Chapter 69
Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 16 min read
Ahankali ta soma bude rinannun idanunta da sukayi mata nauyi, kokarin tashi ta somayi harta miqe zaune,kwata kwata bata lura dashi ba saidata fara kokarin sauka daga kan gado taji kamar an rike hannunta gam,da mamaki ta juyo, take ta sauke idanunta akanshi, yana daga zaune ya jingina da bed board din gadon ya rufe idanunshi sleeping soundly, ga hannunshi daya hade da nata ya rike gam kamar wadda za a kwace mashi ita,tundaga yatsunshi tabi da kallo har zuwa calm face dinshi da gashin baki ya zagaye ta, tayi mamaki sosai ganinta kwance akan gadonshi gashi kuka a gefenta ya rike mata hannu gam, jiya gaba daya bata cikin hayyacinta lokacin daya shugo dakin, sai yanxu take tuna yanda ya dauketa jiyan hankalinshi a tashe, saurin runtse idanunta tayi ta budesu akanshi, ganinta kwance kan gadon nashi ya tabbatar mata bai gano cewa bata da ciki ba kenan.
Hannun nata ta fara kokarin zamewa daga nashi ta kasa, saima dagowa datayi kawai taga ya bude idanunshi tarr akanta, tun lokacin data farka ya tashi shima amma bai bude idanunshi ba, yanajin yanda take kallonshi,harta fara kokarin zame hannunta daya rike.
Lumshe idanunshi yayi ya sake bude su akanta, fuskan nan babu yabo ba fallasa yanda take koda yaushe, sai kwarjini da cika idanu.
Daburcewa taso yi ganin yanda yake kallonta yasa tayi saurin cewa “dan allah kayi hakuri bansan yanda akayi na…”
Zare hannunshi dayayi ya miqe tsaye yasa ta dakata, bedroom slippers dinshi ya saka sannan ya zagayowa ya wuce hanyar bathroom, tunda ya wuce ta bishi da idanu har saida ya shige bathroom din ta sauke ajiyar zuciya ta doka tagumi, bai wani dade ba ya futo daga bathroom din ya tunkari inda take, cikin hanzari ta kauda idanunta lokacin da suka hada idanu, a daidai gaban gadon ya tsaya yana kallonta na yan sakanni kafin ya soma magan acikin kamala “how are you feeling now? Akwai abunda ke maki ciwo”
Cikin sanyi yayi maganar kamar bashi ba, sai taji wani irin sanyi aranta ganin ya sauya lokaci guda, gira daya ya daga mata ganin ta kafeshi sa idanu, saida yayi cliking fingera dinshi ta dawo daga tunanin data shiga, tayi saurin kauda idanunta wani irin siririn murmushi ya kubce mata tace “Alhamdulillah i’m feeling better”
Yana jin haka ya sake magana “zaki iya tashi?”
Da mamaki ta dago for the second time ta kalleshi don tabbatar da daga bakinshi maganar ta futo,bata gama tunanin ba again kawai taga ya miqo mata hannu, tana ganin haka ta gane me yake nufi, kanta a kasa ta daura dan hannunta kan nashi ta miqe tsaye, dake yana gabanta saita zama yar smally a gabanshi saboda ya fita tsayi sosai,da taimakonsa ta shiga bathroom ya bude mata kofa, kafin ya futo ba tare da yace mata komai ba.
Yana futa ta sauke wani irin murmushi, a gurguje tayi hot bath sosai yanda jikinta zaiyi mata dadi sosai kafin tayi wankan tsarki tana gamawa ta dauro alwala ta nado jikinta da towel, saida ta gama ne ta fara tunanin yanda zata futa don bata shugo da hijab dinta ba, gashi tana jin kunyar haka, fatarta sai haske da sheqi takeyi tsakanin kwanakin nan, kallon kanta ta dunga yi a jikin mirror din toilet din, gaba daya ta sauya kamar ba ita ba, wannan dafewar data yi lokacin da take wahala a gida duk ta baje, wani sa’in inta kalli kanta har mamaki take, yanda kasan an sauya ta gaba dayanta, inta koma gida ba kowa ne zai ganeta ba sabod asauyawar tayi yawa dama wahala ce da talauci ta dankwafar da ita ta lalatata.
Sauie ajiyar zuciya tayi ta janyo wani towel din ta nadoshi wajen kirjinta dake cike kamar suna neman yi mata yawa, harta nufi wajen kofar futa taji knocking daga ciki, cikin hanzari nufi kofar ta bude, yana nan a tsaye, daman sallah yayi yana idarwa yaji shuru babu motsi a bathroom shine yayi knocking don ya tabbatar ba passing out tayi ba don jiya Ya tsorata sosai da lamarin ta.
Ganin she’s perfectly fine yasa shi kauda ido ya matsa ta futo shi kuma ya shige daga ciki.
Yana shiga ta nufi closet da hanzari ta fiddo daya daga cikin rigunan da ammu ta saya mata ta saka sannan ta shafa mayukan data bata da turare mai sanyin kamshi kafin ta futo da hujab a hannunta.
Sallar itama tayi don kusan karfe takwas ta gifta, harta isar da sallah bai futo ba harta miqe zata zare hijab din datayi sallar dashi sai gashi ya futo daga bathroom din, direct dakin shiryawa ya nufa ya saka kaya marasa nauyi kafin ya futo, sai faman kamshi yakeyi mai dadi,kafafunshi na cikin bedroom sandals ya futo, harta gyara dakin fess fess hatta wajen beddings saida ta sauya sabo, yana kokarin daukan wayarshi da incoming call ke shugowa ta shugo dakin hannunta rike da mug a hannunta, tunda ya daga wayar yayi shuru baice komai ba saima kallon bayanta daya tsayayi lokacin taba kokarin rufe kofa data shugo, tana juyowa ya kalleta daga sama har kasa, kayan jikinta sunyi mata kyau, pink din doguwar riga daidia jikinta, wajen kanta kuma ta daura veil din kayan ya danyi baya gashin baby hair dinta ya futo,zama yayi bakin gadon har zuwa lokacin wayar na kunenshi yana magana kadan kadan cikin harshen turanci, karasowa tayi har inda yake ta dan jinkirta tana tunanin yanda zatayi ta bashi, bata gama tunanin ba ya mika mata hannu alamu ta bashi, kallonshi tayi harta tsinci shika kallon nata yake, murmushi tayi mashi tare da miqa mashi mug din, yana karba yakai bakinshi direct har zuwa lokacin bai sauke wayar dake kunnenshi ba, tana daga tsaye yasha kusan rabi, bata gajiya da kallonshi a tsaye harya gama sha shi baima san ya gama ba saima miqa mata mug din da yayi ta karba fuskanta wasai ta futa daga daki ya rakata da idanu.
Tana shiga kitchen tabi mug din dayasha tea din da kallo, yau shine yasha avun hannunta willingly? Saitaji dadi aranta sosai.
Noodles ta dafama kanta taci ta koshi anan kitchen din don rabonta da abunci tun jiya da yamma data kasa cin komai.
Saida ta tsaftace ko’ina kafin ta fito zuwa bedroom din, a tunanin by that time ya futa already don tasan kullum saiya futa da safe, tana shugowa taga akasin haka saima ganinshi da tayi a zaune kan gado har zuwa lokacin yana waya, bata jin mai yake fada saboda accent din da yake using british ne, wannan yasa ta kasa gane me yake fada.
Futowa ta sakeyi zuwa sitting room donta ta bashi waje zamanta keda wuya ammu ta shugi donta dubata, bayan sun gaisa ta tambayi ya jikinta nan ta shaida bata babu ciwon bayan ma da kafa duk ya tafi, nan ammu ta mata bayanin abunda ya faru jiyan sannan ta shaida mata ta bar shan maganin.
Sun dade sosai suna hira har sabeehar ta fada mata yanda yau ta hada mashi coffee kuma ya shanye duka, daga yanda take fada ma ammu ta gane taji dadin sauyawar da yayi,
“Ay jiya bakiga yanda hankalinshi ya tashi ba, ya dauka ko wani abu ne daya danganci cikin”
Shuru sabeeha tayi jin abunda ammu tace, saitaji wani iri aranta,ganin haka yasa ammu ta kama hannunta tace “karki damu kinji, just keep focus,komai zaizo mana cikin sauki Insha allah”
Sun dade suna dan tattaunawa cikin maganar da sukayi kwata kwata basu kawo karyar da sukayi na cikin ba saboda sabeeha ta fada mata bai fita ba yana nan bayan wannan ma kar wani ya jisu wannan yasa suka daina maganar cikin.
Saida ammu zata fita tasata dole ta koma bedroom din.
Da sallama a bakinta ta shugo dakin, shi kuka ya fito daga closet, maganinta daya saka a jikin jacket din daya fita dashi da sukaje asibiti ya dauko, gaba daya yama manta dashi sai yanxu,ajiye yayi gefen bedside kafin ya kalleta yace “your medication” ya karashe yana mata nuni da ledar, cikin natsuwa ta amsa shi da “tohm”
Baice komai ba ya nufi hanyar futa daga dakin maganar datayi ya dan dakatar dashi, “thank you”
“For?” Ya jefo mata tambaya ba zato ba tsammani, “uhm…for helping me yesterday”
Yana jin haka ya juyo ya kalleta “don’t think highly of your self, i did that only bacause..”
Ya kalli cikinta kafin ya maida dubanshi gareta, “don’t thank me for taking my responsibility”
Yana kaiwa nan ya fuce.
Bayan futarshi Jiki a mace ta nufi wajen bedside ta dauka maganin ta balla tasha.
Yana futa ya wuce sitting room din sama, hidaya na daga zaune ta hakimce kan kujer tana jiran zuwanshi, yana ganinta ya karaso ya zauna, “sabahal khair” ya gaisheta kai tsaye, abunda ke cinta tayi saurin dannewa ta amsa gaisuwar tashi kafin tace “ya jikin nata??”
Yayi mamakin tanbayar tata sosai ba kadan ba saidai bai nuna ba a zahiri, “hamdullah!!”
Ya amsata a garaje, shuru tayi tana son tambayarshi abu amma tanajin shakjar yin haka yanxu ta rasa dalilin dayasa take dan shakkarshi , kodan ya sauya ne cikin kwanakin nan sauyawar tashi ma tayi yawa sosai, don yanxu ko gaisheta zaiyi baya mata yanda yakeyi ada.
“So yanxu ka yarda da wannan pregnancy din naka ne kenan?”
Yana jin abunda ta fada ya kalleta, kai tsaye ya amsa ta “eh…”
Yana fadin haka ta sauke wani irin makirin murmushi chan kasan maqoshi kafij tace
“Okay then,tunda kayi accepting banida ja akan maganar,”
Jinjina mata kai kawai yayi kafin ta miqe ta fuce daga parlorn.
……
Tun fitar dayayi dazu nan bata sake ganinshi ba har wajen karfe tara na dare, tunda tayi sallah tasha magani takeji wani irin azababban barci yana fuzgarta haka ta hana kanta barci nan ta zauna jiran dawowarsa.
Misalij wajen karfe goma kuwa sai gashi ya dawo gidan da shopping bag daya a hannunshi, yana shugowa yaci karo da barad daya futo daga dakin ammu, taj na hangoshi ya sauke mashi murmushi,yaron shima yana hango taj din yayi saurin karasowa inda yake ganin babu kowa a kasan, daman tsoronshi kaf hidaya ta ganshi da taj din.
“Uncle taj”
“How are you?” Taj ya tanbayeshi yana mai shafa kanshi, “im fine uncle, where anty fatima?”
Shuru taj yayi yama rasa me zaice masa, ya dai lura wannan yarinyar yake nufi, “whos anty fatima?”
“Your best friend mana… opss sorry i mean bibi”
Taj najij haka ya dan duqa a gaban yarin yace “is that her name?”
“Yes uncle…ka manta ne? Kaika saka mata sunan fa?“
“Bi..bi” taj furta ahankali, kafin ya kalli barad din ya sake jefo amshi tambaya “is she nice?”
“Yes uncle shes very nice and calm, itace ma ta..…”
Shuru yaron yayi tunawa da gargadin mamanshi, ganin yayi shuru yasa taj shima baice mashi komai ba ya bude shopping din daya shugo dashi ya deba chocolates da yawa ya zubama barad a aljihunsa kafin yace “ka boye su”
Girgiza mashi kai yaron yayi ya haura sama, yana son tambayarshi ya jikin babansa amma ya kasa.
Saman shima ya haura ya wuce part dinsu direct, kofar bedroom ya bude ya shugo bakinshi dauke da sallama dukda muryarshi bata futo ba yanda za aji sosai kamshin nan ya amsa mashi direct zuwa hancinsa, tundaga nesa ya hangota kwance gefen gadon a kasa ta saka kanta kan katifar gadon, tana sanye sa wasu kayan daban bana dazu ba a jikinta.
Takowa yayi daidai bakin gadon inda take kwance ya tsaya yana kallonta kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ajiye ledar daya shugo da ita sannan ya wuce bathroom, ya dan dade sosai a ciki kafij ya futo ya shurya zuwa kayan barci .
Harya futa tana nan kwance abunda sai faman sauke ajiyar zuciya take, kokarin tashinta ya somayi ta hanyar dan taba in da kanta ke wajen amma ko gizau, kamarma tayi nisa sosai a barci, gashi baya jin zai barta ta kwanta a kasa saboda zazzabi, duqawa yayi a gabanta ya fara taba kafadarta ganin still farkawa kawai ya sungumeta gaba dayanta kamar yar baby ya miqe tsaye,gaba daya batada wani nauyi amma a ido zaka dauka tana da nauyi saboda dirin da take dashi,ahankali ya zame slippers din kafarshi ya rankwafo zuwa gadon ya kwantar da ita kafin ya miqe tsaye ya zagayo gefen gadon ya zauna.
After 2weeks
Cikin satin biyun nan abubuwa da dama sun faru tsakaninta dashi, yanxu ta gama karantarshi tsaf, tasan abunda ke saurin pisaing dinshi off wanda take gudarma hakan sannan, halayyanshi ne da mood dinshi ta kasa karanta dan yau saika ganshi sanyi sanyi gobe kuwa gaba daya saiya sauya, bata fasa kyautata mashi ba kullum ba tare da ta nuna gajiyawarta ba, kullum da safe kafin ya fita zata dafa mashi coffee ta bashi, kafin ya futo daga wanka kuwa zata fidda mashi kayan da zaisa, ranar daya saka wanda ta fidda mashi ba karamin dadi taji ba sosai, yanxu ya fara dan sake mata kadan, don idan ta dafa abunci ma anan part dinsu yana ci sometimes, kuma kamar yanda ammu ta fada mata da zarar yana daki ta dunga kasancewa a tare dashi don ta janyo kusanci taakaninsu yanxu abunda ta dage dayi kenan, ta dan rage tsoron yi mashi magana saboda yana amsa ta sama sama idan ta mashi, abunda yafi yi mata dadi arai shine yanda koda yaushe yake tambayar if she’s okay, kwata kwata baya nuna mata ya damu da cikin amma actions dinshi ke bayyana mata hakan.
Yanxu ya hanata kwanciyar kasa ma, a kan gadon shi take kwanciya, da yake saitayi barci yake kwanciya wannan yasa bata gane inda yake kwana ba, kota farka bata ganinshi a dakin.
Bangaren su afiya babban shiri sukayi na ganin sun zubda cikin nan amma kudirinsu bai cimma ruwa ba, saboda gaba daya sabeehar ma basa ganinta, ba ita kadaiba harma taj din,don basa saukowa yin breakfast, daman wannan damar suke nema kuma bata samu ba, dole suka hakura harsai sun samu chance, bangaren fadwa gaba daya zaman gidan ma ta kaurace mashi, idan ta fita tun safe bata dawowa sai yamma, saboda idan har ta zauna a gida tana tuna cewa akwai wata dake dauke da cikin taj din a gidan zata iya komai, zata iya komai akanshi,
Bangaren hidaya ko gaba daya yanxu ta maida ahankalinta wajen kamfani, product din datake developing yana neman failing,risk din failure din product din yafi samun da za ayi a cikin kamfanin, ita bata ma hango risk din da kamfanin ke ciki, duk wani illlegal ways shi take amafani don ganin kamfanin ya tsaya, wannan investment din data dakatar ba karamin taimakon kamfanin yakeba, taqi accepting haka, a ganinta indai ta cigaba da karbar wannan investment din da zarar aka gano wanda ke bayarwa shikenan tata ta kare.
Ta wajen taj duk abunda ke faruwa a kamfanin yana sane dashi,saidai baiyi yunkure yinkomai ba haka zalika bai nemi ainahin sanin dalilin dayasa hidaya ta cire investment din da yake bayarwa ba cikin airei, kuma tun data nuna batasan komai ba game da identity dinshi shima shuru yayi baice komai ba saima maida hankalinshi dayayi ga abubuwan dake gabanshi.
Mutalib ko bai fasa shigema taj dinba, daman dalilin shigarshi wajen gym dinnan kenan, har saida ya dan samu taj din na kulashi sama sama, wani sa’in ma har workout sukeyi a tare,
Bai taba nuna mashi tun asali daman ya sanshi ba sannan bai fada mashi alakarshi da khaal ba saboda ya rigada yasan ko wanene taj din, baya yarda da mutane cikin sauqi, at the same time baibar tailing hidaya ba, yanxu neman hanya yake yanda zai samu ya gano me takeyi a chan island din, haryau maganar gawar nan da aka musanta akace ta khaal ce bata bar tsaya mashi arai ba, kuma yana ji a jikinshi akwai wata a kasa, kuma yayi alkawarin sai yayi uncovering komai.
9pm…
Wasu daga cikin Kayan da ammu ta kawo mata na barci ta dago taba kalla daya bayan daya, duk cikin kayan babu wani na arziki sai wata doguwar riga wadda zata iya kai mata har gwaiwa, rigar ta saka a jikinta sannan ta dan goga turaren da ammu ta bata kafin ta fito, a zaune ta taddashi chan saqon gado ya daura laptop kan cinyarshi yana sanye da pjs shima farare ya sauke kafarshi daya kasa.
Takowa tayi kamar wata munafuka ta zauna bakin gado, tana zama yaji kamshin nan ya bugi hancinsa, dakatawa ya danyi da aiki ya juyo ya kalleta, yaune rana ta farko daya taba ganinta da kayan barci, duk sanda zata kwanta bata saka kayan barci ashe yana lura da duk wani movement dinta amma yake kauda ido, ganin tana neman juyowa yasa shi kauda kai, ita kuwa ganin tun dazu yake abu daya akan system ta miqe ta fuce daga dakin, kitchen ta nufa ta yanka variety of different fruits types, tana yankawa ta wawwake ta saka a wani clear bowl sannan ta futo bayan ta kashe komai na daki,
Sallama tayi a natse kafin ta rufo kofar dakin ta tako zuwa bakin gadon, slippers din kafarta ta cire sannan ta hau kan gado gaba daya ta zauna ta daura bowl din a kan cinyarta ta fara cin fruit din, ta gefwn idanu take kallonshi ganin hankalinshi yayi nisa wajen aiki, haka kawai wani abu ya dunga raya maga arai, tana ta contemplating tayi ko kartayi, dakyar dai ta samu courage din daukan slice din apple guda daya ta miqar da hannunta wajen bakinsa kamar wadda ke tsoro, chak ya tsaya ganin hannunta saitin fuskarsa, bai juyo ya kalleta ba haka zalika bai cigaba da typing dinba,
Ahankali ta bude bakinta kamar mai rada tace “di..di….ahhhh, apple ne your favorite”
Tana fadin haka tayi shuru tana jiran abunda zaiyi, tama san rejecting zaiyi har hannunta ya fara sagewa tana kokarin dauke hannun nata daga kan fuskarshi kawai ya bude bakinsa, yana bude ta sauke murmushi ta saka mashi apple din a bakinsa.
Ahankali ya soma tauna tundaga bakinshi har zuwa maqogaronshi tabi da kallo, har saida ya cinye, ta sake daukan wani takai daidai saitin bakinsa, ya sake bude baki ta saka mashi, ya cigaba da danne dannen dake gabanshi, ta bangarenshi baima san lokacin daya bude mata bakin nasa ba.
Karshe dai itace tayi feeding dinshi apple dinnan tass, saida ya cinye na bowl din ta kalleshi fuskanta dauke da annashuwa tace “a karo wani?”
“No thanks”
Yana fadin haka ya kashe laptop din ya miqe ya ajiyeta inda yake ajiyewa kafin ya shiga bandaki, ita kuma ta wuce kitchen ta wanke bowl din sannan ta ajiye ta dawo dakin, har zuwa lokacin bai futo ba don haka tayi kwnaciyarta kawai.
Yana futowa daga bathroom ya kashe hasken dakin ya nufi chan dayan bangaren gadon ya kwanta abunshi, sabeeha data tabbatar gadon ya nufo kuma anan ya kwanta tayi mamaki sosai , sharing gado zasuyi a tare? Ko ya manta tana kwance akan gado? Tambayar data dunga ma kanta kenan, ita kanta abun yayi mata banbarakwai, harzata tashi ta bashi gadon ta tuna da maganar ammu don haka tayi kwanciyarta kawai.
Tana cikin wannan tunanin batama san lokacin da barci ya kwasheta ba.
Bangaren taj din sharp ya manta gaba daya yau, don a gajiya yake, kwana biyu kwanan da yakeyi a sitting room ya fara sa mashi ciwon jiki, he’s not comfortable kwata kwata, don bai iya kwana a couch ba, yawanci ma ba kwanciyar yake ba saidai ya zauna yayi relaxing jikinshi a haka har barci ya daukeshi, kwata kwata bai iya kwanciyar couch dinba amma haka yake hakura ya futo sitting room din.
Lokacin sallah nayi kamar kullum ya bude idanunshi tarr, lumshesu yayi ya sake budewa kafin ya yunkura ya tashi zaune yana mai dafe kanshi ya saka slipper ya wuce ya miqe, juyuwan da zaiyi ya ganta kwance ta juya mashi baya, kauda kanshi yayi ya nufi toilet ya dauro alwala sannan ya futo.
Har zuwa lokacin barcinta take hankali kwance, har yayi sallah ya idar, daidai lokacin itama ta farka bakinta dauke da ambaton allah, harda yar miqarta duk yana kallonta ta shga bathroom, …
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID