← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 11 OF 66

Chapter 65

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 34 min read

The next morning….
Kwata kwata bai samu yin barci ba daren jiya sai wuraren karfe shida, ya kasa relaxing mind dinshi kwata kwata, abu daya ya yanke aranshi wansa ya kudirci saiya nemo answer tambayoyinshi.
Ahankali ta soma bude dakin naki, sanye take da wata arbiyar nighties red,blonde gashinta har gadan bayanta, dukda babu wani hasken arziki a dakin hakan baisa ta hango kyakyawar fuskarshi ba saboda hasken bedside lamb, ga dan hasken dake lekowa ta wajen curtains, wani irin makirin murmuahi ta sauke tare da takowa har bakin gadon ta tsaya akanshi tana binshi da mayen kallo, yanda take kallonshi kamar idanunta zai zazzago tsabar masifa da jin shauqi, rayuwarsu a baya take tunawa, rabuwar da sukayi ta shiga damuwa sosai, duk yanda taso su dawo yaqi bata chance, kuma tasan yana sonta sosai, kirsa irin ta mata babu wadda batayi ba, gangancin ta ne ma ya jawo ta bari ya gano ta da wani, don a gidan sa ne ma incident din ya faru, da yake shige da fucenta a gidan shi ba wani abu bane don har pin dinshi tana dashi, duk sanda taga dama tana zuwa daman su turawa ba ruwansu da wannan, kwana ne dai bai yarda tanayi a cikin gidansa ba ko yana nan ko baya nan, toh a ranar yayi tafiya zuwa jamaica, da yake yace mata sati guda zaiyi shiyasa tazo apartment dinshi ta kwana ba tare da saninshi ba kuma tasan baya so,da safe shine ta futa zuwa gym din apartment din nashi, anan ne ta hadu da guy din har tayi mashi tayin zuwa apartment din boyfriend dinta, shiko ya bita suna hawa saman salon ya chanza, shi kuka bangaren taj daman wani business ne yaje yi a jamaica, branch dinahi dake chan ne aka samu matsalar importation kuma dole saiyazo shine yaje,yana zuwa dayake shi workaholic ne baima tsaya yin komai ba ya warware matsalar dake chan din ko kwana baiyi ba ya hau flight din dare, washe gari da safe yana suna isowa ya wuce gida direct.
Sauke ajiyar zuciya tayi tana mai kallon faffadan kirjinshi dake bude yayi unbuttoning din rigar jikin nashi,ga wani kwantaccen gashinsa dake kwance a wajen kadan, hannunta ta sanya ta soma shafa mashi karjin nashi har zuwa wajen cibiyaraa, kamar a mafarki ya soma jin tafiyar da ake mashi a kirjinsa, da yake light sleeper ne yana jin motsi ko yaya ne yake farkawa,

ahankali ya soma bude idanunshi, harya sauke su akan sonata dake shafashi, muryarta chan kasa kasa ta soma magana tana juya idanu, “good morning zaddy” tana fadin haka tayi saurin rankwafowa ta rungumeshi, cikin hanzari yayi saurin tashi zaune ya zareta daga jikinshi, fuskan nan nashi a hade,yana mata wani irin kallo mai tattare da kyama da tsana,ita kallon da yake mata bashine damuwarta ba don haka ta sake kokarin maida jikinta zuwa ga nashi ta fara kokarin kamo fuskanshi zatayi kissing dinshi yayi saurin turata baya rai a bace disgustingly yace “are you insane?“
“Babe please!!!!,i’m sorry about abunda faru, it was a mistake bakama bani chance din explaining kaina ba ka koreni, please give me another chance, i can’t live without you, I couldn’t move on with my life all this while”

Tana kokarin kama hannunshi ya dakatar da ita bayan ya gama sauraronta “don’t you dare!!!!l” ya daka mata tsawa yana tuna yanda ya shigo apartment dinshi tundaga bakin kofa yana jiyo moaning dinta da wani kato, ranar ya shiga tashin hankali da bacin rai sosai, harya karaso wajen couch dinshi yana kallonta tsirara da wani katon banza akanta, yama rasa ya zai masu, ya dade sosai a tsaye hannunshi cikin aljihun wandonsa yana kallonsu, itace ma ta fara hangoshi unexpectedly, shiko saurayin yana ganin taj din ya tabbatar shine boyfriend dinta, don haka yayi saurin maida kayanshi ya fice daga apartment din cikin hanzari, ita kuwa batayi tsammanin taj din zai barshi ya tafi haka ba don harya wuce ta gabanshi baice komai ba haka zalika bai daina kallonta ba, sai ma juyawa da yayi ya wuce bedroom dinshi ta biyoshi hankali a tashe bayan ta maida shegiyar rigar ta wadda bata da banbanci da tsirara,, tund ata shigo baice mata komai ba harta fara mashi magana “babe babe listen to me, its a mistake, I don’t even know how… how..it happens…”
Tundaya dago da rinannun idanunshi ya kalleta tasan cewa she has fucked up big time,daga ranar bata sake ganinshi ba, duk yanda taso ta ganshi ya hanata duk wani access to him, the biggest thing daya tsana a rayuwarshi shine ayi betraying dinshi, yanda yayi wiping dinta a rayuwarshi kamar bata taba existing ba, idan yanason abu he gives it all, his wealth his attention and all.
Bayan rabuwarsu da farko bataji zafi ba saboda daman she doesn’t feel his love, relationship dinsu was like one sided, kamar yasan haka zata faru yaqi bude mata rayuwarshi gaba daya, daman dai itace tayi forcing kanta a rayuwarshi harya amince da ita, saidaga baya data gano koshi waye nan fa hankalinta ya tashi sosai, ta fara neman yanda zatayi ta koma mashi, daman tun farko tana mamakin yanda yake spending on her, harda unlimited black card yana dashi, he’s just leaving a lowkey life ba tareda kowa yasan identity dinshi ba.

Lokacin data gano yabar london gaba daya hankalinta ya tashi sosai, gashi batasan ko a ina yake ba,hartayi giving up afiya ta nemeta da kanta, kamarma bincike tayi akanshi harta gabo cewa ex girlfriend dinshi ce, itace ma ta fada mata komai da asalinshi, nan ne itaa ta fada mata koshi waye, daga nan suka qulle.

“How did you even know where i am?ya akayi kikazo nan?”
Ya jefo mata tambaya kai tsaye, yanda ya kureta da idanu yasa ta rasa irin karyar sa zata mashi, idanunshi nada kaifi sosai,tasan idan ta mashi karya zai ganota don haka ta kora mashi bayani daga farko har karshen yanda suka hadu da afiya da yanda suka zo nan.
“I even told her your identity” ta karashe tana kallonshi gwanin ban tausayi, “babe please!!”
Saurin dakatar da ita yayi da hannunshi yana mai kallon cikin idnaunta yace “tun yaushe kika sani?”
“After our breakup, i was tailing you, na kasa moving on, i couldn’t do that, i love you so much”

Cije lebenshi yayi kafin ya dafe kan shi yace “oh shit”
,kwata kwata baiyi tunanin it will turn out to be like this ba, shuru yayi yana nazari, tunda har wannan zancen yaje kunen afiya definitely hidaya ta ji itama kuma ta sani, amma meysa batace mashi komai ba? Tunanin daya dunga yi kenan aranshi, maida dubanshi yayi ga sonata dake gabanshi, yana calculating maganganun data fada mashi yanxu, “meysa afiya tayi digging rayuwarshi da yayi a london, harta gano sonata ex dinshi shi? What was the reason? Sannan meysa hidaya batace komai ba?yasanta ciki da bai, yana da dalilin da yasa ya boye identity dinshi daga garesu.

Bashi da amsoshin tambayoyin nan nashi amma dole ya nemesu, wannan dalilin ne kawai zaisa yabar sonata a gidannan badan haka ba bayajin zai bari ta sake koda awa daya ne a gidan, she disgusts him, daya kalleta yake tuna yanda ya ganta da wani a gidanshi, daga ranar bai sake amfani da komai na gidan ba, ya sauya wasu that the level of how disgusted he was.

Maganar datayi ne ta dawo dashi daga tunanin daya fada, “babe….please don’t push me away, zanyi duk abunda kakeso, idan har zaisa ka barni a cikin rayuwarka” a shagwabe tayi maganar hoping he will fall for it harda hawayenta, ko kallon baiyi ba ya miqe ya wucw bathroom, shurun nan da yayi mata ya tabbatar mata da bazai koreta ba kenan, ba karamin dadi taji ba ta sauke wani makirin murmushi ta bishi da idanu harya fuce daga dakin ya shige bathroom, “wow ay banyi tunanin komai zaiso min da sauqi ba, yanxu zan fara nawa aikin, zanyi koma menene don ganin na mallakeka kuma na kori wannan ugly maid din da ake cewa matarka ce”
Haka ta dunga magana ita daya da kanta harya dauka wajen 30mins a bathroom din kafin ya fito ya shige closet ya saka kaya marasa nauyi ya fito.
Kamar mayya inda ya barta anan ya taddata kamar jira take kuwa yana futowa ta karaso inda yake dukda yanayin fuskanshi is not welcoming hakan baisa ta kyaleshi ba ta kamo hannunshi, “muje muyi breakfast” ta karashe tana rike da hannunshi, bai hanata ba suka futo daga part din nashi.
Yana gaba tana biye dashi a baya har suka sauko kasa daidai nan su fadwa suka tunkaro hanyar dining din ita da tareeq, tana kallon hannun sonata cikin na taj din tayi kwafa ta wuce dining room, tareeq ya bita da kallon mamaki cikin kwanakin nan ya kasa gane mata kwata kwata, taoro ma take bashi yanxu don ya kasa gane inda ta dosa, she’s a bit suspective.
Zama duk sukayi a dining din ana jiran isowar madam hidaya, basu dade da zama ba sai gata ta iso, kusan a tare suka shigo ita da ammu databi kowa da kallo har idanunta ya sauka kan sonata dake sanye da wata tsinanniyar riga zaune kusa da taj dayayi relaxing bayanshi, seat din dake tsakiya hidya ta zauna, shine ma ya fara gaisheta kafin kowa ya gaisheta sai ammu data karaso itama duk suka gaisheta har zata zauna ta miqe tabar dining din duk suka bita da kallo, ko minti biyu ba a yi ba saigata ta dawo, basu lura da sabeeha dake biye da ita ba a baya saida suka karaso dining din, fuskansu dauke da mamakin ammu.
“Ay bazai yuwu ayi family breakfast ba babu daughter inlaw din gidan, tunda naga har aka iya barin bare ma tayi joining balle kuma na gida”
Tana fadin haka ta maida dubanta ga sabewha da kanta ke kasa, kirjinta na bugu, bata yarda ta dago idanu ta kalli kowa dake wajen ba.
“Seat!” Ammu tayi mata nuni da kujerar dake kusa da ita dake facing ta taj, jiki a mace sabeeha ta ja kujerar ta zauna.
Tunda yaji abunda ammu ta fada kwata kwata bai dago ba saika maida hankalinshi da yayi ga breakfast din da yake.
Sonata kuwa ranta idan yayi dubu ya baci, ta tsani yarinyar nan kamar ranta,ga wannan aunty din tasu da alamu she git her back, dole tasan irin takun da zatayi, su fadwa da afiya kuwa tabe baki kawai sukayi, hidaya kam ko kallon inda suke batayi ba, ita yanxu wannan yarinyar ba itace damuwarta ba kwata kwata saboda tasan kulallaiyar data hada bazaisa taj din yabar yarinyar ba, infact he will never accept wannan auren donma baisan cewa maid bace, bayan wannan ma tasan ita zai bama zabi idan tace a koreta bazai tsallake maganarta ba, ayanxu tana binshi a hanakli ne don karyayi suspecting komai.

Ahankali ta soma magana cikin muryarta mai sanyi da dadin sauraro ga natsuwa, “Sabahal khair ukty”
Ta gaishe da hidaya, tunda ta soma magana taj ya dakata da juya coffee dinda zaisha, yaune ya fara jin muryar ta a zahiri, idan har ya tuna wani abu daya danganceta saidai yaji muryar na echoing a kunnenshi baya iya predicting.

Shuru hidaya tayi kamar bata jita ba, saida ammu tace “hidaya.. bakiji ana gaisheki ba”
Sai alokacin hidaya ta dago ta kalleta sai ta sake kauda idanunta daga wajen, jiki a mace sabeeha ta maida dubanta ga inda taj yake zaune, muryarta har breaking yakeyi wajen cewa “sabahal khair” ta karashe tana mai satar kallonsa, hankalinshi na kan abuncin gabansa, y
Sarai yasan dashi take yayi kamar baima san anyi ruwanta a wajenba, gaba daya kowa kallonshi yayi don ganin reaction dinshi da response dinda zai yi ko zai kulata sai sukaga akasin haka, take hidaya ta sauke wani murmushin samun tabbacin maganarta tayi tasiri kenan, ammu dataga wulaqanci ya fara yawa tayi saurin kama hannun sabeeha ganin tana kokarin gaishe da sauran mutanen da ke dining din har zatayi magana ta dakatar da ita, suna kallon juna ammi ta girgiza mata kai alamun tayi shuru,don haka tayi shuru bata sake cewa komai ba.

Idanunta na son sake kallon inda yake amma tana tsoron karsu hada ido, shiko yi yayi ma kamar ba ayi ruwanta a wajenba.
As usual kullum shike gamawa don bai cika cin abunci da yawa ba musamman idan da mutane, mikewar da yayi yasa duk suka bishi da ido harma da hidaya dake zaune, “zanje gym” yana fadin haka ya fuce daga wajen ba tare da ya kalli kowa ba harma hidayar, sonata har zata bi bayanshi ammu ta mata wani irin mugun kallo ta koma ta zauna,tunda ya miqe harya fuce hidaya bata bar yin mamaki ba, yau taj ne ya tashi kafin ta tashi? Why d sudden change in him? Abunda bai taba yi ba kenan, badan taga abunda yama sabeeha ba zata ce bai gamsu da maganganun da sukayi jiya ba kenan, koda ta shigo ma tayi mamakin ganinshi a dining don ta dauka maganar da sukayi zaita damunshi arai, bama ita kadai ke mamaki ba harma dasu afiya kowa mamaki yake don sunsan baya taba tashi yabar wajen sai hidaya ta miqe tukunna,ammi kuwa daman wannan dabiar gidan datazo ta tadda ba burgeta yake ba.

Koda ya hau sama shiryawa yayi cikin kayan motaa jiki ya dauka duk wasu abubuwan da zai buqata ya fito kunenshi maqale da airpod, yana karasowa wajen parking lot harya shiga cikin mota sonata ta fito, ya hangota tana kokarin karasowa kamarma shirin binshi takeyi, kota kanta baibi ba yayi reverse da motarshi yabar wajen.
Gwiwarta a sake ta koma cikin gidan daidai nan ammu da sabeeha suka fito daga dining daman su kadai suka rage don kowa ya watse, sim sim ta wuce part din afiya kamar munafuka sabeeha ta bita da harara ba tare da ammu ta ganta ba.
“Kinga wannan shegiyar, dolw ta bar gidannann, bada alkhairi suka kawota gidannan ba, bari ma kiga, inaso ki koma part dinshi yau yau dinnan ay daman achan kike zama kuka kayanki na chan ko”
Tunda ammu ta soma magana gaban sabeeha ya bada dam, itafa yanxu anything related to him koda kuwa sunanshi aka kira saitaji wani iri a jikinta, “amma ammu ni ina ganin mubi komai a hankali, kinga yanxu bai san konu wacece ba baima tuna da konu wacece ba”

“Karki damu, dalilin da zaisa nakeson kinkoma din kenan ay, so nake ya sandake din”
Sabeeha dai jinta take amma batajin tana da courage din tunkararshi ayanxu.

Taj ko tunda ya iso gym yana workout mind dinshi baya wajen, tunani kala kala na yawo a kunyarshi, na farko yanxu instint dinshi na bashi dalilin da yasa hidaya ta hana TNT suyi investing a kamfani saboda ta gano shine investor din,

na biyu kuma maganar khaal ta tsaya mashi har zuwa yanxu arai,tun jiya yake wannan calculation din, major abunda yasa yakejin theres something else about maganar khaal datayi mashi shine khaal yasan koshi waye, kuma yasan shike investing a taheel company and yasan dalilin da yasa yake investing a kamfanin saboda bayason shiga harkar business din familyn shiyasa ma yake supporting dinsu ta hanyar investing, so he can say that khaal yasan baya son shiga business din family din.
Na biyu kuma yarinyar nan, he has come to conclusions na yanda zaiyi da ita.
Da wannan tunanin ya shafe wajen awa biyu a gym kafin ya futo ya shige motarshi, wayarshi ya latsa yayi dialing wata number ana dagawa ya soma magana, ya dade sosai yana wayar ban samu naji me yake cew aba don yana daga cikin motar ni kuma ina daga waje harya gama kafin ya ajiye ya juya akalar motarshi, yabar wajen.

Chan bangaren hidaya itama futa tayi ta hadu da lawyer ta ya kawo mata takardun raba aure data buqata, daga nan ma bata tsaya ko’ina ba sai island dinta, as usual tana zuwa babu abunda ya sauya, frustration yasa ta fara kosawa, ajiye wannan mutun is useless to hwe indai bazai fada mata bunda takeson sani ba.

Haka ta dawo gida bayan black ya bata update din abubuwan da taj din ke yi, yawan daga gym sai gida, daga nan kuma baya zuwa ko’ina, tun bayan zuwa gidan khaal da yayi so daya.

***
Budo kofar dakinsu tareeq yayi, shugowarta kenan ya biyo bayanta zuwa part din nasu, batasan cewa yana cikin gidan ba kwata kwata, babu inda bai duba ba a dakin nasu bai ganta ba wannan yasa ya fito ya nufi dakinta, yana shiga yabi ko’ina da kallo, ya dauka tana bathroom don haka ya dan jinkirta shuru bata fito ba wannan yasa ya nufi closet eoom dinta nan ma bai ganta ba chan ma bathroom baiji alamun saukan ruwa ba don haka ya fito kawai ya nufi kofar futa daidai nan ta fito ita kuma daga closet room, da mamaki yake kallonta itama dai tayi mamakin ganin nasa ta waske, hotunan dake hannunta ta ya kalla dukda baya fuskokin wanda ke ciki, “me kake buqata?”
Muryanshi a kasa kamar wani dan boyi boyinta yace, “naga shugowarki ne na shiga daki kuma ban ganki shine…”
“What do you need” ta sake jefo mashi tambaya, “kudi ne? Don nasan shi kake bi,”
Cikin saurin ya tako inda take in a manipulativeway ya soma magana “no babe, ba kudi bane”
“Then menene?” Ta sake jefo mashi tambaya.
“Babe trust me, Kinsan nace maki i will do anything for you ko?, nasan me kike so, kuma zan taimaka maki don ganin kin samu abund akike so, kalla kiga”
Ya bude wayarshi yana nuna mata wani hito, hidaya ce zata shiga cruise boat dinta,
“Akwai wani aboki na dake aiki da jiragen ruwa a marina, private boat driver ne,akwai ranar da mukayi waya dashi yake fada min cewa yana yawan ganin hidaya ta yanda ya santa kuwa saboda,…..”
“Just go straight to the point” fadwa ta dakatar dashi son wannan surutan nashi na banza ne baya adding up kwata kwata, “shine ya tura min hoton nan,babe ina ganin kamar ukty is up to something yace min kusan duk end of the month take zuwa nan, sannan akwai kishin kishin da yaji kamar tana da wani private island, daga mutanen dake kaita da waenda ke mata aiki gaba daya looks suspicious.

Saida ya gama tass ta soma magana “kana bin abokanan useless abokananka na street life djn da kayi kana fada masu where youre married into ko? First of all why are you telling me this? Kanason hadani da yar uwata ne? Idan tana yin wani abu ni menene ruwa na a ciki, dont play silly games with me”
Tana kaiwa nan ta fuce ta barshi taaye saqe, sai kawai yayi murmushi, dake tantirin dan iska ne shima, “ni zaki rainama hankali, kina tunanin bansan kudirinki ba” yana kaiwa nan ya juya har zai futa ya dan dakata yaba kallon closet room dinda ta fito daga ciki, tabbas daga ciki ta futo kuma lokacin da ya shiga ciki babu kowa a ciki, kasa wrapping kanshi kawia yayi yace “hmm,”yanaji a ranshi shes hiding something.


Yauma bayan futar taj ta wuce dakin nasa ta gyara shi fess fess, ta wanke bathroom dinshi, harda kitchen da sitting room dinshi da yayi kura ta gyagyara ta kunna ac kafin ta fuce daga part din zuwa dakin ta, bata sake futowa ba tayi zamanta achan.

Misalin wajen karfe tara daidai ammu ta taso sabeeha a gaba, gaba daya hankalinta a tashe yake tsabar tsoro, a bakin kofa ammu ta tsaya tana mai kallonta, ganin gaba daya ta tsure yasa ammi tace “karkiji tsoro kinji, Bazai maki komai ba kinji” remember our plan?
Girgiza mata kai kawai tayi, ammu ta juya tabar wajen ita kuma ta tsaya qiqam a bakin kofar kamar an dasa ta, da kyar ta iya sa hannu ta bude kofar, a tunaninta ko yana cikin bedroom, tana rufo kofar ta juyo gabanta ya bada wani dam hartana yin baya kamar zata fadi saboda lokaci guda idanunsu ya shige cikin na juna,take bakinta ya soma motsawa tayi saurin sauke nata idon saboda yanda ya cika mata idanu da kwarjini, yana zaune a sitting room yayi relaxing bayanshi akan kujera, sanye yake da wata hoodie da gajeran wando da bai rufe thigh dinshi ba, muscles dinshi sunyi piling rudu rudu,kamar wanda ke jiran zuwanta haka yayi zaman, kuma zuwanshi kenan sutting room achan daki ya rasa abubsa zaiyi shine ya dawo parlor ya danyi wayoyi da mutanenshu dake chan london bayan ya gama dasu ya kafama tv idanu yana kallo, yana tuna wasu moment, a daidai lokacin kuma ta shugo dakin maido da dubanshi da zaiyi ga kofar kuwa take idanunshi ya sauka ciki nata, yana kokarin tun ma inda ya taba ganin fuskarta, tabbas yarinyar daya gani ce a asibiti, kuma ya gane itace wadda ta shugo part dinshi ranar da light ya dauke, aranshi yace “bingo, so wannan ce yarinyar kenan, wanan yar abar?,“
Bin fuskanta yayi da kallo daga samanta har kasa fuskanshi na nan yanda take babu alamun fara’a kwata kwata sai annuri kawai da yakeda,
Take ya tuna dalilen da hidaya ta fada na aura mashi ita da khaal yayi ne, abubuwan dake ranshi yasa na kasa inda ya dosa,shi kanshi ya rasa a wani matsayi zai bar yarinyar,? Yana kallon abun kamar a film, sabeeha baiwar allah yanda kasan an dasa ta taqi motsawa kwata kwata, tana jin idnaunshi na yawo akanta, tana nan tsaye kawai aka budo kofar aka shugo, sonata na hangota tsaye taji gaba daya duniyar ta mata wani irin daci, kishi, haushi, tsana duk babu wanda bai darsu a zuciyarta ba. Cije lebe kawai tayi tana raya abubuwa aranta sai kawai ta suake wani murmushi ta wuce ta gaban sabeeha tana juya duwaiwuka, kamar kullum dai babu kayan arziki a jikinta, takowa tayi har inda yake ta zauna a gefensa tana kashe murya tace “hey zaddy”
Ko kallon ind atake baiba idanunshi na kan tv, tunda ya duake ido daga kan sabeeha ya maida tv bai sake kallonta ba, haka zalika baice mata ci kanki ba, baima damu da sanin meya kawota ba as far as he knows baisan da mutun a wajen ba tunda batayi sallama ba.
sonata dataga kamar yana neman dizgata gaban yarinyar nan kuma tana son ta kunsa mata saboda yanxu tasan ko kallon inda take bazaiyiba, ada ma don taga yana sa matsalar kai ne shiyasa take da iko dashi amma ayanxu yana da iko akan karan kansa,no one is responsible for him, kuma tasan wannan dai maid dinnan dai can never be on his league, yafi karfinta nesa ba kusa ba, ko kasa daya bata isa ta taka dashi ba.

Sabeeha kuwa tun shugowar sonata ta hade rai sosai, taoron nata ma ya kau, saima ta manta lafiyar taj din lau ganin sonata na tunkarar inda yake.

Sonata dataga sabeeha ta kafesu da idanu, wannan yasa ta dora hannunta kan lap dinshi ta sake kashe murya tace “babe, me maid dinnan keyi anan? Wani abu zata maka ne? Dont worry i can do it for you zaka iya sallamarta”
Sai a lokacin ya dauke idnaunshi daga kan tv ya maida kan hannun sonata dake kan lap dinshi tana yawo dashi kan fatarshi,”get your filthy hands of me” ya fada yanda dagashi sai ita ne zasu ji, tana jin harsh tone din da yayi magana dashi tayi saurin dauke hannunta ya miqe yabar parlor ma gaba daya, sonata ma ta bishi a baya tana murmushin yaqe duk dan ta kunsawa sabeeha, sabeeha kuwa taga duk abund aya wakana a wajen sai taji wani irin aranta, daman tayi expecting haka, bai tuba ta ba baima san ko ita wacece ba, gashi dai a gabanta amma tana ji ya mata nisa, kafarta har nauyi take mata, kamar sata juya ta tsaya tunawa da maganganun da sukayi da ammu,dole ta tsaya, dole ta dawo nan saboda ta hanyar nan ne kawai zata samu ya tunata har ya yarda da ita.
Tana nan tsaye sonata ta futo rai a bace, korarta yayi kiri kiri kamarma kyamarta yake da zarar ta tunkaroshi, plans dinta will not succeed idan har bata samu kanshi ba, dole ne ma tasan yanda zatayi don ta sameshi don wannan ce hanya kadai da zaisa ta sake shugowa rayiwarshi tun bayan lokacin daya gano tana cheating dinshi ta kasa samun wanda zai maye gurbinshi a zuciyarta, abunda yafi damunta kuma take dana sani shine rashin samun kanshi datayi a baya, duk yanda taso tayi seducing dinshi yaqi falling, yana da wata taurarriyar zuciya, tana mamakin yan uwansa da suke mashi wani gani gani, basu san koshi waye ba, bata taba haduwa da mutunminda ya iya takunshi ba kamar taj.

tana karasowa inda sabeeha take ta kalleta, har ta fidda bacin ranta a fili ta tuna wani avu saita boye ta soma magana kamar haka, “ wow wow wow…i thought kince ke matarshi ce, ya akayi bai tuna dake ba? Hahaha Listen bari nayi maki clearing kanki ke matarshi ce a lokacin da hankalinshi baya jikinshi sannan kwakwalrshi ta yara, Yanxu kuwa yafi karfin ki, inbanda karfun hali irin na talaka, ungrateful people how can you even think of your self as his wife, you’re nothing but his maid Just a maid, and as you can see now I’m his first love, your title as his wife is just a name, he will never accept you bitch”
Tana kaiwa nan ta kyalkyale da dariya tabar wajen, sabeeha kuwa tunda ta fara magana harta gama jikinta yayi sanyi sosai.
Ta dade a tsaye har kafarta ya soma mata zafi kafin ta wuce sitting room ta zauna a kasa.

Chan bangaren taj yana shiga daki sonata ta biyoshi a baya, gaba daya ganinta ma baya sonyi don gazanta yake gani da zarar ya kalleta,
Kallota daya tsaya yi yasa ta fara tunanin ko tayi attrating dinshi ne wannan yasa ta fara kokarin shafa shi, rai a bace ya kora mata ta fito daga bedroom din rai a bace bayan ta bashi hakuri, cike lebe kawai ta dunga yi abunda take so kamar zai mata wuyar samu….

Tana futa ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya saka kayan barci sannan yabi lafiyar gado abunshi..

Asuba nayi ya farka, daman time nayi yake bude idanunshi, tashi yayi zaune kafin ya miqe ya shige bathroom ya dauro alwala, dayake baya son yawan haske dakin nashi is very dim sai hasken bedside lamp,daman wuraren wajen karfe 5:50 ne,yana fitowa ya shiga closet ya saka jallabiya sannan ya futo ya hau kan carpwt din sallah, saida yayi raka’a tainul fijir kafin ya tada kabbarar sallar fajir, bayja yabsallame ya dade sosai a zaune kar ya soma kulle idanunshi, karar bude kofa da yaji yasa ya maida idanunshi direct zuwa wajen, ahankali ta sako kanta cikin dakin tana duban wajen gadonshi tana fatan allah yasa bai tashi ba, da yake tasan baya tashi a daidai wannan loakcin lokacin da bashi da lafiya sai tayi tunanin habit dinshi ne, kwata kwata batasan cewa ya tashi ba harta wuce ta gefen ind ayake zaune ta shige bathroom ta rufo, alwala ta dauro bayan tayi easing kanta sannan ta futo ta shiga closet wajen inda kayanta yake ta zaro hijab ta saka, sannan ta futo, sai a lokacin ya gane ashe kayanta nw a cikin closet room dinshi kenan harma da towel da panties din da ya gani wanda yasa aka zubar dasu daga bathroom dinshi, yana kallonta ta bude kofa ta fuce saga bedroom din sannan ta karo kofar, sai a lokacin ya tabbatr da anan part din tayi barci kenan.

Sabeeha na fitowa ta fuskanshi qibla ta tada sallah tana idarwa ta hade jikinta waje guda tana tunanin rayuwar datayi a gidan bataji karar futowarsgi daga bedroom dinba harya karaso inda take, inuwarsa ta fara gani kafin ta dago idanunta, suna hada ido hudu tayi saurin gyara zama tana zazzare idanu, kirjinta na dukan uku uku haka ta dake,kanta a kasa tace “good morning”
Ba wannan ne ya kawoshi wajenta ba don haka ya samu waje ya zauna yana fuskantarta, “whats your name” yanda ya furta calmly yas ata dago da sauri suka hada ido, tana kallon yanda idanunshi ke kyalli, saurib dauke nata tayi muryanta kasa kasa tace “fatima!” Kallon bakinta yayi, sai a lokacin ya lura da yanayin hakoranta datayi magana, kauda kanshi yayi ya sake jefo mata wata tambayar, “so ke yar aiki ce?”
Tana jin haka gabanta ya bada wani dammm,

“Waya kawo ki? Who are you exactly? What was your agenda for coming into my life?”Yanxu da ya sake magana sai taji yanayin muryarshi ya sauya, “khaal?”ya sake jefo mata tambaya,

Tana jin haka tayi saurin dagowa ta kalleshi, wani irin kallo yake mata mai kama dana tsana, don haka kawai zata iya fasaara kallon,bai tsaya ma ya amsa tambayoyin da yayi mata ba shurun da tayi ya bashi amsa don haka ya miqe har zaibar parlor ya dan dakata,“you’re just a maid, my maid, keep that in mind and don’t have any stupid thoughts on your head, da zarar na gano abunda nakeson na gane zan sallameki,”

Yana barin wajen ta bishi da kallo, maganganunshi na karshe sun mata zafi sosai kamar zatayi hawaye, tama rasa wani irin tunani zatayi, he was calm at first then kuma lokaci guda ya sauya, tambayoyin da ya mata ne suka dawo kanta, waya kawota? What was her agenda? Duk yanda akayi hidaya ta fada mashi wani abun kenan? Daman ammu ta fada haka zata faru, gashi kuwata ta tabbata, innalillahi, yanxu wani irin kallo yake mata? Bazata iya tantancewa hakan ba, kuka bazatayi kasa a gwiwa ba,bai nuna mata alamun ya ganeta ba kwata kwata.
Ta dade tana nazari har barci barawo ya saceta a zaune ba tare sa saninta ba.

Shi ko baima koma barcin ba yanata fama da waya yana aiki ya dade sosai har wajen karfe bakwai ya fito, ko kallon inda take baiyi ba ya fuce daga part din.

Bata farka ba sai wuraren karfe tara haka,yar wayar da jamid ya taba bata na gefenta, daman yawanci wayar amfanin da take mata duba time ne kawai, ba wani abun take da wayar ba, tana ganin lokaci tayi saurin miqewa zaune, tana nazarin me zatayi da zaisa ya tuna ta, na farko dai routine dinta data saba shi zata fara yi, maganganun ammu na kara karfafa mata gwiwa ta miqe ta wuce bedroom din, tasan a daidai wannan lokacin ya futa don haka ta fara kokarin gyaran bedroom din nashi.

Hidaya dasu fadwa basu san cewa sabeeha tana dakin taj dinba, sonata kuwa data ganta a part din nashi batayi tunanin anan ta kwana ba,sannan kudirinta har zuwa yanxu bata chanza shi ba.

***
Wajen karfe goma na safe ya shugo gidan, da fadwa yaci karo a kasa tana kokarin fitowa daga part dinta cikin shiri da alamu fita zatayi, tubda ya shigo take binshi da idanu, yana sanye da kayan gym yau ko sauyawa baiyiba, don yana gama workout ta nufi gida, daga sama har kasa take binshi da idanu tana hango gumin da ya danyi daga workout din kwance a jikinshi dukda daga ac ya fito,
he’s so attractive yet so calm and hard at the same time,kammaninshi gaba daya ya fita daban daga nasu, donshi kanar ruwa biyu yayo, the arab side of him a fuska ne the physique side of him kuma irin na manyan maza, yawanci fararen mazan saudi zaka gansu kamar solobiyo shidai ya fita daban, tama rasa yanda zatayi describing dinshi, the inner him is like a black American every womans dream,

Ta shagala sosai wajen kallonshi harya wuce ta gabanta yayi kamar dutse ya gani a wajen, “hey baby brother”
Ay kamar da iska take magana, ya wuce sama ba tareda yace mata ci kanki ba, murmushi kawai ta danyi tana tuna wasu abubuwa,da yanda hidaya ke underestimating dinshi, akaha dai zata bisu da ido dashi da hidayar taga wazai cimma wani,haka ta fuce tana murmushi ita kadai.
Tana shiga motarta tayi dialing wata number ana dagawa ta soma magana “any update!”
“Yes boss,”
“Doctor fah? Have you handle him? You need to be meticulous bana son any kinds of problem,”

“Yes boss”
Ana fadin haka ta kashe wayar tana murmushi kawai,dadin yanda take taimaka wa hidaya takeji ba kadan ba.


Bangaren taj yana haura wa sama ya wuce daki, gaba daya yama manta da wata sabeeha, ajiye jakarshi yayi kafin ya soma cire rigar jikinshi, yana cirewa ya ajiyeta a wajen ya rage daga shi sai short tight, kai tsaye ya wuce bathroom yana bude kofar yasa kai cikin bathroom din cikin saurin ta juyo hankali a tashe, suna ido hudu jikinta ya soma rawa shi kuwa ganinta daga ita sai towel take memory din lokacin da suke cikin bathroom yazo kanshi,

burkicewar da tayi yasa juya mashi baya ta fara
Kokarin zura hijab dinta allah yaso ta shugo dashi, taba kokarin sakawa ma ya shugo, innalillahi wa inna ialihi rajiun kawai take aranta,

Allah ya taimaka ma ta daura towel a jikinta da yake akwai towels da yawa a bathroom din ta
allah ya taimaka saida ta saka ya shugo bathroom din, shi baiyi expecting din kowa ba don haka ya shigo kai tsaye, tunda ya kafeta da kallo harta saka hijab dinnan bai cire idanunshi a kanta ba , take kawai fuskanshi ta koma jaa sosai,sabon memory na mashi flashing, ranar da ya shigo bathroom zaiyi futsari ya kasa cire zagiyar wando, sai kuma memoryn ya sake confusing dinshi gata nan ta tsungunna gabanshi zata zare mashi zariyar wandon shi sai lokacin daya shugo bathroom lokacin ta gama wanka harya fara kokarin taba kirjinta a bathroom din sai abun ya mashi kamar itace take kokarin sakashin yin haka, gashi ga ta a bathroom din a lokacin, mekenan hakan ke nufi? Kusancinsu har yakaiga shigansu bathroom a tare ko me? Wannan yar yarinyar? A maid? Har tana zare mashi zaryar wando? Yama kasa tuna what next happens after that, “What the f**k!!!”

Ya fada yana mata wani mugun kallo, jijiyoyinshi sun fito rado rado, tana jin saukar muryarshi tayi hanzarin juyowa ta nufi hanyar futa daga bathroom din, kamar zatayi tuntube haka ta karaso tsakiyar dakin tana haki,shiko ya kasa wrapping mind dinshi, yama rasa dalilin bacin ranshi, me sukayi da yarinyarnan? Abunda hidaya ta fada gaskia ne? Yana ganin ta kamar karamar yarinya,did she take advantage of him da lalurar daya tsinci kanshi Koko yaya? Don ya kasa gane dalilin da yasa ya nemi taba wannan yarinyar.

Sabeeha kuwa kasa tsayuwa tayi a dakin ta fuce bedroom din ta nufi hanyar kofa daidai nan sonata ta shugo, ko kallon inda take sabeeha batayi ba ta fuce daga dakin.
Sonata kuwa suman tsaye tayi don jarabar mamaki, cikin abund abai wuce second biyar ba ta kalli sabeehar harta gano cewa daga bathroom take donga digon ruwa nan akan fusknta, hankali a tashe sonata ta shige cikin bedroom dinshi, tana jin saukar ruwa cikin ta ya duri ruwa itama, ta dauka wajen 20mins tana zarya tsakanin dakin yanda kasan ta dauka 2hrs haka takeji, allah allah kawai take ya fito taji meya kawo sabewha da sassafe dakinsa, badai kwana tayi anan ba?“Haa it can’t be possible” tana gama fadin haka saigashi ya fito daga bathroom, yana ganin sonata ya sake hade rai, daman ranshi a bace yake, wankan ma cikin bacin rai yayi yana kallon gabanshi, dake shedan shugaban yan zuga ne haka ya dunga raya mashi banzan abubuwa akanshi, yanxu haka yarinyar nan taga jikinshi? She take advantage of lalurarshi, sai yaji gaba daya ya tsaneta, ko kallonta baya son yi.

Sonata na ganinshi gaba daya abunda ke kanta ya warware tama mance da haushin da takeji,nufoshi tayi ganin yana neman karasawa wajen walk in closet, “babe good morning”
Ko kallon inda take baiyi ba yace “excuse me” yana fadin haka ya wuce bathroom, tasan me hakan da ya fada yake nufi, ta futa zai shirya kenan, harta juya jiki a mace zata futa ganin yanda ya mata magana ta dakata, wani irin smirking flirty murmushi tayi kafin ta tunkari walk in closet din, tana shiga ta karo kofar wajen yana kokarin shafa body sprays dinshi,
“Are you deaf” ya fada in a harsh to, ay ko sauraron sa batayi ba ta tunkari inda yake tun kafin ta karaso ta dakatar da ita, “dont you dare take a single step” tana jin haka ta tsaya kyam,
Take ranta ya baci ta soma magana , “why are you pushing me away babe? Why? Don’t tell me it because of that maid?”
Da mamaki ya dago yake kallonta, kishi ya rufe mata idanu sosai, “yes, is it because of that ugly maid? Did you sleep with her? Huh?”
Yanda take magana kamar zata tashi sama, ranshi idan yayi dubu ya baci sosai, comparing dinshi da wannan yarinyar kadai da takeyi ba karamin bata mashi rai yake ba, take ya daka mata tsawa
“Get d hell out!!!!, this should be the first and d last time da zaki kara shugo min part dina, idan na kwana da ita whats your problem with that? Isn’t She my wife!!!!!!”
Ay kamar ya buga mata guduma aka, kuma yaga hakan a fuskanta, daman ya fadi hakan ne donya baqanta mata rai sosai,batayi wata wata ba ta fuce daga dakin rai a bace kamar zata amayar da kayan hanjinta don masifa.

Afiya na kwance a daki tana barcin asara sonata ta shugo, tana karasowa inda afiya take ta soma tashinta “babe babe”
Sama sama afiya ta soma jinta, harta bude idnaunta ahankali, ganin sonata na kuka yasa afiya ta zauna tana kallonta tace “yadai?, kuka fa kikeyi? Ko haryanxu kin kasa samunshi? Wai whats so special about him, that thing da kike nema a jikinshi akwai thounsands da suke dashi kuma kina samu, what so special about him”

Sonata najin abunda ta fada ta soma dunqule hannunta tana furzar da huci takaici tace “If i can’t have him then no one should,”
Da mamii afiya ta kalleta don bata gane inda ta dosa ba, “what do you mean”
“Babe i need your help,yarinyar nan jiya a part dinshi ta kwana, qila ma tare suka kwana ,what if he slept with her? What if she got pregnant bfr i do? Plan dina will be ruined i need your help”
Shuru afiya tayi tana sauraronta itafa wannan batada hankali, kallonta kawai afiya keyi, batasan cewa addinin mu bai amince da cikin da babu aure ba, duk plan dinta was ta knock him off and have him sannan ta samu ciki dashi wannan zaisa bazai barta ba, batasan cewa intimacy bfr marriage is prohibited kuma shi zaiza ma bazai taba auren nata ba bayan wannan ma auren baturiya? kafira kuma yar bariki ma? That’s impossible.
“Babe are you even listening to me” sonata ta tamabyi afiya
“Yes come again?”
“Yarinyar nan a dakinshi ta kwana, lets do something bfr its too late”
Afiya najin haka tace “trust me ans just calm down okay”


5pm…
Kusan a tare duk sukayi parking motocinsu, motar hidaya ce ta fara shugowa kafin ta fadwa, gaba dayansu kana ganinsu kasan da bala’i suka dawo gidan, tunda sukaji batun kwanan sabeeha a dakin taj, afiya ce ta kirasu ta shaida masu hakan conference call ma sukayi. kowannensu da abunda ke cikin zuciyarsa.

Suna shugowa cikin gidan hidaya tasa head maid ta kira mata sabeeha, daidai nan taj ya sauko daga sama daman hidyaa ta kirashi a waya.
Duk kusan a tare duk suka karaso, yana zuwa ya zauna kan kujera ya daura kafa daya kan daya, hidaya dai tana mamakin yanda ya dan fara sauyawa, gaba daya attitude da bai taba yi ba take ganin yanayi yanxu,bama wannan ba tukunna, maganar yarinyar nan da afiya ta tsorata su ne a gabansu inda tace masu ay a dakinsa ta kwana, kuma barinta around him is vwry risky, he could easily trust her once again tunda itace wadda ta kula dashi lokacin da baya cikin hayyacinsa.
Sabeeha na futowa tundaga nesa ta hango cirko cirko, ga sonata ga afiya ga fadwa a zaune hidyaa ma a zaune sai taj shima yana daga zaune, tareeq ne dai baya nan.
Tunda ta karaso gabanta ke dukan uku uku,

Hidaya na kallon taj din babu wasa kan fuskanta ta turo mashi divorce paper tace “sigh this up”
Daukan paper yayi ya soma karantawa, takarda ce ta yanda akeyin saki irin nasu achan kasar, yanda addini ya tanadar, aaida ya karance paper tass kafin ya dago ya kalli hidayar, “dis what i should have done already,we wouldn’t know whats she might come up with, tunda wanda ya kawota baya raye, i don’t trust her, yanda yayi kokarin cutar dakai itama zata iya yin haka”
Sabeeha najin haka gabanta ya bada wani dam, tunda hidaya ta soma magana take kallonshi, shi baika san tana wajen ba kwatakwata,
Idanunshi na kan paper,
“Maybe ma harda ita akayi planning kidnap din,” fadwa ta karashe tana mata wani mugun kallo,
ta ajiye mashi pen agabanshi, daman kamar jira take tamafi kowa kosawa tunda afiya tace mata idan har sukayi wasa wani abu zai iya shiga atsakaninshi da yarinyar.

Gaba daya binshi suka dunga yi da idanu ganin yaqi motsawa,sabeeha kuwa a daidai wannan lokacin babu abunda take sai hawaye, wato abunda suka kulla kenan, su maida abun zuwa khaal, sun kulla mashi duk sharrinsu akanshi, yanxu sa sukaga taj din zai iya ganowa shine suka maida kan khaal kenan, ita kuma da khaal ya aura mashi ita dole za ayi zargin bakinsu daya da khaal tunda ya bata property din taj, bayan wannan ma tasan hidaya ta gano cewa khaal ne ya kawo ta gidan ba tare da saninsu ba, so they want to use that against her, “innalillahi wa inna ialiahi rajiun” ta furta ahankali, kunnsshi ne kadai ya jiyo mashi furucinta,sai yaji presense dinta a jikinshi,allah allah take ya dago ya kalleta amma yaqi, baiyi wata wata kawai ya dauka pen din ya sanya hannunshi kan paper din, yana kokarin rubuta saki kawai sukajiyo muryar ammu data futo, barci takeyi amma wani ikon allah haka kawai ta farka a daidai wannan lokacin gabanta na faduwa, wannan yasa ta fito kuma taji gaba daya abubuwan da sukace, tsayarwa datayi tana hangosu jiran decision din taj din kawai take.
“Karka sake ka rubuta komai kan paper nan”
Gaba daya dagowa sukayi suna kallonta,fadwa ce tayi saurin miqewa tsaye tace “why? Saboda me ammu?”
Ko kallon inda take batayi ba ammu ta karaso inda sabeeha take tace “bazata bar gidannan ba, she can never, ko kun raba aurensu abunda ke tsakaninsu zai maido su”
Da mamaki duk suka juyo suna kallonta, hidaya data kagara da zancen ranta idan yayi dubu ya baci da maganganun da ammu keyi, tace “i have said it all, yarinyar nan yau zatabar gidannan, dama chan we have never accepted her she can never be part of this family”

“Well yanxu dole kuyi accepting dunta tunda she’s PREGNANT!!!!!!”
Gaba daya dakin ya dauke wuta kamar mutuwa ta gifta, fadwa afiya hidaya sunji maganar ammu kamar saukar aradu,
“She’s pregnant for him”
Suka ne kawai sonata batayi ba don baqin ciki, hidaya kuwa idanunta yayi jaa sosai, shi mai gayya mai aikin gaba daya ji yayi kamar an toshe mashi kunne sai kawai ya saki pen din, idanunshi yayi jaa sosai ya dago suka hada idanu da sabeeha, take yaji kamar an zuba mashi ruwan dalma a zuciyarshi tsabar bacin rai, sabeeha kuwa baiwar allah kamar ta kurma ihu tsabar furgici, tama kasa karantar yanayinshi gaba daya mai wuyar fasaara, da kyar ta dauke idanunta akanshi ta maida kan ammu, saurin runtse mata idanu ammu tayi alamun tayi trusting dinta, hannunta ammu ta kama ta rike dake ta faman karkarwa, me ammi take nufi da abunda ta fada yanxu? Dauke idanunta tayi daga kan ammi ta maida kan mutanen dake parlorn sai suka dunga mata wani irin gizo, tana hango bala’i cikin idanun kowannensu…..itama ammu karfin hali ne yasa ta fadi hakan…….


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 11 · 0% Book details