← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 52 OF 66

Chapter 105

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 30 min read

Jamila dai kwana tayi tana kukan bakin ciki takaici, da zafin cin amana, idan za akwana ana ce mata ga abunda hadiza keyi da mijinta zata rantse karya saboda ta yarda da hadiza sosai, ta maidata kamar yar uwarta ta jini, ta iya ta musanya yarda bata da alhakin kowa duk don hadizar ta bukaci haka kuma bata waiwayi mai zai biyo baya ba tsabar tsantsan kusancin dake tare dasu, amma ta rasa abunda zata saka mata dashi sai wannan? Kuma akan idanunta ta shiada hakan? Wannan cin amana ko a lahira bazata taba yafe ma hadiza ba, kuma tayi alkawarin saita nuna mata ba a taba jamila a zauna lafiya, dukda tasan hatsabibancin hadizar ita kanta baisa taji tsoro ba, saidai su kanshe kansu don wallahi saita baqanta mata yanda taci amanarta, ashe sunyi shekaru sunayi? Bama tun yau aka fara ba, ranar nan ma ashe raina mata hankali sukayi, kuma wallahi saida taji a jikinta amma ta basar wai ita tana ganin babu wadda takeda kusanci da aminci kamar hadiza, kai kota mutu zata iya barin yayanta wajen hadiza bazataji darr ba saboda tsabar yarda amma haka sukaci amanarta, shi jamilu bai wani dameta ba don tasan zaije waje ya nema, kuma yana bin mata wannan ta sani tun tuni, shine bin kananun yara yan talla shine bin yan 2k one night, dayayi ta’asarsa ita ke bi taba kwashewa amma wannan karan kam abun ya mata zafi, gashi kwance gefenta bayan ya gama maganganu marasa mutunci akanta da wulakanci, wai gata a bushe, wayam babu dadi, kam’bala’i badan tana danne zuciyarta ba sannan kuma tana tunanin yayan dake tsakaninsu ay wallahi data daba mashi wuka ta kashe shege ta huta dan buran’uba.
Safiya nayi ta riga kowa tashi, duk yanda taso ta danne abunda ke cinta a zuciya, kasawa tayi idanun nan a kumbure ta futo har ta wuce hadiza daketa sharar barci, ta dora tafashen ruwa, allah allah kawai take ya tafasa ta kwarawa shegiya, wata zuciyar ta haneta, “tunda har kika iya kaiwa har safiya bayan kinga cin amanar da suka maki ra’ayul ayni ai zaki iya dakawata ki hukuntata yanda zata wulaqanta, yanxu kika watsa mata ruwa taci banza,daure jamila danne” haka zuciyarta ta dunga raya mata.
Haka nan ta hkura ta dora sanwar safiya, indomie ma ta aika aka suyi mata don su halifa sun tashi, sheggun ne suketa barcin asara, tana gama dafawa ta zubawa su halifa suka tafi makaranta ita kuma ta juye masu a tray.
Daidai nan jamilu ya futo,sai faman wage baki yake da asuwaki, kauda kanta tayi ko mutunci gaisuwa bai samu ba saida ya fito daga bandaki yana dariya ta kalleshi tace “ba haihuwa ba ko yaya dari mukayi dakai saina hukuntaka jamilu,”
“Ina kwana mijin jamilaaa ikon allah” jamila ta fada tana kashe murya, sakin baki yayi galala yace “lafiya lau uwar halifa, abunci fa?”
Daman haka yake kiranta dashi, indai bai kirata da jamila ba.

Gashi nan na zuba mana gaba daya, hadiza ta tashi kuwa?”
Kanshi har waji rawa rawa yake yace “bari na dubo ta” ya shige daga ciki jamila ta bishi da wani kallo, kai kana ganin irin kallon nan kasan suna ruwa😂
Cikin parlor ta shiga daidai nan hadiza ta tashi, tana hamma, kallon jamila tayi tace “ina kwana aminiyas”
Saida jamila ta dan dakata kamar ta shaqota kafin tace “lafiya lau, sauko muci tare na zuba mana duka”
Ko kuskurar baki hadiza batayi ba suka zauna, jamila taja kayan kwanciyar data kwanta dashi suka fara cin abunci.
Jamilu sai faman wage baki yakeyi don hardashi,normal normal suka fara hira, don kwata kwata jamila batayi gigin nuna masu ta ga wani abu ba, su ko a wajensu sun maisheta shasha sha saisu kalli juna su kanne ido, jamila sai kawai murmushi tayi.
Wuraren wajen karfe goma sha daya hadiza tayi wanka ta shirya, zasuyi sallama jamila tace “toh maganar kudi ya za ayi kenan?”
Shuru hadiza tayi kafij tace “ni yanxu gaba daya dubu dari uku ce a wajena, kudin albashin mu kenan na wata uku, kinsan dubu hansin hansin wannan tsohuwar ke bamu nida shegiyar yarinyar nan”
“Toh ki turosu duka kuwa don wallahi dakyar idan zasu kai ma, ba ayi maganar kudin mota ba wannan mai sauki ne don zan biya da kaina”
“Allah sarki jami, allah yabar min kawata”
Dariya jamila tayi tace “Ameen kawata”
A take hadiza ta tura dubu dari uku zuwa account din jamila, sannan sukayi sallama kan duk yanda akayi jamilar zata kira hadizar ta shaida mata.
Tana futa jamila ta daura kafa daya kan daya tana kallon alert dun kudin, “hadiza kenan…”

Chan banagaren maya bata tashi bafa saboda over dose tayi ma kanta, bayan kwayoyi data sha har yar kwalba ta kofa, allah baiyi bahijja zata gani ba, haka su laila suka wuce school ita bata samu taje ba, koda daddy ya tambayi mummy maisa batajeba nan ta shiada mashi baqon watan ta ne yazo shine ta mata allura ta huta.
Yadai je a zancen nata a haka amma bawai ya yarda bane, don tsakanin jiya zuwa yau gaba daya yanayin bahijjan ya sauya koda ta shaida mashi tayi retire yayi mamaki sosai don yanda ta kafe bayajin zata iya hakura da wannan aikin nata, don tana son taimakon rayuka, koda yake anan ma zata iya yin hakan ba sai lallai achan ba.
Ya rasa dalilin da Nigeria gaba daya ta fita ranta, taki jinin dawowa, saitayi shekara biyu uku a jere bata yi tunanin zuwa gida ba abun yana bashi mamaki, kuma batun yanxu abun ya faro ba tun bayan data haifi maya.
Misalin wajen karfe goma sha daya ta farka, kanta yayi mata wani irin nauyi sosai, ta dubi time ganin 11 yasa hankalinta tashi, gaba daya batayi aiki da tunani ba, what if dady yaganta a wannan yanayi? Take gabanta ya fara bada dam dam, sallamar bahijja yasa ta sola gyara natsuwarta yanda take taoron dady bata tsoron mummy kwata kwata, its easy to fool mummy amma dady a take yake rafko ta.
Murmushi bahijja ta mata hannunta rike da bowl ta karaso ta ajeshi gefen bedside maya ta wani kauda ido, bahijja ta zauna gefen gadon tare da kamo hannunta tace “baby babu gaisuwa”
“Good morning” ta gaisheta a takaice, “morning baby, kanki na ciwo ko? Ga soup nan na kawo maki”
Kallon bowl din maya tayi kafin tace “thank you”
Miqewa tayi ta wuce bathroom ta wanko bakinta kafin ta futo, bahijja ta kalleta tace “kinyi alwala?”
Girgiza kai mayan tayi ta juya zuwa ga bathroom din.
Agaban bahijja ta futo bayan ta shunfida mata sallaya ta bata da hijab ta tada kabbarar sallah tana kallonta.
Kai ko a cikin sallar mayan ma aikwai dan gyara, at that point bahijja ji tayi ta tsani kanta gaba daya wallahi tsabar takaici.
Mayan na idarwa ta miqe tsaye ta nufi bakin gadon ta zauna ta dauka bowl din, bahijja na kallonta batace mata uppan ba, ta shanye tass, saida ta gama bahijja ta kalleta tare da aje pills dinnan a gabanta ta soma magana “when did this start maya?yaushe kika fara shan different kinds of dangerous pills? Me kikeyi da maganin hana daukan ciki maya?”
Shuru maya tayi ta kauda kanta gefe, tgaba daya tsoro ya gama baibayeta, indai mummy ta gani to tabbas dady ma ya gani”
Sai kawai ta fara hawaye, ta kamo hannun bahijja tace “mummy please don’t tell daddy, please bazna sake ba”
Take bahijjar itama ta soma hawaye, “haba maya? Haba maya? Meysa zaki lalata rayuwarki? Meysa? Kinsan a wani hali na kwana? Ina blaming kaina for this? Idan aure kikeso wallahi zamu maki, amma zina? Zina maya?”
Dake futsararriya ce saita maidawa uwar tata martani, “idan na buqaci ku saurare aiba saurarona kukeyi ba, then why are you judging me now? Why are you blaming me? Inason magana dake mummy amma bakida lokaci na, jiya na dawo cikin bacin rai baki tsaya kin saurareni ba”
Hannunta bahijja ta kama tace “nasan laifina ne baby, laifina ne ki yafeni, daga yau i will stand with you,duk damuwarki karki boyemin, we will over come this, kimin alkawari bazaki sake shan komai ba please”
Girgiza kai maya tayi tace “bazan sake ba” ta fada ne kawai amma a ranta kam babu abunda zai hanata shan waennan abubuwan, suke debe mata kewa.
Wasu tablet ta bata tace “cleanse your self”
“Mummy dady fa?”
“Bai sani ba, ban fada mashi ba, now tell me meysameki jiya? What happened?”
Wata iriyar fuskar tausayi tayi tana kallon mummyn nata tace “mummy aure nakeso, inason uncle taj,”
Shuru bahijaj tayi amma fa saida gabanta ya fadi, saboda wasu yan kalubale datake hangowa, ayau inta fadima nanna itace first person da zatayi supporting dinta amma ba lallai anne ba, ita ke da decision na family din gaba daya,amma duj yanda za ayi saita san yanda tayi ta aurar da maya ga taj din, kodan saboda halin data tsinceta, gwara ta mata auren kawai.
“Kina sonshi?so na zaman aure?”
“Yes mummy, i want him, shi kadai nakeso kuma shi nakeso ya zama mijina”
“Shikenan indai kin min alkawari Insha Allah bazaki sake bin maza a waje ba”
“Yes mummy nayi alkawari”
Da haka suka yi yan kuskus dinsu.

Wuraren wajen hudu bahijja ta shirya ta wuce asibiti, tare da basira, yau itace tayi lunch din da yan asibiti zasuci.
Da sallama suka shugo, yau anne na zaune yanxu an daina mata waennan allurorin da suke sata barci don ta samu progress sosai, saidai sallaman ta kawia da ba ayi ba shima ana saka ran very soon za ayi.
Yau nanna bata samu zuwa ba don daga fadila sai anne a dakin.
Gaggaisawa akayi bahija tayima anne ya jiki tace mata da sauki, suka danyi hira har zuwa magrib.
So take tayima anne maganar amma bataan ta inda zata fara ba, da farko taso ta fara yima nanna maganar saitaga abun zai iya zama matsala idan har bata fara sanarma da anne ba wannn yasa tayi deciding sanarma da anne, futar fadila ta bata wannan damar din ko fadila bata tunkara ba da neman shawarar, so take kawai ta nema ma diyarta mafita.
Zama bahijja tayi gefen anne daman duk dare ana shafe jikinta da towel don bata fara shiga toilet ba komai a zaune ake mata.
Towel din ta dauka ta soma goge ma anne hannu dashi suna dan hira sama sama.
“Da magana a bakinki bahijja..”
Anne ta fada tana kallonta, ckin sauri ta dago, tana mai duban anne din kafin ta sauke murya tace “hakane anne, amma bansan ta yanda zaki dauki abunda zan fada maki ba”
“Menene??”
“Ina neman alfarma ne anne”
“Wace alfarma kenan?”
“Inason a hada karfin zumunci ne…” ta dan dakata ta kasa karawasa.
“Ina jinki kinyi shuru,”
“Daman maya nakeso na hada da tajudeen tunda akwai aure tsakaninsu kuma ta nuna tanason shi shine…”
Hannu anne ta daga tare da dakatar da ita, “keda bakinki kike neman hadin gida?hadin aure? Saboda yarki naso ko? Toh shi yace yana sonta ne? Inace duk cikin yayana kece kika bijirema zabina kika nunamim cewa bazaki taba auren zabin dana maki ba sai wanda kika yima kanki?, toh bari kiji bahijja,ba huruminki bane don yarki ta nuna tanaso saikiyi deciding cewa hakan za’ayi”
“Anne dan allah ki saurareni, inada nawa dalilin”
“Ki rike dalilinki, dalilinki bazaisa na chanza ra’ayi na ba akan kowa,kuma karki sake kiyi tunanin tunkarar nanna da wannan zancen don wallahi zan saba maki bahijja..”
“Anne maisa? Meysa? Ay ba kaifi bane don maya tace tana sonshi, dan uwanta ne jininta ne, nayi imanin babu wanda zai kula da ita kamar shi kuma tana soshi”
“Sai akace maki shi kuma yana sonta ko?“
Shuru bahijja tayi feeling so disappointed, meysa when it comes to iyalan ta kwata kwata anne bata kaunar su, in badan haka ba taga dalilin da zaisa ta nuna kin yarjewarta akan wannan zancen ba, i fact zumuncin su ne ma zai kara karfi,musamman yanda take da nanna.
Hawaye ta somayi don abun ya tabata tace “yaushe shekaru wajen ashirin da biyar kenan, har yau ina ganin banbancin da kike nunawa a cikin mu anne,bkya kaunar majeed haka zalika maya dukdan saboda nabi abunda allah ya kaddara”
Rai a bace anne ta maido da dubanta gareta, “bahijjaaaaa, ni mahaifiyarki kike fada wa magana?”
“Kiyi hkuri idan ranki ya baci, bazan iya yin shuru ba, wannan ne dalilin dayasa nake qin zuwa, na zabi na zauna achan, aurena da majeed mukaddarine daga allah, bashida laifin komai anne, kuma babu wanda ya kaishi turasasa ni kan qin juyama asalina baya, gashi yanxu abun ya shafi yata,dama zai tsaya akanmu da da sauqi, yanxu da ace fadila ce tazo ta nemi alfarmar nan da tuni kin yarda kuma kin amince dake ni tawa yar…”
Tass anne ta wanketa da mari, wanda yasa ta yin shuru, fadila da shugowarta kenan taji kalamanta na karshe sai zuciyarta ta karaya sosai.
“Idan kin gama fada min maganganun da kikaga dama zaki iya tafiya, ban amince ba kuma bazan taba amincewa ba da abunda kikazo dashi, ta dalilinki ko yarki bazan lalata zumuncin dake tsakanina da yar uwata ba, idan aure kikason yi mata nayi mata miji tun tuni, wanda nake tunanin zai iya zama da ita kuma ya gyara halayyenta, ya jure duk wani shirmenta”
Anne na fadi haka tayi mata nuni da kofa, sunkuyar dakai bahijja tayi ta share hawayenta ta dauki jakarta tace “allah ya tashe mu lafiya ya kara sauqi”
Tana fadin haka ta fuce fadila tabi bayanta har zuwa mota.
“Bahijja bahijja meya faru?”
“Ba komai fadila ki koma magariba ta kusa”
“Dan allah ki fada min”
“Babu komai zan koma gida sai gobe in allah ya kaimu”
Tana fadin haka ta shige motarta da daddy ya saya mata jiya tajata.
Komawa ciki fadila tayi har inda anne ke zaune ta dafe kanta.
“Anne, dan allah kiyi hkuri, bacin ranki zai iya zamo mata masifa koma me tayi maki nasan baikai zuciyanta ba”
“Kiramin hajara a waya fadila” anne tayi magana…..
Hadiza na dawowa gida ko hutawa batayi ba ta dingi neman diyarta, rabi ta shaida mata tana bangaren su, koda wasa batayi gigin zuwa bangaren ba tanadai fatan zuwan mayan.
Wuraren 4 sai gasu laila sun dawo, yauma itace a gidan gaba laila kuma na daga baya, ay daga safiyar allah daya saukesu zuwa yanxu ta gama tabbatar da akwai wani abu tsakaninsu, yanda yake mata magana, da yanda take responding kosu da suke yayan cousins dinshi baya masu haka, kuma magana fa da lallami yake mata bawai yanda yake masu ba harshly, so sweet of him gashi wani irin kallo da yake mata hmm…

Tsabar gulma direct part din su maya laila ta nufa, tana zuwa kuwa ta taddata zaune a sitting room, ta daura kafa daya kan daya ta sakala airpod a kunnenta tana jin kida.
Ta bayanta laila ta karaso ta sanya hannunta waje idanunta ta rufe mata su, airpod din kunenta ta cire kafin tace “mey haka? Saikace wasu yara”
Cire hannunta tayi ta zauna kan kujerar tana fuskantar mayar kafin ta soma magana, “yi hkuri sarkin fada ke ba’a iya maki wasa ba”
Tsaki maya tayi tana jin kanta wani himm, itafa yanxu jinta yake matar taj kawai, zatayi rashin mutunci kuwa.
“Na shigo dazu mummy tace bakiji dadi ba, how are you feeling now?”
Yatsune baki tayi tace “I’m okay” tana fadin haka ta maida airpod dinta ga kunnenta tare da daukan bowl din popcorn dake kan center table ta cigaba da cin abunta, laila data lura wani shasha mata kamshi take tayi saita Tashi kawai tayi fucewarta.


Bangaren hadiza tana zaune, zaman jiran call din jamila kawai take, aiko sai gashi ta kira, cikin gaggawa ta daga wayar takai kunnenta.
“Ya ake ciki jamila”
Sauke ajiyar zuciya jamila tayi kamar wadda tayi doguwar tafiya tace “wallahi kinga faduwa nayi a bandaki, na gurde saida akayi min gyaran hannu”
“Subhanallahi, garin yaya”
“Tsautsayi fa…allah ya rufa asiri ma ba gocewar kashi bane”
“Toh allah ya sawaqe, yanxu sai yaushe kenan zaki je wajen bokan?”
Ahanakli jamila ta furta shegiya, kanki kawai kika sani, hadiza bataji ba wannan yasa tace “hello”
“Ina jinki, hannun ne ya danyi min tsami, jibi idan na danji dama dama insha allah zanje”
“toh shiknan allah ya kaimu,”
Sallama sukayi jamila ta janyo kazar data sayo kashashiya ta yagi abarta ta kora da lemo,”


Cije yatsa hadiza tayi, taso ace yau jamila taje wajen bokan nan anyi abunda akayi kawai wannan shegiyar yarinya ta karasa kowa ya huta, cikin yan kwanakin nan fargaba takeyi sosai.

The next day…
Yau ta kasance friday, Da asuba sabeeha ta tashi, bayan tayi sallah tayi wanka tasa atamfa riga da skirt cikin kayan da aka bata, kayan sun dan kamata kadan ammafa sun mata kyau sosai ba kadan ba Masha Allah, hijab din sallarta ta dora akai sannan ta futo.

Backyard tabi zuwa ga part dinshi iska na kadata ta ko’ina saboda sanyin safiya, taba karasowa part din nashi ta danna pins din kofar sannan ta bude ta shiga.
Hasken fitilun kasan a kashe suke wanda yasa ta kukkunnasu don ta samu hasken yin gyara yanda ya kamata.

As usual vacuum ta kunna ta soma vacuuming floor din parlor, saida ta gama tass ta dauko mop ta zuba mopping mist sannan ta fara mopping parlorn tana gamawa ta danyi yan goge goge, tana cikin goge gogen ta dago sama gave stairs take idanunta ya shiga cikin nashi dukda akwai tazara tsakaninsu.
Yana sanye da pjs farare tass riga da wando,
Saurin warware hijab dinta tayi data nannade shi a kirjinta ta gyara tsayuwarta, tundata kunna vacuum dinan ya tashi.
Hannunshi yay mata nuni dashi alamun ta hauro sama, sannan ya juya ya koma ciki.
Saman ta soma hawa a natse tana isowa bakin dakin nasa ta dan dakata, knocking ta danyi daga ciki yace “come in”
Ta shugo a natse bakinta dauke da sallama, daga bakin kofar ta tsaya taki takowa zuwa ciki, saida ya juyo yana kallonta kafin yace “ni zan fara gaisheki ne?”
“Good morning”
Bai amsa ta ba yace “fix the mess” ya karashe yana nuna mata beddings din dake a yamutse kamar anayi aiki akai.
Yana fadin haka ya wuce bathroom domin yayi wanka, ya dade sosai a bathroom din harta gama gyaran ya futo daidai nan tana shirin futa ya dakatar da ita.
“Dauka min kayan da zansa” ya karashe yana zama gefen dresser, coily gashinsa yake kokarin drying don su bushe.
Badan ta soba haka ta shiga closet din tana kunkuni, yanxu ta ina zata fara nemo mashi wani kaya? Saita tuna da hakan da take mashi a saudi.
Bata tsaya wani zabe zabe ba ta zato wash kaftan riga da wando baqaqe ta fiddo su sannan ta futo daga closet din ta jera mashi kan gado, ta mirror yake hangota, har zuwa yanxu mamaki yake yanda ta daina mashi gardama duk abunda yace tayi yi takeyi shi kuma haya son haka, so yake ta dunga mashi stubborness dinann, abun yana sashi shiga shauqi.
“Zan sauka kasa”
Ta furta ahankali, juyowa yayi yana duban kayan dat aje mashi ganin babu innera yasashi cewa “where are the inner?”
Ya kafeta da ido yau ko dan smirking dinnan bayayi, ya wani hade rai, kokarin pissing dinta off kawai yake.
Kamar tasan abunda yake shirin yi wanda batada energy din jayayya dashu as far as bazai fadama kowa abunda ke tsakaninsu ba zata hkura tayi komai ta bishi yanda yake so.
Komawa tayi closet din ta fara budewa daya bayan dayan, yanda kaya suke a shaqe a cikin kowanne drawers da wardrop mamaki abun ke bata, dududu gaba daya ko shekara baiyi ba anan kasar.
Kuma ta lura kaftans sunfi yawa da alamu ya fara sabawa dasu kodan suna mashi kyau sosai.
Tana cikin dube dube ta bude drawer inners dinshi, a jere farare kal, bata tsaya wani dogon tunani ba kawai ta zaro guda daya da vest sannan ta futo.
Tana futowa yanda ta barshi haka ta taddashi zaune, ajiyewa tayi sannan tace “zan iya tafiya?”
“Zoki shafa min” da sauri ta dago ta kalleshi, ya basar kamar baiyi magana ba, “lallai ma, abun nashi ya fara yawa fa” ta fada aranta.
Dagowa yayi ya mata kallo daya wanda yake tafe da sakon ni daban daban.
Cije lebe kawai tayi ta nufi inda yake, yana kallonta cikin mirror yanayinta gaba daya ya sauya zuwa ga bcin rai amma bata da bakin magana.
Man ta dauka ta matsa a hannunta sannan ta mulka shi kafin ta dubeshi itama ta jikin mirror din tace “ina za a shafa?”
“Ina ake shafa mai?” Ya maida mata martani kai tsaye, tayi saurin runtse idanunta hannunta na rawa ta dora shi kan farar fatar gadon bayansa sannan ta fara shafawa ahankali ahankali,kamar bata sonyi, tunda ya ji saukan hannunta akan skin dinshi ya sauke ajiyar zuciya, ga sulbin man gana fatarshi abun saiya hadu biyu, tun tanayi ahanakli harta fara da sauri sauri don allah allah take ta koma cikin gida kar anty rabi ta tambayi dalilin dadewarta, yaci ace ta gama aiki ta koma.
Baimasan ta cire hannunta ba ya shagala sai ji yayi tace na gama.
Juyowa yayi yana fuskantarta sannan ya mata nuni da kirjinshi da gashi ke kwance lub lub kamar na jariri, at that moment pashewa ne kawai batayi ba don takaici, so take kawai tace mashi bazata yi ba amma tana jin tsoron abunda zai biyo baya.
Wani irin malalcin signal ya mata da ido alamun other part din da bata shafa ba, ta hade rai sosai ta dan duka ta deba man ta shafa a hannunta sannan ta matso inda yake tsakankanin kafafunshi ta durkusa don yayi kasa da yawa sannan ta soma shafa mashi,wani irin jan nunfashi yayi har saida taji ya saukeshi akan fuskanta, itako ta cigaba da shafeshi yana sauke ajiyar zuciya, take idanunshi yayi jaa sosai kamar gauta, kujerar ma ji yay kamar bazata daukeshi ba kamar zai fadi, ganin tana kasa kasa don batama san tanayi ba don cikin takaici takeyi badan batada farce bama data karkarceshi, yayi saurin kamo hannayenta biyu, ta kalleshi shima ya bude idanunshi da suke fire, muryanshi ta dishe yace “thats enough”
Yar kwafa tayi ta miqe tsaye ya zare hannunshi daya ya dauka oil ya miqa mata a hannunta, tana ganin oil din tasan na gashi ne, ta karba ta deba cikin sauri ta mulka sannan ta saka yatsunta cikin gashinsa, ta soma yamutsa kan nashi kamar tana mashi massage, baisan sanda ya sanya hannayenshi biyu ba a waist dinta ya janyota sosai, tuni ta dakata da abunda take jin fuskanshi wajen shafaffen cikinta, gaba dayansu sukayi shuru dagashi har ita, ya fara tunanin sanda ta mashi karyan tana da ciki, wallahi ya kaunaci cikin nan dukda babu shi, kuma ya kwallafa rai akanshi, sai yaji dama da gaske akwai cikin, dama zai iya mata cikin ta haifa mashi babies.
“You’re warm” ya furta ahankali, “ waya baki idea din karyan ciki da kikace kina dashi kuma kikace ni na maki”
Dan baya ta soma yi ya sake matsoda ita sannan yace “ya akayi ciki? Tell me how did we do it? Even though kinyi karyansa how did you predict anyi cikin? Did you come up with the idea?”
Tasan inda zancen sa ya dosa ita kuma bata son yi wannan maganar dashi, “please ka sakeni time din school ya kusa”
Yi yayi kamar bai jita ba ya sake cewa, “should we give it a try for real?I mean the baby?”
Dam dam dam gabanta ya bada, itafa bata san irin wannan maganar tana shiga tsakaninsu, gaba daya saitaga taj dinma ya lalalce ya zama wani dan iska iska😂
Cikin sauri ta fuzge kanta tayi baya ko tsayawa kallonsa batayi ba ta fuce daga dakin da sauri.
Tana futa ya bita da kallo harta fuce kafin ya maida dubanshi ga kasanshi, “he can’t believe he’s arouse by her touching, which result him to feel erected lokaci guda, ba tun yanxu ba yasan cewa yarinyar ita kanta weakness point dinshi ce gaba daya.

Misalin wajen karfe 9 da yan mintuna ya futo cikin kayan data dauka mashi, maya ta bishi da mayen kallo, yana karasowa duk suka gaishesa banda sabeeha datayi gumm, maya ta bita da harara, kuma ta lura da hakan arabta tace, “ai gaki gashi nan, ke kika damu da wani zaman gaba mteww”
bude masu mota yayi, sabeeha ta matsa daga wajen seat din baya, yana unlocking ta bude kofar sannan ta shige, su laila suka bita da kallo.
Lallai ma nuna isar yarinyar nan yayi yawa, atunaninsu ko zaiyi magana don da kanshi yace ta dunga zama a gaba sai sukaga akasin haka, baima ce mata komai ba ya kyale, maya tace “chapdijan”
Laila ta dubeta tace “ki zauna kawai a gaban tunda daman nan kikafi so ya hanaki”
Haka dai suka shiga suka zauna kowa yayi shuru babu wanda yayi magana.
Saida sukayi nisa sosai kafin ya soma magana, “whats your course of your” yayi magana yana kallon maya, cikin rawar kai ta fada mashi ya tambayeta cgp dinta tace mashi 2:1
Haka ya tambayi laila itama ta bashi amsa itama ya tambayeta nata cgp din tace mashi 2:2
Ya dubi fatima dake zaune, sai avoiding kallo shi take, “and you??”
Yayi magana a kausashe, tayi kamar batasan da ita yake ba, saida laila tace “fatima dake ake fa”
Sai a lokacin ta dago tace 3:5, gaba dayansu juyowa sukayi suna kallonta banda maya laila tafi kowa mamaki, gaba dayansu duk tafisu kwakwalwa barema maya😂
Maya dai abun ya mata yawa,ay saifa bakin cikinta yafi na da, ta kara kullatar sabeeha.
Shiko taj saida ya bata words of encouragement, don she’s smart.
Maya akayi gumm, taj ko ya dubi inda take zaune yace “you need to work hard on your grades 2:1 is not a good one”
Wani irin embarrassment ne ya lulubeta, tayi yaqe kawai har suka iso bata iya cewa komai ba duk rawar kan nan.
Suna sauka kowacce ta kama hanyarta bare sabeeha datayi gaba don sunada test.

Daga school dinsu bai tsaya ko’ina ba sai wajen da zasu hadu da wanda yasa ya mashi bincike akanta, gaban wajen yayi parking yana kallon gate din mataccen prison din,wayarshi ya daga ya kira mai yin binciken ya shaida mashi ya iso, sai gashi kuwa ya futo daga cikin wannan prison din ya shiga dashi, tunda ya shiga yake yatsinw fuskanshi, wari, bola, datti, ga ginin ya banbaro, kai komai ma akwai a wajen, prisoners din ma kamar mahaukata, gaba daya wajen dai sa a hankali.
Wani dan office mai kyan gani suka shiga inda ogan dake kula da wajen yasa aka kira wanda suke nema.
Wani dan sanda ne ya taho dashi wanda suke nema din gaba dayanshi ka ganshi kamar kwarangwal, ya bushe ya jeme.
Idanunshi daya ma kamar ya lalace don har wani fidda ruwan wari yakeyi.
Kallonshi investigotor din yayi bayan a zaunar dashi sannan yace “ya sunanka”
Ya fada masu, “sunana iliya”
Hoton sabeeha suka nuna mashi ya kalla ya sake kalla sukace “ka santa”
Yayi dariyar yan wii yace “tsakani da allah oga ina zanga wannan a rayiwar nan?”
Tsohon hotonta investigator din ya fidda sannan yace “wannan fa?”
Tuni kawu ya gano wa suke nufi ya jarbi hoton yace “kai wannan yar yayata ce ay, fati”
“Munsan dalilin kawoka da akayi nan saboda satar dakayi kuma baka biya kudin belli ba aka kawo ka nan ko?”
Girgiza kai yayi investigator din ya cigaba, “munyi maka alkawarin fitar dakai dagana indai zaka bamu hadin kai”
Cikin sauri ya girgiza kai yace toh yallabai.
“Mecece alakarka da ita da mahaifiyarta? Sannan ina ne aka haifeta? Waye asalin mahaifinta.
Shuru ya danyi kafin yace “mahaifiyar babarta da babata uwarsu daya ubansu daya, ni kuma kawunta ne, kuma a gaskia lokacin da inna ta dauko ni ta kawo ni nan habuja tun tana karama ne, nadai san babarta tayi aure anan habuja kuma anan aka haifeta, mahaifinta kuma dan taxi ne,shima garinmu daya dashi,”

“Ya alakar ta da mahaifiyarta take”
Rarraba idanu ya somayi yana taoron yin magana amma ganin yan sandan nan akanshi yasa shi cewa “ban gane ba yallabai?”
“Kasan me nake nufi karka bata min lokaci mana, ya alakarsu take?
“A gaskia nidai na taso naga yanda take tsangwamarta, kuma bata barinta tana futa ko’ina, dan ko makaranta dakyar ta bari ta karasa primary,”
“A ganinka me zaisa tayi haka?ko ba yarta bace?”
Shuru kawu yayi yana nazarin yanda yarinyar ke shan wahala wajen hadiza, a gaskia kowa yaga haka zai rantse ba yarta bace.
“ nidai ban taba jin wannan zancen ba, nadai san gaskia yanda ta taso ba haka kowa ya taso ba, don gaskia bata da gata”
Dan nunfasawa investigator yayi, duk wani bayanai da suke san sani sun kasa gano komai, daga kan inda aka haifeta ma.
“Kasan inda aka haifeta?”
“Eh anan habuja ne”
“Zaka iya fada mana wani asibiti ne?”
“Gaskia ban sani ba, kamar yanda na fada maku, tana da shekara biyar inna ta kawoni habuja, don lokacin danazo ma sun tashi daga tsohuwar anguwarsu inda aka haifeta,”
“Zaka iya fada mana inane taohuwar anguwar?”
“Eyy a gwagwalada ne, cikin anguwar rodi”
Da dan wannan bayanan da suka samu daga bakin kawu investigator din ya cigaba da bincike, bayan yayi ma taj bayanin komai sannan sukayi sallama.

Washe gari ta kama saturday, tunda safiyar allah hadiza ta dokama jamila kira,ta tambayeta ya jiki jamila tace da sauqi yauma zataje wajen bokan.
Da haka sukayi sallama hadiza dadi kamar ya karta.
Bangaren su bahijja tun ranar sataje wajen anne sukayi maganar auren hadi da takeso a hada maya da taj bata sake dago da maganar ba amma fa tana kan bakarta.

Hadiza na zaune tana expecting call din jamila maya ta shugo part din, dakin hadiza ta nufa kai tsaye, hadiza kamar ta rungumwta don dadi.
“Ya ake ciki?”
Maya ta tambayeta?
“Karki damu hajiya karama bani na maki alkawari ba yau yau dinann ba sai gobe ba Insha Allah zata bar gidan nan”
“Ay kuwa dai gwara ki san yanda zakiyi inba haka ba wallahi daga ke har ita zan sa a koreki”
“Toh shikann, bayan wannan ma akwai wani abu da kikeso ne? Koma menene ki fada min”
“Me zaki iya min kona fada maki?”
“Zan iya maki komai, kawai ki fadi koma menene”
“Kina tsibbu ne????”
Wata dariya hadiza tayi tace “ah ah ba tsibbu nake ba, amma inada makaman da zan iya yin komai dasu, shiyasa nace ki fada min duk abunda kikeso kamar yankan wuka zakiga komai”
Gyara tsayuwa maya tayi tana nazari kafin tace “wani nakeso amma na kasa samunshi…”
Hadiza ta karashe mata “kinason ya dawo tafin hannunki?”
“Eh…”
“Zan iya sanin waye wannan mai sa’ar?”
“Uncle taj, wannan balaraben”
Tafawa hadiza tayi tana murmuahi tace “kamar kin sameshi ne hajiya karama, indai ina nunfashi sainasa ya biki yana lasar kafafunki”
Ay maya najin haka ta samu waje ta zauna, abunda hadiza keso kenan, “da gaske kike?”
“Wallahi zan iya maki rantsuwa,”
“Toh amma ya avun yake? Me zakiyi?”
“Akwai wani malamin bugu, kina fada mashi damuwarki shikenan, ki bari zakiga example akan wannan yarinyar in takai safiya ba sunana hadiza ba”
Wani irin murmushi maya tayi mai kayatarwa tace “ki fada min ko nawa kikeso, indai zan samu abunda nakeso zan baki kinji, Gaskia kinfi mun mommy, na fada mata inason shi kuma inason na aureshi amma taki yin komai akai,karshe ma cemin tayi wai na hakura dashi, ni kuma wallahi saina mallakeshi, danni aka haifesa wallahi”
“Kingani ko, da tuntuni kinzo kin sameni baki samu wacchan mummyn taki ba ay da tuni an wuce wajen, ke har kulle masu baki duka zanyi duk wanda ya nuna bayason hadin nan,kuma haka zai haukace maki”
“Allah da gaske?, kai nagode” maya ta fada tana rungume hadiza, hadiza baki har wuya, murna kamar ta kasheta.
“Ay babu abunda bazan maki ba hajiya karama, yanda nake son farin cikin kamar nunfashi na”
Maya tayi murmushi tace “daga yau komai ya tsaya tsakaninmu,”
“Toh shiknan,amma ki dawo nan bangaren mana tunda kin saba kawai”
“Mummy bazata yarda ba”
“Kice mata kinfi son nan kawai, ko kinfiso ki zauna achan din? Nan baifi ba mu dunga maganar mu cikin sirri”
“Aiko haka za ayi, bari zanje na fadi mata, nagode hadiza na yarda dake sosai”

Maya na futa hadiza ta soma kulle kullenta, yanxu da farko dai ta kauda sabeeha na biyu kuma faduwa tazo daidai da zama, jini jini ne, ashe ashe mayan ma tana son shi, chap ay yanxu ta samu babbar dama kuwa, kuma dole ta koma bin jigajigan malamanta akan wannan alamari, yanda ta samu yardar maya kuma da alamu zata juyata san ranta idan har ta bata avunda take so ay shikenan, haka nan zata zame mata uwarda bata samu ta zama ba shekara da shekaru.
Wani irin dadi takeji aranta ba kadan ba.
Misalin wajen jarfe shifmda saiga kiran jamila, hadiza na duka tace “akwai matsala hadiza yanxu haka ina hanyar dawowa daga wannan tsiburin kauyen kinji kukan tsintaaye ko?”
Hadiza tace “naji, meysa zaki dawo an samu dacewa ne?”
“Inafa dacewa, wai ya dade da mutuwa wannan tsohon”
Hadiza ta dora hannu a ka “na shiga uku, jamila ya za ayi”
“Kwantar da hankalinki akwai wani chan dana sani, ammafa yafi dayan gaskia, don shi wannan tantirin mugu ne na karshe”
“Toh zakije gobe dan allah?”
“Eh in allah ya kaimu..”
Ditto jamila ta kashe wayar ta dauka remote din tv dinsu ta rage karar tashar data saka, tayi dariya tace “Allah ya kaimu goben hadiza,”

Baiwar allah uta wadda ake wannan shirin tsuburin don a illatata, kwana biyu addua kawai take, kwana take tana sallolin dare, allah baya barci.

The next day ta kama sunday, kusan gaba daya kowa ya hallara dining, nanna, taj ne, harda laila, sabeeha ce ke serving dinsu, tana gamawa nanna tace ta zauna, da har zata qi zama saita zauna kuma tana fuskantarshi don kujerarta na facing tashi.
Laila tayi saurin yima maya message, sai gata kuwa cikin pj, tashi ta kenan daga barci tana gama brush ta fito taji karar notification tama dauka salim ne saitaga laila.
Kannan babu dan kwali anyi packing gashin a tsakiya.
Tunda ta karaso take aikama sabeeha harara, cike da mamaki badan laila tace mata nanna ce tace ta zauna ba ayda ta kora mata, kuma ga taj a wajen bazata iya ba.
“Maya karaso mana zoki zauna” nanna tayi magana tana kallon mayar data shugo kamar a furgice.
“Good morning nanna, good morning uncle taj”
“Morning” nanna ta amsa ta.
Maya taja kujerar kusa da taj din ta zauna.
Itadai sabeeha tunda ta zuba abunci kasa ci tayi, gaba daya she’s so uncomfortable.
“Ci mana fatima”
Nanna tayi magana sabeeha ta danyi yaqe kawai, ta cigaba da chakalar abunci, zungurin kafarta da akayi yasa ta dago tana kallonshi, sai kuma taji yatsanshi na yawo a fatar kafarta, cikin furgice ta kalleshi ya basar kamar baisan tanayi ba, yanda yake tafiyar tsutsar yasa ta soma jin futsari, gashi babu damar tashi, maya na ankare da sabeehar da yanda take kallonshi gashi sai mutsu mutsu take, gashi suna facing juna, tana cikin kallonsu batasan cewa wayarta data dora kan cinyata ba ta sulale ta fadi kasa, wannan yaza ta dan duqa, karaf idanunta ya suaka kan kafafun taj dake yawo ga na sabeeha kamarma yakai wajen cinyanta, wani irin kundumemwn ashariya maya ta antayo tare da mikewa har tana buge kanta, sabeeha tayi saurin tashi tayi baya gabanta na faduwa, maya na kallonta tana kallon maya.
Nanna tace “maya what sort of an insults is this? This is bad table manners dont do that again”
“Nanna wannan yar iskar yarinyar kafarta na gani kan ta uncle taj, she’s trying to flirt with him, daman nace maku yar iska ce, wallahi har maza tana bi”
Nanna ta dubi mayar sannan ta dubi sabeehar tace “maya…wannan wani irin strong allegations ne? Eh?? Kinada hankali kuwa”
Gaba daya kamar mahaukaciya haka maya ta koma, shidai bai dago ba ya cigaba da cin abuncinsa sabeeha ko jikin na bari duk ta furgita.
Maya tayo kanta zata watsa mata mari yanda ta saba ya daka mata tsawa gaba daya sauda wajen ya girgiza, daga kan nanna har bahijja data shugo parlorn gaba daya mamaki ya gama cikasu, ranshi a mugun bace ya dubi maya yace “don’t you dare lay your hands on her”
Kawai sai maya ta fashe da kuka, “na rantse da allah saikin bar gidan nan, daman ba tun yanxu ba take min baqin ciki, ita ba kowan kowa ba, yar aiki ce fa kawai, duk abunda aka mana sai an mata shiyasa take baqin ciki dani, yanxu ma shi da nakeso so take ta kwace shi, ba tun yanxu ba take shiga part dinshi, tana kokarin jan hankalinsa”
Bahijja ta karaso dining din rai a bace tace “whats going on here??”
Nanna dai shuru kawai tayi ta kasa cewa komai, shi da baijin hausa baisan zanjen da take ba,
“Bahijja jata kuje gida please,”
Janta bahijja tayi idanunta sunyi jaa sosai har suka fita kallon sabeeha take da tsana.
Nanna ta dubi sabeeha daketa hawaye tace “jeki abunki”
Sabeeha ta juya ta wuce bedroom shi kuma taj nanna tace ya sameta a daki.
Yana zuwa ta tambayeshi abunda maya tayi magana akai, sai a lokacin yasan kanun zancen, lallai yarinyar nan bata da hankali, ay ba sabeeha kawai ta jefa da adultery allegations ba hardashi, ranshi yayi mugun mugun baci.
Nanna tace “she will stop whatever shes doing a part dinka from now on to avoid any problems”
Take ya kalli nanna yace “no nanna, she will continue her job, i will not tolerate such nonsense behavior from this girl,”
Nanna dai tayi shuru batace komai ba, daga maganganun da naya tayi ta fuskanci kamar son taj takeyi.

Tunda suka shugo part dinsu ta bi ta tayarma da bahijja hankali, ta ind atake futa ba tanan take shiga ba, gaba daya sai bahijjar taji ta tsani sabeehar wallahi, kuma ta yarda da maganganun mayar tunda tagani da idanunta itama, yanda yarinyar ke yawan zuwa part dinshi yayi yawa kuma wallahi bazata taba bari yar hadiza ta shugo gidan nan ba su tsaya a matsayinsu da tanada yanda zatayi ay da ta koresu daga uwar har yar gaba daya.
Har yau bata iya manta abunda hadiza ta mata ba, har yau kuma dashi take ganinta, shiyasa kwata kwata hadizar bata taba yarda su hada ido.

Chan bangaren jamila haka ta shirga hadiza da zancen ta futo fa, kuka tana isowa wajen malamin zata fada mata.
Drop hadiza ta hau direct mai ac ma kuwa daga dutsen habuja zuwa nan maitama, taci kwalliya abunta fess fess, hardasu jambaki, sannan ta aza chewing gum a bakinta, ta futo asalin jamila bala’i yanda ake kiranta a da, sai wani qas qas takeyi, suna isowa bakin gate ta danyi yan daba runta na jikakkun ya bariki ta samu ta shige, drop bai tsaya da ita ba sai daidai gidan, ta biyashi kudinshi sannan ta sauko, tana saukowa ta dubi estate din gaba daya kafin ta maida dubanta ga apartments din santura’ki’s…..”gani nan tafe hadiza, nazo maki da gagarumar tsaraba….


Toh fa, me jamila ke shirin yi? Lokaci yayi ne????? Ku biyoni don jin yanda zata kaya….


MATAR TAJ (destined with you)
   Written by 
          Queenmarh

Book2 
PAID
Chapter 52 · 0% Book details