← Book details Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. Local reading mode
CHAPTER 29 OF 66

Chapter 83

Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 21 min read

Abuja nigeriaa…
Cikin sauri sauri take tafiya, kamar zata tashi sama,tana isowa gargajiya food service spot ta shige ciki, cikin wajen gaba dayan ma’aikatan kowa ya hallara, daga ganin wannan kiran kowa yasan ba lafiya ba don kaff ma’aikatan kowa na taaitsaye.
Madam ce ta shigo sannan ta bada umarnin duk kowa ya zauna a kujerun wajen aka zazzauna ta soma jawabi.
“Nayi aiki daku lafiya kuma naji dadin aiki daku, saidai ina bakin cikin shaida maku ayau zan rufe gargajiya spot saboda zan koma kasar waje da maigida na da yaya na gaba daya, ina mai maki fatan nasara,”
Hankali tashe wata mata tace “innalillahi madam mun shiga uku, wannan aiki dashi nake cida yayana goma, mijina ya rasu shekara uku da suka wuce, ya zanyi ni luba”
Wata ma tace “madam da aikin nan nake biyan kudin makaranta na, babana ya rasu”
Hadiza kuwa jikinta har kyarma yake, samun aiki a abuja da za a baka dubu ashirin a wata ai da wuya, saikaci kwakwa, ga wahalar rayuwa innalillahi wa inna ilaihi rajiun, batayi karuwamci ba inna na raye bazata iya ba yanxu, badan haka ba da shi zata fara kawai wannan masifa har ina, inna ta tafi ta barta da baqar wahala.
Haka tayi bankwana da yan uwanta ma”aikata ta kara gaba, kamar zata fadi tsabar tashin hankali, gidan jamila ta wuce direct allah yaso mijinta baya nan tayi zaman dirshen ta shaida mata komai kamar tayi kwalla, ita ta kanta kawai take yanda zata rufama kanta asiri, ga dan iskan yaron nan dayake jail koya zatayi dashi oho, ga sabeeha data kara zame mata wata masifa achan gefe.

“Hmm kedai bkya nemawa kanki sauki hadiza,keko kikeda yanda zakiyi, wallahi hanyar samun kudi a hannunki take kawata”
“Ban gane ba jamila”
“Matso kiji”
Wasu yan qusqus jamila ta mata tayi saurin zame kunnenta tace, “jamila kinada hankali kuwa? In jefa kaina cikin masifa kenan, ki chanza min shwara wannan batayi ba, bazan taba zuwa nanba da sunan zama ko aiki wallahi kinji na rantse, ko kwakwaran nunfashi bazan iyaba don tsohon tabon dana rufeshi da kyalle zan bude, kuma ba zaiyi kyan gani ba.”
“Hmm hadiza kennan, wallahi kina bani mamaki, shin kin manta da ajiyar da kikayi ne? Idan kin manta saina tunatar dake, ke kike da babbar ajiya a ahalin nan, kodan ajiyar da kikayi ina fatan zaki dawo hayyacinki, idan kinje kiyi ramuwar gayya,“
Shuru hadiza tayi tana nazari chan kuma saita fara murmuahi harda hawaye “kin tabo min inda kemin kaikayi,”
Tafawa sukayi jamila tace “kokefa yanxu nasan asalin hadiza ce ke gabana”

Washe gari da sassafiya hadiza ta hada komatsan ta su fanka ne ta siyar duka harda katifa matar gwari ta saya, su tukwane gado babu abunda ta bari, sabeeha dai ta zuba ido tana kallon ikon allah, batada ikon tambayar maman tata, saida aka kwashe komai tass ya rage ko katifa babu sannan hadiza ta fidda gana masgo dinta waje sannan ta wula ma sabeeha leda tace “tattara kayanki ki fito”
Tana hadasu cikin ledar ta futo hadiza ta kulle kofar sannan tayi gaba sabeeha taja buhun suka kara gaba ko sallama.
Anan bakin kofa ta bawa gwari mukulli tace abawa landlord idan yazo don ko haduwa dashi bazatayi ba sabda akwai dubu goma da zata biyasa amma taci banza.
Gidan jamila suka karasa sabeeha ta tsaya bakin kofa ita kuma ta shiga daga ciki saida ta shafe wajen 30mins sannan ta fito.

Sunyi tafiya mai tsayi har bakin titi kafin su samu drop, nanda maitama saida suka bada wajen dubu biyar hadiza sai faman masifa take, tafiya suke mai dan tsayi har suka iso area din, kamar kullum ko’ina a a gyare fess fess babu qazanta babu hayaniya, har suka karaso estate din, nanfa ake daru drop yace bazai kara koda second daya ne a wajen ba nan yayi dropping dinsu suka karasa bakin entrance sojojin wajen suka taresu, duk bayanin da hadiza ta masu baisa sun barsu ba don ance ta kira daga chan a kira batada number kowa haka suka zauna gefe jugum sabeeha ga uban buhu aka kamar wadda tayi hijira.
Sunfi kusan 30mins suna kallo motoci na shigewa babu dauki, cikin ikon allah saiga motar hamad, kallo daya yayi ma sabeeha ya ganeta dan bayajin zai iya mance fuskarta, fuskar look so familiar.

Nan ya tambayi security meysa suke zaune suka shaida mashi ay gidan santuraki suke son zuwa and they couldn’t contact anyone from inside, nan ya bada umarnin abarsu su shiga dayake sun sanshi basu musa ba yayi gaba da motarshi su kuma aka shaida masu zasu iya shiga aka bude musu kofa, tafiya sukayi mai shegen tsayi kafin su karaso main gate entrance din mansion din santuraki’s, suna karasowa nan ma ba a tambayesu ba aka barsu suka shiga, sabeeha sai mamakin gidan take, tabbas nan suka zo kwanaki.
Direct babban part din hadiza ta nufa kai tsaye, da sallama suka danna bell aka bude kofa, kamshin tiraren wuta da sanyin ac ya masu sallama, dqman sai zafin rana suke saboda dadewa da sukayi, idanun sabeeha har wani jaja suke, tayi laushi sosai fuskanta harta soma duhu.
Yar aikin ce ta jagorancesu parlorn farko suka zauna a kasa, sannan ta wuce ciki donta sanar da masu gidan.
Suna nan zaune maid din ta sake futowa ta bude kofar nanna ta shigo da sallama, tana sanye da lafiyayyan lace ga kamshin dadi da take Masha allah, matar nan bata tsufa kwata kwata, zaka rantse bata haura 50 fa, skin dinta sai glowing yake.
Harzata wuce walkway ta hango su zaune, har wata ajiyar zuciya hadiza ta sauke data ganta, “ah ah hadiza kune”
“Eh hajiya mune, ina wuni”
“Lafiya lau hadiza ya gida”
“Lpy lau,”
Sabeeha ma ta dan dago ta kalleta cikin sanyi tace “ina wuni”
“Lafiya lau, ya sunanki”
“Fatima”
“Masha Allah sannu fatima”
Daidai nan anne ta sauko daga sama, tana sanye da glass fari akan fuskanta.
Main sitting room ta wuce nan, yar aikin ta karaso first parlor ta shiada masu cewa hajiya ta sauko.
Nanna tayi gaba hadiza na biye da ita a baya har sabeeha ta miqa hadiza ta dakatar da uta ta koma ta zauna.
Suna shigowa hadizq tayi saurin zama kasa ta gaisheda anne cikin aminci, nanna na daga gefen anne hadiza ta soma magana harda yan hawayenta. “Hajiya daman ina neman taimako ne, gidan da muke zaune ne akayi rusau, gashi bamuda wajen zuwa gashi inda nake aiki ma madam din ta sallamemu gaba daya saboda zata koma kasar waje da iyalanta, shine nace ko bari nazo neman taimako, ko aikatau ne zanyi”
Shuru anne tayi tana sauraronta har takai aya, kallon anne nanna tayi jin tayi shuru tana kallon hadizar, tasan dakyar ne idan anne zata barta tayi aikatau a cikin gidan saboda ba ayi rabuwar mutunci ba kwata kwata lokacin da ita da babarta sukabar aiki a gidan, saidai kuma komai ya wuce ana maganar abunda ya faru shekara da shekaru kennan fa.
Da mamaki gaba daya daga nanna har hadizar suka dago jin abunda anne ta fada “ba damuwa, albarkacin diyarki ku zauna, duk wani hidimarku ci da sha da sutura na dauka, saidai kuma zaku dunga aikin, sannan duk wata za a biyaki”
“Kai nagode Hajiya, kin gama mana komai, ni basai kin biyani bama, allah ya saka da alkahiri”
Nanna taji dadi sosai doj batayi tsammanin anne zata yarda ba kwata kwata, saboda anne bata mantuwa kwata kwata, idan ta baka chance ta yarda dakai kayi betraying dinta ko kaci amanarta bata sake yarda da mutun.
Nan indo ta shigo ta wuce da hadizar donta nuna mata masaukinsu, nan guest room dake kasa kusa da dakin ma’aikatan gidan saidai ba irin dakunan su bane wannan ya danfi kyau tunda akwai gado akwai wardrop dresser harda ac ma da dan carpet.
Bathroom dinma ba laifi akwai komai shower ne da komai.
Sake shugowa indo tayi ta aje masu ruwa da lemo, nan hadiza ta roketa data kira mata sabeeha, suna gab da wucewa anne ta kira indo, har sabeeha ta tsaya anne tace ta karaso itama, tana zuwa ta dan duqa har kasa ta gaishe da anne, kallonta sosai anne keyi babu kiftawa sai kuma chan tace “ya sunan ko?”
Tace “fatima”
“Kinyi karatun boko?”
Shuru sabeeha tayi tama rasa mw zata ce mata, kawai saita tsinci kanta da kasa yi mata karya tace “eh, inda nayi aiki sun sani makaranta, ina gabda gama course din da suka bani na dawo”
“Me kika karanta?” Anne ta sake jefo mata tambaya
“Business ad”
“Shekarunki nawa?”
“Ashirin da biyu..da uku”
Murmushi nanna tayi tana hango ladabi da hankali a tattare da yarinyar, babu alamun rawar kai kwata kwata a tattare da ita.
“Jeki” anne ta dauke idanunta daga kan yarinyar sannan ta maida ga news din data dauka dake kan table.
Suna bari wajen nanna tace, “oh wani ikon Allah, yanxu wannan yar hadiza ce babu gigiwa babu hayaniya,lokacin da uwarta ke kamarta akwai hayaniya, larai taita fama da ita, ga neman fada, amma wani ikon allah kwata kwata bata kama da hadiza, yanxu haka kamannin nata ta wajen ubanta ne, allah dai ya jiqan musulmai baki daya ameen”
Anne ta ce “ ameen”

Sallamar anty fadila tasa suka dago gaba dayansu, gefenta hamad ne hannunshi da tray na snacks.
“Anne kuna kasa ashe”
Nanna tace “wallahi fadila yanxun nan na shigo nima”
“Ya office nanna?”
“Alhamdulillah dear ina kishiyar tawa”
“Basu dawo daga school ba ita da abokiyar fadan tata”
Dariya akayi nanna tace “yanxun nan su hadiza sukazo kuwa”
“Hadizq dai?”
“Eh wallahi ashe rusau akayi a anguwarsu, abun tausayi wallahi ko wurin zuwa basu dashi”
“Wayyo allah ya rufa asiri, yanxu anan zasu zauna,”
“Eh ta nemi alfarmar a barta tayi aiki sai a biyata”
Jinjina kai fadila tayi tana tuna rayuwar da sukayi a baya, kai hadiza yar rigima ce ta karshe, dama itace abokiyar fadanta a koda yaushe, basa jituwa kwata kwata har gwanda bahijja, ita dake tanada sanyi sanyi tana daukan rashin mutuncinta, dake tare duk suka taso, idan suka fita kuwa saika rantse hadiza ce yar gida, komai itace a gaba gaba, babu mutunci lol.
Anne dake jinsu batace komai ba ta dubu fadila tace, “cikin kayan laila ki duba ma diyarta kayan da bata so, naga yarinyar kamar batada suturar arziki”
Nanna tace “daman anne dole ay, baki gansu bama gaba daya babu kwanciyar hankali, babu jimar arziki, kai ana wahala a kasar nan, allah ya rufa asiri”
“Ameen” duk suka amsa a tare.
Daga nan suka dan taba hira kadan kadan.
Sabeeha na shugowa hadiza tace “me kika tsaya yi?”
Tsoron kartayi fada yasa tace “ban tsaya ko’ina ba,“
“Zquna” zama sabeeha tayi hadiza na fuskantarta tace “inason na maki kashedi ki bude kunnuwanki karki jawo min masifa, babu ruwanki da harkar kowa mu ba kowa bane face yan aikin gidan, babu ruwan da sha’anin yan gidan indai ba aiki muka fita yiba karna sake na ganki da kowa, ban amince ba kuma ban lamunta ba. Abunda ya shafi rayuwar mu a baya bakida hurumin fada ma kowa, dan wallahi kikayi sanadiyar barinmu gidan nan ko aka koremu hmmm, banida zabin daya wuce na aurar dake ga duk wanda na samu”
Maganar aure data kawo saida yasa gaban sabeeha faduwa, saita nemi jin hawaye na neman sauko mata tayi saurin hana kanta yi.
“Dauka kisha”
Daukan ruwan sabeeha tayi ta dan sha kadan, lokacin sallah nayi hadiza ta miqe ta dauro alwala lokacin har indo ta kawo masu abunci, sabeeha da tun ruwan bunun da tasha da safe bata ci komai ba, tana kallo aka kawo abunci a tray kamshi ya gama bugun hancinta, batayi gigin tabawa ba har saida hadizar ta fito daga bayi itama ta shiga bayin, toilet din yayi kyau kuka a taaftace ba kamar gidan hayan da suke ba, duk sanda ta shiga ta futo saitayi amai sosai, jikinta kuwa sai yayi wani jajaja tsabar jininta baya son qazanta, dauro alwala tayi ta fito, ta koma gefe tayi sallah harta idar, har hadiza ta zauna ta fara ci, saida ta koshi sosai ta kara daga platw din sabeeha kafin tayi gatsa ta tashi tabi lafiyar gado.
Saida tayi nisa sosai cikin barci sannan sabeeha ta janyo plate din taci sauran ta koshi dam ta kora da ruwa, harda juice.
Ya allahu its been long rabonda taci proper abunci wallahi, nama zuqu zuqu har ya soma hawa kanta, allah karka barbu da wahalar abunda zamuci a cikin mu Ameen.

Saudi…
After 2days…
Futarshi yake son ranshi, kuma hidaya na ankare dashi, da inda yake zuwa, da wanda yake haduwa da,wani ikon Allah, allah baibata ikon shaida mutallib ba saboda duk hoton da za a dauko mata dake nuna tare da mutallib yake ba a ganin fuskarshi saidai tasa a bincika mata waye shi, ina suka fara haduwa kuma ina taj din ya sanshi.
Mutallib yasha wahala sosai wajen neman detective dinnan kuma allah ya bashi nasara, yabar kasar ma gaba daya amma haka mutallib ya nemoshi sannan ya mashi bayanin komai ya roki alfarma a wajenshi, da farko detwctive din ya nuna baisan komai ba kuma bazai iya taimakonshi ba dalili kuwa wannan case din daya taimaka wa jamid suka bude na khaal yayi sanadiyar aikinsa, daga manyanshi, ya rasa komai ta sanadiyar hakan,gashi ya nemi jamid sama da kasa ya rasa baisan cewa ya samu paralyse ba kwata kwata, sai a yanxu mutallib ke fada mashi, bayan ya bama jamid information dinnan ya hadu dashi a ranar washe gari kuma aka samu labarin ya samu paralysis, abun ya bama detective mamaki wannan yasa shi tunanin sosai sannan yace zai nemi mutallib din if hes ready to open up, mutallib yayi understanding detective din is being cautious,wannan yasa bai matsa mashi dole saiya taimakeshi ba.

Cikin ikon allah a daren ranar wallahi detective din ya kirashi ya zayyane mashi komai da binciken da sukayi shida jamid, da wanda suke suspecting don anyi fabricating results din gawar khaal.
Mutallib baiyi mamakin jin wannan zancen ba, saidai kuma ba kowa ne ya dace yaji wannan ba sai taj, wata qila wannan zai zame mashi eye opener ya kara tabbatar da akwai kullaiyar da akayi akan batun accident dinshi, sannan wannan zai kara tabbatar mashi da khaal has always been there for him.
Rokonshi mutallib yayi akan yanaso su hadu idan babu damuwa, da farko detective din yaso qin amincewa saida mutallib ya mashi bayani qalilan daga cikin abunda ya sani gameda taj, daga baya da detective ya gamsu ya amince da zasu hadu washe gari.
Yana kashe wayar ya kira taj, yana dagawa ya sanar mashi akwai wani abu dayayi bincike akai, damasaidai kuma ya wayance da detective din abokinshi ne tun yarinta, kuma akwai wani abu daya sani game da abubuwan da suka faru a baya don yayi handling file din khaal lokacin da akace ya mutu.
Taj yayi mamaki kuma yaji dadin wannan zancen wannan yasa sukayi planning haduwa da mutallib din gobe.
Yana kashe wayar ya sake duban hannunshi, yanxun nan yazo daukan abu a drawer din gefen bedside dinshi yana budewa yaci karo da black box din da sabeeha ta taba tsintowa a cikin bathroom, jujuya black box din yayi da kyau yana nazarin abubuwan da dama, instint dinshi na bashi dis is suspiciou, wannan yasa ya fara duben duk wani lungu da sako na cikin dakinsa, haba waa, he was double shocked, no triple shocked, ya tsinci wajen guda uku a cikin bedroom dinshii da closet dinshi,no one can tell him koma menene don yana gani ya gane its a spy recorder, waye ya saka? Yaushe aka saka? Meysa aka saka? Duk wannan tambayoyin nashi babu mai bashi amsa saidai kuma yanxu ya kara tabbatar da something is terribly wrong.

Washe gari da safe fadwa na tashi first thing first recorder bedroom dinshi ta saka, daman duk safiya da voice dinshi take tashi, inda yake kiran sunan allah kafin ya miqe ya wuce bathroom, koda ta saka na bathroom dinshi is meant for sound din tafiyarshi,da wankanshi, that keeps her wanting him more and more taita imagining gata nan ita dashi a bathroom kai thats so creepy..🤮

Yau to her surprise taji blank, anyi disabling recorders din, tsabar bacin rai batasan sanda ta buga wayar ba a kasa duk tsadarta ta tarwatse kasa ta fara ihu kamar mahaukaciya.
Bangaren taj yana tashi da safe as’usual ya gama shirinsa yayi ficewarsa.
Yana cikin tafiya yayi noticing kamar ana binshi a baya, batun yanxu ya lura da ana binshi ba kuka bai damu ba but this time around dole yayi stepping up.
Haka yayi motar wani mugun speed take ya bacema motar dake binshi a baya.
Bai tsaya ko’ina ba sai cafe din da sukayi zasu hadu da mutallib, coffee yasa aka bashi da croisaant yayi breakfast fast dashi yana gamawa saiga mutallib ya iso, shima dai baiyi breakfast dinma so anan yayi order sukaci suka koshi sannan suka fita a tare, motar taj na gaba mutallib na biye dashi har suka iso inda zasu hadu kusa da wani beach haka.
Sun dan jira for about 30mins detective ya iso, yana sanye da normal kaya ya saka facing cap, chan wajen wani open place suka zauna detwctive din ya dubi taj, kamar dai shi ya gani a news da ita hidayar kwanaki, wanda akace bashi da lafiya,
“This is tajudeen, nasan kasan koshi waye basai na maka bayani ba, inason musan komai please karka boye mana”
Jinjina kai detective din yayi sai kuma ya danyi dariya yace “banyi mamaki da akace bakada lafiya ba yanxu kuma naga akasin haka,”
Da mamaki taj ke kallonshi don son jin karin bayani, “on the 20th oct of last year, jamid yazo ya sameni da batun case din murder daya faru on the 10th of july, because he couldn’t believe if the death of the person was actaully a murder or a planned murder after the accusation and cases that followed next, on the 9th of july you were kidnapped kaida matarka, and the next day an tsinci gawar uncle dinka, that same day an samu hoton motar da akayi kidnapping dinka dashi wanted kidnapper din tare da uncle dinka, everything seems planned cause it doesn’t add up, aranar da akayi hoton aranar ya mutu, jamid convinced me sannan yayi min pointing out kan cewa this doesn’t add up and i believe that, first of all abunda muka fara questioning shine, what if he was framed? Yes it can be possible but how can we be sure if that? And we got an answer, nida jamid we checked on the forensic results which shows that he was dead, anan mukayi noticing wani abu, saidai the next day daya kamata mu hadu da jamid bamu samu mun hadu ba, i lost his contact and i was questioned for opening the case which leads to my dismissal,na nemi jamid na rasa, I couldn’t contact him, sai yanxu danake jin labarin he had a paralyze, i was shocked, and i definitely suspect ana kokarin ganin an toshe duk wata hanya da zai bayyana gaskia.
Shuru ya danyi chan kuma ya dan nunfasa ya dubi taj cikin ido yace “the first person jamid yayi suspecting yanada hannu cikin wannan ba kowa bane face mayarshi, the ceo of taheel and i can say she’s the primary suspect”
Take idanun taj sukayi jaa sukayi rudu rudu, jijiyoyin kanshi suka fito sosai ba kadan ba, ganin yanayinshi yasa mutallib kama hannunshi ya rike alamun ya saita kanshi.

“Akwai abu daya dazan fada maku, da farko gaskia banyi niyar fada maku ba amma ina ganin you need to know, koda akayi dismissing dina banbar bincike ba, anan ne ma na gano zoben dake hannun gawar da akayi declaring ta shi deceit din da aka tsinceshi dashi wanda ya kasance nashi, akwai traces din prints guda biyu da suka banbanta a jiki, we found of someone else’s on the picture, i couldn’t tell jamid results, but wannan gawar ba gawar khaal bace”

Gaba daya zuba mashi idanu taj da mutallib sukayi in full if shock and surprises, abun yafi tada ma da taj hankali,
“Kana nufin kace akwai possibility din khaal
Bai mutu ba?”
“Yes wannan gawar ba tashi ba”
“Innalillahi wa inna ialaihi rajiun” hankalin mutallib fa ya tashi sosai ba kadan ba har yaso yafi taj dinma.

Shifa taj is lost tunda aka ambaci hidaya as a primary suspect, saiyafara reviewing kanshi? What is he digging? Gabanshi na mugun faduwa yake wannan nazarin.
Karya ta mashi kenan? Its all a lie? Duk abunda ta fada game da khaal duk karya ne? Tace khaal ne ke kokarin ganin ya kasheshi saboda yaci gadonshi? Yanxu dukka karya ne? Innalillahi wa jnna ilaiahi rajiun

Wallahi taj baima san sanda detective dinnan ya kara gaba ba, he’s so lost in his thoughts, mutallib ko ya rasa tunanin mai yake, yanxu akwai possibility din khaal
Na raye? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan wani irin baqin zalinci ne? Saiyakejin gwara kawai ya fito fili ya fada ma taj gaskia kawai.
“Tajudeen..akwai wani abu danake so na fada maka, but ina fatan zaka saurareni, duk wani abu dakaga ya faru yana da dalili”
Miqewa taj yayi tsaye a fusace, bayajin zai iya tsayawa yana sauraron wasu magnganun kuma, wace iriyar dark rayuwa yake living bai sani ba? Is he blind or what,
“Dan allah ka saurareni kaji abunda zan fada maka, tabbas ni ba ayanda ka sanni nake ba, ni yaron khaal ne kuma nine na hannun damanshi wanda ya yarda dashi ya amince dashi, banyi approaching dinka da wata manufa ba sai alkahiri taj, kuma sai dan ganin na rike alkawarin dana daukar ma khaal ”
Hannu taj ya daura a kanshi ya shafa sukan kanshi ya sauke kan kasa jijiyiyin kanshi sun fito rudu rudu, ya dubi mutallib din yace “you’re all
Insane, me kuka maidani ne? Kwallon wasa? Da wannan zai buga wannan ma ya buga, does making fool of me make yall happy?”
“Listen to me taj, abunda kake tunani ba haka baneba kuma duk avunda detective ya fada maka gaskia ne, sannan akwai boyayyen sirrin dake boye wanda kai kanka baka sani ba na bari sai…

Hannu ya daga mashi bai sake kallonshi ba azafafe rai a bace yabar wajen.
Da wanne zaiji, wannan batun wannan detective din ko kuma batun mutallib? The guy he trust’?
Menene boyayyan sirrin da yake magana akai, he needs air to claim duk maganganun da kunanahi suka jiyo mashi,
Mutallib ya miqe yabi bayanshi, ranshi a bace don ya kasa gane inda taj din ya dosa gaba daya, gaskiayr ce baya son ji ko kuwa.
Harya bude kofar mutallib ya maida kofar ji kake bam.
“Why are you running away from all of this bayan sanadinka ne duk hakan ke faruwa, you don’t want to listen to me at all”
“This is all my fault???? You’re saying this is all my faulttttttt!!!!”
“Yesss it’s all your fault mutallib ya daka mashi tsawa, tabbas khaal duk halin daya shiga ta dalilinka ne, wani irin mutun ne kai? why can’t you understand that, daga rayuwar ka achan uk har zuwa yanxu wallahi wallahi bazanyi kaffara ba saboda khaal kake cikin koshin lafiya har kakai yanxu harka zama abunda ka zama, kana tunanin waye yayi supporting din business dinka lokacin daka fara achan uk? Ba kowa bane face khaal, kana tunanin waye ya dunga saving spot dinka a lokacin da ake neman tauye maka hakkinka? Ba kowa bane face khaal, kana tunanin waye ya tsaya maka, yayi protecting dinka ya soka tsakani da Allah? Ba kowa bane face khaal din.., your life was in danger this whole time kuma bai iya runtsawa kona second daya ne, tunaninsui ya rayiwar ka zata inganta, ya zaka samu lafiya, ya zaka bude idanunka ka kalli gaskiayra dake gabanka,”

Bude kofar taj ya sake yi ya shige daga ciki ya kunna tare da yin reverse a zuciye yabar wajen.
Yakai awa yana tuku magnagnun mutallib na yawo kanshi, wa zaiyi trusting? Wa zai yarda dashi,? This is so much for him to handle.

Wato shifa ga gaskiayar a gabanshi amma ya kasa yayi accepting dinta, don bai taba tsammanin jin haka, kaii ya Allah.. tsantaar betrayal baiba, abunda kafi yarda dashi kaf rayuwarka lokaci guda kaga duk karyace ba hakan bane abun da zafi, its hard to believe and accept, he’s hurt, lies upon lie, tunda ya fara binciken nan baiji alkhairi ko daya ba.


Abuja nigeria…
Yau satinsu guda, har sabeeha ta soma farfadowa, daman bataji hutu bane, suci mai kyau su sha mai kyau, ga kaya da anty fadila ta kawo na laila da suka dan kwana biyu aka bata, hadiza bata hanata sakawa ba kuma bata ce komai ba don itama an bata har kala biyar masu kyau.
Aiki kuwa suna yinshi, yawanci ma sabeeha ce keyi, zata tashi da asuba ta shiga cikin yanmatan gidan masu aiki suyi tare, yawanci ma dai ita wanke wanke ake barinta dashi sau kuma harkar yanke yanken veggies da gyaran tafkekwn kitchen din.
Duk inda ta zauna da mutun kafin ta tashi saita shiga ranshi, dukda batada magana bata da hayaniya kwata kwata, ahankali ahankali ta fara sakewa da yan aikin gidan dukda tana kaffa kaffa da kowa sbd warning din mamanta, hadiza ko ba laifi itama tana fitowa aikin, yawanci itama dai aikin cikin gidan nan takeyi, banda sama don akwai masuyi a sama, da farko ma dai bata shige ma mutanen gidan da yake kuma ansan juna haka fadila ke dan janta jiki.
Hamad ko tunda yasan sabeeha na gidan koda yaushe yana part din anne donma dai suna shiri sosai shida ita don tace shine fav dinta, duk shigowannan da yake bai taba haduwa da sabeehar ba kwata kwata ko sau daya kuma so yake ya ganta koda sau daya ne.
Laila da maya ko basu taba haduwa da ita ba basuma san da wasu sabbin mutane cikin gidan ba, don basa zaman gidan kullum suna makaranta weekends kuwa kowa tana part dinsu, maya na wajen anty laila, inta rayo mata ta tafi yawanta ta dawo, laila karama kuwa tana wajen mummynta.

Akwai ranar wata saturday da aka kawo provisions da yawa da za ayi restocking store, indo tasa yan matan zuwa inda akayi parking motar kaya ta gaba su kwaso a shugo dashi ta back yard, a cikin masu debowa harda sabeeha,suna cikin kwasowa hamad ya fito daga main entrance, tunda ya hango sabeeha ya kasa wucewa ya tsaya yana mai kallonta sosai irin kallon kurullan nan,harya wucewa ma ganinshi.
Chapter 29 · 0% Book details