a guest,”
“Who’s that?”
“Mrs hidaya”
Kallon juna sukayi shida ita, sai kawai ya babbake da dariya, “i never expected it to be sooner princess”
Miqewa yayi tare da pecking kumatun fadwa sannan ya futa daga office din.
Nigeriaaa…
Yau kwananshi uku chif a nigeria, tun ranar daya futa da salim bai sake futa ba, yana zaune a hotel, daga ya tashi daga barci yayi sallah yaci abunci sai gym da yake shiga anan hilton din babu abunda yake daya wuce wannan.
Aikinsa kuwa bai fasa ba, kullum yana kan laptop yana bada instructions din abubuwa, sannan tun ranar da sukayi waya da khaal
Bai sake kiransu ba infact wayar dayasa sim din ya kashe, indai ba kiran ditective zaiyi ba baya kunna wayar.
Duk abubuwan dake faruwa achan saudi akan idanunshi, infact komai dake faruwa nakan idanunshi, and everything is going according to his plan.
Saidai abu daya ya bashi mamaki, abunda ke faruwa a kamfani yanxu, it wasn’t his move kwata kwata, dukda yanada shaidar da abubuwan daya alaqanci kamfanin da illegal abubuwan da hidaya keyi bai fiddasu ba, don yasan zai affecting kamfanin.
The question here is who’s behind-this? Tanan ne ya gano bashi kadaine ke attacking hidaya ba, infact ba hidaya ba the company as well.
Yadai zuba ido kawai yana kallon abubuwan da suke wakana.
Yau ta kasance saturday, bayan yayi wanka ya shirya cikin farar jallabiya ya nada kundura akanshi, kai masha allah yayi masifaffen kyau ba kadan ba.
Ya saka rolex a hannunshi tare da feshe jikinshi da turarruka masu kamshin gaske ya futo.
Hannunshi rike da latest 15 max dinshi yana daddannawa, ya shiga lift tare da danna last floor, hankalinshi yaui nisa sosai akan wayar harya futo daga lift, ya nufi eatery din hotel din ya basu card dinshi sannan ya buqaci wajen da babu hayaniya, attendant din ta bashi reserve wajenda vips ne kawai ke zama.
Ciki ya shige kai tsaye walking majestically kamar wani dan sarki hannunshi rike da wayarshi yana kokarin replying merk, chak ya tsaya jin kamar abu ya kwaranye a jikinshi, runtse idanunshi yayi saboda sanyin ruwan dayaji, saurin yin baya yayi yana mai duban jikinshi kafin ya dago kuma ya sauke sexy idanunshi masu mahaukacin kyau akan fuskarta.
Saida ta dan wani razana locking her eyes inti his ta kasa cire bata.
“Excuse me????” Ya furta yana yin baya ganin hanunta na neman tba kirjinshi inda milkshake din ya zuba,
Ta shagala gaba daya batasan hannunta yakai kirjinshi ba tana kokarin gogewa,
Ta dan daburce “i’m sorry…its a mistake..so sorry about that okay?”
Take attendant sukayi noticing dinsu, kamar zasu taugunna masa haka suka soma bashi hkuri,
“Babe is everything okay”
Daga bayanta salim ya kira sunanta, yana karasowa yaga taj a tsaye ga maya a tsaye ta kafe taj da ido cup din milk shake dinnan na hannunta har zuwa lokacin ga attendats a gefensu, “oh noo… maya what have you done”
Sai a lokacin taj ya dago ya kalleshi, yanayin fuskansa kwata kwata bai sauya ba, yanda take bazakace yana fara a ba haka zalika bazakace a cikin bacin rai yake ba.
“Sir….good day…what a coincidence”
Girgiza mashi kai taj yayi, “ke kika zuba mashi?” Ya tambayeta kasa kasa
“Ka sanshi ne?”ta jefa mashi tambaya don batama jin question din dayake mata, she’s lost, ya tafi da imaninta, zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba ganin kyakyawan namiji daya dauke ta gaba daya kamar wannan, abu kamar tsafi, baro baro ya bayyana a fuskarta ta kasa boyewa.
“Yes shine wanda nake baki labari”
Saida ta sake dagowa ta kalli taj din dake cema attendants dinnan suyi mashi prepping buffet din a kawo mashi room service.
“We’re very sorry sir, this is my girl…”
“Just friends…” tayi saurin katse salim, ya mata wani irin kallo kafin ya kauda ido zuwa ga taj da kallon daya ya mata ya sauya akala.
“It’s okay..next time watch your step.. you might tripple”
Wani irin runtse idanunta tayi, tsikar jikinta na tashi, muryarshi nada wani irin tasiri, gaba daya ya tafi da imanin ta wallah.
Yana kaiwa haka ya juya yabar wajen ba tare da ya sake sauraronsu ba ya wuce daki.
“Maya!!! Maya!!”
Bata dauke idanunta ba sauda yabar wajen, har salim yayi noticing waishi kishi yace “lets go”
Suka nufi table dinsu suka zauna, “meysa zakice we are friends?huh?? And why are you looking at him like that?”
Daukan fork da knife tayi tana kokarin yankan steak din dake gabansu har wani kamshi kamshi takeji, tayi banza dashi, abun yayi mugun mugun bashi mamaki itada ke binshi yana mata wala wala, “are you deaf? Bakiji tambayar danayi maki bane?
“Aje steak din tayi ta kalleshi, “what do you want him to him of you? Kazo hotel da girlfriend dinka?inace kacemin he’s important guest to you dady? Kanasan yayi having wrong impression of you kenan?”
Shuru ya danyi yana nazari, tabbas abunda ta fada gaskia ne, sai kuma yayi dariya yana mai kallonta yace “and so? Idan yayi tunanin hakan ma ay dalilin daya kawomi kenan? Isn’t it? To be together and….”
Ya dan lashe bakinsa yana kallon cleavages dinta, ta wani miqe tsaye kamar zata tashi sama tace “zan wuce kaina na ciwo”
Tana kaiwa nan ta wuce wajen lift tana mai jin kamshin sa har zuwa lokacin a hancinta.
Surprisingly har floor din da sukayi lodging ita da salim tana jin kamshin, nan ta tabbatar ma da zuciyarta yana nan, kuma dole tasan koshi waye kafin tabar hotel din.
Koda salim ya dawo kwata kwata qin bashi attention dinta tayi, and he spends almost 200k for the night, karshema futa tayi daga dakin da sunan neman pad wai period dinta yazo unexpectedly nanko duban taj ta futo yi, ta dunga zagaye floors ko allah zaisa ta ganshi.
Karshe ta hakura don its late kuma dole ta koma gida kafin a gane bata nan.
Achan Bangaren khaal tun bayan wayar da sukayi da taj bayan ya kashe wayar idanunshi ya sauka akan international number daya kira da ita , nan ya gane ba number kasar bane, nan yasa mutallib ya duba mashi numbwr wace kasa ce, lokacin da suka gano number nigeria ne mutallib yayi mamaki sosai khaal ko baiyi mamaki ba sai murmushi daya dungayi, gaba daya bakin cikinsa da damuwarsa ta wanye, yaji gaba daya wani irin farin ciki ya lullubeshi.
The next morning….
Dip kamar daukewar ruwa maganar kamfanin taheel ta rufe ruf, investigation din da ake masu ya tsaya chak komai ya dawo daidai, ita kadai tasan me tayi da yasa aka tsaida binciken kamfanin.
Sai a lokacin ta samu wata natsuwa, don adaidai lokacin da kamfanin zaiyi failing tayi making wani smart decision.
Yanxu matsalarta ta gaba duk yanda zatayi bazata bari zancen taj ya sake dagowa ba.
Zuwanta kamfanin basit dukda tasan competitor din taheel ne ta bangaren business, ta buqaci su hada hannu don ta hanyar nan ne kawai zatayi protecting kamfanin taheel,unknowingly to her, it was the worst decision she has ever made.
Yarjejeniya ce sukayi, tunda ta kasance itace mai shares da yawa a kamfanin ta bashi rabin shares din nata don su hada karfi karfi.
Antse ta fito daga mazaunin baya na motar da driver ke tuqata, as always she looks so classy and bossy, ta fara takawa daidai nan secretary dinta ya karaso.
Yana biye da ita a baya jikinshi har wani irin kyarma yake.
Cikin reception ta shiga tundaga wajen security entrance taga dandazon staffs sun zagaye katon screen din dake wajen.
Takowa ta somayi zuwa wajen mutanen dake baya baya suna hangota suka soma matsawa harta samu hanyar isowa wajen screen din, ji kake tsit babu sautin komai saina screen din.
Shades ne baqaqe a fuskarta wannan yasa ba a ganin kwayar idanunta amma yanda idanunta ya sauya da za a gani a zahiri sai mutun ya firgita.
She got the shock of her life cikin seconds daya.
Juyawa tayi kamar wata zakanya ta nufi board meeting hall, tun kafin ta karasa ma masu bibiyar labarai sukayo kanta secretay dinsu ya bude kofar hall din ta shiga daga ciki tabi kowa dake wajen da kallo ga masu daukan rahoto a gefe.
Basit na zaune kan kujerar da is supposedly hers ga fadwa a zaune gefenshi ta daura kafa daya kan daya tana taunar chewing gum.
“Anyone cares to explain What is going on here? Who dares to press a meeting in my absence? As the president?”
“Ex president mrs hidaya, mind your language” abdul basit yayi magana yana mai kallonta cikin ido da ido.
Wata iriyar dariya tayi, tare da takowa har cikin hall din tana bin mutanen dake zazzaune da kallo harma da fadwa da tunda ta shigo ta kauda ido kamar bata taba ganin hidayar ba.
Maido da dubanta tayi ga basit, “ex president??”
“Yes…let me break it down to you i am the highest shareholder of this company so i am the president as per the rules,”
Murmushi yayi yana mai duban mutanen dake zazzaune kowa ya sauke kanshi qasa, “prove” ya aje mata takardun dake shaida hakan, secretary dinta ya karaso ya dauka zai miqa mata ta watsar da takardun, tsabar bacin rai, “impossible..bazai taba yuwu ba, howw howw?”
Kallon secretary dinta tayi tace “get the security”
“i have terminated this partnership mr abdul basit,”
“You can’t do that mrs hidaya” daya daga cikin mutanen dake zaune yayi magana.
Basit ne ya dubeta, dukda glass din dake kan fuskarta yana hango tsantsar tashin hankali akan fuskarta, “this meeting is over, zaku iya tafiya.”
Tana kallo akan idanunta gaba daya shareholders dinnan suka fita daya bayan daya ya rage daga ita saishi sai fadwa,…da ta kasa tantance ita dince ko ba ita din bace, tama rasa wani irin tunani zatayi kan fadwa,
“Get out fadwa!!”
“Why? Meysa zan fita?“
“Ki fita nace!!!” Ta daka mata tsawa.
Wata iriyar dariya tayi har zata miqe basit ya dakatar da ita, “she’s going no where”
Mamaki, shock, tashin hankali babu wanda bai dabaibaye hidaya ba.
yau wani ne kan kujerarta, this chair? Datayi staining sweat da blood akdnshi?legacy din mahaifinta? Tashin farko on a blink of an eye Ya tafi kenan? Inaa bazai yuwu ba.
On the other hand, fadwa? Me zaman fadwa a wajen nan ke nufi kenan?.
Wayarta ta daga ta tura message cikin abunda baifi 2 minutes ba saiga Secretary dinta ya shugo da wani file sannan ya futa.
“Don’t waste your energy mrs hidaya, I’m only doing this to save the company”
Bata saurareshi ba ta fidda takardar yarjejeniyar su ta watsa a gabanshi, “as it is stated above, i can terminate this partnership at any given moment, mr basit, taheel company bata buqatar taimakonka, i don’t need you old rag”
Miqewa yayi tsaye yana dubanta yana murmuahi yacw “you still don’t understand whats going on mrs hidaya, i have overpowered this company, i have 80% share of this company,”
“You trick me?“
“Uhmm zamu iya cewa hakan, so i will advise you to lay low for now okay? Allow me to enhance the image of company, tun kafin a gano slush fund din da kika dunga ajewa, and all the illegal business”
At that point batasan sanda ta cire glass din fuskarta ba, ta maida dubanta ga fadwa da har zuwa lokacin danna wayarta take kamar batasan abunda ke faruwa ba, babu wanda yasan da maganar slush funds da duk wani illegal business dinnan daga ita sai fadwa sai kuma khaal.
“Mss fadwa will take your responsibility and duties, I can’t take the risk of destroying my image as the new president and the highest shareholder of the company”
Sake kallonta hidaya tayi sai a lokacin fadwa ta kalleta itama, wani irin kallo take mata irin “ni zakici amana?”
Sai a lokacin fadwa ta miqe tsaye ta dubeta “ukty…please, this is the only way to save this company,”
Zare glass din dake kan fuskarta tayi ta dauke idanunta daga kan fadwa zuwaga basit din,
ya bita da kallo, tunda ta shigo yake hango kaman mahaifiyarta, yanda hidaya tke haka take itama exactly babu wasa, yanxu data cire glass din ya kalla cikin kwayar idanunta saiya hango fattu karara akai.
Baima san sanda ya furta “fatttuuuuu” ba yana kallon cikin idanunta.
Yanda yake kallonta haka take kallonshi, saiya sauya gaba daya lokaci guda, ta hango wani abu kamar sadness a tattare dashi lokaci guda jikinshi ya mutu tunawa da sahibarshi.
Maganr illegal business dinda ya ambata baisa ta iya maida hankali akan sunan mahaifiyarta daya kira ba, juyawa yayi ya barta sandare kamar wadda aka zarema rai.
“I was so stupid for trusting you basit, This is my company…this is our legacy, there is no way I’m giving in…bakasan wacece hidaya ba, you can never threaten me with those slush funds, i will crush you, wallahi wallahi idan ban maida shares din taheel ba’a haifeni yar halas ba”
Dariya ya kyakyace da ya futa daga hall din ya barta tsaye, wallahi idan ance zai taba ganin tsoro karara a fuskar hidaya zai karyata amma still ta tsaya chak akan batunta, ina ga ta gano fadwa yarshi ce and itace ainahin ma mallakiyar kanfanin…….
Yana futa fadwa ta karaso kusa da ita tun kafin tayi magana hidaya da idanunta sukayi jaa sosai ta wani irin damko wuyanta, “ukty..ki saurareni,ba abunda kike tunani bane”
“…ni zakici amana? Ki Hada baki da makiyi na, ashe daman kudirinki kenan? Dagani sai ke,babu wanda yasan da batun slush funds dinnan,, how did he know about it?, how dare you fadwa“
Dakyar ta runtse idanunta, ta shaqu sosai har idanunta ya firfito tana haki ta tari nunfashinta, “banci amanar ki ba babu yanda na iya ne, he threatened me kuma yayi hakan ne saboda kar a gane manufarshi, and i accepted it saboda ina tunanin ta wannan hanyar ne kawai zamu kwato kamfanin mu, nasan daman zakiyi tunanin ko nice na fada mashi batun slush fund dinnan ba, kiyi tunani mana? Why would i do that? Wannan kamfanin namu nefa? Na mahaifinmu ne fa? Why would i betray you?”
Bangajeta hidaya tayi bafan tayi trusting maganrta ba tace “i’m coming for you”
Tana kaiwa nan ta fuce, tana futa fadwa ta kyakyace da dariya kamar wata tsohuwar mahaukaciya kafin ta dakata tana mai shafa wuyanta da hidayar ta shaqo…
“Bakiga komai ba tukunna, you are yet to taste the thirst of betrayal and youu…. are not coming for me this time around…i am coming for you hidaya, saikin tsugunna a gabana kin nemi alfarma a wajena, and this is just the beginning of your downfall”..
Haka ta dunga magana ita daya kamar wata tsohuwar mahaukaciya.
Hidaya na shiga office dinta ta tadda an cire office tag dinta as the president dake dauke da sunanta a jiki an kafa na fadwa, she just can’t believe this,she’s more embarrassed yau a idanun duniya fiye da matsalolin da suka faru a kwanakin baya.
Wayarta tayi hanzari dauka ta soma dialing number private investigator informant dinta datasa yayi mata bincike akan basit din, harkar dirty business irin wannan tasan yanda akeyinta, cin amana a business ba komai bane ba, partners can be your biggest enemy on a bling of an eye, so she’s an expert on it, tayi hasashen irin haka zata kasance daga ranar dataga ya tunkareta kuma ya bata helping hands just like without asking for anything in return tundataga haka tasan akwai wata a kasa, duk a tunaninta komai is under her control batayi tunanin zai shammaceta ba, wannan yasa tun a lokacin tasa a nemo mata anything da zata iya using against him dat will be useful to her when the right time comes, shiyasa, a take ta umarcesu da su nemo mata komai akan basit, duk wani abu da zaimata amfani a irin lokaci kamar haka.
“Princess, ya naga you’re not happy? Burinki ya cika fa? Kamfanin nan naki ne gaba daya, hidaya is below you,
Abdul basit yayi magana yana kallon fadwa, “no papiiii..this is not enough…banga tsoro akan idanunta ba, she’s definitely going to do something,”
“Nima naga hakan, but babu abunda zata iya, i am the president, and the higest shareholder, inada 80% na kamfanin nan, and she is only keft with 15%, zan iya korarta kora ta wulaqanci idan kinaso”
Last furicinshi yasata ta kalleshi ta saki wani irin murmushi, tare da kamo hannunshi tace “yes…lets do that,i don’t care kozaiyi affecting company, this can be to our benefit, i want her to bow, i want to see fears akan idanunta na loosing komai papi”
“As you wish princess”
…….
Tuki takeyi kamar zata tashi sama tsabar gudu, yau ko driver bata dauka ba cause this is very important to her, tana isowa inda zasu hadu tayi parking motar ta danna mashi kira, juyowa tayi sai gashi tsaye tayi unlocking motarta ya shugo ciki, yana shugowa ya gaisheta cikin girmama, ba tare da wnai bata lokaci ba ya bata file din dayayi profiling basit.
Karba tayi ta soma budewa tana warware igiyar takardar.
“Ka bunciki komai,”
“Yes ma’am,“
Karantawa ta soma yi at the same time yana mata bayanin tarihin shi basit din wanda yasha wahala sosai kafin ya samu yabi didigin tarihin rayuwarsa da yanda yake tafiyar da business dinshi.
“Ya taba aiki a taheel???????”
“Yes ma’am, a shekarar 1980 ya fara aiki, sannan an koreshi sakamakon saida babban project din da akayi a shekarar,”
“No wonder” ta fada tana girgiza kai ta duba next page of file din, yabar kasar zuwa eygypt, and he blows lokaci guda”
“How? Ta inane source din kudin?”
“I couldn’t find a proper answer to that saboda……”
“Then menene amfanin binciken? Why cant you find anything? How did he start the company?, his hands are dirty dole akwai wani abu, there must be some”
“I’m still on it ma’am”
Watsa mashi file din tayi ta kama steering din motar kamar zata balla idanunta yayi jaa sosai tace “you’re useless, this isn’t enough, dole akwai abunda yake boyewa, i need something on him, something….”
Katse ta yayi yana bude file ya miqa mata “there is ma’am”
Idanunta kamar zasu firfito ta kalleshi, “nayi bincike akan duk wani source na income dinshi, da ownership din kamfanin sa gaba daya komai baya karkashin sunansa,”
“So???? Kana nufi yana yima wani aiki kenan?”
“Yes ma’am”
“Who could that be?”
“Shi nake buncike akai,” ya bata amsa
“Nayi trippling payment dinka, Na baka nanda gobe, ka bincika min ko’ina, you need to find who ever is behind him”
Shida yasan irin kudin datake bashi dayaji zata biyashi sau ukun kudin tuni yaji wani energy yazo mashi, yau duk yanda za ayi ba zuwa gobe ba saiya nemo mata abunda take nema.
Jiki na bari yace
“Yea ma’am”
Yana kaiwa nan ya futa.
Ta juya akalar motarta.
Waya ta gani daga school dinsu barad tunda safe ake kira amma bata cikin natsuwar da zata iya dauka, sai yanxu, nan aka shaida mata yayi accident dukda is minor, hankalinta ya tashi sosai ta kasa natsuwa ba kadanba, bata taba jin tayi negleting din danta ba sai yanxu, amma duk da haka yanxu is not a perfect timing to think about that, and tasan for sure he’s on a safe hands.
Gaba daya lisaafinta ya gama juyawa a ranar gaba daya ko rintsawa bata iyayi ba, ta shiga nan ta fita nan, dukdan ta samu yanda zatayi ta maida komai how it is supposed to be, shareholders dake kamfanin gaba daya kowa data kirasu saisu juya mata baya, su nuna mata babu yanda zasu iya, she couldn’t get the support from them, sai a lokacin ma ta gane waenda suka sayarma basit nasu shares din kamfanin and to think of mutanen nan tare sukayi building taheel da mahaifinta abun yayi masifar daure mata kai.
Lallai yanxu she’s tasting the feeling of being betrayed, tukunna ma dai…..
Kwanan ranar a zaune tayishi, ta kasa rintsawa kwata kwata, bata yafiya, kuma batajin duk wanda yayi betraying dunta zata taba yafe mashi, bazat iya runtsawa ba saitaga taheels a hannunta, a gobe goben nan.
Dan rintsawar datayi a study room dinta na rabin awa ko cikawa batayi ba karar wayarta yasa ta bude shanyayyun idanunta.
Call din wanda ta gani ne yasa tayi saurin dagawa takai kunne,
“What?????
“Yes madam, na tura maki documents din,,”
Kasa tsaywa ta saurareshi tayi ta kashe wayar tare da bude e-mails dinta, taci karo da wanda ya tura mata, ga sunan daya bayyana a jiki, (fattu) saida ta nanata fattu dinnan aranta,suna ne mai girma a wajenta don sunan mahaifiyarta ne.
Wayar ta sake kiranshi tace “who’s she? Wacece ita? Menene alaqarshi da ita?”
“Identity dinta is hidden ma’am but…”
“Menene amfaninka if you cannot find her identity?are you not professional enough? Inyi hiring wani ne?? Give me full details, whoever she is, koma wacece,”
Ganin kamar tana neman hasala yasashi cewa
“There’s something else ma’am”
“I hope this will Be helpful if not…”
“Allegedly..na samu wasu bayanai kan cewa yanada diya mace,”
“What?? Yanada ya mace? From binciken dakayi banga alamun ya taba aureba balle ya aje heir,”
“Babu wanda yasan ko wacece ma’am, “
“If that’s the case ya boyeta kenan from the world, but why? She could be his threat kenan”
“Yes ma’am yanda kikayi assuming”
“Inason ka nemomin hotonta,“
Tana kashe wayar kawai tayi murmushi, this is the best news data samu da safiyar nan kuma zata iya runtsawa yanxu, idan har zai boye diyarshi that means bata hanyar daya dace aka haifeta ba kenan, dole ta gano koma wacece don ta hanyar nan ne kawai zata yi amfani dashi ta hanyar koya mashi hankali.
Misalin karfe bakwai daidai ta fito daga gida, as usual looking so dashing, fuskarta a hade babu annuri ta shiga motarta, driver yaja motar suka kama hanya.
Da zamanta da tafiyar tasu bazai wuce thirty minutes ba gaba daya don zataje school dinsu barad ne, karar notification din wayarta yasa ta dago wayar.
Ba tare da wani bata lokaci ba tayi clicking message din tare da rubutun dake tafe da message.
Hoton basit ne da fadwa different types don yakai kusan guda goma on a different occation, sauke idanunta kasa tayi inda ya rubuta “FATTU”
Jikinta hannuta komai ma bari ya somayi har wayar ta sulale ta fadi kasa, kamar mahaukaciya tabi wayar ta dauka tana duduba idanunta kamar zai zagwanyo, innalillahi wa inna ilaiahi rajiu’un,
Hannunta na rawa tayi dialing number shi, “me…me..nene..wannan? Who…is she?”
“Thats his daughter fattu”
Wani irin gajeran suma tayi ta farfardo da gaggawa tace “kasan wacece wannan kuwa? Ya akayi fadwa ta zama fattu? Ya akayi ta zama diyarshi? Ina ka samu wannan? Its possible sun hada bakine shida ita, ay bansan cewa haka take cin amanata ba sai yanxu,”
“Madam…wannan itace fattu, sunanta fattu ba fadwa ba”
“Kai bakada hankali ne? This is my sister…fadwa abdullah taheel”
Shi kanshi investigator din ya rasa ta yanda zai mata bayani, yanda she’s shocked haka shima hes shocked sosai, ya kasa comprehending komai.
Ya akayi yar basit ta shigo gidan su? Bai sani Babu wanda ya sani, gashi nan dai identity dinta a duniya shine fadwa amma a badini ya ce ga basit wato fattu, bincikensa kenan.
Kashe wayar kawai hidaya tayi, a daidai lokacin maganganun abdallah na zuwa akanta, “kina tunanin mahaifinki shine yaci amanar mahaifiyarku ko? Toh ita mahaifiyarku itace taci amanar shi,“
Wannan tsoron da tashin hankalin da fadwa ke son gani akan fuskar hidaya shine ya bayyana, don ni har kamar hawaye hawaye nake gani kan fuskarta, ta umarci driver ya juya akalar motarshi zuwa island dinta.
Gudu suke sosai har suka iso tama manta da wani barad tana isowa ta shiga yatch dinta.
Suna isowa tayi hanzarin shiga motar da zata karasa da ita, har zuwa lokacin wayarta na hannunta tana kallon hotunan fadwa da basit sannan da documents din nan daya tura mata da asuba.
Wayar na hannunta messages suka dinga shugowa rutu rutu kamar yaqi, notifications daban daban daga social media, saiga calls na biyo baya, wannan na kastewa wannan na shugowa, messages din ta fara dubawa bata fuskanci komai ba yoh ta ina ma zata fuskanci abunda ke faruwa, hankalinta a tashe da abunda taji kuma ta gani, wanda take fatan ba haka bane.
Driver na tsayawa ta tunkari cikin uncompleted building din, su black basu san da zuwanta ba don bata zuwa a wannan lokacin kwata kwata.
Ciki kawai ta shiga suna kwakwance sun shawu sosai basu farfado ba ta fada dakin da abdallah ke rufe.
Tana shiga ta kunna haske ya bade dakin gaba daya sannan ta tako har inda yake kwance,”abdallah!!!!”
Shine abunda ta furta kawai, yanajin itace ya tashi zaune gaba daya yayi busu busu da gashi yau shekara kusan nawa ta kamashi, yana mai fuskantarta, yanayinta ya gane cewa ranar dayake jira ta bayyana kenan.
Yau shekara kusan uku ne, ta kulleshi akan mahaifiyarta, akan ya fadi sirrin mahaifiyarta da babu wanda ya sani sai shi kadai.
“Kin dawo ne na sake maimaita maki ko kuma har yanxu baki yarda ba?”
“Karya kake yi karya ne, mahaifiyara bazata tana cin amanar abbu ba, zan iya sawa a kasheka yanxu idan baka karyata kalamanka ba”
“Karki yaudari kanki, idan kinsa an kasheni bazai chanza gaskiyar almari ba, mahaifiyarki itace butulu, itace taci amanar mahaifinki, da kaskantacce, kuma wulaqantacce, wanda mahaifinki ya taimaka wa alokacin da yafi kowa buqata, saboda san ransu suka ci amanarshi,”
“Karya kake!!!! Karya ne bazai taba yuwu ba…mahaifiyata ta kasance mai amana, abbu yaci amanarta, shine yaci amanarta”
“Alamu sun nuna gaskia dake boye Shekara da shekaru sun bayyana a gareki, kuma kin kasa amincewa da hakan?, toh ki bude kunenki dakyau, ko ki yarda ko karki yarda wannan ita ce gaskia daya…”
“Mahaifinki ya kasance mutun mai mutunci mai taimakon na kasa dashi, mai adalci, ya daukeni nida basit ya rufa mana asiri amma hakan baisa mahaifiyarki da basit sun ci amanarshi ba, babu wanda yasan da abunda ke tsakaninsu shekara da shekaru sai ni kadai, don ko su kansu basu sani ba, nayi dakon wannan cin amanar akan idanuna na shekaru, banida damar bayyanawa, haihuwar yar uwarku shine symbol na cin amanar taheel da mahaifiyarku tayi…..yar uwarki Fadwa yace ga abdul-basit.”
Sharrrr saiga hawaye kan fuskar hidaya kamar fanfo, sosai fa ba kadan ba tayi taga taga zata fadi kasa ta zube a wajen.
Babu abunda take sai jujuya kanta, maganar shi ta karshe na yawo akanta..”yar uwarki fadwa yace ga abdul-basit”
Takai wajen minti goma a haka ta kasa motsawa, abubuwa da dama na yawo akanta, lokacin da mahaifinsu ya kawo taj gidan, da irin yanayin da mahaifiyarsu ta shiga, da yanda suka dunga treating mahaifinsu saboda ita, wallahi baqin cikin su ne na yanda suka daina kusantarshi gaba daya yasa zuciyarshi ta buga, sun nuna mashi tsana mafi tsanani musamman ita.
Abdalla dai na zaune yana kallonta bai sake cewa komai ba, tana daga nan zaune aka banko kofar, warrant na arrest dinta aka bada amma zuwa wajen nan da akayi suka tadda yaran black dakeda illegal makami bindigu yasa dole a kama duk wanda ke ciki.
Ba kowa ne kuma ya bada tip din inda take ba sai black.
Yaranshi gaba daya aka kamasu.
“You’re under arrest mrs hidaya abdallah, for……..”
Haka suka dunga jero mata crimes da charges iri iri kanta ma yayi wani irin dumm batajin abunda suke fada kwata kwata.
Aka fidda abdallah aka sashi a mota zuwa asibiti don bashi taimakon gaggawa.
Few minutes ego..
Lokacin da take zaune a mota bayan investigator ya tura mata hoton fadwa da basit, wannan mesages din da suka dunga shigo mata bana komai bane saina abubuwan da aka tashi dashi a safiyar, an fidda evidence dumu dumu na illegal business datake a karkashin kamfanin, bayan ta iso island lokacin data wuce su black, batasan baya tare da yaransa dake sheme sun shawu ba, kuma yaga isowarta, yayi mamaki sosai wannan yasashi sauraron conversation dinsu ta hanyar recorder daya saka a dakin, bayan ya gama jin duk maganar tasu yaci karo da news din dake yaduwa wannan yasa yayi gaggawar tura sako da jiran a bashi umarni, ana bashi kuwa ya fita daga island yabar yaranshi sannan ya samu waya ya kira ya shiada ma police inda take sannan akwai wanda tasa akayi kidnapping idan anje za a ganta a wajen.
Daman already anyi tracking line dinta don anje gidan da warranty din questioning dinta ba a ganta ba, ana tracking location dinta kuwa yayi daidai da inda aka turo report, wannan ya basu damar zuwa don ayi arresting dinta….
Wayyo rayuwa kenan….😭
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID