← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 44

Sashe 2

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah sarki... Imran, Ni sunana Layla wannan cousin sister na ce sunanta Nawraah"

"Nawrah... Layla... Mashaa Allah sweet names" ya fada Yana murmushi dik kuwa da a tsorace yake maganar da yake musu.

Suma murmushin suka masa. Gaba yayi yana mai nuni da wani tankamemen gini me hawa uku yace,

"Nan library ne a first floor... Second floor hawa na biyu kenan shi Kuma gymnasium ne. Sai third ko ince last floor. Shi Kuma cafeteria ne. Amman cafeteria din bata kowa bace"

"Ban fahimci me kake nufi na?" Layla ta tambaye shi tana duban sa da kyau

Nawraah ma idanunta na kasa tana son jin Karin bayani daga gare shi.

Imran ya matsa kusa da su cikin muryar rada yace,

"Jami'ah ce ta yayan masu kudi. Yayan masu hannu da shuni. Duk Wanda kika gani a makatantar nan Wanda badan scholarship ba to ubansa wani ne ko Kuma dangin su sunada hali sosai. Don haka yayan masu kudin sune ke cin abinci a wannan caferia din. Shine Kuma suke amfani da gym din wajen motsa jiki kenan. Sannan sune masu amfani da library din"

"Come again. Bangane me kake nufi ba" Nawraah ta tambaye shi cikin gaskiyar ta

"Shine dai. Nima na kasa ganewa me kake nufi. Na dauka ai makaranta da abubuwan da ke cikin ta mallakar dalibai ce da maluman su da maaikatan dake karkashin su. Me kake nufi?"

Imran ya girgiiza Kai da sauri yana duba bayan sa a tsorace ce ji yake tamkar ana tahowa ta bayan sa. Layla ta dube shi tace,

"Wai wani abunne? Naga tin dazu kaketa dube dube lafiya kuwa? "

Imran ya girgiza musu kai yana ya yafito su da hannu sukayi gaba yace,

"Makaranta ce dake gudanar da karatun ta tsakanin masu hannu da shuni masu kudi kenan da Kuma masu karamin hali Irina kenan marasa gata."

Layla ta daga Kai tana duban sa tace,

"Na tabbata Kafi mu gata Imran. Amma dik da haka alhamdu Lillahi muna yiwa Allah godia a dukkanin halin da Mika tsinci kanmu..."

"Allah shine ahun godia" Nawraah ta fada tana kada Kai cikin tabbatarwa.

Imran yayi murmushi yace,

"To dika Allah ya bude mana ni da ku din. Don tabbas Dr Bintu tace akwai new students da zasu zo makarantar . Dama weekly ana daukar dalibai goma daga different departments zasuyi activities kala kala zaai grouping dinsu. To ni sai sunana ya fado akan Wanda zai nuna sabbin dalibai gurare na ciki da wajen makarantar . Sunana Imran Abbas kamar yadda na fada a baya. Iyaye na ba kowa bane fyace marasa karfi masu neman abunda zasuci yau da gobe. Na samu scholarship din makarantar nanne shekarun baya tun kan na gama secondary school. Jami'ar nan ta tà saka gasa Wanda yazo na daya zuwa na uku a makarantar sakandire tanan birnin, Amman mallakin gwamnati. Duk daliban da sukaci gasar ta lissafi wato mathematics. Zaa basu gurbin karatun a wannan jamia mai tarin iyalan masu kudi. Ai kuwa sai Allah ya nufa naci. Ni da sauran dalibai hudi da mukayi gasar tare.duk jami'ar tabamu gurbin karatu kyauta ba ko kwandar mu. Sauran dalibai yan ajinmu da mikaci gasar aka kawo mu nan makarantar tare. Dauki da dai sai dukkanin su su hudun suka dena zuwa saboda tsabar mugunta da nuna kyama da kyara da yaran masu kudin ke mana. Dik kuwa da badukan su bane. Amman kaso cassain duk suna lacking manners. Allahul Musta'an."

"SubhanAllah menene haka suke yi da har daliban da aka kawo na scholarship kyauta suka dai na zuwa?"

Nawraah ta samu kanta da fada masa wannan tambayar...

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

[4/25, 4:53 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_4_

:::::::::

Imran ya bude baki zai yi magana ke nan sai ga wasu yammata nan su uku sun taho ko wacce sanye cikin manyan kaya Wanda kallo daya zaka yiwa kayan jikin masu ka tabbatar masu tsada ne

Rike kowannen yakeda manyan manyan jakan ku na masu matukar tsada.

"Imraan...."
daya daya cikin yammatan da suka taho ta fada. Tana wani tafiya ahankali tamkar mai tsoron kasa.

"Naam.... Ga ni"

ya amsa da sauri ya rude layla da Nawraah suka hada idanu suna bun Imran da yammatan cike da kallon mamaki daya gauraye fuskokin su

"Ina assignments din? Ka mana kuwa?"

Cewar wata matashiyar budurwa daga gavan sauran tana mai mika masa hannunta alamar ya bata.

Imran ya saka hannunsa a keya yana shafawa muryar sa na rawa. Tamkar zai durkusa alamar ban roko yace,

"Dan Allah kuyi hakuri yau ne ranar aikin volunteer na."

Dogon tsaki taja tana karkada Kai tace,

"Me kake nufi? Baka yi ba ko Mai?"

Muryar sa na Mai cigaba da rawar da take yace,

"Zanyi zanyi idan na karasa"

"What? Me kake nufi eh? " ta Kai hannu zata doke shi kenan.

Wata budurwa itama sanye cikin tsadaddun kaya na masu kudi ta karasa wajen tana janye hannun ta tace,

"Calm down....Pele o... Imran" Ta karasa fada tana murmushi

Imran da gaban sa ke dukan uku uku yana harbawa da Sauri ya dubeta da wutsiyar idanunsa ya sauke da sauri yace,

"Kiyi hakuri b..."

"Ssshh ya isa haka Imran. Karka damu kaji?" Ta yi zaurin katse shi tana murmushi

Imran ya sake dagawa da Sauri ya dubeta yana matsa yatsun hannuwan sa yace,

"Dan Allah ni dai kuyi hakuri.musanman ke ma "

"Imran calm down please.kasan dai ba Wanda zan daka ni ko?trust me"

Ya girgiza Kai dasauri yace,

"Zanje nayi yanzu na kawo takardun ma"

"Imran haba mana.... Ah new students dinne wannan?" Ta fada tana duban su

Imran ya daga mata Kai alamar eh sune..Layla da Nawraah sude sun zuba musu ido suna duban su. Baki daya sun daure musu jiki sun kasa gane menene alakar su wadannan yammatan da Imran? Kuma kamar yana shakkar su sosai ganulin yadda jikinsa yake rawa tamkar mazari, Yana Kuma basu hakuri kamar zai musu sujjada. Kana dubansa Kuma kasan Yana cikin firgici Mai tsananin tashin hankali .

Yammatan suka karasa wajen su. Musanman wadda tazo daga haya din ta matsa daf dasu Nawraah tana duban su.

Ta saki wani tattausan murmushi tana gyara zaman jakar jikin Nawraah dake kafafarta tace,

"Sannun ku fa zuwa jamiar mu.... Ko zan san sunayen ku. Forgive my mistakes. Sunana Ilham ana Kirana da Lily wannan course mates na ne Kuma kawaye na ne na amana.... Iman, Inteesar and Nour... Sai Kuma senior na mu na gaba da mu a couch and mentor kenan... Imraan" ta karasa fada tana nuni da su daya bayan daya..

Layla ta kakaro murmushi tana duban ta tace,,

"Sunanta Nawraah, ni Kuma Layla"

"Wow lovely names....mashaa Allah"

"Mungode" Layla ta sake basu amsa.

Nawraah dai baki daya kwakwalwarta ta tafi yi mata nazari akan abunda Imran da yammatan nan suka tattuna akai. Gashi Kuma lily din tazo ta daga karshe ta sake boye lamarin Mai wuyar maanar ta. Amman dai dik da haka tabbas akwai wani boyayyen lamarin a tsakanin su.

"Ka karasa nuna musu koina Imran?"

"A'a da Saura. Amma mungama two third"

"Alright. Nawraah and Layla ku biyoni na nuna muku sauran"

Jan hannun Nawraah tayi tana sake duban kakarta tace,

"Jakan nan ya mun kyau"

"Nagode"

"Woah ko wani brand ne plus year din daya fito?" Wata acikin yammatan ta wullowa Nawraah tambaya..

Nawraah ta dubi lily tana girgiza Kai kawai

"Kaman yvsl... Kaman kuma givenchy"
Cewar daya daga cikin su..

Lily ta riko kafadar Nawraah tana Mai janyo hannun Layla sukayu gaba. Ta juya tana duban kawayen nata tace dasu,

"Karku cikawa kawayena kunne da tambayoyin ku. Mu hadu a cafeteria. Bara na zagaya dasu"

Kawayen suka kada mata Kai suka juya suna duban su kafin su mike su nufi cafeteria

Jikin Imran a sanyaye ya juya library da sauri don hada musu aikin da suka bashi. Wani bangare na zuciyar sa na Masa zugi da radadin abunda zai biyo baya. Ko akansa ko akan su Nawraah. ..

_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜
[4/25, 11:18 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_5_

:::::::::
Chapter 2 · 0% Book details