← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 39 OF 66

Chapter 92-93

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 34 min read

After an hour..
Gaba daya jugum sukayi a zaune, fadila da hamad na zaune kusa da anne while ya sameer yana tsaye yana safa da marwa tsakanin wajen.
Suna cikin wannan yanayi doctor barau ya futo, lokacin wajen misalin karfe 10 ta gifta ana neman sha daya,inda anne ke zaune ya nufa suka miqe tsaye.
“Alhamdulillah hajiya,…an kara mata jini and she’s stable now zaku iya ganinta, amma agaskia bazamu sallameta yau ba sai zuwa gobe”
Janjina kai anne tayi tare da sauke ajiyar zuciya suka dunguma doctor yayi masu jagora zuwa dakin da aka kwantar da ita.
Anty fadila na rike da hannun anne don jiri jiri takeji,kai yau sunga karamin tashin hankali mai tafe da abun alajabi da mamaki.
Suna shiga daga ciki suka taddata kwance, harda oxygen, ga jinin da aka saka mata a hannu, gaba daya lokaci guda harta fada sosai tayi fayau abun tausayi.
Zagayeta sukayi, gaba daya tausayinta ya dabaibaye su.
Su anty fadila har zuwa lokacin shock baibarsu ba, dayan hannunta da babu canula a jiki anne ta kama jiki a mace,wani irin tausayin kanwar tata ya gama shiganta, dole ta shiga shock, abunda ta dade tana dakonshi aranta, tana jiran baiyya a gabanta, lokaci guda unexpectedly sai gashi.

Chan kasan zuciyarta tanajin wani irin farın ciki mara misaltuwa, sai a lokacin ta tuna da taj ta dubi doctor tace “shi yana ina?”
“Yana lab, he insisted on giving enough”
“Thank you doctor”
Sameer ya rakashi kofa ya futa kafin ya dawo dakin, gaba daya kowa yayi shuru kamar ruwa yaci su, anty fadila ta kalli sameer suka hada idanu har zuwa lokacin kansu a kulle yake da wannan al’amari.
Muryar anne ce tasa suka maida dubansu gareta.
“Kai sameer Ku koma gida zan zauna da ita”
Anty fadila tayi saurin cewa “ah ah anne, ku koma ni zan zauna da ita, tunda kinga yanayinki da kafa”
“Ah ah nace zan zauna ku koma gida dare yayi gobe da safe saiku dawo”
Ya sameer kamar bazaice komai ba ganin yanda tayi insisting, cikin natsuwa da lallabawa yace “anne kiyi hkuri fadilan ta zauna bazai yuwu mu tafi mu barku ku kadai ba”
“Nace zan zauna da yar uwata, bana son jayayya ku tafi gobe da safe saiku dawo”
Sun san halinta in tayi magana bata chanzawa dole suka hkura, harma hamad qin yarda tayi ya zauna tasa suka tafi gaba dayansu tambayoyi qunshe a zuciyoyunsu.
Suna tafiya anne ta dubi nanna dake kwance idanunta a rufe ga alamun hawaye daya bushe a gefen idanunta, babu wanda zai fadi irin halin da nanna ta shiga shekarun baya har zuwa yanxu kamar anne, saidai ma ta bada labari don she stand by her tare sukayi sharing ko wanne irin pain tun a wanchan lokacin don ita ta tsaya mata,tana masifar son yar uwarta ba kadan ba,hajar macece kamila, mai hkuri, mai faran faran, mai boye quncin ta da murmushi, tasha wahala tun kuruciyarta,rabuwar d’a da mahaifa ba abu ne mai sauqi ba musamman a situation irin nata.


Tsakanin yan uwa sai allah, anne ji take kamar ta rage mata zafin da takeji aranta.
Tana cikin wannan tunanin akayi knocking kofar, sannan ya shugo ahankali ya kasa motsawa daga bakin kofar.
Juyowa anne tayi ta dubeshi, take zuciyarta ta karaya, tabbas zuciyarta bata mata karya ba game dashi, daga ranar data sanya idanunta akanshi, take taji wani irin connection tsakaninsu mai karfi tana jinshi kamar jininta.
Ga kamannin hajar nan a fuskarshi kamar an tsaga kara, kamannin harya baci sosai.
Hamdala anne tayi tare da godiya ga allah daya nuna mata wannan rana.
Hannu ta miqa mashi alamun ya karaso jiki a mace ya soma takowa kamar an zare mashi laka.
Gaba daya yayi wani irin jaa, jijiyoyin kanshi sun futo rudu rudu, idanunshi ya sauya kamar garwashi,shi kanshi he can’t believe yau shine agaban mahaifiyarshi, Allah yayi reuniting dinsu ta fuskar da bai taba tsammani ba.
Guilt ya hanashi kallon fuskarta, wani irin heavy abu yakeji a kirjinshi mai nauyi.
“Hajara ki tashi, ga danki ya bayyna a gabanki, you have been waiting for this moment all these years”
Nanna data farka tun dazu ta kasa bude idanunta saboda wani radadi da takeji aranta.
Tabbas ba mafarki take ba zahiri ne, amma ta kasa gasgata hakan.
Anne tun dazu ta lurada ta farka amma taqi bude idanunta kuma taqi cewa komai sai hawaye kawai dake sauka gefen idanunta batace mata uppan ba sai yanxu daya shugo, matsawa gefe anne tayi don ta bashi waje ya karasa kusa da ita.
Tun kafin ya karaso nanna ta bude idanunta masu dauke da tsantsanr bacin rai akanshi ,ta fincike oxygen din dake kan hancinta idanunta kamar gauta, ta fara kokarin tashi zaune ni kaina na kasa fuskantar yanayin ta.
“Karka sake ka tako nan” tayi magana cikin larabci babu wasa a fuskanta hawaye na bin kuncinta.
Dam gabanshi ya bada, da zaa tsaga zuciyarshi a wannan lokaci za a ga yanda he’s broken into pieces.
Kallon anne dake kallonta tayi bakinta na karkarwa tace “banida da a duniyar nan anne, na sallamashi tun shekaru talatin da suka wuce”
Saida gaban anne ya fadi sosai don tabbas cikin bacin rai take magana.
“Haba hajara wannan wani irin furuci ne? Laifinsa ne? Ko laifin iyayensa?”
“Yanda ya mance yana da uwa a duniya, na dade da mancewa inada da wani wanda nakeda alaqa dashi”
Saurin rintse idanunshi yayi dukda baiji abunda ta fada ba don da hausa sukayi magana, amma jikinshi na gaya mashi duk wani furucinta.
“Hajara!!!!!!! Danki ne fa? You have waiting for him over the years”
‎“اغرب عن عيني”(get out of my sight)
(Bana buqatar ganinka)أنا لا أريد أن أراك مرة أخرى
Anne sai ta zama yar kallo, ganin yanda nanna ke magana cikin bacin rai, zan iya cewa bata taba ganinta a wannan yanayi ba sai yau.

A natse ya soma yin baya jikinsa ya mace gaba daya ya futa daga dakin, nanna ta fashe da kuka sosai kamar ranta zai futa.
Kama hannunta anne tayi ta riqe gam ta rungumota jikinta ita kanta hawayen takeyi sosai.
“Hajara kin barshi yanada shekaru bakwai kachal wajen mahaifinsa without second thought saboda laifin mahaifinsa,shin kinsan a wani hali ya taso achan din? Kinsan irin rayuwar da yayi acahn din? yanxu ya dawo gareki why are you pushing him? Fatanki fa kenan gaba daya shekarun nan?”
Rikota sosai nanna tayi cikin shesheqa tace
“Anne na barshi yanada kananun shekaru wajen mahaifinsa amma bayan rasuwar mahaifinsa daidai da second daya banyi abandoning dinshi ba, ina tare dashi a koda yaushe,i try as much as possible to be with him amma sukaqi bani dama, ya nuna baya buqatata a rayuwarshi, ya cire uwarda ta tsugunna ta haifeshi daga rayuwarshi anne saboda banida mahimmaci ko saboda turbar da aka dorashi, Duk trip din da nake zuwa england saboda shi ne, da taimakon qanin mahaifinsa da shima ya kasa samun yardarshi, bai yarda da kowa ba sai kanshi, daidai da rana daya bai taba bani damar kusanci dashi ba, ya rigada ya yarjema kanshi bashida uwa tun tuni, sai yanxu zaizo gareki?”
Tana karashewa ta fashe da kuka cikin kunci da zafin rai, anne bata sake cewa komai ba don kamar tana provoking dinta ne, ta barta tayi pouring heart dinta ko zata ji sauqin abunda takeji.

Daga chan waje bayan futarshi yana jiyo kukanta don ko daga kafa baiyiba, bai taba realizing actions dunshi a baya has made a damage on him and his loved ones ba sai yanxu, idanunshi sun rufe baya ji baya gani a lokacin, bai taba nadama ba kamar yanxu, he’s like a stranger to his own birth mother? Mahaifiyarshi? What has he done? Take ya fara tuna yanda khaal ke tunatar dashi ita tun lokacin da yake karatu a england, ko khaal Dinma baya bashi dama don saiyazo england sau nawa amma yaqi yarda su hadu, gaba daya ya cire kowa daga rayuwarshi, invanda hidaya daya yarda da ita kuma ya yarda da magnagnunta, ya hau tirbar da ta dorashi akai, ya mance da yanada uwa mai kukan rashinsa,wallahi yanxu bazai iya tuna happy memory da yake dashi da mahaifiyarsa ba, tun yana karami.

Kai tsakanin da, da uwa sai Allah, ita ke kuka amma shi kejin radadi a zuciyarshi.
Kafafunshi kamar bazasu daukeshi ba, how can he explain him self? He didn’t deserve her at all, why did he cause her so much pain?.mahaifiya ba abun wasa ba, kamar an mashi tsafi an shiga tsakaninshi da ita.

Yakai wajen awa guda a gaban dakin har doctor ya shiga dakin sannan ya futo tare da sanar dashi anne tace ya shiga, an mata allurar barci.

Kasa shiga yayi don Ya dade hannunshi jikin handle din kofar ya kasa budewa saida aka budo daga ciki.
Anne ce kamar tasan yana tsaye a wajen kofar, tana budewa yayi saurin kai idanunshi cikin dakin ya hangota kwance, anne bata rife kofar ba ta barshi ya kalleta da kyau kafin ta karo kofar sannan taja hannunshi suka zauna a kujerun dake wajen.
Wuraren wajen karfe daya na dare wajen shuru babu hayaniya.
Tunda suka zauna anne ke kallonshi, tausayinsa ma ita takeji sosai, don harga Allah shima ba a san irin rayuwar da yayi ba achan, kuma ko ba a fada mata ba tasan yazo wajen mahaifiyarshi ne adaidai lokacin dayafi kowa buqatarta.
“Tajudeen!!”
Ta kira sunansa a hankali.
Kasa dagowa yayi ya kalleta, ganin haka ya sata cewa “you must be in so much pain kamar yanda mahaifiyarka take ciki ayanxu, it breaks my heart to witness this moment, tabbas ko baka fada min ba ka zo kasar nan ne saboda mahaifiyarka, don’t take her words to your heart, duk abunda ta fada baikai zuciyarta ba ni nasan hajara, gaba daya shekarun nan kana cikin zuciyarta, yama za ayi uwa tayi abandoning danta?”
“I’m so sorry, I’m so sorry for the pain I’ve caused her, ni nayi abandoning din mahaifiyata, ninayi neglecting dinta na mance banida kamarta a duniya,i was so stupid for thinking tayi abandoning dina kuma bata buqatata a rayiwarta shiyasa ta tafi ta barni”

“Babu wanda zai iya maida hannun agogo baya, duk abunda ya faru ya rugada ya faru, lets focus on the future, fushin hajara na kankanin lokaci ne, she can never be upset with you saboda kaine babbar kyautar da allah yayi mata, hoton ka kadai take gani taji sanyi a zuciyarta, daidai da second daya bata taba abandoning dinka ba,“

Wani irin sanyi yaji a zuciyarshi, anne tace “allah mai yanda yaso, shi kadai yasan dalilin daya hadani dakai, ashe kai jinina ne, kuma ni zanyi sanadiyar uniting dinka da mahaifiyarka, daga ranar dana sanyaka idanuna naji ajikina inada alqa dakai, your calmness and kindest heart reminds me of hajara,allah yayi maka albarka tajudeen”
Haka anne ta dunga janshi a jiki dan ya dan samu sauqin avunda yake ji, wallahi ba karamin tausayi ya bata ba, batayi tunanin hajara zata nuna fushin ganinsa ba ita dake begen ganinsa dukda bata fada, duk wani rashin lpy da take da hawan jinin data samu duk ta dalilin damuwa akanshi ne, harta fidda rabon sake amsa sunan mahaifiya a duniya, don wannan kadai yasa ta kasa aure.

Achan gida fa babu wanda ya runtsa, daga sameer har anty fadila harma da hamad,yanda sukaga rana haka sukaga dare.
Koda anty mubina ta tambayi ya sameer meya faru don a dakinta yake kasa ce mata komai yayi sai fada mata dayayi nanna batada lafiya an kaita asibiti.

Bangaren anty fadila kuwa kasa hakura tayi a daren ta soma kiran bahijja dake su safiya ne achan england wannan yasa ta sameta a waya, tana cikin wayar akayi knocking tare da sallama.

“Come in” daga ciki akayi magana bayan knocking da akayi.
Laila ta shugo ganin mamanta na waya yasa tace “mummy please! Wallahi inada presentation gobe da safe i need my phone”

Dagowa fadila tayi dukda tasan dalilin shugowar nata “da karfe sha biyun dare ne zaki buqaci waya? Are you sick?what are you even doing at this hour bakiyi barci ba?”
“Muna prepping general presentation ne ni da maya”
Nuni tayi mata da kofa “kije kuyi da laptop dinki, itama zanzo na amshi tata wayar idan shirman banzq zaku dungayi now get out of my sight bfr i loose my patience”

Jiki a mace laila juyawa ta futa sumi sumi kamar munafuka.
“Me take nema ne?” Daga cikin wayar akayi magana.
“Wayanta na kwace fa shine take wannan susunne kan”
Dariya bahijja tayi kafin tace “Laifin me tayi ne?”
“Na shiga bedroom dinta jiya around 3am kamar ance na leka ciki na tadda yarinyar nan tana tadi a waya, nakai wajen minti biyar a tsaye yarinyar nan batasan ina tsaye ba”
Dariya sosai bahijja tayi kafin tace “haba fadila, takai ace tanayi ay, you can’t stop them”
“Amma karfe ukun dare bahijja? Harta iya soyayyar dare sannan har na tsaya gabanta batasan ina tsaye ba”
“Toh ay shikenan, ya kuke”
“Lafiya Lau Alhamdulillah, shekara kusan biyu kenan bahijja rabonki da gida samunku ma a waya yayi wuya”
“Wallahi inason zuwa fadila babu yanda na iya ne, abubuwa sunyi yawa ga stress ga aiki, saida na dauka bedrest kwanaki”
“Hmm kodai abun ne ya samu?” Fadila ta fada da gyatsine, sanin me take nufi yasa bahijja cewa
“Yanxu idan nace maki inada ciki saiki yarda? At this age?”
“Toh abu na Allah, daman gashi daga maya shuru, kun dauki rayuwar turawa 1 is enough”
“Hmm fadila bazaki gane bane, dukda yanayin aikina wallahi we tried countless of times allah ne bai kawo ba, and i think that’s for the best, don idan da na sake haihuwa bansan ya zanyi ba saidai nabar aikin, I’m still having the guilt of not training maya yanda ya kamata”

“Allah ya shiryar mana su shirin addinin musulunci”
“Ameen” bahijja ta amsata.
Dan nunfasa anty fadila tayi kafin ta ce “dazu muka dawo daga asibiti fa”
“Subhanallahi meya faru? Waye bashida lafiya”
“Nanna!!”
“Nanna?? Meya sameta”
“Ba wannnan ba ma dai tukunna tambayar dana kira na maki kenan, wai shin daman nanna nada da? Auren da akace tayi a saudi?”
Murmushi bahijja dake zaune akan kujeran office dinta tayi, duk cikin yayan anne itace the most closest to nanna tun suna kanana shiyasa duk wani abu daya shafi nanna itace a farko, waya ko saitayi waya da nanna batayi da anne ba, inka gansu saika rantse nanna ta haifeta ba anne ba
“Kwarai kuwa, nanna nada da, danta daya tilo, “

“Yanxu all this while nanna nada da? Danta na cikinta?” anty fadila tayi magana kafin ta cigaba, “amma ya akayi mu bamu taba sani ba? Ban taba jin tayi maganar ba? Ko sau daya”

“Kudai baku sani ba, amma ni tun tuni na sani, hmm ay fadila bansan wace iriyar zuciya allah ya bama nanna ba, shes the most peaceful yet sweetest person on earth, bazaki taba ganin damuwa akan fuskarta ba, she’s always happy while deep down she’s hurt, kinga all those years kafin muyi aure? Wallahi ni kadai nasan halin da nanna ke ciki, zaki yarda idan na fada maki saboda rashin danta yasa bata kara aure ba?“

“Allahu akbar, allah mai iko, wallahi ban taba tunanin nanna nada jininta ba a doran kasa, Toh amma wannan wani dalili ne yasa rabuwar da da uwa haka? Shekara nawa kenan bahijja?”

“Wallahi ni kaina bata taba fada min dalilin nan ba, fadila i think ta barshi a saudi yanada shekaru bakwai, yanxu akalla zaikai talatin da wani abun if I’m not mistaken, don har hotonshi tana nunamin, sometimes idan tayi missing dinshi zaki ganta a daki a zaune tana hawaye, kinsan I’m always her favorite ni kadai take bama labari, alokacin rokona bai wuce allah yasa idan ya taso ya mallaki hankalinshi ya nemi mahaifiyarshi ba, wallahi har yanxu ina rokon allah yasa zasu gana wata rana.”

“Allah ya kawo ranar bahijja don…”

Dip call din ya katse, cikin saurin fadila ta sake redialing wayar bai shiga ba haka ta aje wayar tayi jugum.

Laila na shiga bedroom dinta ta afka kan gado jiki a mace, maya dake duqunqune cikin duvet tashinta kenan tun wajen magrib gudun kar anne tace dole ta sauko ayi dinner yas ata gudo part dinsu laila, tunda ta fara barci bata farka ba sai yanxu dalilin syrup din data sha dayawa.

Kallonta laila tayi kafin tayi tsuka tace “ke kuma sai yanxu zaki tashi? Wannan wani irin barci ne kamar na mutuwa?”
Miqa maya tayi kafin tayi banza da ita ta wuce bathroom ta watso ruwa dannan ta futo ta saka pajamas din laila.
Laila na zaune ta doke tagumi tana kallon laptop dinta dole dashi zatayi presentation din babu yanda ta iya.
“Please kisa maid dinku ta kawo min dinner mana”
Zaro ido laila tayi ta kalleta daga sama har kasa tace?”at this hour zan tasheta ta kawo maki dinner? Kinason mami taci ubana kenan?”
“Ban gane ba? Sbd yar aiki? Ba aikinta kenan ba?At any given time dole tayi aikinta”
“Banda nan part din maya, idan yunwa kikeji ki sauka kasa ki nemi abunda zakici,”


Miqewa tayi rai a bace zata fita laila tayi saurin jan hannunta tace “badai tasota zakiyi ba?”
“Kina tunanin ni zan nemama kaina dinner?”
Saurin dakatar da ita laila tayi jikinta har rawa yake tsabar tsoro tace “kinga tsaya bari na kawo maki karki jawo min fada yanxun nan, daman ina lallabawa a bani wayana”
Tana kaiwa nan ta futa daga bedroom din nasu.

Hawa kan gado maya tayi tare da nade kafarta ta dauka wayarta tana latsa, gaba daya saitaji abunci ya fita ranta, yanxu da tana main house da tuni hadiza ta dafo mata duk abunda takeso, koda karfe hudu dare ne ta kirata waya zata tashi, shiyasa yanxu duk wani hidimanta na hannun hadiza.
Shugowar laila yasa ta dago ta kalleta rike da tray ta dora plate da cup of chilled juice ta aje mata.
“Gashi nan”
Tabe baki maya tayi sannan ta jawo plate din ta soma ci tana latsa waya.
“Ke ban baki labari ba?” Laila tayi magana tana saurin matsowa kusa da mayar.
“Menene?”
“, ke kinga guest din anne daya zo yau kuwa? Ya Allah, wallahil azeem kamar ba mutun ba, he’s so charming and charismatic kai ya ilahi”
“Wai saboda wani zaizo ne daman akayi family dinner? Mtew gwara da banie ba da raina saiya baci, na dauka ko wasu family friends ne zasu zo”
“Kai maya you missed this opportunity, inaga business partner dinsu ne don he looks so filty rich, ke kin ganshi balarabe ne don baya hausa sai turanci, I couldn’t take my eyes off him wallahi”

Tabe baki maya ta sakeyi ta ture abuncin, take taj ya fado mata arai, da anyi maganar namiji mai kyau sai ta fara jin haushi don da kyar zata iya yin arba da namijin da zatace ya hadu kamar yanda taj ya hadu, he’s just ten outta ten, kai yafita dqban cikin jerin maza.

“Har kin koshi?”
“I don’t like the taste” ta fada ta kallon cikin idanun laila
“Mami ce fa tayi? Kedai wallahi kinada problem ba a taba iya maki, hows this meal tasteless?”
kallon native rice din dayaji kifi da nama zuku zuku dake cikin plate din laila tayi, “babu kyau wasting abunci ki cinye please”
“Banci, ki bama househelp Dinku ta karashe”
Girgiza kai kawai laila tayi taja plate din ta soma ci, “leftover din zakici?”
“Toh menene a ciki?”
“Nace ki kaima house help dinku ta cinye sauran”
Girgizq kai kawai laila tayi, tana mamakin halin laila na kyamatar yan aiki, babu abun kaskanci a wajenta kamar masu aiki, shiyas atake tausayin sabeeha sosai, bata taking chances wajen bullying dinta da disgracing dinta a ko ina,


Washe gari da safe gaba daya gidan kowa yaji batun rashin lafiyar nanna da kwantar da ita da akayi a asibiti, duk sai kowa ya damu sosai harma da yan aikin gida,musamman sabeeha, don macece mai kamala da faran faran da kowa ga kyauta ga mutunci sosai sai fatan samun lafiya kawai suke mata.
Tun wajen karfe bakwai hamad ya tashi ya wuce part dun anne.
Rabi dake kula da bangaren nata yasa ta dauko mashi duk wani abun amfani da zasu buqata sannan suka bishi dasu mota ya shiga.
Around 7:30 ya iso asibitin ko jiran mamanshi baiyi ba, ya fito cikin natsuwa ya nufi asibitin.
Yana shugowa daidai wajen dakin nata ya hango taj daya dafe kanshi shi daya zaune, ko kallon inda yake hamad baiba tubda ya dauke idanunshi harya shiga cikin dakin da sallama.
Anne ya hango kan abun sallah, bata tashi ba tunda tayi sallah ta dan nemi runtsawa a wajen.
“Anne…good morning ya mai jiki” ya fada ahankali gudun kar mara lafiya ta tashi.
“Morning dear, ya kuke kowa da kowa?”
“Duk suna lafiya” daidai nan ya karaso inda take ya zquna kan couch.
“Zuwan safiya haka hamad? Baka huta ba”
“Bazan iya hutawa ba ay tunanin halin da ku ke ciki bazqi barni ba, i missed you”
Shiyasa cikin jikokinta take bala’in son hamad ba kadan ba don ya fita daban.
“Toh ay gashi ka ganni saika zo ka tafi ko”
“Please anne karkice na tafi I won’t”
“Toh shikenan ay, wake son zaman asibiti allah na tuba inba dole ba.
Murmusawa yayi tare da aje mata bag din daya shugo dashi.
Anne tayi saurin kallonshi tace:
“Kaga tajudeen kuwa, tunda ya tafi sallah bai dawo ba”
Shuru hamad ya danyi kamar bazaiyi magana ba chan yace “na ganshi zqune a reception kafin na shugo”
“Jeka ce mashi ya shago mana, ko rintsawa yaronnan baiyi ba wallahi”
Kamar bazai tashi ba haka ya miqe tsaye ya nufi wajen kofar sannan ya futa.
Yanda yabar taj din haka ya taddashi a zaune ya dafe kanshi.
Rasa me zaice mashi hamad yayi, sai kawai yace
“Barka da safiya”
Dagowa taj yayi ya kalleshi kafin ya sauke idanunshi ya gyara zamanshi ya amsa shi babu yabo ba fallasa.
“Bismillah!!”
Ya mashi nuni da kofa, sannan ya juya ya barshi zaune.
Miqewa yayi shima a natse yabi bayan hamad din jiki a mace, koda ya shugo ita din ya fara kai idanunshi gareta, ganin yanda take barci peacefully yasa shi sauke ajiyar zuciya.
Tashi anne tayi ta dubeshi tace: “zan wuce gida akwai magunguna na daya kamata na sha, ka zauna da ita okay”
“Ya za a barshi shi kadai da…”
Dakatar hamad anne tayi tace “wuce ka kaini gida”
Tana fadin haka ko kofar magana bata bashi Damar yiba suka fice.

Suna fita anne ta dubi hamad tace “babu wanda ya kamata ya zauna da ita kamarshi, yafi kowa kusanci da ita saboda mahaifiyarsa ce”
Kalmar mahaifiyarsa saida hamad ya sake nanata ta zuciyarshi, shifa bai taba jin anyi maganar nanna tana da da ba,yadai san cewa ta taba aure sau daya kuma bata sakeyin wani ba bayanshi.He’s so curious da son jin wannan zance .
Bayan tafiyarsu ya zauna kan couch bini bini yake dagowa ya kalleta ya kasa samun natsuwa, ga tausayinta ya dameshi, tunowa dq ta dalilinshi take kwance ayanxu.
Kasa hakura yayi ya karaso inda take,kamar anne tasan he needs time with her, ya zauna kujerar dake gwfen gadon mara lafiya, samun kanshi yayi da kamo hannunta kamar wanda kejin tsoron tabata, ya riko hannun gam yana jin dumin mahaifiyarsa, wallahi irin wannan yanayin daban ne bazai misaltu ba.
Ya sumbaci hannunta ahankali ya soma magana yandq bazai tashe ba “aftaqiduk kthyran ya oummi, nayi kewarki sosai, i was blinded into thinking my life was complete without you, it was never, saima juyawa da tayi into miserable life, i had a traumatic days and night without you oummi, bansan dadin uwa ba,bansan yanda zan kalli cikin idanunki ba, i wish i could take out your pains that i caused you ya oummi, duk da an samin tunanin kinyi abandoning dina bana iya barcin kirki bana iya cin abuncin kirki ba tare da tunanin ki ba, shin a wani hali kike? Meke damunki? Meysa kika barni Baki waiwayeni ba? I was selfish all this time banyi tunanin ni wani hali na jefaki ba, ki yafeni ya oummi” yana magana amma baisan sanda ya soma jin lema lema ba akan fuskanshi, kuka da wuya ya sauka akan idanunshi amma akan mahaifiyarshi ya kasa controlling kanshi don she’s his weakness
Duk maganganun nan nashi a kunneta don tunda ya riko hannunta ta farka daga barci amma taqi nuna alamun haka, ka dumin hawayenshi na sauka kan hannunta daya rike she can feel how yanda yake trembling, ya Allah, zuciyarta na mata wani irin zafi ta kasa hana kanta hawayen dake sauko mata dukda bai lura ba. Abu kamar a mafarki haka takejin komai

Misalin wajen karfe goma da rabi sai gasu sun dawo asibitin,hamad, anty fadila, ya sameer.
Da sallama suka shigo dakin, yana zaune kan couch ya dafe kanshi da hannu daya,ya amsa sallamarsu sannan ya tashi zaune a natse duk suka juyo suka kalleshi,
Ya sameer ne yayi gyaran murya ya karaso inda yake ya miqa mashi hannu suka gaisa, anty fadila ta bishi fa kallo sosai, sai a yanxu ta kara tabbatar wa da dan nanna ne, don ga kamanninsu sosai ba kadan ba, da yanayin yanda yake magana da komai, dagowa yayi sukayi ido hudu dashi,ya gaisheta a natse ta amsa cikin mutuntawa kafin ta karasa wajen nanna.
Hamad dai na tsaye daga gefe ya nade hannayenshi a kirjinshi.

“Sannu Nanna…ya jikin? Allah yasa kaffara ne”
Bude idanunta kenan jin sallamarsu, Kallonta nannata tayi da idanunta da suka rine sosai suka fada tace “ku kira doctor ya sallameni”
Hamad ya futa don kiran doctor sai gashi ya dawo.
Ya sameer ya bar taj tsaye ya nufi nanna shima don yayi mata sannu. Shidai sunne kanshi kawai yayi kasa bai karasa ba gudun bacin ranta a natse ya futa daga dakin.

Dudubata doctor yayi don tabbatarta lafiyanta kafin ya kalli sameer “za a iya sallamarta yanxu, amma gaskia dole a kula da lafiyarta, kar a dunga bari tana shiga duk wata damuwa dazai janyo mata shiga shock irin wannan,“
“Thank you doc” Sameer ya fada yana miqa ma doctor hannu.
Ko kallonsu nanna batayi ba, gaba daya yanayin ta ya sauya kamar ba nanna ba, tayi wani irin fayau abun tausayi, kokarin tashi ta soma yi , jiri na dibanta,kayan da aka zo da ita dasu sune a jikinta,ganin yanayin da take ciki yasa anty fadila tayi saurin kama hannunta da babu canula a jiki ta taimaka mata.
Sameer da hamad suma suka mara masu baya.

Daidai nan ya fito daga office din doctorn daya bata sallama, da prescriptions din magungunan da zata buqata na qarin jini.
Nanna ta mashi kallo daya ta dauke idanunta suka fita daga cikin asibitin ita da fadila da hamad, uncle sameer kuma ya dan dakata.
Magana suka danyi da taj kafin ya futo shima suka shiga Motar da suka zo dashi gaba daya, suka wuce.
Suna barin asibitin anne ta kira sameer, yana dauka ya shiada mata an sallami nanna suna kan hanya ma,hamdala tayi kafin suyi sallama.

Babu wanda yayi magana tunda suka shiga cikin motar har suka iso gida, suna isowa suka wuce main house direct gaba dayansu banda hamad daya sake futa da motar.
Anne na zaune a sitting room sukayi sallama,take farin cikin fuskarta ya bayyana tayi saurin miqewa tsaye suka karaso inda take.
“Alhamdulillah!!! Sannunku da dawo ya jikin naki?”
Anne ta tambayi nanna tana kama hannunta suka zauna,murmushin yaqe kawai nanna ta mata batace komai ba sai ya sameer ne yace “ga magungunan da doctor yayi prescribing, sannan ya umarci a gujema duk wani abu dazai daga mata hankali”
Maganar da sameer yayi yasa anne ta dubi su shida fadila.
“Allah yasa kaffara ne, nasa ayi maku breakfast, Ina tajudeen din?”
Shuru duk sukayi gaba daya wannan yasa anne cewa , “barin shi kukayi achan?meysa?“
Bata gama rufe bakinta ba nanna ta miqe ta wuce sama don ko maganarshi bata son ayi.

Binta sukayi da kallo harta hau sama, wallahi duk ta zama wata iriya gaba daya kamar ba nanna ba.
Tana barin wajen anty fadila tayi saurin matsowa inda anne take zaune uncle sameer yayi gyaran murya yace “anne kun barmu cikin duhu, me….”
Saurin dakatar dashi tayi batama bari ya karasa magana ba tace “Zamuyi maganar daga baya, this is not the right time, jafaru ya kira maganar marayun da za ayi sponsoring karatunsu, ayi budgeting abunda ya kamata sai a sanar dani ”
Gaba daya suka hada baki wajen cewa “Allah ya ja da kwana ya kara arziki mai albarka su kuma allah yasa karatun ya amfanar dasu” ta amsa da ameen sannan ta miqe ta bi bayan yar uwarta rabi na biye da ita da warmers cike da abuncin, tuwo na musamman anne tasa a mata da miyar ganye saboda karin jini, da sallama ta shiga part din nanna, a zaune ta taddata bakin gado ta dafe kanta da hannayenta.
Koba’a fada mata ba tasan kuka take yi,nuni tayima da rabi ta aje warmers din ta futa, nanna najin sallamar anne kuwa tayi saurin goge hawayen dake fuskarta ta dago ta kalli anne.
Murmushi anne tayi mata sannan ta karaso inda take zaune ta dafa ta tace “hajara,”
Dagowa nanna tayi ta kalleta sai ga hawaye, ganin haka yasa anne saurin kokarin kwantar mata da hankali.
“Dan Allah kibar wannan hawayen, karya jawo maki wata matsalar, allah kadai yasan yanda kikeji aranki, amma ina rokonki da ki kwantar da hankalinki, ga abunci nan an kawo, freshen up saiki samu ki danci wani abun okay?”

Rabi dake zaune a sitting room din nanna tayi saurin shugowa bedroom din jin kiran da anne ta mata, tana shugowa ta wucewa bathroom kafin ta futo, “bismillah hajiya an kammala”
“Sannu rabi” nanna tayi magana dakyar.
Miqewa anne tayi ta futa “bari na barki zan dawo anjima”
“Toh anne” Nannata amsata

Tun bayan futar anne takai wajen minti talatin kafin ta miqe ta shiga bathroom ta watsa ruwa.


Bayan tafiyarsu jiki a mace ya shiga cikin motarshi, yafi kusan 30mins a zaune bai motsa ba, ya runtse idanunshi saboda wani irin ciwon kai dake damunshi tsakanin daren jiya da yau, kirjinshi ko har yanxu nauyi yake mashi.
Jiki a mace ya tada motar yayi reverse yabar harabar asibitin.
In less than 15min ya iso transcorp, ko iya parling baiba ya aje masu motar a wajen ya wuce sama.
Koda ya shigo dakinsa zama kawai yayi bakin gado ya dafe kanshi, wani irin zazzabin mai zafin gaske na neman dibanshi, kota cikinshi bayaji don rabonda ya sama cikinshi abunci ko ruwa tun dinner din da sukayi a gidan.
Zaman nan dayayi saiya zamana kamar bazai iya tashi ba saboda zazzabin gadan gadan ya taho mashi dole ya kwanta yaja duvet ya rufe jikinshi.

Anne na zaune kan couch ta jawo wayarta ta soma dialing number shi gar sau uku ba a dauka ba,gaba daya abunne babu dadi, tasan yanxu haka shima yana chan cikin wani hali, tund aga mahaifiyar tasa itama.

Yanda rabi ta aje abuncin nan haka ta dawo ta daukeshi don kwata kwata bata taba shi ba, saima kwanciya datayi anne ta shugo dakin saitayi tunanin ko barci tayi wannan yasa ta barta tadan huta.
Anne na fita nanna ta ta jawo hoton dake aje kasan pillow dinta, kurama hoton ido tayi sosai ta kasa daukewa sai hawaye…

40 years back….
Shekarar nanna goma chif a saudi, acikin wannan shekaru abubuwa da dama sun faru da ita, masu dadi da mara sa dadi.

Ranar da allah ya hadata da abdallah shine ranar data fara zuwa makka domin yin umra, don a madina take karatu.
Shigarta kenan ka’aba ta fuskanceta taji wani irin sanyi na dibanta, ranar ta kasance rana mafi sanyi ga wata ni’imatacciyar iska dake kadawa ko’ina kamar za ayi ruwa, gashi lokacin babu irin mutane sosai dinnan don babu cunkoso kwata kwata, take wani hawaye mai sanyi ya sauka kan fuskanta ayayin datayi ido hudu da dakin Allah ta fara dawafi, daidai wajen hajarul aswad ta tsaya tare da shafa wajen ta rufe idanunta, takai wajen minti biyu a haka kunnuwanta suka soma jiyo mata muryoyin dake gefenta saidai muryar mutun daya ce tafi zama a kunnanta inda yaketa yin addu’oi da larabci, saitaji gaba daya kamar ita yakema adduar, tana dena jin muryar tasa ta bude idanunta tare da kallon gefenta inda allah ya bata ikon ganin irin jakar maniyyata da suke sakawa, cikin hanzari ta dago ta dauka jakar tare da juyawa don ganin mai ita.
Saboda yanda kowa ke sanye da ihram yasa ta kasa gane kona wanene wannan yasa kawai ta rike ta cigaba da ibadarta.
Tana gamawa tayi safa da marwa ta sauke umra sannan ta wuce wajen da ake kai abubuwa idan sun bata.
Tana zuwa ta masu bayanin inda ta tsinta abun, wani dan paper form suka bata tayi signing ta saka information dinta don haka akeyi idan har mutun ya tsinci abu saboda gudun kar wani abu ya bata daga ciki, tana cikin rubutawa abdallah ya iso wajen.
Dake tana daga chan gefe wannan yasa batama lura dasu ba.
Tana gama rubutawa ta karaso wajen macen security din dake wajen ta bata paper din, matar ta soma zazzage jakar don shigarda abubuwan dake ciki, kusan kullum sai an samu irin jakar don duk maniyyata irinta suke amfani da saidai banbancin color.
Hajara dai na tsaye har matar ta gama shigarwa tana gamawa dake counter daya ne sai dai babu cudanya wajen mata da maza kowanne da bangarensa ta miqa bangaren maza, abdallah dake tsaye ya tabbatar da nashi ne aka duba id din dake ciki sannan yasa hannun tabbatar da babu abunda aka dauka a ciki, kafin aka bama hajara itama tayi signing.
Magana abdallah yayi da security din yayi mashi nuni da counter din mata adaidai lokacin ta dago bayan ta gama rubutun idanunshi ya shuga cikin nata, suka sallameta ta juya, shima ya karba jakar ya fita.
wannan ne mafarin haduwar taheel da nanna.


Duk wani abu da allah ya rubuta ko allah ya kaddara indai alkahiri ne saiya faru cikin kankanin lokaci, daga wannan ganin dayayi mata allah yasa mashi qaunarta a zuciyarshi, abunda bai taba ji ba,encounter dinsu na biyu shine ranar da aka gudanar da wani babban taro a makanrantarsu,cikin ikon allah kuma ya sake hadasu ta wata hanya daban, ita bata ganeshi ba don saida yayi mata bayani ta gane, baizo mata a matsayinshi ba, da matsayin da yake dashi a kasar yayi mata godiya sosai.

Daga wannan lokaci soyayya ta kullu tsakanin taheel da hajara, hajara itace mace ta farko da abdallah ya fara so, tsaftaccen so yake mata haka zalika itama take mashi,su a nasu aladar babu wani jan lokaci wannan yasa ya nuna mata aurenta yakeson yi, sannan ya buqaci ganin iyayenta.
Da farko nanna ta tsorata don babu wanda yasan dashi a gida sai anne, tsoranta na biyu shine aqidar babansu santuraki, idan mace ta gama karatu shike zaba masu mijin aure, kamar anne data gama karatunta already ya bada ita ga dan business partner dinshi.
With the support and courage din da anne ta bata kuma ta shige mata gaba suka sanarda mahaifinsu santuraki, daga nan mafarin tangarda ta shigo don santuraki bai amince ba, don itama ya mata miji, tana gama karatu.
It was a very hard moment for nanna don tana masifar son taheel,rashin amincewar iyayenta bazaisa ta aureshi ba, dole ta hakura da abdallah.
Ta shiga damuwa sosai ba kadan don anne ce kawai tasan wannan,karatunta ma duk yayi baya tayi wani irin rashin lpy sosai.
Tsakanin yan uwa sai Allah, halin da nanna ke ciki anne ma ta shiga amma dole ta hkura da zabinta tabi na mahaifinta amma bazataso yar uwarta ta shiga irin halin data shiga ba a baya wannan yasa ta sake tada maganar tare da rokon mahaifinsu, alhaji santuraki nada dogon buri da future akan yayanshi, but hajara failed him dalilin halin da anne ta shiada mashi take ciki wannan yasa ya yanke wani tsatsauran hukunci, inda ya yarda saidai ya shaida mata idan tayi regretting decision dinta she has to forget tanada uba.
Anne bata yarda ta fada mata wannan last furucin mahaifin nasu ba akayi auren abdallah da nanna.
Bayan aurensu da shekara guda allah ya azirtasu da d’a namiji inda yaci sunansa (Tajudeen abdullah taheel)abdallah yayi murna yyai murna mara iyaka ba kadan ba, adduar da ya dade yanayi allah ya amsa ta, ya samu magajinsa.
Bangaren nanna babu wanda ya kaita farin ciki itama,koda ta shaida ma anne itama tayi farin ciki sosai ba kadan ba, saidai a lokacin ne nanna ta fuskanshi har zuwa lokacin akwai matsala tsakaninta da mahaifinta, don har zuwa lokacin bai amince kuma ya karbi taheel a matsayin mijinta ba wannan kadai yasa ta kasa komowa gida don batasan da wani ido zata kalli mahaifin nata ba saboda bijire masa datayi ta dauki zabinta.

Anan gida nigeria kuwa, sharridan da santuraki ya gindaya ashe masu tsauri ne, inda ya haramta wa kowa kusantar nanna, koda ta haihu ma anne taso zuwa tare da mahaifiyarsu amma yace bai yafe ba duk wanda yasa kafa ya bita, haka suka hkura amma bata taba bari nanna tasan dalilin ba kenan.

Taj nada shekara uku mahaifiyarsu ta rasu, a lokacin ne nanna tasan duk halin da ake ciki, don mahaifinsu ya shaida mata indai tasa kafa tazo nigeria toh bai yafe mata ba.

Hankalin nanna ya tashi sosai don sai a lokacin ta tabbatar da akwai matsala babba tsakaninta da mahaifinta, kuma bai amince da aurenta da taheel ba har zuwa yanxu.

Tanaji tana gani ta kasa zuwa nigeria tayi kukan rashin mahaifiyarta data kasance itace mai tausasa ta da anne, mai nuna mata komai mai wucewa ne kuma komai daya faru mukaddari ne dağa Allah.
Akwana a tashi taj ya taso da shakuwa tsakanin iyayenshi, musamman nanna mahaifiyarshi, bashida hayaniya bashi da yawan surutu kwata kwata, da farko ma tayi tunanin ko yanada wani mental issue ne aka tabbatar masu da lafiyarshi kalau kawai dai miskilin yaro ne, bai cika wasa ba saidai kullum yana jikin mamanshi.
Taj na gab da shiga shekara bakwai a duniya komai yayi turning upside down on a blink of an eye, aurensu shekara takwas nanna bata taba sanin abdallah nada wasu iyali ba sai a lokacin.

Babu abunda abdallah bai dauke ma nanna ba, gida na alfarma, cima mai kyau, mota kayan jindadi na zamani daidai gwargwado kuma daidai karfinsa daya nuna mata.

Akwai wata ranar friday, nanna na zaune a sitting room tana kallon tv, gaba daya hankalinta ma bayaga tv don gaba daya wani irin faduwar gaba take ji cikin kwana biyu, tayi nisa sosai cikin tunani kamar ance ta maida hankalinta ga tv taga abdallah, janyo remote tayi cikin sauri ta kara volume don jin maganr da akeyi a jiki, take jikinta ya soma bari,ko barci take taji muryarshi zata iya farkawa.

Abdallah ne da kuma wata mata a gaba suna tafiya sai wasu manyan mutane dake biye dasu a baya suna zagayen shops din wajen a yanda aka dauko rahoton.

Inda mai bada rahota ta dora da “an bude sabon mall din daya kasance additional to the taheel companys a nan jedda karkashin ikon matar mai kamfanin, bayan shekaru takwas da suka wuce basu bude sabo ba”

dam gaban nanna ya sake badawa, “karkashin ikon matar kamfani?”
Idanunta ne suka sauka kan sunan “Fattu abdallah taheel”

This is the most shocking moment of her life,
Jikinta na bari idanunta kamar gizau suke mata ganin abdallah ne dai abdallan ta tunda gashi nan zahiri kuma ga asalin sunansa nan data sanshi dashi, babu abunda bakinta ke furtawa sai innalillahi wa inna ilaihi rajiun.
She’s so confused at the momemt taqi yarda da abunda idanunta ke gane mata.

Da a tsaye take zata iya zubewa kasa sumammiya,
Aranar ya kamata ya dawo daman between mondays to friday baya zama a gida sai weekends sabod ayanayin aikinsa daya shaida mata, kuma ya nuna mata bashida muhalli achan da zai iya tafiya da ita saidai ya barta anan.
Yana isowa kuwa yanayin daya taddata ya tabbatar mashi da ta gane gaskiyar dayake ta boyeta shekara da shekaru, daman khaal yayi warning dinshi ba sau daya ba ba sau biyu ba, don aure ba abun wasa bane, bashida yanda ya iya ne dole ya boye mata gaskiar alamari don shine mafi alkahiri dukda yasan watarana gaskia zatayi halinta.
Ba tare da wani coner coner ba tambaya daya biyu zuwa uku ta mashi akan ya fada mata gaskia shin da gaske yanada aure daman tun kafin ya aureta? Yanada wasu iyalan? Bai mata karya ba ya fada mata hakan ne, kuma da matsayinshi saidai ya kasa fada mata dalilin boye mata dayayi shekara wajen takwas.
She felt betrayed, tayi kuka tayi kuka ta göde Allah, abunda bata taba tsammani ba daga gareshi, abdallah lied to her.
Daga nan matsaloli suka dunga shugowa tsakaninsu, gaba daya saita fara regretting aurenshi, ga rabo a tsakaninsu, saita fara tunanin hakkin mahaifinta ne daya hanata aurenshi batabi zabinsa ba ta bujire mashi, yanxu ko ta tsaya babu wanda zai yarda ita matarshi ce ta kasance wani boyayyen sashe a rayuwarsa.
Aure dai yaqi dadi bawai don taqi karbar qaddara ba saidan trust din data bashi ta yarda dashi yayi mata karya yayi breaking trust dinta ya gina rayuwar aurensu da karya.

Ana nan dai a haka ta zauna tayi tunani kan rayuwar danta yanxu idan abdallah ya fadi ya mutu babu wanda zai yarda ita din matarsa ce kuma taj dansa ne tunda ya boyesu a idanun duniya, bazata so danta ya wulaqanta ba wannan yasa ta buqaci dole ya shiada ma iyalansa, abu ne mai wuya don bazai taba barin hakan ta kasance ba saboda yasan halin fattu, wannan yasa yaqi amincewa da haka, ganin haka yasa nanna yanke hukunci idan har bai yi yanda ta buqata ba dole ya saketa ta dauki danta ta koma nigeria, rigima sosai ta afki tsqkaninsu don bazai taba barinta ta tafi da danshi ba, zai iya hkura da komai amma banda dansa.
Ta bangarenshi ya kasa fuskantarta da dalilin dayasa ta buqaci ya bayyana second family dinshi, ba dan komai baneba sai dan taj din saboda kar a duniya ta mashi wani kallon daban tunda kowa yasan bashida wani family apart from wanda ya bayyana a duniya.

Suna cikin wannan iftila’in matsalolin nanna ta fayyacema anne don bata fadama kowa ba, batada abokiyar shawara sama da anne, gurinta take kai kukanta, damuwa ta mata yawa dole ta sanarwa da yar uwarta.
Anne tabi bayan decision din datayi making kuma ta bata kwarin gwiwa


Ranar wata litinin da safe,nanna ta hada kayanta dana danta, aranar tayi alkawarin barin auren gaba daya har abada, tana gabda futa abdallah yazo da khaal domin su roketa akan tayi hkuri yanxu ba lokacin daya kamata ya bayyana su bane, daman ta bashi tsakanin jiya zuw ayau idan har baiyi yanda tace ba zatabarshi har abada wannan yasa ya kira khaal don shi kadai ne yasan komai don shine ya shiga ala’amarin auren nasu.
Babu yanda basuyi da ita ba ta tubure saita bar gidan adaidai lokacin kiran da bata taba tsammani ba yazo mata kiran mahaifinta.
Zata iya cewa shekara da shekarun nan bai taba kiranta ba saidai ta kirashi.
Cikin hanzari ta dauka tana hawaye, maganganun daya fada mata ne yasa ta saki hannun taj data rike.
“Hajara daman na fada maki daga ranar da kikayi regretting decision dinki ki mance ni mahaifinki ne, saboda bakida matsayi a gidana. Zaki samu matsuguni a gidana idan har kika dawo kasar nan yanda kika barta”

Yana fadin haka ya katse wayar hawaye suka sauka kan fuskar nanna, yanda ta saki hannun taj dinnan bata sake riko hannunshi ba ta dubi abdallah don tasan shine ya kira mahaifinta.

Dole batada option, kota hakura ta zauna da danta ko kuma ta koma yanda tazo kasar nan, bata taba tsammanin abdallah zai mata haka ba aurensu bai kareta da komai ba sai tsantsar yaudara da cin amana, ta dalilin aurensu bata da daidaito da mahaifinta tsawon shekara takwas, ta dalilin aurensu ta sadaukar da kusancin dake tsakaninta da mahaifinta tabi zuciyarta data rudeta da sonshi, kamar yanda mahaifinta ya fada gashi nan yau tayi regretting din aurensa datayi.
Daman ance duk abunda babu albarkar iyaye a ciki yana tattare da lalacewa.
Bata waiwayesu ba ta tafi tana hawaye…..


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 39 · 0% Book details