← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 44

Sashe 30

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yajiyo karar horn din motar mahaifin nasu ya dawo. Ya daga Kai ya dubi lokaci cike da mamaki..

Ina baban na su yaje? Bai taba futa ya Kai wannan daren haka a waje ba. Idan ma fita ne Dr bintu mahaifiyar su tafi futa da daddaren ta dawo tsakiyar dare idan aiki ya kicimewa kananun likitoci tana zuwa musanman idan za.ai aikin haihuwa ko zaa curo wani abun aciki na surgery.

Jin motar mahaifin nasa an faka Kuma baa fito ba yasa ya dan daga kansa labulen dakinsa. Dake sashen yana kallon parking lot din gidan

Yana labe ta mudubi yana leko motar mahaifin nasa.. sai da Alhaji sambaso ya jima sosai acikn motar sannan ya futo daga ciki yana rike da wayar sa hannun dama yans magana yana dashare baki kamar gonar auduga.

Kallo daya marwaan yayi masa ya yi sauri ya zare kansa daga ciki labulen daya dage yana duban mahaifin nasu ta cikin window.

Dakin nasa yashiga Kai da kawowa ya tabbatarwa kansa wannan dariyar da baban nasa yake da alama wani babban lamarin ne ya gama nasarar sa.

Wayarsa ya janyo yana dubawa. Ya shiga kan sunan Anees. Ya danna wajen kira yana dafe da kansa...

Anees da alokacin ya na dakinsa a kwance bai bacci ba shima ya kammala sallolin daren sa kenan yana kwance kansa na kallon pop tunani dankare acikin kijrinsa.

Wayarsa ce fara Kara. Ya janyo ahankali yana duban sunan tamkar ba zai dauka ba. Sai Kuma ya dauka ya Saka a kunnen sa .

"Assalamu alaikum"
Marwaan ya fada a nasa bangaren yana sauke numfashi

"Waalykm Salam... Guy" Anees ya amsa shi

"Kana sauraro na?"

"Ina sauraron ka maza"

"Anees ... Bakina ya mun nauyi! Zuciyata ta na tafarfasa... gabban jikina na sassaramun Anees. Ina cikin damuwa"

Anees da shima acikin damuwar yake matuka, yayi kokarin saisaita kansa cikin sanyin murya Mai kwantar da hankalin Wanda yake cikin wani hali yace dashi,

"Kowani tsanani yana tare da sauki aboki na. Meya faru? " Anees ya ce dashi haka don bayasan ya dakko zancen da Nawraah tayi agaban sa..

Marwaan ya sake suake gwauron numfashi, bai ce komai ba..

"Ina sauraton ka marwaan" Anees ya ce da shi cike da damuwa

Marwaan ya dan samu kwarin gwiwar zayyanewa Anees dukkanin abunda ya sani gameda fefen bidiyon nan don shi kadai ne shedar sa a iya abunda ya sani, Yana fada yana Kuka sosai .

Anees ya shiga tausasar sa yana bashi hakuri, shima kukan ya barke da shi suka shiga bawa juna hakuri.

Sai da sukayi mai isar su sannan marwaan ya cigaba da magana ya karkare masa da,

"Anees!! Dan Allah maganar da zan fada yanzu kayi mata duba na tsakani, ka dena cutar kanka dan Allah. Kuma wannan shi kadai ne alfamar da nakeso dan Allah ka mun Anees kaji?"

Anees ya gyara zamanta yana duban screen din wayar tamkar marwaan din yake gani. Gabansa ya shiga dukan uku uku, yanata sako abubuwa kala kala.

"Kana saurarona?"

"Ina sauraron ka marwaan"

Marwaan din ya shiga sanarwa Anees dukkanin abunda yake so ya gayamai. Anees idanuwansa suka furfito waje saboda tsananin mamaki. Yakasa cewa komai. Marwaan din nata Kiran sunansa ta waya Anees ya kasa amsa masa. Marwaan ya katse jin ko network me.?

Bayan ya katse kiran. Ya samu kansa da shiga Whatsapp . Ya danno kan sunan Nawraah ya sauke bahagon numfashi, kafin ya fara mata voice note muryar sa nata rawa, luckily enough Kuma tana online...

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
_K'K'J_
_(M/W/S)_

_BOOK TWO_

_✍️:MX_

_37_

:::::::::

"Assalamu alaikum.... Nawraah...! Kiyi hakuri dan Allah dan girman Allah kada kice ba zaki saurari wadannan maganganun da zan fada miki ba, Dukkanin abunda zan fada wallahi Nawraah ba wasa ko renin hankali ko hada zance acikin sa. Magana ce ta tsakani da Allah abubuwanda suka faru na baya tun muna school yakamata ace kin sansu tun daa ba sai yanzu ba. Amman dubada yadda yake janye jikinsa kada nasani da kema kada kisan masaniyar komai yasa ban gaya miki ba..da fari bansan abun nasa ya Kai haka ba by Allah..amma with time lokaci na ta tafiya ina nazarce da shi Ina bibiye da abubuwa da yadda zaiyi abu yace ace bashi bane. Dukkanin komai dai yakamata ace kin sani Nawraah. Nokewar batada wata muhinmanci. Dubada hakan na sanya kiyayyar sa a zuciyar ki. Domin shi a nasa wajen wata irin kauna ce da yake miki.... Mai wuyar fassarawa, kauna ce yake miki Wanda hankali sai ya auna sosai zai dauka, kauna ce wadda yake miki min indilllahi daga Allah take Nawraah. Ina fatan dan Allah dan Allah ba iska nakewa voice notes ba kina saurara ? Saboda zan karasa miki komai... Nan gaba ma nasan abubuwa zasu bayyana kansu. Dubada cikin hadarin da nake ciki Nawraah... Shysa nake fitowa a mutum nake sanar dake wadannan abubuwan..."

Ya karasa tura mata voice note din yana jiran amsarta da amincewarta don cigaba daga inda ya tsaya.

Nawraah ta sakala earpiece tanata sauraron muryar marwaan tiryan tiryan har ya Kai karshe ta masa reply da ,

"Bangane kan maganganun nan da kake ba. Wanene shi? Meye alakata da shi? Dan Allah idan har ba wani abu bane daya danganceni wanda yakeda dole sai na sani kada ka sake turomin sako" ta tura masa reply

Marwaan ya dauka da sauri ya duba. Ya dan saki tattausan murmushin yake yana girgiza Kai. Ya samu kansa da jingina jikinsa a bango ya cigaba da ce mata,

"Shi ya fara ganin ki alokacin da kika shigo jami'ar mu ta Alharamein. Kallon da ya yi miki bai taba yiwa wata ya mace shi ba ni sheda ni Nawraah, abunda yasa nakeson sanar dake wadannan abubuwan saboda halin rayuwa Nawraah. Dubi matsatsin da muka samu kanmu aciki. Kuma na zama kamar third party a tsakanin ku da shi... Dan Allah ki cigaba da hakuri ki saurara..."

"Wai waye shi meye darangami na da shi? Dan Allah dan Allah ka goge number ta daga wayarka. Dan wallahi duk wani abu daya danganceka banda shi. Ka sani har abadah inshaa Allah kaddara ma ba zata sake hadamu hanya da Kai ba."

"Nawraah calm down please.... Please...nasani Allah yabaki hakuri, sanin hakan shysa nakeso na warware komai duk da shima na nasan irin dakon son da yake miki na..abunda zan cigaba da ce miki shine by Allah Nawraah cuz Anees bama shi da masaniyar zyna gaya miki wadannan abubuwan sannan bashida masaniyar nasan abunda yaketa kunbiya kunbiya dashi acikin zuciyarsa game da ke. nasan zakiga kaman duk duniya a school dinnan ke yafu tsana idnya kinzo waje ya tashi. Idan muna tare dake yazo yaganki sai ya fasa zuwa. Idan kin Mai magana na gaisuwa yaki amsawa da sauran su. Nawraah... Wallahi zan iya rantse maki da Allah Anees yafi ni kaunar ki, ba wai Ina fada bane don kawo wata manufa ta daban..Anees aboki na ne. Kani na ne Kuma babban amini na. Dik duniuya idan kika cire soyayyar annabi bayan shi, da iyayena ba sanda mukai shauwa sosai nake jinsa kaman jini na irin Anees. Na san shi ya sanni. Yasan abunda zanyi da Wanda ba zan yi ba. Haka zalika Nima nasan komai amsa...."

Nawraah na kwance sai ta zauna kunnenta dauke da earpiece din ta tana cigaba da sauraron maganganun marwaan datakeji tamkar ta zuba masa mari ta wayar.

Takaici duk yabu ya isheta na maganganun da yaketa zuba kamar rediyo. Sai karshen zancen sa dataji yace,

"Amma bakomai, komJ zai bayyana kansa. Kawai dama inason na cire yar tsamamr dake tsakanin kune. Wanda kike ganin kaman kiyayya ce yake miki....bari na gaya miki abubuwanda ya yiyyi yace kar na gaya miki ma kar na nuna shi yayi..saboda bayason yayi aikin alkhairi ya fada haka halinsa yake... Kuma na tabbatar idan an sanar miki hakan zai rage miki wani kaso na daga cikin tsanar da kika sanya shi a zuciyar ki...

Nawraah ta zare earpiece din daga kunnenta tana sauke numfashi,

Pause ta sanya a voice note daya turo. Ta runtse idanunta ta matse su... Sannan ta koma tajingina da pillow tana rage volume din earpiece dinma ganin yan dakin nasu duk sunyi bacci karta tashe su...

"Anees shine Wanda ya fara ganin ki Kuma ya kamu da son ki. Nalura da yanayin daya kalleki tun ranar. Bai taba yiwa wata ya mace haka ba..infact ki tanbaya baya kula mata ,baya bin takan mata. Karatu kawai yake abunsa ba ruwanda da kowa, look ko cikin maza course mates Anees bayada wannan huldar kule kule. Sai bada hannu su gaysa ya koma wajensa ya zauna...kullum zaki ganshi da airpods yana sauraron karatu ne ba ruwan sa da harkar abubuwa da yawa na matasa. Ba karya ba. Sister na da muke uwa daya uba daya lily taso Anees amman bai bata fuska ba, yace baya sonta a budrwa yana mata kallon baby sis din sa itama...karamin yaro ne me hankalin manya sosai...."

"Kaga... Dan Allah idan ba akan maganar data shafeni kakeson na sani, ba wannan maganganun nake bukata ba. Yauwa nagode" Nawraah ta rubutawa marwwaan ganin yanata bayani kanta ma baya dauka.

Sai a sannan ya samu kansan da yin murmushi ganin reply din da yayi gaba dayan ranar.
Chapter 30 · 0% Book details