Chapter 106
Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 51 min read
Kai kana ganin yanda take tauna chewing gum dinna tana juya ido kasan bata zo da alkairi ba kwata kwata, nan bakin gate dinsu da shima ba a shiga sai an nemi izini daga ciki ta tsaya, ta gaisa da securities din wajen sannan ta shiada masu wadda take nema.
Saida suka dakatar da ita don sai an kira daga ciki kafin ta shiga.
Rabi na daga zaune tana ninke kayayyakinta data wanke wayarta ta soma ringing voo voo, tana ganin daga waje ne tayi saurin dauka don normally ita ake kira idan za ayi baqi ko idan mutane zasu shugo,
da sallama ta daga security din ya soma magana, “theres a visitor who’s here for rabi”
“Sorry who???” Rabi ta tambayeshi
Kallon jamila yayi yace
“Madam your name”
“Jamila..” jamila ta bashi amsa
Ya maida wayar kunenshi yace “jamila..”
ganin irin kallon da yake mata don wayar har zuwa lokacin tana kunnensa yasa tayi saurin cewa
“Dan allah ko zaka bani ita muyi magana.”
Har zai katse wayar don rabi ta shiada masu babu baquwar da suke expecting ya bawa jamilar wayar.
“Hello!! Hello kina jina, dan Allah ki futo yanxu cikin gaggawa, abu ne mai muhimmaci zan fada maki”
“Wacece wai wannan din?” Rabi tayi magana, “kiyi gaba wata kila kinyi mistake banan gidan bane.” Rabi ta sake magana
“Ki dan dakata kiji, ni kawar hadiza ce, wadda nazo kwanaki,” jamila ta tari nunfashinta cikin gaggawa.
“Toh ay saikiyi bayani yanda ya kamata, bata fada min cewa akwai wadda zata zo ba” rabi ta bata amsa
“Ay ba wajenta nazo ba wajenki nazo, ki futo kona minti biyu ne dan Allah abu ne mai mahimmanci nake tafe dashi”
dan jinkirtawa rabi tayi tana nazarin mezaisa kawar rhadiza ta kirata kuma wai tazo ne saboda ita? kodai wani abun hadiza tayi? ko fada sukayi da kawar tata don daga yanda ranar datazo ta ganta ta gane suna da kusanci sosai, don da farko ma ta dauka yar uwarta ce.
“Toh shiknan” rabi ta bata amsa sannan takashe wayar.
Ninke kayayyakin da rabi keyi ta dakata, tare da daukan lullubinta ta futo da wayarta a hannu.
Kai tsaye gate ta nufa dake akwai dan nisa daga cikin gida zuwa gate din gashi ana kwlala rana saboda ko sha biyu bata karasa ba rana ta futo sosai.
Jamila dai na daga tsaye allah allah akwai take rabi ta futo, har zuwa lokacin taunar chewing gum dinta take hankali kwance.
Rabi na futowa ta gyara tsayuwarta tana duban ta,daman daga dan nesa da security din ta tsaya wajen post din su tana ganin futowar rabi ta daga mata hannu,rabi ta karaso inda take.
“Sannu rabi..”
Rabi ta kalleta kafin tace “yauwa dai sannu,ina fata dai lafiya”
“Lafiyar ce ta kawo haka, da farko dai nasan zakiyi mamakin dayasa nace ki futo ko? Kuma ban nemi shiga wajen hadiza ba don bata san da zuwan nan nawa bama, taimako nake nema a wajenki”
“Toh…dame zan iya taimaka maki kenan?” Rabi ta tambayeta har zuwa lokacin kallonta kawai take
Gyara tsayuwa jamila tayi tana fuskantar rabi sannan tace ''ina tafe da wani babban alamari wanda nake da damar fayyace komai ayanxu kafin lokaci ya kure''
dan nunfasawa jamila tayi kafin ta cigaba ''so nake ki kaini wajen hajiya babba, mgana ce babba''
''toh fa, wace hajiyar kenan?'' rabi tayi magana tana mata wani kallo kallo.
''hajiya anne nake nufi''
''haka kawai saina daukeki na kaiki wajen hajiya? a wani dalilin ? saboda me kenan?''
chewing gum din dake bakinta ta fidda don zuwan rabi baisa ta cireba sai yanxu.
''banida lokacin yi maki dogon bayani amma inaso ki sani cewa wannan maganar ta danganci wannan ahalin''
''kinga bansanki ba, hadiza ce kawai ta kawoki gidan nan,a matsayin kawarta kuma a ganina idan alfarma kike nema ita zaki nema bani ba ''
jamila fa a qage take, so take kawai ta ganta gaban anne, gashi ita wannan datake tunanin zata samu hadin kai daga wajenta ta taimaketa tana neman fada mata maganar banza.
''kinga, bawai dan son raina bane nazo nan, abu daya nake nema wajenki shine ki taimaka ki kaini wajen hajiya anne, dalili daya ne yasa nazo wajen nan badan haka babu abunda yasha kaina''
''kinga babu yanda za ayi fa na kaiki wajen hajiya anne idan baki bani kwakwaran dalili ba, me kike nema daga wajenta?, kibani dalili saina ga abunda zai yiwu.''
cije labba jamila tayi wata dabara tazo mata kafin tace……..
Anan cikin gida apartment din su bahijja, da kyar ta samu ta lallaba maya tayi shuru, don kuka take wiwi, kamar zata zauce, ta inda take futa ba tanan take shiga ba, gaba daya ta tayar ma da bahijja hankali, sai a lokacin ta kara tabbatar da maya na son taj sosai.
“mummy wallahi inason shi, shi kadai nakeso kuma na rantse da allah bazan bari ya so yarinyar nan ba wallahil azeem, ni kadai zaiso ni kadai kuma zai aura…”
Kamo hannunta bahijja tayi da lallama tana mai share hawayen fuskanta tace “baby dan allah ki daina kuka ki natsu ki saurareni,”
Kallonta maya tayi idanunta sunyi jajawur tace “i trust you mummy kinmin alkawari, ni wallahi aure nakeso, idan baku auramin shi ba zan….”
Gaba daya yanda take magana she lost her manners, babu wani zancen kunya, idanunta ya rufe kawai.
Hankali tashe bahijja ta toshe mata bakinta don a tunaninta zata koma gidan jiya ne, don tayi mata alkawarin bazata sake yin abubuwan data kamata dasu ba.
“Ya isa…ni na maki alkawari kuma zan cikashi Insha Allah, zan fada ma nanna, nasan bazataqi wannan abun ba, ki daina kuka kina bata fuskarki,“
Sai a lokacin ta dan lafa da hawayen nata idanun sunyi jajawur, “yanxu fada min meya faru?”
Shuru maya tayi tana kissa abubuwan da zata fada aranta.
“Mummy wannan yarinyar bana kaunar ta bana son ganinta, yar iska ce wallahi, kuma makira ce, saboda an sakata school dinmu gani take kanmu daya, duk abunda aka mana yana kan idanunta, musamman ma ni, gasa take dani a komai, tana bakin ciki dani,is that how is supposed to be? Itafa yar aiki ce, Wacece ita da har anne zata hadata school damu? Duk wani abu da ake mana ana hadata damu?“
Daga yanda take maganganu bahijja ta lura mayan ta fuskanshi wani abu, kodai idanun taj nakan yarinyar kuma tayi imani yarinyar ke cusa kanta, jinin hadiza kenan,batayi mamaki ba.
Kwafa bahijja tayi tana mai duban mayan tace “shikenan, zansan yanda zanyi game da yarinyar nan, yanxu dai zanje nama nanna maganar shi taj din”
Tana fadin hka ta miqe ta fuce daga part din maya ta bita da kallo, sai zazzare idanu takeyi tana huci kamar zaki.
Bahijja na futowa bata wuce ko’ina ba sai sama part din nanna, da sallama tayi knocking sannan ta bude kofar ta shiga daga ciki.
Babu kowa a sitting room wannan yasa ta shiga main bedroom din nanna, nanna nadaga zaune gefen gadonta tana kokarin bude bottle water zata sha maganin sallamar bahijja da shugowarta yasa ta dago.
“Nanna…”
“Naam bahijja bismillah”
Karasawa bahijja tayi bakin gadon ta zauna gefenta tana mai duban magungunan dake gefen nanna tace “zan iya magana dake”
“Yes bismillah…” nanna ta bata amsa da murmushin manya.
Dan nunfasawa bahijja tayi, tana tunanin ta inda zata fara magana, “bahijja lafiya dai? Akwai abunda ke damunki?”
“Bansan ta inda zan fara ba nanna, don magana ce mai nauyi a wajena, banida wani zabi daya wuce nazo na sameki”
“Subhanallahi…”
Bata karasa ba bahijja ta dakatar da ita, “ina neman alfarma nanna, badan ni ba, kuma bawai don son kai ba nanna”
“Haba bahijja me zaki nema a wajena da har zakiyi tunani irin haka? Fada min menene”
“Inason na hada maya da taj don karfafa zumunci mu nanna, maya ta nuna tana son taj, kuma nayi imanin babu wanda ya chanchanci ya aureta kamarshi don shi dan uwanta ne jininta ne, ayau kona fadi na mutu nasan bazata wulaqanta ba, kuma she’s on a safe hands..nason akwai sonkai a ciki don shi bai nuna yana sonta ba, amma….”
Tunda ta fara magana nanna ke kallonta, har saida takai aya, abunda ya faru dazu saida yasa ta ayyana a ranta ko maya sonshi take gashi abun ya tabbata, toh ay wannan ba abun qi bane abun so ne, kuma zai karfafa zumuncin su sosai, saidai kuma….
“Babu abun sonkai a ciki bahijja, indai ta nuna tana son shi ba laifi bane, abu ne mai kyau, kuma idan har allah ya kaddara akwai alkahiri a ciki saikiga albarka a cikinsa, babu wanda ya kaini son ganin zumuncin mu nida yar uwata ya karfafa, kuma yayi qarko bahijja, ina farin ciki da wannan abu, abu ne na cikin gida,kuma ina fatan allah ya shiga lamarin”
Cikin murna bahijja ta dubi nanna harda dan hawayenta cause she’s desperate ta kama hannunta tace “nagode nanna, nagode daman nasan bazaki qi wannan zancen ba,Allah yasa wannan ya zame mana dalilin karfafuwar zumunci mu''
''ameen ya allah, allah ya tabbatar da alkairi, ay bazaka qi naka ba, wannan abun farin ciki ne a wajen mu bahijja, ke yata ce, shima dana ne, mesa zanqi jininki bahijjar nanna'' nanna ta karashe magana tana kallonta tana murmushi, harga allah har cikin zuciyarta taji dadin wannan magana, kowa yana da flawss dinshi a duniyar nan dukda maya bata da kunya kuma kanta na rawa amma wannan abu ne na farin ciki, kuma dubaga yanda bahijja tazo ta sameta da maganar tasan maganar tajema anne kuma bata bada amincewarta ba.
dan dakatawa bahijja tayi, yanayin fuskanta ya dan sauya tunawa da yanda sukayi da anne, ''nasan kinyi magana da anne ko?kuma bata nuna amincewarta ba?' nanna ta tambayeta
dagowa bahijja tayi kamar zatayi kuka tace ''nanna bansan meysa anne take kin maya da majeed ba, ni ce na mata laifi na bujire mata bai kamata ace laifiina ya shafe su ba, komai mukaddari ne daga allah, wallahi har cikin zuciyata inajin guilt din abubuwan da suka faru a baya, yau shekara wajen ashirin da uku kenan, har yau babu abunda ya sauya.
''karki damu kanki kinji? yaya bazata taba qin abunda kika haifa ba harma mijinki, duk wani abu daya faru a baya yariga da ya wuce bahijja, babu wanda ya kaita murna da farin ciki turo maya da kukayi nan, kuma auren maya da taj idan allah allah ya rubuta alkairi ne saitafi kowa murna kinji ko''
da haka sukayi sallama, bayan bahijja ta mata godiya sosai kuma nanna ta bata assurance din cewa komai zaizo da sauqi idan suka hada da addua.
bayan futar bahijja nanna tayi shuru, aiki take sonyi daga gida daya shafi office dinta amma ta kasa, harga allah maganganun su da bahijja abun ya mata dadi har zuciya saidai kuma ta wani bangaren tanajin fargabar yanda abun zai kasance idan ya nuna bayaso don daga abunda ya faru a dining da safe kamar they are not on a good side shida mayar, kwata kwata bata kawo akwai wani abu dake tsakanin shi da sabeeha ba.
itafa uwace, babu yanda za'ayi tayi mashi dole inya nuna bayason mayar,saitake ganin abun kamar tarihi ne ke kokarin maimaita kanshi, ta tuna da lokacin databi zabinta taqi karbar wanda mahaifinta ya bata, kuma babu wanda ya mata dole, saidai bacin ran qin bin umarnin zabi da akayi mata daya biyo haka zalika bahijjar ma, shiyasa har yanxu zafin abun ke cikin zuciyar anne har bahijjar ke ganin kamar har yanxu bata hakura ba, anne macece tsayyayiya mai magana daya, idan har ta nuna rashin amincewarta abun zaiyi wuya.
after few hours.
Bangaren sabeeha..
Bayan tabar dining din jikinta na rawa daki ta koma ta zauna ta doka tagumi hawaye ya soma sauka kan fuskanta, daman abunda take gudun faruwa kenan,ita kanta batasan matsayar auren su ba balle waenda basu san da auren ba, idan aka ga kusancin su dole za ayi tsammanin akwai wani abu tsakaninsu shida ita, don babu wanda zai kawo akwai aure tsakaninsu, gashi yanxu maya ta gansu, fadin irin yanayin data shiga bata lokaci ne,dubaga irin kallon da suke mata gaba dayansu lokacin da maya tace wai ita yar iskace kuma bin taj take,hankalinta yayi nisa sosai a tunani, gaba daya batajin dadin rayuwarta, qila batada rabon jin dadi a duniya shiyasa gaba daya rayuwarta a karkarce take ba kamar ta kowa ba…
Ahankali ya soma bude kofar da instint din ya bashi tana ciki,ba tare da wani fargaba ba ko tsoro, gaba daya abunda ya faru daxu ya tsaya mashi arai, reaction dinta kawai yake tunawa yanda hankalinta gaba daya ya tashi sanda maya ta gansu.
Tundaga nesa ya hangota zaune a kasa,ta juya ma kofar baya sannan ta hade jikinta waje daya.
A natse ya rufe kofar sannan ya fara takowa zuwa cikin dakin, sabeeha da hankalinta gaba daya yayi nisa ga tunanin da take batasan ya shugo ba kwata kwata, yanda ta rankwafar da kanta ga kafafunta ta juya baya babu abund atake sai tunani mai zurfi tana hawaye, unexpectedly kawai taji an dafata daga baya, a tunaninta ko rabi ce wannan yasa bata furgita ba saida ta dago ta ganshi tsugunne gabanta, tuni gabanta ya bada wani irin damm tayi saurin yin baya, tuni idanunta ya sake karadewa tsabar furgice kmar taga dodo, “dan allah ka futa, meya kawoka nan? So kake a sake ganinmu a haka? Wai meysa kake kokarin saka rayuwata cikin hadari? Kasan halin da zan shiga idan mama ta san da wani abu tsakanina dakai? Dan allah taj ka futa daga rayuwata ka rabu dani, abunda ke taakanina dakai bashida wani amfani, dan allah ka sakeni” ta karashe tana fashe da matsanancin kuka har zuwa lokacin jikinta tsuma yake sosai, gaba daya sai yaji jikinshi yayi sanyi don da larabci tayi magana kuka yaji maganganunta yanda ya kamata, baiyi wata wata ba kawai ya jawota jikinshi ya rungumeta ta soma kokarin kwacewa, duk yanda yaso ta natsu qin natsuwa tayi saida ya soma mata magana cikin kunnenta ahankali, “shiii,stop crying”
“Dan allah ka sakeni, idan aka shugo aka ganmu
Haka…”
Saurin katseta yayi da sanyayiyar muryarshi mai sanya natsuwa, “meysa kikeda tsoro?who cares idan an ganmu? …”
girgiza kanta ta soma yi, gaba daya ya kasa understanding dinta,
Bai gama rufe bakiba aka soma kokarin bude kofar dakin nata, tuni ta sandare gabanta ya tsananta bugawa, shikenan tata ta kare, za azo a gansu a haka, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, batasan sanda ta wani turashi ba ta miqe kamar zata zauce tana waige waige, kamar yasan za a iya shugowa dakin yana shugowa ya saka padlock daga ciki, wannan yasa koda rabi ta murda kofar a rufe ta jita.
“Fatim!! Fatimaa!!”
Rabin ta soma kiranta da karfi don a tunaninta ko barci take.
“Kagani ko? Na shiga uku..” ta sake fashewa da kuka ahankli, gaba daya ta wani sauya ta koma kamar jan kosai, jijiyoyin kanta duk sun tashi rudu rudu, ganin haka yasashi dagowa ya dubi dakin gaba daya kafin ya wuce ta gabanta zuwa bathroom, yana shiga ya karo kofar, daidai nan rabi ta sake knocking da karfi, wanda yasa ta dawo hayyacinta ta tunkari kofar tana gyara tsayuwarta ta bude kofar.
Kallonta rabi tayi, tace “meysa kika rufe kofa?”
“Yi hkuri, naga idan na karo kofar bata rufuwa da kanta saidai na saka locks”
Kallon dakin rabi ta soma yi, gaba daya dakin wani irin kamshi yake na daban ba kamar yanda yake ba.
Karo kofar sabeeha tayi bayan ta shugo gabanta na faduwa kar rabi ta gano akwai wani bayan ita a dakin.
Rabi na kalle kallen dakin kamar wadda she’s suspicious of something tace, “babu wanda ya nemeni daga cikin gida??”
Cikin sauri tace “eh babu”
Shuru rabin tayi tama rasa me zata ce ma sabeehar sai faman kalle kallen dakin take, itama dai sabeehar a taorace take kar ta rafko ta,wata dabara tazoma rabi tace “yauwa bari na shiga bandakin ku nayi alwala fanfon bandakina ruwan baya zuwa dole a kira masu gyara gashi kince kofa bata rufuwa ko?”
Tan fadin haka ta nufi kofar toilet sabeeha ta bita da gudu tasha gabanta, hannunta na karkarwa tace “laa ba a wanke yake ba, anty rabi, ko zaki shiga na chan dayan dakin mu”
Binta da ido rabi tayi don a qage take da shiga bandakin tace “ba komai ay alwala zanyi”
Tana fadin haka ta shanmaceta ta bude kofar bathroom din, tuni sabeeha ta sulale a kasa, kirjinta na dukan uku uku, shikenan tata ta kare innalilillahi wa inna ialihir rajiun, ko shiga bandakin kasawa tayi, jira kwai take su futo dashi da rabi,
“Bari na shiga na chan dakin kawai”
Rabi data futo ko second talatin batayi ba ta fada.
Cikin sauri sabeeha ta miqe tana goge fuskanta tace “toh!!!”
Rabi tayi sauri ta fuce daga dakin, ita kuma ta shiga bathroom din, ta soma dubanshi, chan ta hangoshi ga cikin shower, dake ta rataye wani dan zani datake wanka dashi kan karafunnan shower glass din wannan yasa bazaka san da mutun ciki ba, invadan ka kura idanu ka ga kafafunshi ba a wajen, futowa yayi daga wajen hannunshi harde a kirjinshi, ya wani bata fuska, ya nemi giftawa ta gaban ta tayi saurin dakatar dashi, “taj!!!!!!….”
Unexpectedly yaji yanda ta fadi sunan daga bakinta, “dan..allah ka sakeni”
Chak ya tsaya shi bai juyoba shi bai bata amsa ba, saida ya dauka wajen minti biyu a haka kafin ya juyo ya mata kallo daya, sannan ya fuce daga bathroom din.
Yana futa cikin ikon allah baici karo da kowa ba ya wuce part dinshi, tambayar kanshi yakeyi meysa bazaiyi abunda take so ba tunda ba sonta yake ba, daidai nan tunaninshi ya tsaya chak, idan ba sonta yake ba? Me yake da ita? Ya tambayi kanshi, wata zuciyar ta bashi amsa, he’s obsessed with her, kuma yanajin batada kowa yanxu bandashi so how can he leave her? Bazai iya abunda take so ba don he sworn on taking care of her, and protecting her yanda tayi mashi,
halarcin da bai mata ba yake son yayi mata aynxu, kuma abu daya zaiyi a yanxu shine ya nemo asalinta koda kuwa iyayenta abandoning dinta sukayi,koda kuwa ba a sameta ta hanya madaidaiciya ba.
Chan bangaren bahijja tana barin wajen nanna ta dawo part dinsu, ta dauka wayanta ta soma neman majeed, yana dauka suka danyi maganganun su sannan ta tamabyeshi dawowanshi, ya shiada mata zai dawo da wuri, ganin yanda take magana ya gane she’s pressed kamar wani abu na damunta, nan ya tambayeta if anything ia wrong tace mashi tana son suyi wata muhimmiyar magana dashi amma saiya dawo.
Da haka sukayi sallama ta kashe wayar, tana katsew call din fadila ya shugo, tana ganin call din ta daga tare da sallama, suna gana gaisawa ta miqama anne wayar, tunda taji anne ta karba wayar gabanta ya soma faduwa, ta soma tuna maganganunsu kan maganar data kawo na hadin taj da maya, gashi anne tayi warning dinta kan karta sake ta samu nanna da maganar.
“Bahijja!!!!”
Anne ta kirata tare da katse tunanin data shiga, “naam, ina wuni ya jiki??”
“inason kibar abunda kike kizo asibiti yanxun nan”
Daga yanda anne ke magana dole gabanta ya fadi, don babu wasa cikin maganr nata, macece mai magana daya and she’s very hard on kowa,shiyasa when it comes to her basa wasa da maganar ta, a karo na biyu tayi abunda zai shiga tsakaninta da mahaifiyarta amma babu yanda ta iya bata da option ba kowa ne zai fuskanshi what shes going through ba akan maya, dole ta aurar da ita kawai doj shine mafita kawai.
Ahankali ta amsa da “toh!!” Daga chan aka katse wayar.
Jiki a mace bahijja ta shirya cikin gaggawa ta futo, dakin maya ta shiga tana bude kofar jin saukar ruwa daga bathroom yasa ta gane wanka take, zama tayi bakin gado har ta futo daga bandakin da towel a kirjinta, kallonta tayi daga sama har kasa ganin kanta a jike yasa tace “ wanka kikayi?”
Maya dake goge gashinta da towel ta amsa da eh, gaban bahijja ne ya dan fadi, dalilin wani tunani daya ratsa zuciyarta, saikuka taga bai dace ta zargi yar tata ba wannan yasa tace “zanje asibiti, take care of your self baby okay?”
“Okay, mummy saikin dawo”
Bahijja na futa ta gama shafe shafenta ta saka wasu tsinannun kaya da suka dameta ta futo.
Yaufa duk yanda za ayi saita sanar dashi abund ake cikin zuciyarta, ita yar uwarshi ce yayi yanda zq ayi yayi turning dinta down.
Wannan yasa ta futo kai tsaye daga part dinsu zuwa nashi, daman babu wani nisa sosai haka ta karaso kai tsaye ta bude kofar sannan ta shugo, sanyi da kamshin parlorn ne ya bugeta ta , ta lumshe ido sannan ta karaso cikin parlorn,
kai tsaye sama ta nufa tana taku daidai, gabanta na dan fadu, yaune karo na biyu data hauro saman, babu tsoro ko wani fargaba kawai ta bude kofar bedroom din ba tare da knocking ba, hasken fitilun bedroom din duk a kunne suke wannan yasa ta bi ko’ina da kallo, baya cikin bedroom din amma tanajin motsi daga wajen bathroom da closet.
Takowa ta somayi zuwa wajen bata kaiga karasawa ba ta hangoshi tsaye closet don bai karo kofar ba yana kokarin saka riga, dagashi da shorts ya juya mata baya.
Bin jikinshi ta soma yi da kallo tundaga kanshi zuwa gadon bayanahi dake a fadade zuwa ga kugunshi, har kafafunshi da suke a murde, take ta hadiye wani irin mugun miyau ta sake kifta idanunta, wato duk samarinta bata taba ganin mai irin halitta kamar tashi ba, innalillahi, “oh my gawddd” ta furta ahankali tana matse kafafunta waje guda, kallon bayanshi kawai tayi ta fara imaging yanda gabanshi zai kasance wannan yasa ta shiga shauqi, ay da bata gama fadawa koqin sonshi ba sai yanxu, like whattt!!! This is what she has been missing??? Wannan huge pleasure din? Tun a kallo kawai ya sata shiga yanayi balle kuma ta sameshi?.
Ay wallahi indai bata mallaki taj ba saidia idan mutuwa yayi, son wallahi wallahi bazata taba bari wata mace ta mallekeshi ba bayan ita, dan zata iya yin komai akanshi.
Tana cikin tunanin gaba daya hankalinta yayi nisa batasan ya juyo ba, da mamaki yake kallonta, ita ko gaba daya tama gama sandarewa, “what…the…f***” ta furta da dan karfi tana jan nishi don ya ji kalmomin da ta fada sosai a kunenshi, rai a bace ya kama handle din kofar ya banko gam cikin bacin rai ya saka kayanshi sannan ya futo, yanda ya hangota bata motsaba ko inch daya, saima murmuahi datake mashi, a duniyar nan babu abunda ya tsana kamar ayi invading privacy dinshi, and it looks like raini ya fara shugowa tsakaninshi da wannan yaran, inbadan hakan ba how dare she enters his room, peeping him while yana sauya kaya.
Yanda ya hade rai da yanda gaba daya yanayinshi ya sauya yasa gabanta faduwa amma haka ta danne zuciyarta, ya futo daga wajen dan nesa kadan da ita ya tsaya, harshly ya soma magana “ waya baki iznin shugowa nan?”
Koda yayi magana sai taji yau muryanshi yafi mata dadi, its about time yasan cewa itafa ba yarinya bace, a goge take, kuma idanunta a bude suke, tayi mu’amala da waenda suka fishi shekaru ma, idan yana mata kallon yar cousin dinshi toh fah bazai yuwu ba, ita sonshi take kuma dole ta sameshi.
“Ra’ayina nabi na shigo,” ta karashe tana nufar gadonshi ta zauna harda daura kafa daya kan daya.
Da mamaki yake kallonta, ay baisan futsararri bace ba ta karshe sai yanxu, “inason magana dakai”
Ranshi inyakai kololuwa ya gama baci sosai, yama rasa me zaice mata, sai aika mata da wasu irin disgusting kallo da yakeyi, “ba komai ne ya kawoni nan wajen ka ba sai don na fada maka abunda yake cikin zuciyata”
Tana fadin haka ta miqe tare da takowa har inda yake ta taaya gabanshi tana kallon cikin idanunshi, “ina sonka uncle taj,”
Hannayenshi na cikin aljihunsa ya sake kallonta da mamakin futsararta, gashi wani irin mugun kallo yake aika mata, “wallahi inasonka fiye da raina uncle taj, idan ban sameka ba zan iya rasa raina, ina kishinka, banason kowacce mace ta rabeka, banason kowa ya rabeke,”
Shi courage dinta ne ma da futsararta yafi bashi mamaki, tashigo har cikin dakinta ta kalli cikin idanunsa sannan tace wai tana sonshi? Unbelievable to him.
“Ya kamata ace ka gane hakan,tunda na sanya idanunka akanka ka shiga zuciyata, ive been longing for you, i hate seeing you smiling to someone else shiyasa na tsani wannan shegiyar yar aikin, banason ta rabeka, banasonta kusa dakai don kafi karfin hada nunfashi da inuwa daya da ita,“
Ay tunda ta fara magana ranshi bai gama ba ci sai yanxu data ambato sabeeha, saiya tuna da abunda ta masu dazu kan dining, wanda hakan ya bata mashi rai sosai ba kadan ba.
Tana kokarin yin magana ya daga mata hannu daya, sannan ya mata nuni da kofa,ko matsayin ya amsata bata samu ba, maganganunta a banza, take taji wani abu ya chaketa a zuciyarta kamar zata hadiye zuciya don bakin ciki, “meysa kake sakema wacchar yar iskar yarinya fuska? Menene tsakaninka da ita???”
Sai a lokacin ya iya bude bakinshi don da farko baiga yanada time din bata amsa ba sai yanxu.
Calmly yake magana don bayason loosing steezs dinshi yace “this should be the last time zakiyi questioning dina, ni sa’anki ne? Are you insane?????and the next time naji kin kirata da yar iska..” ya wani cije lebe kafin ya mata nuni da kofa “outtt!!!”
Wannan magana dayayi ba karamin hargitsata yayi ba, ta kara tabbatar da dakyar ne idan bason yarinyar nan yake ba abunda take gudu kenan, inva haka ba me zaisa ta ga kafafunshi kan na sabeeha don wallahi kiri kiri taga kafafunshi kan na yarinyar yana yawo dashi, dazun ta rasa yanda zatayi ne yasa ta juya maganar kan cewa ay sabeehar ce ke flirting dashi, saita tuna sanda ranar nan da sabeehar ta futo daga part dinshi a firgice har sukayi fada a compoud ita da sabeehar, wannan yarinya ta tsaneta kamar ranta,tsana mafi tsanani kuma wallahi bazat ataba bari tayi loosing Dinshi to her ba, yar aiki, yar shege, yarda bata da uba, mara gata…inaa bazai yuwu ba.
A kausashe ya sake daka mata tsawa dis time around da dan karfi yayi “i said out!!!!!”
Kukan datake kokarin matsewa ta kasa, tafarfasa kawai takeyi, tana jiyoshi yace “what sort of rubbish” kafin ta fuce, ay idan bata fitar da yarinyar nan daga gidan nan ba a gobe toh ba a haifeta da cibiya ba, saita wulaqantata.
A harzuke ta wuce part dinsu, tana shiga bangarenta ta rufo kofar gam sannan ta bude handbag dinta, ta zaro wasu kwayoyi, batama tsaya duba ko nawa bane kawai ta watsa bakinta, gaba daya sannan ta nufi wajen dressers dinta ta wawatsa kayaj wajen gaba daya suka fashe a kasa ta soka ihu…..”
8pm
Misalin karfe takwas bahijj ta shigo gida, gaba daya jikinta a mace yake, idanunta yayi jaa sosai, ga wani matsanancin ciwon kai datake ji kamar kanta zai rabu gida biyu.
Basira na bude mata kofa ta mata sannu da zuwa ta amsa sannan ta tambayi maya, nan basira ta shida mata tana sama dakinta.
Ko ta kan abuncin da basira ta sauke batabi ba ta nufi sama, zuwa ga dakin maya, tana isowa ta murda kofar taji a rufe tayi knocking “baby!!!”
Shuru babu reponse tana kokarin sake knocking call ya shigo mata tana ganin sunan majeed ta daga wayar sannan tabar bakin kofar zuwaga bedroom dinsu.
Tana shiga ya shaida mata zai danyi dare saboda ya shiga kaduna, batasan maiya kaishi ba amma dai bata kawo komai aranta ba wannan yasa tace “allah ya kiyaye” sannan ta kashe wayar, tana kokarin aje wayar gefen bedside idanunta ya sauka kan hannunta inda aka deba jininta daxu a asibiti.
Maya fa na chan kwance an shawu, gaba daya ta gama zama high don tayi over over dosing kanta just to relieve abunda ke ranta, ko lokacin da bahijja tayi knocking kofar already tayi knocking out batasan inda kanta yake ba.
Bangaren taj futa yayi daga gidan yaje asibiti bai dawo ba sai dare, sabeeha ko kwana tayi gabanta na faduwa, haka kawai ta rasa natsuwarta gaba daya.
***
Ana idar da sallar isha’i jamila ta shugo gidan a gajiye, da jamilu taci karo dayayi bake bake a tsakar gida, jiranta dawowarta kawai yake, don ya kasa gane mata cikin kwana biyu, wani irin zubabban wulaqancin take shirgawa, zata futa sanda taga dama ba tare da ta nemi izininsa ba da zarar yasa kafa ya futa sannan kuma ta dawo a lokacin dataga dama.
Kallo daya ta mashi ta kauda idanunta zata nufi uwar daka ya dakatar da ita.
“Daga gidan ubanwa kike??? Wato yawon ta zubar din naki kika koma?? Ehhh””
Wani irin izgilallan kallo ta mashi ko kunyar yayansu da sukayi zuru zuru suna jiran dawowarta bai jiba,
Tsakin nan datayi ne ya kara harzuka shi yace “kutmar ubanchan, ina maki magana kina min kallon dan iska??? Toh na rantse da allah inda kika futo zaki koma, kai nima dai lusari ne wallahi, daman ya za ayi nayi tunanin bazaki koma rayiwarki ta da ba??? Waye baisan sheqe ayar da baki ba a baya, wato yanxu nayi sanyi shine bari ki fara satar hanya ko??? Toh billahillzi…”
“Dallah rufe min baki munafiki annamimi, matsiyaci, har kanada bakin magana? Har kanada bakin magana jamilu??? Toh bari kaji wallahil azeem ka bini a hankali don wallahi azeem kasan niba kanwar lasa bace, kabarni kawai yanda ka ganni,mtewwww”
Ta doka tsaki tana mashi wani irin kallon tsana,
Tana fadin haka ta shige daki, a harzuke ya bita dakin kamar zasuyi dambe yace “ni kike kira da munafuki matsiyaci???”
“Kwarai kuwa, na hada da tsinanne ma duka”
Tass taji saukar hannunshi kan fuskarta batayi wata wata ba tana dagowa ta wankeshi shima da mari hau sau biyu,tuni yasha jinin jikinshi idanunta sunyi jaa sosai, “fita na sake ki”
Yana fadin haka ta kyakyace da dariya tana kallonshi tace “saki na shida kenan, ay bari kaji ni jamila bazan taba sakuwa ba, saidai idan da kafata nace banayi, kuma inka kwantar da hankali lokaci na zuwa da zan tattara yayana na kara gaba amma kafin nan saina tabbatar na wulantaka da wacchar tsinanniyar tunda har kukaci amanata kaida ita”
Tana kaiwa nan ta wani jawo colar rigarsa yayo gaba yuu, gashi daman a bushe, wallahi jan ido yake mata amma yasan tsaf zata iya masa shegen duka don jamila badai karfi fa, gata yar bala’i, shima kanshi baisan yanda akayi duk abubuwan da yake mata take chanyewa ba ashe ashe, “wallahi wallahi in kaga na hkura da cin amanata da kukayi saidai idan bana nunfashi, kai kasan wacece jamila basai an fada maka ba, ni jamila da bala’i ma an ganni an barni, daman na fada maka duk abunda zakayi karka sake ka kaini bango, albarkacin yayan ka kawai kakeci nake daga maka kafa amma wallahi wallahi….” Hmmm ta cije lebe har zuwa lokacin hannunta na chakume da corlar shi, wallahi gaba daya ya gama tsorata, gabansa ko faduwan da yake allah kadai ya san yanda yake bugawa, ta wani bangajeshi ta wuce uwar daka tana huci.
Ayfa jamilu tunda ya fita daga gida bai iya dawo wa ba sai wajen karfe sha biyu, gaba daya ya tsorata da jamila, daga cikin maganganunta ya gane ashe ta gano cin amanarta da sukeyi da hadiza, amma shine tayi shuru bata nuna ba? Chap akwai kura, yanda tayi rantsuwar nan yasan wallahi bazata barsu ba, shiko yasan hatsabibbancin jamila, zata iya komai wallahi.
Da kyar dai ya dawo gida don bashida wajen kwana ya kwana dakin yayansa su kuma ya turosu parlor, duk zarnin dakin nan haka ya kwanta a ciki don taoron da yakeji kar saiya rufe ido ta luma mashi wuka don kamar yanda tace zata iya komai gwara ya lallabata da safe ya bata hkuri ya nuna mata ay hadizar ce ke bibiyarsa, bada son ranshi ba.
Idan ya rabu da jamila ay ya shiga uku, ay gaba daya yama manta cewa gidan da suke ciki ma nata ne, har yana wani ihun ta futa ya saketa bayan wannan ma mutanen da ya zalumta a anguwar nan ay bazasu barshi ba, ga yaran dayayi ma ciki saboda jamilar tayi rufa rufa an danne komai idan ta tabe masu ay ya shiga uku, ay dole ya lallabata ya mata dadin baki.
Washe gari da asubar fari sai gashi ya tashi, ya share tsakar gida harda dora ruwan wanka, itako barcinta tayi cikin kwanciyar hankali.
Sai wajen goma ta tashi, lokacin yaran duk sun tafi makaranta, yawanci daman suke tashinta neman abun karo, yauko babu wanda ya shugo dakin saboda ya basu dari biyu sun sayo koko da kosai sun karya dashi.
Tana tashi ta fito tsakar gida, ta deba ruwa tayi lafiyayyan wankanta kota kanshi batabi ba, ta hada tea mai kauri da bredi taci harda soyayyan kwai.
Tana gamawa ta shirya cikin wata farin lace, kwalliya fa taci abunta fess fess ta dambara jan baki sannan taci daurin ture kaga tsiya, tana gamawa ta futo da jakarta a kafada, kai kaga jamila kace gasar kyau zata tafi, tayi kyau abunta.
A tsakar gida ta taddashi yana shara, abunda zatace bai tabayi ba tunda sukayi aure, aurenda tun shekaru hudu da suka wuce igiyoyin suka tsinke gaba daya amma ake zaune kamar jahilai.
Jakarta ta bude ta dauko chewing gum har biyu ta bare ledar ta watsa baki sannan ta tauna sautin ya bada qass, kota kanshi bata bi ba ta nufi kofa yayi saurin dakatar da ita.
“Jamila…”
Chak ta tsaya tana mashi wani wulaqantaccen kallo, “jamu dan darajar allah kiyi hakuri, ki yafe min , wallahi ba laifina bane, laifin wannan tainanniyar ce,na rantse da allah bana cikin hayyacina ba ason raina bane sharrin shaidan ne, daman saida na fada mata ni bazan iya cin amanarki ba jamu…”
“Kaga dama ka daina bata bakinga da yafi maka, dan wannan a banza, ni ganau ce ba jiyau ba, munafuki, da idanuna na kamaku turmi da tabarya kuna iskanci, a gidana a dakina, wato gani wawiya ko? Kum shafe shekaru kuna cin amanata,toh wallahi ka sani, na rantse da allah saina dau fansa, yanxu zanje na fara da ita, ka jira naka hukuncin, ka gama yawo jamilu wallahi, karkayi tunanin wai zaka iya guduwa, duk inda kaje saika dawo da kafarka wallahi, don kana tafun hannuna jamilu, yauwaaa”
Tana fadin haka ta tofar da miyau taja mayafinta dake yawo a kasa, “jamila…jamilaaa..!!”
Ya soma kiranta hankali tashe, innalillahi shikenan zata tona mashi asiri, gaba daya ya gama rikicewa.
The santuraki’s…
Monday morning.
Bayan sallar subh bahijja ta futo daga bedroom, babu inda ta nufa sai dakin maya jiki a mace, jiya sai wajen karfe sha daya dady ya dawo, so basu samu damar yin maganar datakeson yi mashi ba sai bayan sallar asuba, koda ta tunkareshi da maganar, saiya nuna kamar baiyi naam da maganar ba, musamman data shaida mashi anne bata bada amincewarta ba, shima dai akwai abubuwan daya hango, wanda yake ganin zai iya zamo matsala musamman tsakaninta da anne, tunda daman har zuwa yanxu bata gama gyaran muamalarta da mahaifiyar tata ba.
Ita bahijja gani take duk sun kasa fuskantarta, don ita datasan halin da mayan ke ciki da yanda ta nuna tana son taj idan har ba’a hadasu ba akwai matsala, tunda har ta nuna tana son auren gwara kawai a mata, don shine kawai solution.
Shi ta bangaren shi yana nusar da ita rashin amincewar anne babbar matsala ce, idan har ta qi to dole tana da kwakwaran dalili, sannan secondly idan maya na sonshi shi yana sonta ne?,
Rasa answer da zata bashi tayi, don tabbas ita tafi kowa going against auren hadi, amma gashi yanxu ita ke son ta hada, duk kawai saboda farin cikin mayan, tabbas tasan abun da son kai amma dai gani take batada solution daya wuce ta hada mayan da taj din, tunda dan uwanta ne, jininta ne.
Haka dai suka rabu suna jayayya akan maganar, ta futo daga bedroom din cikin bacin rai.
Koda tazo part din mayar taji kofar a rufe again sai hankalinta ya tashi ta soma knocking, shuru babu response, tuni gabanta ya soma faduwa, ta sauko kasan wajen basira data futo gyaran part din.
Bayan ta gaisheta ta tambayeta kamar haka “tun yaushe rabonki da maya?”
“Bayan kin fita naga ta futa zuwa cikin gida sai kuma ta dawo ta wuce sama, tun daga lokacin dai bata sauko ba”
Bahijja najin haka ta koma sama, nan ta shiga knocking a hankali gudun kar dady yaji, “maya!! Maya!!!”
Ta soma kiranta, jin shuru yasa ta soma dialing number ta, ga ringing dai tana ji amma shuru daga dakin, tuni hankalinta ya tashi, gashi extra keys na bedroom dinsu, batason komawa kar dady yayi suspecting wani abun, dole haka ta cigaba da knocking.
Ahankali ta soma bude idanunta, ba itace ta farka ba sai wajen takwas ta gifta, ba sallah ba salati, knocking din dakinta ne yasa ta farka, tuni ta miqe da sauri gabanta na faduwa, idanunta yayi jaa sosai kana ganinta kaga wadda ta jima tana barci, motsin budewar dataji ne yasa ta fara tattara nastuwarta, hade jikinta waje guda daman a kasa ta mangare, ana bude kofar kawai ta fara kukan munafurci kasa kasa, cikin sauri bahijja ta shigo dakin gaba daya hankalinta a tashe yake, bata samu daukan keys din dakin ba saida ta sallami daddy ya fita, tabbas a lokacin data dunga knocking babu response jikinta ya bata maya tasha wani abun, don babu yanda za ayi ayita bugun kofa kamar haka bataji ba, kuma tana cikin dakin.
Tana ganinta zaune ta hade jiki kuwa tayi saurin rufe kofar dakin ta shugo zuwa inda take, duk abunda maya keyi da bai dace ba duk yanda bahijja taso ta mata fada kasawa takeyi, ayau kam data tabbatar ta sake shan wani abun ranta ya baci sosai ba kadan ba don ta mata alkawarin bazata sake ba.
“Maya!!!!!, Bahijja ta kira rai a bace, ahankali maya ta dago da fuskartar datayi jaga jaga da hawaye harda majina, ga idanun nan yayi luhu luhu kamar wadda ta kwana tana kuka, tuni gaban bahijja ya fadi damm!!!
A shagwabe maya tace “mummy…mummy” sai tayi luu kamar zata fadi bahijja ta taimaka mata ta tashi zuwa kan gado, “mummy uncle taj…”
Ta dan dakata tare da fashewa da kuka sosai,
“Menene?? Meya faru? Have you been crying all night? Meysa?”
Girgiza mata kai maya tayi kamar munafuka ita bahijj sai tayi tunanin ko tun maganar jiya ne yake damun mayar, wannan wani irin so maya ke ma wannan bawan allah? Bahijja ta fada a zuciyarta.
“Mummy wallahi banason uncle taj yaso kowacce a duniyar nan bayan ni, zuciyana yana min zafi yana min ciwo, wallahi ina sonshi, banason na rasashi”
Ko irin kunyar nan wallahi maya bataji ba, ita gani ma take komai normal ne, kuma idan tayi pressuring mummyn nata dole ace ya aureta dole ta sameshi.
“Ya isa maya, wayace zaki rasashi? Insha allah shine mijinki na sunna, indai ina raye taj mijinki ne da yardar Allah, ki kwantar da hankalinki, kinji ko” tana karashe tana jin tausayin diyar tata
Kauda fuska maya tayi ta wani sauke wani makirin murmushi, kafin ta juyo ta sauya fuska ta dubi mummy nata sannan ta rungumeta “thank you mummy, thank you for supporting my choice, insha allah bazan baki kunya ba”
“Meysa kikaqi bude min kofa? Did you take something??”
“No mummy,ay na maki alkawari bazan sake ba, na kasa barci ne da daddare sai wajen subh na iya barci banma san nayi ba, mummy zanci special pancake dinki please”
Badan ta yarda ba kawai tace mata “okay tohm freshen up saiki sauko kici”
Tana ganin futar mummyn nata ta tashi tsaye, gaba daya abunda ya faru jiya ya dawo mata sabo fil, a yau yau dinnan yanda ta rantse saita futar da sabeeha daga gidan nan saita koreta.
Acahn main house ko yau an tashi da murnar dawowar anne gidan bayan wata uku da suka shafe a asibiti tana jinya, su rabi sai faman hada hada akeyi, kusan ma tare suke komai ita da sabeeha wadda gaba daya tsakanin jiya da yau ta rasa sukuni,gabanta sai faduwa yake.
Hadiza dake zaune daki batasan meke faruwa ba a cikin gida, tunda ta tashi sukayi waya da jamila ta shaida mata ay tana nan zuwa ta kasa sukuni, allah allah kawai take tazo ta mata bayanin yanda sukayi da malamin, don itama ta matsu kawai taga yarinyar nan bata gabanta.
Tana cikin safa da marwa a daki Misalin wajen karfe sha daya kuwa saiga wayar jamilar ta shugo, cikin sauri ta dauka tare dakaiwa kunne, “kin qaraso ne?”
Daga chan jamila ta amsa “eh ina bakin gate, waennan mutanen naku ba barina zasuyi na shigo ba kizo ki shiga dani”
Batama tsaya bata amsa ba ta jawo mayafinta ta aza aka sannan ta futo da wayar a hannunta, ta kofar baya ta bi, sabeeha da rabi dake kitchen suka bita da kallo sabeeha ta dan duqa zata gaisheta ko kallon inda take batayi ba ta fuce, rabi ta kalli sabeehar, sai kawai ta girgiza kai, har zuwa yanxu mamaki take game da maganar da jamila ta fada mata jiya.
Yanxu daman wannan ba yar hadiza bace???” Ta fada aranta, “no wonder shiyasa take yi mata abubuwa, babu kusanci batama damu da ita ba kwata kwata, amma…
“Anty rabi!!!”
Sabeeha ta katse mata tunaninta tana kallon yarinyar tausayinta na ratsata, “yana zubewa” sabeeha ta mata nuni da ruden tuwon da rabi keyi. Rabi tayi saurin rage wutar, suna cikin aiki kawai sukaji sallama, rabi ta juyo da mamaki tana kallon jamila, itaka jamilar kallonta take sai kawai ta waske tana dariyar yaqe, “sannunku da aiki”
Sabeeha ta dan duka tace “ina wuni”
Ganin hadiza na kallonta yasa jamila yatsine fuska kamar batason amsawa tace “lafiya”
“Muje ciki” hadizq ta fada tana yin gaba, mamaki ya cika rabi, lallai wannan katuwar munafuka ce, kamar ba jiya tazo ba tana neman Alfarma ta kaita wajen anne, koda ta tambayeta meysa saita fada mata cewa rayuwar sabeeha na cikin hadari, kuma yarinyar ba yar hadiza bace, sannan akwai wani boyayyan al’amari game da yarinyar wanda take ganin zasu iya taimakawa su kubutar da yarinyar daga cikin makircin hadiza, don hadiza fuska biyu ce, ayanda ta fada mata wai kamar wani dan iska take son ta aura mata dan shaye shaye, babu irin maganganun da bata fada ba kan hadiza, marasa dadi da yasata ta yarda, dubaga abubuwan dataga hadiza kema yarinyar, abunda yasa ta kara yarda ma shine ranar da allah yayi zataji wani conversation din da maya sukayi da hadizar inda hadiza ke fadama maya ay sabeeha ba yarta bace, da farko bata dago kan zancen nasu ba don suna tsaka da yin maganar tazo dakin, harta bude kofa basu san da mutun a wajen ba, abun ya tsaya mata arai lokacin ta kasa gane inda zancen ya dosa sai a yanxu ta gane, dalilin da yasa ta yarda da zancen jamilar ma kenan, yanxu kuma Saita shiga confusion ganinsu tare.
Suna shiga daki hadiza ta wani rufo kofar rufo, jamila ko aka baje kan gado ta wani turo daurin nata gaba dakyau.
“Kai wallahi nasha wahala jiyan nan, ke wallahi badan ke ba wallahi bazan je wannan kasurmugun dajin ba”
Washe baki hadiza tayi ta zauna tana fuskantar jamila tace “allah yabar min jamila”
Suka wani tafa, “ke ay ni kasa barci nayi jiya wallahi da ban jiki ba, na kira layinki ma kwata kwata baya shiga” hadiza tayi mgana
“Yoh ina zakiji ina chan inda babu service” ta karashe tana bude jakarta.
Gyara zama hadiza tayi kafin tace “toh yaya???? Na matsu wallahi naji yaya? An fara aikin?”
“Haba waa kinsan bana wasa hadiza,” jamila ta fada tana fiddo da wata leda da wasu layu guda biyu kafin, hadizq ta wani washe baki, “aiki ne akayi babba, kuma wallahi wallahi ba karamin aiki bane, matso kiji”
“Kinga wannan?”
Ta nuna mata layar tace “wannan layar bakar ajiyace, ba a yi mata ganganci, ba a ajeta sai an daidaici awannin da ko wanne mai nunfashi ke kwanciya, zaki ajeta a kasan abun kwanciyarta da kika tabbatar zata saka kanta a wajen, da zarar ta aza kanta babu ita babu nunfashi…Kamar yanda kika buqata a yau yau dinan zaki shafe labarinta cikin sauqi”
Baki bude hadiza ta karba, wani irin dadi ya lulubeta,”kai jamila dame zan saka maki?kin biyani da komai”
Kallonta kawai jamila tayi a bayyane tana murmushi a zuciyarta kuwa ita kadai tasan abunda take qissawa.
Dayar layar jamila ta miqa mata tace “wannan ta mallaka ce da kikace kinaso,amma baki fada min me zakiyi da ita ba”
“Kema kinsan in na buqaci abu dole akwai dalili,”
“Dalilin kanki ne kona diyarki?, hmm tunda nake zuwa baki taba hadani da ita ba naga yar tamu yanda ta girma”
“Hmm tana chan bangaren shegiyar nan”
“A gaskia ya kamata na ganta nima,”
Wani irin kallo hadiza ta mata tace “zaki ganta karki damu jamila yanxu dai mu kauda wannan dmauwar tamu tukunna”
“Haka fa, yauwa ga wannan ma,”
Ta dauko wani kullin baqin gari kamar charcoal ta miqama hadizar,
“ wannan garin, bakar guba ce mai hadari,”
“Shima wajenshi kika samo??” Hadiza ta tambayeta tana karbar ledar.
“ah ah wannan tawa gudumawar ce, kinga wannan abar da ita nayi amfani wajen…kauda wannan tsohon mijin nawa cikin sauki, sai ganin gawar shi akayi kawai, a ruwa ake zubawa ko a lemon, da zarar mutun yasha cikin abunda bai wuce minti talatin ba saidai a bada tarihin mutun wallahi,”
“Kaiiiiii…ke ko wannan zan bata ne ta fara sha kawai?”
“Ay duk wanda yafi maki sauqi kawai kiyi amfani dashi, shiyasa ma na kawo maki solution biyu”
“Kai jamila allah yabarni dake, wallahi banida kamarke jamila, kin gama min komai,“
Dan murmusawa jamila tayi tace “ameen, in kina dani bakida case, zadai a bani tukwici dai ko?” Tashi tsaye hadiza tayi ta kama gefen zaninta ta qulle layar da kullin maganin kafin tace
“Sosai ma kuwa bari na kawo maki lemo da ruwa ki kashe kishi”
Tana kaiwa nan ta miqe tsaye, ta futa daga dakin, kitchen ta shiga ta hado mata lemo da ruwa sannan ta futo, ta tunkari dakin,daidai nan maya ta futo daga bedroom din nata, daman ta shiga nemanta bata ganta ba,tuni hadiza ta soma washe baki, “hajiya karama, kwana biyu bkaya nemana albishirinki?”
Hannu maya ta daga mata ta dakatar da ita, don yanxu batada time din shirmen wannan matar, “kinga ba surutunki ya sauko dani ba, ki turomin wannan yarinyar zata gyara min part dina”
Jiki na rawa hadiza tace “toh!! Toh!! Yanxu zata zo, ay in gaya maki na samo..”
Tuni ta wuceta vata tsaya sauraronta, dakin hadiza ta shiga, jamila na daga zaune tana taunar chewing gum, hadiza ta aje mata lemo a kasa.
“Hala wannan ma yar masu gidan ce ko?”
Dariya hadiza tayi kafin ta mata rada a kunne,
Tuni jamila ta gwalo idanu, tace “ke da gaske?”
Hadiza tayi dariya kafin tace “Wallahi kuwa…”
“Masha allahu burinki ya cika hadiza” ta fada a bayyne a cikin zuciyarta kuwa babu abunda take sai tunanin yanda mayar ta shugo daki, kana ganinta kaga futsararriya kangararriya, kuma idanunta a bude yake, babu ladabi da biyayya balle girmama na gaba, dan ko kallon mutunci batayima jamila ba.
Suna cikin magana wayar hadiza dake ajiye gefe tayi ringing, tama dauka ko maya ce ke kiran tana ganin mai kiran tayi saurin daukar wayar ta kalli jamila tace “ina zuwa”
Tana fadin haka ta futa, jamila ta bita da kallo.
Dakin da sabeeha ke zama ta shiga kai tsaye, bin ko’ina ta soma yi da kallo ganin dan kwalin sabeeha gefen gadon, tasan yanxu basira bata kwana anan so basically sabeehan ce kawai a dakin, daidai nan sabeehar ta futo daga bathroom, tana ganin hadiza tayi saurin karasowa inda take kanta a kasa, “ay namayi kokari dana barki har kikakai e yanxu, bazan bari ki bata min shiri na ba, ko ki shiga tsakanina da yata, zuwanki duniya da haihuwar ki a banza,” duk a cikin ranta take wannan maganar.
“Wuce kije sama bangaren maya ki gyara mata shi tass yanxun nan”
Da toh ta amsa mata sannan ta dan raba gefe ta futa daga dakin, hadiza na tsaye saida taga futanta sannan ta aje wayarta gefwn gadon sabeehar ta fidda kullin datayi ma layun da ledar, haka ta dauka layar nan ta daga pillow sabeehar tasaka a ciki sannan ta aje pillow din, tana ajewa ta sauke ajiyar zuciya, ko irin dar dar dinan bataji kwata kwata, Rashin imani kenan zuciyarta ta rigada ta koma baqa, bata da imani ko digo daya.
Tana kokarin daukar wayarta da sauran abubuwan nata wayar ta sake ringing, “kai wannan wani irin naci ne”
Ta fada tana dagawa takai kunneta, “dan allah ka daina kirana a daidia lokacin da bai kamata ba, yanxu dana bar wayar da adaki jamila ta dauka fa?”
Jamilu najin ta ambaci jamila yayi saurin cewa “tamu ta kare hadiza, shikenan,wallahi jamila bazata barki ba”
“Ban gane ba me kake nufi?”
“Jamila ta san muamalar dake tsakanin mu hadiza, kuma ta dauki alwashim saita dau fansar cin amanarta da mukayi, da alamu dai ta cin maki don wallahi bazata barki ba”
“ ka natsu kamin bayani.. me kake nufi?”
“Ke bkya kwashewa ne? Ta san komai, ranar da kikazo ta kamamu,kuma dazu da bakinta ta fada min bazata barmu ba dagani har ke, ke kuma ina kiranki bakya dagawa”
“Kana nufin jamila tasan muamalarmu?”
“Kunnanki nawa ne hadiza??? Kinfi kowa sanin jamila wallahi bazata barmu ba,saiki shirya”
Take gaban hadiza ya wani bada damm, tayi shiru kanta ya kasa processing komai, idan har maganar da jamilu ke fada gaskia ne tabbas jamila bazata zauna haka ba, dole saita dau fansa don tasha fada mata abu daya ne zaisa ta tona mata babban sırrınta, idan har ta sake taci amanarta, ay bata taba tsammanin ta jirga shirme ba na biyewa jamilu da son zuciya sai yanxu, kar tasan kar ne ita da jamila, bazata taba barinta ba, jamila annobar macijiya ce, zata iya kai mata sara ta bayan fage don makirace ta karshe ta iya makirci, dole ta kauda jamila kota halin qaqa ne don sirrinta ya rufu, don idan ta tona mata asiri shikenan ta gama yawo.
Gaba daya saita furgice, Ay batasan sanda ta katse wayar ba, jikinta na rawa kamar tsohuwar kamu, kallon baqar gubar dake hannunta tayi, batada wani shiri dole saidai tayi amfani da abunda take dashi, yanda ta mata fuska biyu ta nuna kamar batasan cin amanarta suke ba ita da jamilu haka zata mata itama, zatayi amfani da wannan damar itama takai mata sara.
Jikinta na rawa ta futo daga dakin zuwa dakinta databar jamila, tana shiga taga wayam, take gabanta ya wani bada damm, dagowar da zatayi kuma saitaga kofar bandaki adan bude sai kuma karar saukan ruwa dataji, tuni ta sauke ajiyar zuciya cikin sauri ta dubi lemon da jamilar bata taba ba, ta dubi kofar toilet din, kafin ta maida hankalinta ga lemon, cikin sauri ta soma kunce zaninta inda ta kulle baqar gubar nan ta fiddo da ledar sannan ta bude, hankalinta na ga kofar tana sauri ta maido da dubanta ga lemon ta zuba gubar a ciki, lemon kwali ne wannan yasa ba a ganin abunda ke ciki, tana gamawa ta girgiza lemon sannan ta ajeshi sannan ta soma kokarin kulle ledar daidai nan taji saukar ruwan fanfon ya tsaya, tsabar rudu saida ledar ta fadi cikin sauri ta dauko daidai nan jamila ta futo daga bandakin, ta mata kallo daya ganinta a furgice, sai kawai ta sauke murmushi, lallai sai yau ta tabbatar hadiza jaka ce ta karshe, “kin dawo?” jamila ta fada tana karasowa bakin gadon.
“Eh… ashe kina bayan gida,”
“Wallahi daman a matse na shugo gidan ne”
Yaqe hadiza tayi sanan tace “ga ruwa ga lemo fa”
“Ay kuwa bani na kora makoshi na”
Cikin sauri hadiza ta miqa mata kwalin lemon, “babu kofi ne na yan gayu na tsiyaya?”
“Kedai kawai ki kafa baki kisha, wake ta kofi? Ni wani sa’in ma nafison inasha daga kwalin” ta karashe tana murmushi, allah allah kawai take tasha.
Jamila ko aka gyara zama aka bude cover juice, hankali kwance ta daga takai kurba daya, sanyin lemon ya ratsa ta ta sake kurba, hadiza ko kifta ido batayi ba tunda ta kafe jamila, sai kawai ta sauke wani murmushin jin dadi, “tunda kika gano abunda ke tsakanina da wanchan lusarin mijin naki nasan abu na farko da zakiyi shine yunkurin tona min asiri, ni kuma bazan taba bari ki bata min shiri na ba tunda har nakawo wannan matsayin,daga ke har ita idan na kaudaku banida sauran matsala” hadiza ta fada a zuciyarta
ganin irin kallon da hadiza ke mata yasa tace “Yaya dai wannan kallon da kikemin??”
“na tuna yanda muka taso ne jamila” hadiza ta bata amsa
“Haka aka ganmu kuma haka za a barmu ba”
“Kina ganin mai zai bata wannan amincin namu? Jamila?” hadiza tayi magana tana kallon ta
Sake kora juice din jamila tayi kafin tace “cin amana, kinsan yanda na tsani aci amanata, indai bazakici amanata ba toh bakida yar uwa sama dani”
“In kuma naci amanar taki fa??? “
Chak jamila ta dakata da shan juice din, ta kure hadiza da ido babu kiftawa, yanayin fuskanta ya sauya tace “ke kinsan me zai biyo baya,bana yafiya, musamman idan aka shiga gonata da bai kamata a shiga ba”
“Zaki iya kasheni kenan???”
“Kafin na kasheki saina dandana maki zafin radadin cin amana a bakinki tukunna” tana kaiwa nan kwai ta fashe da dariya, kamar batasan komai ba, yanayinta ya sauya zuwa normal tace “ay nasan ma bazaki taba cin amanata ba ko hadiza?, mubar zancen nan ma, ke kinsan ni da zafi”
hadiza dai mamakin dadin bakinta take da yanda take mata fuska biyu, da gayya ta tambayeta idan taci amanarta me zatayi, bariki kenan, yanxu badan tasan halin jamilar ba da abunda zata iyayi ay bazata taba yarda da ta gano taci amanarta ba.
Shuru hadiza tayi bata ce komai ba saida jamila ta sake dagowa taga ita take kallo cikin ido,da alamu ma nazari takeyi da tunani, yanayinta bai sauya ba kwata kwata.
sai kawai kuma ta fara tafa hannayenta biyu tana kallon jamilar,
“hmm jamila kenan, jamila bakar kunama dafinki yafi harin ki zafi, toh Wasan kwailwayon ya isa haka,…badan na iya takuna ba saiki hallakani ta fuska biyu,” tana fadin haka ta miqe tsaye jamila ta bita da ido, irin bata gane ina zancenta ya dosa ba.
takowa hadiza tayi zuwa gefenta ta zauna kafin tace “Nasan kinsan cewa naci amanarki ammafa Karkiga laifina, nifa aminiyarki ce, munsan sirrin juna, sainaga ba laifi bane don munsan namiji guda daya, ni ban dauki wannan a matsayin cin amana ba da har zaisa kiyi tunanin zuwa nan don ki tona min aisirin da muka binne..kina tunanin zaki raina min hankali????? Hahah kin manta ni hadiza kenan? Nida akewa laqabi da kanwar shedan???Ni da ke Karr tasan karr fa jamila''
Tunda jamila ta kafa mata idanu ko kiftawa batayi ba,sannan bata nuna wani reaction basaida hadiza ta dubi kwalin lemon hannunta sannan tace ''a tunaninki zaki raina min hankali ko? sai gashi da hannun ki kin kawo min sauqin matsala cikin ruwan sanyi''
take jamila ta dubi kwalin lemon da take sha, tsoron da bai bayyana ba a fuskarta ya bayyana, jin kalaman hadizar, hannunta ya soma karkarwa ta dubi lemon datake rike dashi a hannun nata, batasan sanda ya sulale ba a kasa, kalar lemon ya koma baki, gashi dai taste din bai chanza ba, take ta gane cewa hadiza ta zuba mata bakar gubar nan a cikin lemo.
“……Ha..diza ni zakici amana????ni?”
“Ah ah banci amanarki ba,bazan bari ki ga bayana ba dole koni ko ke, jamila ke kin sani, ko ban kasheki ba nasan saikin tona min asiri na”
Tuni jamila idanunta ya soma ja ta fara kakarin amai, “gubar nan kika saka min???“
“Kwarai kuwa, jamila in ban kasheki ba bazaki barni ba, ni nafi kowa sanin koke wacece”
“Allah ya isa tsakanina dake…. Duk da kinci amanata banyi tunanin ksheki ba, sannan ban fasa nemo maki mafuta ba, amma ni zaki….” Ta kasa karasawa jin cikinta na wani murdawa, tana hawaye,”
“Da dai ban sanki bane jamila, bazaki taba kyaleni ba saikin dau fansa, allah ne ya bani sa’ar jifar tsuntsu biyu da dutse daya, kinada sauran minti ashirin daya rage maki, ina fatan zaki amfana da su”
Tuni hawaye ya wanke fuskan jamila harda majina, ta jawo mayafinta kamar mahaukaciya ta nemi futa daga dakin.
hadiza aka daura kafa daya kan daya, babu abunda take sai murmushi, tasan yanxu yanda hankalin jamila ya tashi dole makarin gubar zata fara nema, kuma tana da tabbacin kafin ta samu lokaci ya kure mata, don gubar bata wuce minti talatin a jikin mutun take kashesa,shiyasa ake kiranta da baqar guba.
***
Shugowar bahijja main house kenan ta soma jin ihu daya karade ya cika gidan gaba daya, hankali tashe ta dubi sama jin daga nan ihun yake, rabi ma tayi saurin futowa da sauri, bahijja kamar kafafunta zasu harde tsabar tashin hankali, tana haurowa ihun ya tsananta sosai wadda yasa gabanta faduwa don muryar maya dataji.
Rabi data biyota a baya tabi sahunta,cikin sauri bahijja ta karaso bedroom din don kofar na bude, take gabanta ya fadi dammm ganin maya tsaye, rike da hannunta ga jini na malala duk ya bata rigarta, ga kuma sabeeha a gabanta rike da wuka, jikinta sai kyarma yake hankalinta a tashe, komai ya faru cikin gaggawa ba tare da ta ankare ba.
maya na ganin shugowar bahijja ta sake kwala kara a gigice ta wani yi yuuu zata fadi bahijja tayo kanta jikinta na rawa, “innalillahi wa inna ilaihi rajiun'', gaba daya ta rikice lokaci guda don batasan takamaimai daga ina jinin yake ba.
rabi ta dora hannu a ka,hankali a tashe tace “na shiga uku ni rabi” a dubi sabeeha dake rike da wuka ga jini a hannunta.
Hankali a tashe sabeeha ta soma girgiza kanta tana duban hannunta dake karkarwa, ta kasa cewa komai don gaba daya jikinta ma rawa yake tsabar furgici.
“maya!!!!! Maya!!! Meya samekiii na shiga uku innalillahi wa inna ialaihi rajiun….jinin menene wannan? meya sameki”
Maya dake wani kif kifta ido kamar wadda za a zarema rai,kai kace yanke mata wuya akayi ta daga hannu tayi nuni ga sabeeha dake tsaye in so much shock.
Bahijja ta maida dubanta ga sabeehar, “ita ce…kasheni zatayi..”
Tuni hankalin bahijja ya tashi ta saki mayar tayo kan sabeehar, tana karasowa batayi wata wata ka sauke mata lafiyayyin maruka kusan guda shida a jere both sides of her faces, bata hkura ba ta dago idanunta ya sauka kan wani wire ta zarota, tayo kan sabeeha dashi wadda ta sulale tunda ta wanketa da maruka, kamar wadda aka aiko haka ta dunga zabga mata bulalarnan, bataji bata gani,rabi me zatayi banda ihu, duk yanda taso ta kwace sabeehar ta kasa, yarinya ta nemi rasa nunfashinta maya ko daman zubewar karya ce tayi tuni ta tashi zaune tana murmushi, “hajiya ya isa, dan allah kiyi hkuri, karki illatata, tsautsayi ne”
“Yimin shuru rabiiii” ta dakawa rabi tsawa, “kafin ta kasheta ni bari na kasheta”
Rabi ta kara kai hannu zata karba igiyar ta sake daka mata tsawa “matsaaaaaaa!!!!”
Tana fadin haka ta sanya hannayeta biyu ta dago sabeehar da gaba daya wire nan ya soma fasa mata hannu da jiki ga shatin bulala, dake fara ce saita koma jajawur kamar jan kosai, ta wani irin fusgota kamar tana jan kayan wanki, rabi tayi saurin bin sahunsu,
maya ko ta miqe a guje ta bi bayansu itama, dazu ka ganta zakace batada sauran nunfashi, ashe daman abun nata drama ne.
Haka bahijja take jan ta har zuwa kasa, rabi nata roko amma bahijja bataji bata gani, bata saki sabeeha ba har tsakiyar compund din gidan, tana sakinta ta soma kwaloma securities kira, dima diman sojojin dake tsare gate, aiko sai gasu radada su uku sun taho,
bahijja na haki tsabar tsananin bacin rai ta dubesu tace “ku fitar min da yarinyar nan kafin na illatata, let me not ever see her foot step a cikin estate dinnan”
Maya najin haka ta kyakyale da dariya, yanda ba kowa zaiji ba, plan dinta work out yanda ta tsara, burinta ya cika yau dinan.
Sojojin nan su uku haka suka zagaye sabeeha, rabi ta dora hannu aka tana innalillahi, “hajiya kiyiwa allah kiyi hkuri, yarinya ce karama, kuma macece karsu mata wani abun dan allah”
Rabi na kuka, idanun bahijja ya rufe gaba daya bataji bata gani, gaba daya ta gama tsanar yarinyar ko ganinta bata kaunar yi, yanayin yanda taga maya ba karamin tashin hankali ta shiga ba sai a lokacin ta tuna da mayar data gani a sama unconsciously.
Jikinta na rawa zata juya kenan aka bude tafkeken gate din, manya manyan motocin gidan suka soma shigowa, kamar convoys, babu wanda ya lura da abunda ke faduwa tsakar gidan saida suka karaso dabb, ga bahijja tsaye ba lulubi a furgice ga sojojin guards dake kula da tsaron apartments sun zagaye sabeeha da bama a hangota, kokari kwasarta kawai suke kamar kayan wanki, sannan ga rabi daketa faman kuka a gefe tana bada hkuri sai maya itama a tsaye da riga duk jini.
Motar su ya sameer ce a gaba da suka fara shugowa wadda driver ke tukawa,daya dauko su shida hamad daga airport, isowar su kenan suka wuce asibiti, anne da nanna na bayan motar, sai anty fadila a bayan motar taj sai kuma hamad daya zauna a gaba sai kuma motar daddyn maya dake biye da tasu da shima ya dawo gidan a daidai lokacin, duk babu wanda yasan meke faruwa a wajen saidai ganin yanda sukayi chirko chirko kana gani kasan ba lafiya ba.
A tsanaki sukayi parking ta gaba gaba sannan suka fifito, banda taj daya tsaya cikin motar sa yana amsa wani important call, tundaga shugowar motocin nan gaban maya ya fadi, ba ita kadai ba hatta bahijja amma kuma har zuwa lokacin idnaunta a rufe suke,cikin sauri ta karaso jikin mummyn nata ta kankameta, tana wani rawar jiki, harda dafe kai, bahijja tayi saurin riketa a jikinta.
Kusan a tare duk suka firfito, hamad ya bude seat din baya, bayan ya fito da wheelcahir da za a saka anne, nanna ma ta futo duk suka maida hankalinsu ga inda su bahija suke, uncle sameer ne yayi gaggawar karasowa wajen yana duban guards din suka sara mashi, “whats going on here?”
Bai gama magana ba ya hango sabeeha da suka zagaye ta rakube “subhanallahi whats going on here, meke faruwa anan???”
Daddy daya biyo bayanshi yana karasowa shima take gabanshi ya fadi, yana duban bahijja da maya da duk jini ya bata jikinta yace “innalillahi wa inna ilaihi rajiun? Bahijja???meke faruwa anan,”
Duk kowa yayi shuru babu abunda kakeji sai sheshekar sabeeha ahankali abun tausayi, gashi babu wanda ya bada answer,
“Kunyi shuru whats going on here????”
“Wannan yarinyar…” bahijja tayi nuni ga sabeeha, har hannunta na karkarwa idanunta yayi jajawur tsabar bacin rai, ta cigaba “tayi kokarin ilatar da maya, badan ikon allah yasa na…”
bata karasa magana ba nanna ta karaso don ganin meke faruwa a wajen, tana isowa ta doka salati,wnda hakan yasa bahijja dakatawa bata karasa magana ba “innalillahi wa inna ilaihi rajiun,”
“Meya faru bahijja? jinin menene wannan?”
Abunda ta fada dai shi ta sake maimaitawa “Wannan makirar yarinyar ce tayi kokarin illatar da maya, badan ikon allah ba saidai a tsinci gawar maya,''
''wani irin magana ne wannan bahijja,ki mana bayanin meya faru, meya hadasu da har zai illatarwa,?'' nanna ta sake magana hankali a tashe.
'' na shugo main house naji maya na ihu daga sama, ina hawa sama naga wannan shiadaniyar yarinyar rike da wuka a hannunta ga maya jikinta duk jini unconciously, , she was trying to harm her tana kokarin kashemin yarinya?”
Duk gaba daya sai suka dago suna kallon mayar data langwabe hannunta na fidda jini, a rigarta ma duk ta baci da jini, daman da gangan ta shafa jinin don afi yarda da gaske sabeeha kokarin yankata tayi da wuka,sai faman hawayen munafurci take tana langwabewa.
“Innalillahi wa inna lailihi rashin….wuka? Ta yanka maya??? why??Meya hadasu? a ina ta yanketan”
Nanna ta sake jero jero mata tambaya, rabi dai tayi shuru har zuwa lokacin hawaye takeyi, nanna ko ta kasa gasgasta abundaa taji.
Daddy kam gaba daya lokaci guda ranshi yayi mugun mugun baci, zancen bahijjar gaba daya doesnt add up, idan ta samu maya unconciously bazasu ganta tsaye ba saidai a ganta ranga ranga sai asibiti, kallon maya kawai yayi ya gane kamar bata da gaskia, yanda take ta faman kauda idaanu tana qin hada ido dashi.
''toh tsayuwar me kuke baku kaita asibiti ba?, how badly was she injured? sannan Su wannan securities dinfa? Me sukeyi anan?” majeed ya sake magana, “
“bakaji me nace bane?, na ganta tana kokarin illata maya, she injured her da makami, badan nazo ba kasan me zatayi ne??? Wallahil azeem yarinyar nan bazata sake kwana cikin gidan nan ba, kuma she must learned her lesson don saina kulleta ku fita da ita kafin na ilata ta”
“Bahijja, are you even listening to your self? Kin tsaya kinyi binciken abunda ya hadasu?”
“Bincike???? Majeed bincike fa kace wani irin bincike zanyi i saw her with my own eyes, bawai fada min akayi ba, rike da wuka tana kokarin harming maya, kuma nasan ba kowa ne ya sata ba sai makira annamimiyar uwarta, jinin hadiza ce fa? Menene bazatayi ba? Daman da sun samu waje babu abunda bazasuyi,, har kun iya manta abunda hadiza tayi, kuka barta da diyarta suna zaune cikin ahalinnan to wallahi ni ban mance ba, muna zaman lafiya mun gayyato ma kanmu bala’i da masifa, su fitar da ita tun kafin na illatata don wallahi zan iya nakasa ta…” Bahijja ta karashe rai a bace
Hamad na turo anne basu kaiga karasawa inda su bahijja ke tsaye ba suka juyo ga inda suke jin magana da karfi, kamar yanda kowa ya maida dubanshi ga jamila dake tsaye.
“Ai KUWA DA KINYI BABBAN KUSKUREN DA HAR KI KOMA GA ALLAH BAZAKI TABA YAFE MA KANKI BA'' tana fadin haka ta bisu daya bayan daya da kallo yanda suke kallonta itama, sai kawai ta sauke wani makirin murmushi, aranta tace lokaci yayi.
MATAR TAJ (destined with you)
Written by
Queenmarh
Book2
PAID