Chapter 81
Matar Taj Part 2 Complete Hausa Novel. · about 31 min read
Zuwanshi kamfani ba karamin tarzoma ya tado ba, washe gari gaba daya kafar yada labarai da media ta dauka, waenda basu sanshi bama suka fara sanin shi, mata da maza,ashe jiyan daya zo har an dauke shi hoto first thing first the next day ya zama topic of headline da safe, the return of the taheel heir bayan matsalar kwakwal daya samu, nanfa mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu kowa da nashi.
Mutanen kamfani kuwa nanma suka fara rade rade, ay jiya daga zuwanshi ya kawo masu solution din matsalar da suke ciki, workers are in support of him, shareholders kuwa daman kowa ya gaji da alamarin hidaya, ta kanaynnaye, bata neman shawarar su idan zatayi making decision for the kamfani, abu dai fa kamar wasa wasa ya fara zama rigima don har meeting aka shiga akan wannan zancen akan dole ta sauka ta bama taj yayi handling kamfani, shiko baimasan me ake ciki ba kwata kwata, he’s just prepping yabar kasar gaba daya don he can’t stay here anymore.
Yana cikin hada kayanshi call din mutallib ya shugo, bayan sun gaisa yake fada mashi yanxu yake ganin yana yawo a social media tun safe, yayi mamki sosai don shi saiyayi wata da watanni bai hau instagram ba, and shiba ma’abocin kallo ba.
Yana kashe wayar ya shiga links din da mutallib ya tura mashi ya fara dudubawa, babu abunda akeyi sai sukar hidaya ana maganar cewa tasan ya samu sauki amma taqi barinshi yayi taking over, maganganu dai iri iri daga wannan sai wannan lokaci guda hankalin shi ya tashi, shifa baya son crises din family business dinsu, he’s not interested in that at all.
Yana zaune bakin gado yayi shuru yana duban wayanshi call din hidaya ya shugo, saida yaji wani irin a jikinshi, yana dagawa ta soma magana “kazo nan office ka same rn”
Tana fadin haka ta kashe wayar, miqewa yayi ya zari key dinshi ya futa.
Yana isowa ma’aikata kamar zasu kwanta mashi, wani irin kwarjini yake dashi da haiba yake dashi, he’s walking majestically classy and handsome, duk inda ya gifta suna gaishesa yana daga masu hannu, kana ganinshi kasan girma da arziki ya bi jikinsa, fadwa dake taaye daga office din hidaya tun daga 10th floor take kallonsa, zuwanta babu abunda tayi banda balbala ma abunda ke cin hidaya wuta, saida ta gama zugeta tsaff ta yanda hidaya bataji bata gani.
Babu abunda take sai smirking, its about time for her to step up on them, he’s her next target yanxu.
Kai tsaye ya shugo babu wanda ya tare shi har office din hidaya yana cin karo da fuskar fadwa ya wani hade girar sama da kasa kamar bai taba dariya ba kap rayuwarshi, tun kafin ya karaso hidaya ta miqe tsaye idanunta sunyi jaa sosai, ta nunashi da yatsa, “you are going to fix this? Okay? Bazan taba barin kamfanin nan ya salwanta ba, not now not ever.. now let’s go”
Kallonta kawai taj yake da mamaki kwance akan fuskanshi, mey first love ke tunani ne? Cause ya kasa gane maganganunta daga jiya zuwa yau, yanda take magana kamar tana magana ne da wani makiyinta ko kuma someone that she’s scared of
Futa sukayi gaba dayansu zuwa wajen press conference dake cikin kamfanin, suna shugowa aka fara kyaskyasta masu hotuna, yan labarai sun cika wajen, charaf ta k kama hannunshi ta rike cikin nata tana wani irin makirin murmushi kamar ba ita ya gani ba yanxu a office dinta, haka ta dunga janshi har suka zo wajen zamansu suna facing reporters dake ta faman daukansu hotuna.
Suna zama tayi gyaran murya ta soma magana gwanin ban tausayi.
“We are here to clear the air and the rumors going around, kamar dai yanda kuka sani wannan qanina ne kuma jinina abun alfahari na banida kamarshi” ta karashe tana sumbatar hannunshi harda hawayenta, “some few months ago ya samu amnesia which cause alot of problem and emotional damage to all if us…his relative,”
Ta dan dakata tana matsar kwalla, abunfa kamar drama taj yayi saqe.
Wani reporter ne ya jefi mata tambaya “shin ya samu sauki ne? Kuma zaki bashi makaminshi na shugabancin wannan kamfanin”
Da sauri ta dago idanunta harda kwalla ta daga hannu secretary dinta ya shugo da wasu takkardu harda wani professional likita da aka sanshi sosai a kasar suka shugo tare suka tsaya daga bayanta doc din ya gabatar da kanshi kafin ta bama mutumin answer.
“Wannan shine dr james, shine ke handling case din tajudeen, kuma har yanxu shike kula da lafiyarsa har muna fatan allah yasa ya dawo hayyacinshi, my brother is not just mentally ill, he’s also suffering from brain tumor, he only needs you prayers rn”
Tunda ta soma magana yake kallonta da mamaki? Hidaya ke karya agaban idanunshi kuma akan lafiyarshi saboda kamfani, duk girmanta da yake gani saida ya runtse idanu ayau don tayi mugun bashi mamaki? Daman dukiya da power zaisa mutun yayi haka?”meysa zatayi haka? Why lie?
“But madam ayanda muke ganinshi a haka he doesn’t look like someone that…”
Saurin katseshi doctor yayi yana mashi bayanin ay haka yake, za a ganshi kamar lafiyayye saidai kuma baya cikin hayyacinsa baisan me yake ba kuma yana da cutar mantuwa, kai wata karyar da aka lafto kan rashin lafiyar nan ba karamin mamaki ya bama wasu reporters dinba saidai basuda jaa da maganar doctor din tunda official statement ne.
“Ma’am akwai hirar da kikayi watannin baya da suka wuce and kin shaida mana baida wani amfani don kwakwalwarshi ta tabu gaba daya, shin akwai wani hope din samun lafiyarshi,?”
Kamar jira take ya kai karshe tayi saurin cewa “babu wani hope..babu he will forever stay like this,”
“Ma’am bakya fatan ya samu sauqin ne?”
Sai a lokacin ta lura da tabarar data so yi nan danan ta sauya fuska kamar ba itava abun tausayi ta sumbashi kumatun taj ta shafa kanshi kamar wani dan yaro tace “sai nafi kowa farin ciki idan naga qanina ya dawo hayyacinshi ya samu lafiya, he’s my life, my everything he only has me in this world cause ni kadai ce gatansa kuma farin cikin sa”
Chapp wannan Kalamai nata na karshe sun kara rikita mashi lissafi, ashe irin wannan words din dake futowa daga bakinta are something that are easily comprehended? Sai ya fara contemplating shin daman duk soyayyar da take nuna mashi throughout his life are just like a comprehensive words?
Wallahi gaba daya he’s lost in his thoughts, baima san har ta jawo hannunshi sun futo daga wajen ba, sai binta yake kamar raqumi da akala, suna isowa office dinta ta dubi fadwa tace “take him home”
“Kai kuma babu inda zakaje, you will stay back, and i forbid you from any activity da zaisa ka shiga public, gym da kake zuwa, malls da duk wani encounter din da kake,”
“Why????” Shine kalma ta farko data futo daga bakinshi, har gabanshi ta iso tana mai kallon cikin idanunshi yana kallon nata tace “because i said so, i will never allow you ka ruguza min duk wani tanadi danayi shekara da shekaru, you’re nothing and you can never be anything da zaisa…”
Sai kuma tayi shuru kawai ta dubi fadwa tace “take him home, and makesure that babu any reporter da yayi noticing da motarshi yazo, zansa amaida motonshi gida.”
Taj fa is speechless, ya rasa tunanin da zaiyi, he’s so disappointed, wallahi inya cigaba da kallonta sauran respect din da yake mata zai iya zubewa kasa, baya kaunar karya, balle yayi participacing a cikinta, ta sashi cikin wani state daya kasa gane what is right and wrong, she manipulated him into thinking duk yanda akayi she has her reason for what she did amma he’s giving her benefit of doubt wannan yasa bai musa ba yabi bayan fadwa, saidai abubuwa da dama na mashi yawo a kwakwalwa musamman maganar sabeeha, inda take ce mashi meysa bazai bude idanunshi ba? Waenda ke sanshi su yake nisantarwa waenda basa qaunar ganin shi sune yake saka wa as his top priority.
Yana cikin wannan tunanin fadwa ta bude motarta ya shiga itama ta zaga wajen driver ta shiga, tasaka belt, sannan ta fara kokarin saka mashi ya kalleta tace “akwai reporters anan you need to behave”
Tana fadin haka ta fara janyo belt din kamar tana shafa kirjinshi harta saka mashi ta sauke wani makirin murmushi, tana hango yanda he’s lost in his thought gaba daya, badan hidaya ba bazai taba shiga motarta ba lallai dole ta nemi amincewarshi da yardasa, ta haka ne kawai zata maidoshi tafin hannunta.
Suna cikin tafiya ta soma magana da siyaya.
“Why are you so shocked kamar bakasan how obsessed she is akan power ba da kamfanin nan? She wants it all to her self, there no way zata bari komai yayi slipping a hannunta ba so easily, abubuwan da tayi akan kamfanin nan yafi karfin tunanin ka so i will advice kayi stooping so low karka sa ta fusata ka koma gidan jiya tunda gashi nan ka dawo normal ”
Yana jinta yayi banza da ita saidai gaba daya maganganunta yayi breaking dinsu into his head, trying to understand inda maganrta ta nufa.
Chan gefe ta gangara da motarta tayi parking ta dubeshi, “you need to trust me taj, nasan we are not in a good terms amma inason ka sani bazan taba cutar dakai ba, ina sonka ina qaunarka”
Wani irin banzan kallo ya mata ranshi a mugun bace har zai bude bayan motar tace “kanaso ka kira ma kanka masifa kenan? Bakaji me tace bane? Karka sake kayi abunda zaisa ayi tunanin lafiyarla kalau, kalla!!”
Ta nuna mashi mirror, waenchan da kake gani reporters ne, kuma kana futa zasuyi capturing and i promise me you will be shattered”
“What do you mean?” Ya tambayeta a zafafe, “when the time comes you’ll understand, hidaya bata kaunar bata son ganinka..youre a threat to
her”
Wata irin tsawa ya daka mata dayasa ta zuba mashi ido a furgice, “don’t you dare..dont ever say that to my face, kina tunanin zan taba yarda da maganar ki?karya kike i will never, now step on this car kafin”
“Calm dowm mr T ford”
Surprisingly yake kallonta jin kiranshi da tayi da sunan, mumushi kawai tayi ta kunna motar suka bar wajen.
Yana dawowa gida sama ya wuce rai a bace,sai yanxu yake ganin all his life he’s being controlled, zama yayi yana kara kallon press din da sukayi daxu, daya kalla ranshi ke kara baci, magnagnunta sun bashi mamaki sosai, harya fara tunanin anya hidaya ce wannan? The hidaya that he knows will Never do this, koshi banza ne wannan kadai daya gani bawai an fada mashi ba ya zashi kokonto akan rayuwarsgi gaba daya, wallahi bai taba son shiga cikin family business dinsu ba he’s never interested kwata kwata, why are people around him like this? Haka khaal shima yyi kuma yayi mamakin labarin dayaji yanxu kuma hidaya? Noo noo? Thats impossible, dole she has her reasons maybe kamfanin yana cikin matsala, shiyasa take kokarin ganin ta rike kamfanin a wajen, deep down wata zuciyar tashi na ce mashi are you blinded? Open your eyes and face the reality of your life, saidai kuma tsabar how manipulated he is yasa yaqi bude zuciyarshi da zancen, saidai tambayr kanshi daya soma yi? what’s going on in his life? What has he missed?
Hidaya ko takanshi batabi ba, cause batajin he needs any explanation from her, lokaci guda maganar taj ta rufe ruff kamar ba a taba yinshi ba, kuma shawarar fadwa ce data kawo mata last minutes lokacin da ta rasa yanda zata shawo kan matsalar da take ciki.
Da daddare daidai lokacin da take yawan shiga study room dinta yaje don ya sameta kuma ya shaida mata cewa bashida interest alan family business din, koda ya karasa yana gabda yin kncking ya soma jin magnaganu daga ciki, maganganun are not very clear kuma bawai yayi eavesdropping bane kawai yaji last sentence din nata ne a kunnenshi kamar wake up call, “i was silent and low for a reason not because na barshi ne donya ruguza min plans dina,…i have come this far babu wanda ya isa yayi crashing dina, nor him not even khaal daya shiga gonata ban barshi ba.. kina tunanin turashi da nayi karatu chan england is not for a reason? No!!!“
Magana fadwa ta maida mata saidai ita ba ajin muryarta kwata kwata, dan dakatawa yayi yana nazari maganar me suke? Mey ya kawo khaal a zancen nasu har take cewa shima bata barshi ba? What is the beginning of the discussion,sannan turashi karatu England datayi is for a reason? What was the reason?”
Gaba daya ya kasa puzzling maganganun nata, shigan da baiyi ba kenan ya juya yana nanata magnganun nata akanshi,fadwa ta fito daga ciki, tana ganinshi ta tabbatar yazo wajen hidaya ne, hiw she wish he came earlier dayaji magnagnun dasukayi da hidaya.
Saidai hakan ma bata baci ba its a chance to her wannan yasa tayi wani murmushi, cikin sauri sauri tazo wucewa ta gefenshi tayi saurin watsa papers din data fito dasu a gabanshi intentionally, karaf idanunshi suka sauka kan headline din kan paper don da harufa manya aka rubuta, transfer of inheritance da shares ne
A kasan baiga sunan waye a jiki ba don rubutun sunyi kananu.
Kauda kanshi kawai yayi ya wuce ba tare da ya waiwayeta ba, yanata saqe saqe maganganunsu aranshi.
Fadwa ko tana tattare papers din ta miqe tabishi da kallo harya shige daki tayi smirking ita kadai tasan abund ake ranta.
Tunda ya dawo dakin babu abunda yake sai safa sa marwa,tunanin maganganunsu ya gama addabarshi.
Yana cikin wannan tunanin call ya shugo mashi, unknow number ne wannan yasa yaqi dagawa, tana katsewa wani call din ya shugo rai a bace ya daga wayar yakai kunneshi, to his fullest surprise muryar fadwa yaji, har zai katse wayar ta dakatar dashi da sauri tace “zan fada maka abu daya ko ka yarda ko karka yar wannan choice dinka ne,”
Kitt ya kashe wayar yaqi sauraron abunda ta fada sannan ya danna mata blocking.
Fadwa tunda ta tashi take nazarin yanda zatayi ta shiga tsakanin taj da hidaya, duk wani trick tayi amfani dashi amma alamun sun nuna basa tasiri akanshi, kwata kwata, tsakanin jiya da yau ta kira wayanshi sau ashiri da different numbers baya shiga saboda yayi restricting wayan.
Wata dabara ce tazo mata wadda take tunanin zata iya amfani da wannan don ganin ta cimma burinta.
Achan nigeria yau kwanan sabeeha bakwai cirr, kuma tayi shi ne cikin kunshi da rashin walwala, wallahi harta soma baki, sauro ya gama cicinye ta gashi ta saba da hutu, chan saudi babu sauro sai ac nanko sai azababben zafi, ko arzikin fanka bata samu ba a parlor iya daki ne kawai akwai fanka, skin dinta yayi rudu rudu yayi jaa sosai abun tausayi, tsakaninta da Hadiza kuwa tsangwama ne da masifa, ko gaisheta tayi saita balbale ta da masifa, wallahi ko qaunar ganinta batayi, yanxu haka suna tare da jamila datazo gidan suna kuskus.
“Kinga wannan yarinyar ko wallahi wallahi kadara ce a wajen ki hadiza, ki jata aiki gidan abuncin nan da kike zuwa, ko allah zaisa wani tsoho ya ganta anan wajen ki aura mashi ita.”
Shuru hadiza tayi tana nazari kafin tace, “jamila kinsan abunda kike fada kuwa? In fiddata duniya fa kike cewa?“
“Toh ajiyeta zakiyi? Dole wata rana zaki aurar da ita, bayan wannan ma yanda rayuwar nan ta sauya mai kudi ma yana jin jiki balle talaka? Na rantse da allay idan rusau dinnan da akeyi yayo kanku shikennan kun shiga uku”
Hadiza ta mata mugun kallo tace “dole kice na shiga uku ay tunda kunyi nakanku ke bakida damuwa”
Jamila tace “to ay na baki shawara kinqi dauka, ana takai wake ta kaya? ki sata gaba kawai ko wanke wanke ke tanayi a wajen mene amfaninta in bata nemo ba? Ke zaki nemo mata taci ko kuwa?”
Sun dade suna tattaunawa don da safe ne kafin jamila ta wuce gida, hadiza na shirin fita sabeeha ta shugo, har kasa ta duka ta gaisheta ko arzikin amsawa bata samu ba, wannan kudin da mutallib ya bata su ta zaro ta ajema hadiza a gefe, kafin ta soma magana a natse cikin kamewa, “mama, ga wannan ko za a saya abuncin gida dashi”
Kallon kudin hadiza tayi kafin ta dubeta tace “fita ki jira ni waje”
Tana futa hadiza ta kwashe kudin ta saka a jakarta sannan ta saka hijab dinta ta futo.
Anan parlor taga sabeehar na ninke kayan ta data wanke, mamakin girman yarinyar take sosai ba kadanba, ta ciciko babu alamun rama a tattare da ita, saita fara wondering wani irin gida aka kaita ne haka? Kodai iskanci tace tanayi achan, yanxu dai ba wannan ne gabanta ba wannan yasa tace “tashi muje”
Miqewa sabeeha tayi ta nada mayafin abayar kanta sannan tabi bayan hadiza suka kama hanyar bakin titi a kafa, kwatwa batayi gigin matsowa kusa da maman tata ba don tana gaba ita kuwa tana bayanta har suka samu masu okada hadiza ta biya suka hau.
Basu tsaya ko’ina ba sai Gargajiya food service, babban wajene sosai gaskia sai faman gyare gyaren wajen akeyi ana modernizing din wajen, chan wajen parking lots ko shaqe yake da motoci masu nunfashi.
Lokacin wajen karfe sha biyu na rana mutane dayawa sun fito yin lunch.
Cikin wajen suka shiga ta baya inda ma’aikata suke, kowa da uniform dinshi, masu serving masu dafawa, masu sarrafawa kowa da nashi shashen harda masu wanke wanke da gyare gyare.
Madam din na daga tsaye tana inspection hadiza na hangota tayi saurin karasowa inda take sabeeha na biye da ita a baya tana ta sissinne kai, matar irin yarbawan nan ne.
Gaisheta hadiza tayi sabeeha ta dan duqa itama ta gaisheta daman madam tee suke ce mata.
Kallon sabeeha matar tayi sannan tace “wannan fa”
“Daman yata ce, naga yau aikin da yawa shine nace ta biyo ko zata taimaka da wani abu, madam ta iya komai wallahi babu abunda bazatayi ba”
Kallon sabeeha matar ta sakeyi tace “yanxu wannan yarki ce? Ahh she no dey resemble you o, ke kin taba aiki ne?”
Nan ta girgiza mata kai, wallahi sa’a kawai sukayi don hadiza batayi tsammanin madam din zata bar sabeehar ba.
Aiko barinta datayi dinnan yasa hadiza jawa sabeeha kunne sosai, haka ta shiga cikin ma’aikata, ta soma wanke wanken manya manyan tukwane, don ranar akwai abuncin sadaka da za ayi.
Ay kuwa ta durzu, ga uwar rana baiwar allah ko ruwa bata sa a makoshinta ba, madam ko ta yaba da aykinta sosai don data ganta bata yarda yar hadiza bace don yarinyar tayi kalar hutu sosai.
Sai wajen yamma suka dawo gida da takeaways, harda dubu biyu da madam ta bama sabeeha don yarinyar ta burgeta ga ladabi ga biyayya.
Washe gari haka suka sake komawa, wannan karan ba wanke wanke madam ta sakata ba, turata ta dungayi wajen delivery idan anzo pickup, tama dawowa kuwa zata dawo da kudi an bata tips, aranar saida aka bata wajen dubu biyar, madam bata karba sisi ba ta basu, hadiza ko bakinta kasa rufuwa yayi, ay batansan shawarar jamila zata zame mata alkhairi ba sai yanxu don ranar har tsire ta siya taci ta rage mata.
A kwana a tashi kusan kullum haka suke, yanxu ya zamana kullum tare suke zuwa, wani sa’in ma idan babu aiki haka hadiza ke turata itako ta zauna a gida, sai ya zamana kamar hanyar allahiri ce tazo mata, ta saya sabbin kananun atamfofi guda biyu da atamfar leda guda biyu da hijabi biyu ta dinka, ta bama sabeehar daya saba nanata kaya da takeyi kusan kullum, sannan ta hanata saka wani mayafi, tsoffin hijabanta ta hadata dasu.
Ranar friday da sassafe suka shirya domin ranar akwai abuncin sadaka da wani dan majalissa ya bayar, za a rabawa mutane dari biyu, bayan sunkai wajen suka fara aiki, sabeeha na yanke yanken su albasa da sauransu.
Sunkai har yamma suna aiki sai wajen karfe biyar suka gama, suna cikin shirye shiryen tashi madam ta zagayo baya, daga yanda take magana a waya zakasan anyi babban order ne ko an bata kwangila mai girma sosai,
Baki a washe ta dubesu ma’aikatan nata gaba daya ta masu alamun dasu tattaso, suka zagayeta, “mun samu kwagilar abunci da zamuyi na kwana biyar, saidai kuma wannan karan ba anan zamuyi ba hiring dinmu za ayi, so inason mutane biyar suyi volunteering”
Gaba daya shuru sukayi,aka rasa waenda zasuyi volunteering saboda cikin matan akwai waenda ke da aure, wasu kuma zawarawa ne, hadiza ce kawai da wasu zawarawa biyu suka daga hannu, cikin yan matan kuwa mutun daya ce ta daga hannu,madam na ganin suna neman disappointing dinta, badan tayi training dinsu ba a daidai wannan lokacin data koresu wallahi, tanason idan za ayimata aiki a dunga yi da zafi zafi, musamman idan taji aikin masu hannu da shuri ne musamman wannan gidan da zasuje suyi aiki, millions zata samu wallahi tunda auren farko ne da za ayi a cikin familyn, so dole za a kashe kudi ayi abu mai kyau sosai, kallon sabeeha madam tayi sannan tace “ke ma zaki bisu, tunda kin zama staff”
Hadiza najin haka wani dadi ya lulubeta, batayi tsammanin madam zata dauki sabeehar ba wannan zai bata damar daukan shawarar jamila, tabar aikin anan itama ta dan fara ko a cikin gida ne don tasan customers din madam din kuma tana da numbers dinsu, zasu iya kiranta tazo har gida ma ta masu.
“Gobe da safe zaku zo cikin shirin around 5,akwai duk wani abunda za a buqata achan, sannan zan shirya menu, daga gobe saturday zuwa monday za ayi abinci da safe da rana da kuma dare, both continentaland traditional, duk wadda tasan zata kawo min matsala gwara tayi magana tun wuri, zan hadaku da maza biyu saboda su taimaka sai masu serving uku,”
“Tohm madam bazaki samu matsala ta wajen mu ba Insha allah”
Sauke ajiyar zuciya tayi sannan tace “5am sharp.. za a zo daukan ku by 7, dot, aikinku zai fara da lunch ne banda breakfast gobe”
“Okay ma’am” duk suka amsata cikin ladabi.
Wani irin dadi hadiza takeji yau, dukda ba wannan ne aikinta na farko ba na zuwa gidan mutane, last one da sukaje sun samu kyaututka sosai, harda su soveignair aka basu, fankar dakinta ma souvenir dinne na wani bikin da gomna da akayi anan abuja, bayan wanna an masu tara ta arziki don harda ragowar kayan abunci aka basu.
Washe gari da safe misalin wajen karfe hudu sabeeha ta tashi tayi wanka ta gyara dakinsu sannan ta dafa ruwan shayi ta shirya kayanta guda biyu sannan tasa abaya cikin abaya’s din data dawo dashi ta dira hijab din da hadiza ta bata akai.
Wajen karfe biyar saura yan mintuna kadan suka fito, tsakar gidan babu kowa sai kiraye kirayen sallah dake tashi.
Ataqaice dai biyar daidai ta masu a gargajiya plug, madam anan ta kwana ma tsabar bata son wani mistake, duk wani abunda zasu buqata an shirya shi harda menu din spcial abuncin su, sauranma haka suka iso suma suka zauna, misalin karfe bakwai daidai motar da zata daukesu ta karaso, koya ya dau kayanshi, sabeeha na rike da nata dana hadiza suka fito compound din nan suka tadda madam tsaye sai fama washe baki take, “acema hajiya waennan sune professionals dinmu, kartajo damuwa indai wajen aiki ne,”
Tunda suka tukaro motar hadiza ta tabbatar gidan manya zasuje ba kananu ba din ba a taba kaisu a irin luxury car haka ba, wani sain ma tura su akeyi cikin motar gargajiya plug din.
Ciki suka shishiga sabeeha sai baya baya take har motar yayi occupying kowa ya tage gaba ne babu mutane, wannan yasa ta shiga gaban ta zauna suka fuce daga wajen.
Tafiyace mai dan tsayi kusan kinti talatin, hadiza har gyagyadawa saida tayi anji sanyi ac, bama ita kadaiba harda sauran na bayan, so basu san har an iso ba.
Tunda suka karyo layi sabeeha kebin anguwar da kallo, wallahi saitaji kamar tana saudi, anguwar is so organize, peaceful and elegant, babu tarkacen gidaje sai tairarru da suka gaji da kyau, ga uban securities a anguwar kamar villa lol.
Daidai gaban wani katafaren gida driver ya tsaya yayi horn, securities masu uniform suka leko, ganin motar yasa suka bude gate din ya kutsa kai cikin gidan, sakin baki sosai sabeeha ta dunga yi tana kallon girma gidan da apartment har guda hudu a wajen, gari guda.
Kashe motar Driver yayi ya bude motar gaba daya suka fufito, hadiza ma bin gidan ta dunga yi da kallo kamar ba gidan biki ba babu hayani ba komai sai tarin motoci burjik kamar kamfani.
Driver ne ya masu jagora ta bayan babban apartment din dake tsakiya suka zagaya, sunsha zagaye kuwa kafin ya tsaya daidai inda ya kamata ya dakata sannan ya kira a sanarda isowar masu abunci.
Wata ce ta fito ta masu jagora zuwa bq da aka tanadar masu, wallahi shima apartment ne mai zaman kanshi babu abunda babu a ciki, ga dakuna har uku a ciki yanda zasu sake harda parlor, babu abunda babu a ciki.
Ajiye kayayyyakinsu sukayi, yanmatan suka karbi daki daya sabeeha da dayar yarinyar sukuma sauran suka karba sauran dakunan, mazan kuma aka basu dayan part din.
Wannan matar ce dai ta sake zuwa ta masu nuni da inda zasuyi girkin da komai da aka tanadar masu sannan tace hajiya tace duk abunda suke buqata da babu su fada sukace tohm.
Nan suka fara prepping abuncin rana na baki, babu zama haka suka dunga dorawa suna saukewa, ana lodawa sabeeha kayan wanke wanke.
Sai wajen azahar suka samu gamawa, kuma lahamdulillahi everything looks perfect.
Bq suka koma sukayi wanka sukayi sallah sannan suka ci abunci, daman serving ba nasu bane don akwai waenda zasuyi serving.
Sabeeha tunda ta zauna ta kasa tashi, wani irin ciwon baya ne ya riketa, tasa. Ba period zatayi ba amma abun yayi yawa daurewa kawai takeyi.
Koda dayar budurwar mai suna habiba ta ga yanda ta kasa tashi ta tambayeta menene nan take shaida mata abunda ke mata ciwo, ta tausaya mata sosai don duk yawan uban wanke wanken nan haka hadiza tace tayisu duka don zasu buqaci kayan anjima idan an tashi yin dinner.
Dakyar ta samu tayi wanka sannan tayi sallah ta kwanta ko abuncin bata samu taci ba.
Chan cikin gida babu abunda ke tashi sai guda riiiiriii…a daidai lokacin da aka shugo da amadya cikin gidan, wato ana sallar azahar gidan ya hade da mutane sosai, yan uwa da abokan arziki, dangin amarya dana ango, ango dan gata, babban jika ga hajiya anne ikon Allah, Sufyan Sameer Santuraki da amaryarsa leedarh Yusuf.
Jiya jum’a aka daura aurensu a yola, don yar yola ce, yau saturday kuma za a fara hidimar biki gobe budan kai da yini.
Bikin babu wani hayaniya don ango baya kasar ma ana daurawa amaryar zata bishi chan england, don achan yake da zama tunda ya gama karatu ya samu aiki, haka zalika yan gidan basu fiye son wani kide kide da rawe rawe ba ko gayyar su dinner dasu mother party daddys party da sauransu, saidai a cikin gida zasuyi duk wani hidima, aci mai kyau asha mai kyau ayi ruwan kudi aji dadi rayuwa between familys.
A babban parlor aka zauna dayasha ado, kai kudi yayi allah ka mana arziki mai albarka, kowacce ka ganta zaune babu abunda take aai walwalin,su anty fadila an fito, tasha lace mai masifar kyau da tsada, fuskanta ta danyi makeup mara hayaniya, su nanna da anne na zaune suma dai ba’acewa komai, bakiin anna yaqi rufuwa yau auren babban jika, anty mubina ma na zaune da mubin dinta a kan cinyanta, she can’t believe dansu ne yayi aure yanxu lallai sun manyanta, dangin amarya ma ba a barsu a baya ba don gaba daya sunsha gayu sosai don suma sunada arziki sosai, tarba ta mutunci aka masu sosai sannan aka shigar da amarya bayan ta gaisheda kakanni.
Su laila karama ana daga sama, sai faman tashin maya take taqi tashi, wani irin barci take kamar matacciya tun safe ko wanka batayi ba.
Anty laila kuwa uwar ango tana daga chan bangarenta kamar zata fashe, yan uwanta sun zagayeta gaba daya, masu zigata da masu nuna mata fushinta bashida amfani, don abunda takema fushin bashida amfani.
Tunda ta zauna babu abunda take sai hade haden rai, maysa a matsayinta na mahaifiyar sufyan baza a fara zuwa wajenta ba,? Ita gaba daya auren nan shes not in support of it, sufyan is just 27, dandai ya dage ne yanaso kuma bata isa ta hana ba.
A taqaice dai sai wajen dare aka dungumi amarya bayan an shiryata aka kaita wajen maman ango, taje ta gaisheta, ganin yanda dangin amaryar suma suke jin kansu yasa laila ta sauke nata kasa.
Da yamma sunci wani kwakwa, don aiki suke nonestop, daurewa kaqai sabeeha take, itace dauko kaza jeki kai kaza ajiye kaza bar kaza miko kaza.
Sai dare wajen karfe tara ta samu sarari, tayi wanka tayi sallah ta kwanta jiki duk wajala duk tsami.
Washe gari da asuba suka sake tashi suka fara aiki don yau harda breakfast, za ayi.
Saida aka gama komai suka tuna ba ayi egg sauce ba, tuni hankali su ya tashi, gashi babu kwai balle a fara sarrafawa don ya kare, dole daya daga cikin zawaran tasa sabeeha tabi inda matarnnan ke zuwa dubasu ta sanar da ita, don ba hurumin su bane shiga cikin gidan dandai ya zama dole ne, hadiza batasan da haka ba donta zagaya bayan gidan.
Jiki a mace sabeeha ta bi hanyar da matar nan ke bi ta shiga cikin gidan, lokaci guda kanta ya rabu gida biyu ta rasa ina zatabi, corridors ne har kusan guda uku a wajen, har wani jiri jiri takeji wallahi tsabar gajiya, dauriya kawai take, inda ta soma jin hayani na dan tashi ta nufa a natse tana fatan taga matar, adaidai lokacin maya ta karyo kwana babu zato ba tsammani kawai sukayi gware gwab, smoothie din dake hannun maya ya fadi kasa bottle din ya fashi, rai a bace ta dago batayi wata wata ba kawai ta sauke mata mari a fuska, cikin saurin sabeeha ta dafe kuncinta tana mai dubanta “are you mad? Bakida ido ne? Wacece ke?”
Hamad dake tsaye don yanxu suka gama musayar yawu shida maya din ranshi ya baci batama san ya biyota ba yana jiyo muryarta ya karaso wajen, kallonta yayi sannan ya dubi sabeeha dake rike da kunshinta ta sunkui dakai,
Qaurin dataji sabeeha nayi ne ya tabbatar mata da yar aiki ce wannan yasa ta cewa “kina tafiya kamar wata dabba, bakida ido ne?”
“Maya!!!!” Hamad ya daka mata tsawa yace “how dare you call someone da dabba?”
“Na kirata din kaina kira? Karka shiga gonata, ka fita harkana”
“Well alamun sun nuna kece mai halin dabbobi,wadda batasan darajar mutane ba”
“Fuck off…” ta karashe tana galla mashi harara sannan ta bangaje sabeeha hartanayin baya kamar zata fadi ta kara gaba.
Kallon sabeeha yayi yace “i’m sorry for her behavior,”
Dagowa sabeehar tayi ta danyi murmushin takaici tace “bakomai”
Tunda ta dago hamad ya kalleta ya kasa dauke idanunshi a kanta, yanda yake kallonta haka take kallonshi garta tsargu tayi saurin duqawa zata kwashe glass din ya hanata nan ya tambayeta ina zata je? Kuma wa take nema.
Anan yasa ta tsaya ya kira indo mai aikin gidan gaba daya tazo sannan ya umarci ta kwashe gwalbar, sabeeha na fada mata abunda ya kawota ta futa.
Tunda hamad ya juya babu abunda yake sai tunani, she looks so familiar amma ya rasa a ina ya taba ganinta.
Sabeeha na komawa hadiza ta kalleta tace “daga ina kike?”
“Cewa akayi naje na fada masu babu kwai”
“Shine kika dade haka, uban me kika tsaya yi? Shishigi kome?”
“Banganta bane saida wani ya kirawota”
“Uban waye yace kije? Shin ba ance iyakacin mu nan ba?
Matar data aiketa ce tace “Haba hadiza, kwai kawai nace taje ta fada masu babu saboda ba ayi egg sauce ba”
Acahn parlor maya na shigowa daki laila na ganinta ta gane ranta ne ya baci, “ke kuma dawa?”
“Useless workers dinnan mana, mutane na tafiya kamar wasu blind monsters”
Tabe baki laila tayi don tasan halinta da masifa yanxu haka ka bibiya fault dinta ne.
Biki yayi biki fa, tun wajen karfe biyu aka fara hidima, an jera kujeru anyi decorating wani shashe daga compound, mutane an taru dagin ta ko’ina, amarya ta fito fess fess sai walwali take anyi budan kai anyi hotuna an watsa kudi sosai ba kadan ba sannan an rarraba sovereign na futar hankali, kawayen amarya harda zobunan gold aka basu Masha allah.
Maman ango tayi ma amarya kyautar gold, anne da nanna suka bata sarkar diamond mai kyan gaske, masha allah,lefen amarya ko da aka bude don ba a kaisu yola ba dozin biyar akayi mata, kaya dai hmm ba a cewa komai masha allah saidai ace allah ya sanya alkahiri ya kawo kazantar daki amarya dai yar gata ce yanda ango yake dan gata.
Yan matan amarya da kannen ango sunsha kyau, maya da laila anci makeup an masu kaya iri daya, samarin gidan ma su abal da hamad suma sunyi kyau harda sauran kannun kai wanga family gwanin ban sha’awa.
Bayan an gama abunci an fita dashi masu serving sun shirya, chan bangare su hadiza sun shiga bangaren da aka basu sunyi wanka sun dan huta hadiza data faki fuskar sauran ma’aikatan tayi wuf ta fice daga dakin, daman tanata neman yanda zatayi ta shiga cikin gidan ta samo wa kanta customers, don zata dunga bin manyan mutanen nan tana fada masu su sukayi girki idan suna buqata ta basu number ta, its her own method of startingher own business.
Tunda ta shigo babu abunda take sai famn girgiza kai, gida fa ya hadu ya gama haduwa, “anty duk suna waje”
Wata yar yarinya ta fada ma hadiza dake shirin bin wata hanyar daban kamar shes lost, washe baki tayi aranta tace ashe nima na saje da masu kudin nan.
Inda yarinyar ta nuna mata ta nufa sai gata kuwa a compund din gidan dake cike da mutane sosai, masu gidan kalangu da gidan kwarya anata yi son taya murna.
Daddaga kai hadiza ta soma yi ganin yanda akwta watsa kudi oo abundai sai Allah, masu kudi dai basajin zafin kudi ta fada aranta.
Kamar ance ta juyo karaf idanunta ya sauka kan anne, wani irin dammmm taji gabanta yayi, saurin mutsike idanunta tayi ta bude, ta karajin wani damm damm, juyawa da zatayi kuwa ta hango nanna da fadila a tsaye sunama amarya barin kudin, wani irin jiri ta somaji tayi saurin yin baya ta fita daga wajen, tafiya take amma batasan ina kafarta ke wullata ba har saida ta jiyo muryoyin wasu mutane na cewa , “kai wallahi amaryar nan yar gata ce, aure a gidan Alhaji santuraki ay kamar an tsomaka cikin daula ne.”
Bata tsaya sauraronsu ba ta shige cikin daki ta kullo kofa, allah yaso babu kowa ciki ta fara safa da marwa gaba daya ta gurkice ta zama kamar mai tabi ko wadda taga dodo, babu abunda take sai innalillahi wa inna ialihi rajiun, gaba daya komai na dawo wa kanta, kunci da zafi da rashin datayi duk ya gama dabaibayeta,komai ya dawo mata sabo kamar jiya akayi, the hatred that pain komai ma.
Wayarta ta soma kiciniyar nemowa tama manta cikin jakarta datake ajewa, saida ta burkice kayanta gaba daya ta samo wayar sannan ta fara dialing number jamila, kira daya biyu tana dauka ta soma magana “jamila na shiga uku..jamilaa……”
Yanda take magana yasa jamila gane cewa akwai matsala kenan.
“Kimin bayani menen? Meya faru?”
“Jamila gidansu na dauko kafata na kawo kaina..innalillahi jamila zuciyata na zafi,”
Doka salati talati tayi yanda hadiza zataji daga chan kuma bangarenta sai ta sauke wani murmushi kafin tace “toh se me? Malama ki kwantar da hankalinki, akwai wanda ya ganki ne cikinsu?”
“Ah ah babu inda muke zaune daban”
“Shine kiketa faman tada hankali? Yoh zama su iya tuna koke wacece? Zasu wani tuna da rayuwarki ne hadiza?”
“Ya zanyi jamila? Eh,in suka ganmu fa nida sabeeha karsu..”
“Kinga natsu, ki cigaba da harkarki ko sun gankin sai me? Zama ne akayi ba zaman dadi ba aanoda haka ba komai bace ke a wajensu haka zalika kema babu wnai abu tsakaninki dasu”
“Toh shiknan, amma kina ganin ba komai?”
“Eh ki kwantar da hankalinki”
“Toh.. zan kuraki anjima”
Tana kashe wayar ta wuce dakin da sabeeha ke ciki tana kwance ta raqube, kallo daya hadiza ta mata ta dauke kanta, ta futo zuwa daki tasamu guri ta zauna sai hawaye, “laifinka ne, laifinka ne”
Abunda take fada kenan.
Abuncin daren data kasa concentrating kenan dole ta futo akayi da ita idanunta nakan sabeeha, dataga tana faman riqe baya wannan yasa tace taje ta kwanta ta huta.
Dake kowa yaga yanda yarinyar ta wahala babu wanda yace takk.
Kwanan ranar hadiza ido a bude tayishi, ta kasa zaune ta kasa tsaye, babu abunda take sai hawaye data tuna baya, saiyanxu hankalinta ya fara zuwa ga yarta.
Washe gari da safe akayi breakfast aka gama, daman daga breakfast sai lunch da za ayi kawai don ranar za akai Amarya airport kowa zai watse.
Hadiza fa kasa sukuni tayi saida ta kira jamila, ta dan tausasa ta kafin ta kashe wayar.
Sunyi abuncin rana sun gama suna jirane kawai a sallamesu sannan akaisu chan gargajiya plug, kowa ta hada kayanta jiran driver kawai suke, har sun fito indo ta jagorancesu cikin gida, tunda hadiza taga sun shiga ciki gabanta yake fadiwa ta kasa dannewa tace “ina zamuje kuma na dauka mota zamu wuce kawai?”
“Hajiya zata sallameku tukunna”
“Ah ah madam ay za a bama koma menen mu wucewa zamuyi”
Wani irin harara sauran matan suka watsa mata tana neman yi masu baqin ciki indo dai batace masu komai ba.
Sabeeha na bayan uwarta kanta a kasa hadiza kamar karta bisu haka taji.
Basu tsaya ko’ina ba sai main parlor inda babban hoton marigayi santuraki ya mata iso tun daga nesa, cikin hanzari ta dauke fuskanta suna daga baya baya, indo ta masu nuni da waje suka zauna.
Kusan a tare anne da nanna suka sauko, zama sukayi kan kujera suka gaishesu kafin anne ta soma magana, “welcome gargajiya team, kunyi kokarin sosai”
“Thank you ma” duk suka fada a tare, maqudan kudi kusan bandir uku anne ta bawa indo ta basu su raba sannan tace wannan kyauta ce kawai ta basu kudin aikinsu kuma madam zatayi sorting dinsu don an biyata already.
Nanma godiya sukayi sosai kafin su miqe gaba daya su suka nufi hanyar futa, daidai nan anty fadila ta shugo, dake hadiza ce karshen futa wannan yasa sukayi clashing, saidai basu kalli junansu ba, “dakata” hadiza taji abun kamar saukar aradu, daukan wayanta daya fadi anty fadila tayi sannan tace “kin yadda wayarki, kodan yar karamace baki lura ba”
Dan dagowa hadiza tayi ta amsa har zata juya anty fadila tace “Hadiza!!!!! Wa nake gani kamar hadiza!!”
Chak hadiza ta tsaya, anty fadila ta juyo gabanta ta kalleta da kyau tace “la’ilaha ilalahu hadiza ashe rai kanga rai? İkon Allah anne nanna hadiza ce hadizan baba larai”
“Wace hadiza kenan?”
“Baba larai mai aikin mu tun muna maitama?”
Sai a lokacin nanna ta gane baki bude tace “hadiza!!! hadiza dai, ikon Allah”
Yaqe hadiza ta somayi kamar wata munafuka tace “laa fadila, kece haka? Iko sai allah, wani ikon allah tunda na shigo ban shede ku ba kwata kwata, hajiya”
Cikin sauri ta tunkari inda anne ke zaune, babu abunda take sai kallonta, lost in her thoughts gaba daya, “ina wuni hajiya, ya iyali”
“Lafiya lau nanna tayi saurin amsawa anne ma ta amsa, “ya baba larai da yaranki”
Shuru ta danyi chan kuma sai tace “allah yayima inna rasuwa watannin baya, cutar daji ta kamata”
“Allahu akbar..allahu akbar allah ya jiqanta da rahama yanxu larai ta rasu?” Anne ta fada tana mai duban Hadizar
Sabeeha data tsaya jiran babar tata, sauran matan duk sun shiga mota daya daga cikinsu tace kike ki kirata mana mu tafi yamma nayi”
Anatse sabeeha ta soma tafiya a daidai lokacin hamad shima na kokarin shiga cikin gidan yana ganinta ya ganeta sai kuka ya kauda kanshi kawai.
Ciki ya shiga tabi bayanshi ta dan taaya daga baki bakin kofar,
“Ina diyarki kuwa?”
Sallamar sabeeha data biyo bayan ta hamad ce tasa duk suka dago, hadiza taji kamar an lulubeta da bargon azaba…….
“
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
“
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID