Chapter 85
Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 33 min read
Suna shiga cikin motar dashi wasu mutane biyu dake zaune a baya sukayi wrapping din kanshi da wani kyalle baki, har suka bar wajen bai iya ganin fuskokinsu ba.
“Suwaye ku? Me kuke nema dani? Me na maku?”
Wanda ke zaune mazaunin gaba ne ya jiyo yana taunar cingum, kunenshi daya kamar an taune shi sai gefen idanunshi da yayi baqi sosai, “hahaha, dakayi shuru da bakinka qwaro, daya fi maka, at long last dai mun kamo ka”
“Ku fada min ku suwaye, me kuke nema dani”
Da sukaga ya ishesu da tambaya sai kawai suka toshe mar baki.
Hayakin vape da taba duk ya cika motar gaba daya.
Abuja nigeria…
Share hawayen dake fuskarta tayi sannan ta guara zaman wayan a kunenta “malam ko ke fa, yanxu tunanin yanda zaki samarwa kanki matsuguni zakiyi a cikin gidan nan, inace akwai babban yayansu a gidan, na rantse da allah in nice ke saina aure shi, tuni da taimakon malam zan hauqe mashi”
“Hmm jamila kenan, mutanen da suka wulaqantani, suka cimin mutunci, suka min abunda bazan taba mantawa kike cewa na shiga cikinsu?, ay wallahi saina tarwatsa farin cikin gidan”
“Na nawa kuma kawata, hahah.. ke dai har yanxu wallahi hadiza kanki baya jaa, an an toshe maki basira gaba daya, yanxu idan kika auri wannan sameer din menene bazakiyi ba, ka kudi a arziki, sannan kuma ta bayan fage ki ci dunduniyar su ki balbala masu wutar masifa gidan ya tashi gaba daya kawai”
“Hmm kina tunanin zan iya hakan ne? Wannan, matar nan a tsaye take akan iyalanta,”
“Toh ay shikenan, shawara nake baki, kuma saikinfi kowa amfana da shawara, kinsan abunda nake nufi ay”
Wani irin murmushi hadiza ta sauke, nidai ban taba ganin hadiza tayi irin wannan murmushin ba sai yau”
Suna sallama da jamila ta wanke fuskarta tass sannan ta fito daga bathroom, yanxu lokacin yin dinner ne wannan yasa ta futa kitchen don ayi da ita, tunda suka dawo gidan ba wani aikin kirki hadizar keyi ba, yawanci duk sabeeha keyi, saidai kaga ta fito jefi jefi, zuwa kitchen, ko ta shigo dinna. Saidai kaji tana bada order yi wancen ajje wanchan dauko wanchan, har kusan fada saida sukayi da indo dake itama idanunta a bude yake, ta nuna mata fa kartaga wai dakinsu ya banbanta dana yan aiki, yanda suke aiki ana biyansu itama haka zatayi ita da diyarta.
“Ke asma’u fita da wannan warmers din, zuwa dining”
“Anty indo”
“Kawo na taimaka maki” hadiza ta fada tana mai karban warmers din.
Sabeeha na daga bakin sink ko juyowa batayi ba, saima aikin gabanta da takeyi kawai.
Nanna ce kawai da hamad zaune kan dining banda anne, yawanci ita a sama take saboda ciwon kafa.
Kallon hadiza nanna tayi, murmushi kwance kan fuskarta as always tace
“Sannun ku da kokari hadiza”
“Yauwa hajiya barka da dare”
Sallamar laila ce tasa duk suka juyo suna kallonta musamman hadiza, har wani irin murmushi tayi ganinta, “yau anan zakiyi dinner ne kishiyallare”
Dariya laila tayi tace “nanna yau tuwo mami tayi, ni kuma gaskia banson cin tuwo harga allah”
Ta karashe tana mai janyo kujera ta zauna, hadiza ta kalleta tace “bari a kawo maki plate”
“Tohm nagode”
Ciki hadiza ta shiga ta futo ta aje mata plate din laila tace “ina…uhm bansan sunanta ba, dan allah kuyi hkuri da abunda maya tayi mata dazu”
Kallon mamaki nanna tayi mata tace “me mayan tayi masu”
“Wallahi nanna ni kaina bansan me tamata ba, dazu da kikace mu dauka cake a fridge shine..”
Saurin katseta hadiza tayi “haba ba komai, itama sabeehar ay laifinta ne”
“Sabeeha” ya maimaita sunan a ranshi, yana jinsu saidai baice qala ba saima cin abuncin dake gabanshi da yakeyi, “me ya hada ta da wannan mara kunyar? Koma menene yasa maya ce batada gaskia”
Wayar laila ce tayi kara, har hadiza ta juya zata koma tajiyo muryar maya doj a handsfree tasaka, “kina ina ne”
“Ina part din anne, kizo yau anyi dambu”
Kashe wayar kawai maya tayi,
Cikin abunda baifi minti biyu ba sai gata, babu ko sallama, daidai nan hadiza ta shugo parlor da wani plate din a hannunta,
“Amaryar dady babu sallama”nanna ta fada tana mai duban mayar data ja kujera ta zauna, hamad kuwa wata iriyar zagbgegiyar harara ya watsa mata ko ta kanshi batabi ba.
“Salam!”
“Wa alaiki salam!” Nanna ta amsa ta,
Aje mata plate a gabanta hadiza tayi sannan tace “me zaki ci a zuba maki”
Wani irin kallo maya ta mata irin banganeba, ganin nanna na wajen yasa ta waske “zan zuba dakaina”
“Toh akawo maki lemo?”
“Barshi bana buqata”
Binsu da ido nanna da hamad sukayi, shifa bayason a raina babba ko kadan, ji dai yanda take ma wannan da zata haifeta magana babu respect ba komai,
“Jeki kawai hadiza, in tana buqata zata dauko da kanta” nanna ta fada
Jiki a mace hadiza ta juya.
Bayan sun gama dinner anan parlor suka yada zango hamad ya wuce sama sukayi hira da masoyiyarshi anne, sai wajen tara saura ya sauko kasan, anan ya taddasu sun bace, laila na waya maya kuma ta kurama wayanta ido, “keee”
Ya kira maya don a daidai saitin ta ya tsaya, “are you deaf?”
A harzuqe ta juya ta kalleshi , “bakasan sunana bane, ko ke aka rada min?”
Cije lebenshi yayi kafin yace “kije anne na kiranki”
Ay saida gabanta ya bada wani irin daram, baima tsaya ya sake kallonta ba ya wucewarshi, ta miqe ta wuce sama.
Da sallama tayi knocking kofar bayan an bata izini ta shugo, anne na zaunw kan babban carpt din parlornta gabanta shaqe da warmers na abinci data gama ci, sai cup din tea da take sipping.
Zama maya tayi a kasa kusa da ita tace “barka da dare anne na, you called for me”
“Yes i did”
“Inaso ki tattaro kayanki gaba daya daga part din sameer ki dawo nan,”
Hankali a tashe ta kalleta, harga allah batason dawowa nan wallahi, part din anty laila tafi sakewa sosai achan, babu takura babu tsangwama, idan zata futa sau dari babu wanda zai tsaya questioning dinta, shes just living her best lif.
“Anne, I’m comfortable achan, and ina taya anty laila yan gyare gyare”
“Wani gyare gyren zaki tayata tanada helpers har guda uku?”
“Anne….”
“That’s final…and secondly karki sake treating helpers din gidan nan yanda kikayi treating yarinyar nan daxu, suma mutane ne kamar kowa and sunada gata, treat each and everyone one of them with respect understood?”
“Yes anne”
“As from today Hamad zai dunga kaiku school and shi zai dauko ku, jeki saida safe”
Miqewa maya tayi, ko iya amsa mata saida safe batayi ba ta futa rai a bace kamar ta kumbura ta face.
Tana saukowa ta soma dialing number mummy ta.
Cikin shesheka ta soma magana “Mummy na gaji, na gaji, I don’t want to stay here anymore please its been 2yrs now mummy”
“Meya faru baby? Whats wrong talk to me?”
Aka amsata daga chan, “nidai kawai na gaji, i hate the environment here, i missed you i missed daddy dan Allah kumin booking flight na dawo”
“Haba baby na, yanxu fa zaki shiga final year, i promise you zamuzo nida dady, aiki ne sun mana yawa kinji, i missed you more than life its self my dear,dont cry okay,”
Rai a bace maya ta kashe wayar, daman tasan bazasu yarda ba, ita ta gaji da garin nan, ta gaji, she missed everything, her lifestyle, rayuwanta achan england her friends komai ba, gashi yanxu an fara saka mata strictness tun ranar da nanna ta ganta a hotel”
Samun waje tayi nan bakin compound ta wajen backyard ta zauna tana hawayen takaici.
“Zaki bata kyakyawar fuskarki da hawaye,”
Dagowa tayi taga hadiza tsaye, hannunta rike da smoothie data lura da shi sukafi sha ita da laila.
“Waya bata maki rai kike kuka?“
Wani irin banzan kallo maya ta mata, “kiyi hkuri idan tambayar danayi ta bata maki rai, amma duk wanda ya bata maki rai allah bazai barshi ba, kuma an dau hakkin ki da daddaren nan an sakaki kuka”
Wani irin sanyi maya taji aranta, saitaji kanta na wani irin girma sosai, “ga smoothie, indo tace kinason shansa da sanyinsa ko”
Kallon smoothie din tayi sannan ta amsa, kura mata idanu hadiza tayi har saida ta saka straw din a bakinta tasha kusan rabi, murmushi hadiza tayi ganin tayi kamu babba.
“In zauna a kasa in jira ki gama” batajira amsarta bama ta zauna a kasa tana kallonta jefi jefi,wayarta ne tayi ringing ta amsa, “haba babe sai yanxu zaka kirani?”
Chan akayi magana wadda daga maya sai wanda ke maganar sukeji, “dan allah kayi hkuri,zamu hadu, im in a tight position rn”
Tana gama magana sai kuma tayi wani makirij murmushi hadiza na kallonta harta gama wayar ta miqa mata sauran smoothie din harta tashi hadiza ta miqe tace “toh saida safe”
Ko kallonta bata sake ba ta wuce part din anty laila ta shaida mata abunda anne ta fada, ran anty laila ya baci sosai don ta rasa meysa anne kejin haushin duk wanda yazo kusa da ita, me akema mayar da suke tunani? Inba suna tunanin wani abun take mata ba mey zaisa tace ta koma part din, kai abunnan ya bata mata rai sosai.
Washe gari ta kama sunday, duk wani preparation da anne tasa a mata anyi komai, kama daga registration da sauransu, harkar masu kudi, duk wani abu daya kamata a nema anne tayi providing wanda bai samu bama tace za a kawo daga baya.
Wajen karfe bakwai da rabi na dare anne tasa aka kira hadiza da sabeeha, saman suka hau har inda take sabeeha sai kallon saman take ya burgeta sosai don gaskia masu arziki ne sosai nesa ba kusa ba, saidai ba komai ke dadata ba don taga abubuwa sosai na morewar rayuwar a saudi, nan dinma dai ba banza ba.
Tunda hadiza taji anne na nemansu sama gaba daya ta rasa natsuwarta, ta kira jamila yakai sau goma bata dauka ba, sabeeha ko ta tambayeta yafi sau ashirin shin ko tayi wani laifi ne, don har kusan marinta saida tayi, duk a tunaninta ko tayi wani abun da ya jawo za a koresu, hakanan ta wuce saman sabeeha na biye da ita a baya.
Suna shugowa parlor ba kowa sai kamshin turaren wuta mai dadin gaske dake tashi.
Shugowar ta kamar shugowar wata basarakiya, she’s a definition of strong woman, bata daukan nonsense sannan bata yarda kwata kwata a taba mata ahalinta, the santuraki name has been going for over decades.
Zama tayi hadiza ta dan duka daga zaune wani irin maqoqon baqin ciki na bullo mata a zuciyarta, wallahi bata kaunar matar nan kwata kwata ko kadan.
“Hajiya ina wuni ya kafa”
Kai tsaye anne ta amsa ta “lafiya, ya baqunta”
“Hajiya ay babu baqunta, gida ne nan din ay”
“Masha allahu”
Muryarta a sanyaye tace “Ina yini”
“Lafiya lau”
Shuru ne ya dan biyo baya, kafin anne tayi gyaran murya tace “gobe ki shirya zaki bi su laila makaranta, duk wani abunda zaki buqata yana wajen hamad”
Da mamaki hadiza ta dago, don bata gane kan zancen ba “hajiya ay bata zuwa makaranta”
“”Gobe zata fara”
Shuru hadiza tayi tama rasa me zata ce, “duk abunda kike buqata ki fada”
Sunkuyar dakai sabeeha tayi, wallahi taji dadi sosai aranta ba kadan ba, bata tabsa tsammanin tana da wani rabo na karatu ba tun bayan dan wanda tayi a saudi,”allah ya saka da alkahiri allah ya kara budi ya kara arziki mai albarka”
Murmushi anne tayi tace ameen”
Sai a lokacin hadiza ta dawo daga tunanin data shiga, ta dan murmusa harda sunkwi dakai tace “allah ya albarkaci zuria, ya kara arziki mai albarka mun gode sosai hajiya kun gama mana komai”
Girgiza kai kawai anne tayi ta sallamesu suka sauka kasa, tun daga corridor suka raba hanya hadiza tayi waje sabeeha ta shiga daga ciki tayi shimfida ta kwanta.
The next morning ta kasance monday morning, the first week of new session kenan, cikin shiri laila ta futo ta nufi part din anne dukda akwai dan tazara tsakanin nasu, tana shugowa ta wuce sama other side part inda maya ke ciki, koda ta shiga barcinta take hankali kwance ba takura,dakin yayi kyau sosai wallahi ba kadan ba.
Jan bargonta laila tayi tace “wakeup 9 ya kusa ki tashi haka nan”
Yaudai ta tashi other side of the bed, don tunda maya ta tasheta take masifa, ahaka dai tayi wanka ta soma shiri, shafa chan goga chan haka ta dunga yi, laila ko tunda ta fita daga dakin kasa ta sauko, hamad ya shugo, indo yasa ta kira sabeeha, aikuwa sai gata ta fito sanye da kayan laila da aka bata sai kuma hijab data zabga akai.
Murmushi laila tayi tana matsowa kusa da hamad tace “yaya whats her name”
“Ask her your self” ya bata amsa
“Kai amma tana kama da..”
karasowar sabeeha da gaishesu datayi yasa laila dakatawa tace “good morning to you too, finally na samu course mate”
Murmushi sabeeha ta danyi mata hamad ya kauda kanshi.
Kamshin turarenta ya tabbatar masu ta iso fa, hamad yayi gaba abunshi bashida time dinta, tana saukowa ko kallon inda laila ke tsaye da sabeeha batayi ba tace “muje”
Gaba tayi laila tabi bayanta sabeeha followed them too har gaban range rover dake parke,
“Ya hamad wazai zauna a gaba”
Sai a lokacin maya ta dago taga sabeeha, take yanayinta ya sauya, “ina wannan din zataje?”
“School” kai tsaye laila
Ta amsata
“Wani school din?”
“School dinmu mana,”
“Wtf, house maid din ce zata bimu school? Kula damu zatayi achan din kokuwa”
Ran hamad ya baci ya futo ya budema sabewha kofar gaba yace “get in”
Jiki a mace sabeeha ta shige,maya ta kama kugu, “wai meye haka ne?”
“Ki shugo dan allah zamuyi latti fa”
A fusace ta bude bayan ta shiga ta zauna, tana mai hararan kujerun gaba, ta rasa me kawo yar aiki yake nufi? Nannying dinsu zatayi ko menen?
“She’s schooling with us, jiya anne ta fada ma ya hamad nima wajenshi naji”
Message din da laila ta tura mata ne yasa ta doka wani zagi, “kam bala’i, wallahi bazai yuwu ba”
Kasa kasa laila ta soma mata magana “anne fa tace dole ta dunga binmu school, why are you untop of your voice? Zaki hanata zuwa ne”
“But this is so unfair, ya za ayi a hadamu da yar aiki? Disgusting people? Ay abun kunya ne ma idan aka gane, sannan kuma a hadamu a mota daya?”
“Not a single word from your uncontrollable mouth, idan kika sake magana cikin motar nan you will get out”
Bakinta fa baya shuru, batasan naga da ita ba “that will be been better”
Bai kulata ba ya cigaba da tuki, sabeeha dai tayi shiru kuma duk taji abunda ta fada don daga murya take sosai, aranta sai takejin wani irin zafi,
Har cikin school ya shiga dasu, afusace maya ta futa afiya tabi bayanta ya rage daga sabeeha saishi a motar.
Wani envelope ya bata dake kunshe Entry card da wasu document haka harda timetable din course din da take.
Hannu buyu tasa ta karba taki yarda su hada ido dashi, tun ranar,
“Your Entry card and other accessories da zaki buqata, zan baki number na take it down, idan wani abu ya taso just give me a call”
Godiya ta mashi sannan tace “banida sim a wayar”
“Okay” kawai yace mata sannan ya fito itama ta fito ya jagoranceta zuwa cikin makarantar, dake
Shima anan ya gama karatu so yasan wurare sosai haka ya dunga zagaye da ita ya nuna mata wurare sosai sannan ya hadata da lecturer da zai engaging dinta in some activities din da ba lallai ta iyasu ba ko ta sansu karya zamana ita ce aka bari a baya.
Koda ta shiga first lecture she was so uncomfortable, dukda kowa na harkarshi, haka ta samu chan kuryar class ta zauna, kuma tunda aka fara karatun tana dauka dake kanta na jaa sosai.
A second class suka hadu da laila, she was so nice to her wallahi, harta saya mata lunch ta kawo mata auditorium dinsu.
Lokacin tashi nayi hamad yazo ya daukesu, maya dai sai faman gunguni take, rai a bace har suka iso, su auka fara fita sannan ya bama sabeeha sabon sik card tayi mashi godiya ta wuce cikin gida.
Da sallama ta shugo dakinsu ta tadda hadiza na cin abunci, ko kallonta batayi ba saika sabeeha ce ta mata sannu da hutawa.
“Keda wa kuka tafi makarantar?” Itace first question datayi mata.
“Nida su biyun nan bansan sunayen su ba sai yayansu”
Girgiza kai hadiza tayi aranta tace “samun waje”
Da daddare sabeeha ta cire sim din da mutallib ya bata a samsung din ta saka sabon, tunda ya bata wayar bata taba kunnata ba sai yanxu, tana saka sim din number shi kawai ta fara gani yayi saving da ya hamad, saita samu kanta da dan murmusawa, don yanada kirki sosai bashida fada kamar dayar kanwar tasa jarababbiyar, ita dayar kuma babu ruwanta very nice.
Saudii..
Yau kwananshi biyu a hotel, and so far that’s what make him relax and revive abubuwa da dama, rabonshi da mutallib tun ranar and he regret yanda suka kare not in a good terms, he didn’t listen to him yanda ya roki hakan, abunda yasa yayi reflecting har yayi dana sanin rashin jin daga gareshi shine tunawa da yayi da sabeeha, haka ta dunga rokonshi akan ya saurareta yaqi, ya amince da ita yaqi, ya fuskanceta yaqi, al’amarinta ya mashi katutu azuciya, he feel guilty of his action, the way he treat her the way ya dunga wulaqantata its pains him.
Abun na biyu kuma maganar detective da yayi, he has come to conclusions of yanda zaiyi, he wants to be center minded, leaving all emotions behind, dole ya gano komai.
Knocking da akayi mashi ne yasa yace “yes come in” Aka shugo, wannan baturen ne yaronshi ya shugo fuskanshi wasai, “morning sir”
“Morning merk”
“Your suit and the cards are all ready” baturen ya fada
“Thank you merk”
Fita merk din yayi shi kuma ya miqe zaune kugunshi na daure da towel ya sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya tako gaban dresser yana kallab attractive muscles dinshi, “i have to do this” ya fada beneath his breath.
A gaggauce ya shirya cikin suit din da suka amshesa sosai ya saka rolex dinshi sannan ya zauna ya saka sock da givench covers ya miqe tsaye, kokarin bottoning wandonshi ya soma sabeeha ta mashi flashing sanda bashida lafiya, tana saka mashi button din riga, saurin runtae idanunshi yayi yana hango yanda take mashi smiling.
kauda tunanin yayi hanzarin yi kafin jikinshi ya mutu ya saka tie ya feshe jikinshi da turare, kai masha allah la kuwwata illa billah, he looks damn richyyy cute and handsome, irin mafia boss dinnan, curly hashin nan sai kyalli suke, fuskar nan sajen dake wajen ya kwanta baki lub, ya cika namiji cikakke ingarma lols
Wata gucci bag ya dauka dake dauke da surface a ciki da wasu important abubuwa sannan ya fito gabanshi na faduwa, addua yayi take yaji duk wani abu ya kau mashi ya shiga lift ya sauko kasan.
Yana fitowa baturen nan ya bude mashi seat din baya har da dan sukwi dakai, hannu kawia ya daga mashi ya shiga bayan ya zaune shi kuma ya zagaya dayan side din ya zaune shima driver ya jasu.
Motar ba motar dayazo da ita bace, wata zabgegiyar ford ce, bayanta an kafa T-ford a jiki, the only car he designed for him self, guda uku ce kawai kaf duniya.
Tafiyace mai dan tsayi sukayi babu abunda yake sai kallon window da yanda ciyayi ke yawo, “everything is set sir”
Juyawa taj yayi ya dubeshi, ya dan maida idanunshi kan screen din gaban shi ya kalla shima kafin yace “good job merk”
Daidai taheel company motar ta tsaya, kai zo kaga idanuwa kowa ya juyo yana son ganin wazai futo, bai wani ja masu rai ba ya futo, maiestically kai kuzo kuga kallo, baki a sake mutane ke kallon shi, surprisingly unsurprising, waenda suka san lafiyarshi lau basuyi mamaki ba don toshiyar baki aka masu, tafiya yake kamar bahubali ana matsa mashi ana sunkuyawa to show utmost respects to him, kwarjini da haibarsa kadai bazaisa ka tunkareshi bama.
Kai tsaye ya shigo reception nanma suka bishi da ido, kowa na tsoron tunkararsa karma mutun ya rasa aikinsa.
Merk na gefenshi suka shiga lift basuyi landing ko’ina ba sai office dinta.
Nanma secrwtary dinshi na ganinsa harzai tafi ciki ya dakatar dashi, dole ya tsaya merk ya bude mashi kofa ya shugo daga ciki.
Unexpectedly kawai ta ganshi ya shugo dagowan da zatayi, saida gabanta ya dan fadi, kai tsaya yaja kujerar baki ya zauna ya daura kafa daya kan daya, yau ko tukarar inda takema baiba.
“Good morning mrs hidaya”
Kambuuu, hidaya nitsewa ne kawai batayi ba ta zuba mashi ido, is he insane?
“Ba tare sa wani bata lokaci ba i have a deal to make”
Mikewa tayi ta zagayo gaban table ta hade hannu a kirjinta tace “taj taj taj…yaushe ka girma haka har kana take dokokina, har kanada audacity din tsayawa gabana trying to make deal with me? Ka fara shaye shaye ne? Ni kake fadama wannan magana”
“Mrs hidaya this is an office, not here to argue”
Nade hannayenshi yayi yace “i have 2
Options, give me a position or i take what is rightfully mine”
Damm taji gabanta ya sake badwa saidai bata nuna mashi komai ba saima wani irin kallo da take mashi mai wuyar fasaara, yana hango tsantsar tsana, irin muguwar tsanar nan don shi kadai ne shimfide kan fuskarta har saida ya dauke idanunshi akanta don he couldn’t believe it, so this is it? Wannan ne kadai zai bashi answers to his questions and he will truly see whats been hidden for over the year, THE TAHEEL COMPANY!!!
Ga mamakinshi sai yaga ta fashe da wata muguwar dariya irin sosai dinnan fa, saida tayi mai isarta ta ta tsagaita ta kalleshi “tajudeen lallai ka girma, you want a title right? An office? Okay go ahead”
Kallon cikin idanunta yayi, yana kara mamaki ba kadan ba, “is this who really she is, did he think of her other way? What really is she?
Miqewa yayi tsaye ya juya zaibar office din, “be careful you might trip over, and don’t think of playing games with me”
Hidaya fa ? Hidaya ce ke mashi wanna. Magana kamar wata enemy dinshi? Bai tsaya ya kara sauraronta ba ya fuce.
Gulma ta gama karade office ko’ina, babu abunda ake fadi sai the coming back of the heir”
Reporters kuwa duk sun gama cike campanu, waiting for opportunity amma babu.
Office aka bashi as the ED, office ne mai kyau don yana gaba da coo, da GED rank wato group executive director rank din hidaya kenan.
Tunda ya zauna babu abunda yake sai nazari, hes so lost in his thoughts about everything about reaction din hidaya daya kasa comprehending, kallon wayanshi yayi yana son kiran mutallib amma wani abu nace mashi ya bari.
Chan bangaren mutallib kwananshi biyu a wani daki, shidai tunda suka saka mashi wani abu aka toshe mashi baki sai hayakin da suka dunga busawa bai iya tuna komai ba, yanxu dai sun cicire daurin da sukayi mashi.
Bude idanunshi yayi widely da suka mashi nauyi, ya dubi ko’ina da kallo its just a uncompleted building, sai wuta da suke burning a dro, suna zazzaune suna cin gashin kasa ogansu na daga gefe yana danna laptop yana busa vape.
Dagowan da zaiyi yaga mutallib din ya tashi, dariya ya soma yi ya miqe tsaye “ka farfado, inace kai kwaro ne, nemanka ya zame mana wahala, for over a month”
“Who are you me kuke nema”
“Me muke nema? Kai muke nema, saboda an bamu kwangilar nemoka”
Hankali tashe mutallib yace “waye ya baku kwagilar? Me zaku yimin”
“Hahahah haaaaa kasheka zamuyi”
Tale yaji gabanshi ya fadi ogan yace “kai
Matsoraci ne amma youre smart, but… i keep wondering why wannan bastard din zaiyi spending billions of dirhams to find you”
“Whats he called again” ya tambayi sauran yaranshi, “tareeq”
“Yes tareeq”
Tunani mutallib ya soma yi waye kuma tareeq, hankali da atashe yake don ya dauka yaran hidaya ne daketa nemanshi ruwa a jallo sai yaji akasin haka.
Laptop din oga ya dauka ya juyo mashi gabanshi yace “whats the deal with this? Definitely harkar kudi ce”
Kuri mutallib yayi da ido yana kallon screen farko duhu ya gani chan kuma ya soma ganin haske sabd lighgs da aka kunna, to his greatest and surprisingly emotional surprising wa zai gani?????? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, khaal ya gani zaune an daure shi da wasu karafuna a kafanshi, a cikin wani daki da babu abun kirki sai katifa da gado, an kawo mashi abunci a lokacin kamar wani prisoner, fuskanshi yayi biji biji da gashi kamar tsohon mahaukaci, ya wani irin rame sosai dakyar ya gane shine.
Jikin mutallib har rawa rawa yake taabar tashin hankali, “ina kuka samu wannan waye ya baku? Waye wannan tareeq din? Ina yakaishi? Me kuka mashi”
Haka ya hayyayko zai shaqo daya oga ya daga tar dashi
“Heysss calm downnnnnnnnnn, waye wannan din? Aikin waye wannan?”
“Kai zaka fada min azzalumai mugaye”
“Shur the fuck up…”ogan ya mashi blow garda fasa baki dole mutaab ya dakata ya saurareshi.
Hoton tareeq suka nuna mashi da akayi publishing online lokacin da hes wanted tashin farko mutbb ya ganeshi, yasan shi a gidan taheel tabbas kuma mijin daya daga cikin matan ne saidai baisan ko wacece ba but tabbas he can be thier dirty dog da zai dunga masu aiki amma meysa ya nemi a bashi wannan? Why? Ko yanada nasaba da mutuwarshi kenan? Tambayar daya fara ma kanshi kenan, take ogan ya mashi bayanin ya da tareeq din yazo wajensu da flash din ya basu aiki kan au nemo shi su bashi, hankalin mutallb ya tashi sosai, tabbas mutuwar tareeq na nasaba da wannan sannan ya kara tabbatar da sune suke da hannu da alamarinnan, amma ta yaya zai nemo khaal how? Shi kadai ne zai iya explaining komai, oh god amma hes so happy wayyo harda hawayenshi bawan allah, yayi murma sosai sai gangs dinnan suka zama
Abun kallo suna kallonshi kamar yaro, harda rungumesu ya dunga yi kamar ba dasu ya gama zaginsu ba.
Saida ya gama murnarshi ya dubesu ya soma magana “ daga kan 1 million dollar zuwa sama, zan baku abunda yafi haka, i have a job for you”
Take suka soma cewa “woooooooo”
Taj na zaune a office yana nazarin kiran mutallib saiga call dinshi, yana dagawa ba tare da wani bata lokaci ba ya soma magana “khaal is alive, kazo waje kaza yanxu ka ganema idanunka”
Jikin taj har mazari yakeyi tsabar rudu, ya fizgi key ya fuce a guje.
Cikin abunda baifi 10 mins ba sai gashi uncompleted builiding dinnan babu tsoro ba fargaba ya shuga, yana shugowa aka fara tafawa gangs dinnan, wato karyar da mutbb ya zabga masu shine yace tJ ne zai biya su idan har suka amince sukayi abunda ya buqata,
Tunda taj ya fara kallon clip dinnan gaba daya jikinshi ya mutu jiniyiyin kanshi suka fito ridu ridu, ranshi a mugun baci, wallahi kasa kallon yanda khaal ya koma yayi da yanda wanda ya shugo kawo mashi abunci ya turo mashi kamar wani dabba kai ya allah abundai ba a cewa komai, amma an cuceshi wallahi cuta kai tsanini, idanun taj sunyi jaa sosai, he has anger issues sosai kamar zaiyi exploding haka yakeji, bayaji zai iya yafema koma wanene yayi wannan abun.
Basu waje gangs din sukayi tak dake zaune ya dafe kanshi ya kasa cewa komai saida mutt ya tabashi sannan ya zauna gefenshi ya soma magana “nasan its vwdy hard for you to believe musamman ga waenda baka taba expecting ba, inason kasan worse than this happens everywhere, bazaka taba sanin dalilin hakan ba kuma, saidai kuka allah baya barci, komin daren dadewa gaskia zata bayyana my friend, im sorry for this”
A sanyaye ya soma magana “but why why why?”
“Power, taj thats it”
Sun dade sosai suna plans…
Ahankali aka soma bude wata kofa ahankali, take haske ya bade ko’ina ya mamaye gurbun duhun daya karade dakin, ahankali ya soma bude idanunshi da sukayi mashi wani irin nauyi sosai ba kadan ba, cikin hanzari wanda ya bude ya shigo dakin ya zura hannunshi cikin aljihun ya fara kakarin bude wani abu, cikin gaggawa yakeyi babu ji babu gani har saida ya bude, yana gama budewa ya kama hannun wansa ke zaune ya dagoshi tsaye ya taimaka mashi da kyar suka fito waje, ashe babu wani hasken kirki don ana gab da magrib ne, dagowan wanda aka fiddashi ya bani damar kallonshi dakyau, da farko ko kadan ban kura da waye ba saida ya kurza idona da kyau, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, khaal…..
Kai ba a cewa komai sai innalillahi kawai, Ya qanjame ya koma kamar…🥺 this is too much for me to handle.
Wanda ya fidda shi ne ya dubeshi da kyau, sai faman girgiza kai yake mashi don kwata kwata bayajin don kurma ne, this is the only opportunity da yake dashi da zai iya taimaka wa khaal din, ya sanshi farin sani don ya taba taimaka mashi kafin hidaya ta daukeshi aiki saboda bayaji kurma ne, saidai shi bai sansa ba kwata kwata, janshi yake sosai kamar ranshi har suka fito daga tsungurmim island dinnan basu taaya ko ina ba sai bakin katon ocean din waje, ita toi risky to dive into The water amma dole ne saboda ta haka ne zai iya cetonsa kawai.
Cikin dan karamin boat ya tura khaal sannan ya hau shima ya fara turawa iya karfinsa, bawan allah shi kadai haka ya dunga turawa yana zufa yana ihu yana gumi, saida sukayi kusan awa guda tukunna suka iso bakin beach, suna isowa mutumin ya sake janyoshi ya kamashi da kyau duk sun jigata sosai, janshi ya dungayi sosai har zuwa wata motar sasake da akeyi ya sashi ciki sannan yasa abokinshi da shima kurma ne ya jasu suka bar wajen a guje.
Daga chan ciki black na kwance kamar wani shemamman zaki, around wajen karfe uku daya daga cikin yaronshi ya shugo hankali a tashe ya soma magana “ogaaaa ogaa he escaped”
“Who escaped????”
“The old man”
A fusace black ya tashi aguje ya wuce wani daki yana shiga ya bude kofar yaga mutunmin a ciki, yana juyowa ya kwadama yaron mari, hankali a tashe yarin yace bashi ba, wiki da ido black yayi don yasan tashi ta kare yau yau dinnan,
Baima san sanda ya bangaje yaron nashi ba ya zagaya chan baya cikin wani qurqun daki ya bude me zai gani wayam babu kachar da suka sama khaal, hankali tashe ya zaro wayarshi ya soma dialing wasu special numbers, kira uku yayi na hudu aka dauka, tuni ya duka qasa kamar mai neman gafara “he escaped”
………
Kwanan khaal uku wannan driver hidaya dake kawota cikin island a mota ya kawoshi gidansa, bawan allah ya kasa kaisa asibiti, dole ya dunga bashi traditional treatment saidai abun ba gaba ba baya.
Chan wajensu taj da mutallib neman khaal suke gaba da baya, taj ya baza kudi kamar his life depends on khaal, khaal ne kadai zai fayyace mashi komai game da rayuwarshi da aka boye aka gina mashi illusional life.
Achan office kuwa hidaya ta burkice ta haukace, she’s loosing it, ana bata pressure left and right, the only confidence da take dashi suke bandb comapny da take partnership dasu wannan kadai ke sata having power da babu wanda ya isa yayi manipulating title dinta.
Ta bangaren fadwa wani karamin haukan itama takeyi, kwananta hudu bakwai bataga taj ba, saita birkice ta zama kamar wadda aka ma asiri, ranar data gano ya koma office kuwa karkashin ikon hidaya abun yayi mugun bata mamaki saitayi tunanin ko sun hade kaine shida ita don dama tana suspecting akwai wani abu tsakaninshi da hidayar da suke boyewa, imagination ontop imagination take having, kai itadai gaba daya she’s weird and scary.
On the fifth day cikin ikon allah khaal ya bude idanunshi, amma ya kasa cewa komai sai hawaye, saida suka sa mashi maganin ciwon ido ya samu idanunshi ya dawo daidai, sai kuma bakinshi da he couldnt talk, she ma don bacterias ne da other stuff da baza a rasa ba irinsu steriods suka fifito mashi, with the help if vitamins yaji sauqin bakin nashi, amma still yaqi cewa komai.
Haka mutumin nan ya dunga taimaka mashi sosai haryaji sauqi soaai saidai abunda baza a rasa ba, shi kanshi he wants to recover quickly ko dan taj..
The next dai dakyar ya iya miqewa sabda yanda hes so weak, haka yayi insisting akan dole su kaishi wani waje, haka nan suka badda kama hardashi suka fita a cikin mota.
Basu suka tsaya ko’ina ba sai taheel comapny, basu shiga daga ciki ba suka tsaya khaal ya dubi building din sai hawaye, his heart is so heavy, tunanin yanda zaiga taj da sabeeha kawai yake babu hali.
Sun dade sosai a wajen motarsu ta juya daidai nan ta taj ta kunno kai, kuma har kallon motar da khaal din dake ciki saida yayi coincidentally allah baiyi zasuga juna ba.
The follwing week komai ya tabarbare, wato akwai abunda basu sani ba har yanxu, taj is one of the biggest shareholders kuma shi ne the person behind wanda ke basu budget as the side support, shine wanda hidaya tayi stopping batasan cewa yana providing ta wasu bangaren dukdan cigaban kamfanin.
Ta wannan hanyar ne yake pressuring kamfanin ya cire duk gaba daya handy support din da yake badawa na budget kuma duk basusan koshi waye ba.
Kamfani dai na neman yin kasa saboda ba a bi risk strategy ba yanda ya Kamata gashi taj ya tsaida support din da yake badawa, daman risk managers sun fada mata providing products dinnan a haka zai iya jawo cashflow shortage,
Nanfa shareholders suka dage dole ayi bid da vote, suna buqatar change of service dole
Hidaya ta sauka, gashi press suma sai faman suka suka pressure ta ko’ina suna neman sanin meke faruwa a kamfanin, rumors din taj dama chan lafiyarshi kalau ta gama karade ko’ina, daga wannan sai wannan.
Saukowa khaal yayi daga cikin motar da sukayi parking gaban gidanshi, an cire tag din da aka sassaka yayi mamaki soaai don jiya ya karanta news din yanda akayi mashi sharri da karyayyaki, harda gidajenshi da aka kwace aka mashi sharrin kidnapping taj da sabeeha, ba karamin mamakin gidan yayi ba don hakan na nufin gidan ya koma nashi kenan ko an sayar, only god knows yanda akayi dashi, cikin kwanakin ya rasa ta yanda zai ga mutabl, don yanason yasan halinda taj ke ciki da sabeeha sai kuma iyalanshi, yasan hidaya bazat barsu haka ba ya tabbatar da haka.
Saida yazo gaban gidan nasa nema damuwar iyalanshi suka tado mashi sosai, ian zai gansu a wani haki suke ciki, trauma din daya shiga a wannan wajen for over months bayason tunawa, ya hana kanshi da tuna komai shiyasa ya kasa bude bakinshi ma.
Bawan allah ga girma ga hypertension, ga wahalar dayasha cikin wajenda baya fatan ko enemy dinshi ya shiga wannan wajen, hawayen dake sauka kan fuskanshi yayi saurin gogewa ya juya ya fara takawa zai gangara inda sukayi parking, baima lurada motar dake tahowa ba hes so lost sai ji kake qiiiiiii dam
A guje suka fito gaba dayansu mutallib na daga mazaunin gaba, futowarsu kenan, yana yima gangs dinnan jawabin khaal, instint dinshi na bashi suje gidan, tunkan su karasa gidan kuma wannan tsohon ya hawo titin, kwata kwata baiji horn din da suke mashi ba, dake harkar yan buga buga da bige bige babu hankali, da mugun speed ya shigo street din wannan yasa ya kasa kauce mashi suka dan bugeshi.
Zagayeshi sukayi gaba dayansu, waenda suka tajo tare da khaal suka hango abunda ya faru suka fito cikin hanzari.
Sandarewa mutallib yayi ya kasa motsawa kwata kwata, sai duqawa da yayi ya juyo da mutumin da kyau don tabbatar da abunda idanunshi ke son nuna mashi, innalillahi wa inna ilaihi rajiun “khaal” ya furta a hankali,
Duk juyowa sukayi suna kallonshi don saida sukaji ya ambaci sunan tukunna suka sake kallon mutumin da mamaki, mutumin da suke nema saboda kudin da aka masu alkawari gashi a gabansu, dole suyi protwcting dinshi at all costs kodan kudin da za a basu, waenda sukazo da khaal din au taorata ma sukayi da sukaga gangs din, saida mutallib ya masu bayanin koshi waye don har hitonsa da khaal saida ya nuna masu kafin su shige mota dashi sukabi bayansu sai asibiti, gudu suke kamar yaqi mutallb sai faman kiran taj yake baya samunshi, shi kuma suna wajen meeting ya saka wayan a silent.
An bashi taimakon gaggawa sosai ba kadan ba, har suka samu ya fita daga cikin dangers.
An hour past bai farfado ba and taj baiyi responding ba suna tsaitsaye ogan gangs dinnan ya taho wajen mutallib, wayanshi ya nuna mashi mutallib ya kalla group chats din da aka turo da top terror groups dinsu, an baza hoton khaal da wannan driver din ana nemansu duk wanda ya gansu za a bashi kudi masu tsoka sosai.
Tashin farko mutallib ya kalli gang leader din yace mashi, “kudin da mukayi alkawarin baku, taj zaiyi doubling times 3, in order to have it, inason kuyi protecting wannan mutumin, just take him as a treasure”
Murmushi gayen yayi, don yasan tabbas zasu basu kudin nan don taj ya tura masu half deal din da sukayi dole duk yanda zasuyi bazasu taba bari khaal ya kubce masu ba.
Nan ya tattara yaranshi ya basu dogon warning wannan yasa mutallib ya nema discharge subar asibitin don zasu iya cimmasu don su kadai sukasan irin mutanensu, aiko suna barin wajen saiga wasu mugan yan ta’adda sun badda kama har sun shigo asibitin harda mata sunyi shigar likitoci saidai allah bai basu sa’a ba kwata kwata.
Taheel company,
Meeting din da aka gamayi ko shiga hidaya kasayi tayi, tama rasa ya zatayi don tabbas stock din kamfanin na sauka sosai, gashi stakeholders sun saka mata pressure sosai, kuma idan har batayi sorting wanna issue dinba zasu iya tunanin yin vote, kuma dole komai hannun taj zai koma, inaa bazata taba barin wannan ba har gwanda taga baya nunfashi data bari hakan ta faru.
Yana zaune office 10mins kenan da gama meetings din da yayi, bude wayar da zaiyi yaci karo da imessage din da mutallib ya tura mashi, “alhamdulillah, khaal is alive!”
Sai ga hoton khaal da suka dauka a asibiti, miqewa yayi tsaye yanajin wani irin guilt, bakin ciki, da takaicin kanshi sosai ba kadan ba.
Cikin hanzari ya kira wayar mutalln yana dagawa yace “khaal, he’s alive?”
“Yes, mubar asibiti yanxu, cause his life is in danger, i dunno what happen exactly amma duk yanda akayi he manage to escape, taj basuda imani, basuda imani, for over 7 months yana kulle kamar prisoner, sunyi torturing dinshi, sun wulaqantashi, wanda yayi saving dinshi yace he couldn’t talk, he couldn’t walk, they maltreated him, sun cuceshi,”
Idanun taj sunyi jaa sosai ya buga table din gabanshi yafi sau nawa hannunshi har yayi jajawur sosai.
“Zan tura maka address din hideout din da zamu kaishi..you have to be very careful tajjjj…”
Dip wayar ta katse, daidai nan aka budo kofar, fadwa ce ta shigo sanye da wani arnen kaya, tana ganinshi taji wani sanyi duk ilahirin jikinta, takowa ta somayi har inda yaje ta tsaya gabanshi, “ka gama hide and seek din nata?”
“You’re playing with fire taj…hidaya will make your life miserable”
Azafafe ya dago wallahi ya karade ya sauya kamar ba taj ba yace “just the way with khaals????”
Unexpectedly taji maganar, harta daga hannu zata kama nashi yayi wani irin kama wuyanta ya turata bangon office dun saida idanunta suka fito kwalala, temper dinshi ya gama hawa sosaiiii kuma zai iya mata illa adaidai lokacin wallahi taji shaqa kuwa ba kadan ba sai faman kakari take tana kama hannunshi yaqi sakinta saima kara sqeezing wuyanta da yake ya fita hayyacinshi gaba daya
“Just prayy…just pray khaal survives this, if not… if not…i will make your live unbearably miserable, i will make yall pay for the pain”
“Tajjjjj…” tayi wani tarin mutuwa tana bugun hannunshi, wallhi bai iya tantace waye ne a gabanshi, he’s in so much anger.
Saida merk ya shugowa yayi saurin kama hannunshi da kyar ya iya dawowa daidai ya bangajeta.
Su fadwa anji qamshin mutuwa lols.
Futa yayi a fusace daga office din baya ganin gabanshi baya ganin bayanshi kwata kwata.
Fadwa ko jakarta bata iya dauka ba a guje ta wuce office din hidaya, “ukty ukty…you need to stop him, taj will make us all miserable, hes one step behind to knowing everything, yace zai tarwatsa taheel company, he will make sure that you don’t get a penny, and he promises to makesure that goes to our mothers grave”
“Wait what” hidaya ta miqe tsaye, hankali a tashe “kiyi wani abu mana”
Miqewa hidaya tayi tama rasa wani tunani zatayi, fadwa data fita furgicewa saita fuce kawai bata tsaya ko ina ba sai gida a furgice, tana shiga dakinta ta haukata ko’ina tana ihu, daga karshe tayi locating wayarta data fashe tass ta tsaga mata hannu tsabar sauri tayi dialing number, ana dagawa ta soma ihuuu sosai fa kamar wadda za a kashe “papiiiiiiiiiiiiiii, you need to fucking do something i’m going crazyyyyy”
Direct bai tsaya ko’ina ba sai hideout din, gabanshi na dip dip dip, mutallib ya karaso dashi, kafarshi yayi mashi nauyi ya kasa yin komai, har gaban khaal dake kamar matacce mutallib ya ajeshi, duk dauriyar taj saida ya kauda ido wani abu waishi hawaye ya sauko masa kadan ya maidashi, he has to be strong he needs to be strong.
Zaman nan da yayi gaba daya driver hidaya ya zayyane mashi komai ta hanyar rubutu don baya iya magana kuma baya ji, da yanda ya taimaki khaal suka fito da yanda yayi noticing din khaal, da ayyukan da yakema hidaya.
Taj dai tunda ya sunkuyar da kanshi kasa dagowa yayi kwata kwata, jiran khaal kawai yake ya bude idanunshi, yana ganin abun kamar mafarki ne ba gaskia ba.
Khaal kamar yaji presence dinshi a wajen, ahankali ya soma bude idanunshi harya saukesu kan taj dake zaune gefenshi, ya dade ashe yana kallonshi basu lura ba saida sukaji ya furta “Ta…ju..deen”
Da sauri taj ya dago, sukayi ido hudu da khal mutallib yayi saurin matsowa, taj dayaga yana kallonshi sosai saurin cire idanunshi yayi daga na khaal, kunya, tausayi, haushin kanshi, guilt duk sun mashi yawa, abubuwa sun mashi katutu sosai
Hannunshi khaal ya kama don ya dauka mafarki yake, taj is back on his feet, he’s healthy ya dawo hayyacinshi, allahu akbar, the next thing daya fito daga bakinshi kuwa shine “ina fatima? Tajudeen ina fatima???????”………
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID