← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 44

Sashe 3

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haifa ta shiga nuna musu ko'ina da ko'ina daya dace daga nan ta nufi da su gymnasium inda wasu daga cikin vvip students suke motsa jikin su..

Idanun sa ne ya sauka akanta alokacin da yake kokarin daga wani babban karfe yana motsa jiki da shi..

Ta juya manyan idanun ta tana bin ilahirin babban dakin motsa jikin da kallo...

Bangaren mata na daga can baya wata mata murdaddiyar mata daga gani taci karfe itace ke koya musu

Yayinda mazanma akwai me kula da su shima a murde gabobin jikin sa suke..

"Nan ne gym na Alharamein university..... Amma ba kowane jig and jah bane yake zuwa nan. Free ne for all students a lokacin da aka buda jamiar. Amma da aka samu shareholders da yawa sai aka mayar da shi premium card ne. Kowane student member sai yanada premium membership card sannan zai iya shiga ya motsa jikin sa..."

"Lalle lamarin na manya ne..." Cewar Layla tana jijjuya Kai

Nawraah kuwa bata samu bakin magana ba illa dai ta sauke gauruwar ajiyar zuciya mai tarin ma'anoni...

Juyar da manyan idanunta keda wuta suka sauka akan marwaan daya taso ya kasa cigaba da motsa jikin da yake.yana tafe yana goge fuskar sa da hankici.

Inda suke ya fara dosowa yana murmushi. Iily ta juyar da janta tana kokarin hango anees dake can baya yana motsa jikin sa.

"Dear sis"

"Naam bruh.. Ina yaya Anees?"

"Gashi can yana exercise.... Kinsan su ne?" Ya tanbayeta yana Mai Saka yatsaa yayi nuni da Nawraah.

Iily ta kada masa Kai tana murmushi tace,

"Imran akace yayi volunteering so I lend a helping hand"

Marwaan ya tabe baki yana Mai Karkatar da hankalin sa kacakan kan Nawraah da take saye fuska.don ganin mazan yawanci ba riga suna atisaye ba kadan ba kunya ta cika ta da fargaba.

"Mind to show you gorgeous around?" Ya fada yana kallon Nawraah sosai

Yi yayi tamkar ba tasan yana magana ba. Ta riko hannuwan layla tana janta..

"Ku jirani mana. Kamar kinsan makarantar ne zaku tafi?"

Itadai Nawraah bata tanka musu ba ta janye hannun Layla suka karasa fita .

Marwaan yabi bayan su da sauri har yana hadawa da gudu...

Yana juyawa hango su suna tsaye ita da Layla..

Yayi azamar riko kasan mayafin Nawraah yana jefa mata wani kallo na please ta ba shi lokaci kankani..

"Please ...kinji beautiful?"

Ya sake jeho mata tambaya yana danne kasan leben sa

"Same department kuma?"

"Criminology...." Layla ta amsa shi tana dubansa dakyau

Sanye cikin manyan kaya na yadi, kansa ba hula kwantaccen gashin kansa ya kwanta luf

"Mashaa Allah! Allah yabada saa"

"Aameen"
Nawraah ta amsa cikin sunkuyar da kanta a kasa

"Chan swimming pool ne, Da na gefen sa kuma cit, can campus library da sauran su"

"Mungode .."
Suka hadi baki wajen amsa shi

Gaba suka yi, Nawraah ta dubi Layla,

"Wannan makarantar an hada yayan manyan sosai."

"Sosai ma. "

Iily na ganinsu tayi sauri ta mayar da wayarta acikin jaka. Ganin tayi message, calls, Whatsapp call, Duk yayi shiru bai ce komai ba"

Ta sake dubawa tana dage ta leka yana kwance akan wani gado na atisaye rike da wayar sa ahannu...

"Muje ko?" Iily ta tanbaye su ranta ba dadi

"Eh tohm"

Rankayawa sukayi gaba daya suka futa daga harabar farfajiyar gymnasium din zuwa main campus central mosque..

"Nan ne masallaci. Idan kuka gama sai lectures block b ne. Auditorium one thousand seaters.."

"Okay elective course ne? Bakya yi?" Nawraah ta tanbayi lily

Lily ta girgiza kanta tana danne hawayen da yake so ya bujere ya zubo mata tace,

"Kai na ke ciwo bazan samu attending ba"

"Allah Allah yakara sauki" suka hada baki wajen yi mata sannu,

"Ameen nagode"
Gaba tayi ta daga musu hannu alamar bye bye..

Masallaci suka shiga suka rage cikin su suka daura alwala. Suka tada sallah sukayi sallar su bayan sun idar ne sun dan huta. Suka nufi cafeteria don cin abinci sannan su biya dakin lakca..

*CAFETERIA/WAJEN CIN ABINCI*

_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜

[4/28, 12:25 AM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_6_

:::::::::

Suna dosa kansu wajen babbar kofar da zata sadaaka da cikin wajen cin abincin. Kofar ta bude... Bayan sun shiga ta komai ta rufe da kanta.

Layla ta riko hannun Nawraah tana mata rad'a.

"Kinga kamar a film da ake nunawa chab"

Nawraah tayi murmushi kawai tana duban harabar wajen cin abincin... Baki dayan daliban wajen suka tsaya suna duban su.

Da masu cin abinci da masu shan abin sha. Sun rarraba kansu. Wasu sunyi group iya mata, wasu maza zalla. Wasu mazan da matan duk a hade. Wasu kuma samari ne da yamma ta suke zance..Kowanne dai da abunda yake yi...

"Layla zomu tafi .. Nan wajen anya na talakawa ne kuwa?' Nawraah ta fada tana duban Layla

"Ke kin cika saurin karaya. Ya zaki ce nan din ba abunda kudin mu zai iya saya? Jami'a ce fa..."

"Shikenan muje..."

A haka suka karasa inda tulin abincin sayarwar yake kala kala gasu nan a jajjere kala kala na gidah dana waje..

Layla ta tabo kafadar Nawraah tana mata nuni da wata stir fry spaghetti sai kamshi ne ke tashi daga cikin ta..

"Nawa ne da ke?" Layla ta radawa Nawraah.

Nawraah ta wulkita idanu tana hararo wajen kwanukan abincin tace,

"Nera dari ce.. ke fa?"

"Nima darin ce sai wata danayi dan taru a asusu na curo"

"How may I help u?" Wani ma'aikacin wajen abincin ya tambaye su yana bude murafen wasu kwanukan dake cike da kaji sun gasu da kifi

Layla ta sa hannu a baki tana cizawa tache,

"Where's the menu?"

"Here... Ma'am.."

Karba tayi tana nunawa Nawraah. Idanun su suka firfito waje kaman zasu fado saboda tsananin mamakin kudaden abincin da suka girgiza su..

"Karamin abu anan na dubu biyar ne layla shi yasa nace miki anya wajen nan zamu iya shigar sa? Dukan kudin namu idan an hade su dari uku ne fa. Ko ruwan sha ma kina ganin dari takwas ne na roba me sanyi babu ma sachet water.."

Layla ta sauke gauruwar bahaguwar zuciya tana mayar masa da menu din. Nawraah sai janta take subar wajen Layla taki ta sake cewa dashi,

"Ba kuda awara ko gurasa haka?"

"Awara? Gaskia babu... "

"Ba wani abincin me karamin kudi haka daga nera dari?"

"No babu" ya fada yana tamke fuska hade da rufe food flask din wajen da murafen su,

"If u'll excuse me. I will attend to another next person. Mungode"

Barin wajen yayi ya komai daya bangaren harda gaishe da su yana murmushi .

Yammatan nanne kawayen lily na dazu da suka da kawa imraan tsawa suna masa tsiwa da fada.

ATM card dayar ta zaro ta mikawa waiter din tana duban sauran kawayen nata tace,

"Me kike so kuci?"

Layla ganin tun dazu sun tsaya tare dazu hakan yasanya ta karasa kusa da su tana tambayar su,

"Dan Allah Ina ake sayar da awara ko gurasa haka?"

"Awara? Gurasa? Acikin cafeteria dinnan?" Daya daga ciki ta amsa mata sauran suka fashe da daria.

Hakama sauran daliban baki daya da suka fara babbaka daria. Gashi dakin cin abincin amsawa yake idan ana magana. Daman wajen anyi tsit kowa yana sauraron su.

"Eh ba a sayarwar ne ko yaya? Tambaya ce fa kawai nayi sister" Layla ta sake cewa da su.. Nawraah nata Jan hannunta su bar wajen taki.

"Sis what? Ohh please... Sunana Imaan, Wannan sunanta inteesar waccen Kuma Nour..."

"Okay Allah sarki tohm Imaan Ina zamu samu kenan?"

"Well I dunno ... Sai dai ku tanbayi dalibai yan scholarship haka. Dan nan baa sayar da abubuwan da kike fada... "

Bata sake cewar wani abun ba. Tayi gaba sauran na biye da ita.. maaikatan wajen na biye dasu da trays din abincin da sukayi ordering..

Layla ta juya ta dubi Nawraah.

Jikin su a sanyeye suka futa daga cikin cafeteria din sauran daliban ciki suka fashe da dariaa

Suna futa suka hadu da imraan dauke da takardu na a4 a hannun sa. Da alamar aikin da suka bashi ya kammala.

"Ahh" ya fada yana kallon su

'mun sake haduwa..." Layla ta bashi amsa tana murmushi

Nawraah ma murmushin kawai tayi. Cikinta sai kugin yunwa yake.

"Akwai masu awara kuwa haka ko gurasa anan makarantar mun shiga nan cikin cafeteria dukkanin abincin da suke dashi yafu karfin mu"

Imran take yaji zuciyar sa ta sosu yatabbatar an guma musu wani abun takaicin acikin cafeteria din. Don haka ya dan sauke ajiyar zuciya kamar yana bayani da papers din dake hannun sa yace,
Chapter 3 · 0% Book details