← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 44

Sashe 38

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta sanya yatsanta daya tana duban labban nata da saukayi jazir saboda tsabar mugunta sunbar da Anees yayi mata. Don kuwa mugunta ce tunda ba niyya tayi ba. Daga temakon bada agajin gaggawa Kuma sai lamarin ya juye ya koma na tsotse totse da shafe shafe?

"Nashiga uku" ta fada tana dafe da kirjinta ganin idanuwanta na sake tariyo mata tundaga sanda ya hade ta da kirjinsa...

"Naw... Rahh" tajiyo shi yana Kiran sunanta.

Hamdala tayi a zuciyar ta jin numfashin nasa ya sesetu kenan tunda gashi ya kira sunanta. Gwara iyayensa su dawo su tarar dashi kalau.

"Naw.... Rah...Mai sunbar farfado wa... My CPR..."

Nawraah na jiyo shi ta girgiza Kai kawai. Wanke bakinta sosai tayi da mouthwash din tagani sabo awajen. Ta Kuma wanke fuskar ta, ta bude kofar ta futa daga bandakin tana Mai adduar futa daga bandaki .

Mayafi ta tashiga gyarawa... Idanuwan Anees na kanta musanman yadda ta yafa shi yanzun yayi mata kyau sosai. Sumbar gaban goshin ta ta furfito yayinda kyakkyawar surarta ta sake futa sosai musanman ta gaba.

Anees ya samu kansa da Jan kasan lebensa ya ciza yana sakar mata wani irin kallo da shi kansa baisan taya yake yin sa ba..

Ganin kallon da yake mata yayi yawa ne yasa ta dan karasa nesa dashi tana dubansa tache,

"Dan Allah ka mayar da abun bakin naka kaji?"

Yadda tayi maganar ne tamkar a shagwaba da ta sake narkar da Anees ya kasa nutsuwa ya riko hannun ta yache,

"Dan sake fada muji.... Yadda kikai magana kinji?"

Nawraah ta turo baki gaba tana yamutsa fuska tache,

"Kada su Mami su dawo please ..ka mayar"

"Sai Kin sake mun ... Ko na sake wani agaban su Mami"

"Ka sake mene?" Ta tambaye shi cike da fargaba

Anees yayi dariya Wanda har sai data bada sauti yache,

"Ki sake kissing na .... Deep and passionate"

"Gaskia ba zan iya ba"

"Okay then..... " Ya fada yana jefar da robar gefen sa

Nawraah ta dauka da sauri tana goge ta da tissue. Idanuwanta sun kawo ruwa tache,

"Dan Allah ka mayar"

"Kinyi alkawari?"

"Na me Kuma?" Ta tanbaye shi tana waywayawa kofa jin kaman zaa shigo

Anees yayi murmushi yana riko hannunta,

"Me kike tsoro ne wai? Matata ce ke fa. Ni mijinkine. Kuma karewarta Mami ce ma tace mun ke matata ce...."

"Kunya mana kaji"

Yadda take magana da bakinta da labbanta masu kamshin vanilla ga muryarta mai matukar dadi tana ratsa masa magudanar jiki da kewaye yache,

"Ina kaunar Ki sosai, zai iya kasancewa, niba ajin ki bane, ba irin namijin da kike so bane, amma inaso ki saka a zuciyar ki cewa nayi alkawarin zama irin namijin da kike mafarkin samu a rayuwar ki, nasan ke din KWANKWASON JIMINA ce MAI WUYAR SHAFAWA... nidai dama nake bukata.... I love you beyond your wildest expectations.."

"Tohm naji mayar kaji ?"

Anees ya girgiza Kai.... Aka sake kwankwasa kofar, Nawraah ta dube shi da sauri tana hada hannuwa alamun roko.

"Sai kin amince...."

"Wai dama haka kake?" Ta fada fuskarta na turbunewa zatai kuka. Saboda ta dauka kunya ce dashi da ko hannu aka saka masa a baki ba zai gatsa ba...

Hannunsa ya Saka ya nuna gefen kumatunsa. Ba yadda Nawraah ta iya. Ta sunkuyar da kanta tana runtse idanu ta sakar masa sumba agefen kumatunsa.

Daidai lokacin da aka sake kwankwasawa . Anees ya dauki robar da sauri ya mayar bakinsa yana daria.

Yayinda Nawraah ta ja kujera can gefe tana cewa,

"Yes! Come in"

Hajia Qibdiyya dake wajen kofa ita da Dr abubuakhar dollars ta dube shi tana murmushi ahankali tache,

"Shysa nace maka mu dan tsagaita awajen sayo abicninnan. Mu dan basu lokaci ko kallonta ne yayi yaji dama. "

Alhaji dollars yayi murmushin shima yana girgiza Kai yace,

"Yaran yanzu kenan. Ubangiji Allah yasa an daura a saa Allah yasa abokan zaman juna ne har gaban abadan"

"Aameen As-sadeeq dina, daya tamkar dadunu"

Murmushi yayi ya saka hannu ya lakuce mata kumatu...

Suka murda kofar dakin suka shiga bakunansu dauke da sallama....

HANSATUWA💜

_K'K'J_
_(M/W/S)_

_BOOK TWO_

_✍️:MX_

_46_

:::::::::

Nawraah ta amsa musu tana kakaro murmushi. Ta mike ta dan sunkuya ta karbi ledar hannun hajia Qibdiyya.

"Sannun ku da dawowa"

"Yauwa Nawraah habibty. Komai dai kalau ko?"

"Eh" Nawraah ta amsa ta

"Sannu Nawraah"

"Yauwa Abba"

Suka nufi gadon da Anees yake akai. Ya karkatar da Kai yana duban su. Ya lumshe idanunsa ya bude yana murmushi

Hajia Qibdiyya da Dr dollars suka nufi kansa suna masa magana. Hajja qibdiyya na shafa kansa. Yayinda Dr dollars ya ke gyarawa Anees din wandok jikinsa daya tattare wajen kafafuwa...

"Kici abinci Nawraah karya huce"

'tohm Mami"

Nawraah taja kujera ta koma gefe can ta bude abincin tana ci. Da farko kamar ta amayo da shi haka takeji. Don wani irin taste ne taji abincin ba irin Wanda ta saba ci ba.

Sai datayi loma ta uku ta fara jin dadin abincin. Ta tuno Amnah da suna tare da tuni da ita zasu cu. Ko hamma ashfeef.

"Wai yau itace a kasar turkiye.... Yayinda ashfeef ke wata kasar shima.? Sun samu kwanciyar hankali da nutsuwa. Abunda Saka rasa shine jigob rayuwar su Wanda har abada duniya ba zata taba musu dadi ba sai dai su bibiyeta a haka... Wato iyayen su... Malama Hindu da Mallam Junaidu. Da Kuma babban wansu Hamma ashfeef..

"Allah ya muku rahama.. ya sa Kuna aljannatul firdaws aameen"

Ta fada ahankali tana goge hawayen daya zubo daga idanun ta ..

Knocking kofar akayi. Nawraah ta mike ta bude kofar. Likitocin ne suka shigo su uku dauke da wani babban silver tray haka da wasu magunguna da allurori akai..

"Sannun ku Dr"

"Yauwa babanmu.. ya jikin nasa da sauki?"

"Da sauki Alhamdulillah har mun fita mun sayo abinci, mun barshi da matarshi tace komai kalau"

"Yayi kyau" likitan ya fada . Dake cikin harshen turanci suke magana.

Wajen Anees suka nufa. Suka dagoshi. Suka sanya wani karfe ta bayansa. Robar bakinsa suka zare sika wullar a shara..

Wani ruwa suka dauka a roba, aka zuba magani cikinsa suka sashi ya kurkura bakinsa da shi..

Sannan sukayi masa allurori aka sanya wani ajikinn wani ruwan yana shiga jikinsa...

Sai magani da suka bashi ya hadiya kala biyu. Sannan sika sake dubawa dinkin nasa komai kalau.

"Yauwa Alhamdulillah... Sai magana ko Anees?" Likitan daya ya fada yana murmushi

Anees ya kada kansa alamar eh. Kansa akan Nawraah yace,

"Naji sauki ai Dr"

"Kana dai kan saukin Anees" Mami ta fada

"Akwai cigaba sosai mashaa Allah. Don haka daga gobe inshaa Allah zai fara cin abinci. Sannan Kuma kada Kumanta mutum daya ne zai zauna dashi. Kafin jikin yakara sauki"

"Toh Dr inshaa Allah. Yadda kache hakan za'ai"

Futa likotocin sukayi daga dakin. Dai dai sanda Nawraah ta karasa cinye abincin nata Tasha ruwa tana hamdalah.

Dr dollars ya dubi agogon dake wutsiyar hannunsa yache,

"Kuje ko kar dare yaja sosai."

"Ah zaka zauna abban su? Da har zan zauna ma tunda Kai ma ba dadi kake jiba"

"No karki damu na wartsake ai. Kuje din Allah ya tashe mu lafiya"

"Auta sai da safe?" Hajia Qibdiyya ta ce da Anees. Tamkar ya fasa kuka haka yaji...

Shi yafuso abar masa Nawraah..

"Ya akai ne auta?" Hajia Qibdiyya ta sake tanbayar shi

Ya sanya hannu a bayan keyarsa yana sosawa yace,

"Na dauka dika... Zaku zauna"

Hajia Qibdiyya tayi murmushi tana girgiza Kai tache,

"A'ah... Sai ka warware duka inshaa Allah. "

Nawraah tayi hanzarin zuwa kofa tasa hannunta akan handle din Anees ya kirata yana wani hade rai,

"Zo nan..."

Nawraah ta juya bayan ta, ta dauka da wata yake. Sai Kuma ta tuna su kadai ne a dakin ta dube shi tana nuna kanta

Ya kada Kai. Alamar eh da ita yake

"Zo kwi sallama Nawraah" cewar hajia Qibdiyya

Nawraah da gaba daya gwiyoyin jikinta sunyi sanyi don ta kara tsorata da lamarin na Anees don da kunya tayi gabas yamma yayi..Ashe..

"Sai da safe" ta fada kanta a kasa

"Gyara dankwalin ki da mayafin...haka" ya karasa fada yana jan dankwalinta ya rufe sumar gashinta data futo

Daman tundazu yake aika mata harara da drs din suka shigo ashe ashe abunda yake Kona masa rai kenan. Yaja mayafin nata ya rufe gaban kirjinta sosai zuwa bayanta...ita bata masan gashin nata ya fito ba. Kuma ya fun mayafin ya sauya .

Nawraah ji take tamkar kasa ta tsage ta fada. Agaban surikai wannan abun kunya.

"Yauwa to muje .. to auta ai da safe"

"Tohm Mami" ya fada yana gyara yadda yake a zaune

Dr dollars yaja kujera gabansa ya zauna yana dubansa

"Sannu kaji"

"Tohm Abba"

Hajia Qibdiyya da Nawraah suka fita zuwa harabar asibitin motoci gasunan jere harda na haya.

Suka kira direba daya ya dauke su. Hotel dinsu ya Kai su. Nawraah Allah Allah take su karasa. Hajia Qibdiyya ta nuna mata dakin da zata zauna

Nawraah ta mata sai da safe ta shige cikin dakin kunya duk ta cinyeta. Tabbas Anees ko kadan bashi da kunyaa

Sam ta kasa hada idanu dasu Mami tun farkon sunbar da ya mata a hannu ya zuwa yanzu daya saka hannuwansa ya gyara mata dankwali da mayafi..

Lalle kishine dashi babba ma kuwa...Tun ba'aje ko'ina ba?

Haka dai tayi alwala tayi wanka tayi sallar nafila tabi lafiyar gado ta kwanta ba jimawa kuwa bacci ya dauketa mai nauyi saboda matukar gajiyar da tayi....

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
Chapter 38 · 0% Book details