← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 44

Sashe 25

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ai kinsan shi rashin hakuri ne dashi. Kuma akan kudi sam kamar kuda yake bashida zuciya. Ga zalama . Jiya sai kashe wayata nayi ya dinga kirana Whatsapp call da nomal call da video call duk naki kula shi. Ga uban messages ta media appz da yake turomun. Sai daga baya can dana kunna na masa message nace ya turo account number na Saka masa. Kinsan Kuma meyace?"

"Kai ai na sani,Sam shi wallahi bashida hakuri"

"Rabu dashi dai. Banda signing ma wace wahalar yayi? Ni kuwa da kudina da gumi na na samu kadarorin nan suka dawo mallakata. Har yanzu ma ownership papers (takardun shedar mallaka) basu gama zama ready ba saboda cike ciken kwangiloli sunyi yawa so kaman layi ne akayi saboda supreme court ne tunda kinga manyan plots ne da sauran su. "

"Kai Alhaji ateeks gaskia yanada matsala wallahi..su yanzu shi din bayan kudin da aka bashi harda mallakin kadara yake so Kuma?"

"To gashi kuwa? Ai haka yake shi. Idonsa Koda yaushe akan kayan ka. Idanuwan sa rufe suke akan kudi"

"To Allah ya kyauta. Ka jefe shi da wani filin ko gona kawai"

"Ai daman.abunda zanyi kenan, gonar nan dake kauye ta wajen Hannafi , zan bashi idan be yadda ba matsalar sa ce wannan"

"Ato yanzu naji batu. "

"Ina yaran suke ne?"

"Lily na sama. Marwaan Kuma bansani ba kasan fushi yake har yanzu "

Alhaji sambaso yaja dogon tsaki yana karkada kafar sa yace,

"Shidin banza, Haka zai hakura ya daina kuwa..."

"Ni bama wannan ba. Kasan na sake Kiran matar bappan na Nawraah tache mun Wai mijin nata yaki amincewa data fara maganar ma zai tashi. Sannan Wanda na Saka suna duba mun way abouts din marwaan ance baije makarantar ba tun da ya fita kwanaki dayaje wajenta suka hadu. "

"Rabu dashi dan uban sa. Ai jira nake komai ya tabbata mu tattara mu tafi har shi dan ubansa. "

"Gaskia dan wannan abun kunya har ina? Ace dan ka yana neman auren yar matsiyata? Ya case din hit and run dinnan kuwa? dama kwanaki headquarter sun kiraka suna cewa an fara bincike akan bonets din motar ka."

"Kai ni na manta ban gaya miki ba ashe. Ai rashin kudi Alhaji takaici ne. Gaba daya controller sai ya kirani , yake cewa Ka kawo ko dubu ashirin ashirin ce abawa yaran nan, shikenan a bar zancen sai su cewa dayan bangaren that's gidan dollars kenan ana nan ana bincike har yanzu."

"Shi din ogan na su?"

"Eh shi controller ma command din gaba daya, Dama tashi kinsan nawa na tura musu?"

"A'ah Alhaji"

"Dubu hamsin hamsin, nace ka basu shi Kuma na Kara masa dari biyu. Ya kirani yacemun paper da aka rubuta report dinma sun konata. Nace madallah aikinsu yayi kyau"

"A hayye kudi masu gidah rana"

'bari kawai. Aiki game kare ka. Sannan Ina nan Ina tunani akan yadda zanbi shi mijin ita matar da kike fada aji matsalar sa abashi ko meyake so, su tattara su tafi. Ba shikenan ba?"

'Shikenan kuwa Alhaji. Ka gama magana"

"Ai sai dai idan ban zauna ba. Kudi ne fa yake komai yanzu. "

"Tabbas. Allah yabar mu cikin sa kuwa"

"Aamin dai."

"A kawo abinci?"

"Munci agidan Dr. Amma me akayi?"

"Stir fry rice ne. "

"Akwai ragowar cake dinnan me madara?"

"Tres leches?"

"Eh"

"Akwai"

"To akawo mun sai shayi. Shikenan "

"Tohm"

Shigaa tayi kitchen tana dokawa mai aikin su kira. Mai aikin tanata bacci sai dataje ta kwada mata dundu sannan ta tashi a firgice suka nufi kitchen din tace ta dora mata ruwan shayin Alhaji.

A tsaje a jikin kitchen cabinet ta jingina nan da nan ta hankadawa kawar tata kudin da receipt tana nanata mata da,

"Dan Allah kawata ki temaka a sake rike shi ya saki bakin bakin aljihunsa.. Duk da yanzu ma bakiga ba ca yai na tura ko nawa nakeso kinsan bayason fushi na. Zan kiraki da safe. Nagode "

Tana tura mata da sakon ta kashe data dinta gaba daya. Ta jera komai a tray ta Kai masa.

"Hajia an gama?"
Ai aikin ta tanbayeta tana sakin hamma

"Eh jeki"

Ta datse kofar kitchen din ta koma wajen mai gidan nata. Nan Suka shiga ci suna hirar su har dare yaja sosai tukun suka nufi makwancin su..

*DR. ABUBAKHAR DOLLARS DWELLING*

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

_K'K'J_
_(M/W/S)_

_BOOK TWO_

_✍️:MX_

_30_

:::::::::

Bangaren sa ya wuce kai tsaye. Ya shige bandaki bakinsa dauke da addua..wanka yayi hadi da tsarki. Ya sauya kayan sa zuwa na bacci. Ya bi lungu da sako na jikinsa ya saka turaruka masu matukar dadi da sanyaya rai.

Wayoyin sa ya dauka da MacBook dinsa ya nufi bangaren mai dakin na sa. Bakinsa dauke da sallama ya shiga

Kamshin turaren wutar yanzu ba iri daya bane da kamshin wanda su kazo dazu sukaji. Lumshe idanu yayi ya bude. Kullu yaumin da irin kamshin turarukan da gidan nasu yakeyi.

Kwarai matuka mai dakinsa hajia Qibdiyya akwai tsafta da gyara. Dukkanin abubuwan da namiji zai samu daga mai dakinsa ta gari hakika hajia Qibdiyya ta wuce ta zarce ma.

Ya matsa inda kaskon wutan keci. Daya a local kasko na karfe daga can gefe. Dayan kuma electric burner ce ke konashi. Wani irin calming and soothing scent.

Ya matsa wajen electric burner din yana karanta sunan turaren daya gani ajikin kwalin turaren dake gefe. 'omani khajingru... By yerwa incense and more.

Ya sinsinar cikin kwalbar yana runtse idanun sa. Saboda kamshin daya gauraye shi. Mai matukar kwantar da zuciya da sakata cikin nutsuwa.

Ya karasa wajen dayan kaskon yana duba jikin kwalbar.."sandal twist".

"Nice" ya fada hankali yana ajiye kwalbar a gefe.

Dai dai lokacin da mai dakinsa hajia Qibdiyya ta sakko daga sama ta karasa parlorn kasan su.

Sanye take cikin wata riga ta bacci doguwa pink color. Ta dora wata rigar akai domin ta cikin me hannun vest ce ta saman kuma dogon hannu ne da ita

Karasawa yayi wajenta da sauri yana riko hannunta. Ya samu kansa da kai mata runguma yana shakar kamshin khumrahs din dake tashi daga jikinta. Ya dauki hannunta yana sinsinar sa shima. Wani kamshin oud kullaccam ne ke tashi daga jikin hannun ga kamshin khumrahs din data shafa.

Ya kai hancinsa kan gashinta dake tashin kamshin scented hair cream na man shafawa a gashi na kamfanin turaren yerwa incense and more man kitso me kamshi da hair spray me kamshi shima.

Baki daya kai baya wari ko tsami dinnan na lokacin zafi da saka masa ruwa na tsarki da sauran su. Duk hajia Qibdiyya ta shafa ta kuma fesa na fesawa.

Ya samu kansa da Kai hancinsa kan kafadar ta yana sinsinar kafadar kan rigar ta dake tashin kamshin tiraren wuta na kaya data turara na kamfanin tiraren yerwa incense and more.

"Mariya....Tahhhhhhh" ya karasa fadan sunan yana jan taahh din cikin wata siga

"Naam baban su, sannu da zuwa"

Murmushi yayi ya kamo hannunta suka zauna akan kujera yan duban ta sosai yace,

"Allah ya miki albarka . Hakika banda bakin godia agare ki Mariya. Nayi saa nayi dace da samun mata tagari uwar ya'yana ..har gaban abadan bazan daina yiwa Allah godia ba bi saga wannan babbar kyauta da yayi mun na auren mace saliha, Mumina, Mai ibadah, Mai tausayi, Mai tarbiyya, Mai Kamala, Mai kyau, wadda ta iya girki da daukar wanka Kuma ma'abociyar turare. Mariya komai kin hada a mace. Gaskia na yi babbar sa'ar samun ki uwar 'ya'yana"

Murmushi ta saki tattausa tana girgiza kanta hadi da kamo hannunsa tana matsawa da duban cikin idanunsa ta dan langabar da Kai tana turo baki gaba cikin kissa da shagwaba tamkar wata yarinya tache,
Chapter 25 · 0% Book details