← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 44

Sashe 23

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hasbun Allahu Wa ni'imal wakil ..." Anees ya furta yana jujjuya kansa cikin alhinin maganganun da sukayi

"Sai addua kawai Allah yasa mu dace".
.
"Amin .. to Mami kashe iyayen nasu da wan nasu. Shima iyayen su Marwan dinne an tabbatar?"

"Hmm Anees kenan. Ba zanyi mamakin tambayoyin da kake ba sabida ni Kai na ba dan naga sheda ba wallahi bazan yadda ba. Amman komai nagani Kuma naji. Kusan ince Dr bintu ma tasan komai game da lamarin amman kaga Koda nake gaya mata rasuwar malama hindun nunawa tayi batada masaniya Anees. What a cruel world. Wannan rayuwar da ba abakin komai take ba yau ga naka gobe ga ka waninka. Amman wai ace musulmi yan uwan musulmi sune suke kashe kashen rayuka kamar cinnaka? Saboda mahaifiyar su Nawraah malama Hindu marigayiya kasan da zamuyi tafiya sai Dr bintu face dan Allah ta dinga zuwa tana mata abinci cuz taji yadda nake kuranta abincin ta, na taba aikenta karbo sako ma to harta taya su abinci Alhaju sambaso wai yayi ta Santi, to sai take neman alfarma. Na roki Hindu tace ba damuwa sai tayi,

"Anees baiwar Allah nan tagama musu abinci ta Kai. Ita da Nawraah dinnan ne kuwa sukaje . Yarinyar ta saka recoding a waya tana recording wakar Maher Zain da ake a tv din parlorn. Sai ita marigayiya taje takai abinci sai ta jiyo suna maganar kadarorin mahaifin ku Alhaji ateeks ya amince da sauran shareholders komai ya koma mallakin Alhaji sambaso. Anees wai har bintu ce zata dinga zagina tana fadan sunaye akai na da mugun alkaba'i . To sai ita marigayi Hindu taji, hannunta rike da kwanukan abinci a tray sai ta zubar a kasa. Saboda dimaucewa na abunda ta saurara. Sai bintu tayi kanta. Marigayiya Hindu ta shiga magiya tana cewa ba abunda taji ita daga rajat ma tabar aiki. Bintu tace tadama kunnu. To annanne Nawraah taje daukar wayar mahaifiyar tasu. Na karkare maka zance dai Alhaji sambaso shi ya kashe marigayiya Hindu hit and run case ne. Ya bigeta ya gudu abins a,a then later bayan abubuwa sun faru mijin ya gano Alhaji sambaso ne ya kasheta cikin fushi kagane sunata mayarda magana wa juna. Sai Alhaji sambaso ya tura shi mahaifin Nawraah malam Junaid. Ya fadi ya mutu"

"Sai kache film Mami? Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun "

"Hmm Anees rayuwar nan,kaji tsoron mutum kaji sai babban wansu bayan rasuwar uban. Yana amfani da wayar itamalama Hindu marigayiya nan yan gano recodings din ya saurara sai yaje wajen Alhaji sambaso din. Kai Inna lillahi Wa inna Ilaihi raji'un "

"Meya faru Mami?" Anees ya tanbayeta cike da damuwa

"Long story short ... Alhaji sambaso ne ya sa aka raba shi da ran sa. Kasan ta yaya?"

"Yadda muke maganar da Nawraah tace mun cause of death din shi yayan nasu...saboda tace a ranar da wan nasu zaa kashe shi ne yabata wannan wayar da komai yake ciki. Yache ta yi amfani da ita idan ta fara school amman karta ta bude media and files sai tana ajin uku zuwa na karshen gama jami'a. Tache yanayin sa ya sauya cikin firgici yake..."

"Eh eh Mami"

"Katuwar mota ce tazo ta bige su acikin motar yake taxi, komai da komai nasa ya kone. Subhan'Allah . Yaa Allah ka rabamu da zama ajalin wasu. Ka Kuma raba wasu da zama ajalin mu. "

"Gaskia dai astagfirullah. Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun..."

"And you know the most funny and cruel part?"

"No Mami. I'm all ears"

"Wai tsabar mugunta sune suke aika musu food stuffs irin suna claiming saint and caring, sannan bintu taba yaran scholarship a alhaaramein har su gama jami'a irin ga masu tausayin nan. Kai wasu abubuwan ma ba dadin fada ,Ga matar bappann su hates them plus sauran dangi sunki karbar su. Wato Anees sai kana raye ake yi da kai da iyalan Ka idan ka rasu bawon albasa ma yafi ka da iyalan ka daraja da matsayi awajen su. Allah ya sa mu dace"

Ameen Mami"

"Ga fate ya hada 'ya'yan su soyayyah. Har zancen aure ya shiga tsakanin su sunason juna. Iyayensa sunki saboda ba dangin kudi bane plus wadannan abubuwan Subhan'Allah

"Allah ya shiga lamarin su"

",Ameen"

Door bell ce ta fara Kara. Anees ya mike zai bude ya fara duban fuskokin bakin ta cikin wata tv dake gefe tana haska hotunan fiskokin Wanda zai shiga ko zai fita ta na'urar camera

"Baba da baban marwaan ne"

Hajiya Qibdiyya ta janyo hijabin ta dake gefe ta zura. Anees ya bude kofar yana musu sannu da zuwa .

Sukaa shiga bakinsu dauke da sallama. Suka gaggaysa duka. Kafin hajia Qibdiyya tace su koma kan dinning ga abinci nan.

Alhaji sambaso ne da dr abubukhar dollars suka nufi dinning Mami tayi serving din su abinci suka ci. Bayan sun kammala suna yar hira Alhaji sambaso ya dubi hajia Qibdiyya yace..

_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜
[5/15, 10:25 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_BOOK TWO_

_✍️:MX_

_28_

:::::::::

"Hajjaju what's your take akan kadarorin nan da aka yi mana fin karfi? Saboda kinji mutumin yana cewa shi baya ma san atada maganar abarta kawai... "

Hajia Qibdiyya ta kakaro murmushin yake, tana kambama karfin hali na mugunta irin na Alhaji sambaso.... Shine fa ya kwace kadarorin Amma saboda muguntar tasa ta zarce qima shine yake magana ahankali cikin harshen ban tausayi Kai kache bashida masaniya ko hannu aciki...

"Hakurin shine kawai mafita..dubada anja lokaci mai tsayi. Kuma anyi mai yiwuwa ba wani abu daya canzu. Ba rabo bane..."

Alhaji sbaso ya girgiza Kai irin ya jinjina maganganun da tayi ya dubi Dr abubuakhar dollars yache,

"Lalle ka zuga madam . Itama tabi bayan ka tache a hakura. Amman gaskia ko su waye basu kyauta ba. Amma ni dai duk da kun hakura ni bazan hakura ba. Idan yaso ko wasu wajen ne sai a baka su ka biya ko da 20 percent ne kadai. "

"Ah haba Alhaji Banda wata wahalar Allah. Ba rabo bane. Nan gaba idan da yi wuwar a saya wasu din sai ayi. Amma for now dai bana goyan baya kan wai mu sake mallakar wasu dukiyar ta hanyar shareholders. "Hajiya Qibdiyya tayi hanzarin cewa hakan kafin Dr abubuakhar dollars ya bashi amsa.

"Kun dai dage akan ma tsaya daya kenan. To shikenan Allah yasa hakanne yafu alkahiri Amin"

"Ameen baban Marwan... Tunda baa sake yin wata babbar maganar data danganci kadarorin ko?"

"Gaskia ban sake jin maganar ba. Allah dai ya kyauta " Alhaji sambaso ya fada yana jijjga Kai hadi da kwafa irin anyi muguntar nan baa kyauta ba

"Ai shiysa nace maka abar zancen kadarorin nan, Allah daya bashi su ya karba ba zai hanani wasu agaba ba. Sannan a yanzun duk rayuwar da muke a baya ta jin dadi da walwala ba abunda ya rage mana shi. To iya hakanma alhamdulillah gidan ba abunda aka nema aka rasa ko zuwa wajen wani ko wata a rollka. " cewar Dr abubuakhar dollars..

"Hakane Kam ka gama magana..." Alhaji sambaso ya fada yana kurbar ruwan robar dake hannun sa.

"Bari naje sama..idan na sakko bakwanan to. Allah ya tsare hanya. A gayda min aminiyata da yarana"

"Ah ni ba na manta ba. Aminan juna kenan. Tace lalle na kawo gaisuwar mai kima cikin kwando kwando. "

"Allah sarki. Nima Ina amsawa a million. Dan Allah karka manta"

"Ah ni na isa na manta? Ai sai ahanani shiga gidan idan na manta sakon ki"

Daria sukayi baki daya. Ta dubi Alhaji Abubakhar dollars Mai gidanta tache dashi

"Akwai abunda zaka bukata na ci kafin ka dawo?"

Dr. Abubakhar dollars ya bude baki zaiyi magana Alhaji sambaso ya rugashi,

"Ah madam wato zaa sakeyin haddadiyar wakewa kenan amma sai na tafi . Ah lalle Anees kana jun wanj wariyar launun fata ko?"

Anees yayi murmushi Kawai yana kada Kai. Yarasa bakin magana domin baki daya idan ya dube shi mamakin abubuwanda akace ya aikata yakeyi. Kuma.har yakeda kwarin gwiwar da muguwar zuciyar dake mu'amala da su bayan ga zagon kasan da yayi musu, Ga Kuma lefin kashe rai fiye da daya.

Haka dai ya gama zubar maganar sa. Dr dollars na biye dashi a baya. Shi dama bai cika magana ba. Alhaji sambaso ne me magana sosai.

Futa sukayi atare. Hajja qibdiyya tayi sama dakinta , Bandaki ta wuce ta sake yin wankaa, Ta sauya kaya zuwa na bacci wato pajamas dama tunin ta turara su da turaren wuta na kaya ta shafa musu oudiyya set din kamshi na kamfanin turaren Yerwa incense and more.

Ta taje kanta dake tanada yalwataccen gashi tayi parking dinsa da ribbon ta yafa dan karamin mayafi ta sauka zuwa kasa.

Tea ta dafa na ginger da cinnamon hadi da pinch din sunflower seed. Ta saka turmeric da Madara kadan.

Ta aika maii aiki ta bawa wani matashi dake sharewa su Anees dakunaa ya wanke bandakunan su ya Kuma Kai musu abinci.

Lafiyayyen girkin dazu ne aka sake reheatinh dinsa a microwave aka mai hadin juice na fruits da aka matse sai flask na tea. Da cubes of sugar and milk.
Chapter 23 · 0% Book details