← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 44

Sashe 18

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr bintu ta danyi shiru. Can ta tuno ai nusaiba ba kaunar su nawraan take ba don haka tace,

"Magana ce ba wani boye boye. Kema ai kinada ya mace Kuma kinason tayi aure inda zata huta kema ki huta ko kuwa?"

"Kwarai dagaske hajia. Itace Layla yata diya kwaya daya mace. Ita ce kanwar Ahmad da kika basu gurbin karatu kyauta a jami'a"

"Mashaa Allahu..Allah ya raya mana su to. To azahirun gaskia. Dan waje nane. Da na kenan wallahi bamma sani ba. Sai zuwa yayi ya same mu wai yanason aje anema masa auren wata yarinya. Na karkare miki zance dai baban sa yake tanbayar sa wacece? Mulki ne da su ko sarauta yar wace zuriyar ce? Kinsan meyace?"

Nusaiba ta saka hannu a kirji ta dafe..yayinda idanuwanta suka furfito waje tache,

"Nawraah?"

Dr bintu ta kada mata Kai cikin tabbatarwa tache,

"Nawraah wai yake so da aure. Tsakani da Allah Ina shi Ina Nawraah?"

Nusaiba ta gyara zama idanunta sun kada sunyi jazir saboda bakin ciki tache,

"Ina bazeyiwu ba. Wai yanzu de yaron wajen ki zai auri wata Nawraah? Banda sharrin farar fuska na bilicin kwailin fa take, baka ce wuluk kamar bayan tukunya, sai shegen yauki da iya feleke na Nawraah ai ba kyakkyawa bace..Banza abanza ma irin ta" ta karasa fada tana sharce gumin daya tsattsago na bakin cikin zantukan ta.

"Kema dai kya fada. Ruwa ai ba saan kwando bane. Ko cikin kawayen mu dukkanin su yaran su yayan manya suke aure masu usuli da kudi ko sarauta ko yan kasuwa manyan attajirai da ake ji dasu a fadin kasar nan. "

"To yanzu hajia batun karatun nasu fa da sukeyi?"

Dr bintu ta girgiza Kai tana duban Nusaiba tache,

"Dan me ake karatun ba dan ayi kudi bane? Idan aka baku kudin da zai isheku baki daya rayuwar ku baa an rufe babun ba? "

"Hakane kam..."

"Toh wannan shine abunda ke tafe dani..Ina Kuma faran zaki karba kokom barar mu?"

"Ai kin kawo babban abunda ko waye ma zai amince. " Nusaiba ta fada tana jin zuciyar ta na zafi. Kenan Nawraah har samari masu kudi take da? Gaskia ba zata taba barin Nawraah ta yi aure ta shiga gidan nasu hali ba.

"To yanzu Ina zancen mu ya kwana?"

"Toh hajia ba matsala. Bari baban su ya dawo. Sai muyi maganar ko kuwa? Don kinga ita nawraahn ma sai na tausashi mai gidan yaje ya yi mata magana ya hilata su sannan"

"Banason adau lokaci ne Nusaiba "

"Hajia bakida damuwa. Ni ma bana goyon bayan auren nan nasu. Zan shiga cikin lamarin kakki damu"

"Tohm shikenan sai na jiki. Ga wannan ba yawa" ta karasa fada tana mika mata wata envelop dake dauke da kudade aciki

Nusaiba ta karba envelope din tana riketa gam tana murmushi,

"Angode hajia. Sai kinjini inshaa Allah"

"Ba damuwa"

Har bakin kofar mota ta rakata tanata dashare mata hakora. Dr bintu ta shiga mota tatafi tana kambama son kudi da zuciya irin na nusaiba. Yayinda Nusaiba ta koma gidah ranta fes ga kudi da kayan abinci da burikanta da zaa cika.

::::::::

Da sauri ta ajiye wayar data kammala da marwaan agefen gado tana zare wa Amnah rigar makarantar dake jikinta tace,

"Ki wanka sai ki canza kaya muje gidan Mami kafin marwaan yazo. Idan muka gaysa sai na zo na dauke ki mu dawo gidah ko?"

"Tohm Adda"

Amnah ta shige bandaki bakinta dauke da addua tayi wanka. Nawraah ma tashiga bayan Amnaan ta fito itama tayi wanka ta zura wata riga marar nauyi ta dora hijabi akai.

Abincin da aka musu ta dakko ta zubawa Amnah faten doya ne da bushasshen kifi da ruwa su kaci suka ajiyewa su Raudah nasu.

Tana rike da hannun Amnah suka shiga gidan nasu hajia Qibdiyya. Kai tsaye suka nufi parlornta bakunan su dauke da sallama bayan sun danna door bell an bude musu.

Suna zama ba dadewa sai gata ta sakko tana murmushin ganin su.

"Ah lale marhaba Amnah da Nawraah na ne, Sannun ku"

Nawraah tayi murmushi. Suka durkusa suka gaysheta itada Amnah. Sun zauna a kasa kamar kodaa yaushe ta tilasta musu suka koma kan kujera suka zauna

Bayan sun gaysa ne tasa akawo musu abinci Nawraah tace sunci, duk da da haka ta saka a kawo musu snacks da lemuka da ruwa da chocolates. Ta kuma sanyawa Amnah acaroon tache ta kalla.

"Nawraah mucigaba da addua fa, inshaa Allah komai zai bayyana. Jiya munyi magana da baban su Anees yake shedamun anyi bincike akan sassan jikin motar da aka gani atare da kayan marigayiya. So akwai progress inshaa Allah"

Nawraah tayi murmushi tache,

"Allah ya amince Mami. Nima dama kusan abunda ya kawo ni wajen ki kenan.... Akwai yan wasu abubuwan da na keda su Wanda Ina tunanin zasu zama mukulli na bude ko ince bankada dukkanin boyayyan lamarin "

Hajia Qibdiyya ta kada kai tana duban Nawraah tace,

"Mashaa Allah, kamar Mai da me kenan?"

Nawraah ta dakko wayarta acikin jaka ta dubi hajia Qibdiyya tace

"Mami ko zaki iya tunowa?"

Hajia Qibdiyya ta dubi wayar tana duban Nawraah.

"Waya ce dai gatanan a hannun ki.."

"Kin manta wata waya da kika bawa ummyn mu?"

Hajia Qibdiyya jikinta ya fara rawa kamar mazari ta duba wayar tana jujjuya Kai,

"Wallahi itace. Allahu Akbar. Itace tabbss. Ya akai wannan wayar tazo hannun ki Nawraah?"

"Daga hannun ummy tajr hannun hamma shir. Daga hannun hamma Ashir tazo hannu na. Hamma Ashir yamun wasiyya kan karnayi amfani da ita har sai na shiga babban aji na uku zuwa na hudu.."

"Me hakan ke nufi kenan Nawraah?"

Nawraah ta dan sake muskutawa dawayar a hannun ta tana kokarin mikawa hajia Qibdiyya tache,

"Ko zaki saurari wannan ma....

Bata karasa fada ba aka budo kofar parlorn aka shiga. Marwaan ne da Anees suka shiga ciki bakinsu dauke da sallama . Da sauri ta mayar da wayar cikin jakarta. Suka amsa musu sallamar da sukayi...

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
_K'K'J_
_(M/W/S)_

_BOOK TWO_

_✍️:MX_

_23_

:::::::::
   Suna shiga yayi tozali da ita. Samun kansa yayi da tsayawa daga bakin kofa yana biye da ita da wani irin kallo tun daga kan kafafunta dake sanye cikin bakar safa ya zuwa kan kyakkyawar fuskar tah...

Marwaan ya karasa wajen su da sauri ya zube kallon sa fes akan sahibar zuciyar sa Nawraah...

Ita dinma shi take kallo tana murmushi hadi da saye fuska.

"Ah Marwaan" hajia Qibdiyya ta kira sunan sa tana murmushi

"Mami Ina wuni...?"

"Lafiya kalau marwaan. Ya su dr?"

"Suna nan kalau Alhamdulillah"

"Mashaa Allah! Meye haka kai kuma kaa tsaya daga can sandar ba'are?'"
Hajia Qibdiyya ta fada tana duban Anees dake tokare ajikin bango.

Sai a sannan Nawraah ta cire Kai ta dora akan sa. Idanuwan su suka sarke dana juna tayi azamar janye nata da sauri don kwayar idanunsa kansa ka tsaya kana duban sa sosai. Yanada wasu irin idanu tubarkAllah manya manya masu dauke da gashin ido Zara Zara baki wuluk

"Au wai bai taho ba? Yan mulkin sun motsa kenan" marwaan ya fada yana duban Anees.

Anees da ya kasa magana ya Kuma ki takawa daga inda yake zuwa wajen su Mami. Ji yayi bugun zuciyar sa ya sauya yana wani irin bugu sosai daya kasa tantance Wa saboda har wani zillo yakeji acikin kirjin sa.

Ba kadan ba Nawraah ta sakeyi masa kyau. Har ya sake cire Kai ya mata kallo na biyu. Bai sanda ya sauke ajiyar zuciya ba

"Mami...Ina zuwa" ya fada da sauri yana juyawa ya fuce daga parlorn

Nawraah daman jikinta ya bata sai yabar parlorn. Kasancewar yadda yake kyamatarta aganinta ba zai iya zama idan tana waje ba. Don haka ta dubi marwaan kawai ya daga kai suka sakarwa juna murmushi..

Juyawar da zaiyi yaga hajia Qibdiyya na duban su yayi saurin sakaa hannu a keya yana sosawa...

"Ina wuni?" Nawraah ta gayshe shi tana lankwasa hannuwanta.

Ya saci kallon hajia Qibdiyya yaga su take kalla.

"Lafiya lau" ya amsa ta yana mikewa tsaye

"Mami bari na je"

"Har zaka tafi marwaan. Ka tsaya Kaci abinci mana"

"A koshe nake Mami...." Ya fada yana satar kallon Nawraah datayi kicin kicin kanta akan tv

"To shikenan. Ka gayshe da Dr."

"Zata ji inshaa Allah" ya amsa da dan karfi ko Nawraah Zata waiwaya su hada idanu

Tana hankalce dashi don haka taki juyawa tana cigaba da kallon tv dake nuna hotunan faifon bidiyon fim din wasan na tom and Jerry.

Fucewa yayi bayan ya sake zuwa wajen bakin kofa yana dan daga murya,

"Mami shikenan"

"Tohm ka gayda gidah"

Ransa ya Kai koluluwar baci ganin Nawraah tayi kicin kicin bayan tasan wajen ta yazo. Amman ta nuna tamkar ma bata taba ganin sa ba

Wayar sa ya zaro agaban riga ya danna mata kira. Dauka tayi tana duban screen din tasan sarai daman shine zai kira.

"Ki dauka mana ba Kiran ki ake ba?"

"Ba komai Mami"

Hajia Qibdiyya tayi murmushi tana duban ta tace,

"Marwaan ne ai ko? Tashi kije mana ko na baki waje zai zauna anan?"

Nawraah kunya sai ta lullube ta, Daman hajia Qibdiyya tasani? Yaushe ta sani? Kunya duk ta sake gauraye ta. Ta Saka tafukan hannuwanta tana rufe fuskar ta.
Chapter 18 · 0% Book details