← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 44

Sashe 33

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Of course gidan ki ne ko nawa? Zan jira kine kinje kina ta bacci?"

"Subhan'Allah" ta fada tana dafe kanta saboda tsananin sara mata da yakeyi.

"Daman ba mafarki nake ba Alhaji? Dama ba wasa kake ba Alhaji. Wai dagaske lamarin jiya ya faru Alhaji?"

Ta fada tana jujjuya kanta hawaye na zurara mata. Alhaji sambaso ya dubeta yana tabe baki

Katuwar mota ce ta shigo tana nishi. Alhaji sambaso ya mike da sauri yana ajiye cup din hannunsa akan tray.

Dr bintu itama ta mike tana bin bayansa ganin zai fita,

"Menene haka kike bibiye dani?"

"Lefi ne dan na bika? Beside mota ce tayi kara gatanan ta ta shigo zanga motar meye"

"To tunda ke kika aiko su ai se ki fita kuyi magana ko?"

Girgiza Kai tayi tana ja baya ganin yayi wajen kujera zai koma ya zauna,

"Kayi hakuri"

Ta fada tana komawa parlorn ta zauna. Ya saki tsaki yashiga dakinsa ya fita wajen.

Zungureriyar mota ce katuwa ta wani babban company dake kawo kayan gidah na gadaje da kujeru yan kasar waje.

Akwai wani sashen babba da har yafu Wanda suke ciki kyau acikin gidan yake shima yana facing Wanda suke ciki. Daga baya ya sayi kango ya shigo dashi gidan ya gina sabon an masa komai na wuta da ruwa a bandaki daman kayan gidan kujeru ne baa Saka ba da sauran su. A baya ta bashi shawarar ko idan marwaan yayi aure ya zauna anan . Idan yaso tunda fuska biyu ne gidan sai afutar masa da gate dinsa daban.

Bude baki tayi cike da mamaki gabanta nata bugawa. Zuciyar ta na hasaso mata tabbas suprise (bazata) ne yake son ya Mata bayasan tasan komai akai shysa ya fara acting dinnan.

Ta tabbata sabon gidanda ke cikin nasu da akayin shine Wanda zasu koma ciki kafin su tafi.

Wani murmushi ya kufce mata. Tana sake leka windown tana hango maaikatan nata shiga da kayan cikin gidan wasu Kuma tun da suka shiga basu fita ba da alama jere su suke

Bakinta ya sake hangamewa da farin ciki lokacin data hango wata motar ta sake shiga duake da kwalaye na kayan kitchen kuloli ne da sauran su komai da komai dai na alfarma.

Ta murmusa komai ta haye sama tana jin zuciyarta na mata dadi. Bandaki ta shige ta fyallo wanka ta sauya kaya zuwa wani hadadden lace ta zuba sarka da dankune harda su jambaki ta zurara da hoda. Ta feshe jikinta da turaruka masu matukar kamshi da kwantar zuciya.

Ta gama shiryawa ne. Lily ta kwankwasa kofar ta shiga ta shirya tsaf zata futa,

"Maa"

"Naam Ina zuwa?"

"Salon"

"Okay tohm sai kin dawo"

"Baba ya fita?"

"A'a na dai hawo sama wanka"

"Okay"

Fita lily tayi ta tsaya da mahaifin nata Alhaji sambaso suka gaysa tace salon zata ya bata kudi. Ransa a murtuke ya dakko dubu daya ya mika mata,

"Baaba dubu daya fa ka miko mun"

"Eh abunda zan iya bayarwa kenan. Idan bazaki karba ba kawo"

Bakin lily a bude ta kasa cewa komai. Ga maaikata nata shige da kawo cikin sabon sashen da akai.

"Banaso" ta fada tana mika msa kudin

Ya karba ya cusa a aljihu. Takaici yasa ta kasa cewa komai ta shige mota ta tasheta ta fita.

***

Marwaan da ciwon Kan da yake yaki tafiya. Wanka yayi. Abincin da aka Kai masa yaci ya sauya kayan sa zuwa kanana riga da wando na English.

Fita yayi tsakar gidan na su don hayaniya dayake ji anata magana. Manyan motoci ya gani sunata sauke kaya suna shigarwa sabon sashen.

Ganin mahaifin sa yasa ya karasa wajen sa ya tsugunna,

"Baba Ina kwana..?"

"Lafiya"

"An tashi lafiya?"

"Lafiya"

"Baka tafi aiki ba kenan. Inata sauri"

"Dama tafi zaka ganni ne yan zu a haka?"

Marwaan ya girgiza kansa yace,

"A'a baba. Allah yabaka hakuri"

Ya juya ya shige cikin gidan sashen mahaifiyar su Dr bintu. A tunanin sa har yanzu mahaifin nasa bai daina fushin dashi bane shysa.

Yana shiga parlorn Dr birtu na sakkowa. Ya gayshe ta amsa tana murmushi,

"Ka gayda baban ku?"

"Eh"

"Ya kukai bai gaya maka can gidan gyaran me ake ba?"

"Bai fada ba. Kinsan fushi yake da ni"

"Ni dinma. Amma nafi kyautata tunanin can gidan da ake jere zamu koma kasan da an barshi akan idan kayi aure a futar maka da gate ka zauna aciki"

'oh ai ni banason zama agidah ma. Nafison wata area ko wani garin ko kasar"

"To ai gashinan nanma Allah ya dubi zuciyar ka. Mu zamu koma, don kada nayi fada nasan shine da kansa yasa aka sayo komai aka jeren Kai Alhaji"

"Okay bai gaya miki ba?"

"Bai fada ba.kila kayan sawarmuma Kai mana zeyi can din. Hahah ya hutassheni ma ai. Allah na tuba ba hanawa zanyi ba. Tunda dai ni zan zauna aciki da iyalina"

Marwaan yayi murmushi kawai kansan a kasa,

"Kaci abinci?"

"Eh"

"Toh mashaa Allah"

Suna dai ta zaune suna hira jefi jefi. Har maaikatan suka kammala jera kaya aka wanke gidah aka tsaftace koina. Maaikatan suka tafi da motocin su.

Alhaji sambaso ma ya fita... Bai dawo ba har bayan wajen biyu na dar, ranar ma a dakinsa na kasa ya kwana bai bari sun hadu da Dr bintu ba ma ya sake fita

Akan kawo manyan talabijin kayan kallo da sauran su aka jera. Dr bintu dai nata murna tana hasaso yadda zatai recording ta turawa kawayen ta an gyara mata gida sabo.

Bayan anyi ishai abadan. Sai ga motoci har da jiniyar yan sanda sun shigo gidan. Ta daga labule tana lekawa. Ganin Mata na fitowa daga cikin moticin

Ta dafe kirji tana ware idanu tace,

"Alhaji daurawa marwaan aure yayi batare da masaniyar sa ba"

Sauka kasan tayi da sauri jikinta na rawa. Lily dake parlor tabi bayanta

Ai kafin su fita ma. Tuni matan sun shiga cikin parlorn suna sallama.

Suka koma ciki ta tsaya a tsaye ta kasa zaune,

Gaysheta sukayi ta amsa tana duban su da kallon karin bayani.

"Yar uwar ki ce muka kawo"

"Yar uwa wata iri Kuma?"

"Abokiyar zaman ki"

Dariya ta fashe da ita tana tafa hannuwa,

"Abokiyar zama wace iri? Oh ko makociya ce aka kawo mu gaysa?"

"Abokiyar ki zaman ki dai a matsayin na uwargidah, Kuma yaya awajenta yanzu. Mukace bari mu fara kawota ku gaysa ki sa mata albarka"

"Bayan Allah batan hanya ko ince gidah kukai banan bane gaskia. Ko gidan su izzu ne nan naga ana biki kaman" lily ta fada tana duban mahaifiyarta ta

"Nan ne dai.. Ba nanne gidan Alhaji yusufa sambaso ba?"

"Eh" lily ya amsa

"Marwaan aka daurawa aure?" Dr bintu ta fada tana kokarin bude lafffayar amaryar

"Waye haka?.oh ko dan sa? A'ah! shi kansan dai arzikin ya fada. Mai gidan naki ne dai ya karo aure. "

Hannun Dr bintu na na rawa ta yaye fuskar laffayar amaryar..

Wa zata gani? Kubra kawarta kuma aminiyar ta datasan kowane sirrinta ce sanye cikin laffayar ta saddaa kanta. Kamshi sai tashi yake daga jikinta. Kanta an yarfa mata kananun kitso ya fito ta gaba.. Yayinda hannunta da kafafuwanta sun sha lalle maroon da black

"Kubrahhhhh?"

Dr bintu ta fada a razane. Ta sulale ta sume a wajen.... Tana bude idanu ta ganta a asibiti marwaan da lily akanta......

Ta Kalli gefe an rubuta a bango 'Emergency unit... Amenity annex'

...

https://t.me/BlumCryptoBot/app?startapp=ref_7XYZOnMEWU

Kuzo ta fashe da mu a Blum🥳🥳🥳 ga link nan. Allah yasa my dace Amin
.

ATUWAA🧕

_K'K'J_
_(M/W/S)_

_BOOK TWO_

_✍️:MX_

_40_

:::::::::

"Maa kin farfado? Alhamdulillah" marwaan ya fada yana murmushi

"Maa" lily ta rungumeta cike da jin dadin itama

Dr bintu ta daga hannu dakyar tana duban roban ruwa da yake shiga jikinta ana mata kari.

Hawaye suka shiga wanke mata fuska. Tana kokarin tashi daga kwancen da take ta kasa ..

"Karki tashi maa.. ki dakata tukun"

"Meya faru da ni....duk mafarki nake ko?.

Marwaan ya girgiza kansa yana duban lily yace,

"Ba mafarki bane maa. Amma dai dagaske bakida lafiya doguwar suma kikai.Alhamdulillah Kuma kin farfado"

"Yanzu yusuf yayi aure? Yusuf ya auri kubrah? Kubrah fa aminiyata innalillahi Wa inna ilaihi rajiun"

Lily zubar da hawaye takeyi takasa cewa komai sai marwaan ne mai samun kwarin gwiwar amsa mata.

"Kiyi hakuri maa kinga bakida lafiya kinji? Karki saka hakan a ranki. "

Dr bintu ta barke da hawaye sosai harda shessheka tamkar karamar yarinya

"Yanzu Ina yusuf din?"

Marwaan ya sosa keyarsa yana datse harshe bai ce komai ba

"Ba kuce komai ba yana Ina yusuf din?"

"Maa yana gidah"

"Bai zo ba?"

Suka gyada mata Kai a tare. Wasu siraraan hawaye ne suka zurara daga idanunta. Ta Saka hannu ta share hawayen tana mayar da kanta gefe tace,

"Waya kawo ni asibitin?"

"Ni da lily"

"Lalle.... Humm yusuf kenan. Kubrah Allah ya Saka mun"

"Ma wannan dai aunty kubrah din?"

"Itadai"

"Subhan'Allah"

"Auren cin amana..kema maa kin yarda da mutane. Matar nan komai tasani . Ashe Ashe" lily ta fada tana gyara zamanta akan kujera dake kallon gadon marasa lafiyar da Dr bintu ke Kai. Yayinda marwan ke a tsaye.

"Rashin sani mana, kubrah taci amanata. Yusuf yaci amanata. Allah kana gani" cewar dr bintu

Haka dai sukayita bata hakuri ... Ruwan da aka sanyaa mata ya kare. Aka mata allurori suka Kuma bata magunguna.

Gidah marwan ya mayar da su. Suka taimakawa mahaifiyar tasu suka shigar da ita sashen ta. Kasancewar dare ne.

Wanka tayi kawai ta kwanta akan gado tanata juyi. Hawaye nata zuba daga idanunta. Ta dakko wayarta tana duban chatting dinsu da kawartata da tazama kishiyarta wato hajia kubraa. Duk matsalolin Mai gidan nata take gaya Mata da yadda zaa shawo kansa awajen bokan su ya sake barke Mata bakin aljihu...

Mikewa tayi dakyar ta leka window ta saman ta hango dayan gidan da kubran take da Alhaji Sambaso. Ko'ina yayi dau da hasken shima. Idanunta ta runtse alokacin data ga an saki labulen dakin datake hango window.

"Shikenan yusuf zai kwana da wadda bani ba? Kubra aminiyata zata kwana daki daya da miji na uban yaya na? Innalillahi Wa inna ilajir rajiun"

Ranar dai haka tayita zulumi tana koke koke tana surutai. Bacci barawo ne ya sacheta
Chapter 33 · 0% Book details