← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 5 OF 66

Chapter 60

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 18 min read

Update!!

Yanda ya fada saida gabanta ya bada wani dammm, muryar shi Nayin amo, at that moment jikin hidaya ne kawai ke dawainiya da ita badai hankalin ta ba don hankalinta ya gama barin jikinta gaba daya, ko ba a fada mata ba she can tell ya dawo hayyacinsa, he has regain his memory…
Gaba daya daga sabeehar har doctors din dake tsaye da nurse duk mamaki sukeyi, doctor ne ya karaso inda yake zaune yace, “calm down sir,”
“Why should i calm down? I fucking need an explanation, and who’s this? Wace wannan”
Yayi nuni da sabeeha, tunda ya fara magana jikin sabeeha ya soma tsuma,
first love!” Ya sake kiran hidaya datayi tsaye gaba daya hankalinta ya gushe saida ya sake kiran sunanta kafin ta farfado, ta ma kasa yunkurawa saboda yanda kafafunta suka sage, meke shirin faruwa kenan? Badai abunda take tsoro bane ke shirin faruwa? Hankalinshi ya dawo?”Tambayar da take ma zuciyarta kenan aranta, da yake a bude tabar kofar lokacin data shugo cikin dakin wannan ya bama fadwa data biyo bayanta damar jin duk abubuwan dake faruwa kuma tabbas muryar taj din taji, don haka itama ta shugo tayi sake tana sauraron yanda yake magana.

Dakyar hidaya ta tako zuwa inda yake kafafunta na janta, don ta tabbatar da zargin da take, tana karasowa ta kama hannunshi cikin nata dake ta faman karkarwa yanda yake kallonta haka take kallonshi, gaba daya ya zama confuse ganin yanda suke kallonshi kamar yau suka fara ganinshi, ga sabbin fuskokin da bai taba gani ba a gabanshi, banda hidayar daya gani a tsaye don ko lura da fadwa baiyi ba.
Tana riqe da hannunshi ta soma magana,”big baby!”
“Yes first love,” ya amsa ta
“I can’t believe this, ka tuna komai yanxu? You remember everything?”

Da mamaki yake kallonta ganin yanda take magana surprisingly, “did something happen to me? Meysa kuke kallo na haka? How did i end up here?” Yanda ya karashe zaka gane hankalinshi a tashe yake, yayi wani irin jaa lokaci guda,gaba daya a cikin duhu yake babu abund ayake nema sai karin haske, ganin yanda hankalinshi ya tashi yasa doctor ya soma magana, “sir you had an accident few hours ago, you were rushed to the hospital kaida wann…”
Saurin dakatar da doctor hidaya tayi tace “Alhamdulillah alhamdulillah!!!!! You’re awake finally” tana karashewa ta rungumeshi tsam a jikinta, “oh my god! Big baby, youre back, this is unbelievable”
sabeeha sakqe tayi tana kallon sabon drama da take shinfida tana kallon ikon allah, fadwa kuwa juyawa tayi kafafunta na karkarwa ta fuce daga dakin, she can’t believe abunda kunnuwanta ke juyo mata, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, tama rasa wa zata kira a waya a daidai wannan lokacin, afiya ce ta fado mata arai tayi saurin dialing number ta, saida ta kirata kusan sau uku kafin ta dauka, kamar ma daga barci ta tasheta cikin fada tace “why are you calling da safiyar allah nan dan allah, its 6am here in dubai”

“Afiyaaa!! Listen to me, shikenan komai ya lalace”
“Me kike nufi?”
Jikin fadwa har tsuma yake wajen furta,
“ Hankalinshi ya dawo, he has regain his memory”
Zumbur afiya ta miqe zaune, babu wani kayan arziki a jikinta tace
“What do you?,”
“Are you stupid ne? Bakiji me nace bane? Hankalinshi ya dawo he has regain his memory,”

“Na shiga uku” afiya ta fada hankali a tashe kafin ta tari nunfashin fadwa ta cigaba “shikenan… daman ni nasan za ayi haka saida na fada maku lets end him once and for all kuka tsaya, kuna wani kwana kwana, now what if he remembers everything? How we treated him, shikenan…shikenan, we have lost all, wallahi we can’t compete with him,”
Wani irin dogon tsaki fadwa tayi tare da kashe wayarma gaba daya, afiya is not helping d matter kwata kwata
Wayar na tsinkewa afiya ta miqe hankalinta a tashe ta wuce dakin sonata, ta soma banging kofarta,…

Komawa cikin asibitin da fadwa bata sake ba kenan ta shige motarta tabar wajen.
Chan cikin asibiti kuwa, taj na daga zaune yayi saqe yana sauraron hidaya, ganin tana kame kame yasa shi maida dubansa ga calender dake gefen gadon da yake zaune “wait what?? 2023?? Yaushe muka kai 2023? Was i in coma or what?”

Doctor ne ya tari nunfashi sa wajen cewa “sir please you have to calm down first, lets observe you firs, zaka iya tuna last activity da kayi?, i mean inda kaje ko something that you’ve been up to?”
Shuru taj yayi yana kokari tunawa chan kuma ya kama kanshi dake sara mashi yace “i just got into my car, was driving then…then”
Ya dan dakata ya kasa karashewa saboda wani irin Dummm da yaji kunenshi yana mashi, take wani memory din yayi mashi flashing,daya faru lokacin daya masu amnesia,hankalinshi lokaci guda ya sake tashi don kwata kwata he can’t recall sanda hakan ta faru dashi, abu yanda kasan a mafarki haka yake ganin komai, ganin haka yasa hidaya saurin cewa, “hey look at me don’t over think your self, karkayi tunanin komai, ka kwantar da hankalinka i will explain komai idan muka je gida, banason wani abu ya sameka okay?”

Shi Kwata kwata baya jin abunda take fada ma saboda wani hajijiya daya dunga ji, yanda kanshi ke mashi wani dumm, dan dole ya koma ya kwanta kan gadon, yana mai dafe kanshi.

Duban doctor hidaya tayi tace “za a iya sallamarshi yanxu?”
“No ma’am we can’t do that, akwai necessary test da ya kamata ayi mashi,musamman yanxu dana lura kamar he can’t recall yanda akayi yazo nan, and it looks like kamar ya mance da wasu abubuwan it can be a result of shock due to the accident ko yanada wani issue ko lalura kafin ya samu accident?”
“I don’t need any fucking test, Bakaji me tace bane? Dişcharge me right now!”

Ya daka ma doctor tsawa, yanda yake magana daga gani yanada temper, hidaya najin haka ta tabbatar kwarai hankalinshi ya dawo jikinshi he’s back,take taji wani irin sanyi a ranta dukda fargabar da take ciki, agabanshi bata magana daya a musa mata,thats the level of respect he has for her,for now burinta daya kawai ta fiddashi daga asibitin karsu gano wani abun, idan har suka gano to tabbas shima likitoci zasu fayyace mashi komai, wanda hakab zai zame mata babar matsala, don he will suspect her, and he will be disappointed, wanda bazata taba barin hakan ya faru ba, tunda ya dawo yanxu dole tsarin plan dinta ya sauya, she can’t lose to him never…don haka ta tattara duk wani kuzarin daya rage mata ta dubi doctor tace“Can we talk privately about this?”
“Yes” doctor ya amsa ta kafin ya dubi nurse yace “prepare for QR test immediately”
“Yes sir” ta amsa shi kafin su fice gaba dayansu, sabeeha na daga tsaye kamar gunki, tayi saqe kamar wanda aka kwashewa ruwan jikinta, kanta a kasa ta kaasa dagowa ta kalleshi,sai hawaye dake tsiyaya akan fuskanta,har suka fice bata motsa ba daga inda take.

Gaba daya jikinta yayi sanyi kalau,dakyar ta iya dago fuskanta ta kalleshi, ganin ya runtse idanunshi sannan ya dafe kanshi yasa ta sauke kanta kasa, tana tuna yanda yayi mata dazu,babu abunda take sai nazarin komai abunda ya faru ayanxu, yanda yake magana tabbas haka ya tabbatar mata ya dawo hayyacinshi, allahu akbar, yau adduar ta amsu, ya dawo hayyacinshi, kullum fatan allah yasa ya dawo hayyacinshi, abun yazo mata a bazata lokacin da bata taba tsammanin haka ba , ta wani bangaren cikin zuciyarta kuwa fargaba take sosai, sai tsoro daya cika mata zuciya, kamarma bai ganeta ba? Yanda yake kallonta dazu tana hango tsananin furgici akan fuskarci, yana mata kallon wadda bai taba sani ba kamarma ya mantata gaba daya, “innalillahi wa inna ialaihi rajiun” ta soma ta soma furtawa yanayin bugun zuciyarta na sauyawa.

Taj dake kwance ya dafe kanshi babu abunda ke running a mind dinshi sai memories din dake zuwan mashi da bai san yaushe akayi hakan ba.

Hidaya na futowa tare da doctor suka wuce office dinsa, suna zama,ta soma mashi bayanin rashin lpy da taj yayi, sannan ta dora mashi da ya samu amnesia shekara daya da ta wuce around 2022 kuma yanzu tana kyautata tsammanin ya dawo hayyacinshi ne,kuma tana zargin ya warke, saida ta fayyace mashi komai daya danganci health record dinsa kafin ta buqaci a sallameshi da gaggawa, tayi hakan ne don hana doctor yayi wani dogon buncike.
“Inason a sallameshi kawai,akwai consultants dinshi da yake kula da progress dinshi they will take it from here”
“We will do that ma’am amma sai mun tabbatar bai samu wani injury ba daya danganci accident din da sukayi cause he’s our responsibility now”

Ganin doctor na neman jayyaya akan sai yayi bunciken health dinshi yasa tace “he doesn’t need any of that, idan ma yana buqatar hakan
Akwai neurologist specialist din dake managing health dinshi, saboda haka inason a sallameshi”

Dan dole doctor ya amince, aka bashi Referall sannan yayi discharging dinshi.

Sai a lokacin hankalinta ya kwanta ta fito, tana futowa ta nufi dakin da aka kwantar da taj din, har zuwa lokacin yana kwance ya dafe kanshi, bashida natuswa kwata kwata, sabeeha na ganinta kawai taji gabanta ya sake faduwa, tsoronta daya allah yasa ba wata qulalliyar ta qulla ba, karasowa hidayar tayi ta tsaya gabanshu tace “big baby! Muje gida”
Yana jin muryar hidaya ya miqe zaune dukda kanshi na mashi ciwo, cikin izza da sautin muryarshi mai dadin sauraro calmly yace “where’s my car keys?”
Shuru hidaya tayi ta daburce ganin ya kafeta da idanu, “lets go with my car”
Da taimakon hidayar ya miqe tsaye, daidai nan idanunshi ya sauka kan sabeeha itama idanunta ya shige cikin nashi, ganin yana kallon sabeehar har zaiyi magana hidaya ta dakatar dashi “muje”
Sabeeha najin haka ta biyo bayan su suka wuce parking lot inda hidaya tayi parking.
Hidaya ce ta bude mashi seat din gaba ya shige, sabeeha kuma ta shige seat din baya ita kuma hidaya ta zauna mazaunin driver, babu yanda ta iya dan dole ta umarci sabeeha ta biyosu don tasan tabbas saiya tambayi ko wacece ita bayan wannan ma dole yanxu she has to pretend saboda karya fuskanci komai.

Tunda sukabar asibiti Tsit kake ji a cikin motar, hidaya dai har zuwa lokacin ta kasa wrapping mind dinta, fadin irin tashin hankalin da take ciki ma bata lokaci ne, mafita kawai take nema, abun yazo mata a daidai lokacin da bata taba tsammani ba, sai a yanxu take dana sanin qin bin shawarar fadwa, abunda ke bata confidence daya ne ganin kamar bai tuna komai ba, saidai damuwarta daya ayanxu what if ya tuna ranar da accident din daya jawo mashi lossing memory for a year? Inaa bazata taba barin haka ba, dole she has to do koma menene don ganin bai tuna ba, she won’t allow him to remember that, idan ya tuna shikenan komai ya wargaje, bazatayi moulding dinshi yanda ta saba ba bayan wannan ma zatayi lossing yardar dayake mata for over those years, yama za ayi ta bari ya gane she’s behind all of this? No never, she will never allow that, he trusted her all his life, itace komai nashi, baya tsallake maganarta kuma bai taba ba koda sau daya ne kaf rayuwarshi, kuma ayanxu ma for the second time thats what she’s going to use.

Sabeeha dake zaune abubuwa da dama ke yawo a kwakwalwarta, sai ayanxu tunanin mutabb yazo ranta, ayanda taji wajen likitan dayayi attending dinsu ya shaida mata su biyu kawai aka kawo asibitin, fatanta allah yasa ba wani mugun abu ne ya sameshi ba.
Bayan wannan ta soma tunanin meysa ake binsu a baya kuma akeson kashesu? Su waye suke binsu a baya? Ko hidaya ta gano waye mutalib? Ita kadaice kawai tazo ran sabeeha a daidai wannan lokacin, kuma tasan itace ke nemansa, don mutabblib din ya fada mata da kanshi, gaba daya ta dauka mutuwa zasuyi data tuna yanda truck dinnan tayo kansu sai kawai ta runtse idanunta tunawa da yanda taj ya damqo hannunta a lokacin harya furta allahumma ajirninfee musibati, tabbas a daidai wannan lokacin ya soma dawowa hayyacinshi don bata taba jin yayi addua neman tsari ba, ko yayi magana irin ta masu hankali ba.
Tama rasa me zataji aranta, dadin dawowa hayyacinshi ko akasin haka?
Tana cikin wannan tunanin ta dago da kanta ta kalleshi, gashi dai taj din data sani ne amma yanxu sai takejin kamar bashi ba, saiya sauya mata lokaci guda kamar bashi ba, wani irin kwarjini da haiba take gani a tattare dashi, har zuwa lokacin idanunshi a rufe yayi relaxing akan kujerar gaba har suka karaso gida, da kafarshi ya fito daga cikin motar hidayar, yana fitowa yabi gidan da kallo, its feel strange to him sai yake jin kamar ya dade bai shugo gidan ba, zagayowa inda yake hidaya tayi tace “muje”
Gaba yayi hidaya na bunshi a baya,sabeeha ma ta mara masu baya.

Harya daga kafarshi zai shiga sai kawai ya dakata,hidaya fa gaba daya hankalinta a tashe yake yanxu da duk wani motsinsa, ganin yaqi motsawa daga inda yake yasa tace “muje ka huta”
Ta kama hannunshi suka shige daga ciki, suna shiga ya fara bin gidan da kallo, suna karasowa sitting room suka tadda ammu da tareeq da fadwa a zaune, sun sakata gaba suna sauraron labarin warkewar da taj din da yayi lokaci guda.

Ammu na ganin shugowarsu tayi saurin miqewa dukda tana jimamin mutuwar mijinta hakan baisata yi guda ba ta karaso insa yake ta rungumeshi sai hawaye, “allahu akbar allahu akbar, ina godiya ga Allah, oh my sweet boy you’re back? You remember me? Ka tuna ni?ashe dai zuwana yayi albarka, masha Allah yanxu hankalina zai kwanta,” ta karashe tana hawaye, taffin hannayenta na kan fuskanshi tana shafashi kamar yau ta fara ganinshi tsabar murna.

Da mamaki yake kallonta yana kallon su fadwa dake kallonshi harda tareeq, dukkansu ba karamin tashin hankali suke ciki ba, fadwa da hidaya sai kallon juna sukeyi kamar wasu munafukai.

Dakyar ya dake dukda yana jin zafi aranshi gashi ya zama so confuse da alamarin ya Dan rankwafo ya Rungume ammu tsam a jikinshi yana dabbing bayanta,cikin natsuwa da muryarshi mai daukan hankali yace “how can i forget you my fav aunt,I’m sorry for making you worried “
Kallonshi ammu tayi hawayen farin ciki na sauka kan fuskanta tace “tell me meke damunka yanxu? What are feeling now? Are you okay?babu abunda ke damunka?”
“I’m fine ammu”

Fadwa datayi tsuru ta kasa motsawa saida tareeq ya tabo ta ta kalli taj din ta soma yaqe, tace “alhamdulillah! How are you feeling now? We were so worried about you,”
Dagowa yayi yanayin fuskanshi lokaci guda ya sauya ganinta da yayi kawai kamar baya son magana yace, “I’m okay now!”
Kauda idonta tayi ganin irin kallon daya mata,sai yanxu ta kara tabbatar da yayi recovering, idan zaima kowa magana ko zai amsa mutun haka yake banda hidaya, shiyasa suke mashi kallon mai ji dakai da nuna isa dukda qani ne a wajensu, kwarjini yakema kowa.

Tareeq ma baiyi shuru ba hardashi a masu nuna murnar samun lafiyar tashi a fili.

Shidai taj haka yabisu don harga allah baisan akan me suke magana ba kawai dai ya bisu a haka ne, kanshi fal yake da neman amsoshin tambayoyin da ke ranshi.

Ammu ce ta sake kallonshi har lokacin bata bar mamakin ganin ya samu sauqi ba compare to last time datazo lokacin mutuwar khaal, lokaci guda ya sauya kamar bashi ba, da yana daga tsaye sai ya dunga dariya yana wasu abubuwa kamar na yara, lokaci guda kuka ya dawo asalin taj din da suka sani shekara da shekru,sai kawia ta sake fashewa da hawaye tunaw ada yanda khaal ya damu dashi sosai, kusan kullum saiya kirata kafin ya rasu, bashida magana saita taj, ita ce shaidar aon da khaal kema taj, ya shiga damuwa sosai lokacin da taj din ya samu amnesia ya manta komai ya manta koshi waye ma gaba daya.
“How i wish khaal na tare damu, he will be so happy to see your recovery”
Tunda ta fara magana taj ke kallonta, bai gane inda maganar tata ta dosa ba, Hidaya kuwa na jin ammu na shirin baro mata aiki ba zato ba tsammani tayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa “mu barshi ya huta tukunna, daga baya sai muyi maganar”
“Kaje ka huta” hidaya ta umarceshi.

Hanyar stair ya nufa cikin natsuwa majestically suka bishi da kallo, har yakai sama ya jiyo muryar ammu na magana, “jeki taimaka mashi mana”
Ta kalli sabeeha dake tsaye , hidaya ce tayi saurin dakatar da ita tace “ammu, please mu barshi, he’s having a tough time now, yana buqatar time shi kadai, and beside doctor yace kar a dunga damunsa”

Kallon hidayar ammu tayi sai kawai ta kauda kanta gefe ta wuce part dinta da take sauka nan kasa kusa dana su afiya, haushinta takeji sosai tun lokacin mutuwar khaal na qin protecting iyalan khaal din datayi lokacin da aka kwace property dinshi da yanda tayi outcasting dinshi harda press conference dinnan datayi, wannan abun ya tsaya mata arai, wannan yana daya daga cikin abunda yasa ammu taji akwai matsala kuma akwai avunda ke faruwa a gidan wanda bata sani ba kuma khaal bai taba gaya mata ba.

Ammu na wucewa su fadwa ma suka bar parlorn ya rage daga sabeeha sai hidaya, kallon sabeeha hidaya tayi yanayin fuskanta ya sauya sosai tace “as for you, as you can see baisan koke wacece ba, he doesn’t remember who you are cause you’re not important, koda wasa let me not see you around him not a single word from you”
Takowa tayi inda sabeehar ke tsaye hidaya tayi kafin ta kure ta da idanu fuskar nan babu digon imani akai tace “its not like he will be happy to have you as a wife, you are nothing but his caregiver, sannan karkiyi tuannin bansan yanda kika shugo gidannan ba a matsayin yar leken asiri, korar daga gidannan shine avu mafi sauqi, idan kinason na barki ki zauna a gidan nan you have to do what ever i said to you, inba haka ba i will make your life miserable, let me give you a sounding warning,not a single word from you, koda wasa naga kin rabe shi, I’m going to do my worst”
Shuru sabeeha tayi saida ta gama sauraronta tass, gabanta na mugun bugu, haka ta dake ta bude bakinta tana kallon hidayar cikin idanu babu tsoro ko fargabarta ko digo tace “kina tsoron karna fada mashi rayuwar da yayi a gidan nan lokacin da baya cikin hayyacinshi? ki kwantar da hankalinki, bazan fada mashi komai ba, saidai inason ki sani allah baya barci yana kallon duk abunda ke faruwa, yanda ya dawo hayyacinshi lokaci guda alokacin da babu wanda yayi tsammanin haka, a sannu a hankali zai tuna komai, its just a matter of time duk karyar da zaki fada mashi bazatayi tasiri ba saboda karya fure take bata yaya,i dont care if ya karbeni a matsayin matarsa, all i know is that I’m his wife and no one can change that”
Tana kaiwa nan tabar inda hidayar ke tsaye ta nufi part din data taba zama a ciki, lokacin sa jamid ya kaita, daman ba tun yanxu ba take shanye duk rashin mutuncin da hidaya keyi, haka kawai taji lokaci guda wani confidence yazo mata, daman tana threatening dinta da taj dinne, tsoron kartayi mashi wani abu yasa take yin shuru bata cewa komai kuma bata iya tunkararta, tundaga ranar da mutallib ya fada mata cewa hidaya ce sanadin accident din taj da abubuwan data dunga yi donta cutar dashi da kwayar data dunga dura mashi wadda ta kusa illatashi tundaga ranar ta daina jin tsoranta gaba daya kuma tayi allawarin saitayi protecting dinshi, tsoron hidayar babu abunda zai haifar mata saidai yayi ta bata damar yin abunda taga dama, yanxu kuwa data tabbatar ya samu lafiya batajin hidayar zata iya yin wani abun,ada datayi ma don taga bashi cikin hayyacinshi ne yanxu kuwa abunda take mai hankali bazai dauka ba, ko kusa ma bazata iya kokarin citar dashi ba ayanxu.

Tunda ta fara magana har yakai aya har tabar wajen hidaya bata gama dawowa daidai ba mamaki ya gama cikata, Ai kamar ta bugama hidaya guduma akai Haka taji, Saqe tayi tama kasa yin komai, bata taba expecting haka daga wajen sabeehar ba…


***
Bangaren taj jiki a mace ya shugo part dinshi yabi ko’ina da kallo, komai na part din nashi ya sauya, kamar anyi refurnishing komai, komai looks weird to him, ga kanshi sai wani tsannain ciwo yake mashi sosai, bayason tunanin komai don da zarar ya fara tunanin yakeji kanshi na sarawa.

Abund aya lura dashi shine, duk yanda akayi wani abu ya faru dashi, ko yayi loosing memory dinshi ko kuma he was in coma, definitely akwai abund aya sameshi, don babu yanda za ayi ace rana daya kawai ya bude idanunshi ya ganshi a 2023, how is that possible, he can recall is bayan ya dawo daga london, ko sati gida baiyi ba koma menene ya faru dashi.
Da kyar ya lalaba kanshi ya wuce bedroom dinsa yanajin wani irin zafia ranshi ya rasa dalilin, dakin ya shige nan ma an sauya komai, duk wasu abubuwan shi na amfani babu.
Idnaunshi ne ya sauka kan gadonshi, kamar mai son tuna wani chan kuma ya kauda idanunshi ya sauke Sigh of relief gaba daya jikinshi ciwo yake mashi babu abunda yake nema sai shower, kai tsaye ya nufi kofar bathroom dinshi ya bude, kallon bathroom din yayi har idnaunshi ya sauka kan towels din dake rataye guda biyu, yellow da white, juyawan da zaiyi idanunshi ya sauka kan panties dake hange akan hangers, yayi mamaki sosai ganin panties din saiya fara tunanin kodai wani yayi mashi amfani da part dinshi? To ko hes mistaken ba nan ne part dinshi ba? Ko anyi re-arranging gidan ne?” Tambayoyin daya dunga ma kanshi kenan.
Basar da zancen yayi ya soma rage kayan jikinshi, farar fatarshi ta bayyana sosai, kallon kanshi ya dunga yi ta mirror, ya rame sosai, he feels so light, sai yake ganin kanshi kamar bashi ba.
Ya dade sosai a bathroom yayi wanka kafin ya fito daure da towel a kugunshi, kasa dauke idanuna nayi akanshi, gaba daya ya sauya kamar bashi ba, lallai hankali ke gani badai idanu ba, yanxu da hankalishi ya dawo jikinshi ya koma mutum completely.


closet room ya nufa yana shiga ya bude closet din,gaba daya babu kayanshi ko digo daya, sai set of kaya ne farare a jere a ciki sai kuma kayan mata daya gani daga gefe a Jere fess fess sai kamshi suke mai dadin gaske.
Mamaki ya dunga yi har zuwa lokacin, tsuka kawai yayi ya rufe closet din kawai ya futo ya wuce bedroom din ya kwanta….


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 5 · 0% Book details