← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 44

Sashe 7

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai gadi ya daga kai cikin tabbatarwa. Ya nisa kafin ya janyo wani liytafi a kusa dashi dake kan desk yace,

"Ya sunan ka?"

"Auwalu Hamidniyya Lebanon"

Mai gadin ya daga kai da sauri ya dubee shi,

"Bawan Allah...." Ya karasa fada yana nuni da bappah Auwallu da kasan biron sa.

Bappah Auwalu yayi murmushi yace

"Ka sheda ni yanzu"

"Sai da ka fadi sunan wallahi. Na tuna kana zuwa Kar mu tsaya ma wani lokacin muyita hira, kayi hakuri dan Allah wallahi baki daya ka canza mun ne"

Bappah Auwalu u ya sosa keyar sa yana murmushi yace

"Kasan rayuwar sai a hankali Kam"

"Hakane Kam wallahi ya'yana. Allah dai yasa mu dache yayi mana maganib abunda yake damun mu..

"Aameen Yaa Rabbi"

"To ka shigo ka zauna a waien zaman ko. Bari a kirawo su"

"To godia nake. "

Ya shiga cikin wani babban daki da kujeru aciki. Nanne inde baki sukazo suke zuwa, suke gaisawa da yan uwansu na ciki, Wasu Kuma suke daukar yaro wato adopting da foster parents keyi... Wasu kuma kawai suna zuwa su dan kakkawo tallafi ga marayun. Na daga abunda hali ya kama. Irin su kayan abinci, ko surutu. Ko raba maganin sauro da gidan net din..

Bapoa auwalu yana zaune yana matsa yatsun hannun sa sai ga shigowar Nawraah rike da hannun Amnah data fiye ta zama yar karama itama

Bakinsu dauke da sallama suka shiga. Mai gidan ya dubi agogon hannunsa ya saita lokaci acikin wani babban abu me buga kararrarwar lokacin magana ya kare.

"Nawraah, Amnah..." Bappa awualu ya kira sunayen su yana karasawa kusa da su ya riko hannun Amnah ya rungumeta yana hawaye,

"Amnah..."

"Naam.m bappah"

"Ina wuni bapoah?" Nawraah ta gayshe shi tana gyara tsayuwar ta

"Lafiya kalau. Nawraah Ashe Amnah ce bataji dadi ba har kika dene zuwa makarantar? Wallahi bansani har sai da nake tanbayar Layla ba dadewa nace su Ahmad kuwa sun fara zuwa jami'ar tache kwana biyu bakwa zauwa batasn ko sunje ba. Take cewa kina jinyar Amnah bakyaa lillahi Wa inna ilaihi rajiun "

Nawraah ta kakaro murmushi don ta kwanta masa da hankali tace,

"Ai dake ba wani ciwo bane bapoah"

Ya girgiza Kai yana daya duban Amnah,

"Haba Kalli ba. Kalli Amnah fa. Da haka take? Dubi yadda ta dawo fa. ? Nawraah nan gidan marayun ba waien zaman ku bane. Ku dawo gidah dan Allah kinji?"

Nawraah ta sake kakaro murmushi tana girgiza Kai tafe,

"Bappah auwalu nanma ya isa Allah. Akwai wajen kwana mai kyau, akwai bandaki , akwai wuta. Kuma ana bamu abinci daidai gwargrwado. Duk wadanda mike tare da su kowanne da irin tasa kaddarar jarabawar ta rayuwa... Rashin lafiyar Amnah Kuma abu ta dauka taci a shara. Amma kalau muke Allah Kuma Allah cikin ikonsa wani dalibi shine yayi mana fafituka wajen tsayawa aka Wa Amnah komai da komai bappaah. Dan Allah ka ragee damuwaa da kake akan mu, Kai nema naga ka fada bappah. Bakada lafiya ne?"

Bappah auwalu ya sauke zuciya. Daman yasan ba zata amice ta dawo ba don idan sun koma nusaiba sasu zatayi agaba

"To yanzu ya jikin nata? Amnah ba inda yake miki ciwo?" Ya karasa fada yana Kai hannunsa kan goshin Amnah da cikinta dake shafe kamar marar tueo. Duk ta jeme sai kashi

"Da sauki sosai ma. Jijjuya fa ta dingayi ta suke. Allah ne yayi da kwanata agaba"

"Amma Nawraah menene dalilin da zaki nemoni ba ko a waya ne?"

"Bappah Banda waya . Baka.haka ba gaba daya hakulan mu a tashe suke. Banason Kuma na daga maka naka hanalokin bapoah"

"Karki sake wannan gangancin kinji ko Nawraah? Zaku iya yanke hulda da nusaiba ita kadai. Amman banda su Laye. Itace Bare. Zan iya sauya mata yanzu Amma ku yayan ciki na ne abunda yayi junaidu shi yayi ni Nawraah. Kisa a ranki. Wannan abubuwan da zasu zam tarihi inshaa Allah. Sannan ki tsaya ku cigaba da karatu kinji?"

"Inshaa Allah bappah.."

"Ina ashfeef?"

"Yana garejin mota"

"Shine me waya ahannun sa ko?"

"Eh shinemmm, nima inada wadda hamma Ashir yabani Amma yace sai na shiga level two inshaa Allah"

"Mashaa Allah to duka abunda yake faruwa kafin na bullo ko Kuna bukatar wani abun Ashfeef ya dinga Kirana kinji?"

"Toh inshaa Allah bappah. Amma ba komai ba kakka damu

"Banason musu kice to kawai"

"Toh bappah." Tana rufe baki kararrarawar karashen zancen su ta buga

Bappah Auwalu, ya mike yana lalubo aljihunsa yan nera tamanin ya dakko yan ashirin guda hudu ya mika mata,

"Rike wannan kwa sayi wani abun"

"Bappah daka barshi ba abunda mukebukata Allah"

"Ki karba dai yaushe muka fara yar haka"

Hannu biyu ta Saka ta karba tana rissinaawa

"Angode bappahh Allah yakara arziki aamin

"Aameen aamin. Allah ya muku albarka. Ya tsare kuryciyar ku har girman ku kinji! Layla tache jami'ar taku gatanan ce. kudai kuje da tsarin da iyayen ku suka horeku akai. Ba ruwan ku da shiga harkar kowa.

"Inshaa Allah bappah"

"Yauwa Allah yayi albarka sai na sake bullowa"

Toh bappah"

Har bakin gate suka raka shi Yana daga musu hannu suna daga masan ko da ya juya sai daya goge hawaye wai yau iyalan junaidu ne agidan marayu basuda gata kwata kwata, Allah mubuwayi ne gagaraa misali...

====

Sannu ahankali haka rayuwar taci gaba da garawa. Yau da dadi gobe akasin haka, kwanaki nata shudewa, safiya ta koma rana, ranata ta koma yammaci , yammaci ya koma dare

Su Nawraah suka cigaba da zuwa jami'ar Alharamein university. A satin ma su ashfeef suka fara zuwa, Ahmad da Shareef accounting suke karanta, Layla da Nawraah kuma criminology.

Mai karatu alkalmi yayi kadan wajen rubuya muku yadda zazzafar shakuwa ta shiga tsakanin marwan da nawraah. Sunyi matukar saho da juna Wanda duk sanda ka Dora idanun ka akan su sai kaha tamkar mata da mini ne sahoda yadda suka dache da juna. Duk inta ta Saka jafa yana biye da ita.... Duk inda ka
_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY

[5/1, 6:47 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_BOOK TWO_

_✍️:MX_

_11_

*Zaune* ta ke, A babban parlorn da ke gidan na su... Ta daura kafar ta daya kan daya. Gabanta wani teburi ne cike da kayan motsa baki... Da sanyayyen robar ruwa da kwalin lemo na 'ya'yan itatuwa.

Idanunta saqale cikin gilashi ta sake duban number a karo na uku na cikin screen din dake wayar hannun ta. Sau uku tana kira not reachable a iya zaman da tayi na lokacin..

Dawowar su kuwa ko da yaushe sai ta kira duka numbers din nasu bata samu. Ta sauke katuwar ajiyar zuciyar mai cunkushe da damuwa.

Baki daya bata jin dadin kiran da take musu bata samu. Zuciyar ta nata kawo mata labarai marasa dadi..

Ta sake sauke wani gwauron numfashi tana runtse idanun ta hadi da furta,

"Inna Lil Laahi Wa Inna Ilaihi raji'un... Allah ya jikan ki Hindu, Allah ya gafarta miki. Allah ubangiji ya bamu iKon kula da iyalan da kika bari. Kai rayuwa, Mai rai ba a bakin komai yake ba. Allah kasa muyi kyakkyawan karshe Aameen"

Ta yunkura zata tashi sai ga shigowar mai gidanta parlorn bakin sa dauke da sallama...

Amsawa tayi ta nufe shi da sauri tana masa sannu da zuwa. Suka rungume juna. Ta harde hannuwanta a ruwan cikin sa. Kasancewar ya fita tsayi. Rumfa ya mata da faffadan kirjinsa. Ya Kai hancin sa kan dankwalin kanta daya dan zame ana hango gashinta batai kitso ba. Sai kamshin turaren man gashin Yerwa incense and more ne ke tashi. Sunba ya kaiwa gashin yana lunshe idanun sa. Ko'ina na jikinta kamshin yake yi.

"Sannu da zuwa Habibi...." Ya jiyo sanyayyar muryarta ta daki kofar kunnen sa.

Ya daga kanta yana duban idanunta hadi da saka hannu ya tallabo bakin ta da sauri ya kai mata sumba. Ta kallo baya da sauri tana murmushi. Shima murmushin yayi..

Ya riko hannun ta suka zauna akan kujera. Kallonta yake cike da zallar so da kauna tamkar zai mayar da ita cikin sa.

"Kinyi kyau Mariri na... "

Murmushi tayi tana rufe bakinta tache,

"Yau Kuma da wannan sunan ka tashi?"

Daria yayi yana cigaba da kallonta ya riko hannun ta cikin nasa yace,

"Ya za'ai na manta sunan da nake Kiran ki dashi muna saurayi da budurwa uhm? Shaukin so na dawainiya da ni. Idan kika kirani da As-sadeeq dinnan har cikin bargon 'kashi na nake jin ki Mariyatul Qibdiyya ta" ya karasa fada yana sinsinar gefen wuyan ta

Murmushi tayi tana duban sa hadi da damtse nasa hannun cikin nata tache,

"Kafi kyawu kyau... As-sadeeq dina daya tamkar da dubu. Yadda kake faran ta wa duban mutane ubangiji Allah ya cigaba da duban ka da idanun rahama ya nunka ma ka dukiyar Ka, Allah yakara maka hakuri da juriya, lafiya ingatacciya ya hobbasa dik wani samun ka ya yaye maka damuwar ka... Har gaban abadan kai ne mamallakin zuciya da gangar jiki Kai da ilahiran rai da jijiyoyi na gaba daya... Ni din taka ce kayi yadda kaga dama dan gata na.. abun alfahari na a koda yaushe" ta karasa fada tana sunkuyar da Kai kasa hadi da wulkita idanu kar wani ya gano su.
Chapter 7 · 0% Book details