← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 44

Sashe 32

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don haka murmushin wani abun ne na daban kenan? Ko visa dinsu ta fito? Ko wasu abubuwan ne na kadara ya sake mallaka? Saboda duk da dare ne amma dubada manyan futulin wutan da suke wajen sun haska ko Ina tamkar rana kana iya hango fuskar sa tar yana ta murmushi yana dariya. Zaka gane yana cikin madaukakin farin ciki marar misaltuwa.. Kawai dai baa jin me yake cewa saboda akwai tazara sosai a tsakani.

Don haka ta koma ta zauna a bakin gado tana jiran shigar sa. Ya jima kafin ya kare wayar ya shiga cikin gidan . Kai tsaye ya nufi dakinsa ya watsa ruwa ya kwanta..

Shiru shiru Dr bintu bataji ya shigo ba. Ta leka taga ya gama wayar

"News ko ball yanzu haka ya tsaya kalla Alhaji da daren nan" ta girgiza Kai ta sauka kasan tana rausaya..

Shiru taji ba alamar karar kayan kallo ..ta shiga babban parlorn da yake a matsayin nasa nanma ba karar tv.

Bandakunan palukan ta kwankwasaa duk baya ciki.

"Ko wani abun zai dauka a dakinsa?" Ta fada ahankali tanayin hanyar dakin nasa.

Ganin abubuwan takardu kawai da sauran documents muhimmai yake a dakin nasa. Baya kwana a dakin a nata suke kwana..
.

Ta kwankwasa kofar dakin tamurda handle din ta jiyotaa datse.

"Alhaji" ta kwankwasa kofar tana kiran sunansa

Shiru bai amsa ba. Yana kwance akan gadonsa yana danna wayar sa.

Ta sake kwankwasawa da karfi tana cigaba da Kiran sunan nasa. Mikewa yayi daga kwanciyar da yake harda sakin siririn tsaki ya saka hannunsa akan mukullin ya bude..

Baki a wangame ta dube shi. Har yayi wanka ya Saka kayan bacci. Ga Kuma wayar sa ta datake ta faman Kiran nasa rike a hannun sa yana dannawa,

"Ya akai?" Ya ce da ita yana kauda Kai

"Ya akai? Ya akai ka fa kace mun yusuf" Dr bintu ta tanbaye shi cike da mamaki dauke a fuskar ta.

"Idan ba komai zan rufe kofa"

Bankada kofar tayi ta shiga cikin dakin tana daddaga fullallaka da bude drawer ko zataga wani abun na daban ko takardu da sauran su.

"Yusuf lafiyar ka kuwa yau? Kasan me kake cewa? Anya daren nan ba zazzabin ne ya tashi ba? Tun dazu daka fita kace kana zuwa zaka dawo baka dawo ba sai yanzu ba dadewa shine ka shigo dakin ka kayi kwanciyar ka kabar ni can hotiho, inata sake saken abubuwa na dauka ma ba lafiya ba, wani abun ya faru dakai don baka taba haka ba..

Alhaji sambaso ya yamutsa fuska yana zura wayarsa agaban aljihun rigar kayan baccin dake jikinsa yace,

"Bintu ba nasan hayaniya kingane? So bacci nake ji ki fita zan rufe kofa"

"Bazan fita ba. Yau ni kake cewa haka yusuf? Ba inda zani. Sai ka gaya mun inda kaje da wa kuka hadu. Me kake shiryawa. Sannan dawa ka tsaya kana waya ajikin motar ka bayan ka dawo. ? Sannan meya hanaka tahowa dakin mu kamar ko da yaushe zaka zo nan dakin da anfi shekara nawa ba a kwana acikin sa. Har kana cewa in fita maka zaka rufe kofa yusuf ni kake gayawawa haka?"

"Ba zaki fita ba?"

"Bazan fita ba"

"Okay zauna ni bari na bar miki dakin" ya futa daga ciki ya barta a tsaye

Cike da mamaki tabu bayan sa da kallo. Har ya koma dayan parlorn akan kujera ya kuna ac ya kwanta yana juya mata baya

"Yusuf, Idan wasa kake mun dan Allah dan Allah ka dena bakaji zuciyata ba. Gaskia banason irin wannan wasan banaso Allah . Wasa da halayyar da bata ka ba ba saboda Allah. Ni kawai ka fito ka gaya mun menene farin cikin nima na samu nutsuwa amma wannan wasan naka ya yi yawa haka. Dan Allah kaga dare ne Dan Allah. Dama inason nace maka ma nusaiba matar bappan su Nawraah dinnan tace mijin ya amince zasu bar naduka. Ta turomin sako ta text message. Kaga yakamata zuwa da safe ko cikin daren nannma ka gama yanke abubuwan da za'a basu idan ma ta bank ne ai ta bude banki sai a tura mata su tattara su tafi. Inata kira baka dauka a awaya. Na tutturo maka messages nanma ba reply sannan na maka mail ma shima shiru bakace komai ba. Na shiga dimuwa sosai Alhaji. Dan Allah bar wasan nan haka bakaji zuciyata yadda take duka ba wallahi. Kaji? Kaji yusuf dina..?" Ta karasa fada tana kokarin zama a bayansa ta saka hannu tana riko kafadar sa.

Alhaji sambaso ya kafa ya shureta. Sai ga Dr bintu a a kasan kujera dabas a carpet tayi zaman dabaro saboda shurewar buguwar da yayi mata.

"Alhaji wasan har dana shudewa yau?"

Wata wulakantacciyar harara ya bita da ita yana yamutsa fuska. Ya daga yatsa daya ya mata nuni da shi,

"Na gaya miki banason takura, bacci zanyi, zaki wanii zauna a bayana kina kokarin riko kafada ta. Akan wani dalilin? Tashi ki bani waje"

Mamaki ne ya cikata ganin yadda yake magana furucin da lafuzan da suke fita daga labban bakinsa sam ba yadda ya saba magana bane. Bai ma taba mata irin wannan magangunnan ba haka. Tabbas ba wasa a fuskar sa domin a daure take gamau.

"Alhaji"

"Dan Allah dan Allah meye? Kinada takura wallahi "

"an Allah idan akan kiraye Kirsten dana maka ne nonstop da turo Sako kayo hakuri. Ba snaj abun bane kauna ce tasa Wani damuwa... Daman so nake naji ko lafiya ne? Na Kuma sheda maka da sakon amincewar su Nusaiba barin naduka baki daya harda su Nawraah"

"To meye hadina da su? Na fasa bayarwa su zauna kar su tashi."

"No Alhaji nasan ba wani hadinmu dasu, Amma kasan ai dasu Nawraah zasu tafi baki daya. Kuma kai kace a bata offer dinnan da mai gidan yaki karba kwata kwata baka nata tunanin abunda zaka bashi ba ma ya amince? to gashi dai ya amince tace zasu tafi. Kadarar ko kudin dakace zaa basu. Nake tuni nace ko yanzu da daddaren amata transfer ko zuwa da safe ko ya kagani?"

Wani irin dogon tsaki yaja da har sa Dr bintu ta daga Kai tana duban window ta dauka siren ne na yan sanda ko motar kwana kwana .

Sake sakin wani yayi yana nuna mata kofa, cike da fada yace

"Wake miki wasa? Tashi ki fita. Bakida aiki sai maganar kudi kudi kudi kudi kudi dai. To wallahi ki bude kunnuwan ki ji kwandala bazan sake baki ba. Karki bari na sake maimaita miki"

Baki bude Dr bintu take dubansa tace,

"Yusuf... Yusuf Kai ne haka? Yusuf yau ni kake gayawa wadannan maganganun? Kasan me kake cewa kuwa?"

"Kwandala bazan bayar ba. Su zauna ko su tafi su ta shafa ba abunda ya dame ni. Tashi ki bani waje. Tashi!"ya karasa fada a tsawance, ya jawo kafadarta ya futar da ita wajen kofa ya rufe kofar da mukulli...

Mamaki ya gauraye ta. Da baya baya ta jingina da kujerar dayan parlorn ta yi zaman yan bori..hawaye suka shiga wanke mata fuska..

Baki daya ta kasa cewa komai..sai datayi kukanta mai isar ta sosai sannan ta koma sama ta dau wayar ta ta kira kawarta hajia kubra ta gaya mata dukkanin abubuwan da suka faru.

Batayi bacci ba har aka kira sallar fajr tayi sallah har wayewar gari. Sai kuka kawai da take tayi duniya ta mata zafi baki daya...

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

_K'K'J_
_(M/W/S)_

_BOOK TWO_

_✍️:MX_

_39_

:::::::::

  *Bayan wayewar gari* mikewa Dr bintu tayi ta shige bandaki tana duban fuskar ta a mudubin dake bandakin..

Baki daya duk ta zama wata iri lokaci daya ta futa hayyacin ta...idanuwanta sunyi luhu luhu saboda kukan data kwana tanayi...

Wanke fuskar ta tayi. Tayi brush ta futa daga cikin bandakin . Wayarta ce keta faman karar kida.

"N"
Shine sunan dake rubuce a matsayin wanda yakira din.

Katse wayar tayi tana sauke numfashi. Nan aka sake kira har su biyar. Ana shidan ta dauka tana sakin tsaki ta kara a kunnenta

"Ya akai?"

"Hajia Nusaiba ce fa ko lambata ce ta goge a wayar ki?"

"No nasan ke ce. "

"Daman mun shirya ne tun dazu. Ga su Nawraah ma duka a tare damu. Ku muke sauraro."

Dr bintu da gaba daya ahautsine take. Itama kanta balain dake gabanta yayi yawa, tace da ita,

"Nusaiba kawai kuyi hakuri ba abunda zan iya cewa akai."

"Bangane ba hajia. Bangane ba" nusaiba ta fada cike mamaki

"Àbun nufi shine tafiyar nan an soke ta.. Nagode" tana gama fada ta danna mata block

Kasa ta sauka gabanta na tsananta bugawaa..sai kwaraara addua take tana Allah yasa Alhaji maganganun da ya fada wasa yake ba waai na gaske ba.

Ta karasa fada tana sauka kasan. Ba kowaa yaran nata basa nan don haka tace kila bacci sukeyi basu tashi ba.

Parlorn jiya ta kwankwasa, ta dan sakaya hannunta ta murda handle tashiga ciki.

Yana zaune ya sauya kayann sa zuwa wasu fafare. Bai Saka hula ba..

Daga Kai yayi ya dubeta alokacin data yi sallama..ya amsa a hade yana kauda Kai,

"Alhaji" ta fada tana kokarin zama akusa dashi yayi saurin matsawa yana mata wani irin kallo.yana janye plate din gabansa

"Har an maka serving abinci kana ci Alhaji?"
Chapter 32 · 0% Book details