← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 44

Sashe 42

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tunda bakwa neman nu daga can ma wani garin zamu"

*No haba Muna neman ku mana ... "

"Ina Nawraah?"

"Tana bacci....*

"To ga amanar yar mutane nan anbaka Anees. Ka kula da marainiyar Allah."

"Ah Mami me yasa kike cewa haka kaman Wanda ni dayane tare da ita duk gakunan Mami ai kune iyayen ta"

"Yanzu da batadasu ai Kai ne iyayen ta. Sai ka tsaya ka kula da ita"

Anees yana tsaye sai ya zauna yana dartse harshe ya famo cuwonsa da yayi yache

"Mami kina maganaa kaman ba zaku dawo tare asibitin ba ku cigaba da junyata"

Hajia Qibdiyya tayi murmushi tana kallon Dr dollars dashima kallonta yake,,

"Anees mufa ka ganmu nan a airport straight gidah zamu koma . Sai jikin naka yayi sauki. Idan ya Kara sauki sauki dawo inshaa Allah. Muna komawa abban ku yace ayi lefe babba da gidan daya babbaku a gyara naka idan Kun dawo ku zauna"

Anees mamami baki bude sai ya rasa me zeyi kukan farin ciki ko dariya yache,

"Nagode sosai. Allah ya biyaku da aljanna."

"Aaaameen jam'an idan Nawraah ta tashi ka ce Muna gaysheta idan mun karasa zamu kira waya inshaaa Aallah"

"Tohm Mami inshaa Allah... Anees ya fada cike da farin ciki ya zube akan gado yanata murmushi yana Murna harda daga kafa... Ya matsa wajen Nawraah tana dubansa tana lunshe ido, yache,

"Wifey da ga ni sai ke muci karanmu ba babbaka. Ya fada yana gyara mata kwanciya a jikinsa...

Ko bayan ta tashi take tanbayar Anees Ina su Mami har yanzu basu zo ba.

Anees yayi murmushi yana gyara zaman rigar sa yace,

"Sun koma su... Mu Kuma zamu bi bayan su"

"Bangane ba Ina sika koma hotel?"

"No can dai gidah. Sun koma.... Sai mu lovebirds"

Nawraah kunya ta isheta. Taja bargon ta rufe har kanta tana tukwikiyewa..

Anees ya sake matsawa dad da itan yache,

"Na baki Kai na, Raina, zuciyata Kai dama gangar jikina Nawraah. Dadin da kika shayar Dani baa magana. Sai dai nace Allah ya Saka miki da alkhairi. Yadda kike gwarzuwa Mai dauke da zumar dadi mai dandanawa, wifey na ma rasa ta Ina zan fara... hakama kedin komai naki daidai ne cute, and sweet Omo yadda zan bayyana miki..

Jin rashin kunyar da yake rada mata ne yasa ta saki yar kara tana rufe fuskarta gam

Anees yayi murmushi ya koma gefe kawai shima yana tunnaninn dadda'daan daren nasu da bazai taba goge masa ba a kansa..

°°°°=°

Sabuwar rayuwa suka shiga yi. Ko da aka sallame su daga asibiti. Daman vvip hotel din da su Mami suka kama baiyi expiring ba.

Don haka akwai sauraron wata uku ragowar zaman su, plus wasu kwanakin da aka biya musu, Anees ya wartsake ragal. Soyayya ba kama hannun yaro haka sukeyinta tamkar cin kwan makauniya...

Wata ukunnan da sukayi agarin Nevsehir dake cappadocia ta yankin Istanbul.

Soyayya ce sun zuba ta fiye da yadda alkalami zai rubuta. Suna Kuma kaunar junan su tamkar zasu cinye juna mashaa Allah...

Sun zaga gari ko'ina sunyi touring na turkiye sosai. Don har Istanbul suka je suka zaazagaya sauran garuruwan irin su Cyprus da sauran su...

Hajia Qibdiyya dake gidah kuwa tanata shirya rantsattsin lefe na Nawraah. Gidan da mahaifin su ya bashi ma shima anata gyarare shi an zuba furnitures da komai..

Bayan sun waiwayo Nigeria ne. Yan uwa tamkar zasu hadiyesu. Ranar da Nawraah taga lefenta sai datayi kuka sosai na farin ciki.

Lefen nan ko gidan shugaban kasa aka kaishi sai anyi santin sa.

Hakama gidan da zasu zauna, komai yayi acancan na masu kudi

Tuni Nawraah ta dakko Amnah ta dawo da ita gabanta. Domin idan ta kalleta fuskar mahaifiyar su marigiyya Hindu kawai take gani ko a baya. Dan zaman da sukayi a cappadocia ma ya sanya ta sake maraicin kanwartata sosai....

Dare ya zama safiya safiya ta zama rana, rana ya zama yammaci lalle Allah qadirun ne aka manyashau..

Rayuwar kowane bangare nata tafiya... Gwanin ban shaawa. Alhamdulillah

Daga Kuma kasar wajen ne inda Anees yayi karatun PhD wato Manchester suka nemi yarjewar sa don ya dawo karkashin kasar su da iyalinsa su fara aiki sun dauke shi aiki da gidah da mota da scholarship na yaransa da dukkanin komai...

Nawraah dai batasan komawar su wata kasar, Tafusn Naduka musaman sabida yanuwa datake dasu, gasu Mami ma.. Amma barin kasar da garin baki daya bataso munsaman da kaburburan iyayen ta Dana dan uwanta yana burnin naduka..ji take kaman tana tare dasu ne Amman sun dan mata nisa...

Ta Kuma Dan fara damuwa arashin samun ciki dabata dashi, duk da dai ita kadai take damuwa, iyayen mijinta da yan uwansa basu taba mata gori ba. Amman ita tana kokarin son tasamu ciki, Musanman ganin dukkanin yan gidan marayu kawayen su da sukayi aure sun haihu tuni, Su wasila da Raudah da faty... Nawraah ta tsaya akan auren su sanda zasu yi, Ta Kuma sake fadada gidan marayun da gyare gyare da abubuwa. Domin ba zata taba mantawa da gidan marayun da suka karbe su a alokacin da duniya ta juya musu baya. Ciki harda yan uwan mahaifin su da suke gani a matsayin nasu iyayen Amman sun fito since basa kaunar su ba zasu rike su ba. Dukkuwa shekarun baya akai hakan komai ya wuce.... Amman abunda suka musu ba zasu taba mantawa ba!!!

MX🧕💜
*_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_✍️: MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

_👇_
*_wattpad: mssxoxo00_*
*_arewabooks:mssxoxo_*

*_BOOK ONE: COMPLETED☑️_*

*_BOOK TWO: COMPLETED☑️_*

*_PG :50_*
*_FINALE/KARSHE_*

_*(COMPLETED BOOKS/THE END/AN GAMA LITTAFIN DUKA 1& 2 KAWAI NE DAMA BOOK DIN)☑️*_

____

To haka rayuwar ta cigaba da garawa, yau da dadi gobe akasinta... Kowanne bangare na cikin koshin lafiya.

Farin ciki da kwanciyar hankali hadi da tarin arzuka sun wanzu a gidajen baki daya

Musanman gidan Anees Abubakhar dollars da Mai dakin nasa Nawraah...

To daman komai lokaci ne Kuma sai Allah yaso a sanda yake so yake amincewa da dukkanin kowa da komai..

Nawraah ta takurawa kanta rashin haihuwar da batayi. Gashi sun jajje asibiti ance kalau Allah ne bai kawo ba, Amma itada Anees din komai nasu ma lafiya ba matsala yake..

Damuwar tata ta karu ne alokacin da Layla ta haihu da namiji aka sanya masa sunan marigayi bappah Junaidu suna cewa dashi junior...

Nawraah kwananta biyu agidan Layla suka sadaa zuminci sosai bayan suna ta koma nata gidan dake wata gra...

Ashfeef da Ahmad ma an Kai kudin auren su don har an daura auren ma dake basasan taro a biki. Don haka sukazo kasar bayan wani lokaci Kuma sika koma da matan nasu can kasar wajen da suke ...

Ashfeef ya auro can tsatson su na nesa dinnan dake yankin bunza. Yayinda ahmad ya auro Mai awarar nan dai da Nusaiba tace batasonta.

Nusaiba ta fito daga gidan yari ta koma can Kauyen su dake yankin bunza can garin su. Kowa yace ba zai aureta ba yaji munanan halayen ta...batada aiki sai bin yaran kauye tana duka. Ga bakar sata data keyi. Tana fiffika, zawara yan uwanta mata suka koya mata hankali da ruwan tulu suka zuba mata karatun ta nutsu ko su koreta daga garin...

Bappah Auwalu ya sake samun kwanciyar hankali da nutsuwa... A can gidan sa shida matar sa.

Yayinda Nawraah ta sayi nasu na da Wanda mutumin ya sayar ta sake saya awajen sa..

Ta samo wata mata da basuda matsugunun zama. Tace tabasu har Sanda sika mallaki nasu. Lokaci zuwa lokaci takanje gidan nasu ta zauna tana tuno rayuwar su ta baya ... Komai yanzu ya wuce ya zama labari..

Alhaji sambaso ya samu tabin hankali. Shi kadai yake surutai..An yanke masa zama a kurkuku na shekaru da yawa sannan ga aiki da ake sanya shi na dako a kurkukun da ebo ruwa. Bashida aiki sai yayita zama shi kadai yana cewa,

"Ni na kashe uwa da uban da dan nasu... Na Kuma kashe 'da na marwaan. Marwaan fa. Na kashe marwaan jamaa... Kuma sun sace mun dukiyata dana kwace da kyar...."

Wani lokacin Idan ya hana yan dakin gidan yarin nasu bacci da surutunsa sai su tashi su lakada masa na jaki. Bashida kowa bashi da
yan uwan dake kula dashi ko su kawo masa ziyara, kowa ya rabu dashi.

Domin da a baya daya keda kudi bayayiwa yan uwansa na can kauye . Don haka kowa ya manta dashi. ...

Dr bintu an saketa daga gidan yari ta samu ciwon nakasar hannu daya baya aiki. Sannan idonta daya ma ya shanye da daya take gani .

Batada aiki sai kuka ta koma gidan su wajen
Yan uwanta. Suma basa kulata . Kowa yana kyamatarta tamkar yadda takeyi a baya..

Daki daya aka bata itada yarta lily. Bandaki ma na tsakar gidah Kuma na kasa. Sai hamamin doyi ne yake tashi. Har layin shiga sukeyi. Sannan ba ruwa sai ta ebo Wanda zasuyi amfani dashi a layin borehole na tuka tuka....

Dr bintu kullum sai tayi hawayen dana sanin rayuwar daga girba a baya. Yanzu komai da take kokarin yafaru akan bintu da iyalinta shi ya maye nata gurbin.

Sun rasa dukiya. Mujin datake so ya haukace, An kwace dukiyar tasu dama ta haram ce. Daidai da cokali babu. Amaryar da Alhaji Sambaso ma yayi tuni ta shallare tabar gidan daman batasan kudin damfara bane tarin arzikin na su. Don haka hukuma bata tafu da ita ba..

Acikin 'yaya biyu da Allah yabata jal a duniya.. marwaan babban dansu namiji ya mutu sanadiyyar mijinta Kuma mahaifi ga mamacin akan neman duniya.. gidajen da take takama dasu harda Wanda take ciki da sauran kadarorin an kwace dika Ashe kudin Haram ne ya cinye kwangilolin mutane harda na aminann sa dr dollars...

Rabon dataci kaza ta manta. Ga lily yar tata ta zama mai budadden idanu kullum futa take da dare ta dawo da safe.. rayuwar Dr bintu na cikin wani hali na tausayawa. Amma koma menene itace ta janyowa kanta rayuwa take koya Mata hankali, take girban abunda suka shuka a tun kan aje lahira..

°°°°°°

DR. ANEES ABUBKHAR DOLLARS AVENUE:

Nawraah na zaune tanata tunani ita kadai. Amnah kanwarta tayi bacci a dakin ta dake gidan.

Ta baza turaren wuta na kamfanin tiraren Yerwa incense and more Mai suna mukammaria.
Chapter 42 · 0% Book details