← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 30 OF 66

Part dinsu ya koma yana shiga yaga wannan mara kunyar, da kallon banza ta bishi, ya dauke kanshi yana mamakin yarinyar sosai.

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 5 min read

Yanajinsu suna maganar shiga part din anne.

Atare suka fito suka nufi part din anne, saman suka fara zuwa suka gaisheta sannan suka wuce wajen nanna, dake tafi sakewa da kowa sosai ga faran faran wannan yasa suka dade sosai wajenta kafin su sauko, laila tace “bari na dauko mana cake din da nanna tace mu dauka”
Ta tashi ta wuce kitchen, tana shugowa babu kowa sai sabeeha data juya mata baya tana wanke few cups, “please akwai cake a fridge ki saka min a saucer guda biyu ina parlor”
Tana fadin haka ta juya zuwa parlor, sabeeha data tabbatar ita kadaice kitchen din babu yanda ta iya haka ta dauka saucer ta yanka cake din ta saka guda biyu sannan tasa fork ta aje kan tray ta fito,
Hanyar parlorn tabi tana tsoron karta bata, allah ya taimaka ta hango yanmata biyu zaune ga muryar dayar data mata magana na tashi alamun ma waya take.
Karasowa tayi har parlor maya na danna waya ita kuma laila na waya, har ta aje gabansu laila
Ta mata alamu da hannu ta miqo mata nata ta miqa mata tace “thanks tare da mata murmushi tana mamaki ko wacece wannan din don bata taba ganinta ba, harta juya maya da bata kalleta ba tace “ubanwa kika ajema wannan?”
Itafa maya batama yan aiki da sauki, shiyasa duk yan aikin suke cewa bata da mutunci laila ko babu ruwanta.
Takowa sabeeha tayi ta dauka nata ta karaso inda take ta miqa mata sai a lokacin maya ta dago ta kalleta, tashin farko ta gane ko wacece, saitayi kamar zata karba plate din bata karba ba ya fadi kasa ya fashe tass a kas, a zafafe ta miqe ta wanke ta da mari for the second time, batasan ko ita wacece ba.
“Ke wace iriyar donkey ke, illiterate stupid human, haka ake serving a kauyenku? Why are they bunch of useless people in this house huhhh get the fuck out of my way,”
Harta juya ta sake tsaidata, ran sabeeha ya baci sosai ta danne “go and get another one rubbish”
Juyawa sabeeha tayi laila dake waya ta dubi maya ta girgiza mata kai itako maya ko ajikinta.
Wani sabeeha ta sake kawowa har gaban maya, wallahi ko kallonta batayi balle tasa ran zata karba data “ko na aje maki a kasa?”
Wani irin banzan kallo ta mata tare da miqa hannu zata karba, sabeeha ta ankare da abunda tayi dazu take son ta sakeyi, kuma bazata bata dama ba wannan yasa itama ta miqa hannunta daidai jikin maya din tana aje mata plate din a hannu maya ta sakeshi unknowly zai zuba jikinta ya bata mata jikinta gaba daya, icing din.
Wani irin kara tayi ta miqe tsaye tana mai duban sabeehar harta daga hannu zata wanke ta da mari sabeeha tayi baya abun ya kara kular da maya, taji lokaci guda ta tsani sabeeha kamar ranta, laila tayi saurin kace wayarta, sabeeha bata ankara ba ta shiyo ihun hadiza, “keeeeeeeeee” wallahi saida ta tsorata,ashe ta dade a tsaye tana kallon abunda ke faruwa run dazu, idanun ta sunyi jaa sosai kamar wadda tayi kuka, nan har inda maya ke tsaye ta tako ta dubi sabeeha tace “dan ubanki sa’ar kice, kizo har cikin gidansu tana magana kina tsaye?kuma tasa kiyi mata abu kika zuba mata a jiki” ji kake tasssa marin da maya batayi mata ba hadiza ta sauke mata tace “tsugunna ki bata hakuri naceeee!!!!” Ta daka mata tsawa, hawaye na sauka idanun sabeeha ta duqa kafarta na karkarwa tace “kiyi hkuri bazan sake ba”
Murmyushi maya tayi, wannan matar ta burgeta sosai, dukda bata san ko ita wacece ba haka ake dealing da yan aiki waenda basuda kunya samm.
“Dan allah kiyi hkuri kinji, laifina ne da ban nuna mata banbancin na gida dana waje ba”
“Ohh so kece maman ta kenan, bunch of weird people every where, the next time kika kara ganina ki tabbatar kin chanza hanya, rubbish”
Tana fadin haka ta wuce kamar zata bangaje sabeehar da hadizar ma gaba daya, maya ta girgiza kai ta duqa ta kamo sabeeha tace “I’m very sorry dear”
Murmushin yaqe kawai sabeeha ta mata ta juya ta bi bayan maya, hadiza ta dubi sabeeha “tashiiiii”
Sabeeha da jikinta har na neman yin rawa ta miqe tabi bayan hadiza.

Wani irin janyota hadiza tayi ta kusa gwarata da bango tace “so kike ki hawo min bala’i? So kike a koremu daga gidan? Ke zaki ciyar damu? Wannan talaucin da muka baroshi kikeso mu koma? To wallahi zan jaa maki warning, daga yau hanyar da sukabi kikabi sai ranki yayi mugun baci, ko cikin idanunta kika sake kalla ban yafe maki ba, babu ruwanki da harkarsu, ke ba kowa bace face yar aikin gidansu,yauwa”
Tana fadi haka ta futa a fusace sabeeha ta zauna zaman dirshen sai hawaye.

Anne data fito tun ihun maya na farko tundadaga sama take kallon duk abunda ya wakana a kasan.

Dakinta ta koma tayi dialing pa dinta yana dagawa ta soma magana “inason ka nema min final year entry admission a baze university as soon as possible”
“Yes ma’am” ya amsata.

Saudi…
Taj na barin wajen mutallib yabi motar shi da kallo, jiki a mace ya juya wajen tashi motar yana kokarin shiga wata baqar mota van ta tsaya, wasu mutane su biyu suka fito suna sanye da baqaqen kaya da facing cap, daya ya tsaya ta bayan mutallib yace “don’t move” chak mutallib ya tsaya jin bindiga a bayanshi, “turn around”
Nan ya jiyo a hankali suka sashi cikin motar suka taci dashi, innalillahi wa inna ilaihi rajiu’un
Ko su waye waennan suka dauke mutallib allah kadai masanin gaibu ya Allah….


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 30 · 0% Book details